Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mamaki ya tsayayn Kallon ta wanda ita sam batasan ya shigo ba.


Hannunsa ya zuba a aljihu kawai yana kallonta.


Jitai am buga mata wara uwar tsawa wacce tasa seda ta firgita tai hanyar toilet:":"


Gidan ubanwa zaki a toilet maza zoki fice tinkafin ranki ya 6aci"""' se yanzu taga ashe shine dan hk ta saki fuskarta gamida dafe k'irji tace wlh ya musaiyyet ka tsoratani na firgita.


Eh nine wayace kita6amin kaya? Wama yace mk kayana ba a goge sukeba?

Taku tayi har gabansa tana murmushi shiko idonsa akanta cikin d'aurewar fuska ""a haka tazo har gabansa tsugunawa tayi gamida rik'e kunne tace kai hkr bazan sakeba.


Kallonta kawai yk yace ok tashi kije na nagode ko amma nex time karki kara karan banin ta6a kayana kinjiko.


Komai nasa burgeta yake ciki kuwa har fad'an dayake mata domin tindaya fara mouth d'insa kawai tk kallo.


Yace jeki inason zan wankane""" jiki ba k'wari ta mik'e yabita da kallo.



Tsaki yayi yace narasa yadda zanyi da yarinyar nan amma bari dad ya dawo wlh seta koma gidansu.



Karfe uku dede me aiki se buga d'akin zarah take amma taji shiru ''' a k'alla takai minti shabiyar tana knocking amma ba a budeba.


Zarah kuwa najinta kawai zazza6ine ajikinta ga yunwa tanaji ahaka ta taso dakyar ta bud'e kofar"""" tana budewa sukai ido hud'u da Merry sanye cikin kayan aiki wanda akai dominsu masu aikin.


Zarah tace lfy ? Cikin ban garma merry tace dama na shirya miki lunch ne tin d'azu shiyasa nace ari na sanar dake.

To kawai zarah tace ta koma d'aki.

Tana shiga toilet ta shiga don yinwanka kallo ta tsaya yi ganin haduwar toilet d'in sosai ya burgeta komai yayi ga kuma kayan kamshin toilet nan da yawa gamida sabulai masu kamshi da mayukan wanke kai .


Seda tai wanka sannan ta fito always ta d'akko wanda dama tin kafin su taho ta fara period.


Doguwar riga ta atamfa tasanya dikin ya matseta sosai gashinta ta gyara tai simple makeup.

Turare ta fesa sannan ta fito dan cin abinci.


Flask ne dayawa gasuna jere taci duk abunda take so .


Farfesune na kifi dana kaza se white rice da stew d'in cabbage wanda yasha nama aciki' Se juice na kwali da kuma wanda aka hada agidan ''' se potatoes soyaiye da kuma wainar kwai.


K'ugu zarah ta rik'e tana kad'a kai tace eh ga mayunwaciya ba ai dole yasa akawo min wannan cimar sbd game cikin zani """ Amma mutumin nan d'an rainin wayone wlh.


Zama tayi ta zuba kadan a plate tafaraci.





Tini 'yan kawo amarya suka je gida yayinda aka basu kud'i da turamen atamfofi.


Sosai Lari taji dad'i yayinda suke gaya mata kyan gidan zarah.





Karfe 7 dede iyalan sun hallara a babban palour wanda Alhaj Sa'id ne se momy fa 'eza da khairat se Musayyet.



Alhaj yai gyaran murya yace musayyet yabatun aikin nan ince komai ka kammala? Musayyet yace eh dad angama komai shiyasa ma na taho 'yace gud kallon fa'eza yai yace amma de anan zaki zauna ko kinga momyn ki taji dad'i.

Cikin jin dad'i tace eh dama nazo kenan saboda nagama karatu aiki kawai nk jira "" dad yace masha Allah seki bawa Musayyet takardun naki kinga seki aiki a d'aya dg cikin compayn mu ko?


Cikin jin dad'i tace ngd dady Allah yaja kwana.


Nusayyet ko jiyai kamar an watsa masa ruwan zafi se harara yake aika mata dasu itako ta gefen ido tk kallonsa tana murmushi da wannan damar ne zata samu auran misayyet.



Sosai ya had'e rai yace dad datayi zamanta agidansu acen ma ai seta dinga tafiya aikin ko?

Alhaj Sa'id yai murmushi irin nasu na manya yace a a tai zamanta nan gidan nima zanji dad'i koba komai ai kun k'aru kunzama ku 3 a gidan ''' danguntun tsaki Musayyet yayi wanda shikad'ai yaji abunsa nan take ya tashi yace yanason zuwa wani gunne.


Mony kallonsa kawai take domin ta gano bayason zaman fa'eza a gidan ""' murmushi kawai tayi tace Alhaj yakamat fa katafi kabar 'yar mutane a gida tin jiya ita d'aya tinda kowa ya tafi ai sekaje Allah ya tashemu lfy.


Da sauri khairat tace dad nima zani?

Kumatinta ya shafa yace to shikenan semu tafi tare amma yanzu zani unguwa na dawo semu tafi yareko?

Kai kawai ta d'aga masa nan ta kama tsalle da murna .



Tashi yayi yace to madam seda safe """ kallonsa tai tace mukwana lfy.

Fita yayi nan securities da escort d'insa suka rufa masa baya.


Momy murmushi tayi tace namiji kenan ."""" Fa'eza tace momy naji kina cewa yabar 'yar mutane kina nufin k'aramar yarinya ya aura?
Momy 'yar dariya tayi me ciwo tace eh fa 'eza yarinyace kimma girmeta a shekaru babu yanda na iya halin namiji sede ka barshi kawai.


Tsaki fa-eza tayi tace wlh harkin samin tsana yarinyar aikin banza.

Momy tace kul karna kuma kumajin hakan .
Dake tasan halin momy bataso ayawaita magana inde ta 6acin raine yasa tai shiru da bakinta.



Musayyet kuwa d'akinsa ya koma ya kanta yanajin haushin abinda dad yace wai fa'eza ta zauna agidansu.


Wayarsa ya ciro yafara kiran layin zarah.


Zaune take a d'aki tayi tagumi idonta hawaye na zuba taji ringing d'in wayarta.

Da sauri ta d'auka sede ba suna "": cikin murya sirirya tace hello wace ?

Murmushi yayi yace nine de na ran nan kintina?


Ta gano muryarsa dan haka tace menene to ko yauma momyn kake nema?

Dariya ta bashi ya gyara kwanciya yace no yau baby nake nema.

D'an murmushi tayi tace malam kai hkr da matar aure kk magana """ be d'auki zancen da mahimmanciba a tinaninsa kawai batason magana dashine.

Yace haba baby ai kya tsaya kiji mena keso dg gareki.


Wasa take da hannunta tace to inajinka yace wlh tinda naji muryarki ran nan naji kin kwantamin a rai dan Allah karkice bakya sona pls.


Jitai maganar ta soketa har cikin zuciyarta se jiyai kawai tana kuka kuma takashe phone d'in.


Sosai hankalinsa ya tashi zubur ya mik'e akan gado yana k'ara kiran layin sede akashe wayar take.

Bango ya kaiwa duka nan take idonsa yaija""' menene matsalar yarinyar nan shikam da yasan inda take da yaje ya lallasheta gashi wayarta a kashe .

Yanajin kukan tane har cikin zuciyarasa.


Kansa ya kifa a kan k'aramin center table ya fara kuka Allah ya jarrabe shi da son wacce bema ta6a ganintaba wannan wane irin abune gashi ga dukkan alamu a cikin damuwa take.



Zarah cilli tai da wayar ta fara kuka kamar ranta ze fita """" yau gashi wani matashi yana furta mata kalmar so Alhali tana gidan aure'"" ga dukkan alamu koma wayeshi tabbas shid'in kyakyawane kuma ze iya nunawa mace soyaiya amma an tashi an bata wani babban mutun wanda ta tabbata be iya soyaiyaba kuma koma ya iya ita yai mata girma bazata iya ba """ kuka ta k'ara fashewa dashi me cin rai.


Alhaj Sa'ed yana zuwa aka bud'e musu gate suna d'aga masa hannu ''' seda akaje wajen parking da motaci sannan susuja koma baya shikuma yai musu sallama ya tunΔ·ari gidan cikin farinciki.

Zarah na kwance tana sana'ar ta ta kuka taji knocking wanda ta tabbata megidan ne da ido ta zaro waje tana k'ara sautin kukanta.







Ummulo ce take 😘
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*

*MUTUM*


Creating And Written by
*UMMEE* *MUKTAR*🎁


SADAUKARWA ga my k'awa
Fateemah Zarah 😍 Allah yabar manake kodan musha chapterπŸ˜‚ Sarkin Comedyn Family And Friends inayinki irin over d'in nanπŸ€—.




πŸ…Ώ10


Zarah ido ta zaro waje ta saki kuka gamida k'unshe baki tanaja baya seda taje har k'arahen gadon jikinta se rawa yk ''
Knocking ya farayi wajen so hud'u amma yaji shiru kamar bame rai a cikin d'akin """" wani d'an guntun murmushi yayi irin nasu na manya be hkr ba yak'ara knocking amma tsit kakaje ""'

Wayarsa yaciro yafara kiran layinta amma wayar na kashe ' Ahankali ya furta tokode yarinyar nan tayi bacci agogon hannun sa yakalla seyaga k'arfe 8:31 kallon k'ofar ya k'arayi yace may be kotayi bacci ne amma yakamata naga lafiyarta """'

Duk abinda yake fad'a zarah na jinsa itakam tsoro ne fal ranta gamida fargaba"'" cikin sand'a ta bud'e k'ofar toilet ta shige namma ta banko k'ofa tai zaman ta a wani hadaddan bahon wanka karami madedeci kamar dan ita akayi ,...


Haka yaita knocking amma shiru " kai tsaye wani corridor ya nufa wanda ze sadashi da wasu dakuna na musamman """".



Yana zuwa ya cire kayansa ya shiga wanka gami da d'auro Alwala.

Haka yaita sallah yana rok'on Allah akan Allah yabasu zaman lfy ya kore sharrin dk cikinsa ya kuma bashi ikon yi musu adalci.

Bayan ya idar jallabiya yasaka ya hau kan bed ya d'au remote ya kunna A.C ya kwanta sede bacci ya gagareshi domin yaci burin wannan ranar amma yarinyar nan taki bude masa kofa ''' ..zaune ya tashi yace kai inagafa bacci tayi ai dole tai bacci da wuri domin kuwa tagaji.

Laptop d'insa ya d'akko ya shiga tura wasu sakonni .


Zarah kuwa jin shirune yasa ta fito da alamun ya tafi """ idonta ta goge takoma toilet tasakw wani wankan ta shafe jikinta da mayuka masu sa fata tai kyau sannan ta zura kayan bacci.. jitai cikinta na k'ugi domin kuwa tanada olcer tana sata saurin jin yunwa """ tin wajen karfe 7 na daren merry ta jera abinci a dining amma zarah bata fitoba.


Zarah cikin murya k'arama tace wayyo cikina yunwa nakeji """ A hankali ta tashi nan ko idonta yagane mata wani k'aramin firij dk d'akin da sauri ta nufeshi tana bud'ewa kuwa taga nau in drinks kala kala harda cake wanda yk acikin kwali sannan kuma k'unshe a cikin leda me Δ·'yalli da sauri ta d'ebo ta meyawa da drink tafaraci .


Seda ta k'oshi tai brush sannan ta kwanta barci taja bargo tai addu'a se bacci.



K'arfe 12 na dare Musayyet babu alamun bacci a idonsa tinani kawai yake ta ina zega yarinyar nan ""? Hak'ik'a shikam yakamu da soyaiyarta wayarsa ya jawo ya k'ara bugawa amma still a kashe tk d'an tsaki yayi ya kwanta idonsa na kallon saman d'akin ,,,,, .wayar ya kuma dauka ya kalli number wacce yai mata saving da funny gal. Wahasp ya shiga aiko nan yaga itama tana hawa online amma alamu ya nuna kwana biyu bata hauba murmushi yayi kawai me k'aya tarwa """yana shirin aje wayar yaga kiran fa' eza na shigowa""""" da mamaki yabi number da kallo yace wannan kuma ubamme tk nema a wannan lokacin?


Be d'aga ba hk taita kira wajen so 6 yace oh no wannan ya rinya a kwai mayya cikin fad'a yai pickin call yace what?

Daga ita se wata riga wacce da ita gara babu tace haba ya Musayyet wai dan Allah menai mk ne duk kabi ka tsaneni kamar ba 'yar uwakka ba ?


Numfashi yaja ya gyara kwanciya yace menene to ?

Murmushi tayi ta samu abunda take nema dan hk ta kashe murya tace wlh nakasa baccine ? Kansa ya shafa sannan yace kuma ni meye nawa acikin rashin yin baccinkΔ±? Kuka tafara tana cewa Addu'a nakeso kazo kaimin irin wacce kaimin watannin baya lokacin ina tsorata d'in nan wallahi yanxuma ina rufe ido sena dinga ganin kamar wasu baqaqen mutane sunamin yawo. Cikin ransa ya yarda domin yasan tana da Aljanu .

Fa 'eza nada Aljanu wanda tasha fama dasu shekarun baya .


Hakan yasa yanzu ya yarda da zancenta """"":
Wani ihu ta k'wallah wanda shikansa seda ya razana da sauri ya aje wayar
cikin azama ya tashi ko riga babu jikinsa .




Sauri yake Sosai ya nufi d'akin fa"eza dan besan a wani hali tk cikiba.


Yama manta daya fad'awa momy hankalinsa duk yayi gaba.


Yana zuwa ya turo k'ofar d'akin aiko yaganta se juyi take akan gado.


Da sauri ya nufe ta tsayawa yai ko ta6ata beba ya farayi mata addu a yana tofa mata """ tashi tayi tafara cilli da kayan d'akin ganin zataiwa kanta rauni yasa ya cukumeta ya riketa sosai ya kwantar da ita akan gado yana kwalawa momy kira .


Momy kam sam batajiba kasan cewar a kwai 'yar tazara tsakanin dakunan su.



Musayyet yarasa yanda zeda ita Addu a yk mata amma kamar tinzurata yake ":"" gaura mata mari yayi aiko ta zuba wani ihu nan yasake karamata wani aiko nan take tace ya Musayyet nifa kake duka.


Dagata yayi daga dannar da yai mata yace sannu ko ai yanxu dasukaji duka sun dawo hankalinsu """ hanyar fita yayi da sauri ta biyoshi ta rungumeshi tace dan Allah ka Aure ni wallahi inasonka ina mk son da bana yiwa kaina.

Da k'arfi ya finciketa yace oh yanzu nagane Ashe Aljanun naki naki na iskancine ""'toki kiyayi had'uwarmu nan gaba bazakiji da dad'iba daga yai waje tabishi da kallo zuciyarta na mata suya .



Wannan wane irin mutunne me taurin rai da bak'ar zuciya haka.



Amma wallahi bazata k'yaleshi ba su zuba su gani.




D'akinsa ya nufa babu kowa agun momy kuwa a time d'in ta fito wucewarsa kawai tagani gashi ko riga babu jikinsa """


Da sauri ta nufi d'akin fa'eza amma bata bud'e k'ofa ba jitai fa"eza na kuka tana cewa nizakaiwa hk wallahi sena aureka komai abunka.


Da sauri momy tai d'akin taga fa 'eza zaune jikin gado tana kuka ,,,dafata tayi tace lafyanki kuwa ?
Da sauri ta rungume momy tana kuka tace momy shine ya Musayyet ne ..


Cikin damuwa momy tace subahanallahi meyai miki.?



Kuka taka'rayi tace momy ya Musayyet ne tinda yadawo kullun seyazo dakina nace masa miyi aure yak'i wai akwai wacce yakeso ta k'arashe maganr cikin kuka.


Momy jawota tai dg rungumar datai mata suna fuskantar juna tace da gaske kikeyi?

Cikin kuka tace eh momy ki tambayeshi nasan baze fad'i gaskiyaba .


Momy kallon gadon tayi wanda yk a ya mutse kuma ta tino da wucewar musayyet data gani dazun ko riga babu jikinsa .

Kai ta dafe tace innalillahi wa inna ilaihi raju'un" wannan wane irin abun kunya kukesi kujawi mana ?

Kanta momy ta dafe wanda ke mata ciwo yanzun gamida runtse ido.

Tayama za ai haa ta faru gashi taga hujjoji da idonta babu damar t k'aryata.
Inda wani ne ya fad'a mata haka zata k'arya ta domin tasan ba halinsa bane shida ko mata basu dame shiba .""" Amma ba a shedar mutun dari bisa d'ari tunda harsuka kad'aice shida ita to shed'anne na ukunnsu.
Ta k'ara dafe kai tace ya ilahi.


Musayyet nashiga d'akinsa yace zanyi maΔ£anin yarinyar nan wato ni zataiwa iskanciko?



Kai ya dafe take gabansa ya fad'i jin irin bugun da momy take kuma tana k'wala masa kira cikin d'aga murya a wannan daren.












Love you All my fansπŸ€—πŸ˜˜
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*

*MUTUM*



Creating And Written by


UMMEE MUKHTAR🎁


This page is urs

Nafeesa
Mom fauzah
Maman umar
Maryam usman.

Nagode sosai Allah yabar k'aunah❀.





πŸ…Ώ11


K'ofar yabi da kallo wacce momy ke bugata kamar zata 6alla"" cikin rawar jiki ya nufi k'ofar yasa hanu ya bud'eta""" yana bud'ewa momy ta hankad'o masa fa'ezah har tana cin karo da kafad'arsa kamar zata fad'i yana kallonta ko k'ok'arin rik'eta beba dan mugun haushinta yakeji yanzu.

Momy idonta taf da hawaye take kallon jikinsa daga k'asa har sama """ shima jikin nasa yabi da kallo yanaso ya gano abunda Momy Δ·e nufi,cikin muryar kuka ta soma magana cikin kuka tace yanzu Musayyet irin tarbiyar danai mk kenan?


Wannan shine sakamakon kulawar dana baka tin kana yaronka harkawo girmanka? Kafad'amin menai maka da zaka sakamin da irin wannan bak'in fetin ? Dama na sani nasan cewa turaka k'asar waje da Alhaj yake dole idonka ya 6ud'e ,nan ta d'urk'usa tazube kan carpet d'in dake d'akin ta soma kuka me cin rai"""" Musayyet kam sam besan abunda tk nufiba dan haka da sauri ya durk'usa yana rik'e hannunta da zimmar ze d'agata tai saurin tankwa6e hannun ta d'ago kai cikin muryar kuka tana cewa karka ta6ani ,,,karka soma ta6ani tinda ka riga ka canja Ashe a hakane kk nuna baruwanka da mata amma cikin zuciyarka ba hk bane?

Kallon fa'eza yai wacce ta k'ame a jikin mirrow jikinta se rawa yk dan batai zaton haka abin ze kasanceba.

Musayyet kuka yafara yana cewa Momy menayi dan Allah wallahi bansan kome kk nufiba. ?
Tsaye ta mik'e goge fuskarta ta kalle shi sannan ta kalli fa'eza da sauri fa 'eza tai k'asa dakai tana matse hannunta .

Momy tai wani murmushi me ciwo tace kana nuna kamar bakasan komai ba ko? To muje a haka amma kasani cewa seka auri fa'eza tinda kaine wanda kafara saninta a matsayin 'ya mace """"" inaso ka shirya cikin lokaci k'ank'ani fa'eza zata zamo matarka.


Tana fad'in haka tai waje da sauri har tana tuntu6e sotake kawai tajita a d'akinta.

Musayyet kallon fa'eza yai ya doka mata harara memakon yaga fuskarta cikin tashin hankali amma se yaga tana murmushi""""



Kallon ta yai cikin tsoro dan yanzu kam ya gano gadar zaran data shirya masa""".. wani yawu ya had'iya me d'aci tana lura dashi dan hk tai dariya tace baka had'iyi yawuba Musayyet se randa kaji waliyammu suna cewa kazama mallakina ta har abada ""' kasani cewa duk abinda nakeso sena sameshi kota tsiya kota arzik'i daga ta fice tana kad'a jiki.

Tana shiga ta fad'a kan gado ta saki wani kuka tana shafa kan khairat wacce keta bacci abinta .

Wannan wane irin abune ? Yau mijinta ya ni santa da ita ranar bak'in cikine agareta dan dama idonta 2 ba bacci takeba.

Gashi a ranara ne Musayyet da Fa'eza sukai mata abinda bazata ta6a mantawa ba.


Ita kam data san hk zata faru da fa'eza bata zauna a gidan ba .

Kuka ta k'ara saki dg k'arshe tai Alwala ta fara sallah ko zuciyarta taimata sanyi.



Fa 'eza na fita Musayyet yasa kuka ya kwantar da kansa ajikin pillow yana dad'a k'ank'ame pillow d'in cikin kuka mara sauti """ seyanzu ya fahinci abunda fa'eza tai masa sosai yaji ciwon abun a ransa """ Abunda be ta6a yiba yau shiza ai wa sharri akan sa? Lalle kaidin mata babbane.

Abinda yafi jin ciwo shine Momy tace seya aureta A kowane time za a iyayin maganar auran, shikam meze da ita yarinyar da batada kunya bare mutunci.



Dama nasan turaka k'asar waje da Alhaj yake dole idonka ya bude,, kalmar data sake dawo masa kenan dan hk ya dafe kai yace ya ilahi.

Kuka yaci gaba dayi daren ranar ko runtsawa beba hk ya kwana cikin kuka da 6acin rai.



Fa 'eza kam daren ranar kamar sallah haka taita juyi akan gado takasa bacci dan farin ciki.




A subar fari Alhaj sa'ed ya farka wanka yayi yasa coffee d'in jallabiya yq nufi masallacin dake gidan .... koda ya dawo kai tsaye bangaren zarah yayi ya sake knocking wajen so 3 amma shiru ' murmushi yayi ya nufi bangarensa .




Zarah bata farka ba se wajen shida na safe tana tashi ta nufi toilet brush a farayi sannan tai wanka ta d'ora da Alwala duk da cewa ba sallar zataiba amma yanada kyau ka zauna da Alwala.

Tana fitowa wani d'akin tayi wanda shima a cikin d'akin yk kaya ta sauya wani material ne coffee me ratsin adon zuma a jiki sosai tai kyau abinta duk da simple make up tayi....... kan gado ta koma ta kwanta tai lamo tana kallon adon dake jikin zanin gadon me uban tsada da kyau.




Idonta ne yagano mata phone d'inta wacce tai wurgi da ita """ tashi tai zaune ta dauki wayar se kuma ta kama juyata a hannunta tanaso ta bud'e amma tana tsoron kada wancen ya kuma kiranta.




Amma ai koba dan shiba zatai amfani da wayarta ko dan mahaifanta da kuma aysha.

Nan tasa hannu ta kunna ta gabanta n fad'uwa seda wayai tai minti goma a hannunta bataga alamar kiraba sannan ta saki jikinta gamida sauke ajiyar zuciya.



Da wurwuri Musayyet yabar gidan bayan ya shiraya kansa cikin k'ananun kaya sosai yai kyau amma kallo d'aya zakamai kagano idonsa ya d'an fad'a kad'an.






Kota kan drivern sa bebi ba wanda tin daya fito yake gaidashi amma ko kallonsa beba ""' hk ya figi mota yabar gidan.


Da mamaki drivern yabi motar da kallo sbd wulak'anta mutun ba halayyar Musayyet bane.




Babban Company ne wanda a time d'in karfe 7am ma 'aikata masu goge goge ne kawai sukazo kasancewar se 8am kowa ne ma'aikaci ke zuwa .


Amma se gashi yau tin kafin time yayi Musayyet ya riga kowa zuwa """ wanda shi baya tashi zuwa se wajen 9am ko zuwa 10 .



Da sauri suka 6ude babban gate d'in me adon golden suna sara masa gamida gaisuwa """ sama sama ya amsa yai ciki suka biyoshi da laptop d'insa da wata bak'ar bag k'arama wacce papers ne a cikinta masu mahin manci.




Har office suka bishi suka a jiye mΔ…sa sannan sk fita.


Sosai office ya had'u iya had'uwa kujera yasamu ya zauna ya kifa kansa da table yana k'wallah .



Wayarsa ta hau ruri har wajen so 4 ana biyar 5 d'in ya daga murya kasa kasa yk magana ""ok kawai yace zaku iya samuna ina nan daga hk ya aje phone d'in.






8 dede breakfast ya kammala agidan amarya zarah amma ta kas fitowa """ yunwa ce ta isheta dan hk cikin sand'a ta fito da sauri ta nufi dining .



Tea ta had'a ta zuba potatoes da waina kad'an a plate ta plantain ta soma ci.



Kamar daga sama ta hango shi ya fito fuskarsa dauke da smile yana nufo ta"" ai da sauri ta had'iye tea d'in data kur6a tai k'asa da kantΓ₯.


Sanye yake da jallabiyar dazu setaga yayi kyau sosai kamar yaro sede shekarun dayake dasu.



Har yazo gun kanta na k'asa bata d'agoba .



Salamu alaiki ya gimbiyar mata Abumma ba gayyata ? Da ftn sahibar tawa ta kwana lfy a gidan mijinta. ? Yai maganar fuakarsa ck da smile yana me jan kujera ze zauna.



Murmushi ya k'arayi yace baby ina kwana tinda baza a gaisheni ba.

Da sauri ta d'ago kai suka had'a ido setaga yamata kwarjini bakinta na rawa tace dama dama yanzu zan gaisheka """sosai ta bashi dariya nan ya kama kwaikwayonta yanda tk magana.

Mamakinsa tk amma tai shiru yai dariya yace to a hadamin tea nima""' cikin rawar jiki tagyad'a masa kai alamar to nan ta kai hannu zata d'uki cup shima yakai nasa hannun ze d'au spoon aiko hannunsu ya had'u dana juna "


Da sauri ta kalle shi shima idonsa akanta ko kiftawa bayayi sbd wani shock yaji.












I love you All😊
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€




*AURAN* *BABBAN*

*MUTUN*

Creating and Written by

UMMEE MUKHTAR🎁

Kwana 2

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment