Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inna kiraka zaka ki d'aukan min waya, koda zaka d'auka ka zageni dan Allah ka d'auka rashin jinka yana sani cikin wani hali n...... Kuka ne yaci karfinta Sosai wanda yasa dole tayi shuru

Yarima kasa magana yayi sai bayanta da yake shafa mata, jin sautin kukan nata har cikin kanshi yasa ya d'ago ta tare da kallon fuskanta da ya baci da kuka Sosai, murmushi Yarima yayi tare da fad'in Kinga kina ta zubar min da hawayenki, my princess plz ki daina I trust you sai yasa na dawo gareki and naje na sami Abba ya yarda ya bani izinin zuwa zance har mu fahimci juna manya su shiga, ya kuma nunamin yaji dad'i yanda na Fara neman izini sabanin mazan yanzu basa haka, yace ya yaba dani ya yarda da irin tarbiya na, duk da na fito gidan sarauta ban nuna iko ko sarauta ba wajan zuwa wajanshi, my princess Abba mutumin kirki ne, lallai na yarda iyayenki Sun baki tarbiya domin Abba yayi min magana na dattaku....... My princess I really love you, Ina miki son da nida kaina ina mamaki, jiya nayi fushi dake amma gaba d'aya na kasa sukuni, saida nazo na ganki na samu nutsuwa...... Ganin ta lumshe ido yasa ya kura ma fuskanta ido, ji yake kaman ya tafi da ita, yana Mata son da bai taba tunanin Zaima kowa irinshi shiba,

Hura mata iska yayi a fuska wanda yasa ta bud'e ido da sauri idonsu ya had'e suka fara kallon juna, cikin ido gaba d'ayansu wani irin son junansu suke ji, Sun d'auki lokaci suna kallon juna Kafin bariki tayi k'asa da kanta dan bazata iya juran ci gaba da kallonshi cikin ido haka ba, wannan dinma da tayi tana mamaki, ta rasa mai yasa Yarima ya banbanta da sauran maza, yana Mata wani irin kwarjini da bata ji akan sauran mazan da tayi hulda dasu,.....

Katse mata tunani Yarima yayi tare da fad'in daka ina habib ya kiraki Ina kika je?

Cikin sanyin murya tace ina gidan wata kawar innata ce, naje amso maganin ciwon kai na Hausa, Ina can habib yazo, nama bar wayata a gida tana caji.....

Yarima yace ok but yaushe zaki koma Gida? I dnt knw why bana son wannan anguwar domin mutanan da nake gani a cikinta, plz ban son kina yawan zuwa my princess ya karasa maganan cikin damuwa....

Tace Yarima Karka manta y'an uwana suna nan

Yace eh I know, bawai nace ki daina zuwa bane, kawai Ina so ki rage zuwa ne plz, and my princess plz ki daina irin wannan dressing din, sai a gida na, ki dinga sa hijab dinki inso samu nema harda nikaf plz banso kowa yana ganinki .....

Bariki murmushi tayi tare da fad'in Yarima wannan jallabiya ce babu komai ai dan nasa, shima kaman hijab ne.....

Yarima yace, Nop akwai banbanci nidai bana so ana sawa, Kinga yanda yayi miki kyau kuwa? Only god knows maza nawa kika burge da kika fito.... Sai yasa tunda yau naga Abba Yaban izini very soon za'a turo ayi bikin kowa ya huta in kika zama tawa sai inga Wanda zai kara cewa yana son ganinki.......




*jiya saida Nayi typing har 2read more komai nawa ya goge na whatsapp 😭😭😭😭 ol my chats yanzu ma saboda nacin my mum my salmaty yasa dole nayi typing dinnan, plz duk Wanda sukai min magana ban basu amsa ba suyi hakuri Wlh komai nawa Ya goge in important magana ne zaku iya Yimin resending message din pls, nayi bayani ne Kar a kaini gaba ace in anyi min magana bana kulawa, maryam ba haka take ba, kowa nata ne thanks*









~MARYAM OBAM~
[8/22, 7:24 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 8*








Bariki dariya tayi, tana mamakin irin kishin Yarima Aliyu, gashi baya iya boye kishin shi, dole saiya fito dashi......

Katse mata tunani yayi da fad'in dariya koh??

Tace a'a Yarima kawai naga kana tunanin daba haka bane.....

Yace miye ba haka bane? Tell me, tunda kika fito zaki cemin maza basu kalleki ba??

Tace Yarima yanzu fah dare ne Waye zai kalleni? Inba Kai ba.

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace my princess you r too much kin iya Kare kanki..... Anyway yaushe kike son Ayi bikin mu?? Domin Idan Mai martaba ya turo lokaci kad'an za'a sa.

Bariki rufe fuskanta tayi cikin jin kunya tace Yarima *BANDA ZABI* sai abunda su Abba sukace.....

Yarima Aliyu yace hakane but Nasan Kema kina da lokacin da kike so ayi in muka shirya basai mu fad'a ba!?

Tace hakane

Yarima yace ni ko yanzu aka bani zan tafi dake.....

Ido ta zaro lokaci d'aya kuma ta saki dariya Sosai, tace Yarima ni nafi son yakai Nanda shekara d'aya.....

Da sauri Yarima yace what?? Amma dai you are joking koh? Ni bamma tunanin yakai nan da wata d'aya....

Bariki tace Yarima watsa d'aya yayi wuri, ni Ina tunanin nan da wata uku....

Yarima yace hakan yayi miki???

Kai ta d'aga alaman eh, domin Kafin nan ta Gama istabra'i sannan zata samu lokacin gyara kanta Sosai duk da tasan komai tayi bazata dawo budurwa ba, amma zata gwada duk wani kayan gyaran jiki danta d'an gyara kanta.....

Katse mata tunani yayi da fad'in gobe ki koma Gida Zanzo in ganki a can da rana insha Allah,

Tace Yarima gobe kuma?

Yace yes ko you don't want to see me ne?

Da sauri tace a'a kawai naga kullum sai kazo, baka zama ga amarya a gida, inaga ya kamata ka zauna ka bata hakkinta, da lokacinka

Yarima yace ok hakane, zan zauna bazan zoba har sai kin nemeni, sannan ita amarya Ai tare muke kwana da ita.....

Ganin yanda ta canza fuska yasa yayi murmushi danya Lura taji haushin magananshi ne.....

Kamo hannunta yayi tare da matse su duka biyun, yace my princess I love you so much, plz ki dinga kulan min da kanki Sosai...

Kallonshi tayi ganin shima ita yake kallo yasa tayi k'asa da kanta, cikin sanyin murya tace Yarima....... Shuru kuma tayi tana jin nauyin abunda zata fad'a.....

Yarima Aliyu yace ina jinki my princess.....

Hawaye ne ya zubo mata Mai zafi da sauri tayi k'asa da kanta dan karya gane tunda hannunta na nashi hannun..... Cikin rawan murya tace Yarima Idan ka aureni kaji ba yanda kake expecting ba zaka iya saki na????

Yace ban fahimta ba?? Mai kike nufi?

Tace Yarima Ina nufin Bayan auren mu kaji ba yanda nake ba I mean..... Shuru kuma tayi lokaci d'aya tasa kuka mai sauti........

Yarima ido ya kura mata cikin rud'ani...... Tare da tunanin mai take son fad'a mishi haka???? Ganin kukan nata na k'aruwa yasa ya fara share mata hawaye cikin tausayinta....... Ya fara magana kamar haka Zainab Ina son ki fad'amin abunda yake damunki ko miye I will accept you a yanda kike, ina miki so dani kaina ban taba tunanin zanyi ma d'iya mace irin wannan son ba, tell me maike damunki????

Kasa magana tayi sai kuka da take ta faman saki cikin tashin hankali da damuwa,....

Yarima kam ido ya kura mata ganin taki magana sai kuka,... Yace Zainab kodai kina pretending ne bakya so na.......

Da sauri tace a'ah Yarima Ina Sonka, kaine rayuwa na, Ina maka son da baki bazai iya fad'anshi ba, sonda nake maka sai yasa nake tsoran fad'a maka abunda nake son fad'ama a halin yanzu saboda ban San yanda zaka d'auki abun ba......

Katseta yayi tare da fad'in Zainab tell me?? Fad'amin Mai yake faruwa?? ......plz Zainab tell me abunda yake damunki kin sani cikin damuwa......

Kuka take Sosai lokaci d'aya ta fad'a jikinshi ba komai take son fad'a mishi ba sai rayuwarta wanda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya yasa ta kasa fad'a mishi sai kuka tare da nadama

Yarima tunda ta fad'a jikinshi ya kasa furta koda kalma d'aya ne sai Shafa mata baya da yakeyi tare da tunani Kala Kala akan Mai take son fad'a mishi?? Lallai akwai wani abu mai muhimmanci daya danganci rayuwarta da take fargaban fad'a mishi, to miye abun??? I need to knw, tunanin baya ya farayi tasha son fad'a mishi magana amma saita kasa, lallai akwai wani abu a tare da ita toh miye wannan abun?? I have to find out........

D'agota yayi tare da fad'in Zainab kukan ya isa haka, what I want you to knw is dat Ina sonki I cnt live without you...... Zainab tun a mafarki Allah ya had'ani dake har na had'u dake a zahiri, ina son ki sani had'uwa na dake had'in Allah ne, na Fara sonki tun Kafin inga Fuskanki, ina son ki sani bawai saboda kyanki ko wani abu nake sonki ba a'a kamalanki da mutunci da yanda kike suturta jikinki yasa na kara sonki koda na had'u dake...... So Zainab dnt be afraid to tell me what in ur mind..... Zainab Abu d'aya zaki aikata in barki duk irin sonda nake miki domin bazan iya juraba dan Indai zan ganki Abun zan dinga tunawa shine *ZINA* duk da Nasan rasaki a rayuwa ta kaman baraza na ne a tare da rayuwa na, bana tunanin koda a mafarki Zaki iya aikata hakan, ina matukar kishinki Sosai harta habib da kike mu'amala dashi hakuri nakeyi badan ina so ba, tunda kince kaman dan uwanku ne, ban son inga wani abu yazo inda kike Inba niba........ Ido ya kura mata tare da fad'in tell me wht on ur mind I need to knw......

Bariki jikinta yayi matukar sanyi Sosai lallai Yarima in yasan wacece ita ya barta har abada..... Tsayawa tayi da kukan amma hawaye na zuban Mata a ido Sosai amma yata iya tata kaddaran kenan dole ta fad'a mishi gaskiya domin hakan shine zai sa ta sami salama duk da itama ba zata iya juran rashin Yarima Aliyu a rayuwarta ba, domin so ya mata shigar sauri sonshi ya shigeta Sosai wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba.......

Katse mata tunani yayi tare da fad'in Zainab tell me plz....

Shuru tayi tana kokarin yin magana amma ta kasa domin muryanta ya dashe......

Ganin haka yasa Yarima fad'in kiyi shuru kibar wannan kukan plz Kinji my princess?

Kaita d'aga mishi alaman toh

Yarima Aliyu idonshi na kanta ya tabbata akwai abunda take boye Mai, but koma miye zai sani..... Ganin tasa hannu a kanta alaman yana mata ciwo yasa yace my princess ciwo Kai din yake miki?

Kaita kara d'aga Mai alaman eh , bud'e kofar motar yayi ya shiga wajan driver ya kunna motar,

Da sauri ta d'ago ta kalleshi ganin yaja motar yasa ta kura mishi ido, taga Ina zashi da ita...... Karan wayanshi ne yasa ta dawo daka duniyar tunanin data fad'a

D'auka yayi tare da fad'in USMAN sorry yanzu zamu dawo, zan kaita pharmacy ne a bata magani she has a headache..... Yana fad'in haka ya kashe tare da fad'in Ameen

Yarima cikin gari suka shiga inda aka bama Zainab magani, tare da sai mata kayan fruit sannan suka kamo hanya, bayan sun karaso Bariki suka gaisa da USMAN sannan Yarima yayi mata sallama akan taje tasha magani, ta kwanta ta huta sai sunyi waya......

Bariki gidanta take ta koma ta shiga d'akinta ta kwanta bayan tasha magani bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita

Usman tun a mota yake tsokanan Yarima Aliyu, akan dole ya mutu akanta yarinyar tana da kyau sai dai karama ce ba wata babba bace......

Yarima dai banza da USMAN yayi domin haushin yanda yake ta fad'in Tana da kyau yakeyi, d'an tsaki yayi cikin ranshi yace bazan kara zuwa dashi ba, tunda Kalle min Mata yake tayi...

Yarima bayan sun koma direct gefenshi ya nufa inda yayi bedroom dinshi yayi wanka, yana cikin sa jallabiya danya kwanta

Gimbiya zinatu ta shigo d'akin tare da fad'in Yarima .....

Yace ya akayi....

Tace ina son magana dakai

Baice mata komai ba sai zama da yayi akan gadon d'akin tare da d'aukan wayarshi yana dannawa.....

Kollonshi tayi cikin jin haushin rashin kulata din da baiyi ba, tace haba Yarima wai mai yasa kake haka, yau kwana na uku a gidan nan a matsayin matarka, amma baka da lokaci na, kullum inka fita sai dare, karka manta wannan baya d'aya daka cikin abunda miji ya kamata yayi ma amaryanshi, duk wani ango zama yakeyi a gida in yayi aure ya dinga kula da matarshi, yau koda bazawara ka aura ai kayi d'auki balle ni budurwa....

Yarima Aliyu kallonta yayi tare da d'an sakin murmushi yace d'auki?? Akan me? Bayan har yanzu ban San maina aura ba......

Cikin faduwan gaba tace kaman ya Yarima ban gane ba ...

Idonshi na kanta domin yana son yaga yanda zatai reaction amma ga mamakinshi sai yaga batai yanda yake zato ba, kenan gimbiya budurwa ya sameta dagaske, inko hakane ya kamata ya dinga bata hakkinta duk da bawai yana jin Sonta bane a ranshi, amma tunda ta kawo budurcinta sai yaji tayi girma a idonshi, duk da Abun ya bashi mamaki, dan baiyi zaton haka dinba......

Jin kukan gimbiya zinatu shiya sa yarima ya dawo daka duniyar tunanin da yake...... Ganin yanda take kuka yasa zuciyar Yarima tayi karaya tare da tausayinta , tashi yayi ya ka mota ya kwantar da ita akan jikinshi yana fad'in plz ki daina wannan kukan.....

Cikin kuka take fad'in haba Yarima dole inyi kuka, yanzu Yarima ace Ina amarya amma kullum saika fita, kuma inka fita sai dare, har an fara magana akai na, ana fad'in baka d'auki na , kasan gidan sarauta akwai ya'da magana haba Yarima mai yasa baka sona? Maina rasa......

Hannunshi yasa akan bakinta yace ya isa haka,

Ganin kaman Yarima ya tausaya mata yasa taita Mai juye juye a jiki,

Nan sha'awa ta motso ma Yarima Kafin ace Mai har an fara harka.......





*********
Alh madu ne shida hjy babba kallon hjy babba alh madu yayi yace abunda yasa na kiraka dagaske ne bariki zatai aure ko wasa takeyi??

Hjy babba yace haka tace kuma ina ganin kaman dagaske take, dan naga gskya yanzu bata bin maza, inma tanayi Toh a boye takeyi....

Murmushi Alh madu yayi tare da fad'in ok, ina son kayi min bincike akan wa zata aura sannan a ina yake, ina nufin Ina dai son sanin Waye shi da kuma sanin daka inda ya fito.....

Hjy babba yace an gama ranka ya dad'e

Kud'i alh madu yaba hjy babba, sannan ya tafi

Alh madu yace bariki Nasan bana gamsar dake, amma ni kina gamsar dani, inko dai bani zaki aura ba, shima wanda yake son canza ki dole ya rasa ki,inko na bari kinyi aure toh sai dai in zaki amince ko kinyi aure kici gaba da bina murmushi ya saki tare da fad'in zan nuna miki ni Alh madu ba'amin wargi.........



*AYSHA BAGUDO..... na amsa sa'ko Ina matukar godiya Allah yabar k'auna da zumunci, Allah yasa zumuncin mu har abada Allah ya tsole idon makiya, Wlh naji dad'in sa'kon da kikayi min Sosai ngd ngd, ina matukar kaunarki kaman yanda kike kaunata Allah ya biya miki bukatunki na alkhairi, makwabciyata ta gidan Aljanna insha Allah*


[8/23, 6:47 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 9*






Bariki bata farka ba sai da asuba, jin kiraye kirayen sallah shine yasa ta farka, kuma bata tashi da ciwon kai dinba, tashi tayi ta fad'a toilet, alwala tayi tazo tayi sallah, tare da ro'kan Allah akan ya shiga lamarinta...... Koda ta idar kasa komawa bacci tayi sai kayanta na sawa data fara sawa cikin karamin akwatinta domin zuwa wajan iyayenta na bariki danta d'an Fara kwana a can, gashi yarima yace ta koma yau dinma.

Bayan ta d'iba kayanta na kwana biyar tasa cikin akwati ta rufe tare da ajiye akwatin a gefe, kwanciya ta koma amma ta kasa bacci domin ba komai take ba sai tunani, a duk lokacin da taso ta fad'ama Yarima gaskiya saita kasa, sai kuka yazo mata in tayi kokarin ta daure ta fad'a mishi saiya kashe mata Giwa da fad'in bazai auri mazinaciya ba... Wani hawaye ne ya zubo mata Mai zafi, Tana son Yarima bata son rasa shi, lallai Indai tana son samun Yarima a matsayin miji shine ta boye mishi labarinta har abada..... Da sauri ta girgiza kai tare da fad'in labari na bazai taba boyuwa ba domin komin daran dad'ewa sai gaskiya ya fito, lallai fad'ama Yarima gaskiya shine mafita amma sai bayan na aureshi, zanyi kokarin in fad'a mishi gaskiya ranan daya aureni Nasan May be yayi min uzuri, tunda ba haka nake ba, kaddara ce ta fad'amin wanda nida kaina bazan iya cewa ga abunda ya faru ba, koda za'a samun wuka a wuya ban San yanda Abun ya faru ba......





*******
Haulat ce take jan akwatinta daka gani tafiya za tayi....

Hjy habiba tana bayanta tana fad'in yanzu sai yaushe kuma?

Haulat tace mum sai dai munyi waya, kawai

Farhan ne ya fito tare da fad'in muje in kaiki train station.....

Hjy habiba tace farhan ka Bari driver ya kaita mana,

Yace no mum Bari in sauketa

Babu yanda hjy habiba ta iya, dole farhan da haulat suka fita.

Haulat na gaba farhan na mazaunin driver, ta kalli farhan tace plz mu biya ta gidan Hjy Umaima zan amsa sa'ko.......

Farhan yace ok, amma zaki missing train din 8, sai na 10 zaki hau,

Tace babu damuwa

Juya motar yayi sukai gidan Hjy Umaima, haulat ce kad'ai ta shiga..... Ta d'an jima Sosai ban San mai suka tattauna ba sai gata ta fito ta shiga motar ta kalli farhan tana y'ar murmushi wanda shima din ita yake kallo tace muje.....

Mai yakon suje din saiya kama hannun Haulat yana fad'in haulat dagaske aure za kiyi????

Tace aure kuma? A'a

D'an shuru yayi yana nazari, toh tace a'a Bayan mum dinshi tace aure za'a Mata.....

Katse Mai tunani haulat tayi da fad'in, farhan zanyi aure Indai na samu Mai sona kuma wanda nake so, da an taba son had'ani da wani Wanda bana so..... Wanda shine silan fad'awa ta cikin k...... Da sauri tayi shuru domin taso tayi baran barama.

Farhan yace inaji haulat

Tace andai fasa auren nawa

Wani irin ajiyan zuciya farhan ya sauke, tare da kallonta cikin ido yace haulat zaki aureni???

Da sauri ta kura Mai ido, tare dajin bugun zuciya, lallai farhan ya had'u ba tun yau take sonshi ba, tunda ta Fara ganinshi, domin yanda yake nuna mata kulawa, wanda ko wace mace tana son taga ana nuna mata caring..... Sau da yawa rashin nuna halin ko in kula da maza suke nuna ma matansu suke sa su Fara neman mata y'an uwansu, misali namiji ya fita office, ko kasuwa, kodai wajan da yake Sana'a, bazai kiraki ba, may be in kin kirashi bazai d'auka ba, namiji inya auri mace babu kalaman love duk sai ya daina, in baki da lafiya babu sannu koya jiki, inya biya kud'in magani shikenan, maza kuma kuna da laifi Sosai wajan fadawan wasu matan halaka, mace tana son Mai kula da ita Sosai, yau koda auren dole akama mace bata son miji..... Indai yana kyautata mata wlh sai kuga ta Fara sonshi..... Amma kai miji babu kyautatawa daga tayi abu sai hantara...... Idan tana da k'awa taga tana kyautata mata in bata da lafiya, bini bini ta kirata tana ya jiki kaza da kaza, in kawar Tana bin mata haka zatai ta janta a jiki in aka samu Mai raunin imani ganin yanda kawar tata take mata inta fito mata da kudirinta saita yarda ta amince Mata...... Wlh maza kuma kuna da laifi Sosai, damme bazaka dunga nuna ma matarka soyayya da kulawa ba,bayan aure shikenan daka anyi aure sai a fara d'aure fuska haba haba maza ya kuke haka, sannan saika gama d'aure fuska in dare yayi ka lallabo kana Kai hannu ko kunya babu😏........

Farhan ne ya Katse ma haulat tunani da fad'in.... Haulat why r you silent and stare at me lyk this????

Murmushi tayi tare da fad'in nothing, kawai Ina mamakin abunda kace ne......

Farhan yace mamaki kuma? Kodai bazan samu karbuwa bane? Haulat tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, Wlh haulat so nake na aureki inhar kin amince Kece mace ta farko dana Fara ji ina burin in aura.......

Haulat wani irin murmushi ta saki tare da fad'in farhan zanyi tunani akai, yanzu dai muje train station Kar in makara.....

Tada motar yayi suka wuce kabuwa station, koda suka je saida suka zauna bayan yasai mata ticket, zama sukayi suna jiran lokaci,

Haulat ba komai take tunani ba, sai abunda suke aikatawa da hjy habiba, Uwar farhan gashi d'anta yau yace yana Sonta, in kuma tace bata son farhan tayi karya, tashin hankali uwa da d'a....... Ido ta lumshe tare da fad'in Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan farhan bai kamata in daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yihuwa naga tsiraicin mum dinshi na cita..... Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d'anta Kai no way.......

Farhan ne ya Katseta tare da fad'in when zaki dawo? Koni inzo kaduna?

Dariya tayi tare da fad'in mudai yi waya kawai..... Dai dai lokacin aka fara fad'in su tashi train yazo.....

Tashi haulat tayi tana kallon farhan tare da fad'in sai munyi waya

Kai ya d'aga alaman ok tare da bata Wani karamin Leda daya ciro cikin aljihun shi,

Amsa tayi tana fad'in ngd tare da tafiya..... Koda haulat ta shiga jirgi tunanin farhan tai tayi wanda ta rasa dalili........ Bud'e ledan daya bata tayi taga wani kwali karami anyi raping dinshi bud'ewa tayi taga wani zoban zinari Mai shegen kyau, bata san lokacin data saki murmushi ba........





*******
Yarima Aliyu ne zaune gaban iyayenshi yana mi'ka musu gaisuwa, mai martaba yace yaushe zaka Fara aiki a asibitin ka?

Yarima Aliyu yace Abba duk sanda ka bani umarni Niko yau zan iya Fara aiki....

Mai martaba yayi murmushi domin duk cikin yaranshi babu wanda yake so kaman Aliyu bawai dan yana d'a namiji ba kawai, a'ah harda irin biyayyan da yake mishi... Mai martaba yace saika shirya cikin satin nan ka Fara sannan akwai wani fili da nake dashi a u/sarki saika Fara ginawa tunda a can zaka Fara aiki, Nasan wata rana iyalanka zasu bika can din in aiki yayi yawa .......

Mum din Yarima tace Kai Masha Allah, ina taya Yarima godiya

Mai martaba murmushi yayi tare da fad'in kin ara bakinshi kenan kinci Mai Albasa

Yarima yace Abba na gode Sosai Allah ya kara girma, Allah ya biya dan gidan Aljanna

Mai martaba ya amsa da Ameen tare da fad'in waziri zai baka takardun filin sannan zai nuna maka filin,

Mum dinshi tace sai ka Fara ginin mata biyu koh?

Yarima kasa magana yayi, sai mai martaba da yace ginin mata biyu kuma? Aure yace miki zai K'ara?.....

Mum tace eh gashi nan ya fad'a maka da bakinshi....

Mai martaba ya kalli Yarima Aliyu tare da fad'in ina jinka??

Yarima ya fara magana da fad'in Abba dama dama akwai dama....

Murmushi mai martaba yayi tare da fad'in dama me? Gaba d'aya ka kasa magana, mai martaba yaci gaba da fad'in Aliyu inaso ka sani bazan hanaka k'arin aure ba, amma sai dai Ina Mai baka shawara kayi hakuri nan gaba domin baka dad'e dayin aure ba ko sati d'aya bakayi dayin aure ba, inaso kayi hakuri nan gaba kad'an sai a taso da maganan auren

Please Login or Register in order to submit comment