Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka aje se wani soson wankan sabon brush da oralb suka sanya se Airfreshner suka turara room d'in da turarukan wata irin nasu masu kamshi suka jawo suka kulle.


Haka ka idar su take inde bako ya fita dg room d'in sa to sukan shigane su sake komai sabo sugyarashi .

⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š

πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

AURAN BABBAN

MUTUM


Crtng And Wrtn By

UMMMEE MUKHTAR🎁


πŸ…Ώ49

Wani lambu suka samu suka zauna wanda aka gewayeshi da kujeru na Alfarma dg kusa dashi wani babban swimming pool ne wanda akai masa zane na heart ruwa kwance cikinsa garai garai me sanyi dashi.


Musayyet ya zaunar da Zarah dg d'aya daga cikin kujerun dk zagaye agun dede saitinsa yana kallonta """"" yana kallon yanda ta k'ara haske da murjewa daga 'yan wannan kwanakin ,,,, eh lalle zama yakamashi anan inde Zaransa zataji dadin hakan.



Zarah na kallon yanda yakafeta da ido murmushi kawai tana kallon kallon gefenta taname wasa da k'aramin mayafin rigar dk mak'ale a wuyanta wanda tai rolling dashi.

Smile yayi lokacin dayaji phone din sa na ruri nan ya dauka ya mike tsaye gamida zura hannunsa cikin jeans din dk jikinsa yana amsa wayar.


Ok shikenan dady nan da kwana 7 ne tafiyar? To dady insha Allah zani """ a a my son nasanka bakason zuwa spain bansan meye dalilinkaba kode har yanzu k'yank'Γ½amin nasu kake?
.dariya Musayyet yayi yana kallo Zarah ya daga mata gira tai murmushi '"' yace no Dady ai yanzu ma girma banajin tsoron komaΔ±.


Hmmm Dady yai murmushi yace shikenan seka shirya komai na tafiyar daga nan zuwa lokacin .




Bayan sungama wayar ne yadawo ya zauna yn kallonta ya shafa kai yace hubby na tafiya zanyi yanzu dady ke sanar dani zaki iya zama ke d'aya kuwa.


Zarah jitai gabanta ya fad'i ta sunkuyar dakai tana maida k'walla wanda ke shirin zubowa.


Tasowa yai ya durkusa kan grass wacce ke malale agun ya kama hannunta yana shafawa yace is ok karki damu wasa nk miki""" taya za ai nayi tafiya nabar rayuwata kinsan hakan baze yuwuba duk inda zani kina tare dani kamar yanda zan kasance tare dake.

Se nan ta d'ago kai tana murmushi ya lek'a idonta yana smile yace sarkin kuka .

Smile tayi kawai batasan meyasaba bataso yi nesa da ita kwata kwata tariga data saba da jikinsa me laushi a 'yan kwanakin nan batajin zata iya nesa dashi.

Yace Zarah kinsan Manbila?

Kai ta girgiza masa yai murmushi yace nan ne asalin garimmu cen cikin wani daji wanda ba mutane dayawa cikinsa """" Kwata kwata bukkar dake cikin dajin batafi guda 7 ba wanda yawancinsu kiwone aikinsu """ basu cika zama waje d'ayaba sede dg wannan gari zuwa wannan gari .


Sunan mahaifita Shatu wanda sedana girma nagane duk me suna shatu ana nufin Aisha kenan.

Babana shine Malam Musa wanda tinkafin nai wayo Allah yai masa rasuwa .

Se yaiyena guda 2 duk mata wato Mulabi da kuma Sa 'ade.


Allah ya Alabarkacemu da shanu masu yawan gaske wanda duk rugar tamu bame yawan shanun mahaifina koda yk daka d'anne sukafi na makotammu """ Tin in yaro jinina yafi haduwa dana yayata Mulabi wato momyn Khairat """"" Musayyet ya kalli Zarah yaga ta zuba ms ido tana kallonsa sotake kawai taji yanda akai sukabar garin.



Tai kasa da kanta tace Allah yajikan baba yasa yahuta

Ameen Musayyet yace yana me kallon gefensa .


Yace tin ina shekara uku nasaba da shiga cikin shanu wanda ba abinda sukemin haka na maidasu abun wasana """kullun dagari ya waye Allah Allah nk na isa gunsu yayinda anty na ke dorani kan wata karamar saniya tana zagayawa dani.


Bishiya kam yanda kikasan dan biri da minfita kiwo da zarar an tsaya huta k'afa ko rangadi ko an tsaya dabbobi su sha ruwa senai saurin hayewa kan bΔ±shiya hk zasuyita nemana harsena musu gwarancina cewar gani anan sannan zasu sakko dani.



Zarah dariya ta kufce mata tasa mayafi ta kare face din ta ya kamo hannun yana daria yace dariyar me kike?

Batace komaiba illa wata dariyar data sk kufce mata yasake matseta jikinsa yanaiwa wuyanta kiss.

Zaki fada kosena sake abin jiya?
.da sauri ta tsaida dariyar ta turu baki tace toba kaine kace wai kamar dan biri ba.


Shima dariyar yayi yace eh man amma yanzj banajin zan iya wannan tsalle tsallen.





Akwai wasu mutane wanda ba Musulmai bane duk inda sukasan akwai wata k'aramar ruga sukan kai mata harine sukashe su kuma su debe duk abinda suke dashi tin daga kan dabba zuwa abincin ci.


Hakanne yasa bayan rasuwar mahaifiyarmu yazamana cewa semu uku muka rage .


Watarana cikin dare wa 'yan nan mutanan suka kawo hari wanda tin daga nesa mukafarajin ihunsu kamar na tsuntsaye wani tsohone ya farga da hakan cikin sauri yai inkiya wa mutanen rugar tamu kafin kame meye sun shigo cikin dajin .

Nan suka fara aikin zalincinsu wanda alokacin yaiyena bacci suke nina hau tashinsu.

A gigice babbar yayammu ta farka ta kaiwa Mulabi duka itama ta farka cikin kuka ta hau sheda mt abindake shirin faruwa .



Jikinsu na rawa suka hau kuka duk da yarone ni amma nai musu inkiya cewa dasuyi shiru kar ajisu.


Ta cikin bukkar suka lek'a nan suka hango har sunnawa wasy bukkoki wuta sun kwashe abinda ke bukkar.



Cikin kuka naga sun hau keta bukkar tamu ta baya da wata k'aramar wuk'a da alamu hanya sukeyi.


Ni momy tafara sawa sannan waje sannan sa ade ta fita itama momy ta fito dakayr jikinsu duk ya kuje da zanar bukkar kasancewar su farare nan da nan jikinsu ya hau jini kuma yai ja jawur .



Da sauri momy ta koma ta dakko wani kullin k'yalle wanda daurin kudine cikinsa ,,garin fitowarne tsautsayi yasa ta soke da wannan zanar bukkar a cikinta tasa k'ara sa ade tai sauri janyota ta rungumeta ganin yanda jini ke zuba ta gefen jikinta """ dankwalin kanta tasa ta daure mata cikin sannan ta goyata ni kuma tana rike dani muka nausa cikin daji """" ga uban duhu gashi dare yayi ko gabammu bama gani haka mike tafiya .


Hasken wuta kawai muka hango yayinda na juya bayana ina hango bukkar mu naci da wuta.


Sa ade ta gyara momy abayanta tana kuka mukaci gaba datafiya.



Zarah ta share hawaye tana kallonsa da tausayi fal cikin ranta.

Musayyet yai murmushi yace haka mukaita tafiya sosai nagaji amma banyi koda kukaba bami auneba seji mukai munfada cikin wani rami me dan zurfi.

Gashi duhune haka sa ade taita kokarin ganin munfito amma hakan beyuwuba haka ta hkr nasa kuka dan jin wani zafi a kafata .


Dake cikin duhune haka ta laluboni ta rungume ni jikinta inata kukan k'afa ta zafi akemin dan sosai nakrjin zafi narasa kona meye.

Rarrashina takeyi amma nakasa shiru itama kuka tasa yayin Momy take shashshrkar kuka tana kukan cikinta.


Zarah bamuda kowa balle musan inda mk nufa .


Daren ranar ba wanda yai bacci sbd azabar kukan danake sunyi rarrashin sun rasa ko kukan me nake.




Seda asuba tayi gari yafara haske suka fahinci a inda mike tashin farko kafata sukafa dubawa dan ganin komenakewa kuka jiya.


Nan sukaga kafata ta kunbura taija ashe kunamace ta harbeni.

Sosai hankalinsu ya tashi sukafara kokarin fita dg ramin.


Seda suka jera manyan duwatsu sannan daya tafara fita aka mikoni sannan momy ta fito.

Gab dazat fitone taga kunamar kwance jikin dutse momy ta koma ta dauki wani dutse ta rotsa mata """ saga 'k'wayaye nan dayawa kwance cikin cikinta.




Tana fitowa ta kwanta gefe tana maida numfashi sa ade se sannu take mata yayinda ta tsinko wani ganye kore ta dakashi da dutse ta murza jikin k'afa ta .


Dan kwalin dk daure cikn momy jini ya 6atashi dan haka sa ade ta cireshi ta dakko nakan momy ta daura mata bayan itama an goga mata wannan koren ganyen a zagayen cikinta.


Haka muka dauki hanya sa ade na goye dani yayinda mony ke tafiya a ahankali har muka iso gun wani rafi.


Alwala sukai sukai sallah nima sukai min wanka ta goyani mukaci gaba da tafiya.


'Ya'yan itatuwa sune abincimmu wanda muke tsinka akan hanya.


Se kuma ruwan rafi wanda shine ruwan shammu.


Munbar rigar wanda seda mukai kwana 4 muna tafiya sannan muka hadu da wasu samari suma fulanine sa6e da sandunan su se zomaye a hannunsu .

Da sauri sa ade tace Mulabi ga wasu cen koma iya neman temako gunsu?...



Momy ta dafe cikinta tana haki tace a a sa ade ni yanzu tsoron mutane ma nakeyi """ tunda sune sanadiyyar barimmu rigarmu gara mu kalesu sonake mufita akusada da garimmu.







Sa ade tace a a gaskiya gara munemu temako de ni wlh nagaji da tafiyar nan bakiji kafafunaba .





Daf da zasu wucene suka hango su zaune jikin Bishiyu samarin suka yo kansu suna tambayar ina zasu """"" momy tace a a akwai inda zamu kuje abinku kawai


Sa ade tai saurin cewa kyace da inda zamu bayan gurin zama muke nema .


Samarin suka dubi juna sukai murmushi sukace subiyosu sunada gun da zasu basu su zauna har tsawon rayuwarsu.


Ni kaina duk da inada karancin shekaru hk kawai naji ina tsoron mutanen .


Momy ta kafe kan cewa subarshi sun gode amma sa ade tace sesun bisu.


Suma samarin hk sukaitayiwa momy dadin baki har suka amince sk bisu.







Samarin na gaba muna bayansu cikin wani daji me duhun gaske suka jamu se kalle kalle nk ni kaina zuciyata rawa tk akan mutanan.



Sannu sannu har muka zogidan suma na bukkane guda 3 suka nuna mana wata bukka mk shiga yayinda suka kawo mana fura da kuma nono kowanne kwaryarsa daban




Nan dk a yunwace mk mukafara sha muka koshi .


sa ade ce ta fito ta iske samarin zaune da alamu wani abun sk kullawa na mugun abu akan yaiyena tace ko kunada maganin ciwo kanwatace taji ciwo ajikinta do Allah kutemakamin.


Saurin yace akwai magani ina zuwa.

Wata bukkarya shiga ya dakko wata jaka ta fata sannan ya fito suka rankaya inda muke zaune da momy .



Momy na kwance ta bude gefen cikinta dan yasha iska dan gun ya dan tashi .


Ba sallama suka shigo momy tai saurin tashi zaune tana rufe cikinta batai maganaba har sk zauna.



D'ayan yace sannu ko momy tace yauwa.

Miko mata wani garin magani yayi yace akwa6a da ruwa tasha gun daga hk ya fita yana kissima abubuwa dayawa aransa akan momy.

Momy ta dubi sa ade tace kirage kula mutanan nan banaso zuwa jibi insha Allah zambar gu nan hankalina ve kwanta dasuba baki ganin iri kallon daya ke min ne?



Kede Mulabi kinfaye mugun zato kan mutun aradu daga temako seyazama bala'i?





Samarin zaune abayan bukkarsu D'ayan yace waiko gaka abunda nagani ne ?




D'ayan wanda sunansa ja e yace nariga ganinkoma meye kuma aradu banbari tsuntsu dg sama kenan.




Yanzu yazamiyi.


Ummmm bari zami su saba damu mukuma maida maitarmu ciki dan karsu gane daga nan ninasan me za ai.



Dariya sukai dukkan ninsu sukaci gaba da busa sarewa me dan banzan dad'i game sauraro.


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


AURAN BABBAN

MUTUM


Crtng And Wrtn By

UMMEE MUKHTAR🎁


.kuyi hkr wlh kwana 2 ina busy ne sbd school shiyasa kukaji tsit ☺



πŸ…Ώ50



Cikin dare hk suka ishemu da bush bushe yayinda sk hura wuta da karare dan jin d'umi lokaci lokaci suna kallo bukkarmu """" bacci na nake amma seda momy ta tadani tabani kindirmo nasha ta wankemin baki sannan ta kwantar dani """"koda na kwanta ba bacci nakeba domin hk kirun nakejin tsoron kasnacewarmu agun ....

Sa'ade ta d'aga d'an mayafin daya kare bukkar wanda shine labule ta hango samarin zaune se hira sk suna dariya d'aya dg cikinsu ne ya rukida'a ya koma zomo ,,,, yayinda d'ayan yana ganin haka ya koma 6era suka kasa gudu cikin duhun daji.


Sa""ade tace kinganiba wlh mutanan nan shu'umaine jifa ana zaman zama ji yadda sk maida suffarsh.


Momy tatashi zaune dafe da ciki tace tomeye bak'onki anan dan kinga hk zasuyi avunda yafi hk ""ince ba zaman daji sukeba kuma fulanin asali ....



Sa'ade ta kwanta kusada momy suka fuskanci juna tace yanzu ina zamu idan munbar nan ?...momy ta shafa kaina na lumshe ido dan dama inajinsu ba bacci nkb.

Tace nima bansani ba nafi tausawa yaron nan gashi bamu ta6a shiga binni ba koda saud'ayane.

Se babammu shine wanda yata6a shiga yai wajen wata d'aya anan yaji sunayen yaran binni inna kona haihuwa yasaka sunan Nabeel .


Sa""ade tace Allah yajikan su da rahma rayuwar duniya ba komai bace face wata aba k'alilan kalli kamar bamj rayuwa dasuba ya wuce sunzama tarihi hk muma wataran zamu zama tarihi.

Daren ranar basuyi bacciba hk sukaita hira wanda Nabeel shima sam bacci yak'i zuwar masa duk da yn yarone amma se tinane tinane sk hanashi bacci.




Da subar fari sukai alwala gamida sallah gurin ba kowa tsit se kukan tsuntsaye """da alama samarin basu kwana agunba """""



Seda rana tafito sannan samarin sk dawo hannunwansu sa6e da namun daji kala kala kama daga tsuntsaye zuwa masu kafa hud'u.



Kamar abun kirki sk hau gasawa har cikin bukkarmu sk kawo mana yayinda su momy sukai musu godiya samarin sk fice .



Ni suka fara bawa nace banaci dan hk kawai nima nk tsoron mutanan """ suma basu Ciba nan gafe sk ajeshi sukai shirh suna tinani.


Fitanayi dan nani fitari duk girman gurin narasa inda zanyi sedana zaga bayan gurin na tsuguna.


Magana naji kamar dg sama wanda bako tantama nasan ta samarin nance dan kuwa nagane muryarsu.



Kabari idan dare yayi kai seka fara shiga idan suka neme yi mk gardama kasa wannan wuk-ar ka yanka ta abanza zamu temakesu .


Fitsarun da bn gamaba kenan na taso ahankali na kom inda mk .



Bancewa yaiyena komaiba harsedana tabbatar samarin sunbar gidan cikin hausawata mara fita nahau gayamusu abunda naji wanda na tabbata damu suke.



Sunajin haka kuwa sa-Β°ade ta kama momy ta rike hannunta ni kuma ta goyani cikin sauri sauri muka bar gun..
..


Tun da mk fara tafiya ba wanda yai magana har yamma tai mana muna cikin wani daji jikin wata bishiya muna hutawa.



Hawa bishiyar nayi wi nagani ko mun kusa zuwa bakin hanya amma naga akwai tafiya me yawa agabammu.


Ban sakkoba ina kan bishiyar kamar dg sama na hango d'aya dg samarin nan se dube dube yk da alamu musuke nema .



Cikin sauri na sakko nahau gayamusu nahau gaya ms na hango d'aya sunbiyo mune miyi sauri mugudu.






Cikin sauri muka 6uya bayan bishiyar dk me girmace .


Ta gabammu yazo ya wuce se zare ido yk hannunsa rk da sanda da kuma wuk'a.


Wata hanya yabi seda mk tabbatar tai nisa fito tofa tinda mk fara tafiya bamu hutaba seda garin Allah yawaye danni goyani sukai avaya aduk sanda na farka cikin dare zanji tafe suke ko hutawa basayi kuma basa magana sede laluben hanya.



Seda mukai kwana 3 ahanya sannan mk fito kan hanya ..



Kudi suka bada aka fito damu zuwa wani dan kauye namma bamu zaunaba mukaci gaba da tafiya har mukai akori kura aka fiddamu dg k'auyen tafi tafi har muka iso babbar wata tashar mota .



Ga mutane da yawa da alamu mota ake jira.

Nansu momy suka sayi kyan sawa kala dai dai irin namuna filani nima sksiyamin da sauran kud'in dk gunsu.


Kadancewar akwai toilet agun nan suka shiga sk sake kaya nima suka samu wata rumfa daba kowa cikinta sk sauyamin.





Se yamma motar tazo da gudu aka shishshiga nan tk motar tacika yazamana babu waje.



Haka mk hakura wata bata sake zuwaba sewajen magriba.

Shiga mukai sannan aka dauki hanya.



Kwandas'ta nata kar6ar kud'i yazo kansu momy tace ina zakune?
Kallonta yai sannan yai dariya yace kuda kuka hau motar bakusan inda kuka nufaba shinbakusan wannanko motar ina bace?.
Koda yk filani lamarinku se a barku kunfaye sakarci da abun dariya.

.gaba d'aya mutanen motar sukasa dariya.

Fuskar momy na kalla senaga sam batajk dadin maganar da kwandas tan yaiba .

Na had'e rai kasancewar akwai wn buzukusa damu dauke da butar k'arfe hannunsa amma babu shayi ciki "


Cikin zafin rai na fizge butar na rafkawa kwandas 'tan nan yasa ihu jama"ar dk motar sk hau salati direba ya tsaya yai parking kowa ya fito shiko kwandas'ta ihu kawai yk domin wajen idonsa nasamu.


Nan da nan guri yacika su momy se bada hkr suke amma direba yace sam baze yardaba ....


Niko inajikin momy se faman fushi nk dan naso ace bakinsa nasamu na bige ba idoba .

Hkr akaita basu dakyar aka samu suka daure masa gefen idonsa da tsimma sannan sk amshe kud'in gurummu duka wai zeyi magani dasu.

Sam sukaki yarda su amshemu amotar sk shiga sukaja sk tafi sk barmu .



Sa'ade tace oh damar hk yaron nan yk da zuciya?

Dubafa yarone amma wai har yasan yatarewa yaiyensa fad'a.


Momy ta kwantar dani kafadarta tace karka sake hk kodan gaba kaji idan kaji ana fada da manya kadena shiga.
.
Bancemata ko kalaba danni har ynz haushin sa nakeji cikin raina




Muna hk wt motar tazo wucewa mk tare mk shiga nan me motar yace kaduna zashi.



Se bayan munshiga ne momy tarokeshi kan cewa yatemaka ms basuda kudin zuwa.

Motar aka tsaida yace gaskiya sede kushiga boot dan bazaku taremin wajen zaman fasinja dazasu bn kud'i ba .




Ba musu mk koma boot ahakamma ai mungode """godiya sukai ms meyawa sannan aka fara tafiya.






Duk yawancin mutanen dk motar ba wani wanda yk da kaya wanda za asa a boot.



Tafiyace anayi ana hutawa har tsawan kwana 2.




Atasha aka zubemu kowa yakama gabansa.







Yunwa ce tasa na kasa koda magana "" lura sukai da hakan s'ade tace yaron nan yunwafa ykj .


Momy tace nima na lura da hakan.

Game abinci cen muje komasamu.


Wlh banason sk kaina a tsaka me yuwa amma kodan yaron nan bazan iya jurewa ba.



Sallama sukaiwa me abincin ta amsa nan sk roketa tabasu abincin da zasu bawa yaronnan inyaso ko aikine sa mata .



Matar babbace sosai ta kallesu sosai 'yammatan suka birgeta yaran matan fulanin usili kyawawa dasu .


Tace bakomai kuma zaku iya samu .



zuba ms tai meyawa duk suka cinye ga mamakinsu se sukaga tasake zuba musu wanda yafi nada yawa.





Nan ma sukaci har suka rage ""nuna ms kayan wanke wanke tayi harda shara """cikin sauri suka gyara wajen yai tsaf alwala sukai sanna n sukai sallah.






Har yamma suna wajen basu motsaba matar ta lura da hakan tace bakuda inda zakune?

naga dare yafarafa gashi shi rin tashi nk.







Sa'ade tace eh bamuda inda zamu bak'ine mu don Allah kitemaka mn.


Matar tace toni sunana hajja mama gidana yana nan vaya sede gidan hayane amma ni kadai nk zaune.

Idan kunga zaku rikΓ  temaka kamin ne da aiki sena daukeku akwai makaranta kusa da gidan shi yaron se a sanyashi.

dan naga alamar kamar bakuda kowa ko?




Momy tace eh hakane mngode Allah yasaka da alkhairi bamuda kowa gaskiya kam.


Matar tai murnushi tace kunga har abincin dare inayi amma svd wani dalili nadena kutashi mutafi zan kulle wajen.





Nan sk gyara wajen aka rufe shagon sk kama hanyar tafiya cikin ransu suna mamakin saurin amincewa datai dasu.


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š

AURAN BABBAN

MUTUM

Crtng And Wrttn By

UMMEE MUKHTAR🎁



πŸ…Ώ51

Gidane me d'akuna 2 se band'aki da k'aramin tsakar gida ,,,, suna shiga ta nuna musu wn daki tace nan ne gun kwanansu.

Godiya sukai mt sannan sukai alwala sukai sallah dan magriba tagabato .


Bayan sun idar sukai wanka sannan sk kwanta .


Hk rayuwar su taci gaba da tafiya tsawon sati d'aya kenan tare suke fita da hajja mama zuwa gun seda abinci yayinda sk mata aikace aikace.


Atamfofi ta siya musu kowa 2 akai musu dinki abinka da kyawawa sega shi sunfito kai kace yaran masu kudine.


Satinsu 3 tare da hajja mama cikin dare ciwon ciki yakamata ko safiya bata kaiba Allah yai mt rasuwa.


Nan fasuka tsure sk shiga tashin hankali dan iya zamansu tare da ita tn kyautata musu dede iyawarta.


Adaren suka tashi suka fita suna bubbuga kofar gidan wn bawan Allah dk makwabtaka dasu sk sheda ms.

Sosai ya tausaya ms yace suyi hkr da asubar fari zezo tare sauran jama ar gari a sallaceta.


Hk suka koma gidan ina rike da hannunsu duk inda zasu muna tare.


Kwanan kuka sukai daga baya sukai tai mata karatu da addu o I.


Da sassafe ko kofar gidan yacika harda mata sk shigo.

Wasu tsoffi ne sukai mata wanka aka sallace ta aka kaita .



Koda mutane sukaga har rana tayi ba a dora tukunyaba se kowa yafara zame jikinsa yana warewa ........πŸ˜… kun san mutuwar yanzu inde baka dashi sekaga gidan mutuwar ma wlh bazama akeba sbd babu muwalati🀭.




Washe gari da sk dawo sukaga duk uwar darince se bawanda yasake dawo wa daga mazan har matan.

Hk aka barsu abun tausayi.


Sunyi alqawarin bazasu ta6a mt kudin taba zasuyi mata sadaka dasu .


Hk suka fito cikin gari suka samu gajiyaiyu suk basu duk da suma suna bukata amma basu ta6aba .


Zaune suke qaraf agidan bako k'wayar hatsi dazasuci.


Oh ni yanzu yazami gade gurin zama munsamu amma babu abinyi yazami?



Momy tace kaina ya kulle kode zamu fita neman temakone ko masamu na jarin abincin tunda kinga wancen kudin da mk sadakar banamu bane hakkintane.


Sa ade ta numfasa tace hakane kuma kinga .

...

Sallama sukaji a kofar gida da sauri sk leka.


Wani mutun sk gani tsaye bako fara a be bari sun gaidashiba yafara jawabi.


Amm dama kafin ta mutu ta fada mk gidan banata bane ko yaya?



Momy tace a a amma kai hkr dan Allah zamuke biya ai mana afuwa .

Har yaushe zaku biya kunga damafa rangwami nai mata amma yau wata 6 kenan bata biyaba gashi kuma ta rasu. Ni gidana duk wata ake biyana tinda ta mutu yakamata kubarmin gidana .



Nabaku nan da kwana 2 .


Yana fadar Hk yai gaba avinsa.




Suka kalli juna suka numfasa gamida komawa ciki.


A tsakar gida sk zube suka rafka tagumi kowa yai shiru.



Kinga mubar mai gidansa tinkafin yai mana wulakanci sede kuma idan minfita ina zamu.


Sa ade tace shine abin ai .



Tsawon Kwana 2 daga makotansu ake basu abinci kuma yaune megidan hayar zedawo.




Tinda safe suka kwashe kayansawarsu suka bar gidan suname zubda kwallah.



Tsaye suke bakin tati misalin karfe 11 na safe kusan kowa ya fito kasuwancinsa kowa kagani sabgar gabansa kawai yk yayinda duk inda suka wuce se an kallesu an sake kallo sbd zun kara kyau da haske kamar ka ta6a jini ya fito """kai daga gansu kasan Allah yayi halitta agun amma kallo daya zakai musu kasan cewa su d'in bak'ine .


Nabeel na rike da hannun sa 'ade se kallon pistol d'in wasan yara yake yana me murmushi shikadai abinsa .



Motoci sk jira su ragu atirin sannan su tsallaka.


K'arar jiniya mutanen suka dinga jiyowa tindaga nesa haka yatabbatar musu cewa masu garinne tafe ahanya wanda dama tini ana ta sanarwa cewar cewar ze zo bud'e sabbin hospital d'in dayasa

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment