Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabar 'yan uwansu dg sassa daban daban .





Jirgi ya sauka aka shiga fitowa kowa cike yake da murnar ganin dan uwansa.




haka Aisha da Zarah sk sakko rike da hannun juna kamar wasu larabawa sanye cikin dogwayen riguna wanda sukai musu matukar kyau..





Wasu samari guda 2 se 'yammata 3 suka taho da dasuri sunawa Aisha marhaban kowanne seda suka hada kafada irin gaisuwae larabawa yanda suke din nan .




Cikin harshen larabci suke tambayar Aisha wacece wannan ?
.amsa tabasu cikin harahen su cewar a jirgi suka hadu kuma shine zuwanta na farko .



Haka suka gaisa da ita kamar yanda sukaiwa Aisha ba yanda zatai tinda hk Al adarsu take.







Aisha tace gashi zamu tafi wace unguwar kika nufa ne?




zarah ta daga kanta ganin wani bak'in hadari dake hadowa tace la karki damu yanzu wanda nake jira zezo a fada yayinda take k'ara kallon bak'in hadarin.






Aisha tace a a bazan tafi na barki ba ke daya zan jira har kema azo daukanki.









Zarah ita kam bataso ta takurawa Aisha ne yasa tai mata hakan.





Zarah tace yanzu zezo dan allah kutafi karki 6ata lokaci "" da kyar Aisha ta yarda ta tafi sukai sallama da zarah wanda bayan tafiyarsu ne da minti 10 ruwa ya kece kamar da bakin k'warya .












Zarah takasa shiga wajen da mutane ke zaune wanda duk larawabane gani take kamar kallonta zasutayi kasan cewarta bahaushiya ,hakan yasa ta raku6e jikin wata bishiya dede wani dogon gini ta k'ankame jikinta ruwa nayo feshi dede setinta.









Rawar dari kawai take kanta harya fara ciwo.









Musayyet a kwance A Green view hotel hankalinsa kwance kallo ma yake da alama wanda kesa shi kara nishadi shiya manta da wani zashi Airpot dakko Fa eza.








Seda yai minti 30 sannan yatashi ya fito ya shiga mota ya nufi gida "" dare yayi alokaci wayarsa yagani wacce tinda safe ya wullar da ita kan bed ya fita.




yn kunnawa yaci karo da tex din dady wajen 20 duk na fad'ane da nuna rashin jin dadin kashe wayarsa da yai.







Kai tsaye dady ya bugawa aiko Dady na dagawa yafarai masa fada abinda be ta6ai masa ba kenan arayuwarsa.






Musayyet yai shiru yn bashi hkr Dady yace kai saurani kasan girman lefin dakamin kuwa ayau din nan ?



idan bakason ranka ya 6aci maza katashi kaje ka dakko yarinyar mutane kasan hanyr dazatai eyyye ,,,wata sani a k'asar inba kaiba:


musayyet yace kai hkr dady nasan nayi lefi amin afuwa

Sallama sukai Musayyet yace lalle fa eza zakici ubanki tinda kikasa akamin fada .


seda yai wanka yasake kaya sannan ya fita.









Hankalin Aisha yakasa kwanciya tace wa kanin mijinta me suna Hamza AΔΎ khaiyam cewar ya juyar da motar zuwa Airpot.



Kai tsaye nan suka koma aka barau suka shiga wanda zarah a lokacin tabar jikin bishiyar ta koma wani babban palo na zaman matafiya.




suna shiga sk ganta se kunya ta kama Zarah Aisha tai murmushi hannunta kawai ta kama suka tashi sukayo hanyar fita """


Aisha ta budewa Zarah gidan baya suka zauna tace hmm kawata seda nace miki mutafi ki kaki yanzu muje gidana ki huta.


Zarah tace to ngd babban mayafi Aisha ta lilli6e Zarah dashi sannan suka dauki hanyar KEMPINSKI NILE CITY.



Wanda a time dinne Musayyet yashigo da motar sa Airport d'in sukuma suna fita Zarah kanta na k'asa tana rawar sanyi ya shigesu zuwa ciki .









Yana yin parking ya fito ruwa na dukansa bedamuba ya shiga yafara duban fa eza amma ba ita ba alamunta babuma kowa agun se ragowar larabwan da basu tafiba wanda baza sufi su 16 ba agun.





Wajen ma aikan waje yaje ya tambayesu shin basuga wata yarinya ba ?



Balaraban ya kalleshi cikin harshen turanci yace ok you mean nigerian girl?



MUSAYYET yace eh balarabn yace ai sun jima da tafiya wasu dazu sunzo sun dauke ta amota.











Musayyet ya dara hannu aka yace nashiga uku suwaye to wa'yan nan mutanen ?.



Wayara ce tai k'ara yaa dubawa yaga kiran Dady ne.

jikinsa na tsuma ya dauka yace helllllo dady ""

dady yace kaganta koba kaganta ????

Musayyet yarasa meze ce masa yai shiru cen yace a a wallahi.


Dady yace what kasan kuwa wacece to saurareni dakau kaji ba wata bace matar taka illa Zarah "" maganarta doki kunen Musayyet har jiri na dibasa yi saurin dafe wani k'arfe yana runtse ido.






Kasande ni bani ne mahaifinka na asaliba ba kuma na fada mk hakan bane dan wani abu a a sedan nasanar mk cewa akwai Aure tsakaninka da ita ,,,"" Wannan shine babban Suprise d'in danace zan maka Amma shinekai wasa rere ka6atar da 'yar mutane to wallahi nabaki nan da awa daya kalalubota duk inda ta shigΓ₯ kaji na fada mk.





Dady ya kashe wayarsa yana huci wannan wane yarone haka .





Musayyet ko yakasa cire wayar dg kunnensa kansa nasara masa idona yai ja yarasa inda ze nufa ze kai da komwa yake yace zarah itace matata? Ya dafe kai yace oh my Life ,,,da gudu ya fito dg Airpot din ya fito babban titi yana waige waige.












Ummuloce taku whasap no.09059343174

⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN* *BABBAN*

*MUTUM*

Crtng And Wrtn By

_UMMEE_ _MUKHTAR🎁_



πŸ…Ώ41




Gudu yake A mota tare da kallon kowace mota dake kan titin wai ko zega Zarah amma be ganta ba """" daga k'arshe ya fito dg motar ko parking beba ya shiga tare duk motar datazo wuce wa """" se mota ta tsaya haka zeta lek'e lek'e waiko tn ciki




Dare ya fara sosai har motocin dake kan titin suka fara raguwa """ Musayyet ya d'ora hannu aka ya Ilahi ina yarin yar tayine suwaye suka dauke ta?


Me zancewa Dady idan har yau ban gantaba,, kai banajin koda na ganta zan iya gaya masa"""to Amma idan yace na bata suyi magana fa? Ya qara furta hakan yaname shafa face d'insa da idonsa da sukai ja.



Gefen titin yadawo ya zauna lokaci lokaci yana bin duk wanda yazo wucewa da kallo .


Tashi yai ya shiga mota ya hau zagaye kowane layi inya shiga nan ya fita nan ""duk inda yasan mutane na taruwa dama inda basa taruwa seda yaje amma ba ita.



Kuka yasanya ya kifa kansa da sitiyarin motar yana dukan kansa """ Zarah wai itace matata kode da wasa yakemin """A cikin maganaΕ•sa banga alamun wasaba.


Wannan shine dalilin dayasa yabarta ta zauna a gidammu?

Ya sani ze iyai masa komai Arayuwa, domin tin yn yaro ko kallo yake inde yaga abu yace yanaso tofa ko babu shi A k'asar seya samo masa Aduk inda yake.


Kuka ya kara sanyawa yana tina mahaifansu dasuka rasu """ yana tina inda sukai rayuwa cikin k'ungurmin daji ba yawan mutane se dabbo bi da tsuntsaye ""Amma wai gashi shine beyi rashin komaiba Arayuwa duk ta sanadin Dady , Wanda dg k'arshe gashi ya sallama masa matarsa ta sunna domin kawai farin cikikinsa.


Hawaye ya share yana me kallon titi sannan ya kunna mota ya nufi gidan Television .






Yana zuwa suka tarbe shi cikin yaren larabci suke magana inda yai musu bayanin 6atan Zarah """ nan suka buk'aci daya basu pic din ta ta nan ne za afi samunta da gaggawa.


Hannu na rawa Musayyet ya ciro wayarsa ya shiga tura musu har guda 3 """transfer d'in kudi yai musu ta bank wanda kudin cigiya ne.



Number waya ze basu suka ce ai sunada number base yabasu ba .

Godiya yayi ya fita kai tsaye gidan redio ya nufa nan ma yabada sanarwa """ . Be koma gida ba haka yaita yawo a gari tare da sauraren kiran waya dg kowane bangare tsakanin gidan television da redio.

Duk ya fita hayyacinsa lokaci daya Abun tausayi

Aisha basu zame ko ina ba se KEMPINSKI NILE CITY wanda Anan tamfa tsetsen gidanta yake na Alfarma nagani na fada ginin Larabawa masu dashi.



Fadar tsaruwar gidan 6ata time ne domin komai k'irar gold akayishi wato ruwan golden .




Masu gadi suka wangame babban gate din suka shige ciki.


Nan suka fito Zarah se k'areww gidan kallo tk Aisha ta rike hannunta sukai ciki se hira tk mata .




A wani palo suka zauna wanda girmansa ya wuce misale domin upstair 4 ne a palon ta ko ina zk iya hawa sama

Aisha tace Zarah zauna ina zuwa ko.


Zarah tace to . 'Yam matan wani daki suka nufa suma dan canja kaya


Zarah ta bude baki tana kallon kyawawan fitulin dk mak'ale a tafkeken palon tai saurin yin k'asa da kanta cikin ranta ko cewa tk oh """ Abin da nk gani A TV yau gashi azahiri wannan waje haka gaskiya Aisha bansamma wace irin sa a ce da ita ba.


Jitai Hamza Alkhaiyam yace mata" min fadlik khudh Ashyi """ tai saurin juyowa tn kallonsa Cup tagani a hannunsa karami me dan murfi abun sha a wa /////// itakam daba dan taga cup d'in tea a hannunsa ba sam bata gane meyake nufiba

Da murmushi ta amsa tace masa shukran ":"" shima fara a yai mata yabar gun.




Zarah takai cup din bakinta taji wani kamshi ga dadi dk ratsa kanta .



Mintuna kadan Aisha ta dawo rike dawata leda me kyau tace nabarki ko yi hakuri fa ina shiga megidan ya kira .


Ga wannan kinga wani room cen kije ki wanka seki sauya kayan jikinki.



Zarah tai murmushi tace dakin barshi bakomai.


Aisha tace kinga ki daukeni yayarki kuma kanwarki Aminiyarki dan Allah,,,, kece kadai fa wadda nk ganin minyi dede da juna a shekaru kozan girmeki befi irin da 2 yrs d'in nan ba.



Zarah tace shikenan bari na kara hutawa senai wankan. Aish tace to. Kallo Aisha ta kunna TV musu yayinda kannen mijinta suka shiga aje musu abinci kala kala .



Gaba daya suka zauna sunaci wanda yai dede da shigowar Dr Muhammad sanye cikin fararen kaya riga da wando me ratsin kore.



Da gudu Aisha ta tashi ta rungumshi sunaiwa juna oyoyo.





Zarah na kallonsu har sk zo suka zauna kannensa sk gaidashi nan take suka juye harahen Larabci wanda anan tk shedawa mijinta a jirgi sk hadu da ita harma wanda zezo daukanta yai delay shine sk taho tare.







Da turanci sua gaisa da Zarah cikin kulawa yk amsawa har yn tsokanar Aisha wai tasamu k'awa.


Dariya sukai gaba daya Zara ko cikin ranta tace ai wlh nima makarantar koyon larabci zan shiga .



A tv aka hasko hotunan zarah tare da bada number ga dk wanda ya ganta yakira dan Allah.



Muhammad da Aisha da ido sukebin TVn da kallo suna kuma kallon zarah Aisha tace Alhamdulillah da sauri Muhammad ya shiga sk number awayarsa ringing daya aka dauka """ Kamar jira ake akira dama .


Musayyet ganin bakuwar number da sauri ya dauka yace an ganta? Ko jira a gaisa beba yahau tambaya danA k'age yake
.


Muhammad yai dariya yai masa kwantacen gidansa yace ai yasani koba gidan Dr Muhammad ba
?




Sosai yai mamaki taya akai ya sanshi Amma yace eh nan ne .



Da sauri ya figi mota se gidan Aisha .





Zarah jikinta yai sanyi har tsuma take dan har yanzu bata yarda da zancen momu cewa Musayyet ne mijinta ba.









Aisha ta taso gunta ta kama hannuta tace muje ciki.




Wani daki sk shiga ta nuna mata toilet .

Wanka zarah tayi ta goge jikinta ta fito Aisha ta nuna mt wata riga Ash colour me santsi da mayafinta se takalmi shima Ash.



Godiya tai mata tace no karki sake banaso murmushi tayi kawai ta shiga gyarawa.


Aisha tace nifa ina tsoro kar yayanki yace sace ki mukayi.



Dariya Zarah tayi tace haba de wane irin sacewa daga taimako.





Kai kinga na manta Ance dana sauka na kira amma kinga na manta""" Aisha tac yanzu idan min fita palo seki kira ko.



Zarah tace eh.




Zarah kam tayi kyau sosai harta gaji rigar kamar dan ita akayi kasancewar kusan tsawonsu daya da Aisha .




Bayan ta kammala Aisha ta feshe ta da tura re sannan sukayo palo.




Ba kowa a palon zama sukai suna ci gaba da hira kai kace sunjima da juna.


Muhammad ne ya fito rike da waya a hannunsa yai waje yana magana.






Yana fita ya tadda musayyet Tsaye jikin mota se zage zage yake kamar wani zaki.


Da fara a face d'in sa ya karasa gun Musayyet suka gaisa cikin harshen Arab nan yabashi damar shigowa ciki .


A tare suka shigo wanda yai dede da dagowar kan zarah sunata dariya ita da Aisha da alamiu hira tayi dadi.








Musayye ne kan gaba kamar shine megidan πŸ˜‚ se kalle ko ina yk ta ina ze fara ganinta?



Karaf sk hada ido da juna Zarah zumbur ta mik'e tsaye tana kallonsa ko kiftawa batai """ Musayyet kam jiyai kamar anjona masa shocking tsikar jikinsa duk ta miΔ·e baya ko dauke idonsa dg kallon Zarah .



ASHE DAMA DA GASKE DADY YAKE .



zarah itama cikin ranta tambayr kanta take Ashe zasu kasance A inuwa daya?
o



Muhammad da Aisha kallon ikon Allah kawai suke da alamu wannan masoya ya wuce a ce soyaiyar yaya da qanwa ne .



A hankali Musayyet ya fara taku yana me nufarta itako ta tsaya kamar soja bata ko motsi.





Murmushi kawai Aisha da mijinta sk suna ganin soyaiya Zallah.




Sedaya zo har gabanta ta yanda yana iya juyo Ajiyar zuciyarta sk kalli juna cikin ido """ Bakinsa kamar meson magana itama batai Auneba taji hawaye na zubo mata kan face.


A hankali Musayyet yasa harshe ya lashe hawayenta Aisha ta runtse ido gamida nifar Muhammad ta kama hannunsa sukai cikin daki se dariya suke.


Zarah ta rufe ido tanajin yanda bakinsa ke zagaye sassan face dinta har k'afafunta na gaza daukanta .


Wata runguma yai mata yana kuka cikin sauti mara fita itama kukan take yana shakar turarenta me kamshin gaske.

Da sauri ya cikata yana me tino wani Abu cikin ransa""" shin me yake shirin yi Shifa har ynz beda tabbacin Abin da Dad yace masa
.




Dafe kai yayi jikinsa narawa""" juyo wa yai yn kallon Zarah wacce itama tajuya baya tana ganin Abun kamar amafarki.

















Hannunta ya rike yana murzawa cikin nasa batare daya kalli inda takeba.

⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

AURAN BABBAN

MUTUM


Crtng And Wrtn BY

_UMMEE_ _MUKHTAR🎁_


πŸ…Ώ42


Mik'a Godiya ga Tarin Makaranta Wannan Novel Ngd Ngd🀝🏻😊






Zarah najin yanda Musayyet ke murza hannunta amma sam takasa hanashi sede kunya da mamakinsa ta lilli6eta """ A hankali yai tattaki gareta ya juyo da kafad'unta zuwa gareshi kanta na sunkuye yasa face d'insa dede kunnenta cikin murya tajan hankali yace ina miki barka da zuwa Momy na,,, Ko zaki iya kiran matar gidan tafito miyi sallama?



Motsi tk da mouth d'in ta wanda Musayyet duk juyin datai idonsa akanta""" sake rad'a mata yai kamar d'azun cewar tai magana matar gidan ta fito sutafi """ Ahankali tace ta d'aga masa kai Alamar to.

Murmushi yayi sannan yacikata ya koma waje d'aya ya tsaya kamar soja.


Zarah tarasa ta inda zata fara nan cikin murya k'arama tafara kiran Aisha """

Aisha wacce suke d'aki da mijinta tun d'azun sunata hira akan Zarah cewa da Alamu kode matarsa kode mosiyarsace irin wannan kallon juna haka.


Muhammad yace kin manta ganina dake haka nakafe ki da ido ?

Tai smile tace hmm kajika bari naje,,,,: naji kamar tana kirana zomuj tare ""watakil tafiya zasuyi .
Muhammad ya rike hannunta suka fito da fara-'a """..Akan face d'insu.




Musayyet ya maida kallonsa gakansu yn sha'awar soyaiyarsu """ Zarah ko kamar wacce aka zarewa laka tayi lakwas da ita """"jin muryar Musayyet tayi yana fadin mungode fa Allah yasaka da Alkhairi """yau da ban kuba dana rasa k'anwata yai maganar yn me kallon Zarah.



Aisha tai murmushi tace ai bakomai munzama d'aya yanzu sekabamu Adress idan an kwana 2 zamuzo muma ta fad-a taname jijjiga hannunu Muhammad wanda ke kallon ta yace hakane my k'albi.




Musayyet yai murmushi yace hakane ai ba wani 6oyaiyen waje bane """ idan kika marrit hotel to layin dake tsakaninsu na 3 wato El Tawrah council Zamelek palce"""" a nan ne gidan nawa yake Area B"""


Muhammad yace nasani bama nisa Insha Allah zaku gammu.



Musayyet ya Mik'a masa hannu sukai musabaha """Zarah tai murmushi tace to Aminiyata ngd sekin ganni.


Aisha ta Mik'a mata hannu da fara 'a arta Zarah ma haka suka dad'a yiwa juna bankwana .




Har bakin gate suka raΔ·osu aka zuba trolley d'in ta a boot, seda suka shiga mota sannan suka juyo gida rungume da juna .





A mota Musayyet yakasa furta kalma koda guda sakamakon wani yanayi dayakeji atare dashi.


Anya ba wasa suke masaba?

Kod turota akai tai karatu anan ne?


Ashhhhh Abunda yaji kenan Zarah ta furta yai saurin kallon gefenta gamida parking yace momy na what's wrong?


Kai tadafe had'i da cuno baki tace kaina ne





Hannunsa na rawa ya dafe kan nata yaji da d'an zafi kadan yace sorry Momy na munkusa zuwa gida .



Idonta ta bude a hankali jin yace mata Momy wato shima yasan kamar Auran nasu na wasane shiyasa yake cemata momy.



Ta kalle shi tace thanks""".. yai smiley yace for what?


For Averything.

Murmushi kawai yayi yaci gaba da driving har suka zo gida.

Da hanzari gateman wanda ke kira da Ahmad yazo ya bude gate yana musu marhabin .






Shiya fara fitowa ya bude mata murfin mota ya rik'e hannunta yajawo ta jikinsa ya d'ago face d'in ta yace muga idon """kokinajin bacci ne?


Zarah mamakinsa take wai yau my son shine rungume da ita haka?


Tai k'asa da kanta tn kokarin kwacewa yai smile yacikata gamida bu'de boot ya dakko trolley d'in ta """"" ...jikinta na kankame da hannunta haryazo inda take ya kuma riketa sukai ciki itakam se mamakinsa take """lalle bede kunya.





Babban palone suna shiga sanyin AC ya bugeta ti saurin dafe kanta ta runtse ido.


Musayyet be kula da itaba wani daki ya nufa ya aje trolley d'in sannan yadawo palo.



Kanta ta d'aga tana kallon palon sak ba abunda yarabasu dana Aisha """wato ta fuskanta duk kusan masu kudin Larabawa hk tsarin ginin su yake gwanin ban sha'awa.





Shima upstair 4ne sannan duk adon golden ne se kaye kaye irin na Arab kama daga flawera kyawawan kwalaben turaruka da irin frame frame masu adon zinare.







Akwi rooms kamar guda 5 manya dasu wanda hade suke da toilet gefe guda kuma akwai spare part na chairs da glass table medium me kyau dashi.




Zarah bata gama kalle kallen taba taji an d'afeta da jiki me laushi kamar lallausan zanin gado.


Wani ihu tasanya Alokacin Musayyet na k'ok'arin dakko mata juice a firij""" wurgar da kwalin juice d'in yayi yn k'ok'arin ganin Abunda takewa ihu.



Dariya ya kamayi ya zube kan wata farar kujera yn kallon Zarah yana shafa kai.


Wajenta tayo be au neba yajita akansa ta cukumeshi kamar zata shige cikinsa.




Kukan gaske yaji tanayi Abunda yasa yΓ i saurin dagota kenan yai cilli da farar magen data hau jikinta.

Rarrashinta yashiga yi yana rungumeta gamida shafa bayanta yn cire mayafin data zagaye kanta dashi.


A hankali Salon yasoma sauyawa da wani zazzafan romance dayake mata ita kam kokarin janyewa take amma ya rumgumeta sosai .


Da sauri ya cikata yana rufe ido yana budeshi " dafe kai yayi ya mike tsaye yana nufarta yayinda ta durkushe a kasa.


A hankali ya maida zancen wani salo yace is ok she's gone .


Ta d'ago da kanta tana kallon d'aya bangaren taga ko magen ta tafi""" Aiko magen tagani kwance kan wani lallausan carpet tayi lamo tn kallonsu.


Se yanzu taga kyawun magen farace me 'yar k'iba ga gashinta fari me yawa kamar Auduga dan alaushi.



Murmushi taiwa magen ga mamakinta se taga magen tataso har da sauri tana nufo ta .



Zarah tai saurin matsawa kusa da Musayyet ta dafe lap d'in sa shiko da ido yake binta dan tafiye tsoro da yawa.


Magen na zuwa gunta ta Mik'a mata hannu "" da sauri itama magen ta Mik'a mata hannu kamar suna gaisaawa d'in nan ""..Zarah ta kalli musayyet da busasssun hawayenta tai murmushi



Shima smile yai mata ya dauki magen yanai mt wasa hadi da shafa kanta """""...itama magen wasa tk masa kamar jira take ya tsokaneta.



Zarah murmushi takamayi gamida nufar wani daki "" Musayyet tsaye ya mike magen na kafadarsa yace ina zaki?





Bata juyoba tace zani na kwanta ne.





Yai tattaki har gun ta yace Amma zaki iya kwana ke daya kuwa?




Wasa take da hannunta tace eh zan iya kwana.




Yace to muje na rakaki.




Har dakin yarakata kuma har zuwa yanzu magen na hannunsa a rungume yace akwai snack A firij koda zakici """tace na koshi nΔ±


Yace toko girka miki wani zanyΔ±?



Tace a a .







Smile yayi yace ok seda safe """batare data juyoba tace to.






Kofar yaja ya rufe sede ya tsaya yn wani tinani .



Seda yai 10mnts sannan yabar wajen ya nufi tangameman dakinsa.






Wa yarsa ya cira yafara kiran Momy bayan sun gaisa tace ina Zarah ?



Yace tana daki to inaga ko tayi bacci ma ynz.



Allah sarki ashe ka ganta ?



Yai murmushi yace damafa wani mall taje siyan wani abu ko wajen ban bari ba tadawo.

Momy tace masha Allah kahadani da ita gobe ko.



Yace to Momy .



Sallama zasuyi yai saurin cewa Momy wai da gaske kun Auramin Zarah ?


Ita kuma fa'ezan wa kuka Aura mata?




Momy ta kalli dady wanda duk yanajinsu yai murmushi nasu irinna manya "" momy tace Fa eza Abokinka Umar ne ya Aureta .

Ita kuma Zarah muka yanke shawaran Aura mk ita """idan kuma baka sonta sekai mata visa ka dawo mana da abarmu gida.






Musayyet da sauri yace haba momy daga tambaya?





Dariyar Dady yaji shida momy ai da Sauri ya kashe wayar cikin jin kunya yana murna da farin ciki ya d'aga magensa sama yana juyata .





Toilet ya shiga danyin wanka cike da farinciki fal ransa ,,,, "" wai yau shine Zarah tazama mallakinsa.




Adaki zarah tsorone yakamata ganin girman room d'in gari guda dashi wanda aka shinfida masa white bedshit se pillows wanda zasukai 8 manya da kananu.





wanka tayi ta fito daure da tawol ajikinta daman tayi alwala ""zama tai Abakin mirror tana busar da gashin kanta.



Musayyet bayan ya fito dg wanka 3qauter ya sanya se karamar riga bayan ya feshe jikinsa da turare ya nufi dakin zarah
..



da gudu magen ta biyoshi wai zata bishi yasa hannu yace mata shiiiiiiii go back ba inda zaki bini ya fada yn me yiwa magen murmushi gamida rufe k'ofa.

































Miyauuuuuuu Anbar mage gadiπŸ˜ΈπŸ˜ΈπŸ˜ΈπŸ˜ΈπŸ˜ΈπŸ˜ΈπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ€£








My WhatsApp

2 Comments On AURAN BABBAN MUTUM
avatar
hausa

1 year ago

Reply

Yes Thanks

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to hausa

Aha

Please Login or Register in order to submit comment