Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace bros nifa bani na fito da itaba

Kallon bariki yayi yace Oya muje in kaiki gida

Tace Yarima plz muje mu shiga, zaiyi magana tace dan Allah, karka sa mutane suyi zargin wani abu tana maganan tare da kokarin San zubar da kwalla.....

Ganin haka yasa yayi dan tsaki tare da fad'in karki Fara cewa zakiyi min kuka a nan, dan naga kina da Arhan hawaye, babu yanda Yarima ya iya dole ya shiga shida abokanan shi da amarya da kawayenta, cikin hall din yayi mugun tsaruwa, wajan zaman amarya da ango daban su biyu, y'an jarida da masu hoto sai d'auka suke, kowa yana fad'in amarya da ango sun dace dinner din ya had'a manyan mutane ciki harda Mai martaba, Yarima bai San zaizo ba saida Ya ganshi shida abokanan shi, harda Mai girma governor da wasu masu mukami a gwamnati sun halarta, anyi watsi da naira kaman baza'a mutu ba, an yanka cake daka nan akace amarya da ango suzo suyi rawa, nan suka fara rawa duk da bariki ba a sake take ba, dan tana jin tsoran ko akwai wanda ya Santa a wajan, nan aka fito ana watsa musu naira mum din Yarima tayi musu liki Sosai, a cikin masu likin idon bariki ya sauka akan Alh madu, dam gabanta ya fad'i, musamman irin murmushin da taga yana sakar mata, gaba d'aya jikinta taji ya saki babu kwari, Yarima kaman ya Lura da ita gashi kuma mutane sunyi yawa ko ince maza dan haka Yarima yaja hannun Zainab suka koma suka zauna, Anci ansha kowa ya watse, Yarima yakai bariki gida da jikinta yake a muce ganin Alh madu a wajan dinner, yanda ta gode Allah ta canza layi ma balle ya mata barazana, toh inya fad'a ma Yarima fah?? Nan taji gabanta ya fara fad'i

Bariki harta Washe gari tana cikin zullumi Kar asirinta ya tonu, haulat Dai da khairat sunyi Mata kara domin a gidan suka kwana, dasu kuma ake komai, bariki na kwance haulat tace wai lafiya kuwa naga kinyi shuru??

Bariki tace kalau nake

Haulat tace dan bani wayarki in bud'e hotspots banda data gashi Ina son tura Abu.

Password din wayar bariki ta cire sannan ta mi'ka ma haulat wayan.....

Toh rana dai bata Karya inji masu iya magana yau juma'a aka d'aura auren Zainab musa da angonta Yarima Aliyu, akan sadaki naira dubu hamsin inda dubban jama'a suka shaida......

Bariki tunda taji an d'aura take ta godema Allah, domin anyi auranta cikin nasara ba tare da Yarima yasan gaskiya ba, a hankali tace yau zan fad'a maka koni wacece Yarima Indai aka kawo ni gidanka,..... Karfe hud'u dai dai aka zo aka d'auki amarya inda aka tafi da ita Zaria a can zata zauna Kafin a dawo da ita kaduna, gefen Yarima Nada aka kaita inda aka gyarashi harta wanda suka kawo amarya bariki hayansu tayi, an karrama amarya da danginta wajan su abinci da duk abunda suke bukata, nan sukace zasu wuce tunda sun kawota, anyi musu shatara na arziki Kafin nan suka wuce......

Wajan karfe 9 Yarima ya shigo d'akin amarya ba tare da Aboki ko d'aya ba, dan yace kallon da suka mata wajan dinner ya isa haka, bariki na zaune akan gado Yarima ya shigo tunda ya shigo gabanta ke faman fad'i, inda take ya nufa tare da cire mata gyalen dake kanta yace Alhmdlh tsarki ya tabbata da Allah daya nuna min wannan ranan, janyota yayi jikinshi yayi mata wani irin runguma, har tana jiyo ajiyan zuciyarshi, lokaci d'aya ya saketa tare da d'agota ya sauketa k'asa yace my princess muje muyi alwala muyi ma Allah godiya..... Gabanta taji yana fad'i yaka mata Yarima yasan gaskiya Kafin wani abu ya shiga tsakaninsu, wayarshi dake ajiyu yayi kara d'auka yayi yaga number kaman Karya d'aga, sai kuma ya d'auka, ban son mai aka fad'a mishi ba naga ya kashe da sauri tare da fara danna wayar duk wannan abunda ake suna tsaye shida bariki suna kallon juna amma shi idonshi nakan wayar.... Lokaci d'aya hawaye ya fara zuba a idonshi tare da fad'in today is our wedding night, the day dat I have waiting for since d day dat I have meet u, but you destroy my life, you have cheated me..... Cikin tashin hankali tace Yarima maiya far.... Yace keep quiet tare da ri'ke kirjinshi alaman yana mishi ciwo yana kokarin yin magana ya fara tari Sosai lokaci d'aya yayi k'asa......


*TOH MASU MIN KORAFI IN K'ARA YAWAN RUBUTU YAU DAI NA K'ARA, AMMA KUDA KUGA WANI POSTING DIN SAI NAN DA KWANA UKU, BUT IN NAGA COMMENTS DINKU YAU YAYI YAWA MAY BE GOBE IN MUKU*





*not edited*


~MARYAM OBAM~





~MARYAM OBAM~




~MARYAM OBAM~







[9/1, 7:12 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*WANNAN PAGE DIN NAKU NE*
*JANAF, SA'ADATU ALKALI TSAFE, MAIMUNA MATAR ABDULLAHI, MRS ADAM Y'AR MUTAN KAGARA, PRETTY MARDY, HAFNAN, XINNE SMART, AMENAT KABIR KIRU, ummyONtop, DEEJAT THANI, FARIDA BASHIR UMMU SAFWAN, HAUWA S ZARIA, BINTA UMAR ABBALE, AYSHA ALTO, FAUZY MB, UMMU AFFAN, SIS FAUZY Y'AR AMANAN KAINUWA WRITERS, WANNAN PAGE DIN DUKA NAKU NE*




*BOOK 2*


*PAGE 17*







Tari yake Sosai, bariki kuka ta Fara Tana fad'in Yarima Mai yake damunka?? Tare da tabashi tana son d'ago Shi ,hannunshi da yasa a baki yana tari ya cire ya fara kokarin tureta alaman tabar tabashi, amma jikinshi babu kwari ya kasa tureta din...... Wani irin tari yayi tare da yunkurin yin amai saiga jini nan..... Wani irin ihu ta saki mai ban tsoro tare da kiran nashiga uku Yarima maiya sameka??

Ganin jinin a bakinshi yana fita yasa ta fita da gudu, tana fita taga fadawa tace dan Allah kuzo Yarima zai mutu, tana maganan tana kuka da ihu, kuzo mu kaishi asibiti..... Da sauri suka shiga wasu kuma suka je fad'ama iyayenshi, koda fadawa suka shiga ganin Yarima sukayi a kwance yana wani irin nishi ga jini na zubar mai a baki, da sauri suka D'aukeshi suka fita dashi, suna cikin sashi a mota mum dinshi tazo, ganin halin da d'an nata yake ciki yasa ta Fara fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, Yarima maiya sameka, lokaci d'aya kuma tasa kuka, shiga motar tayi da sauri suka nufi asibiti...... Bariki Kafin ta karaso har Sun wuce dan haka ta Fara cewa sauran fadawan muje ku kaini dan Allah inda suka je..... Ganin kanta ko dankwali babu yasa wasu kuyangi dake tsaye wajan suka karaso suna fad'in Allah ya taimaki gimbiya, ki koma ki saka mayafi sai a kaiki,.

Sai a sannan bariki tasan a halinda take da gudu tayi ciki, inda ta d'auko mayafinta tana kokarin fita wayar Yarima dake d'akin ya fara K'ara dole yasa ta koma ta d'auki wayar babu suna number ne ke kiranshi harya tsinke bata d'auka ba..... Fita tazo yi lokaci d'aya kuma ta tsaya cak domin tunawa da abunda ya faru da Yarima, wanda tunda aka kirashi ta rasa gane kanshi,har wannan abun ya sameshi, danna wayan tayi da nufin ta shiga taga Mai aka turo mishi, gani tayi akwai password, shuru tayi tana nazari Mai Yarima ya gani?? Kodai wani ya fad'a mishi koni wacece?? Gabanta taji ya fara fad'i tunawa da kalaman daya Fara Mata Kafin ya fad'i...... Wani irin kuka ta saki mai ban tausayi, tare da fad'in shikenan2 sunyi nasara Sun fad'ama Yarima koni wacece kuka take Sosai, lokaci d'aya kuma ta fita da gudu inda taga mota na jiranta shiga tayi domin aka kaita asibiti da yake fadawa sun San asibitin da suke zuwa nan aka nufa da ita dan suna da tabbacin can aka Kai Yarima, tana mota tana kuka......

Kafin kace Mai har labari ya bazu cikin masarauta, Yarima Aliyu bashi da lafiya rai a hannun Allah, har wasu na cewa jini ke fita a bakinshi hala amaryanshi ba budurwa bace, wasu kuma suce kodai wani abu tayi mishi?? Haka dai ake ta jita jita, koda kuyangin gimbiya zinatu suka fad'a mata cikin tashin hankali itama tayi asibitin.....

Yarima Aliyu ko Kafin akai asibiti, ya daina koda motsi, ana zuwa akai emergency dashi, likitoci sukai kanshi aka fara dubashi, tare da bashi taimakon gaggawa....

mum ta kasa zama sai kuka takeyi ga fadawa a wajan da yawa, kowa ya shiga cikin damuwa.

basu dad'e ba saiga bariki ta karaso Tana kuka, tare da fad'in mum Ina Yarima?? Ina Yarima?? Mum din ri'keta tayi tare da rungumeta, ta kasa ko magana sai shafa ma bariki baya takeyi alaman tayi shuru......

Suna cikin haka saiga Zinatu tazo cikin Tashin hankali ganin Bariki wajan mum ko ba'a fad'a mata ba tasan itace amaryan da Yarima ya auro, da sauri ta nufi bariki ta fincikota tare da watsa mata Mari Tana fad'in mai kika ma Yarima?? Mai kika mishi?? Kuka ta saki Zinatu tare daci gaba da fad'in Wlh Idan wani abu ya sameshi saina kasheki W.......

Mum sai yanzu ta iya magana, tace Zinatu kina da hankali kuwa?? A gabana kike wannan abun?? Shi Yarima dinne yace miki ita ta mishi wani abu??

Cikin kuka tace mum, daka ita sai shi, Nasan wani abu tayi mishi......

Mum tace ya isa haka, plz ki barni inji da abunda yake damuna ban son rigima....

Bariki kam tunda zinatu ta mareta take ri'ke da wajan Tana kuka, ko bata tambaya ba tasan itace Uwar gidan Yarima Aliyu...... Bariki tasan lallai ko ba'a fad'a ba dole kowa yayi zarginta, abunda Zinatu ta fad'a gaskiya ne..... Kuka tayi k'asa tanayi tare da fargaban Kar wani abu ya sami Yarima dan bazata iya jura ba.....

Kowa na cikin Tashin hankali, ga doctors har yanzu basu fito ba...... Suna nan zaune saiga Mai martaba shida Hafsat Sun zo cikin Tashin hankali.

Mum ganin Mai martaba yasa ta tashi ta nufeshi tana kuka, tare da fad'in ina jin tsoro Kar Yarima ya mutu Aman jini yakeyi Ina tsor.....

Toshe mata baki Mai martaba yayi, tare da fad'in ki daina fad'in haka, Hafsat itama kuka ta Fara cikin Tashin hankali.....

Duka kowa shuru yayi babu Mai rarrashin wani, suna nan tsaye d'aya daka cikin doctors din ya fito, suna ganinshi suka nufeshi tare da fad'in Dr ya ake ciki, ganin Mai martaba yasa yace ranka ya dad'e wacece Zainab a cikin nan??

Da sauri mum tace ga tanan tare da nuna bariki, yace ok tare da kallon Bariki yace taso muje......

Da sauri ta tashi tabi Dr, kowa da abunda yake sakawa, Zinatu ta Fara fad'in mum kin gani ko kin gani wlh itace tayi mishi wani abu.....

Kowa shuru yayi ya kasa cewa koda uffam.... Suna jira suga ikon Allah......

Koda Bariki suka shiga oxygen din da akasa ma Yarima yana k'asa alaman yana son d'aukewa, kuma yana saka zero shikenan mutum ya mutu, da sauri Dr yace plz ki mishi magana sunanki yake ta kira pls say something karku rasa shi.......

Da sauri ta ri'ke Mai hannu tana kuka tare da fad'in Yarima karka bari wani abu ya sameka..... You know that I can't live without you, plz Yarima ka tashi kasan ina Sonka kaine rayuwa na, wlh bazan iya juran inga wani abu ya faru dakai ba......

Lokaci d'aya oxygen din ya fara k'aruwa alaman numfashin shi yana son dai daituwa.... Likitocin ganin haka yasa suka fara kallon juna alaman jin dad'i an fara nasara..... Bariki kuka take Sosai tana fad'in karya mutu ya barta....

Idonshi dake rufe ya fara zubar da hawaye...... Lokaci d'aya numfashin shi ya dai daita......

D'aya daka cikin doctors din yace ma Bariki yauwa komai yayi dai dai mu jira muga kuma yanda Abun zai kasance amma muna bukatar ki zauna har muga farkawanshi, muna nufin Kar kibar asibitin nan har sai munga ya farka ....

Cikin kuka tace babu inda zani Ina nan tare dashi

Dr din fita sukayi, inda suna fita Mai martaba yace ya akayi?? Mai yake faruwa dashi??

D'aya daka cikin Dr din yace ya samu bugawan zuciya ne, ina tunanin yaga abunda ya bashi tsoro ko mamaki, kuma daka duka alamu abunda ya gani ko yaji yana d'aya daka cikin abu masu muhimmanci a rayuwanshi, hakan yana faruwa wasu ma rasa ransu suke, a gskya masu rasa ransu ma sunfi yawa amma shi yayi Sa'a ko ince mun samu mun ceco rayuwanshi tare da taimakon Allah da kuma wannan baiwar Allah dake ciki, magananta da yaji shine yasa zuciyarshi ta Fara harbawa, inda badan ita ba toh gaskiya dasai dai kuji mummunan labari , dan haka dole ta zauna dashi muga yanda Allah zaiyi.....

Mai martaba godiya yayi ma Dr din tare da fad'in zamu iya ganinshi?? Sannan kana ganin zai tashi babu wani matsala??

Dr yace zaku iya ganinshi amma plz Kar kuyi magana, sannan zai tashi insha Allah Indai yarinyar na kusa dashi kuma yana jin magananta a kusa dashi.....

Mai martaba yayi ma Dr godiya, sannan suka shiga d'akin, ganin Bariki sukayi a zaune kusa dashi hannunta na ri'ke da nashi tana kuka.....

Kowa tsayawa yayi yana mamakin irin wannan Abun musamman mum damai martaba, ita dama zinatu bata shigo ba domin maganan Dr yasa taji wani iri tare da takaici..... Mum ce ta k'arasa kusa da inda Yarima din yake tare da kamo d'ayan hannunshi, fuskanshi tayi fayau ga hawaye a idonshi na zuba..... Mum itama hawayen ne yake zuba daka idonta, kowa dake wajan ya tausaya mishi...... Mai martaba ganin mum nason kuka mai sauti yasa ya kamota sukai waje, Hafsat da Bariki suka zauna a d'akin

Zinatu ce ta shigo d'akin ganin zinatu yasa bariki tashi tabar d'akin domin irin kallon da taga zinatu din nayi mata, kuma ko babu komai ya kamata ta dan bata waje ta gana da mijinta duk da bai farka ba.....

Fita Bariki tayi tana fita, Mai martaba yace Zainab ya kika fito?? Ko wani abu kike bukata??

Tace a'a Abba cikin jin kunya, na d'an basu waje ne.....

Mai martaba ya gane ta fito ne saboda Zinatu.......

Mum tace Zainab bai kamata ki fito ba ai, maza ki koma Kinji.....

Tace toh mum jiki a sanyaye Bariki ta shiga, abubuwa sun mata yawa, na farko Tana zullumin Mai aka fad'ama Yarima a waya, sannan maiya gani, duk wannan Abun suke ta faman Mata yawo a Kai..... Koda Bariki ta shiga zintau fita tayi

Bariki zama tayi kusa da Yarima tare da kurama fuskanshi ido, har yanzu yana hawaye, gaba d'aya zuciyarta ta tsinke, shidai har yanzu bai farka ba, toh wannan hawayen fah????..... Kiran Hafsat akayi a waya ta tashi tabar d'akin Tana fita kaman ance Yarima ya bud'e ido , a hankali ya bud'e idonshi ya sauka akan na Zainab wacce itama shi take kallo tana murna tare dason yin magana murna ya hanata......

Murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya ri'ke tare da matse su.....

A hankali tace Yarima Ina Sonka I can't live without you, tana maganan tana kuka, tace I was scare with your condition I......

Hannunshi yasa ya rufe Mata baki yana kokarin yin magana ya tsaya alaman ya tuna da wani abu....... Lokaci d'aya ya sake mata hannu tare da fad'in leave from hare I hate to see your face........

Cikin kuka tace Yarima zainab din'ka ce Yarima nice maina......

Ya daka mata tsawa tare da ri'ke kirjinshi yace I said leave from here ....... Su mum dake waje Suka shigo harda su zinatu, ganin Bariki na kuka Yarima shima hawaye ne ke zuba a idonshi gashi ya ri'ke kirjinshi...... Kallon iyayenshi yayi tare da fad'in mum tell her to leave from here....... Kowa kallonshi yake cikin mamaki da sauri Hafsat ta fita kiran doctor...... Mai martaba yace Aliyu matarka ce kake koranta?? Maita maka??...... Yace Abba plz tell her to leave I don't want to see her face.... Why am I still alive.... Dai dai lokacin doctor yazo yace kowa yabar d'akin........ Bariki da sauri ta fita Tana kuka lallai ta tabbatar an fad'ama Yarima ko ita wacece kuka take Sosai tare da barin asibitin ba tare da sanin kowa ba......



*Hmmmm Ashe masoya novel's din bariki suna da yawa?? Ban taba sani ba sai jiya🤣🤣🤣 lallai kuna son posting naga ruwan comments harda Wanda ban San suna karantawa ba, jiya Sun zuba comments, tunda hakane nima daka yanzu zan daina posting kullum Indai bakwa zuba comments kunga 50 50 kenan kuyi rowan comments inyi rowan posting😆😆😆 Ina sonku masoya novel's dina*







~MARYAM OBAM~
[9/2, 8:56 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO......*

*HASSAN ATK, MMN TWINS MAI DADDAWA A BANI NA GOMA🤣🤣, NAFISA ISA SHEHU, HAUWA LADAN KAURA NGD DA K'AUNA, 80K, MARYAM KANO MMN SAHLA, HAFSAT ALHASSAN😍, KINA RAINA MY SWT FRIEND HABIBA BUSY MY KAWAR AMANA*




*BOOK 2*


*PAGE 18*






Bariki kuka take Sosai tana tafiya a kafa, tafiya take bata san inda take wurga kafarta ba, ba komai bane a ranta sai yanda Yarima yake nuna tsanan ganinta, ta tabbata abunda take boyewa take burin in sunyi aure ta fad'ama Mai, wanda take burin Sanar Mai an samu wani ya fad'a Mai..... Zama tayi a k'asa gefen titi Tana kuka cikin Tashin hankali, bata taba tunanin abubuwa zasu cabe Mata haka ba, tunda take shirya wannan abun bata taba tunanin Idan ta fad'ama Yarima gaskiya dole iyayenshi Suma su san gaskiya tunda tayi amfani da iyayen bariki, gaba d'aya dana sani takeyi Wanda hausawa ke cewa k'eya ce, da yake dare ne Sosai babu mutane sai motoci dake Faman wucewa, suma motocin jifa jifa suke wucewa ba Sosai ba......

Bayan iyayen Yarima sun fito dasu zinatu, kowa da abunda yake sa'kawa cikin ranshi game da wannan al'amarin.....

Zinatu kam dad'i ya cikata Sosai, tare da aiyana ma ranta lallai Yarima ba virgin ya sami matarshi ba, tunda har Ya nuna baya son ganinta, yake nuna mata tsana k'arara, ji take kaman tai ihu dan murna, tare da fad'in da Gimbiya Amina batai bacci ba dana kirata na bata wannan kyakyawan labarin, amma Allah ya kaimu gobe......

Sunyi wajan 20mnt a wajan, sannan mai martaba yace Ina Zainab??

Nan mum ta kalli Hafsat tace ina tayi??

Hafsat tace nima ban sani ba mum,

Nan mum ta tambayi fadawan dake wajan ko sunga inda tayi??

D'aya daka cikin fadawan yace ta fita, daka ganin alama kuma waje tayi dan yanda ta fita da sauri tana kuka......

Nan mum tayi hanyar waje fadawa suka bita, itama hafsat bayan mum tabi....

Fita sukayi suna nemanta amma basu ganta ba, fadawa sukayi gaba suna dubata, wani daka cikin fadawan ya dawo da sauri yana fad'ama mum ga tacan a zaune a k'asa Tana kuka

Da sauri mum suka nufa inda take, tana nan zaune a k'asa Tana kuka mai cin rai..... Mum d'agota tayi tare da fad'in Zainab lafiyanki kuwa zaki fito bakin titi ki zauna kina kuka??

Zainab bata ce mata komai ba, domin har yanzu kukan take.....

Mum tace maza kuzo a kaiku gida, kuje ku huta tare da kamo hannunta sukai asibitin..... Suna k'okarin shiga sai ga Mai martaba shima yana fitowa, ganinshi yasa suka tsaya harya karaso inda suke.....

Mum tace Dr din ya fito ne??

Yace a'a nazo inga ko kun ganta Ashe ga tanan, suzo a kaisu gida dare yayi......

Da sauri bariki tace ni zan zauna dashi....

Mum tace Zainab kiyi hakuri kuje gida gobe da safe sai kuzo Kinji??

Kai ta d'aga amma badan taso ba, sai dai dan bazata iya musu da mum ba, haka suka tafi gida ita da Hafsat da Gimbiya zinatu damai martaba domin mum ce zata kwana dashi..... Duk da sun so suji maike faruwa in Dr Ya fito amma mum tace suje babu wani matsala tunda aiya farka......

Koda kowa ya fita, Yarima Aliyu ido ya lumshe tare da kwanciya yana Mai jin zafin abunda ya gani.... Dr ne ya mishi y'an dube dube sannan yace haba Aliyu, kana son sama kanka damuwa plz ka kwantar da hankalinka an fad'amin you r a doctor so nasan Idan na fad'a maka ka sami bugawan zuciya zaka San abunda ya kamata kayi wajan cire ma ranka abunda ya razana ka...... Yarima baiko Kalli Dr ba balle ya kulashi sarautar ta motsa..... Dr yaci gaba da fad'in Yarima ka gode ma Allah, amma kana son Zainab dinnan da yawa, Allah y.......

Yarima Aliyu ya Katse Dr da fad'in ina son a sallameni......

Dr yace sallama?

Yarima Aliyu yace yes yanzu

Dr yace a'ah ka Bari ka K'ara samun sauki, domin har yanzu baka dawo Normal ba.....

Yarima Aliyu tashi yayi dakyar ya zauna tare da fad'in Dr i am a Dr too I knw how to handle myself, and kace na samu buguwar zuciya?? So zamana a nan baida amfani dole inje gida a nan zan samu nutsuwa...

Dr shuru yayi yana nazari, maganan Yarima Aliyu gaskiya ne, Idan mutum ya sami buguwar zuciya irin haka, iz either an fad'a Mai wani abu ko ya gani, so inya duba yaga abun iz not true a hankali zai Fara samun lfya domin ya samu nutsuwa.......

Yarima Aliyu tashi yayi jiki babu kwari, kaman zai fad'i yayi sauri ya ri'ke hannun Dr din.......

Doctor din yace kayi a hankali, ka zauna let me call your parent su ri'ke ka, taimaka ma Yarima yayi ya zauna yana cije baki alaman yana jin jiki.....

Yarima Aliyu ba komai bane yasa yace a sallameshi sai dan yayi magana da Zainab bariki, akan yaudaran da ta mishi and baya jin zaiyi accepting d'inta a matsayin mata, matar data gama watsewa a duniya ko wani namiji ya santa t.........

Bud'e kofar da akayi yasa ya d'aga ido da yake zubar da hawaye, ganin mum da fadawa yayi, nan Dr yace su taimaka sukai Yarima Mota, kamashi sukayi suka fita, mum kallon d'an nata take cikin tausayawa.. Bayan an fitar da Yarima mum ta kalli Dr tace nidai banso ka yarda ya koma Gida ba, ina jin tsoran Kar wani abu ya sake samunshi.......

Dr yace karki damu, a gidan zaifi samun nutsuwa, Idan mutum yayi irin haka kika ga yace yana son tafiya akwai abunda yake son tabbatar wane, wanda shine yasa ya fad'a irin wannan matsalan, sannan komai ya faru call me.....

Mum godiya tama Dr sannan ta fita.

Bariki bayan sun karasa gida gefenta da aka kaita nan ta shiga, bedroom tayi Kai tsaye, ta zauna a k'asa tana kuka kaman ranta zai fita, wayan Yarima dake hannunta tayi k'ara alaman an turo Mai sa'ko, ajiye wayar tayi a gefe...... Tabbas tasan wannan ba komai bane, tunda tun Farko ta zabi sabama Allah, dole taga bacin rai, dama duk Wanda ya kauce hanyar Allah kuma yasan yabar hanya Mai Kyau dole ya had'u da ukuba tun a duniya, ita Allah na Sonta da rahma tunda harta gane ta kuma yi nadama, sai dai irin hanyar da tasa kanta koda kayi nadama sai an samu masu goranta maka, in bakayi wasa ba harta jikokinka sai anyi musu gori da fad'in ai kakarsu tsohuwar karuwa ce da, ko kuma ayi ma y'ay'anki ace ai uwarsu karuwa ce, in tayi aure tama miji laifi yace ta biyo halin uwa, tasha a nono, kai Wlh rayuwan bariki batayi ba ko kad'an... Kuka ta K'ara saki cikin jin zafin bata rayuwarta da tayi duk da kaddara ne ya sameta..... Wacce

Please Login or Register in order to submit comment