Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayin suna romancing juna, kafin daga baya Dr Jamil yayi dif Yana k'ok'arin janye bakinsa cikin nata suka dawo normal ,yana maida ajiyar zuciya ..

Yana Shirin soma magana sai ga abban yesmin da ummanta su k'araso gurin "kana nan tare da babynka a she ?

"Dr Jamil ya kalli yesmin sannan ya juya ya kalli abbanta ya girgiza masa Kai al'amun eh" Ina nan Ina ban hakuri "
Abban yesmin yayi murmushi yace "ai gara ka bayar da hakuri dan naga al'amun baby ta d'auki zafi da Kai sosai ko da yake Kai kayi laifi ai"
Dr Jamil yace " ai yanzu kam ta huce dan tun d'azu nake aikin rarrashi tana zuba min shagwa'ba... suka sake yin murmushi gabad'ayansu "yayinda ita dai umma murmushin dole tayi dan gaskiya ta tsani ganin diyarta kusa da Dr Jamil"

Abban yesmin ya juya har yayi taku day'a umma ta jawo hannun abban yesmin "Abban yesmin kai ma ka zauna ayi hirar da Kai mana ,ko ita ta yesmin din ta taso muje ciki gurin Sauran yan'uwanta ,tayi maganar tana jefawa yesmin din wani kallo daya sa hantar cikinta motsawa har bata San sanda ta mike jikinta a sanyaye ta soma k'ok'arin barin gurin ba"

Ahankali abban yesmin ya tsurawa umma ido Yana kallonta , ya lura tana yawon shishigi a tsakanin Dr da yesmin , ya rasa dalilinta na kin ganin aminishi tare da diyarsa "
"ya kula duk sanda ta gansu tare hankalinta na tashi akan hakan ,Kuma bata son ganinsu tare ,shi dai yasan ko giyar hauka Dr Jamil ya sha ba zai soma ganganci a kan yesmin dinsa ba ,illa zallar shakuwa dake tsakaninsu ,Kuma bata Isa ta katseta ba ...yana kallonta ta juya sannu a hankali tabi bayan diyarta "


Gefe guda umma ta janyo yesmin Wanda kad'an ya rage bata buga kanta da bango ba , sannan ta dinga zazzaga mata fad'a da balai iri iri ,"idan na sake ganin kina wannan d'an iskan rawar jikin a kanshi ,sai na 'bata Miki rai ,shashar banza kawai shashar wofi kina girma amman kullun kamar kina cin Kashi ,dubi sauran yan'uwanki kiga rayuwarsu ,haka kikaga suna yi ?
",daga cewa Ina Dr jamil yake ,shine duk Kika wani rud'e Kika gigice " sau nawa zan fad'a miki bana son kusancinsa dake ?
Kuka yesmin ta rushe dashi ,banason ganinki kusa dashi ,a halin yanzu na tsani naganki tare dashi ........ta k'arasa fad'ar haka tana d'auketa da mari ...

Yesmin ta dafe kuncinta inda umma ta mareta kana tace "dan Allah umma kiyi hakuri ,amman ki daina tsanarsa dan wallahi bazan iya ....sai Kuma tayi shiru ta kasa karasawa tana sunkuyar da kanta kasa hawaye na tsiyaya .

"Me ye bazaki iya ba aciki fad'a min Ina jinki ?

Ta girgiza mata Kai hawaye na cigaba da gangaro mata "magana fa nake Miki kina jina kin kaki yi min shiru "
" To ..to ni umman gaskiya Ina son Dr jamil .......

Taga taga umma tayi ta jingina da bangon gurin wanda bancin shi sai dai aga tayi fad'uwar yan bori , tayi mugun kafeta da idanunta tana dubanta cike da matsanancin mamaki kafin daga baya tasoma waige waige ko wani bai ji abinda ta fad'a ba "


k'arasowa tayi ta zuba mata ido tana jin wani irin zallar 'bacin rai, ji take gabad'aya nan duniya yesmin tagama tozartata ," a yaushe diyaryata ta kamu da sonshi da har zata iya fuskantarta da maganar ?
Tsabar bakinciki bata San sanda ta rufe da duka ba "sai dai ki mutu mara kunya, ko kunya bakiji ba ,ki rasa wanda zakice kina so sai abokin babanki, aminin mahaifinki Wanda sukayi aure rana day'a ,kina ganin Dr da ya haihu da yanzu Yana da yara age mate dinki ,shine dan Baki da kunya zakice wai wani Wai kina son shi ,to wallahi idan na sake jin kin furta kina son shi sai na miki mahaukacin bugun da sai kin bakunci lahiri .

"wannan dukan dana miki nafila ne , ni tashi ki bani guri ,yesmin ta mike jikinta na rawa har ta juya umma tace "dawo nan "yesmin ta dawo ta tsaya nesa kad'an da ita " Sauran naji kinyi zance da wani Kuma ki goge hawayenki yanzu banason ganin digon hawaye akan fuskarki ,ganin babu al'amun saduda a tattare daita yasa ta kamo hannunta suka nufi lunbum gidan.

tana shiga ta zaunar daita "rarrashinta ta soma "marwa ki bar kuka hakan nima banso dukanki ba ,amman me yasa Kika zabi soyayya da aminin mahaifinki ?
Yesmin tayi shiru taki cewa komai saboda Koda tace zatayi maganar ma batasan me zata fadawa ummanta ta fahimta ba "
"ko wani Abu yake Miki da Kika zabi rayuwa dashi ? Umma ta jiho mata tmbyr da bata yi tsamani ba .
Kirjinta na bugawa ta girgiza mata Kai "to why yesmin da zaki lakata rayuwarki da sa'an ubanki ,kice shi kike so "shawarata karki soma fad'awa abbanki wannan matanar dan shi sai yafini shiga damuwa da tashin hankali daga karahe yayi miki dukan mutuwa "

Tsawon minti goma suna zaune umma na mata fad'a mai ratsa jiki ,tare da muna mata illar auren tsohon da take son yi , yesmin tayi shiru taki cewa komai , illa hawaye dake gangaro mata, hannunta umma "ta kamo cikin nata tace "shikenan kukan ya Isa haka ,ba dai Dr Jamil kike so ba ?
Da sauri yesmin ta d'aga mata al'amun eh "okay ki kwantar da hankalinki karkiyi maganar da kowa ni zan San abun yi ,tana magana tana goge mata hawaye har hawayenta ya tsaya tayi tagumi tare da tsura mata ido tana tunani har kusan la'asar suna zaune agurin ....

Bangaren faruk kuwa duk wunin ranar kasa samun natsuwa yayi ,hakan tunanin yesmin yaki barin zuciyarsa ta huta ,wani irin zallar kaunarta ne ya dinga jin Yana shiga zuciyarsa Yana mamaye kowa ni sashi na jikinsa , gabad'aya ya kasa samun sukuni da natsuwar zuciya ,duk inda tayi yana binta da idanushi Yana jin kamar ya fixgota ,ita din irin typing din da yake so da muradi ce ,komai nata yayi masa .
yayi shiru kawai ya soma tunanin irin rayuwar da zasu gudanar da ita idan ya sameta a rayuwarshi ,a tunaninta dayake ,wai gasu a makwanci daya Yana aika mata da salon wasanin daban daban Yana kissing dinta na fitar hankali Kiran sallar magariba ne ya dawo dashi cikin haiyacinsa ..

*******

Washegari umma da yesmin suna zaune a lambu ,tana sake tausasa zuciyarta akan Dr jamil sai ga faruk ya k'araso gurin, umma na ganinsa ta fad'ad'da fuskarta da murmushi , tana jin Ina ma a ce faruk diyarya take son ai da bata san irin murna da dadin da zata ji ba ... "

Muryarsa a hankali ya Gaishe da umma , Yana sunkuyar da kanshi kasa , al'amun jin kunya , yayinda tuni umma ta mike tsaye tana amsa masa gaisuwarsa , tare da nuna masa kujerar data mike "a'a kiyi zamanki umma ga wasu kujeru can "
"karka damu kayi zamanka anan wucewa zanyi yanzu ,ta juya inda yesmin take zaune tana shafa mata kirjinta al'amun ta kwantar da hankalinta ,sannan ta juya tana tunanin yesmin .."

Bayan tafiyar umma faruk ya tsura yesmin ido har baya kaunar abinda zai sa ya d'auke idanunshi akanta ,yarinya ta had'u sosai gata da wani irin kyau mai tafiyar da ruhi , a zaunen da yake kawai yaga ya kamata ya soma amayar mata da abinda ke ransa tun kafin wani yayi masa shigar sauri ,dan yasan irinsu nan da nan an kama , ahankali yasoma magana "yesmin..... ya Kira sunanta cikin wata irin muryar mai bugar da zuciya ,banza tayi masa ,sannan taki d'agowa ta kalli inda yake , gabad'aya ma tayi kamar bata San yana gurin ba "
"Yesmin ya sake kiranta ta sake masa banza bai damu ba ya cigaba da magana "a iya tsawon rayuwata ban ta'ba cin karo da abinda nake so Kuma ya d'auki hankali ba sai jiya dana dira a garin nan " Ina sonki soyayya irinta aure ... take maganar tashi tasa numfashinta k'ok'arin barin jikinta while zuciyarta ta shiga dokawa da karfin gaske ta d'ago da sauri tana duban bayanta dan a tunaninta ko da wata yesmin din yake dan bataji ya ambaci sunanta ba , murmushi gefen baki yayi a daidai lokacin data juyo ta kalleshi ,ya soma magana Cikin salon jan hankali " dake nake ba da wata ba ko akwai wata zaune a gurin nan ?
" Ta girgiza masa Kai tana k'ok'arin dawo da numfashinta da yake barazanar d'aukewa "me zaki ce akaina Ni dai na gani Kuma Ina so da Aure ya k'arasa fad'ar haka yana matsowa tayi saurin kawar da fuskarta ,da kyar faruk ya cigaba da magana Cikin karfin hali dan a kallon da yake mata zai dan Sha fama kafin ta amince amman duk runtsi duk wuya zai yi hakuri dan yarinyar ta cancaci fiyye da haka , za'a iya yin komai akanta " kiyi tunani akaina ,sannan karki duba halakar dake tsakaninmu kice zakiyiwa zuciyarki dole no ki soni tsakani da Allah kamar yadda nake sonki ita kam kallonsa kawai take ga dai shi yaro matashi mai kyau amman Ina ko digon son shi bata ji a ranta ba ,asalima bata jin zata iya rayuwarta dashi ,ya kalleta tashi muje muga gari "

"Kayi hakuri ka tafi kawai abunka kaina ke ciwo "okay shikenan bari na bari zuwa duk lokacin da kikaji sauki ,ya dade agurin zaune har sai daya ga ta mike shima ya mike suka jira suka soma tafiya sun kawo harabar gidan sai ga motar Dr Jamil tashigo gidan ......


Mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_HAJIYA MARYAM _

_(JIKAR KULU )_


warning!!!

don't read this novel if you know you are not married...


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan labarin na kudi ne ,ga masu bukatar karantawa zasu biya 300 ,a tuntu'bi wannan number's din dominn k'arin bayani 08059623096 or 08032384602 ,ko kuma a sauke manhajata a play store domin samun tsofaffin littafaina da sababbi masu zuwa ,a shiga searching a rubuta sunana kamar haka *AYSHA A BAGUDO* sai a sauke manhajata cikin sauki "

Page 17


"Cak yesmin taja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiyar da take , ta tsaya kawai tana kallon shigowar motarsa ,har sanda motar ta k'arasa shigowa harabar gidan , ta nufi inda aka tanada domin ajiye motoci,
bata d'auke idanunta a kan motar ba ,yayinda faruk shima ya ja ya tsaya, ya kasa barinta, yana jiran ta motsa su k'arasa shiga cikin gidan .


Shi kuwa Dr jamil bak'aramin tashin hankali da hargitsi zuciyarsa ta shiga a lokaci ba, saboda ganin da yayi musu ,duk da shi da kanshi ya bawa zuciyarta damar samu wani ,har ma da yi mata fatan samun wanda ya fi shi a komai ,amman a yanzu daya ganta tare da faruk hankalinsa idan yayi dubu to ya tashi ,banda dokawa babu abinda zuciyarsa ke yi ,tunda yake bai ta'ba ganin abinda ya d'aga masa hankali har ma yayi k'ok'arin bugar masa da zuciya kamar ganin yesmin dinsa tare da faruk ba ,gani yake kamar zata iya yarda ta amincewa faruk din har ma ta mallaka masa kanta ne "

"Me yasa zaka damu kanka alhalin kaine ka bukaci hakan daga gareta ? Zuciyarsa ta jiho masa tambayar ,
Runtse idanunshi yayi gam yana cinza lip's dinsa na kasa ,"tabbas ni ne na bukaci hakan gashi tun ba'aje koina ba zanyi nadamar abinda na aikata , "me zanyi kenan ?
"Babu abinda zakayi illa lokacin yayi da kamata kayi aure ,ya furta hakan cikin ransa .....
"To wa zan aura ?
"Wacece zata iya dani ?

" Kusan minti goma suna tsaye batare da sunyi k'ok'arin shiga ciki ba ,yayinda zuwa wannan lokacin faruk bai yi sanya a gwiwa ba , wasu kalamain soyayya masu sanyi da shiga zuciya yake fad'awa yesmin, amman ita Sam ba shine a gabanta ba ,bare wasu kalamansa na banza , gabad'aya ita hankalinta da natsuwarta suna ga Dr Jamil dake zaune cikin motarsa "


Da kyar Dr Jamil ya kashe motar, tare da yunkurawa ya fito cikin wasu had'add'un manya kaya , dark green dinki kaftan mai hannun links, rigar da kad'an ta wuce gwaiwarsa, idanunshi manne da farin glass kamar Koda yaushe .

tun sanda ya fito daga cikin motar , harabar gurin ya sauya da kamshi turarensa mai sanyi da kashe sansar jiki ,faruk na jin yadda ta sauke ajiyar zuciya , yayinda gabad'aya yanayinta ya sauya wanda ya rasa dalilin faruwar hakan .

lumshe idanunta tayi sakamakon wani sanyi da taji yana mammayeta gangar jiki , tun daga tsakiyar kanta har zuwa sansar jikinta take jin son shi na dawainiya daita "

Kulle motar yayi ya jingina jikinsa da jikin motar ,ya hard'e kafafunsa kamar yadda matasa kanyi ,kana ya ciro wayarsa daga aljihun wandonsa ya soma neman layin amininsa, batare daya kalli inda suke tsaye ba, duk kuwa da yadda yake jin zuciyarsa ke bugawa , Kira day'a biyu abban yesmin ya d'auka "ya'akayi abokina ko har ka k'araso ?
"Na karaso Gani a compound Ina jiranka" "okay bani minti biyu , ka k'arasa lambu ,yanzu zan fito "
jin abinda abban yesmin ya fad'a yasa Dr Jamil ya soma takawa a hankali , idan ka kalleshi zaka d'auka a natse yake ,amman sam abun ba haka bane d'auriya ce kawai irin tasa ,da kuzarin daya sanyawa gangar jikinsa, ta gefensu yazo ya wuce, yana baza musu musu kamshin dad'd'ad'en turarensa mai kashe jiki da tsuma zuciya ,yayinda har lokacin idanun yesmin ke kanshi ta kasa daina kallonsa dan ahankali ba k'araminn kyau yayi mata ba , faruk ya gaishe shi kasancewar yasan ko shi din wanene ga mahaifin yesmin .

fuskar Dr Jamil cike da fara'ar dole ya d'an tsaya jim ya amsa "kana lafiya faruk ?
iya abinda ya iya furtawa kenan ya wucesu kirjinsa kamar zai tarwatse tsabar bakinciki da tashin hankali daya tsinci kanshi ciki , amman idan ka kalli fuskarsa bazaka iya fahimtar yana tattare da damuwa ba ..

Juyowa faruk yayi a natse bangaren da yesmin take tsaye ,yaga gabad'aya ta mugun tattara hankalinta da natsuwarta akan Dr Jamil , kafad'arsa ya d'an kai ya goga tata kafad'ar "wannan kallon fa da kike binsa dashi ?
Take tayi firgigib ta dawo haiyacinta batare da ta amsa masa ba ,illa takaicin nuna ko in kular da Dr Jamil yayi mata ,hakan ne ma yasa taki gaishe shi a lokacin da faruk ya gaishesa ,
bugu da K'ari kuma zuciyarta ta shiga chakwalkwalin chakwakiyya " kenan da gaske dai tunaninta zai tabbata Dr jamil ba sonta tsakani da Allah yake ba kawai zallar sha'awarta yake ..
"Hankalinta yayi mugu mugun tashi taji kamar tabi bayansa taje ta saka masa kukan ya dawo mata da burduncinta daya rabata dashi ... amman taga idan tayi haka fallas kanta kawai zatayi ,saboda ga faruk ya kasa ya tare yaki tafiya ,bare ta samu damar binsa ,cikin haka sai ga abbanta ya fito kunnenshi manne da waya yana magana kasa kasa .

Da wani irin kallon mamaki ya bisu dashi, dan bai ta'ba ganin diyarsa tsaye da ko wani irin nmj ba , Koda kuwa cikin yan'uwansa ne ,idan ka ganta tare da wani namiji sai dai shi ko Dr Jamil , Yana Shirin d'auke kanshi akansu faruk yayi saurin rusunawq ya gaisheshi ,ya amsa tare da wucesu ya cigaba da amsar wayarsa "

Hankalin yesmin a matukar tashe ,ta juya tayi cikin gida, zuciyar na wani irin mahaukaci buguwa da karfi ,faruk ya biyo bayanta yana kiranta amman tayi banza dashi .
Surutai kawai ta hai yi "Dr Jamil baya sona ni kad'ai nake wahala akanshi "kalmar son daya Sha fad'a min a baya , a she karya ne ba gaskiya ba?
"Koda yake bai kamata kiyi saurin Yanke hukunci, alhalin yasan faruk d'anuwanki, kuma ai ma bai San abinda ke zuciyar faruk din ba ta Yaya Zaki saurin Yanke hukunci rashin nuna damuwarsa akanki ?
Wad'an nan maganganun, da tayi da zuciyarta, ya d'an kwantar mata da hankali .


Lokacin da Abban yesmin ya Isa lambu ya iske Dr Jamil zaune akan daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin ya zabga uban tagumi , idanunshi gabad'aya sun kad'a sun jajir, karasowar yayi kusa dashi amman har lokacin Dr Jamil bai San da tsayuwar mutun a gurin ba .

jin saukar hannun abban yesmin a saman kafad'arsa , yasa ya dawo cikin hankalinsa, ya d'an lumshe ido Yana kirkiro murmushin dole, abban yesmin ya kasa zama ya cigaba da tsayuwa agurin" tabbas akwai abinda ke damun aminin nasa , wanda ba tun yau ya fahimci hakan a tattare dashi ba ,amman a yau ya kudurci anniyar tambayarsa abinda ke damunsa , sunansa ya Kira a hankali "Jamil me ke damunka na lura tun kafin tafiyarmu London kake cikin damuwa ka d'aure ka fad'a min
damuwarka?
ya fad'i haka Yana janyo kujera kusa dashi ya zauna "

Kasa had'a idanu dashi Dr yayi ,illa murmushi da yayi yace "kai haba ni kuwa me zai dameni har da zanyi tunani ,idan ma akwai abinda ke damuna bai wuce tunanin yarinyar da zata taimaka ta aureni mu k'arasa rayuwarmu tare daita ba "
a tare suka sa dariya suna tafawa " Kai din za'a taimakawa ? Inji cewar abban yesmin ..

Dr Jamil ya dage masa girarsa day'a yana zare farin glass din dake manne da idanushi ,ya makale a aljihunsa gaban rigarsa " sosai kuwa, ko ka manta sheakaruna a yanzu ne ?
"Ina fa zan manta amman duk da haka ka wuce taimako , dan akwai masu shekarunka da har yanzu ba'a sa shi a lalle ba Kuma idan sun tashi aure yan shila zasu aura ..."
Sake kwashewa da dariya sukayi "Allah abokina sai dai gaskiya Ina son ganinka tare da iyali domin shima cikar kima da darajarka ,idan kuma tsohuwar zuma zamu komawa to sai kayi bayani ? Abban yesmin ya k'arasa maganar Yana guntse dariyarsa .

Dr Jamil ya had'e ranshi sosai kamar bashi, ya gama dariya yanzu ba, yace "na dawo da macen data gujeni saboda bata haihuwa Dani ba ?
" No imposible i cant do that , aiko matan duniya sun kare bazan dawo daita gidana ba , Allah dai ya had'a kowa da rabonshi mafi alkhari " amman nida leemat har abada "
" To ameen inji cewar abban yesmin ,haka dai suka cigaba da tautaunawa har suka kawo kan cutar annobar coronavirus data addabi kasashen duniya a yanzu ,Dr Jamil yace "kasan wani aboki ..?
Girgiza Kai abban yesmin yayi yana sauraronsa, Dr Jamil ya numfasa ya cigaba " wannan cutar babu abinda zamuce ,sai allahumma ajirni fi musibatihi wakhalfini khairan minha ,sai Kuma yawon istigari , sai dai ita wannan cutar, Ina tabbatar maka bazata kama muslimai kon mutun daya ba ,idan ma takamashi bazata masa illar komai ba ,sai lafiya da zata Kara masa, sannan ya cigaba da samun 'yan kudad'ensa yana zubawa a aljihu , albarkaci annabi muhammadu ....abban yesmin yayi saurin karashewa da s.a.w yana riko hannun amininsa yana dariya "ai gskiya ne nan hirar tasu ta koma kan annobar data addabi kasashen duniya "


Can cikin gidan kuwa gabad'aya jikokin hajiya fatima zagaye suke daita har yesmin ,sai dai ita sam hirar da suke bata gabanta ,hankalinta na can gurin Dr Jamil, jira take ta samu damar kebewa dashi "cikin haka Yaya faruk ya shigo d'akin ,shigowarsa tasa day'a bayan daya yammatan suka shiga gaisheshi suna barin d'akin ,shi Kuma Yana amsa musu da kyar kamar wanda aka yiwa dole , d'akin ya saura daga shi sai hjy kaka da wedad sai ita .

A hankali ya samu guri opposite dinta ya zauna yana fuskartata, yayinda yesmin ko kallon inda yake bata yi ba saboda ta shi take yi ba ,damuwar ta zarta shigowarsa mahimananci tana cikin tunani kawai , taji muryar yaya faruk "hajiya kaka da yake shima haka yake kiranta "daga jiya zuwa yanzu na yanke shawarar gaya Miki yarinyar da nake son aure "
yesmin na jin haka kirjinta ya buga ..... gabad'aya jikinta ya d'auki rawa sai dai ta kasa kallon inda yake , hjy kaka da suka yi murmushin jin dadi, yayinda a cikin zuciyar hjy kaka ta fara adduar Allah yasa acikin jikokinta ne .


Cike da matsanancin murna tace "Ina jinka wace mai sa'ar ce tayi dace ?
" Wallahi hjy kaka Ina son yarinyar sosai "but I'm not sure ko zata so ni ?
Wedad tayi dariya tace" karka damu yayana "she will love you more than yadda kake sonta " ka kuwa San yadda ka had'u kuwa ?
"Wedad ai ba kyau ne ko wani Abu ke sa so ba ,wannan daga Allah ne kin gane ai ?
"Haka ne Yaya inji cewar wedad " ita wannan yarinya Ina sonta fiyye da komai tunda na ganta na kasa samun sukuni ,na kasa samun natsuwar zuciya Ina jin...

"Yesmin da sai lokacin ta kalleshi tace " yanzu ka fad'a cikin duniyar soyayya ,but kar ka zurma gabad'aya ,koma nace karka ka fad'a soyayya mai tsanani" faruk ya tsura mata ido Yana kallon d'an karamin bakinta da take motsawa a hankali kamar ba ita ke furta maganar ba yace "why "

Ta mike tsaye daga mazauninta tana bashi amsa "does who fall in luv she'd tears "faruk ya kalli hjy kaka da wedad yace "Wai haka ne kanwata ?
Wedad tayi murmushi tace "gaskiya ban sani ba Yaya, saboda ban ta'ba soyayyar ba, amman ita da fad'i haka, ai banga tana sharar hawaye ba,yesmin ta kalleta kamar tace wani Abu, sai Kuma tayi shiru, ta nufi window bangaren dama dan ta nan kad'ai zata samu damar hango Dr Jamil da abbanta, sai dai zuwa wannan lokacin shi kad'ai ta hango zaune ,yana rike da waya Yana daddanawa " shi kuwa faruk shiru yayi ya kasa amayar da abinda ke ranshi ,Yana tunanin Anya kuwa wani bai yi masa shigar sauri ba kuwa ?
Anya wani bai gama da zuciyarta ba ?
A kallon da yake wa kwayar idanunta tana cikin shaukin soyayyar wani, tun da ya d'aura idanunshi akanta kullun idanunta a jeme suke alamar zubda ruwan hawaye "ya kayi shiru yayana ka fad'a mana wacece kake so ?
Faruk yayi shiru ya cigaba da kallon bayan yesmin dake tsaye "karka ji komai yayana ka fad'a min babu fa macen da zata ce bata sonka ,kasa a ranka kana furtawa za tace....
Saurin dakatar daita yayi da hannunsa "na fad'a miki ba haka bane wedad , kyau kudi mulki ba shi

Please Login or Register in order to submit comment