Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai baqo agida toda wuri ake karyawa dan kar a shiga hakkin bak'o sbd batasan koda wuri mutun yk karyawa ba kasan cewar su basa breakfast da wuri.



Zarah na shiga daki tasa kuka Ammice ta turo kofar tace a a ' a a kukan me kike kuma haba Zarah .


Zo nan ta zaunar da ita bakin bed tn share mt hawaye tace kinga ko mijin da zaki Aura ? Yarone mekyau" gashi da alamu beda son magana bare har yai hayaniya.





Zarah idonta na rufe tinanin Musayyet kawai Muryar Ammi taji tana cewa bude idonki kiga kalar mijin tin kafin ku hadu.



A hankali ta bude idonta Nan taga pic din Musayyet sanye cikin qananun kaya white shirt ce ajikinsa yn zaune cikin wasu korayen flowers ya dafe face d'in sa daya tsunsa """yayi matukara kyay ga wani arnen smile kwance akan face d'in sa .




Zarah ta bude idoda rawar baki ta kar6i pic d'in tace Ammi Ammi wannan ai dansanefa.



Ammi ta mik'etsaye tn kar6anr pic din tace eh ai ance d'an Abokinsane ze iya zama dansa .






Kinga kinsanfa no dawuri zamu wuce bari naje mufara shiri .


Fita Ammi tana kar6ar pic d'in tace bani dashi zan tafi wannan ai mijine na nunawa a dangi gashi me kudi ga quruciya ga kyau gashi qarewama banan zk zaunaba kai masha Allah "" fita tayi zarah ta bita da kallo tana dafe kai .






To kode Ammi tayi mistake ne wajen daukan pic d'in da aka bata?

Tayama zata aureshi hakan baze faruba .





Zarya tashigayi a dakin ta tsaya gabana mirror tn kallon kanta """ eh tayi kyau sede 'yar rama a wuyanta kadan.








Zama tai tana tinanin fa eza """ Yanzu ai suna tare da Musayyet shine wato ko gidan ma bezoba tsaki tayi nan take taji kishi cikin ranta wanda bata ta6a jin irin saba.













Wayarta ta dauka ta shiga kiran Musayyet akaro a farko hannunta har rawa yk wajen kira.














Yn office ya zabga tagumi yayinda mutane dank'am zaune suna jiransa .






Ringing yaji da sauri ya dauka gani sunan Wacce ke kiran.

⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š



πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

*AURAN* *BABBAN*

*MUTUM*


Crtn And Wrtn By

_UMMEE_ _MUKHTAR🎁_



πŸ…Ώ39




Seda yai murmushi snn ya d'auka yace hello momy """ sedata jingina jikin bango wanda aka lanyace shi da wallpaper ruwan milk se kyalli take""""
Ajiyar zuciya tayi tace ina fa eza?

Gira ya d'aga sama gamida aje biron dk hannunsa sannan yace fa eza kuma?

Zarah ta turo baki tace eh.



Tsaye ya mik'e yace tn gida mana bakwa tare ne ? nifa ina Cairo momy kokin manta.?



Kallon phone din tayi tace hakane amma jiya ai mun kaita gidanta .


Da gaske momy dan Allah bani aka aurawa itaba?

Shiru tai ms dan tana gani yama raina mt wayo ""wato an kai masa itane gidansa kafin yadawo.



Yace hello momy ina zuwa ina zuwa " d'if Musayyet ya kashe phone din ya shiga kiran Momy.



Da sallama ta dauka shiko gogan koma gaisheta beba cikin zumudi yace Momy ina fa eza?


Momy ta zauna kan carpet tace fa eza kuma tana hanya nan da lokaci kadan ka shirya ka tafi Airport tarbarta se anjima.


Kashe wayar tayi tabar Musayyet sororo yarasa maganar waze yarda da ita Zarah tace masa sun kaita gidanta.

Sannan Momy tace masa anjima zata taho wannan wane irin Abune sekace wata Aljana.


Aje wayar yayi ya zurawa waje ido yana ganin yanda mutane ke kai kawo kasancewar acen saman yake """"


Ta glass yake kallonsu yana sha'awar yana yin shigar matan k'asar n Alqahira sanye cikin dogwayen riguna shiga takamala.


Zarah yafara tinani tabbas idan tasa kayan nan zasuyi mata kyau.



Tsaki yayi ya zari key ya fito mutane se gaidashi suke sede ya daga musu hannu kawai ya wuce lifta ya hau ya sakko qasa driver yaja suka wuce gida.






A motane ya turawa Zarah tex ta whasap cewa ta turo masa pic dinta sbd yayi kewarsu dayawa.



Tn kwance tn danna waya ta shiga whasap nan taga tex dinsa """" murmushi tayi ta shiga tura masa masu kyau kuwa shima yn tura mata harda na ma aikatansa maza da mata wanda suke tare"""

Ta tambayeshi tace wannan wacece kusa dakai daga hannun dama?

Yai dariya yarubuta mata da cewa tn d'aya dg cikin ma aika tansune .


Ta ta6e baki ta turamasa da alamar jin haushi """ dariya ta bashi yai mata reply da sunanta zainab .
Tace kagafa baturiyace .


Yai smile yace a a kode balarabiya ai nan duk yankin Misrah ne .


Se yanzu ta tuna cewa hakanne fa duk yanki d'ayane .

Haka sukaita hira harta manta da cewa momy tace tai wanka ta shirya.
Shima har yaje gida cikin nishadi yk ko takan maganar momy be biba sukaita hira da Zarah.







Ammi ce ta shigo da 'yan uwanta cikin shirin tafiya tace au yanzu dama tin dana fita ba abunda kikai kina nan se faman danna waya kk.



Zarah ta aje wayar tasakko k'asa tace Ammi nima zan biku dan Allah.


Ammi dariya tayi tace bakiji abinda megidan yaceba ""cewar zakuzo nanda wata3 ki hkr mana ai kamar yaune.



Taso muje kimana rakiya Zarah tace dama ai zan rakaku .


Hijab tasa fari me santi dan karami suka fito babban palo.


Godiya Momy tai tai musu had'i da raba musu wata bag me d'auke da sunan Zarah da Nabeel.
Leshi ne dan ubansu aciki se a tamfa super turare da kuma envelop na rafar kudi kowanne 50k ne aciki.



Zarah kallon bag din kawai take tana jinjina sunan aranta Nabeel .



Har bakin motoci tarakasu tana kuka Momy na rungume da ita tn murmushi tace Zarah kenan meye kuma ma kukan yi shiru mana .

Malam hadi yai fara a yace kuruciya kenan se abarta kawai""" zata dena ne Hajiya mude mungode Allah yasaka da Alkhairi .



Alhaj Sa ed yace bakomai ai Zarah tamuce Allah yabar zumunci Allah kuma ya kaiku gida lfy




Ameen suka amsa gamida fita dg gidan suna daga musu hannu




Zarah ta share hawayenta Momy tace to saura ke 'yata muje ciki na shirya mk kayanki .

Hannu zarah taja Dady na rik'e da Khairat sukayo ciki .





Daki zarah ta shige yayinda momy ta nufi dakinta ta dakko mata wani magani .

Khairat dakinta ta wuce takama yin game

Da sauri momy ta dawo zatai hanyar dakin zarah dady yace a a kaga uwar amarya saurin me kime kuma?






Murmushi tayi tace wlh na manta da wani abune dg cikin kayan gyaran jikin zarah shine nk saurin kai mata.



Dady yai murmushi yace shi abun na meye
?





Momy tace base kajiba ta dan jima agidanka ai dole na gyara wa kanina ita.


Dady ya mike tsaye cikin wasa yace iyyyye to zonan bani abun.


Dariya tayi zata gudu yai saurn shan gabanta ya kwace sk zube kan kujera suna haki momy tace dan Allah kabani lokaci na kurekawa saura fa awa daya .


Dady yace Allah sekin gayamin kona meye zn baki.



Momy ta 6ata rai gamida juyae dakai tace tona matsine shikenan ?


Dariya yayi.harda kwantar da kansa kan cinyarta ya jawota momy ko ido taware tn kallon ikon Allah.



Dady seda yai me isarsa sannan ya tashi tsaye yace kadaki wahawalar da kanki domin wallahi iya zamana da Zarahban ta6a kusantar taba idan kuma baki yardaba ki tambayeta .


Momy itama ta mike tace dan Allah da gaske kake Abban khairat?



Ya kama kafadunta suka kalli juna yace Mulabi momy a dago da kanta dan tinda yafadi sunantsa na ai nahi tasan babu alamar wasa a maganar """ tace na am
Yai Ajiyar zuciya yace wallahi idan harkin yarda dani toki yarda bamu ta6a kwanciyar aure tsakanimmu ba sbd wasu dalilai.


Na farko de yarinyar ba waisona takeba ni kuma banso na takurata tinda ma fahinci yanayinta """.se kuma rashin samu wadataccen lokaci .

Ki yarda dani mulabi da gaske nk koki tambayeta.




Momy tasauke numfashi tace haba Alhaj wlh ma yarda kuma ngd maka garama da akai hakan kaga kanina namma wani babban tukwaicine agareshi.


Dady ya lakuce mt hanci yace oh sonkai k'irik'iri jama 'a.


Dariya sukai momy ta shiga daki dan hadawa zarah kayanta.






Sanye take da doguwar riga brown se mayafinta wanda tai rolling dashi sam batai makeup ba se powder da lipstick data sanya.



Hand bag ce kawai ahannunta bata dauki komaiba koda kuwa kayan sawane sbd momy tace mata karta dauki komai.


Bakin bed ta zauna su momy da dady suka shigo sanye cikin shiga ta alfarma se murmushi yake .



Khairat ta haye kan cinyar Zarah tace nima zan biki.



Zarah ta qaqaro smile tace nima zanso hk.


Kanta na qasa tace dan Allah kubani na tafi da ita banida kowa nawa acenidan ina ganinta nasan inada wani dan uwa najikina.





Momy ze tai magana Dady ya daga mt hannu yn murmushi yatsuguna yace Zarah karki damu kada kisan yawa ranki wn abu kinji acen nema kike da dan uwame sonki fiye da kowa ze baki kulawa, na tabbata bazaki rashi ba taso muje ko.






Zarah ta goge siririn hawayenta suka fito momy rike da trolly guda 2 kanana sbd idan taje cen ze siya mata kayan sawa irin nacen ,,,, a boot aka zubasu sk dauki hanyar filin jirgi.





A mota dady yabugawa Musayyet cewa yafa shirya gasunan suna filin jirji """kasande awowin dk tsakanin cairo da Nigeria so yakamata kakasance cikin shiri kada kabar 'yar mutane na jiranka """lalle yakasance akan idonka jirgin ze sauka sekasa ido akan masu fitowa dg jirgin kafahinta?







Seda yai cilli da hular dk kansa gamida yarfe hannu irin oh shrt din nan sanna yace to dady nagane seta zo dif kashe wayar""""Abun yaso yabaiwa Dady dariya amma yai shiru har sukazo airport.





Suna zuwa dama yarage saura 15mnts dan hk suka isa wajen screening .


Momy ta rungume zarag tana shar mata hawaye tace zonan .



Waje daya suka ke6e ta kalli zarah wacce jikinta ke rawa danbata ta6a zuwa filin jirgiba gashi ita kadai wai zt tafi.



Momy tace kalleni zarah .


Zarag ta dago kai da rinannun ido ta kalli momy """"".. momy tace ke yakamata na farayiwa Albishir cewa kokinsan mijin da aka aura mk?



Zarah ta girgiza kai Momy tai murmushi Tace to Musayyet ne kada ki dauka dan Alhaj ne a a kodaya k'aninane uwa daya uba daya"""""zarah ta zaro ido tana kallon momy baki na rawa tace momy da gaske kike kuwa taya haka zata faru dani ? Ni ni nifa duk kun rikitani kuka tasomayi momy tace a a banaso karki fara kin""""" kafin taqarasa aka shiga sanarwa nan aka fara shiga jirji momy ta share mt hawaye tace ki hkr minyine dan farin cikinku zarah dakun sauka idan kunje gida ki kirawoni awaya kinji////



Zarah ta daga kai tana daukan trolley dinta taje gun dady tai suka dada yin sallama ta rungume khairat sannan ta wuce sk bita da kallo cikin farin ciki da jin dadi.






Kahirat tace momyn yaya ki gaida yayana shima yanacen Cairo kice injini idan ze dawo yatahomin da dadyn k'asar tafad'a tana juya k'ugu.



Fara a zarah tayi tana goge hawayenta tace zan fada masa nima zan taho mk da tawa kinji I love you


.


Daga nan ta shiga seda aka tabbatar komai tai nomal na matafiya sannan aka daga hannu alamar anbashi damar tashi.






Nan jirgi yafara tashi sama Zarah ta runtse ido kirjinta ma bugawa tana tina maganar momy kinsan wanda kika aura kuwa?


To musayyet ne to musayyet ne . Haka kalamar taita amo a kunnenta da kwakwarwar kanta




Tasa hannu ta dafe kai tace wannan wane irin wasane kuma ? Taya zasuyimin wasa da avunda nafi kauna araina .




Ina ftn hakan yakasance gaskiya .


Alokacinne jirgi yai sama sosai baka hango abunda ke k'asa .







Musayyet suna gama waya da dady ya kashe wayar bak9 dayanta yai wanka yace bawanitarota da zani koda zani se dare wlh seta bushe agun """ wajen hutawa zani se dare zan dawo wlh. tafara ganin iskanci kenan tinkafin tazo tinda har ynz banji momy tamin maganaba kan sharrin da fa eza tai min.





Kenan yaudarata tayi datace zata fad'a.


Wanka yayi yaci abinci sanye da kananun kaya ya fice warsa dg gidan

















Ummulolo na gaidaku _*πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜*_


⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*

*MUTUM*

Crtng And Wrtn By

_UMMEE_ _MUKHTAR🎁_





πŸ…Ώ40





Omar kejan k'afar fa eza cikin wani salo na so da k'auna amma tak'i tashi """ tin wajen k'arfe 5am ya farka yai wanka a gida yai sallah beje masallaci ba ya koma bacci """


se wajen 6 yafara tashinta amma sam tak'i tashi sema wani k'ara shigewa bargo tk abinta



Murmushi yayi ya bar dakin kai tsaye kichen ya nufa yafara fere potatoes""


Bayan yagamane ya gyarashi ya soya ya had'a tea y zuba a flask " waina ya soya ya kai kan dining ya aje ""

Daukan ledojin jiya da daddare yai ya bud'e kajin ya zuba a Oven yai steaming ya juyesu a plate ya dawo palo """ juice ya hada dashi kwali 2 duk ya aje ya koma daki.



Yana zuwa yaganta zaune ta zuba tagumi kanta na qasa .


Da alamu kuka take ma """yazo har gabanta ya tsuguna ya kama hannunta suka hada ido, shima cikin fuska taban tausayi yafara magana.






Dan Allah kiyi hkr my sweet kinsan Aure nufine na Allah """ nasan nai mk ba dede ba daban furta miki cewa inasonki baki da baki ba""""..Sena Abba na da zancen shi kuma yaiwa mahaifanki magana dg ciki harda Abban Nabeel.


Hawaye ya zuba a fuskarta dan ya Tina mata sunan datake fad'awa Musayyet lokaci datake yarinya bata iya fad'ar sunan sede tace masa Abeel.



Tsaye ta mik'e sede jiri daya kwasheta umar yai saurin rungumota yn mata sannu.


Toilet ya kaita yai mata wanka tayi shiru harya gama mata yace taina tsarki.


Fita yayi ya barta ya dawo daki ya zauna gamida tagumi.



Har wajen minti 20 bata motsa ba umar ya k'ara lekowa yaganta zaune cikin bahon wanka hawaye kawai take .



Jikinsa yai sanyi ze magana ta daga ms hannu alamun bataso yatafi kawai .


Ba musu ya dawo daki ya k'ara yazama jiyai kansa na masa ciwo.



Sedata k'ara minti 10 snn tai wankan tsarki ta fito .


Da sauri yatare ta ya koma toilet ya dakko tawol yn goge mata jiki wanda ita ta manta bata gogeba .



Kai tsaye doguwar riga mara nawi ya dauko mata da brezia pant da siket se hijab duk ya aje mata yace tasa idan tayi sallah yn palo yn jiranta.


Kai ta daga ms kawai ya bita da kallo ya fita yn girgiza kai cike da nishadi.
...
.



Bayan ta idan gurin zama ta nema ta dakko wayarta ta shiga neman layin Musayyet amma wayar akashe.




Umar jin shiru yasa shi dawo wa zaune yaganta hannu yakamata ya mikar da ita sukayo palo.



Kan dinin sk zauna Abun yabata mamaki ganin yadda ya shirya mata komai.


Umar ya shiga hada mata kayan breakfast wanda zuwa ynz rana tayi sosai.



Cikin murya me laushi tace waya hada wannan?

Da fara a a fuskarsa yace nine """ Murmushi tayi seyaji tace masa sannu.



Dadi yaji aransa yashiga yin fara a har cikin ransa yakejn sonta na shiga zuciyarsa.

Fa eza hk kurun taji yabata tausayi amma data tino da abunda yai mata setaji haushinsa takeji.


Bayan sun gamaci ta dawo kan chair ta zauna shima ya biyota yana danna mata kafafunta da alama tausa yake mata.

Tureshi tayi tace haba meye hk kabarni na sarara mana se bina kake kamar wata jela.


Umar tai smile yace ai ni nafi jelar ma agunki yakamata ki damu da wanda ya damu dk .


Ta kalle shi cik da tsiwa tace to bazan damun ba ai ba ninace kasoni ba"""" son maso wani kawai kakeyi yakamata kai nesa agunda ba a damu da kaiba kagane ai.



Umar na kallonta face dinsa cike da smile kallo ya kunna time by time yn satar kallonta.


Wayarta ta dauka taci gaba da kiran Musayyet amma akashe """ tsaki tayi ta cillar da wayar .

Umar yace Momy zaki bugawa ?

Ta wurga mai harara tace Musayyet nake nema ba Momy ba.


Seda umar yaji ba dadi fuskarsa ta sauya amma ya danne ya kakaro smile yace may be yn gun aiki ne .



Koma yn ina me yai ruwanka dashi cewar fa eza.


Umar bece komaiba ya tashi ya shiga debe kayan da sukai breakfast ya maida kitchen ya zuba omo a wata roba k'arama yafara wanke wanke.




Fa eza jitai kamar k'arar plate dan hk ta salalla6a ta lekashi"" wanke wanke taga yanayi kuma yana dafe kai dk masa ciwo.



Wata uwar dariya tayi tace ai dama da wanke wanken kai kama wallahi kuma abunda kaimin jiya kaci Allah ya isa tana fada tai hanyar umar ya bita da kallo yn murmushi lalle fa eza bayan kuruciya kamar abun nata da isknaci aciki""" dariya yai yaci gaba da aikinsa yn tina abun da tace masa wai yace Allah ya isa "" shida Hakkinsa.





*ZARAH*



A jirgi kuwa Zarah idonta rufe maganar Momy ketai mata yawi arai wai Musayyet ne mijinta wani murmushi tayi cikin ranta tace kuci gaba da wasa da hankalina """Amma ninasan bata yanda hakan zata faru koma waye mijin haka zan kar6eshi babu yanda zanyi kowa da k'addararsa.




Wayarta ta dakko ta shiga kallon pic din Musayyet tn murmushi """ wayar tasata a flightmood ne"" jitai ance mata Assalamu Γ€laiki "" Zarah ta juyo dan gani wake mata magana.


Wata mata tagani sanye cikin doguwar riga baqa sanye da niqaf a face dinta.



Zarah ta amsa mata cike da kulawa " ga mamakinta setaga matar ta mik'a mata hannu Alamar su k'ara gaisawa.


Zarah ta mika mata """" Matar tace sunana Aisha kema Egypt d'in zaki?


Zarah tai mamaki sosai jin matar tayi hausa domin duk jama ar dake jirgin farar fatane""" Zarah tace a a ni Cairo zani.


Matar tai murmushi tace ai duk country d'ayane turawane suka sanya mata sunan egypt "" zaki iya kiranta da Misrah ko Alqahira koma cairon sede yanki da suka banbanta da juna.




Zarah jitai kamar ta nutse dan kunya tai murmushi ""

Aisha tace da alamu ke bakuwace ko?



Eh zuwana na farko kenan zarah ta fada tana k'ara kallon matar """ da alamu kamae yarinyace irinta amma sbd tasa niqaf bazaka ganeba.




Aisha tace nima naje gidane kasancewar mijina beda lokaci sosai hakan yasa natafi ni kadai.


Zarah tace Allah sarki .



Karatu kike son yine anan ? Matar ta tambayeta """" .Zarah gumi ya karyo mata itako mezata cewa mata nan ? Taya zata gaya mata cewar ita seta sauka ma ΕΊata san inda ta nufa.




Zarah tai ajiyar zuciya tace a a gun yayana nazo.



Aisha tace Ayya shidin anan yake da zama?


Zarah da sauri tace eh.



Robar ruwa me sanyi ta mikawa zarah guda daya ta amsa tace ngd .


Seda Aisha tasha ruwan sannan ta cir niqaf din dk face dinta.



Asheko yarinyar ce Zarah ta fada cikin ranta.


Aisha yarinyace dabazata wuce 21 ba .




Ta kalli zarah tace kinga ni anan nake aure .


Shekarun baya nazo karatu nan ne na science tin ina 18yrs.

Allah da ikonsa yahadamu soyaiya da wani me suna Muhammad Al Khaiyam Balarabe ne kuma matashi kyakykyawa. bbban doctor ne sosai wanda k'asar keji dashi .

Yanada hospital nasa nakansa wajen guda 5 babban cikinsu shine Al NASREE Special Hospital.


Se gidan cin Abinci na ALJUMERAH BUFFET Resturant ,, DA kuma RUSTIKA Restaurant.

Lokacin yanada mata me suna Zainab itama balarabiyace se Allah yai mata rasuwa , yaji mutuwar matarsa sosai aransa duk da itama yarinya ce karama dan har na girmeta kasancewar sun mata auran wuri kuma auran dangine.







Bayan shekara daya yace ze aureni nace nida nk karatu kuma ba jinsin mu dayaba danginsa bazasu bari ya aureniba kamar yanda nima banida tabbacin nawa zasu yarda na aureshi.



Hakade taitamin maganar ina sharewa duk da inasonsa kinsan larabawa da kyau.



Zarah tai murmushi tace ynz kenan bakwa tare?
Aisha tace a a """ ganin naki yarda dashi wata rana ina class kawai yazomin da iyayensa " nai mamaki araina sukace su duk abunda Muhammad keso suma suna sonsa bare Addinimmu daya ma.





Ganin sun yarda yasa naiwa iyayena magana abu kamar wasa har suka yarda ""musamman sukaje nigeria sk nemi aurena aka basu bayan binciken da sukai me zurfi suka gano shidin fitaccene a kasar dama wajenta.


Dangin Abbana sosai sk nuna hassadarsu da k'in aurena dashi tin da dama cen basa son ummana hakama kishiyar babana taita zuga babana akan karya yarda """" seda kakana yasa baki wato wanda ya haifi Abba na .


Mutalakawa ne dama gobnatin jaharce ta dauki nawin karatuna .





Yanzu haka munyi aure dashi yana bani kulawa sosai munason juna bayason 6acin raina ko kadan.



Γ€bbana ya mutu sanadiyyar accident da yayi ganin koda yaushe ina tinanin ummana yasa mijna dakko ta ta dawo nan baki daya ya siyamata gidanta daban kuma akai mata katin shedar zama 'yar k'asa.


Naji dadi sosai araina ynz hk koda yaushe idan naso ganin ta hk zanje koda kuwa zanyi zuwa 5 a rana mijina bashida damuwa ""yn kula da ita kamar ita ta haifeshi Yanzu bari kiga musauka kannensa na nan najirana sbd munyi sabo dasu sosai.












Zarah tai ajiyar zuciya tace ikon Allah gaskiya kinada sa a Aisha
Ni sunana Zarah kuma inada Aminiya m sunan ki """"" Aisha tai murmushi tace zaki k'awance dani?



Zarah tace meze hana inai miki fatan zama me dorewa da miinki tare da samun kwanciyar hankali me dorewa a rayuwa.



Aisha a rungume zarah tace idan kinyarda zan maye miki gurmin Aishan nigeria.


Zarah tai dariya tace na yarda nan sukai dariya yayinsa jama ar jirgin ke kallonsu da rashin sanin mesuke cewa kasan cewar bajin yaren hausa sukeba dan Aisha da Zarah ne kadai hausawa a cikin jirgin.





Musayen Number sukai wanda atime dinne aka shiga sanarwa jirgi ze sauka .




Babban filin jirgin Le meridein Cairo Airpot cike yake da mutane farar fata da bak-ak'e kadan wanda sukazo

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment