Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kee sa a soka ba, ke dai ki tayani da addua Allah yasa wani bai wa rayuwata tsaiko ba ,yana gama fad'ar haka ya mike ya nufi bangarensa na gidan ..

A hankali yesmin ta juyo tana kallonsu ,kafin daga baya ta fice daga d'akin cikin sand'a ta nufi hanyar lambu, yadda ta hango shi d'azu, haka ta iske shi ,tana gama k'arasawa gurin ta amshi wayar dake rike a hannunsa .
"a hankali ya d'ago kanshi yana kallonta, dan yasan babu me masa haka sai ita , yana kallonta ta ajiyar wayar a kasan grass din dake shimfed'e a gurin ,kana ta durkusa bisa gwiwonta "uncle jamil ta Kira sunansa wanda take ya ji jikinsa ya sake yin sanyi, "da gaske baka Sona ko ?
" for gud 5 second ya d'auka zaune yana kallonta da tsantsar shaukinta da mamakin a kan fuskarshi saboda shi yasan bai ta'ba cewa baya sonta ba ,ya dai jadadda mata ta samu daidaita, ba dan bai sonta ba ,ai soyyarta a jininsa take bama zai ce ga lokacin daya shigesa ba .

A hankali ya mike tsaye ya kamo hannayenta duk biyu ya mikar daita tsaye Yana kallon cikin kwayar idanunta dake cike taf da ruwan hawaye ,itama din shi take kallo zuciyarta na matsanancin dokawa , "tun da baka sona ka barni a yadda nake kawai na cigaba da rokonka kasoni " girgiza mata kanshi yayi a rud'e yace "waye yace Miki bana sonki ?

Murmushi tayi tana cizan gefen lip's dinta , ganin yadda ya rud'e "baka Sona mana kalli yadda kake min kamar bakasani ba, ka ganin tsaye tare da Yaya faruk amman ka nuna rashin damuwarka a kaina "

Cikin saurin murya yace "no no ba haka yake nufin bana sonki ba yesmin, bama haka ba faruk d'anuwanki ne , ko bayan yan'uwanta akwai wani Abu ne a tsakaniniku ?
Ya tambayeta yana zaunar daita a kujerar da abbanta ya tashi ,madadin taba shi amsa tambayarsa sai kawai ta matso da kujerarta kusa dashi sosai ta d'aura goshinta a kafad'arsa ,tana jin yadda ya sauke naunayen ajiyar zuciya da karfin gaske .

sheshekar kukanta yasa ya juyo tare da d'ago fuskarta " why yesmin me yasa kike k'ok'arin son kowa sai yasan abinda muke ciki ?
"Kina son wani abu ya cigaba da faruwa a tsakanimu ne ko kuwa ? Ya k'arasa maganar Yana ciro hanky daga aljihun gaban rigarsa, ya shiga goge mata hawaye dake tsiyaya akan kuncinta, hannunshi ta kawar gefe guda , ya bita hannunta da ido Yana kallonta .
ta lumshe masa ido "d zaka aureni ko kuwa na hakura da Kai kamar yadda ka bukata ?
" Ni..........."
"no d, yes or no ,just tell me the truth ?
"No yesmi amman Ina so..."bana son jin komai daga bakinka bayan wanda naji a yanzu ,daman baka dace da rayuwata ba, amman ka dinga min abubuwa da suka dole na soka, ba dan ka cancata ba "
"Allah ko ?
"Yes of course sam baka dace dani ba, Allah ya saka min abinda ka min ,yadda karabani da burcina , Ina rokon Allah ya baka damar sake aure a rayuwarka ,ka haihu a yiwa diyarinka abinda kamin ,ka rabani da burcina sannan kace bazaka aureni ba ,to kaje Allah ya saka min ...... tana gama fad'ar haka ta juya tana Kuka saurin mikewa yayi ya riko tsintaiyar hannunta ,ta juyo suka had'a ido.... ji tayi babu abinda feeling kamar ta shige jikinsa a lokacin taji dumin jikinsa Koda hakan zai zamo karo na karshe a rayuwarta ,ta had'iye wani Abu daya tsaya mata a koshi tare da fixge hannunta ta kwasa a guje madadin ta shiga cikin gidan ,sai ta nufi bangare baya ta zauna, tana risgar kuka tamkar wacce aka aiko uwarta da ubanta sun mutu kuka take kamar ranta zai fita ..

Shi kuwa Dr Jamil dawowa yayi tamkar mutun mutumi a tsaye a gurin ,gabad'aya ya rasa abinda ke masa dadi ,komai ya tsaya masa cak ,numfashi ma da kyar yake fixgowa ,wani abu yaji yana yawo acikin kwalkwaluwarsa ,so yake ya samu Wanda zai karya Masa kalamanta garesa, domin yafi tunanin ba daga bakinta suka fito ba, hanyar da tabi yabi da gudu yaje kallo ,kafin daga baya ya shiga Kai kawo agurin goye da hannunwansa , "yanzu shi yesmin ta tsaya ta farfad'awa son ranta ?
"Lallai *son rai* ya Kai shi ya barosa, yarinyar da aka Haifa gabansa, ta girma a gabansa ,take respecting dinsa tamkar shine ya kawota duniya, amman yau an wayi garin tana iya farfada masa abinda taga dama saboda ya aikata *son rai* daita "
Ya dade tsaye agurin kafin daga baya abban yesmin ya dawo suka fita.

yesmin bata shiga gida ba sai data ci kukanta ta koshi sannan ta goge fuskarta ,ta nufi cikin gidan tattare da nadamar abinda ta yiwa Dr Jamil, duk ma abinda yayi mata bai kamata tayi Masa mugun fata ,irin haka ba ,sosai ta dinga bleming kanta tana zubda hawaye,ranar kwana tayi cike da bakinciki da 'bacin rai abinda nayi masa "

******

Bangaren Faruk kuwa zaune yake a bangarensa duk abun duniya yabi ya damesa, dan yadda yesmin ke yi masa a tun sanda ya furta Yana sonta ,ya nuna masa al'amun bata son shi "

ganin zaman na shi bai da wani amfani yasa ya tashi ya nufi d'akin hajiya kaka, dan nan yafi tunanin take ,Koda ya shiga d'akin ya iske zaune rigingine tayi shiru tana kallon celling d'akin har lokacin soyayyar Dr Jamil na nan damkare a cikin zuciyarta , ya k'araso gareta ya zauna kusa daita "me yasa kike son zaman kadaici ?
Taji sautin muryarsa cikin dodon kunnenta ,"kullun baki da aiki sai tunani , fad'a min waye ke k'ok'arin tarwasa farincikin kanwata naje na samesa na kwance masa notikan jikinsa ?

Bata sanda murmushi ya bayyana akan fuskarsa ba ,dan haka nan maganarsa ta bata dariya tace "Kai Yaya ,me yasa kake damuwa da damuwata ne ?
"Saboda Ina sonki yesmin " ya bata amsa atakaice ,Yana kafeta da idanushi .
Cinno bakinta tayi "ni dan Allah yaya ka daina cewa kana so nah "

"Saboda me to ?

"Sabida ......sai km tayi shiru ,haka nan taji kunyar maganar da zata fad'a masa "saboda kina son wani ko ?
Kawai ta tsinci kanta da girgiza masa Kai "
Yayi murmushi yake "na sani ai kina soyayya da wani wanda ni bazan iya hanaki ba ,amman ki duba lamarina yesmin .
" ,ban ta'ba jin soyayya ba sai a kanki ,ban ta'ba expecting zan tsinci kaina a soyayya a halin yanzu ba sai a kanki .

"A kalamanki na wancan ranar nasan kina cikin soyayya ,kina ciki wad'an da soyayya tayiwa kazar kuku har take Shirin wargaza farincikita..." amman zan so ki bawa umar faruk damar shiga rayuwarki , zai canzaki ,zai mantar dake komai .... ,zai sa ki manta kin ta'ba son da wani i promise you ...

Tayi murmushi a ranta tana jin bazai iya raba zuciyarta da soyayyar Dr jamil ba ,sam bataji zai kama kafar Dr a iya soyayya ,uwa uba iya juya mace da sarrafata ..
Murmushi shima yayi kamar yadda tayi "i will surprise you yesmin kawai ki bani dama ,zakiyi mamakin yadda zaki soni fiyye da wanda kike so amman sai kin bani dama ..."


"Okay zan yi tunanin a Kai "kiyi tunani mai kyau a kaina plz ,baki ji yadda zuciya take yi a kanki ba ,tayi murmushi dan zantuttukansa dariya suke bata ,dan ita kaf tunaninta bata ga muhallin da zata bashi a cikin zuciyarta ba, bare ta bashi damar da yake nema daga gareta ..

******
A cikin kwanakin faruk ya matsa mata sosai ,duk abinda ya san zai sakata farinciki shi yake mata ,kwata kwata ma ya'ajiye batun soyayyarsa a gefe , k'ok'ari yake yaga ya gina kyautatawa ta musamman a cikin zuciyarta ,ta yadda lokacin da zata fad'a tarkonsa ba zata sani ba ,cikin haka suka fara weac ,haka ya dinga jigilar kaita yana d'aukota sai dai idan baya nan direban da abbanta ya d'auko mata ya kaita ,yanayin karatun exam ,da kulawar faruk gareta yasa ta rage damuwa da Dr Jamil, ba daan bata son shi ba ,dan sonshi a jininta yake amnan ta dan ji saukin rad'ad'i azabar da take ji a kansa "

*********

Bayan wata day'a
Wanda zuwa lokacin abban yesmin da ummanta har ma da yesmin sun koma gidansu dake g.r.a"

Abban yesmin ne zaune a bakin swimming pool tare da yesmin har ma da Dr Jamil wanda hankalinsa yake a tashi ,ya rame sosai ,sakamakon shariyar da yake fuskanta daga yesmin dinsa , dan a halin yanzu dan ko kallon inda yake yesmin bata yi ,duk wani rawar jiki da take yi a kansa ta daina ,taxt message kiran da take masa a waya ta daina ,ya damu sosai har ya soma nemanta , amman yadda take amsa masa da yadda take reply din test message dinsa ,ya nuna masa al'amun akwai wanda yake amfani da dama da karfin soyayyar da yake son rusa na shi gwanatin soyayyarsa a zuciyarta, ganin idan yayi shiru zai iya cutar da kanshi alhalin ya hanga ya hango itace kawai macen da zata iya dashi, da Kuma samar masa farinciki da yake muradi a rayuwarsa ,hakan yasa yayi tattaki tun daga maiduguri zuwa ga mahaifinta domin amayar masa da abinda ke ransa ....

Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 18

Bayan sun gaisa da abban yesmin , Dr Jamil ya d'an saurara ,yaji ko yesmin zata gaishe shi kamar Koda yaushe .
amman yaji tayi shiru taki cewa komai ,hakan ne yasa shi maido hankalinsa da idanunshi har ma da natsuwarsa inda take zaune kusa da mahaifinta ,ya tsura mata idanunshi masu matukar kyau da tasiri a jikinta har ma da zuciyarta ....

"Zuciyar ce ta dinga dokawa da mugun karfi , sakamakon idanunshi da take jin yana yawo a sansar jikinta, cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya ta d'ago kanta ta tsura masa nata ido ,shiru kawai tayi tana kallonsa tana karanta yanayinsa ,yayinda shi Kuma yake kallonta, fuskarsa tattare da sagwaron damuwa da tashin hankali .


ahankali ta d'auke kanta saboda wani sabon son shi data ji ya dawo mata sabo fil a yanzu daya tasata gaba ,yana kallonta da wad'an nan idanunwa nashi masu birkita 'kwa'kwaluwa da tsuma zuciya .

"Anya kuwa zata iya rabuwa dashi kamar yadda ta shiryawa zuciyarta ?
" zaki iya rabuwa dashi mana, idan dai kin shiryawa haka ,zuciyarta ta bata amsa da hakan "to me zanyi da zai zamo very easy gareni ?

"Kai bazan iya rabuwa dashi ba ,bayan zuciyata bata rabo da tunaninsa kullun cikin tunaninsa da begensa nake , "
Cike da matsanancin kaunarsa ta sake kallonsa taga ita din yake kallo har lokacin fuskarsa tattare da damuwa haka nan itama ta tsincin kanta cikin tsananin tashin hankali ..

" Gyaran muryar abban yesmin yayi yace "marwa jeki kawowa uncle dinki wani Abu ya sakawa cikinsa mana ,ko har yanzu fushin kike yi dashi ?
ta lumshe idanunshi tana kirkiro murmushi "abba kenan ai na huce kamar yadda fad'a maka ,Ina ma ka ta'ba ganin diya tayi fushi da ubanta ? Murmushi sukayi gabad'aya amman ban da ita .
Abban yesmin yace "gaskiya ne wannan ,Allah yayi miki Albarka "ameen abbana ,ta mike a natse tasoma tafiya kamar wacce batason taka kasa ,yayinda Dr Jamil ya bita da kallon kasan ido yana jin yadda kirjinsa ke bugawa akanta ,"sam bai ta'ba tsammanin idan ta juya masa baya ,zai shiga damuwa da tashin hankali ba, sai yanzu da take k'ok'arin banzatar da lamarinsa .
"cikin minti biyar ta dawo hannunta rike da tire , ta k'araso inda suke ta ajiye akan tablet din dake tsakiyarsu ,batare da tace komai ba "yauwa diyar Albarka sannu da k'ok'ari " inji Dr Jamil a ciki ta amsa masa dan haka bai sake yunkurin cewa komai ba har sanda ta tsiyayo driks a cup guda biyu tasoma mikawa abbanta sannan ta juyo tana k'ok'arin mikawa Dr Jamil, kad'an ya rage zuciyarta bata tarwatse ba ,saboda wani abu daya fito daga cikin kwayar idanunshi ya shiga nata idanun ,rausayar da idanuta tayi cikin nashi ta mika masa ,ya amsa cikin rashin sani hannunsa ya shafi yatsunta ,wani irin zirrrrrrrrr sukaji a tare ,saurin cire hannunta tayi tana yarfewa kamar wacce aka jona jikinta da wutar lantarki..
A matukar firgice zuciyarta na wani irin bugawa ta koma ta zauna ta d'aura kafarta day'a kan day'a still tana jin idanunshi ajikinta suna yawo .

Dr Jamil ya ya kurbi ruwan lemun kad'an ya ajiye ,Abba ya nuna masa cula wanda soyayyen naman kaza ne aciki ,ya girgiza kansa ya bud'e bakinsa zai soma maganar data kawo shi kenan , sai ga shigowar motar faruk harabar gidan .

tun motarsa ta shigo ,yesmin ta d'auke idanunta a kan Dr Jamil, ta maida kan motar faruk har sanda yayi parking ya fito cikin wasu had'add'un kanana kaya da suka matukar amsar jikinsa ,a hankali ya fito ya soma takowa zuwa inda suke zaune ,idanunshi na Kan yesmin, ta d'an sakar masa murmushi, dan kawai ta nunawa Dr Jamil ,ba fa shi kad'ai bane cikakken namiji mai kyau da izza ,dama duk wani tsari na yanayin jiki ba.
faruk ya kashe mata idonsa day'a yana fad'ad'a fuskarsa da fara'a ,yana gama k'arasowa inda suke yesmin taja masa kujera dake gefenta "welcome bro ga guri ka zauna kusa dani "
a madadin ya zauna kamar yadda ta bukata, sai ya rusuna cike da girmamawa yana gaishe da abban yesmin da Dr Jamil .
cikin sakin fuska suka had'a baki gurin amsawa inda abban yesmin yace "ya batun aikin naka kuwa "
Faruk ya shafa keyarsa yace "na tura takarduna tun a Abuja jiran nake tukunan "
"Okay Allah ya taimaka yasa a fara a sa'a " ya shafa keyarsa al'amun jin kunya yace "ameen "
Ya juya, yesmin tayi saurin riko hannunsa, ba Dr Jamil ba hatta zuciyar abbanta sai daya buga dan firgici ,da faruk dine ya rike mata hannu bai san abinda zai yi masa ba ,amman sai gashi itace da kanta ta rike shi , gabad'aya suka tsura musu ido kawai suna kallonsu sautin muryarta ce ta dawo dasu gabad'aya "Ina kuma zaka Yaya faruk, kaima ka zauna ayi hira da Kai mana , ta k'arasa maganar tana kirkiro dariyar dole ..

Shi kuwa faruk wani irin sanyi dadi ne ya ziyarceshi shi from know where ya samu guri ya zauna kusa daita Dr Jamil ya runtse idanunshi gam dan shi kad'ai yasan abinda yake ji a halin da yake ciki , gabad'aya ya tsani ganin yesmin tare da faruk ita Kuma ya lura ta soma shishige mashi ..
Faruk yayi shiru ya kasa samun natsuwa yana faman shafa keya yana neman hanyar magana ,Abba ya dube faruk yace "ya'akayi ne faruk akwai magana ne ?

Faruk ya kalli abban yesmin cike da matsanancin jin kunya ya soma magana " wato tun dawo wata daga demark, na dira a garin nan, na tsinci kaina cikin tsananin kaunar yesmin....."

d'agowa tayi da sauri ta tsura masa ido da mamaki a bayyane a Kan fuskarta dan bata yi expecting zai iya furta kalmar sonta a koina ba .
Shi kuwa Dr jamil tunda yake a rayuwarsa bai ta'ba jin maganar da ta fad'ar Masa da gaba irin wannan ba,nan take wani gumi ya soma karyo masa ya tsinci kansa a wani irin bakin ciki na daban da bai ta'ba tsintar kanshi ciki ba, nan take jikinsa ya soma rawa gumi kuwa sai yanko masa yake ta ko wani a sansar jikinsa ...

"Abban yesmin dan Allah ka taimakawa rayuwata ka bani aurenta ,idan ba haka ba komai zai iya faruwa dani , faruk ya k'arasa maganar yana had'e hannuwansa duka guri day'a, abban yesmin ya numfasa kana yace "shikenan faruk ai wannan Abu ne Mai kyau kazo dashi ,karfafa zumuci ,sai dai ka bani nan da zuwa wani lokaci zan yi magana da yesmin idan ta amince da soyayyar ka ,ni kuma nayi maka alkwarin baka marwa....... "

Dr kaji bayanin faruk ko ?
Dr Jamil bai ce komai ba ,sosai yayi zurfi cikin tunanin maganar faruk da soma tun second biyu da wuce , "shikenan burinsa ya zamo tarihi, tun da gashi faruk ya rigashi fad'awa mahaifinta .
"Mikewa abban yesmin yayi tare da d'aukar wayarsa data soma riging ya nufi bangarensa..

Yesmin tayi murmushi ganin yadda yanayin Dr Jamil ,ya sauya a lokaci daya komai na shi ya tsaya , uncle jamil ka taimaka ka sanya baki ,naji ance babu Wanda yesmin ke so, da jin maganarsa kamarka, nasan kana cewa wani abu zan samu karbuwa ta ban mamaki a gurinta , Shi dai Dr bai san sanda ya tsinci kanshi da fadin ,karka damu ai har ma ka rigada ka samu dukkanin wata kar'buwa a gurinta, na tayaka murna da zaka samun yesmin a matsayin mata........... "
maganarsa ta daki kunnuwanta sannan ta zarce har cikin tsokar dake makale da zuciyarta ,ji tayi kamar ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta ta rusa ihu saboda jin abinda Dr Jamil ya fad'a ,damuwar da take k'ok'arin boyewa acikin zuciyarta ta so bayyana ,take idanunta suka cicciko da ruwan hawaye amman tayi saurin maidasu tana runtse idanunta .

" Dr jamil yace " Bari na baku guri ku cigaba da ..sai Kuma yayi shiru ya kasa karasawa ,cikin hanzari ya bar gurin, gudun kar asirinsa ya tono.

bayan tafiyarsa faruk ya kalli yeamin kanwata me zaki ce ?"kin dai ji abinda Abba yace ,gasky ban ta'ba expecting Abba zai ji dadin maganar aurensu"

Kanta a sunkuye yake zuwa lokacin sai dai jikinta yayi balain sanyi , murmushin dole tayi tace " yaya faruk me yasa kayi abinda kayi plz?

"Na fad'a maka ka bani lokaci !!,ka bani lokaci!!! saboda komai yana bukatar natsuwa tunani da Kuma shawara ,so please ka ban d'an lokaci kadan zan baka amsa "to nagode kanwata, idan bake na aura ba, bazan ta'ba aure arayuwata ba, saboda babu macen da ta dace da rayuwata sai ke ,I love you so much yesmin .. murmurshi kawai tayi ta mike jikinta na rawa ta soma tafiya da kyar ,shima ya mike ya bita suka jera ...

Sam dr Jamil ya kasa samun sukuni, parlour'n sama na gidansa yaje ya tsaya ,ta yadda zai iya hangensu ,hangosu tsaye yayi jikin motar faruk ,ya kara jin wani balain kishi wato ma yesmin tana son faruk ,tunda har tana iya hira dashi, yana kallon faruk ya kamo hannayenta ko me yake fad'a mata ?
kafin daga baya ya bud'e motarsa ya shiga yana d'aga mata hannu sannan ya kama gabansa ,yesmin da Dr Jamil kam su kad'ai suka San abinda ke damun zuciyarsu ..

Yana kwance a parlour'nsa na kasa hawaye ne ke gangaro masa, bai san adadin lokacin daya dyauka agurin ba sai jin tsayuwar mutun yayi akansa, wata irin zabura yayi Yana goge hawaye dake bin gefen idanunshi, abban yesmin ya gani tsaye Yana dubansa cike da matsanancin mamaki ,ya zauna kusa dashi "abokina meye damuwarka ne ?
"dan girman Allah ka fad'a min damuwarka "
Dr Jamil ya runtse idanunshi yayinda zuciyarsa ta dinga dokawa da sauri sauri ya riko laulausar tafin hannunsa "plz abokina karka boye min bamu saba boyewa juna komai ba, tun tasowarmu har kawowa yau, me yasa kake son boye min damuwarka yanzu ?

Shiru yayi na wasu yan dakika sannan ya soma magana "nayi zubar da hawaye har hawayena sun kafe ,na koma na zuci yayinda na zuciyar ma yake k'ok'arin kafewa , yanzu ma Allah ne ya taimake ni yasa hawayen zuba ...abban yesmin yace "fada min meke saka zubar da hawaye da sakaka damuwa ?
"Ina sonta har soyayyarta na neman haifar min da ciwon Kai da hawan jini ,hakika soyayya bata sallama ,bata neman izini ,kawai mutun tsintar kanshi zai yi ciki ,Kuma daman haka soyayya take," some lose ,some gain ,some smile, some cry ...…..ya k'arasa maganar kirjinsa na bugawa .

kura masa ido abban yesmin yayi kafin daga bisani ya numfasa yace "wacece wannan yarinya ?
"Ka fad'a min ko wacece ita ,waye ubanta a Ina take ?
Idan Kuma baka son nasan kowace sai na tashi na kama gabana ,,

ya mike yana k'ok'ari barin parlour'n Dr Jamil yayi saurin riko hannunsa "ai kai ne mafi cancarta jin komai habib ..

"Wato habib a tun lokacin da .. ....


Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 19

...madadin ya cigaba da magana kamar yadda ya soma sai yayi shiru tare da runtse idanunshi da suka rikid'e suka canza kala , yana jin nauyi da kunyar abinda zai fad'awa amininsa ,yadda bakinsa ya kasa furta komai haka zuciyarsa ta daina aiki na wucin gadi , gabad'aya ya ma rasa me zai fad'a masa ,"ce masa zaiyi ya d'auki lokaci yana saduwa da diyar cikinsa har ya kamu da matsanancin soyayyarta , ko kuma cewa masa zai yi ,yana sonta ne ya bashi aurenta ?
Ya tambayi kanshi yayinda 'Kwa'kwaluwarsa ta shiga cajin neman mafutar abinda zai cewa aminin nasa .

" Jin yayi shiru ya kasa cigaba da magana yasa abban yesmin sake riko tafukan hannuwansa dake cikin nasa, yace "a tun lokacin da aka yi me Dr Jamil ka fad'a , gabad'aya na matsu naji wace yarinya ce ?

"Sake runtse idanunshi yayi sosai ,daga cikin idanunshi babu abinda yake gani sai duhu da kuma yanayin daya ga yesmin dinsa tare da faruk , wanda hakan ke nuna ta soma son shi, ko kuma yace tana son shi ,to shi yanzu me ma yasa zai

Please Login or Register in order to submit comment