Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abunta, ansa Mata drive.

Dr yace hjy tana d'auke da ciki na wata uku, abunda yasa ta fad'i saboda jikinta yayi weak, is lyk Tana cikin damuwa so..... AI tuni mum tayi k'asa sumamma, shiko Mai martaba kasa magana yayi sai Innalillahi'wa inna ilaihirajiun da yake ta faman furtawa cikin ranshi, ganin mum tayi k'asa yasa ya d'agota da sauri inda Dr ya d'auko ruwa aka yayyafa Mata ta Farko .

Kuka tasa tare da fad'in Hafsat kin cuceni, kin gama dani, yanzu irin tarbiyan dana baki kenan? Kin d'auko mana Abun kunyar da ban taba jiba ko a zamanin baya ba, ace y'ar gidan sarauta tayi cikin shege, kuka Mum take Sosai cikin 'kunan rai, tare da ba'kin cikin abunda y'arta ta d'auko, shiko Mai martaba kukan zuci yake lallai basai kayi abuba Allah yake jarabtanka, koda baka kasance mazinaci ba, Allah yakan jarabceka da samun mata mazinaciya ko kuma cikin y'ay'anka, lallai babu yanda Allah bayayi akan wannan al'amarin, Allah yakan jarabci bayinshi tako Ina, yaga ya za suyi.

Zainab dai itama tana zaune tana hawaye, lallai abunda ciwo, ganin yanda mum take kuka saita tuna da dad d'inta, irin halin daya shiga sanda yace tana da ciki, Wanda ita bata san Wanda yayi mata ba, sai yanzu Bariki take k'ara ganin laifin kanta wanda komai dad d'inta zai Mata bai kamata ta fad'a Bariki ba, danta kuntata ma mahaifinta ba, gashi yanzu abunda tayi shi take girba,tayi aure amma saboda rayuwar da tayi baya ya bata mata rayuwar auranta, kuka ta saki mai sauti wanda hankalin kowa yayi kanta.

Mum kallon Bariki take irin yanda take kuka, jikin mum yayi sanyi, lallai abunda mijinta yake fad'a mata gaskiya ne, kaddara tana kan kowa, gashi yanzu ya fad'a kan y'arta, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun. Hmmmm Allah sarki rayuwa kenan, kowa baya yarda da kaddara saiya fad'a kanshi, sannan zai san kaddara ne, Abu Indai ba'a kanka ya fad'a ba to wajan kowa ba kaddara bane wasu sai su dinga fad'in dagangan mutum yayi ko kuma ace shiya sa kanshi, Hmmm mutane suna bani mamaki, wlh baki shi yake Kai mutum ga halaka, sai kuji mutum yana fad'in Wlh ni ai duk wacce take karuwanci ita taso maganganu dai irin haka, toh Wlh y'an uwa ku iya bakinku, Domin kuwa Allah zai iya jarabtanku ku fad'a cikin harkan karuwancin sai yaga yanda za kuyi, sai yasa a kullum ake son mutum ya dinga fad'in Alheri, kaman dai irin abunda mum ta dinga fad'i akan Bariki ita bata haifi karuwa ba, sai gashi y'arta da cikin shege, lallai dubaranka ko wayanka bashi bane zai sa Allah ya'ki jarabtanka, Allah yana jarabtan bayinshi ta hanyoyi da dama domin ya gwada imaninsu, wasu ta dukiya, wasu ta ciwo, wasu na talauci babu yanda Allah bayayi, sai dai muyi fatan Allah yasa mu cinye ko wace jarabawa da zata zo mana a rayuwa.

Mum tashi tayi tare da nufa inda Yarima da Bariki suke ta Fara bashi hakuri tare da fad'in lallai ni uwa ce, wacce ban kasance mai fahimtar abunda d'ana yake soba, ni uwa ce Mai son kanta, tunda na nuna nafi son y'ay'ana akan na wasu, na kasa amsar kaddaran data fad'a ma matarka, Ina gudun kaci gaba da zama da ita, yau gashi nima Allah ya jarabceni y'ata d'auke da ciki ba tare da aure ba, ciki harna wata uku, lallai Allah ya nunamin ishara, kamo hannun Bariki tayi tana fad'in dan Allah ki yafemin Wlh Ina jin kunyar kaina irin munanan kalaman dana dinga fad'a miki, gashi nasa d'ana ya miki saki har uku, banyi la'akari da cewa Kece rayuwarshi, ba idona ya rufe Ina ganin kaman kin mallake min d'ana kuka yaci karfinta Sosai.

Bariki cikin kuka tace mum kiyi hakuri, nayi imani da kaddara, lallai na yarda sakin da Yarima yayi min yana cikin kaddara na, ban taba ganin laifinki ba, abunda kika aikata ko wace uwa abunda za tayi kenan, babu wata Uwar da zata so d'anta ya zauna da macen da tayi rayuwar Bariki, lallai nima na cuci kaina kuka ta saki mai sauti wanda duk wannan abunda suke idon hafsat biyu tana ji itama hawaye take, lallai tayi kuskuren mallaka ma Umar jikinta gashi yanzu baya Raye.

Mai martaba daya kasa magana sai yanzu ya iya bud'e baki, yace Zainab daka ina kika fito, Ina son ki fad'amin koke wacece dan a nemi iyayenki mu samman yanzu da kike da juna biyu ya kamata musan iyayenki

Bariki taba cikinta tayi tana mamaki dama ciki gareta? Wani hawaye mai zafi ya fito mata nan ta Fara bama Mai martaba Labarin irin abunda ya faru da ita harda irin rayuwar da tayi a bariki, ta k'arasa maganan cikin kuka mai ban tausayi .

Kowa ya tausaya mata,ciki harda hafsat dake kwance tana jinsu, jikin mum ya k'ara sanyi Sosai, tare dayin nadaman abunda ta aikata ma Bariki, lallai tayi kuskure babba, ashe itama babban kaddara ne ya fad'a mata, had'e da Sharrin matar uba, lallai wasu matan bazasu ga annabi ba, tayi sanadin lalacewan yarinya danta k'i yarda da kudirinta na aikata mad'igo, Mum jikinta yayi sanyi Sosai, gashi ta raba d'anta da ita, koya rayuwarshi zata kaya?

Mai martaba yace dama ke yarinyar Sheikh musa monguno ce? Ikon Allah, d'azu dashi muke waya kan cewa yazo Nigeria nace mishi muna asibiti, nasa aje a d'aukoshi daka airport Wanda na tabba sun kusa zuwa nan bada dad'ewa ba, Abokina ne tare mukai karatu a k'asar misra, lallai abun yaban mamaki, Yarima yasa in gayyato shi akan yana son ya gabatar da lacca, Amma Zainab kinyi kuskure babba, iyaye ai iyaye ne, komai suka miki bai kamata ki k'ara bata rayuwarki ba danki kuntata ma mahaifinki, haba zainab ina iliminki? Kin aikata babban kuskure a rayuwa.

Kallon Yarima Mai martaba yayi tare da fad'in ko kasan shine mahaifinta dama??

Yarima yace eh Abba, ranan da aka d'aura mana aure na gane tamin k'arya, inda daka baya ta fadamin gaskiya, shine na bukaci ka gayyatoshi dan nasan inka kirashi zai zo, kayi hakuri Abba Nayi maka k'arya akan ina son yazo yayi lacca, Nayi hakan ne danka kirashi yazo in dai daitashi da y'arshi, ni bamma san abokinka bane, dani dakai na zani wajansa har misra din.

Mai martaba yace lallai Aliyu kayi jahadi, Allah yayi maka albarka, karan wayar Mai martaba ne yasa ya d'auka tare da fita waje, Jim kad'an sai gashi ya shigo da sheik musa monguno da matarsa Falmata wacce tasha hijab har k'asa kamar wata mutuniyar kwarai, idon sheik musa monguno ya sauka akan na gudan y'ar tasa Aiko yana ganinta ya fara nunata da hannu lokaci d'aya kuma ya fad'i k'asa....... Hmmm muje zuwa muji maike faruwa?





[9/11, 11:22 AM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*MY DEAR MY LOVELY FRIEND QWEEN PHAREEJAY*




*BOOK 2*


*PAGE 27*












Bariki ihu ta saki cikin tashin hankali, nan mum ta fita da gudu kiran Dr, yayin da Falmata take ta zunduma ashar kan cewa Bariki zata kashe mata miji, Bariki kam kuka take tana manne jikin Yarima, Falmata k'okarin cafko Bariki take, Yarima kaman ya Lura da hakan yasa ya dawo da Bariki baya tare da shiga gaba.

Dr shigowa yayi inda ya bu'kaci su mum damai martaba da Falmata su fita danya samu ya duba patient din, nan Dr Ya fara duba sheik musa monguno, cikin ikon Allah ya Farfado nan ya fara kuka tare da zufa dake faman keto mishi, tashi yayi tare da nufa wajan da Bariki take inda ya fara kuka yana neman gafaranta akan abunda yayi mata, wanda yace Wlh bai San ya akai har shida kanshi ya koreta ba,

Dr fita yayi domin yaga ba wani serious ciwo bane, suma yayi and kuma ya Farfad'o, ganin Dr Ya fita yasa su mum shigowa.

Falmata ganin mijinta ya tashi yasa ta Fara rusa kuka lokaci d'aya kuma ta Fara dariya tare da fad'in Nina sa akama Zainab ciki saboda ka tsaneta Wlh nice nasa aka mata hahahaha hahahaha sai kuma ta saki kuka lokaci d'aya kuma taci gaba da fad'in

Nice nasa mata kwaya cikin juice tasha, tayi bacci Mai nauyi, Nasa driver ya mata ciki, hahahaha bayan nasashi na koreshi, daka karshe ya faramin barazana nasa aka kasheshi har lahira, wlh nice nasa aka mata ciki, saboda ta'ki yarda dani, ni kuma ina sonta Sosai ina son in lashi zumarta, Wlh Ina Sonta Sosai dan Allah ku bani ita, ko ku aura min ita, sai kuma ta k'ara fashewa da dariya taci gaba da fad'in abunda yasa nasa aka mata ciki saboda ina son Dad d'inta ya tsaneta, yace ta d'auko mishi abun kunya, kuma Nayi wannan tunanin ne saboda Kar wata rana ta tauna min asiri dan yana jin magananta, kuma in ya tabbatar tana da ciki zai daina yarda da ita, bayan nasa anyi mata ciki, nasa akaje min maiduguri wajan wani boka inda na amso mugun sihiri Wanda na rufe mishi ido da baki sai abunda nace, duk da lokacin sihirin baiyi wani tasiri Sosai ba, dan Bayan ya koreta yaita fama da ciwo tare da damuwa yana mamakin Wai shine ya Kori y'arshi da kanshi, ganin irin damuwan da yakeyi gashi ana kawo mishi hotanta da shigar banza, hakan yasa hankalinshi ya tashi Sosai, ganin irin halin daya shiga yasa na tafi maiduguri dakai na wajan boka, gashi ina takaicin ban haiyu dashi ba, yau Idan ya mutu ba wani kud'i zan samu Sosai ba, inda Nayi mishi bayani, tare da cewa Ina son a cire mishi tunanin Zainab harta danginshi kona mamanta karsu nemeta, boka yace wannan aikin akwai hatsari Sosai sannan akwai zunubi Sosai, domin raba y'a da iyayenta babban aiki ne, nan nace ma boka na d'auka, boka yace dad din Zainab yana matukar son y'arshi Sosai koda anyi aikin muddin ya ganta komai zai lalace, Indai kina son aikin yayi tasiri karki bari su had'u, nace ma boka babu damuwa

Yace an gama, za'a tura mishi Aljani, wanda zai dinga juyashi, nan na amince boka ya k'ara min kashedi Idan na Bari suka had'u komai ya faru dani Kar ince bai fad'amin ba? Nace na amince domin a lokacin idona ya rufe.

Bayan na dawo Abuja naga aiki yayi, domin a lokacin tunanin Zainab yasa dad d'inta ya rage ibada, domin yana cikin ciwo, wannan ne yasa nayi nasara akanshi, har Aljani ya shige shi, saboda ina fargaban karsu had'u nasa muka koma misra gaba d'aya inda na bu'kaci Nima Ina son inyi karatu a can, wannan ne dalilin komawarmu k'asar misra yana business dinshi ta Nigeria da kasashen da yake yi, amma maganan zuwa Nigeria gaba d'aya nasa an cire mishi a rai, kwasam sai gashi yace min zaizo Nigeria amininshi yana nemanshi zai gabatar mishi da wani lacca, a lokacin na tsorata domin kuwa harta wa'azin da yake zuwa nasa an hanashi, sai gashi ya kawo min maganan zuwa Nigeria yayi lacca, da Farko naso in hanashi sai kuma Nayi tunanin muzo dan Ina son zuwa maiduguri wajan boka inji ya akayi ko aiki ya fara sanyi ne, ashe asiri ne zai tonu.. Dariya ta saki Tana fad'in Wlh koda zan mutu saina ciki Zainab Ina sonki.

Kowa dake wajan salati yake cikin takaici tare da jimami, da Allah wadai da halin Falmata

Dad d'in Bariki nan take yace Falmata na sakeki saki uku, kuma insha Allah sai Kinga abunda kika aikata, kin cuceni kin batamin rayuwar y'ata, lallai Falmata sai nasa an hukunta ki W.....

Mai martaba yace kayi hakuri, baka ga halinda take ciki ba, Mai martaba ya lura da Falmata kaman ta haukace.

Falmata tace saime cikin ihu, ni dama ba Sonka nake ba, saboda kud'i na aureka, da naga y'arka sai naji Ina Sonta, tunda naga irin suranta kuma Wlh sai na cita,hahahha Kaga koda ka mutu nida ita zamu zauna muci kud'inka, sannan ta dinga biya min bukata, Hahahahahaha sai kuma ta saki kuka tare da fara k'okarin cire hijab d'inta, nan mum ta k'ara fita ta kira Dr.

Koda Dr yazo dakyar aka ri'keta tana ta fusge fusge, andai samu an d'aureta dakyar inda sheik musa monguno yace zai sa a maidata maiduguri domin wlh ko sisi bazai bada ba wajan yi mata magani ba.

An ro'ki Dr akan su Fara dubata inda Mai martaba ya bada umarni tare da fad'in ba'a saka sharri da sharri, Dr yace gskiya wannan asibitin mahaukata za'a kaita, mai martaba yace babu damuwa a kaita, zai biya ko nawa ne, nan akai Gaba da Falmata. Kai rayuwa kenan wannan shi ake cema sakayya, lallai Allah ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya cuci kanshi, duk irin abunda Falmata tayi gashi ya koma kanta, kai Mata mata Wlh muji tsoran Allah.

Sheik musa monguno kuka yake tare da ri'ke hannun Zainab yana tambayanta akan ta yafe mishi

Cikin kuka tace babu abunda yayi mata, tace Dad niya kamata in nemi gafaranka, dana biye ma shairin zuciya, tare da kokarin San in kuntata maka, ta wajan aikata aikin sabon Allah, Dad na cuci kaina da yawa, dan Allah ka yafe min dad ta k'arasa maganan cikin kuka

Janyo y'ar tashi yayi tare da rungumeta su duka suna kuka abun tausayi.

Yarima Aliyu jin kukan hafsat din yake har cikin ranshi.

Hafsat da tun ihun da Falmata ke zabgawa yasa ta tashi ta zauna, nan itama ta fad'o daka kan gadon d'akin ta zube a gaban iyayenta tana kuka akan su taimaka mata su yafe mata.

Mai martaba yace duka su tashi suyi gida, acan za'ayi magana, hafsat jikinta yayi sanyi ganin mahaifin nata ko kallonta baiyi ba, lallai ta aikata babban kuskure na yarda da Umar wajan bashi jikinta, kuka take Sosai, inda gaba d'aya suka fita Bayan an tambayi Dr ko akwai wani damuwa, Dr yasa anba ma Hafsat magani sannan yace Bariki tana bukatar hutu Sosai, inda so samu ne ma a bata bed rest, da Farko Yarima Aliyu yace ta koma a bata gado, amma tace a'a a gida zata fi samun hutu, babu yanda ya iya dole ya biye mata itama aka bata maganin suka nufi Gida, duka a babban falon Mai martaba suka zauna inda Mai martaba ya kira waziri akan yazo, domin yana son yin magana yau wanda tun tuni yake son yi.

Kowa ya hallara, inda Mum tace ina zinatu ya kamata tazo itama, mai martaba yace Aliyu yaje ya kirata.

Yarima Aliyu fita yayi amma bai soba, domin duk zuwa asibiti da yayi bata tako k'afa tazo ba, and yanzu kuma maganan daya shafi Zainab za'ayi sai yake ganin kaman bai kamata tazo wajan ba, tunda kishiyar Zainab dince ita.

Direct gefenta ya shiga tun Kafin ya k'arasa d'akinta yake jiyo maganansu ita da gimbiya Amina, wanda yama manta tazo, gimbiya zinatu tana fad'in ai Wlh inda badan wannan maganin dana sama Yarima yayi mishi karfi ba, toh da Wlh zai gane niba virgin bace, ki duba fah ki gani baya cikin hayyacinshi har Ya iya gane niba virgin bace, dariya gimbiya Amina ta saki tare da fad'in hmmm ai tunda yaga wannan jinin na tabbata dole ya yarda ke budurwa ce.

Gimbiya zinatu tace yauwa wai jinin miye kika Aiko min dashi?

Gimbiya Amina tace Wlh fadawa naba kud'i suka kawo min, nace musu kona dabba ne kona mutum suje asibiti su siya, bayan sun dawo suka cemin Sun yanka raguna uku, shine suka kawo min jinin

Dariya gimbiya zinatu ta saki tare da fad'in ashe jinin rago ne, Yarima ya d'auka jini nane, kai gskya anyi bidiri, dariya suka saki.

Gimbiya Amina tace shidai duka baiyi dace ba, ita wancan amaryan tashi ba budurwa ba, Kema gaki, yatsa da ayabar roba yasa kin rasa budurci.

Gimbiya zinatu tace uhm Kedai bari, ni bada sanin namiji ba budurci ya gudu, hmm inda Yarima bai saki matarshi ba Aida tasha gori wajena Wlh da habaici

Gimbiya Amina tace toh Kema dai Kibi sannu a hankali, domin wlh idan Yarima ya gane kin mishi wannan yaudaran kashinki ya bushe, shi yanzu yana miki kallon budurwa ne

Yarima Aliyu dake tsaye yana jinsu cikin tashin hankali, gaba d'aya jikinshi yayi sanyi, ji yayi kaman ya juya amma wata zuciyar tace ka shiga ka nuna musu kaji komai, dan haka ya kutsa Kai kalman Innalillahi'wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, ganin gimbiya zinatu da gimbiya Amina zindir haiyuwar uwarsu jikinsu manne dana juna.

Yarima Aliyu tunda ya furta wannan Kalman na Innalillahi wa inna'ilaihira jiun bai k'ara cewa komai ba, sai hawayen dake idonshi dake zuba, tare da fad'in wannan wace irin jarabawa ce cikin ranshi, juyawa yayi ya fita jim kad'an sai gashi da mum d'inshi itama Abun ya bata mamaki, gimbiya zinatu da gimbiya Amina, Sun kasa koda motsi ne

Yarima Aliyu kuka yake yana fad'ama mum dinshi abunda yaji, suna fad'a tare da fad'in mum ban kasance mazinaci ba, amma Allah ya bani Mata fasikai,mum.. Kuka ya hanashi k'arasa abunda yayi niyan fad'a.

Mum rarrashinshi take tare da fad'in yayi hakuri ya d'auka wannan shine jarabawanshi na rayuwa, uhm su mum kenan yanzu an gane kaddara da jarabawa uhm.

Yarima yace mum bazan zauna da macen dana Kama tana aikata mad'igo ba, na tabbata duk macen dake aikata lesbians kallon hoto take ma mijinta, tana mishi kallon sakarai, mum bazan iya zama da itaba, lallai laifinta yafi na kowa muni, mum kice ta tafi bana son ganinta,

Zinatu da sauri ta taso tana kuka tare da ri'ke kafan Yarima tana bashi hakuri akan bata dad'e da fara aikata wannan aikin ba, dan Allah Yarima ka yafe min Wlh yi kawai nakeyi, amma bawai Ina jin dad'inshi ba, kuka take Sosai tana bashi hakuri

Mum tace tashi kisa kaya ki samemu falon Mai martaba, tare da kallon gimbiya Amina tace ke kuma ki shirya ki koma Gida, abunda kuka aikata dakai na zan fad'ama iyayenku, tana fad'in haka taja Yarima suka fita, tana fad'a mishi karya sake yace zai rabu da matarshi, tare da fad'in a farko tayi kuskuren raba shi da wacce yake mutuwar so, bazan k'ara Bari ka saki matarka ba, itama Zainab Ina neman hanyar da zaku dawo tare ne.

Koda suka je cikin falon idon Yarima Mai martaba ya kalla, yace maiya faru? Mum shuru tayi haka shima, yarima, muryan Gimbiya zinatu suka ji Tana fad'in dan Allah Abba kuyi min rai Nasan na aikata mummunan laifi, wlh shairin shaidan ne, dan Allah Abba kaba Yarima hakuri karya rabu dani Ina sonshi, wlh ban taba aikata mad'igo ba sai shekaran jiya, duka salati suka saki kowa kallonta yake cikin jimami da Tashin hankali .

Jin kowa na salati yasa gimbiya zinatu kallon mutanan dake d'akin, wanda idonta ya rufe bata ko Lura dasu ba, sai yanzu cikin jin kunya tare da tsanar kanta da kuma gimbiya Amina da tasa ta Fara aikata wannan abun.

Mai martaba ne yayi gyaran murya tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, kai duniya kai duniya Mai take son zama ne, da farko dai zan fara da Zainab yanzu Zainab zaki bi dad d'inki ne ko zaki zauna a nan har sai kin haiyu?

Bariki cikin sanyin jiki tare da zubar da hawaye tasan ta rasa Yarima har abada tace Abba zanbi Dad Dina

Da sauri Yarima yace ban amince ba, wanda bai San maganan ta fito ba

Kowa kallonshi yayi,

Mum kam kuka take k'asa k'asa domin tasan d'anta bazai jure rashin Zainab ba, kai ta cuci d'anta, ta rabashi da farin cikin shi

Mai martaba yace Aliyu karka manta yanzu Zainab ba matarka bace.

Yace Abba Zainab har gobe tana matsayin matata

Mum da sauri ta d'ago tana kallonshi, bama mum ba duk wa inda ke falon, yace Abba sanda mum tace in saketa na rubuta mata saki biyu Naji bazan iyayi mata uku ba, bayan na bata takardan naga mum bata damu data duba takardan ba hakan yayi min dad'i amma ganin yanda mum ta korata yasa naji a jikina kaman mum bazata taba Bari in dawo da ita ba, lokacin dana Fara ciwo nan take na dawo da ita, Zainab yanzu tana matsayin matata, takardan dana bata yana hannunta

Mum wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da furta Alhmdlh, Allah na godema.

Bariki tace Yarima Wlh sanda kaban takardan ban duba ba, harna yaga shi saboda ba Abun kallo bane, ashe saki biyu ne sai kuma ta saki kuka.

Mum ta tashi taje kusa da ita tana fad'in kiyi shuru zainab, wlh nafi kowa murna, inda Yarima saki uku yayi miki, dana shiga uku, kai Allah na gode ma, naso in aikata kuskure a rayuwa, naso bata rayuwar d'ana da kaina, sai yasa akace ba'a yanke hukunci cikin fushi, yau gashi naga yanda naso jefa yarana halaka sai kuma itama ta saki kuka, Bariki ganin haka sai ta dena Nata kukan ta Fara rarrashin mum.

Mai martaba yace yanke hukunci cikin fushi babu abunda yake haifar wa, sai dana sani, A kullum ana son Kafin ka yanke hukunci ka Fara bincike inka tabbatar, saika zauna kayi tunani akan maiya kamata, inko kace zaka yanke hukunci cikin fushi lallai zakai dana sani, Allan yasa kun fahimta.

Mai martaba ya kalli sheik musa monguno, ya fara bashi irin rayuwar da y'arshi ta shiga, bayan ya koreta har zuwa auran Yarima da tayi.

Sheik musa monguno kuka ya fara tare da fad'in Falmata ta cuceni, ta batamin rayuwa data y'ata, kallon Zainab yayi tare da fad'in ki yafe min inda ban aureta da hakan bai faru ba.

Mai martaba yace ka daina fad'in haka, sheik ko ka manta Idan Allah yasa abu zai zo gareka dole sai yazo, sannan sheik asiri yana bin hali ne, na tabbata koda Falmata bata maka asiri ba, zaka iya Koran Zainab, domin lokacin kana cikin fushi, zaka yanke hukunci cikin fushi, domin zaka ga a matsayinka na babban Malami y'arka ta kwaso cikin shege na tabbata koda babu asiri zaka iya koranta, daka baya kayi dana sani, sai yasa akace ba'a yanke hukunci cikin fushi, a lokacin duk da akwai sihiri a kanka Bayan ta tafi aika nuna kayi nadama, tare dason ganinta.

Sheik musa monguno yace hakane, tabbas asiri yana bin hali, asiri yana tafiya ne da halin mutum, Allah ka k'ara tsare mana imanin mu, kallon Yarima yayi tare da fad'in lallai Aliyu ban San da wani baki zan gode maka ba, domin kayi babban jahadi na ceto rayuwar Zainab, duk da kasan irin rayuwar da tayi daka baya, bayan tayi maka k'arya kaci gaba da zama da ita, lallai ban tunanin duk irin sonda nake mata cewa nawa yafi maka, lallai ka fini son Zainab, tunda harka iya zama da ita, sa'banin nida nake mahaifinta sanda take bukatar kulawata Sosai lokacin na juya mata baya, duk saboda fushi tare da kunyar duniya, kai kaico na, Yarima Allah yayi maka albarka.

Yarima ya amsa da Ameen tare da kallon zainab wacce itama shi take kallo, Yarima ido ya kashe mata, da sauri tayi k'asa dakai tana murmushi tare da tsoran Allah yasa wani baiga sanda ya kashe mata idon ba.

Mai martaba kallon waziri yayi tare da fad'in, Ina son aje a sauke sarkin u/k daka kan kujeranshi, domin bai kamata a barshi yana shugabantan al'umma ba, a sami wani kamili Dattijon arziki a saka, amma yau nake son a bashi takardan murabus, domin duk mutumin da zaiyi Abu saboda kud'i ciki harda yaudara ba mutumin arziki bane, bai kamata ya dinga shugabantan al'umma ba, nan take waziri yace an gama ranka ya dad'e

Mai martaba kallon hafsat yayi tare da kiran sunanta da sauri ta d'ago cikin faduwan gaba tace na'am Abba, tana hawaye

Yace hafsat Mai kika rasa? Mai kika nema kika rasa? Hafsat wani irin tarbiya ne bamu baki ba? Dama kin San kina da ciki shine kike k'okarin yin aure da cikin wani? Hafsat kin bani mamaki matuka.

Cikin kuka tace Abba ka yafemin Wlh cikin Umar

Please Login or Register in order to submit comment