Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka giggina a garin.

Nan mutane suka fara matsawa gamida duban titi.



Nabel hankalinsa nakan kayan wasan yara yayinda wata ball iska ta d'auketa daga kan teburin kayan wasan ta cillata kan titi.



Ai da gudu nabel ya nufi kan titin kamar wanda aka wulla waishi yaje dakko ball aiko nan wani me babur ya bigeshi .




Ihu suka sanya su sa ade da Momy sukai kansa dama sauran jama ar dk gun .



Haka me babur d'in yaci birki yazo kansu ya kar6i nabel dake jikin sa ade ya rungume shi ajikinsa yn kuka kamar ransa ze fita """ abinda yai matukar bawa kowa mamaki kenan.





Hattasu momy kallonsa suke suna mamaki.



Shiko me babur kuka 2 yakeyi ya fitone dan zuwa ya shedawa dan uwan mahaifiyarsa rashin lafiyar ummansa tana gida numfashinta na fita kadan kadan sam baya temakonsu duk da irin tarin dukiyar dayake da ita abunda zasucima gagararsu yk se kuma gashi ya bige yaro wanda ko kudin kaishi kyamis ma bedashi na biyu kuma tausayin yaron ne fal zuciyarsa ganin yanda yk zub da jini.






Gurun ya cika makik da jama a yayinda aka rasa wanda zece akai yaron asibiti """" tun daga nesa Alhaj Sa ed ya hango taron jama a hakan yasa ya shedawa president kan cewa akwai abinda ke faruwa agabansu.

Nan take president
yabada umarnin atsaya don ganin abunda yafaru
.





Anan akai parking da motoci sojoji da escorts suka zagaye gun sannan suka fito.




Nan da nan jama a ka watse aka bada fili kafin kace meye tini gurun yacika da jama a.



Saurayin daya kade nabel yayi zaman dirshen shida su sa ade da momy se kuka suke



Tin da Alhaj sa ed ya fito ya hango yaron kwance jikinsa duk jini da sauri ya isa gun shida president suna musu sannu.


Saurayin yana dago kai yaga ai shugaban kasarne kusa dashi wanda shi duk karar jiniyar da motocin sukesam bejiba sbd yashiga wata matsalar ba yan wacce yabaro agida ta lalurar ummansa.


Alhaj sa ed tinda ya hango su Momy yaji wani abu aransa wanda yarasa komene .


Alhaj sa ed dakansa ya dauki nabel yayinda yabada umarin matan ma sutaso hardashi saurayin.



Nan danan suka mke su momy se d'arare d'araran jiki suke domin kuwa mutanen da kwarjini suke ainun.



Mota daban aka zubasu ciki yayin da matashin ke kiciniyar daukan babur dinsa president yace yabarshi nan .


Jiki na rawa ya shiga mota yana leken dan babur dinsa yn addu a Allah ys kar a sace masa.







Kai tsaye wani tsadadden hospital aka nufa ba 6ata lokaci aka kar6i nabel wanda dama su president sun wuce gun taro dadyne kawai yace suje shi yakai yaron asibiti.





Mintuna kadan Alhaj sa ed ya dawo gun su momy yai musu bayanin cewa yaron yai bacci kuma zeji sauki karsu damu.


Har kasa sk sakko suna masa godiya yace vakomai...nan ya juyo kallonsa ga matashin saurayin daya bige yaron yace fadamin wani abu mana naga kamar kaima vaka cikin nutsuwarka me kk kallo harka bige wannan yaron ?


Saurayin ya durkusa har kasa yace wlh tinanine yamin yawa ummata batada lfy amma bafa sani naba dan Allah kai hkr karka sa a kulle ni wlh ni kadai duk duniya take dashi ni kadaine danta yanzu hk tana gida batada lfy da wuyama inna koma nasameta da rai yakai karshen maganar yn fashewa da kuka.




Momy dake me saurin kukace tini tasa kuka sbd tausayin matashin Alhaj sa ed ya kalli momy ya jinjina irin tausayin datake dashi yace ba abinda zan mk yaro yanzu katashi muje gidan naku ko.



Momy tai zumbur tace nima zani dan Allah.


Sa ade ta kalleta tace hmmm .



Alhaj sa ed yai murmushi suka rankaya sk fita baki daya.







Wata unguwa sk nufa wanda dama daka ganta kasan unguwace ta talakawa .


A tsakar gida suka tadda matar tayi amai harta hanci idonta akakafe kamar ta mutu.




Da sauri saurayin yai kanta ya rungume ta yn kuka momy da sa ade sukai kanta suma suna kuka kamar damacen sun santa.




ALHAJ sa ed ya share hawaye yace kutemaka masa adakkota asata amota insha Allah tana da rai.


Da sauri aka sata mota sk nufi asibiti.




Itama daki daban aka bata .


Suka dawo wani babban palour sk zauna.




Fita dady yayi mintuna kadan yadawo ya shiga dakin da musayyet ke kwance """ su momy na kallonsa duk sanda ya gilma kowa yana ai yana mutunci da kulawa irinta wannan bawan Allan.




Momy tace wa saurayin kokasan wannan bawan Allah wayeshi kuwa?



Saurayin ya dago kai yai wani guntun murmushi yace zaki mamaki idan kikaji koshi waye .

Me bawa shugaban kasa shawarane tafannin ilmi.


Sa ade ta bud'e baki tace an shiga uku kenan kamamu zasuyi kan cewa munbari ka kade yaro.?



Saurayin dariya ta kufce masa yace a a kede kawai ki tsaya ki kallo wannan mutuminin kowa yasan shi mutumin kirkine .


Momy tace Allah sarki hk akeson shuwagabanni an gari Allah yasaka ms da alkhairi.


Ameen suka amsa yayinda suka hangoshi rike da hannun Musayyet dauke da kayan ciye ciye se dariya musayyet kewa Alhaj sa ed shima yanai masa tamkar uba da d'a.



Kansa d'aure da bandage karami dede inda jini ya zuba.





Baki suka bud'e su sa ade
Suna kallon ikon Allah
Matashin saurayin yai murmushi yace kadan ma kuka gani.

Mutumin kirkine shi d'in.


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

AURAN BABBAN

MUTUM

Crtng And Wrtn By

UMMEE MUKHTAR🎁


πŸ…Ώ52.


Kai tsaye dady gun wasu flowers ya wuce yn nunawa musayyet shiko yn dariya .



Se dare matar ta farka inda ba lefi tasamu sauki dady yabawa saurayin nan kudi me yawa yace yaja jari wanda kudin sunfi k'arfin aja jari domin masu yawan gaskene.


Da kansa dady ya fita yayo musu take away yabasu sukai ms godiya suna yaba halin kirki irin nasa awani palour suka kwana har tsawon kwana uku inda ake kula da musyyet kuma Killun dady zezo da kayan ciye ciye da takeaway""""" yamma likis akabasu sallama wanda dady bayanan hk suka jira yadawa domin sudada yimasa godiya.



Yace bakomai ynz ina suka nufa inyaso seya kaisu .

Anan ne sukai shiru sa ade tabashi lavarin sufa bak'ine basu san ko inaba.
Labari sk bashi tin aslin fitowarsu yayinda yai shiru tsawon minti 3 sannan yace su shigo sutafi.

Bamusu sk shiga dan sunsan baze cutar dasuba.

Gidane na alfarma me kyan gaske wanda se wane da wane ko kuma gogaggun 'yan siyasa.

Tinda sk shiga sk kalle kalle har suka shiga gidan komai normal kuma babu kowa cikinsa """ abunda yabasu mamaki kenan amma sukai shiru wani bangare ya nuna musu yayinda yaja hannun musayyet sukai room dinsa.


Babban dakine wanda sam basusan yanda za ai amfani da wasu abunba.

Dakyar sukai wanka suka maida kayansu sukai sallah.


Da daddare da kansa yafita shida musayyet sukaje shopping a wani babban mall yayinda yajido musu kayan sawa dana kwalliya kamar hauka .

Hk yajido wa musayyet shima nasawa dana wasa dan komai yagani seya nuna masa yanaso shikuma dady cikin fara a da jindadi ze dakko abun .

Se dare cen suka dawo tsawon kwana kin nan dady ne ya nuna musu komai na amfanin gida danaci .


Sosai suka shak'u da juna dan komai anutse sukeyinsa suna burgeshi har inyaje gun aiki bashida tinani sena momy wacce tace masa sunanta mulabi.


Anan ne yabasu labarin sa shidan asalin adamawane mahaifansa sun rasu wajen hadarin mota harma da 'yan uwansa wanda sunje bikine akan hanyarsu ta dawowa ne Allah yasaukar ms da wannan iftila I.
Hk al adar su take inde ana biki to ana gayyane ayi motoci kamar 2 maza da mata atafi harma da yara.


Amma yanzu yanada dangi acen yn zuwa gunsu suma kuma sukan ziyarceshi.



Sosai sk tausaya ms harda kuka sukai musu addu a da kuma kara yimasa godiya daya tallafi rayuwarsu




Musamman dady asa ake zuwa hargida akoyar dasu ilimin boko dana islama """musayyet ko tini ansa shi school kuma yadena kwana gunsu dan wajen dady yk kwana sunzama kamar uba da d'a kwata kwata basason rabuwa da juna """kome yagani tofa musayyet ne zefara zuwa ransa .


Shinema yasanya masa wannan sunan .


Cikin ikon Allah suka kama soyaiya tsakani dady da momy har takaiga sunje adamawa anyi komai.


Awajen walimane minister yaga sa ade yaji ta kwanta masa """sati me zuwa akai komai yayinda sua sakarwa matan nasu kudi kamar hauka..

Shekara 3 tsakani aka haifo fa 'eza .



Niko kasar waje yaturani karatu .


Hk rayuwarmu takasance yarike mukamai da ban daban harta kaishi ga matsaΓ½in dayake kai yanzu
. wannan shine labarimmu.


Zarah tai ajiyar zuciya gamida murmushi taraso hadi da zama kan lap dinsa tai ms kiss ta shafi face dinsa tace mutun baya ta6a zama wani abu arayuwa seya sha wahala.

Gashi ta dalilin hakan kazama wn abu kafima wanda yake tare da mahaifansa domin yaba ka kulawa da duka soyaiyarsa gareka .


Musayyet yai murmushi gamida rike k'ugunta yace natakaita miki komaine agajarce amma nikadai nasan irin sonda yakemin .


Rungume juna sukai sannan sk koma sama danyin wanka.


Daren ranar Zarah ta murje kunyarta ta nuna masa tsantsar soyaiya dayanda itama takejinsa aranta yayinda Shima ya nuna mt har kukan farinciki seda sukai suna ftn mutuwace zt rabasu.







Kwanansu 6 a hotel din suka wuce zuwa china wani company na dady wanda hadin gwiwane shida wani d'an china """" takalma da kayan sanyi nasawa akeyi se zannuwan gado irin mash laushin nan kamar jikin zaki wanda companyn babbane kuma bangare 5 cikinsa.

Suna sauka ajirgi akazo da mota dan tafiya dasu tinda dama tini yai wata cewa yn tafe

Zarah kam tayi kallo lalle tafiya mabudin ilimine abunda tk gani a tv yau gata ga 'yan china gasunan gajeru da dogwaye kyawawa da munana.


Kai tsaye wata unguwa sk nufa wanda gidajen dk cikin unguwar fadar tsaruwarsu 6ata lokacine.

Unguwar shiru kamar bame rai cikinta se kukan tsuntsaye kakeji.


Wani katafaren gida sk tsaya musayyet ya kamo zarah suka fito cak yadauketa har zuwa cikin gidan wanda tsarin ginin turawane mekyan tsari.


Dakuna dayawa gasunan hk palors da toilet se swimming pool da komai na jindadin rayuwa.



Kai tsaye wani garden suka nufa sannan sk zo dede gurin swimming pool din musayyet yaa hannunta suka fada ruwa .


Dariya sukeyi yana mt cakulkuli tn zillewa yayinda yadora kan bayansa yana tafiya da ita haka akwance cikin ruwan.


Seda suka jima ahaka sannan sk fito suka tsane jikinsu sukai ciki ..


Kaya suka sauya sannn sukai sallah .








Washe gari dakansa yatashi yahada komai tanata bacci haryai wanka.



Dakansa yatada ita yai toilet da ita ya maida kofa gamida cire kayansa yace dama wankqn danai bafita nai sosaiba seki saken wani.



Dariya tayi tana watsa masa ruwa a face .




Breakfast sukai yn shirin fita tace seta bishi.






Smile yayi yace ta sake kayanta yn jiranta.


Doguwar riga tasanya fara me shape da ita me ratsin green se karamin mayafi tai makeup sosai tai kyau kamar 'yar baby ya rike hannunta sk shiga mota.







Suna tafe yn nuna mata gurare duk inda sk wuce se anbisu da kallo domin kuwa iya kyau sunada kyau .









Suna zuwa aka shiga gaisawa da kananun ma aikatan haryaje babban office din manajan gun .



Gaisawa sukai cikin harshen china zarah na kallonsa tana mamakin ashe ya iya yarensu.


Hannu manajan ya mika mt da sunan gaisawa amma musayyet yak saurin tare wa yace base sungaisawaba .






Bajimawa Mrs pan ya k'araso wanda tinda suka fara magana da chinanci sukeyi hk musayyet yajuya baki kamar dama cen yarensane sukaita tattaunawa har tsawon awa daya wanda zarah na dg gefe zaune kan wata lallausan chari me kyan gaske.






Baccine yafara dauketa dan hk ta kwanta nan da nan tai bacci.


Seda sk gama meeting ne yatasheta lokacin ba kowa agun se shi kadai da ita tana bude ido yasakar mt smile yace sarkin bacci daga zama se bacci.


Ta turobaki tace toba kuneba se wani wanciho yi kukeyi nibansan ma mekuke cewaba



Dariya yayi mata ya kama hannunta suka fito duk inda sk wuce se sungaidashi yayinda yk amsawa cike da kulawa ta musammam harda kyautar kudi .











Seda sukai wata biyu acen sannan zarah tafara zazza6i da yawan bacci.



Har gida doctor yazo yadubata yai mt test anan ne yanarda shi cewar matarsa tanada cikin wata daya da sati daya.



Murna musayyet yashigayi yayinda yabawa doctor zhoncin kudi me yawa amadadin albishir .


Shima doctor murna yk dan kudin da aka bashi meyawan gaskene.






Seda doctor yafita musayyet yahau kan bed din yatsareta da ido itako kanta na kasa yakama hannunta yn smile yace kuma shikenan se kikai cikiko?


Muntsininsa tayi me zafi ya kyalkyale da dariya yace au lefi nayi danna fafi gaskiya.


Zarah ta rufe fuska tn murmushi tace ai kaine kayi cikin ba waniba.


Dariya yayi ya kwantarda ita kan kirjinsa yace a a banda sharri ynzu kinga cik ajikina ?




Pillow tasa ta jefa masa ya rungumeta yana dariya yanai wa Allah godiya yace tafadi abunda takeso kafin subar kasar nan dan jibi zasu koma Nigeria .


Da murnarta ta Rungume shi tace banason komai se soyaiyarka .



Murmushi yayi ya kara rungumeta yn shafa bayanta .


⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–‹

πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

AURAN BABBAN

MUTM



🎁




πŸ…Ώ53



A kwana kin nan Musayyet shiyaken komai yayinda suka fita yafara jido layan baby .

Kafin sutafi seda suka sake meeting akan harkar company k'in zama tai agida ita lalle seta bishi don yasaba mata da tafiya duk inda zashi tare.


Ahanyane take cewa wai yanaji kana magana dayarensu ne koko damacen ka iyane ?

Murmusho yayi ya kalli gefensa inda yake driving yace na iya kinsan a kwai school dayawa anan wanda inde kazo karatu tosekafara koyan yarensu tsawon shekara daya ta nanne zakafi sanin yanda abubuwa sk tafiya dede.


Amma bakowace school ce keyin hakaba.


Zarah tace lalle nikam wannan yare yana bani dariya .



sungama kallama komai suka nufi Airport don zuwa Nigeria.





Aysha biki yataho kayan sawa me yawa ta dinka harda na zarah da sunan intazo tabata an huta kawai.



Alhaj Sa ed zaune kusa da Momy yana mata sannu khairat na danna mata k'afa .


Momy sannu aman ya tsaya ne ? Ummm ya tsaya baby na Dady ya shafi kanta yace ai taji sauki bazata sak aman ba.


Sallama sukaji kamar dg sama khairat ta tashi da sauri dan ganin kosu waye .


Dady yace shikenan ansamawa khairat k'ani tadena zaman kad'aita data keyi yanzu momy zatai magana kenan su ka shigo .


Da sauri ta mike da murnarta tn musu sannu da zuwa Musayyet da fara a face dinsa suka karaso zarah akanta na kasa Dady yacd shine kuma ba sanarwa haka akeyi.



Dariya musayyet yayi yace ai hkr dady bamason wahalar dakune.


Zama sukai kan carpet din dk malale a palon suna gaidasu yayinda suke amsawa cike da kulawa.



Tini aka cika ms gun da kayan ciye ciye yayinda musayyet yace su shigo da kayan dk cikin motar.


Kayan tsarabane kala kala harda kayan wasan khairat wanda zarah ta siya mt .


Dady na kallon musayyet da zarah yasan lalle suna cikin kwanciyar hankali sunyi kyau dasu .



Bangaren musayyet suka wuce da dare yayi tace bazata kwana a inda yakeba yayinda ya rufe kofar yace ba inda zata .


Haba dear ai se a ace bamuda kunya taha zamu kwana waje daya.

Dariya yayi yadauketa yace lalle yarinyar nan nine banda kunyar koke?


Murmushi tayi tana wasa da hannunta ya kamota ya kwantar da ita yn mata wasa gamida kashe fitila.



Bikin aysha yarage sati daya dan hk suka shirya gaba dayansu suka nufi kano.


Anan ne momy ta kula da yanayin zarah tagane cikine da ita.


murna sosai tayi sannan tayi ftn Allah yaraba lfy.



Gidan ammi suka sauka musayyet ko hotel ya koma crn Bristol palace""" bayan sun gaisa da Ammi.



Abinci aka dire musu ammi da murnarta tarbesu .



Kayan tsarabarsu aka fiddosu amota ammi se murna ake.

Da dare yayi malam yadawo aka gaisa .


Ammi tini ta kula da yanayin zarah dan hk suke bata kulawa komai idan zatai se momy tak saurin amshewa ko kuma ammi.




Aysha na shirin fita Zarah ta shigo ai da ihu sk rungume juna har umman aysha ta jiyosu ta leko taga zarah ce da murnar ta tace a a yau kune agari amarya ya megidan .


Zarah tai fara a ta gaidata tace lfy lau umma da ftn mumsameku lfy
Lfy lau sannu da zuwa




Tare suka fita dama gun gyaran jiki zata dan hk suka wuce tare.


Musayyet kullun ya kanzo sugaisa yayinda yake zama da zarah susha hira insun gama ya shiga gari da mota yn ganin yanda garin kano yk.



Ranar daurin aure musayyet yazo harda dady guri ya cika bayan gama daurin auranne yace zarah fa shi tafiya zasuyi .


Momy tace baka isaba abunda ko gama Bikin ba aiba .


Ammi tace yaran zamani kenan dariya sukai shide ya fita yn sosa kai.


Aysha da zarah yagani sun shigo tamakar itace amaryar ya tsareta da I do yna kallo.


Aysha tai murmurshi tacd ina yini""""" yai fara yace lfy lau amarya kinsa matar tawa se yawo tk ko.



Dariya tayi tace amin afuwa ciki ta shige ta barsu nan Zarah ta shafi face dinsa yajawota jikinsa ya shafi cikinta yace kinga idan wani abu yasami baby na akanki zan rama .


Dariya tayi sannan sukai hira ya fice.



Gaba daya suka shirya aka tafk gidan bikin yayinda aka kama waje babba kuma me tsada .




Washe gari tunda wuri aka wuce zuwa Abuja amotoci yayinda sukai sallama dasu ammi.





Wajen la asar sk isa Musayyet tun a hanya ya dauje hanyarsa ta zuwa gida tunda momy tace seya kyale zarah taje gidan amarya haushi yaji don hk ya dauke hanyarsa tun suna tafe.






Gidane mekyau ma alfarma komai yayi






Zarah daki guda sk koma da aysha sunata hira yayinda sauran jama ar suke masu bangaren daban .



Se goma naseer ya shigo da abokansa yayinda ya tabbatar da mutan agidan .


Dariya abokan sk shiga yimasa yacire hula yace akn uba wlh sena shiga dakin matata suna nufin dan sunzo shikenan bazan kwana adakin matataba.



Khaleel yai dariya yace to kai mara kunyar ina ne dazaka Shiga dakin matarka danginta na nan .




Naseer yai Murmushi yace kude kumuje.







Seda sk wuce 6angaren bakin sk isa bangaren amarya .




Suna kwance kan gado itada zarah sunyi rub da ciki sunta hira sukaji sallama.



Da sauri aysha ta figi mayafi tayafa zarah se dariya tk yayinda tafara shirin tashi.












Kai zarah yanzu tafiya zaki dan Allah """ zarah ta juyo tace a a zama zanyi a hada dani ta kuma shekewa da dariya aysha taja mayafi tana dariya itama.










Sallama sukai zarah ta amsa sk shigo ita kuma tai saurin ficewa tini ta daura nik'af dan kar wani ya ganta.


Waya taiwa musayyet ya dasuri ya dauka tace kazo ka daukeni ina nan Area B .


Murmushi yayi yace ai na dauka kwana zaki ayi amarcin dake.



Dariya tayi tace kafiye tsokana fa


⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š

πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


AURAN BABBAN

MUTUM


From Ummee Mukhtar

πŸ…Ώ54


END


Kwatance tai masa yazo har inda take ya dauketa suka tafi gida""""


Kai tsaye wani katafaren gida suka wuce wanda nesa yk da gidan momy .


Tace a a yanaga munwuce kuma ba gidan momy zamuba .


Musayyet kallonta yai yana mu murmushi yace munta kwana agidan momyn kenan ni hanani sakewa sukeyifa shikenan mutun ba dama ya huta da matarsa .



Mumushi tayi batace komai ba har suka iso.


Yn parking ya bude murfin kofa ya dauketa cak yai cik da ita tana dariya.


Kai tsaye wn room ya ajeta gamida cire mt kayan to jikinta shima yana kokarin cirewa tatashi da gudu tai hanyar wani toilet yak saurin kamota ta rufe idonta dariya yayi ya rungumeta gamida daukanda ya shiga toilet




Wanka yai mata bayan yacika bahon wanka da ruwan d'imi wanda yasha kayan kamshi da sabulai masu kamshi .

Cewa yai itama seta masa sannan zasu fita """tn murmushi ta hau yimasa shi kuma yana mata cakulkuli tana zamewa cikin ruwan shi kuma yana rungumota .

Alwala sukai sannan sk fito bayan sun gogd jikinsu ne sun shafa mai suka sanya kaya gamida tada sallah.



Koda sk idar sleeping dress ta sanya zata kwanta yace lalle setaci wani abun kafin tai bacci """tace nakoshi yanzuma amai nakeji sosai wlh.


Kamota yai ya kwantar da kanta zuwa lap dinsa yn shafa gashin kanta yace me kikeson ci yanzu.


Tace ba komai bacci kawai nakeji.


Yace ok .

Rungumeta yai ya rage hasken fitilun room din ya canja launi zuwa light blue .






Da asubah sukai sallah suka koma bacci se wajen goma ya farka ya zame jikinsa ya wuce kitchen ya dafa indomie waccd tasha vegetables da kifi ya hada tea se juice ya aje kan dining.



Karfe goma da rabi dady yakiarashi awaya yace ya baka fito sallar asubah bane banganka ba.


Musayyet ya hau sosa kai yace umm umm dama danaga dare yayi shine mk wuce daya gidan amma ayi hkr.


Dady yai murmushi irin nasu na manya yace bakomai ai hakamma yayi dede momy na gaidaku .


To dady zanzo anjima.

A a kai zamanka ka huta kajiko nan da sati 1 kazo kasan ba jimawa zakai anan ba sosamune nafison zamanka acen kana kula da harkokin cen .



Musayyet dama hk yakeso yace to dady ba matsala hakan za ai.



Dady yai murmushi dan ya gano bayason zaman nan




Zarah ce ta fito dg toilet brush tayo sanna tayo palor .


Yn ganinta ya aje wayar suka rungume juna yana jan jelar gashinta yace se yanzu da alamu wanna cikin yanada son jiki .


Kallonshi tai tn smile tace to ai kai yayo

Kallonta yai yace iyyee lalle yarinyar nan gama breakfast din yau zakiga yanda ake son jiki yinin yau bazan barki ki hutaba.
Zarah ta mara raice haba dan Allah nifa tsokanarka nk.


Dariya tabashi yace ai dankinga na kyalekine vakison tausayinki nakejiba sbd ga cikin jikinki ga kuma gajiya amma tinda hk kikace zakigani yau.



Zarah tai dariya tafada cin abincin ya matso daf da ita yafara bata itama tn bashi har suka kosar da juna.






Yinin ranar hk suka yishi cikin farinciki yayinda ya matsa mata da abu daya har sedata shiga wani room ta kulle door tn dariya sannan ya kyaleta .


Murmushi yk ya tsaya dede room din yace daga yau kyasa cemin baby na ni yayo .



Dariya take sosai tace bazan sakeba dan Allah katafk gidan momy .

Au korata ma kike ba inda zani .



Se bayan kwana 2 sannan sukaje sk gaida momy yayinda sk sameta se amai tk.


Hankakin zarah yatashi tace akira doctor momy tace a a kawai zazza6ine kuma ze dena.


Musayyet kallon momy yk takara haske yace karde ace cikine da momy """ya fada cikin ransa.







Sati 3 a tsakani sk koma Cairo anan ne sk bude sabuwar rayuwa me cike da farinciki yayinda sk ririta juna kamar sucinye juna .

Sun kara kyau da haske kamar ka ta6a jini ya fito .

Haka ya maida hankalinsa ga harkokin companyn dake cen .



Ryuwarsu abar burgewa ce ga duk wanda ya kallah yayinda yk matukar kishinta.





Seda watan haihuwarta ya kama sannan ya bigawa momy waya yasanarda ita """murmushi tayi tace ai na dauka bazama gayamana ba ninan natadani komai kasan me jego akwai son yaji
.
Zamuzo nan da sati daya base kunzoba .


Musayyet yace to momy.






Sati daya atsakani suka isa cairo harda su ammi da dady harda mahaifin zarah.

Mamaki sukai ganin momy da ciki ashe dama cikine da ita.



Sosai sukai murna zarah da musayyet dan ganin mahaifan nasu """"ammi se raba ido take wai yau itace akasar waje.



Bangare guda aka basu kowa da nasa momy da dady se ammi da malam


Musayyet da kansa ya jere musu kayan abinci .





Haka suka wuni sn hira washe gari sk fita ganin gari yayainda akabar zarah da musayyet agida khairat ko tn gidan fa eza

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment