Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasan Auran Abbanka ya kusa """" seda yai jim sannan yace to momy insha Allah jibi ina hanyar dawo wa kitana di kayan dad'i dariya tayi tace bazan ba inkayi zuciya kai aure.




Murmushi yayi yace inna dawo akwai labari .


tace da gaske ?


Yace Allah momy daga haka seda suka dauki tsawon awa daya suna hira daga k'arshe sukai sallama.








Kwanciya yayi yana murmushi yana tina hirar da sukai da yarinyar dabe santaba gashi tana nema tazauna a zuciyarsa.






kalma d'ata tak ya tuno da take cewa kaima kasan BABBAN MUTUN zaura shine ka bugo kamin rashin mutunci.




Tsam ya mik'e tsaye yana zagaye tafkeken d'akin zuciyarsa na masa wani iri wandabe san komeye ba.






kubiyoni dan jin yazatakasance tsakanin MUSAYYIT DA ZARAH



Shin musayyit kode d'an Alhaj sa'id ne?


ummulo ce taku har kullunπŸ€—πŸ€—πŸ˜˜
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*
*MUTUM*

Creating And Written by

*Ummee* *Mukhtar*

*HIKIMA* *WRTS* *ASOO*🎁



πŸ…Ώ 4


A subar fari mutan gidan suka tashi dan gabatar da sallar Asbah bayan sunyi ne wasu daga ciki suka koma bacci " yayin da wasu suka zauna zaman hira .




Zarah da Aysha tin 4:30 suka tashi suka zauna suna hira bayan sunyi sallar Asbah ne suka koma bacci.



Misalin 7:00 kiran a wayar Zarah ya fara ruri yayinda suketa bacci abunsu.



Aysha ce ta farka ta d'aka mata duka tace tashi inaga Angon ne ke kirah """ Mik'a Zarah tayi ha'd'i da salati tana mutsitstsika ido tace yanzu akan wannan kike tashi na ?


Wama ya fad'a miki yanada lokaci na mutum kullun a tafiye tafiye daga wannan k'asa zuwa wannan k'asa " kai ta mayar ta kwata gamida yara pillow tana cuno baki.



Haka wayar ta gama ruri " Aysha na shirin kwanciya ta kuma jin wani kiran ya shigo tashi aysha tayi ta jawo phone d'in setaga number amma ba suna d'agawa tai gamida sallama .


Kwance yake a d'aya daga cikin sofa d'in dake palourn hannunsa rik'e da cup na green tea yana sha kad'an kad'an aje cup d'in yayi yace mrng funny gal how are u anda how was ur lst 9t? Aysha k'unshe bak'i tayi tanaso tai dariya cire phone d'in tayi tana k'ara duban wayar """ am sorry barina tashe ta bacci take me wayar .




Tsaye ya mik'e yace no karki tashe ta batta tai baccinta amma pls idan ta tashi ko plashing ne kimin kinji dan Allah.


Da sauri tace to to .


Kashe phone din yayi ya kama had'a mahimman kayaiya kinsa domin yau yakeson tafiyama tinda yariga daya kammala komai daya kawo shi.






Mamaki aysha take waye to wannan kode kabeer ne wanda ya tafi da har yanzu bedawo ba?


Tace kai bashi bane wannan muryar sa kamar ma ta larabawa ba haka voice d'in kaber takeba.



Kwanciya tayi abunta gamida aje wayar akan table.



Ta kwas dede suka farka a time d'inne suka fito dan kar6ar breakfast.


Kitchen suka nufa da kansu suka hada komai suka koma d'aki.



Bayan sun karya wanka sukai suka fice yayin da Zarah ta d'auki jakarta wacce take d'auke da kud'i.


Aysha tace muje mugaisa dasu mana kafin mu fita "Zarah cewa tai ita ba inda zata kawai tataho su tafi.



Kai tsaye gidansu aysha sukaje umma suka samu tsakar gida se a lokacin take dama koko.





Har k'asa suka gaidata ta amsa cike da fara 'a tace a a kune da wuri hk?



Eh umma zami dilkane shiyasa kuma zamuje gyaran gashi.


Oh ai gara kuje da wuri ai tinda gobe ne d'aurin Aure .nan da nan idon Zarah ya cika da k'wallah aysha nakallonta dan hk taja hannunta sukai ciki.



Haba Zarah dan Allah kidena sa damuwa bakisan abinda Allah yk nufi da Auran nan ba amma duk kinbi kim damu "nasani da ciwo ba dad'i domin ba kalar mijin da kike mafarkin samu zaki aura ba amma kisani cewa komai muk'addari ne ke kuma hk taki tazo miki pls kisawa ranki ruwan sanyi.



Se sannan k'wallah ta zubo mata tace bakomai ya wuce na dena k'awata.




Dake basa rabo da kayan gyran jiki a a jiye nan da nan ska had'a komai suka koma wani d'akin na daban suka fara.






Seda sukaci abincin rana sukai wanka sanna sukai shirin tafiya saloon.



Umma na zaune tana jin 'yar redion ta zarah ta tsuguna gabanta tace gashi umma .



Da murmushi umma tace meye wannan d'in kuma?



Jakar ta zuge nan taga kud'i fal ta rufe baki tace ke ina kika samo wannan?


'Yar dariya zarah tayi tace umma karkice komai dan Allah na kine kena bawa kΔ±yi duk abinda kikeso dasu dama kin dad'e umma kina neman jari to gashi Allah ya kawo miki kema kici k'udinki.



Kallonta umma tayi aysha na tsaye se murmushi take kawai" umma cikin rawar baki da sanyin murya tace kamar ya naci kudina zarah
?



Eh umma ai kud'immu ne suke hawa kai suyi d'are d'are akai sbd haka dan Allah karma kifad'awa umma na dan bata sani ba wannan daga cikinirin kudin dayake banine.




Kuka umma tasa sosai ta rungume zarah tace Allah yai miki Albarka Allah yabaki abinda kikeso ngd ngd zarah """ kuka take sosai zarah ta goge kwallar data tarar mata tace umma zamu tafi se gobe zamu dawo cikin sauri umma tace to to zarah nima inason naje yanzu zan tashi to kawai sukacs suka fice.


Nan suka bar umma se kukan dad'i take domin ko 50k bata ta6a rikewa ba.

Suna fita aysha tai taiwa zarah godiya.

Kai tsaye berud road sukaje aysah tase waya babba HTC ta siya tase sabon sim na glo .

Umma shiryawa tai taje gidansu zarah amma ba wata tarbar kirki da larai tai mata dama ta zone ko akwai aikin daza ayi.


Wajen saloon sukaje wanda se karfe shida suka bar gun suka wuce gida.

Tj multi pps sukaje kaya tasewa aysha na musamman d'in kakku masu tsadar gaske.

A gajiye suka dawo nan suka tarar da mutane sunfi na jiya domin wasu sunzo daga cen garin ummanta """" fuska tamke zarah take gai da kowa yayinda aysha fuskarta ke sake se tsokanarta suke amarya kinsha kamshi.


Wani haushi ne ke kamata mustu mutsu kawai take da mouth d'inta wanda da alamu so take tai magana .


Larai ce ta watsa mata uwar harara hannun aysah taja sukai ciki.



Suna zuwa suka taradda abinci an aje musu.



Kaya suka cire yayinda zarah ta dakko musu marasa nawi daga ciki kayanta .



Abincin sukaci kad'an saboda har yanzu akoshe suke.



Larai ce ta shigo ita a baba maryam hannunsu rike da wasu flaks har biyu .



Da murmushi larai tace amma fa kinyi kyau wane gum gyaran jikin kikaje dan na san anja kud'i da yawa gashi daga farawa tsakanin jiya da yau har kin kara fresh dake.

Da sauri zarah tace um cen beautiful bride mukaje .



Ah koda naji ai dama sun iya sa fatar amarya kyau da shek'i " toga wannan kicinye duka kinajina ko?


Eh umma kawai tace baba maryam tace wannan zaki faraci shine na kaza wannan kuma na auran shila ne ki daure ki cinye za a akawo miki sauran na shane seki shanye abune anyi shi a k'urace .



Kallon juna sukai zarah da aysha.

Fita su larai sukai sukaja musu k'ofa.


Wallahi bazan ciba se kace wani saurayi zan aura cewar zarah"""" ' yar dariya aysha tayi tace ki daurw kici kinga nasan musamman aka yishi sbd ke .





Zarah tace sede muci tare "zare ido aysha tayi tace rufamin asiri wace ni .



Leda zarah ta samu ta juye komai a ciki na abinda aka kawo mata tasa hijab ta fita .



Ina zaki kuma cewar aysha ke k'yaleni kede kisa ido .


Da sand'a ta fita ta zaga ta baya ta wulla akwandon shara.

Dariya ta shigo tanayi ta cire hijab tace nasa a shara """".baki aysha ta bud'e tace shame? Zarah tace shara ai kinjini .

Dariya aysha tayi tace to Allah ya kyauta.



Yanzu idan akagani fa? Cewar aysha, zarah tace Bama wanda zegani .


Au na manta wlh d'azu da safe wani ya kira wallai bakiji muryar sa ba kamar arab gaskiya ko ban ganshi ba duk inda yake nasan ya had'u.




Zarah d'aga kai tayi sama alamar tinani cen tace oh jiya ma kira wai momh yake nema niko nace masa wannan baby ce.
Kawai ina bacci na nake gayamiki mutumin nan ya kira ni wai wani dawa nake magana.

Ya ban haushi wlh.




Aysha tace kinsamme wlh duk yadda akai sonki ma yake cewa yaifa kina ina nace bacci kike amma yace waina kyaleki kisha baccinki karna tasheki idan kin farka nakirashi ni kuma sam na manta.





Zarah tace uhmmm kyale shi irin masu had'an number nanne idan sunyi sa'a sunsamu mace shi kenanse suce suna sonta.



aysha kayya banajin wannan irinsu ne gaskiya .


Hmmm zarah tace kawai zata mik'e kenan kiran wayar Alhaj sa'id ya shigo tana gani ta Kashe phone d'in gaa d'aya tasa ajakarta.




Aysha batace komai ba tana shan juice sede murmushi kawai datake kawai.




Seda sukai sallah sukai shirin kwanciya idonsj biyu amma hira suke aysha tace shikenan fa dg gobe angama .

Uhmm kawai zarah tace ina jiyewa bawan Allan nan rashin mutuncin da zan shuka masa wallahi da kansa seya sakeni se yayi dana sanin aurena .




Ah karki haka kawata in kikai hk kenan baki dauki shawarata ba kenan idan kikai haka baki kyauta ba.

Hakuri shine maganain komai fa .



Juya kai zarah tayi hawaye na bin kuncinta gamida rufe ido.






Musayyit zaune a cikin jirgi ji yake zuciyarsa na masa ba dad'i meyasa har yanzu yake jin wani abu a zuciyarsa gameda wannan yarinyar amma koma menene daya sauka ze nemi inda take murmushi yayi ya maida glass d'in dake face d'insa ya shafi sajensa wanda ya kwanta a kyakyawar fuskarsa.



Wata baturiya ce ke yawo tana raba irin abincinsu wanda ya k'awatu da ganyaiyaki kala kala " nan tazo dede gun musayyit ta aje masa a k'aramin table amma yaceta d'auke ya k'oshi.







Farin cikine kawai a ransa wanda besan dalili ba lokaci lokaci yana tina fuuny gal d'insa.


UmmuloπŸ˜˜πŸ€—
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€



*AURAN* **BABBAN*MUTUM*




Creating and Writting
By
UMMEE MUKHTAR🎁



πŸ…Ώ5





ABUJA


Wani katafaran gida wanda komai k'urin lakka bazaka iya gano ina ne k'arshen gidan ba saboda tsabar nisan gidan , koda ka shiga haka zakaita wuce wurare tamkar ka shiga wata unguwa me nisan gaske.


Gidan gaba d'aya zagaye yake da ma aikata wanda suka had'a da security's and bodyguards, sojoji masu uniform da marassa uniform.



Wani bangare dg cikin gidan na hango wanda da alama anan mamallakin gidan matarsa take.


A time din karfe 10am""" palour agidan da d'akuna kamar kamar zasuyi magana sabod yawansu.

Ko wane palour adonsa da banne ko ina akwai kayan kallo firij dining area A.C. da sauransu.


Kowane daki akwai gado toilet 3chairs karamin center na glass kayan make up da sauransu yanayin gidan kai ka rasntse a hotel kake saboda yawan gurare wanda duk inda ka kalla se sun tafiyar da hankalinka sbd kyau da tsaruwa.


Ga mata nan masu aiki kowacce da uniform white shirt and red jeans.


Fulawo yi ko ba a magana gasunan se rangaji suke suna fitarda kamshi.


Wasu manyan maza nagani kaida ganinsu kasan sunci suntada kai duba ga yanayinsu da kuma kayan Alfarmar dake jikinsu.


Wani mutun na hango fari ne sosai sanye yk da farar shadda wacce kudinta idan aka fada zakai matukar mamaki agogon dk hannunsa ma kaida gani kasan yaja kudi.


Yanada kyau sosai kamar kata6ashi jini a fito sede kana kallonsa zaka gano shekarunsa duba da yanda furfura ta fara futo masa kadan kadan.


Hira suke cikn harshen turanci wanda a time din suke shirin tafiya daurin aure"""


Wata mata nagani dauke da turare a a hannunta se fara 'a take da alama itace matar gidan " tana zuwa ta fesawa Alhaj sa'id ,"" Abokan nasa kuwa dariya sukai ciki tsokana suke cewa ah lalle kin cancaci kyauta madallah da matar Arziki irinki ' dan murmushi tayi ta gaidasu yayinda Alhaj sa id wata kunya takamashi domin yana matukar ganin darajarta domin tayi masa halacci arayuwa.


Kudi suka hau aje mata dami dami tin tana godiya har tai shiru se murmushi kawai tk.



Fita sukai dukkaninsu Alhaj Sa'id ya sumbaceta gamida shafar fiskarta yace semun dawo ko.


Kai kawai ta d'aga masa harya fice yayinda hawaye kebin fuskarta.





Da sauri ta share fuskarta ta koma inda 'yan uwanta suke wanda sukazo jiya domin biki.



Suna fita motacine masu yawan gaske ko wacce da driver nan suka shiga se filin jirgi.



Zarah zarah wai dan ubanki har yanzu me kikeyine a d'aki daurin auran nan kinsan fa shad'aya da rabine shine bazaki fito ki gyara jikinki kiyi kwalliya ba?. Cewar Larai.


Ah k'ila gyarawa suke kinsan kwalliyar yaran nan ta zamani bare su zainab da hafsat ga sunan duk sunzo d'azun zasu gyarane """" baba maryam ce ke maganar.

Am wai yanaga ba a d'ora komai ba ne ko tukwane banga an d'oraba ?



Larai tai murmushi tace ai order na bada kinsan yanzu in kanadashi base kasha wahalar komai ba ai tun bikin saura sati d'aya na bada kud'i ayo sede kawai kiga an kawo nan da anjima zakigan su ' kawo da ranama zasu kawo wani.


Eh lalle shiyasa naga wlh banga tukunya ba to kinga ai muma hutummune " Ah to cewar wata dake shirin shiga toilet wanka.








Zarah na kwance a d'aki se kuka take jikinta ya d'auki zafi aysha se lallashinta takeyi akan tai shiru amma tak'i


Sauran 'yam matanne wanda zasu kai su biyar wanda duk 'ya'yan 'yan uwane domin zarah ba wanda ta gayyata suma hakurin suke bata amma kamar tirata suke.




Shigowar Larai kawai suka gani hannunta d'auke da wayar caja se huci take """ Zarah na ganin ta ta mik'e tana jan k'afarta zuwa jikin bango.


Larai tace wuce muje muje nace ko"""" zarah kuka take sosai tana cewa ammi dan Allah kiyi hkr """" mari Larai ta d'aukr zarah dashi wanda seda aysha taji kamar ita aka mara ta rintse idonu .




Jan hannuta tayi ta cillata toilet d'in dake d'akin tace ai ba wanka kika wuce nai miki ba so kike kitsinkan mutunci kuma wallahi baki isaba .





Aysha cikin tsoro tace Ammi kiyi hakuri zatayi """ kallon banza Larai tayiwa aysha tace ke rufemun baki 'yar karere nayi magana dake ? Waya samma koke kike hure mata kunne saboda kinga zatashiga daula "irinku nada yawa adoran k'asa na sani kawai fitowane da bazaki ki nuna ba se zagon k'asa zaki fara wankan ke kuma kose na danno k'ofar nan .





Zarah tafi jin bak'in cikin kalaman da Larai ta fad'awa aminiyarta me lallashinta kuma mebkaunarta Akan wankan da akasata setayi.




Aysha kanta na k'asa tana wasa ta farcenta yayinda ta hadiyi yawu na takaici.




Larai kanta tsaye ta shiga tafara wanke zarah sosai itako se kuka take abinta .



Sauran yan matan suma basujj dadiba duk fita sukai farfajiyar gidan suka zauna.




Wanka suma suka yi yayinda suka shiga fesa kwalliya.


K'ofar gidansu zarah cike yake da 'yan d'aurin aure kowa ka gani cikin farin ciki domin kowa ma murnar zeyi tozali da matemakin shugaban k'asa.


Malam Hadi anci shadda gezna fara kana kallonsa kasan a farin ciki yake,



Jiniya suka faraji yayinda kallo ya koma kan hanyar wacce da sassafe mlm hadi yasa aka share layin kaf dinsa aka kafa runfuna.

Nan Manyan k'usoshin gobnati suka fara fitowa kama daka kan ministoci 'yan majilasu govnoni da kuma manyan ma'aikata.


Malam hadi da sauri ya nufesu se washe baki yake yana cewa sannunku da zuwa mutane nan aka shiga hotuna unguwar gaba d'aya tacika da jiniya sojoji rik'e da bindugu kamar za a fita yak'i.



Alhaj Sa'id da murmushi yabawa ml hadj hannu sukai mufabaha hannun mlm hadi se rawa yake dan murna da zumud'i.





Nan suka zazzauna a inda aka tanada don d'aura auran .wayarsa ya ciro wacce se walwali take yaiwa zarah tex kamar hk.


My baby ina ftn kina lfy yau Allah ze cika mana burimmu
I love you .



Nan ya kashe phone din gaba daya aka shiga daurin aure mutane se hotuna suke.





Zarah na zaune fuskarta tai ja daure da tawul ajikinta iya cinya se kuka take k'asa k'asa Larai ce dasauran 'yn uwanta se lallashinta suke akan ta daure tai kwalliya me kyau aysha na gefenta tace wa Larai Ammi zami mata yanzu .


Larai kallan aysha tayi tadanyi fara'ah dake tasan zata gyara mata 'yarta tace to ku daure ayimata da wuri gasucen sunzo.




Fita sukai sy larai aysha ta rufo kofa tazo suka fara gyara zarah Abun mamaki gani sukai kawai ta tsaya ta dena kukan se ajiyar zuciya datake yi.




Daga waje sukaji ance an daura auran Auran Alhaj Sa'id wati vise president da Zarah Habib Akan sadaki naira million 10 .nan aka d'auki tafi yayinda wasu ke mamakin adadin sadakinta .


Malam hadi kamar ya suma dan dadi jiyake kamar yafi kowa sa'ar haihuwa.




Zarah najin haka ta rik'e kanta wanda ke juyawa ta runtse idonta se kuka kwanciya tayi tana burgimase shure shurw take su Aysha da hafsat na rik'eta.




Larai kuwa wata uwar gud'a ta rangad'a ita da matan gidan se barka suke wa juna sunfita zakkah a dangi.





12 dede MUSAYYIT ya sauka a Airport fuskarsa dauke da fara'a nan naga mutane sun baibayeshi suna masa barka da zuwa yana amsawa cike da kulawa yana raba musu kudi""" hak yake aduk sanda yai tafiya ya dawo dake sun saba da ma aikatan haka zeta basu kudi kamar banza.




Wani ne yace yalla6ai zamu kaika ne ko kuwa kayi waya gidane ? Musayyit ya cire farin glass din dk face dinsa yace no kaini kawai zakuyi inaso naiwa momy na surprise ne.

Murmushi sukai dukkan ninsu sukace girman kane yalla6ai.


Phone dinsa ya ciro kai tsaye layin Zarah ya fara kira wacce yai mata saving da funny gal Amma a kashe so 5 yana bugawa amma shiru.


Suit d'insa ta saman naga ya cire yana furzar da iska alamar beji dad'in hakan ba. Yaso ya fara jin muryarta domin itace a zuciyarsa amma hakan be yuwuba.




Wayar Dad ya buga itama akashe kallonsa yai yace we can go """ nan wata mota ta parka me d'an banzan kyau suka d'auki hanyar gida.








Ummulo ce taku inasonku masoya wannan novelπŸ˜˜πŸ‘„πŸ’žπŸ‘πŸ»
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*
*MUTUN*


Creating and written
By

UMMEE MUKHTAR🎁

SADAUKARWA ga Mom manal
Nafisa
Fulanin tashi πŸ˜‚
Ummu taufeeq
Amrath Amrath
First lady ko nace last lady🀣
Ummu nawaz

Allah yabar k'auna mutane naπŸ‘πŸ»πŸ€—.



πŸ…Ώ6







Bayan an gama d'aurin Auranne aka shiga gaggaisawa da mutane yayinda ake raba manyan bags wanda ke d'auke da manyan goro biskit sweet leman kwali da kuma shaddodi acikin kowa jaka.


Kowa murna yake da hakane suka nemi cewa zasu shiga gidan domin a gaisa da iyayen Amarya """ ai Mlm hadi da gudu sauri sauri yana washe baki yace ah bismillah bisimillah ai gidan kune nan ranka ya dad'e baya ya dawo ya tsaya yayinda yakewa Alhj Sa'id da mutanen sa nuni dasu wuce kan gaba.


Mutane da yawa sungano tsagoron son k'ud'insa da kwad'ayi ne yasa shima bada yarinyar ga babban mutun irin Alhaj Sa'id.


Murmushi Alhaj Sa'id yayi yafar wucewa yayinda sauran ke take masa baya.


Cikin gidan kuwa se gud'a ake ana Zarah tayi goshin da ba kowace mace ce keyiba seme sa'a a rayuwa.



K'amshin turare ne me kamshin gaske yaja hankalinsu wanda sukai duba ga hnayr da k'amshin ke fitowa se sukaga Ashe Angone da mutanensa.



Nan naga ikon Allah ai gaba d'ayan matan dake gun k'asa naga sun durk'usa kamar masu neman gafara suna gaida vise president.


Laraice kan gaba wajen iya durk'usa se godiya takewa masa yayin da shi kuma ya durk'usa cikin girma yana gaidata da sauran Abokan nasa.


Cikin rawar murya Larai take amsawa mlm hadi kuwa baki yak'i rufo.


Alhaj Sa'id duba yake ga kowane kusurwar gidan soyake yaga Zarah amma yanajin kunyar tambaya.

Baba maryan ce ta lura da hakan tai saurin cewa bari akira amaryar da kawayenta.


Cikin sauri suka mik'e da Larai suka nufi d'akin dasu Zarah ke ciki.



Kanta a dafe suka sameta amma make up da Aysha sukai mata yana nan sede idonta da yai ja Alamun harta gaji da kukan datakeyi.


Larai ce tafara shiga nan ta iske su sunata kwalliya da fesa turaruka Larai da baba maryam suka wash baki Larai tace yauwa ku d'ad'a gyagygyarawa ga k'usosgin gobnati cen A farfajiya ko kuma Allah yaci daku kuyi mana kamun babban kifi.

Gaba d'aya 'yan matan sukasa dariya Aysha ko fara ah babu a fuskarta bare zarah dako d'ago kai batai ba .


Larai tace maza ku tashi muje kema harda ke ga angon cen nason ganinki.


Zarah mutsi mutsu kawai take da bakinta ita haka take aduk sanda abu be mata dadi ba setai ta mismis da baki wanda ita kanta batasan dalili ba .



Larai ce ta k'ara fesheta da tirare gamida kara mata wata powder a face dinta nan ko tai wani kyau dam cen din ita me kyance.




Hannu ta kamata suka fito da sauran yan matan harda aysha.



Tin daga nesa ya kafe da ido ko k'iftawa ba yayi Yayinda fiskarsa d'auke da Murmushi """" Ministern K'udi'i na lura dashi dan hk da sauri ya d'an zungureshi nan ya dawo dg duniyar tinanin daya shiga .


Itako ko d'aga kai bataiba don batason kallonsa bare jin muryarsa.Abokan sa kam sosai suka yaba kyan zarah gata yarinya me jini ajika lalle abokinsu yayi sa'a.


Nan 'yam matan suka shiga gaidasu cikin kwarwasa suna amsawa aysha ma hk """" Alhaj Sa'id magana yaiwa da d'aya dg cikin escort dinsa nan aka shiga bawa matan dk gun kud'i ko wacce 30k a cikin ambulan.




Murna kam ba amagana nan suka tashi suka fita matan se godiya suke """" Alhaj sa id mutunne me kunya sosai shiyasa ma yakasaiw zarah magana kwata kwata.



Zarah kam tazo iya wuya jin kirarin da matan ke masa shida mutanen sa wanda dagaji kasan idon su yarufe akan kud'i suke yin hakan.




Da sauri ta koma d'aki alokacin wani lesa ne a jikinta ruwan zuma anwa d'inkin karamar riga me dan banzar tsadar gaske.


Kuka kawai take.
Larai kuwa tura 'yam matan take akan suje suyi musu rakiya har wajen shiga mota k Allah yasa wani daga cikinsu yace yanaso.



Aiko da sauri suka fita suna yauk'i baran hafsat dake dama akwaita da felek'e


Wayar aysha na hannun hafsat yayinda aysha tini dama tabi zarah d'aki sukad'ai suke damuwarsu dake dama abokin kuka ba 'a 6oye masa mutuwa.


Aysha tace hakuri zaki zarah an riga da 'an daura sede miyi hakuri " d'an kwalin kanta zarah tacire ta had'a hannayent biyu akan fuskarta tana kuka.



Aysha tace zakisani kuka nima dan Allah kiyi shiru nan aysha ta fara kuka haka suka had'u sunayi tare zarah najin kukan aysha da sauri tace na dena amiyat daga yu na dena kuka shine zeyi kukada harya sake ya aureni.


Aysha ta d'ago

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment