Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa abbanta, bayan a gaban shi faruk din ya furta yana sonta da aure ?
uwa uba yaron na ganin kima da mutuncinsa har rokonsa yayi ya sanya masa baki ,yanzu azo a wayi gari yaji ance shima sonta yake ,me zai d'aukeshi ?
" ai girma ya fad'i daga lokacin zai zamo baban kwabo a gurinsa .

"Koma dai menene shi ya hakura daita ,zai yi iya yi ya manta daita a duniyarsa ,zai yi jinyar zuciyarsa zuwa wani lokaci ,kafin ya samu wacce ta dace da rayuwarsa ya aura , dama Kuma haka duniya take, ta gaji haka arayuwa ,ba komai kake so kake samu ba .....

Shiru ne ya ratsa parlour'n , Dr jamil bai yi yunkuri sake cewa komai ba ,yana zaune jugun ,tunani kala kala ne a cikin zuciyarsa ,har ga Allah baya son rasa yesmin a rayuwarsa ,ba dan komai ba sai dan tasirin datayi a cikin zuciyarsa ,yana jin tsoron rasata ,yana jin tsoron abinda zai je ya zo .....
"Haba jamil ka fad'a min damuwarka da yarinyar da kake so, ko yar gidan uban waye ,wallahi zan nemo maka aurenta, kaji na rantse ,ko yarinyar bata sonka ne ?
Ya jefa masa tambayar yana tsura masa ido saboda ganin yadda zuciyarsa ke beting fast ,"ka kwantar da hankali plz ka fad'a min bata sonka ne kake fargaban fad'a min?
"Tana Sona Habib soma kuwa mai tsanani ,haka nima Ina son yarinyar fiyye da tunaninka ,sai dai wani abu yayi min shigar sauri , wanda yasa na rasa .....na rasata ta har abada bazan sameta ba , amman na d'auki kaddara habib ,"na rasata a lokacin da banyi tsammani ba ,saboda daf take da zamowa mallakin wani ....

Jiki a sanyaye abban yesmin ya zare hannunwasa dake cikin na Dr Jamil ,ya dafe goshinsa dashi "oh my goodness God Dr me yasa kayi wannan sakaci ?
",kunbikunbiya ka dinga yi da soyayarta tun kwanaki ko ?
Dr Jamil ya d'aga masa Kai al'amun eh "
Abba ya furzar da iska Mai zafi yace "okay duk da haka bazamu yi sanya a gwiwa ba ,ya kamata mu..."bai kamata ba habib ya katse shi ta hanyar fad'a masa haka ,"babu abinda zamu iya a kan lamarin daya wuce hakuri .....
"Ni na hakura kayi min adduar na manta daita da a rayuwa wanda nasan hakan da wuya da ciwo a rayuwata ....

Shiru sukayi gabad'aya kowanne da abinda zuciyarsa ke sakawa ...
Lokaci yaja sosai habib yana tare da Dr yana rarrashinsa tare da bashi baki ,kafin daga bisani yayi masa sallama ya bar gidan yana matukar tausaya masa .

*******

Tsawon kwanaki uku kenan yesmin ke cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ,ta saka wancan, ta kwance wancen,duk a kan Dr Jamil, kallo day'a zaka mata kasan tana cikin damuwa ,har ummanta ta fuskanci tana cikin damuwa ,saboda yawon tunanin da take ,gashi tayi wata uwar rama , a safiyyar ranar ce ummanta ta tsareta a d'akinta lokacin da tazo gaishe daita, bayan ta gaisheta tana Shirin barin d'akin umma ta Kira sunanta ,ta juyo a hankali tana dubanta "kizo kin wani tsaya daga can ni kike son na biyoki tayi mgnr ranta a 'bace ?
,ta tako kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta samu guri kasa ta zauna ta tankwashe kafafunta tana kallon yatsun hannunta , gabad'aya tayi wani iri daita duk ta daburce , idanunta ne suka cicciko da ruwan hawaye "yesmin ......umma ta sake kiran sunanta "
Ta d'ago kanta a hankali tana kallon umma ," a cikin kwanakin nan ,na lura kina cikin damuwa kinyi baki kin rame meke damunki ?

Yesmin tayi shiru ta danne kukan dake Shirin kufce mata, jikinta da zuciyar suka d'auki rawa "kin yi shiru kina jina ,"meke damunki?

still shiru tayi tare da sunkuyar da kanta dan bata san me zata cewa ummanta ba ,idan ma ta fad'a ba fahimtarta zatayi ba ,sai ma k'ara mata damuwa da zatayi"

"ko duk son Dr jamil din ne ya maidake haka ?

A gigice ta d'ago kanta tana kallon mahaifiyarta hawaye na gangaro mata bisa kuncinta, dan zuwa lokacin ba zata iya rike hawayenta ba .
"Kuka yesmin akan soyayyar tsoho," ke yanzu ko kunya bakiji ba ace kina son tsoho sa'an babanki, inda matashi mai sabon jini ke haukan sonki "
"me zakiyi da Dr Jamil saboda Allah da annabi banda fitina irin taki ?
"Aiko gama fad'ar haka da umma tayi, ke da wuya yesmin ta rushe da kuka tana sarke hannuwanta cikin juna dan ita sam bata ga wani abun ki a gurinsa ba ,wata Killa ma abinda yake mata wani matashin bazai iya ba ,ita dai da zaa aura mata shi tana son kayanta haka ,Kuma zata zauna dashi ,ta rayu dashi muddin rai. ... .

"Umma ta tsura mata ido tana kallon ikon Allah tana sake mamakinta ,a wasu lokutan tana bala'in jin haushin diyarta akan Dr Jamil ,yayinda wani sa'in bata jin hakan ,dan babu abinda sabo baya jawowa ,a yanzu ta gama fahimtar ba son Dr Jamil diyarta keyi ba ,kawai dai tsananin sabo ne dake tsakaninsu , amman zatayi iyakacin kokarinta taga ta yanke wannan halakar ...

sannu a hankali ta mike ta kamota ,ta zaunar daita a gefen gadon, har lokacin ta kasa d'auke idanunta akanta kuka take sosai .
"kukan ya Isa haka yesmin nasani bayin kanki bane ,sabo ne wanda hausawa kewa lakabi da sabo turken wawa ...
" bancin babu yadda za'a yi ace kina son Dr jamil bayan ga faruk had'ad'den matashi mai jini ajiki ,Wanda jininsa ke rolling ,matashin da duk wata matashiya zata so ya zamo mallakinta ..

Sosai yesmin take kuka har da shesheka " shi Dr Jamil din da kike so yana sonki ne ko kawai taron aradu da fad'in Kaine ya sa kike hauka akansa ?
Yesmin ta d'aga mata Kai tana zubda hawaye, "Yana sonki kika son cewa ko me ?
Ta sake d'aga Kanta ,sallati umma ta saki tana jujjuya hannuwa "lallai ya cika tantiri ai kuwa ba zai ta'ba samun nasara akanki ba ,ke bama sonki yake ba ,wallahi ko ya aureki wuya zaki Sha a hannunsa , mutumin da bai haihu ,har matarsa tagama tsawon zamanta a gidansa ko 'batan wata bata ta'bayi ba, shine ke Dan karambani da iyayi ki rasa Wanda Zaki zaba abokin rayuwarki sai tsoho mara haihuwa?

"yesmin Anya kuwa kin kyautawa kanki ?
"To nabari kiji na Gaya Miki kamar yadda na fad'a miki a wancan ranar ,karki sake abbanki yaji wannan mgnr , dan shi abinda zai Miki sai ya fi komai radadi da muni a gareki ,ta k'arasa maganar tana tausasa muryarta "ke yanzu a kanshi kike wannan kuka kmr ance Miki nice ko abbanki wani ya mutu ?
"Aiko mutuwa mukayi iyakaci kukan da zakiyi kenan shasha mara tunani ,ga yaro na sanki kice ke sai tsoho ,Ina umartaki ki aure faruk ,domin zai fi kula dake akan wannan banzan Dr din ,faruk zai gatantaki ,saboda son da yake miki , duk wani Abu da kike tunanin wancan tsohon banza zai Miki faruk zai Miki fiyye dashi ,shima da yake wankenke jini .........

Yesmin ta fashe da Kuma tace "duk duniya bani da Mai Sona wallahi irin uncle jamil ,bani da masoyi kamarsa Kuma baxlzan ta'ba samu Mai Sona kamarsa ba ni dai Ina son shi umma ta fad'a cikin daburcewa ..
Ai kuwa umma tayi shiru ta tsaya kawai tana kallonta dan maganar ta zo mata banbarakwai ,kusan minti goma tana zaune ta kafeta da ido tana kallonta mamakinta fal cikin zuciyarta ...


Ganin yadda hankalinta ke k'ok'arin barin gangar Jikinta ,yasa umma rungumota zuwa jikinta "ya Isa kuka ta shiga rarrashinta tana goge mata hawaye ,"kiyi hakuri, ki auri faruk kinji , sannan karki bari abbanki yasan da batun nan,dan komai zai iya faruwa, nasan bazaki so sa'bani ya shiga tsakanin abbanki da uncle jamil ba ,ko kina son suyi fad'a a sanadinki ?

Yesmin ta girgiza Kai umma tace "to kukan ya isa ,ki d'aure mubi komai a sannu kinji diyar Albarka....
Umma ta cigaba da rarrashinta ,tana tauye yarinyar ne ,bisa rashin sonta ga Dr Jamil, shiyasa kullun take tsoratata da karta sake abbanta yasani ,wanda ita tasani matukar habib zai ji ,to da wuya bai bashi auren ba ,kodan farinciki yesmin din ....

********

Yesmin taso kwarai ta share da lamarin Dr Jamil ,ganin yadda yayu watsi da lamarinta, gashi ko nuna damuwarsa ba yayi idan ya ganta da faruk sai ma murmushi yake sakar mata , murmushin da tayi wa lakabi dana yaudara da wulakacin ,yanzu ma shigowarsa kenan daga maiduguri ko gidansa bai shiga ba ,yashigo gidansu ,aiko idanunshi sukayi mugun gani ,faruk da yesmin ne zaune a gaban kofar shiga parlour'n gidan ,suna hira , ta gabansu yazo zai wuce ,faruk ne kawai ya gaisheshi, amman ita yesmin da idanu ta bishi ..

Koda yashiga parlour abbanta kasa aiwatar da komai yayi ,yana jiran shigowarta shiru, nan ya K'ara shiga wani sabon tashin hankali mara misaltuwa ,jikinsa banda rawa babu abinda yake ,shigowarsu ce ta yanke masa tunani ,Kai tsaye dining suka nufa dan Daman ummanta ce ta kirasu suzo suci abinci ,suka ci abinci sannan faruk ya kama gabansa , ita kuma ta janyo cup wanda had'in kayan fruit ne a ciki .

yadda batace masa kala ba, haka shima baice mata ba ,har sanda abbanta ya shigo ya mika masa hannu suka gaisa ,yana tambayesa yanayin aikinsa ,ya amsa da alhamdullahi mun godewa Allah daga nan suka zarce da tautaunawa, har inda Dr Jamil yake sheida masa ya samu matar da zai aura a maiduguri aure zaiyi na da wani lokaci ,baya ma son a d'auki lokaci mai tsawo dan...... ..
wani irin tari ne ya tsarketa ta dinga tari babu kaukautawa tana dage kirjinta ,kafin kace me tuni har abbanta da Dr Jamil sun taso, Abba ya riketa yana yi mata sannu amman tari kawai take har da hawaye , had'a baki suka yi suna jero mata sannu while Dr Jamil na shafa bayanta zuwa kanta Yana faman jera Mata sannu ,abba ya tsiyaya mata ruwa a cup ya bata tasha, da kyar suka samu tarin ya tsaya daga nan basu sake cigaba da magabar ba Dr jamil yaki matsawa kusa daita yana jin tamjar ya soma rarrashinta dan yasan dalilin shigarta wannan halin,hannunta ya riko yana kallonta yana sake mata ,cikin haka ummanta ta shigo sama sama suka gaisa da Dr , kana ta soma tmbayr abinda ya samu yesmin ,Abba ne ya fad'a mata batare da Bata lokaci ba, tace "shine kana tsaye wani Kato ya wani rike ma yarinyar ka hannu tare da tsareta da idanuwa kamar zai cinyeta ,ba Dr jamil ba hatta abban yesmin yaji kunyar abinda umma tayi , kafin yayi wani hanzari yaji tasoma magana cikin fushi "dan a sakar mata hannu , idan son samu ne a dinga nesa nesa ......
Ya Salam ya furta yana a cikin ranshi yana zame hannunsa dake cikin nata ,jikinsa yayi mugu mugun sanyi ,ya dawo tamkar mutun mutumi a gurin , Bata jin kunya irin na ranar ba ...
"Taso muje ta mikawa yesmin hannunta ,da kyar ta saka hannunta cikin na umma zuciyarta na dokawa,umma ta rungumota suka nufi hanyar d'akinta ..
Habib ya juya a zuciye zai bita Dr Jamil ya riko shi ,"Ina zaka kabarni ?
"Dan Allah karka mata magana ,idan kayi wani Abu zamu samu matsala da Kai .....ya fad'i haka yana k'ok'arin barin d'akin ,wannan abinda umma tayiwa Dr Jamil yayi matukar d'agawa abban yesmin hankali ,amman yaki ce mata komai kamar yadda Dr yace masa , amman gabad'aya wunin ranar ya d'auke mata wuta ,wata magana bai sake shiga tsakaninsu ba ,ko abinta ma kin ci yayi , ya kurducewa ranshi sai ya ganar daita kuskurenta akan abinda tayi dan ya lura da take taken akan Dr jamil " shiryawa yayi ya bar gidan ..

Bangaren yesmin kuwa , zance abbanta da Dr Jamil , ya d'aga mata hankali matuka har taji bazata iya hakura ba ,taga gara kawai taje gidansa, ta sameshi suyita takare ,suyi duk abinda zasu yi ,amman wallahi sai ya dawo mata da budrcinta daya rabata dashi ,bazata yarda ba, tunda bai sonta to ya maida mata budurcinta ...cikin sand'a ta fice daga gidansu babu tsoro a zuciyarta kamar Koda yaushe idan zata shiga gidan ..



Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 20


..A hankali ta tura kofar shiga parlour'n tare da kutsawa ciki tana jin kirjinta na wani irin dokawa , kallo day'a tayi parlour'n ta d'auke kanta saboda bata ganshi a ciki ba, dan haka ta juya ta nufi bedroom dinsa, tana fidda numfashi sama sama while zuciyarta na dokawa , nan ma bata ganshi ba, sai dai ko ina a d'akin very neat ,ga kamshi turarensa dana airfreshener dake tashi a kowace kusurwa dake cikin d'akin ,lumshe idanunta tayi a hankali ,tana jin yadda kirjinta ke bugawa da matsanancin karfin gaske ,jikinta a matukar sanyaye ta nufi kofar baya, dan zuwa lokacin tafi tunanin yana bayan gidansa ,wanda kusan irin wannan lokacin can yake zama yana karance karanceshi na yau da kullun ..


Sosai taji zuciyarta tana tsananta bugawa ,amman ta kudurce a ranta komai zai faru ,sai dai ya faru ,amman sai ya dawo mata da budurcinta daya rabata dashi matukar bai zai aureta ba ...

"Zaune ta hango
shi akan kujera mai zaman mutun day'a ,idanunshi na kallon sararin samaniyya , gabansa k'aramin table ne mai d'auke da ruwan nerstly water ,sai jarida wanda ba zata iya tantance ko wace iri bace , tsura masa idanunta tayi tana kallonsa yayi zurfi cikin tunani...


Ahankali ya sauke naunayen ajiyar zuciya da numfashi a tare ,zuciyarsa na matukar zafi ya janyo robar ruwan ya kafa a bakinsa ya shiga kwankwad'a yana runtse idanunshi ,sai daya shanye tasss sannan yayi wurgi da roban ,ya sake runtse idanunshi , rungume hannuwanshi duka yayi a kirji ,yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsashi ,"duk d'aukar da yake a can baya ba soyayyarta ce ke dawainiya da rayuwarsa da zuciyarsa ba, shakuwa da sha'awarta yake ji ,a she abun ba haka bane ,zuciyarsa cike take fal da matsanancin kaunarta da shaukinta wanda bai san ranar da zai fita daga ciki ba ....

Sai dai abu mafi muni da tashin hankali gareshi a hanlin yanzu ,bai wuce yadda yaga mahaifiyarta ta d'auki karan tsana ta d'aura masa ba ...
"To me na yi wa hafsat yasa take tsana yanzu bayan ada can baya ba haka take min ba ?
" Ko kuwa tasan halin
da nake ciki ne da yarinyarta ?
Yayiwa kanshi tambayar zuciyarsa na kokawa ,
"Kai da wuya idan ta sani "dole idan tasani ta sanawar habib ,shi kuma dole habib ya nemi shi da batun , kawai dai ta tsani ganina tare da yesmin ne yanzu ,
idan kuwa haka ne ta tafka babban kuskure a rayuwarta, domin rabani da yesmin bak'aramin tashin hankali bane, har ma gara ni akan yesmin din , dani zan iya jurewa duk runtsi duk wuya ita fa ?
Saukar tafi hannu yaji a saman kafad'arsa, an dafa shi a hankali a juyo .. ..

"Karaf idanunsu suka sarke cikin juna ....
murza idanunshi yayi domin sake tabbatarwa, "shin itace a gabanshi ko kuwa wata halittar ce daban a gabansa ?
Dan sam baiyi tunanin ganinta a daidai wannan lokacin da take nuna masa ko in kula akan lamarinsu ba ,asalima tafi maida hankalinta akan faruk ne .

Nan ta tsaya tana kallonsa da kyawawan idanunta masu tsuma zuciya,
Idanuwanta suka cicciko da ruwan hawaye, tana kallonsa tana jin kamar ta Isa gareshi ta shige cikin fad'ad'd'en kirjinsa mai dumi da ni'imar kwantar da hankali ,ko zata ji dadi ,sannan ta ragewa kanta damuwar data ciki a kanshi ,wani irin kallonsa take tana karanta yanayinsa ,shima kallonta yake ,sai dai shi yanzu fuskarshi kunshe take da murmushi mai d'auke da lissafin damuwa iri iri ,daban daban ....

Ahankali ta soma k'ok'arin isowa zuwa inda yake tare da k'ok'arin kai gwiwonta kasa da had'e hannuwanta duka guri day'a al'amun tausayawa take nema daga garesa, da tsantsar mamaki a kan fuskarshi , da sauri ya mike tsaye daga zaunen da yake, ya riko hannuwanta duka cikin nashi ,ya mikar daita tsaye bisa kafafunta, yana kallon cikin kwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye,lokaci day'a yanayinsa ya canza , murmushin dake shimfed'e a Kan fuskarsa ta d'auke, ta koma tsantsar damuwa da matsanancin tashin hankali , gabad'aya ya gigice ya rud'e muryarsa na rawa yace " no karki yi kuka yesmi "
"Meye damuwarki da har zaki durkusa min ...?

"Ta matso hawayen dake boye a cikin kwarnin idanunta, hawaye suka gangaro shar...shar...yace "no ba wannan na tambayeki ba ,banason ki sake wannan ganganci bani ba, ko ga wani ,ke din macece mai matukar daraja da kima ,bana son ki sake durkusawa kowa please ...ya fad'a yana ciro hanky cikin aljihun gaban rigarshi ya soma goge mata hawayen dake gangarowa bisa kuncinta on- expecting yaji ta buge masa hannu tana aika masa da wani irin kallo mai tattare da zallar tashin hankali...


" Bai gama mamakinta ba ,ya ji sautin muryarta ya doki cikin kunnneshi "Karka sake ta'bani d ......"
" Ban zo nan dan ka fad'a min w wata kima ta, ko darajata ba, nazo ne dan ka dawo min da budrcina daka rabani dashi matukar ba zaka aureni ba ........ "Ta k'arasa maganar tana matso hawaye masu zafi, yayinda zuciyarta ta cigaba da bugawar da take a tun sanda suka kasance tare "


"Sosai maganarta ta doki kunnuwansa, sannan ta wuce har cikin kahon zuciyarsa inda yayiwa maganar ma'aji mai kyau ,wani iri ya soma ji ajikinshi ,ji yayi kamar ta kunno masa tarin sha'awarta dake kwance a cikin kokon ranshi ne "
"Wayyohly Allah yesmin kinyi nisa acikin duniyata , murmushi ne ya su'buce masa kana ya shiga dubanta .

Cikin wata irin kasalalliyar murya yace "Yesmin kenan ,lallai har yanzu da sauran kuruciya a tattare dake, ko Kuma nace kina tsakiyar kuruciya , Ina kika ta'ba ganin an dawo da budurci ?

"Ai budurci daya ne, idan ya tafi ya tafi kenan har abada baya dawowa yesmin ,amman na godewa Allah da nine na amshi budurcin .........

"Karaf maganar ta fad'a cikin kunnen abban yesmin, da yake k'ok'ari zagayowa gurin shan iska ,dan cikin gidan ya fara shiga bai ganshi ba ,dan haka yayi tunanin samunsa a gurin ,sai dai gashi zuciyarsa tayi karo da mugun ji ,da mugun gani ,zuciyarsa ta tsaya cak ta daina aiki na wucin gadi ,bayan ya dafe kirjinshi da hannuwansa duka,numfashinsa ya dawo ya cigaba da aiki a gangar jikinsa a daidai lokacin da tsayuwa ta nemi gagararsa ,yayi taga taga baya baya ya jingina bayansa da bango idanunshi cak akansu "su din ne ba wasu ba ,yesmin dinsa ce tare da abokinsa amininsa mafi kusanci a cikin al'amuransa na yau da kullun ....
"Mutumin daya fi yarda dashi fiyye da kowa da komai dake cikin duniya ....
"Yau shi aka wayi gari yana furta kalmar godiya ga Allah bisa raba diyarsa da budurcinta da yayi ....."wacce irin rayuwa ce haka ya salam?
Numfashi ya dinga janyo wa da kyar tana fitarwa tamkar mai cutar asma ....

" yayinda ita kuma yesmin ta zuba wa Dr Jamil kyawawan idanunta kawai tana kallonsa tana jin wani irin zallar 'bacin rai na ratsata ,hawaye na cigana da bin kuncinta ,ya riko hannunta tayi saurin gogewa duk akan idon habib dake dafe da kirjinsa ...... "karka ta'bani ........ ta juya fussssss tana wani irin kuka ,da wani irin hanzari ya fixgota ta juya ta fad'a cikin fad'ad'd'en kirjinsa ya matseta gam yana fidda numfashi .....

Mutsu mutsu ta shigayi a jikinsa, tana wani irin kuka tana fad'in ka sakeni d tunda baka Sona, " ka cutar dani D.. kana kallo za'a bani Yaya faruk ,alhalin kasan Kai ne a cikin zuciyata saurin ware ido habib yayi Yana kallonsu cike da matsanancin mamaki mara misaltuwa ..

A hankali Dr Jamil ya Kai bakinshi daidai Kunnenta ya shiga rad'a mata magana Cikin Sanyayyiyar muryarsa "Ina sonki yesmin Allah kad'ai yasan abinda ke boye daya saukar mana da wannan kaddarar ... "Allah yesmin Ina sonki ,nazo da Shirin amayarwa abbanki abinda ke raina faruk ya rigani ..then what will I do ?
"Na hakura dake yesmin shine mafi sauki , tun farkon ganina dashi nasan yana sonki yesmin, Wanda zan iya cewa idan ban fi faruk sonki ba, soyayyarmu zata zo daidai .

A matukar fusace yesmin ta bud'e idanunta sosai tana kallonsa kafin daga bisani tashiga aika masa da harara lokaci guda Kuma hawaye ya biyo baya " "sorry baby am just ...."bana son jin komai daga bakinka D.. tunda har zaka iya daidata soyayyarka da wacce faruk yake min,kana k'ok'arin fada min cewar faruk ya fika Sona ba ........?

" ke kinsa irin son da nake mik , amman hakan bazai hanani fad'ar gaskiya ba .
" Kuma misali nake ,saboda yadda nake hango tarin son da yake miki...

Muryarta cike da kuka tace "to misalinka bai yi ba , ka ma daina misalta haka ,domin kuwa kafi shi sona ,Kai ne mutumin dake sona tun ranar da na fado duniya daga cikin mahaifiyata ..
Kai ne mutumin da kake sona tun ina yarinta ......
"Kai ne mutumin da kake son ganina cikin farinciki Koda kuwa kai zaka rasa naka farinciki.....
"Ka kalli kanka kaga yadda ka dawo d...... "Ka rame kayi baki ka fita haiyacinka, kullun kana cikin kunci da bakinciki, duk ka dawo wani iri kamar ba Kai ba " yaushe faruk ya fara sonna?
" sai da na girma na zamo mutun na mallaki hankalina sannan ya soma sona.
"hakika ni yesmin nasan kana sona so na gaskiya .....
Tana gama fad'ar haka ya rungumeta a jikinsa Yana jin wani irin sabon sonta na ratsashi, yana jin kamar shima ya sakar mata kuka ,yana jin Ina ma ta kasance matsayin matarsa yanzu ,duk duniya babu macen da yake so sama daita .......yana sonta son da bazai iya kwatantawa va ...."me takamata yayi domin mallakarta a rayuwarsa ...?

shigewa tayi

Please Login or Register in order to submit comment