Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

...

Tattara iya karfinta tayi ta fixge daga jikinsa, tana dubansa cikin yanayi na damuwa da tashin hankali "Me ka d'aukeni ?
"Ko nayi maka kama da idiot ne ?
"Ko ance maka zuwa yanzu bansa mizanin ,da adadin matsayin abinda ake Kira soyayya ba ?"Kaje kawai , just go......" Ta juya .

Ya sake riko tsintaiyar hannunta jikinsa na rawa ,yesmin kuwa hawaye shine abinda ke fita daga cikin kwarnin idanunta ,fixge hannunta tayi dake rike da hannunsa ,ta juya ta bar shi tsaye Yana duban hannunsa ,da gudu ta k'arasa cikin motar tana goge hawaye "haladu ja motar ka maidani gida ....."
Kuka take sosai tamkar ranta zai fita tana jin wani irin rad'adin azaba .

"Jingina bayansa yayi da motarsa , Yana kukan zuci ,hakika shi yanzu ,bayan tarin soyayyarta gareshi har tausayinta yake ji sosai, to amman ya zai yi kalmar nan dai da tafi tsana ita za suyi hakuri ......


"Har haladu ya figi motar da karfi suka bar gurin, bai san a wani yanayi yake ba ,a hankali ya d'auki ledar turaren da sauran kayayyankin data watsa masa ya koma motarsa ya zauna ,hawaye yake son zubarwa ko zai rage tarin damuwar da yake ciki ,amman sunki fitowa ,shiru yayi tare da yiwa motar key ya fixgeta da karfi ,Allah ne kad'ai ya Kai shi gida lafiya ..


******
Kuka take sosai har suka Isa gidan , ko sallama batayi ba tashiga parlour'n ,inda ta iske bakinsu suna nan har lokacin basu tafi ba , kallo day'a umma tayi mata taji gabanta ya Fad'i ,sai lokacin tayi data sanin turata amso dinkunan ita kad'ai ,"Ina kayan dinkunan suke naga hannunki babu komai ?
" Bamu je ba ...ta Fad'i haka kai tsaye sannan ta nufi hanyar d'akinta batare data tsaya gaida mama ta Abuja da aunty kubura ba, gabad'ayansu suka bita da kallo ,umma tayi shiru kawai batare da sake cewa komai ba..

********
Da misalin karfe shida na yammacin ranar abban yesmin ya dawo ,sun kulle a d'akinsa ,shi da yan'uwansa ,suna tautaunawa duk akan batun auren yesmin din ne ,kwarai umma taso taji akan me suke tautaunawar amman batasamu damar jin komai ba ,har suka gama ya rakosu suka shiga mota suka bar gidan ..

Bayan tafiyarsu sai ga Dr Jamil yazo gidan ,bayan sun gaisa da abban yesmin , suka nufi lambun gida, suka zauna abban yesmin yayi shiru ya tsurawa Dr Jamil ido Yana duban yadda yayi Baki ya rame tamkar bashi ba .

Ganin shirun yayi yawa yasa Dr Jamil yayi gyaran murya sannan ya soma magana Cikin karfin hali "Habib Ina tunanin akwai laifin da nayi maka wanda ban san da zamansa ba" dan haka Ina neman yafiyarka kayiwa Allah kayi hakuri ..."

"Me yasa kayi tunani kayi min laifi ? Abban yesmin yayi masa tmbayar yana mai tsareshi da idanunshi "zuciyarsa na masa wani iri ,a duk sanda ya tuna abinda yayi masa yana jin tamkar ya mutu ya bar duniya gabad'aya ya huta ..

"Tabbas nayi maka laifi habib ,laifin kuma mai girma tunda har kana iya yin wasu abubuwa batare da sanina ba , karka manta babu haka a tsakaninmu ,mun taso tare ,mun girma tare, munyi rayuwa tare ,habib nasan halinka kasan halina ,babu abinda bakasani nawa ba Habib ,ko baka fad'a min ba nasan nayi maka laifi ...
"Ranar da zan bar garin nan Kira nawa nayi maka baka d'auka ba ?
"Idan kuwa ba laifi nayi maka ba habib babu yadda za'a yi kayi ignore kirana ...."
"Na bar garin cikin damuwa da tashin hankali, amman damuwar rashin d'aukar kirana da rashin biyo Kiran , yafi komai damuna ,kayiwa Allah ka fad'a min laifina dan gaba na kiyaye ..."


Abban yesmin ya runtse idanunshi ,alkwari yayi wa kanshi ,duk duniya babu Mai jin wannan sirrin, ya barwa ransa muddin rai, duk runtse duk wuya, bazai furta masa ba kuma bazai fad'awa wani ba ....
Dr jamil ya maso sosai kusa dashi ya dafa kafad'arsa "plz habib bana jin dadin yanayin da nake ganinka ,kalleni kaga yadda na dawo, Ina cikin damuwa sosai, abubuwa sunyi min yawa, kamar na mutu haka nake ji .........


",Is okay jamil ba zaka mutu yanzu ba ,har sai ka sake aure kaga d'an kanka ,sannan baka yi laifin komai ba ,nima kwanakin nan haka nake jin kaina ,kaje gida ka huta, sannan ka soma Shirin aurar da diyarka yesmin ...

Naunayen ajiyar zuciya Dr Jamil ya sauke ,ko babu komai ya d'an ji dadin furucinsa ,"Shikenan amman a lissafina jibi ne d'aurin auren ?
"Haka ne inshallahu ranar jama'a zan d'aura auren yesmin "
Dr Jamil ya danne abinda yaji ya caki kahon zuciyarsa yace "to yaya za'ayi da bugo iv ?

"Karka damu abokina an bugo ,har sun Isa inda ya dace ,Yana gama fad'ar haka ya mike juya ya soma tafiya , shima Dr Jamil da sauri ya mike yasoma kokarin barin gurin, Yana danne hawayen dake k'ok'arin zubo Masa, tafiya kawai yake har ya shigo gidansa ,bai san a wani hali yake ba ,da sauri ya shige d'akinsa ya fad'a saman gadonsa ya runtse idanunshi tare da sauke ajiyar zuciya kana ya shiga balbale ma'ballin gaban rigarsa ,so yake kawai ya samu damar da zai yi kuka son ranshi har ya godewa Allah ...


Wayarsa ya lalu'bo daga cikin aljihun wandonsa, ya soma neman nayin yesmin ,ya kirata yafi sau goma ,amman taki d'auka , har ya hakura ya ajiye wayar sai yaji al'amun shigowar message ,ya lalu'bo wayar yana dubawa sakonta ya gani, dan haka ya mike zaune , Yana shafa kirjinsa dake cike da kwantaccen gashi ..

_Why are you disturb me ,? karka sake kirana ,domin bana bukatar mutane marasa tausayi irinka cikin rayuwata ,uncle Jamil ka barni zuciyata ta huta ,bana bukatar cigaba da mutun irinka Wanda zuciyarsa bata da kyau, ka fita acikin rayuwata, zanyi rayuwa da wanda mahaifina yake Shirin aura min ba irinka ba da kullun kake bani ciwon Kai ....._


Yayi shiru kawai yana kallon sakon data turo masa ,Yana sake karantawa kirjinsa na dokawa ,take gumi ya rufeshi ,ya rasa abinda ke masa dadi ,ya rasa yadda zai fahimtar daita , ... ahankali ya soma rubuta mata reply "

_you feel so sad and tell what ur heart feel.. alhamdullahi you know that before you accept me , take an action and make a right decision ,naji kin daina Sona ,kiyi hakuri nima bazan sake baki ciwon Kai ba ,zan zauna haka iya tsawon rayuwata ,nasani bani da zuciya Mai kyau ,yanzu babu fuskar sakewa balle a samu damar cewa Banda zuciya mai kyau, ko fad'amun wani zance , Allah ya K'ara min ,dana taso daga wata uwa duniya domin na ganki naga halin da kike ciki ,ba laifinki bane marwa nawa ne aci amarci lafiya bye for now_

Lokacin da ta gama karantawa sakon tsaki ta ja , yayinda kirjinta ke bugawa da karfin gaske tafi two second zaune tana kallon sakonshi da tsantsar mamaki akan fuskarta Sam batayi tunanin fad'a mata haka ba jikinta na rawa ta shiga rubuta masa wani text ..

_"kaje ka karata da muguwar zuciyarka"_

Tana gama tura masa ta d'aura duka hannunwata bisa kanta ta rushe da wani gigitaccen kuka Mai tsuma zuciya "da gaske dai uncle Jamil ba sonta yake ba ?
"lallai ta tafka babban kuskure a rayuwarta ,"yanzu me zata cewa mijinta idan ya tambayeta budurcinta ?
"Ina zata ce masa ta Kai ?
"Wayyo ni yesmin me yasa ,nayita bawa uncle Jamil jikina yana mora ?
"Ya Allah ka saka min abinda yayi kuka take sosai har washegari bata daina kuka ba da tunanin abinda zata fad'awa angon nata .....


******

Tana kwance umma ta shigo d'akin ,har ta k'araso ta zauna kusa daita, ta soma rarrashinta ,bata motsa ba ,hawaye ne ke zubo mata tana jin rad'adin zance umma ,
"Kiyi hakuri da wannan auren yesmin ni da kaina Ina cikin damuwa mara misaltuwa saboda bansa wanda abbanki zai aura Miki ba "kiyi hakuri ki mikewa Allah lamarin ,nima shi na mikawa ,abinda yafi alkhairi Allah ya tabbatar mana ki tash kije ga mai gyaran jiki can tazo tun d'azu tana jiranki "da kyar umma ta samu ta lalla'bata ta tashi taje gurin Mai gyaran jiki "



Washegari gari ranar jumma'a aka d'aura auren yesmin da muhmmed a kofar gidan malam wato mahaifin abban yesmin , yesmin kam ta rasa Mai ke Mata Dadi ,duk duniya ta Mata zafi ,duk kyan Abu a ranar muninsa take gani ,kallon mutane kawai take suna Kai kawo Wai sunzo Taya iyayenta murna ,yayinda ita take neman Mai tayata jimamin rasa masoyinta datayi ,ita kam yanzu tasan Bata da sauran farinciki abinda yafi damunta shine wa aka aura Mata ?
Dr Jamil ne ya fad'o Mata ko wani hali yake ?
"Tabbas haushin bai aureta bane yasa take ganin kamar bai sonta ba ,amman har ga Allah tasan masoyinta ne .
"Wayyo uncle Jamil masoyina Allah cika maka burinka ko a lahiri ne ka aureni ,na zamo matsayin matarka a duniya kam nasan ka rasani forever.......



Mmn sudais ce


💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 24

"Komawa tayi ta kwanta lamo akan katifarta hawaye na tsiyaya a gefen idanunta ,tausayin kanta da Dr Jamil take jin yana sake shigarta .


" Allah sarki rayuwa ,duk yadda Allah ya tsara maka rayuwarka babu yadda zakayi ka canzata , kaddara tana fad'awa bawa daidai yadda Allah ya hukunta gareshi ,sai ko addua ta sausauta kaddarar kan bawansa ,bata yi tsammani zata waye gari a matsayin matar wani ba uncle jamil dinta ba ..


Kuka Mai tsanani take sosai har da majina , numfashinta na sama da kasa tamkar zai bar gangar Jikinta ,yayinda sheshekan kukanta ke sake ratsa zukatan tsirarrun mutane dake d'akin ,da kyar ummanta ta rarrasheta , sannan ta koma cikin jama'a ,sai dai ta matsu abban yesmin din ya shigo gidan ,tasan dai zuwa wannan lokacin dole tasan dawa aka d'aura auren, tunda diyarta ce data tsugunna ta haifa ba tsintota tayi a bola ba ,bare a nuna mata fin karfi ......


"Duk wani program da za'ayi yesmin ta nuna Bata so a barta kawai , taji da damuwarta.
Dan haka abbanta yace abarta kada a tukura mata tunda bata so ,walima kawai akayi ,Kuma har wannan lokacin babu wanda ya sanarwa umman yesmin da wanda aka d'aura auren bare uwar gayya ..


*******

Zaune yesmin take akan kujerar dress mirrow ,tana kallon madubi ,amman bisa ga dukkanin al'amun hankalinta baya ga madubin, yana can tunanin wanda mahaifinta ya d'aura mata aure dashi ,"ko yaya yanayinsa yake?
Tayiwa kanta tambayar zuciyarta na dokawa da karfin gaske"ko zai kasance kamar D dinta ? Ta sake tambayar kanta ,"Kai Ina bama zai Kai ko kwatankwanta shi ba ,ai Dr Jamil daban yake ,ko bai fishi komai ba ,bazai ta'ba samun matsuguni acikin zuciyarta kamar yadda Dr Jamil ya samu ba "

aunty Salma wacce ta shigo yanzu, ta matsa mata ta shirya ,wani ratsantsen lace ta saka Mai shegen kyau ,tayi kyau sosai,sirrin dake tattare da amarci ya sake fito da aininhin kuruciyarta ...
sai dai duk da haka kallo day'a zaka yiwa fuskarta kasan babu walwala ko kad'an atattare daita , sai tarin damuwa da tashin hankali ,tun randa suka rabu da Dr Jamil Bata sake ganinsa ba, ko jin duriyarsa bataji ba ,bare ta leka ko ganinsa tayi ko zata samu natsuwar zuciya .

aunty Salma ta dafa kafad'arta " haba yesmin ki kwantar da hankalinki mana ,ki duba kiga yadda mahaifiyarki ta shiga damuwa duk dan akanki, Sam kinki sakin jikinki kiyi walwala kamar sauran amare .....
"Duk da yadda auren naki ya kasance bai kamata ki zamo haka ba ,mutun fa baya butulcewa kaddararsa ,abinda yafi dacewa dake kenan shiyasa Allah ya kaddaro Miki ,Kuma babu wani mahalukin daya Isa ya canza shi ko hana faruwar hakan...

"kiyi hakuri kiyi walwala ki rungumi kaddararki da hannu biyu biyu sai kiga komai yaxo Miki da sauki ,ta dan tsaya kawai tana kallon aunty Salma tana tunanin maganarta ..
Rarrashinta aunty Salma tayi sosai ita kuma kuka ya kufce mata.
"Aunty Salma ba zaki gane yanayin da nake ciki ba ,dole nayi kuka Ni kad'ai nasan yadda nake ji a cikin zuciyata ,rashin wanda kake so kuma ka saba dashi ba Abu ne Mai sauki ba......

bayan fitarta ,yesmin tana nan zaune ta had'e kanta da gwiwa tana risgar kuka kamar ranta zai bar gangar Jikinta ,yayinda kirjinta ke wani irin dokawa ,tana jin kamar ta mutu ta bar duniya kowa ya huta ....

*******


Umma zaune a d'akin abban yesmin bayan ta idar da sallah , dan d'akinta har lokacin cike yake da yan'uwanta masu jira Kai amarya gidanta, sai dai kallo day'a zaka mata kasan zuciyarta cike take fal da matsanancin damuwa da tashin hankali tamkar yadda yesmin take ciki ,abban yesmin ne ya turo kofar d'akin ya shigo bakinsa d'auke da sallama , cikin fararen kaya , hannusa yasa ya cire hularsa ,ya ajiye a Kan mirror ,yana shafa sumar kanshi ,sannan ya samu guri ya zauna akan gado yana dubanta ,"sannu da zuwa tayi masa tana d'auke kanta daga kallonsa "

"Yauwa hafsa ya taro ?
Sai data sauke naunayen ajiyar zuciya sannan tace "Alhamdullahi sai fatan alkhari ,"to allah yasanya alkhari a cikin rayuwar auren "
A ciki ta amsa da "ameen "sai dai har yanzu bakace min komai game da auren ba,
da Kuma wanda ka d'aura auren dashi ba "


Murmushi yayi yace "hafsa kenan Wai duk akan wannan ne kika yi wani kici kicin da ranki kamar zan siyar miki da yarinya ,ba fa kifini son yesmin ba ,ko a caca na ciyota bazan d'auketa na bawa Wanda bai dace da rayuwarta ba "

"Na aurar da marwa ga wanda yafi cancata ga rayuwarta ,kuma zatayi farinciki nan gaba a gidan aurenta ,fatana idan kinji wanda ta aura kiyi murna kiyi farinciki"

ta'be baki tayi tana dubansa ,yayinda aranta tace "idan kaga nayi murna ko farinciki to faruk ne yazamo miji gareta .....
"Kinyi shiru ?
"To me zance maka Abban yesmin tunda kayi son ranka ,kamar daman can kana jin haushin yarinya ko Kuma tayi maka wani gagaru min laifi ne yasa ka aikata hakan gareta "

"Bazaki fahimta ba amman bari na fahimtar dake yanzu ,nasan matukar kika san dalilin da yasa na yiwa yesmin wannan auren Zaki fi kowa jin dadi ,yayi shiru kana ya numfasa Yana dubanta ko zata Fad'i wani abun ,ganin tayi shiru taki cewa komai yasa shi k'ok'arin cigaba ,har ya bud'e bakinsa sai kuma tunanin alkwarin daya d'aukarwa kanshi akan bazai fad'awa kowa dalilin auren ba ya fad'o masa ,dan haka yayi shiru ya kasa cewa komai ,ta tsura masa ido tana son jin dalilin "Ina jinka ka fad'a min dalili ?
Tayi maganar a daidai lokacin da wayarsa ta d'auki k'ara,
"Ina zuwa ya mike tsaye tare da ciro wayar ya fito daga d'akin yana amsar wayar "girgiza kanta kawai tayi "Allah ya kyauta ,"ko a kauye an daina irin wannan auren daka yiwa diyarka .."
Ta mike ta fito daga d'akin ranta a 'bace .

********

Misalin karfe takwas na daren ranar , Abban yesmin ya sallami kowa, yace "duk masu jiran Kai amarya suna iya tafiya dan shi da kanshi zai kai yesmin gidan mijinta, "sabon salo, sautin daya karad'e gidan kenan ,mutane nata cecekuce akan tsarin daya zo dashi ,ta yaya ga tarin yan'uwa da jama'a ta kowani bangare amman yace "shine zai kaita kamar wata mara gata "

daya bayan day'a mutane suka soma bawa kafarsu iska, gidan ya saura sai tsirarrun dagin, suma 'yan ganin kwakwaf ne ,Abban yesmin ya tura ummanta cewar ta fito ya kaita.

"Koda umma ta shiga d'akin ta isketa kwance babu yadda take numfashi ma da kyar take fitarwa tamkar mai cutar Asma , hankalin umma a tashe ra karasa gareta ta dagota ,ta rungumeta ajikinta ,jikinta yayi wani irin mugun zafi kamar garwashin wuta ,kwantar daita tayi ta shiga bayi ta dibo ruwa a cikin karamin roba da towel ta dawo kusa daita ta dagota ta cire mata kayan jikinta ta soma goge mata jiki ,tana rarrashi ,bayan ta gama goge Mata jiki ta maida mata kayanta ta sake shiryata ,sannan ta fad'a Mata sakon abbanta , aiko gama jin sakon ke da wuya yesmin ta rushe da wani sabon kuka, numfashinta na k'ok'arin barin gangar jikinta ,"take everything very easy yesmin " idan kikayi sanadiyyar rasa rayuwarki wanda mahaifinki ya hadaki dashi bai da hassara ,ki daure wata rana sai labari , Allah yabaki zaman lafiya agidan aurenki , Allah yasanyawa rayuwar aurenki Albarka ,kuka take sosai tare da kamkame umma ajikinta "ba zani ba umma ,karki bari a tafi dani gidansa wallahi ba zani ba ni banason wanda Abba ya bani umma ki taimaka karki bari akaini .....
tana kuka umma na kuka suna rungume da juna da kyar umma ta zareta ta fito daga d'akin .


Kin shiru taki fitowa yasa abban da kanshi ya taka ya shiga har d'akin nata ,aiko gama shigowarshi d'akin ke da wuya ,ta mike tana janyo numfashin da kyar ,biyu take ganin abbanta dake tsaye agabanta yana bata umarni, taku day'a biyu tayi ta tsaya cigaba s tafiya ,ta rike kanta da hannuwanta duka saboda jiri na neman kaita kasa ,da sauri Abba ya k'araso gareta , ta zube jikinsa sumammiya " subuhanallahi ya furta da karfi yana kiran sunanta "yesmin !yesmin !!!

"Hafsa ...ya kwallawa umma kira ta shigo d'akin a gigice tana dubansa "me ya sameta na ga kanar bata numfashi ?
"Eh suma tayi ......."
Ya fad'a ya cicibota ya kwantar daita akan bed tare da cire mata mayafin dake lullu'be da jikinta .

umma ta juya da sauri zata bar d'akin "Ina Zaki kuma ?
"Zan Kira likita ne "ki barta kawai zoki tsaya tare daita, Ina zuwa zanje nazo da likitan da zai dubata " kafin nan ki dibo ruwa ki yayyafa mata, yayi maganar kamar zaiyi kuka ,dan shi kad'ai yasan yadda yake ji akan abinda yayiwa tilon diyarsa .."wannan shine hukuncin abinda yaga yafi dacewa da rayuwarta dashi kansa, ya fice daga d'akin cikin sauri kamar zai tuntsura.


Kasa furta komai umma tayi ta Isa kusa da yesmin ta zauna bayan ta dibo ruwa tashiga shafa mata a fuska tana zubda hawayen tausayinta..


Kwance yake akan doguwar kujerar Mai zaman mutun uku dake zagaye da parlour'n ,har lokacin ya kasa daina mamakin faruwa abinda ya faru a safiyar yau din ne , sannan har lokacin yana assessing maganar, yana tuna lokacin da yake karanto masa dogon shirhi fuskarsa dauke da murmushi .

Bai jima da kwanciyar ba ,aka soma kwankwasa kofar parlour'n ,Yana daga kwance ya bawa mai kwankwasa kofar umarnin shigowa ,Wanda yashigo parlour'n a lokacin ne yasa shi mikewa da sauri ya zuuna tare da zuba masa ido ..





Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 25

"Zuba masa ido kawai Dr jamil yayi yana cigaba da kallonsa zuciyarsa na harbawa , Shima abban yesmin din kallonsa yake, yana jin abubuwa guda biyu a lokaci day'a a kanshi farinciki da bakinciki .

bangaren Dr jamil Shima zuciyarsa cike take fal da tashin hankali bai ta'ba tunanin faruwar abinda ya faru a safiyar yau din ba ,yau tazo masa da abubuwa da yawa ,tashin hankali da farinciki mara misaltuwa " sai dai har lokacin zuciyarsa rawa take ,ya kasa tabbatar da abinda aminin nasa yayi masa "shin gaske ne marwa ta zamo Mata a gareshi ko kuwa kunnuwansa ne suka jiyo masa hakan ?
gabad'aya ya kasa gasganta haka , har lokacin da abban yesmin ya k'araso garesa ya riko hannuyensa tare da mikar dashi tsaye bisa kafafunsa still yana dubansa ....


Muryar Dr Jamil can kasa tamkar mai koyon magana yace "da gaske ne abinda ya faru a safiyar yau din nan ko kuwa mafarkin dana saba yi ne ya faru dani ?

"Gaske ne ba mafarki ba ,idan ma mafarki ka d'aukeshi muje yanzu ka tabbatarwa kanka "ya k'arasa maganar yana kamo hannunsa suka fita daga Parlour'n ....


"A yanzu ya sake tabbatar da irin tsananin kaunar da habib din ke masa ,tabbas habib masoyi ne na hakika wanda samun irinsa ke da wuya a duniyar nan , duk duniya bashi da masoyin daya Kai shi daraja a cikin zuciyarsa .


"Kai tsaye ya zartar da hukuncinsa akansa ,to Yaya a kayi ma yasan Yana son yesmin din ?
"To ko yesmin dince ta sanar masa cewar tana son shi ?
Yayiwa kanshi tambayar ,yayinda wasu wurare a cikin kirjinshi ke bud'ewa suna sake bawa Abban yesmin matsayi da girma cikinta, Duk yadda ya Kai da jin kima da darajar amininsa Kuma surikinsa a yanxu a cikin zuciyarsa ya kasa ...
"habib ya nusarsheshi abubuwa da dama a rayuwa ..
"Kimarsa ta zarta komai garesa"shi kuwa me zai cewa wannan abun alkhari da yayi masa ..?
"Da me zai saka masa da wannan hallaci da mutuntakar da yayi masa ?

"Jikin Dr Jamil a matukar sanyaye ya shiga cikin gidan zuciyarsa na wani irin dokawa da karfin gaske , d'aga kafafunsa kawai yake, yana cigaba da tafiya ,yayinda zuciyarsa ke Allah Allah ya d'aura idanunshi a kanta .

Suna gama shiga gidan Kai tsaye d'akin yesmin din suka nufa, abban yesmin ya tura kofar d'akin ya shiga bakinsa d'auke da sallama"assalamu alaikum "
d'ago Kai umma tayi da niyyar amsawa idanunta ya sauka akan Dr Jamil dake k'ok'arin shigowa , sai da gaban ya Fad'i data gansu tare kallo day'a tayi masa ta d'auke idanunta ,haka nan ta tsinci zuciyarta da shiga cikin damuwa da tashin hankali,"yaya har yanzu bata farfado bane ?inji cewar Abban yesmin .
take gaban Dr

Please Login or Register in order to submit comment