Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kake son yi, amma fah shawara ce ba umarni ba.....

Yarima Aliyu yace Abba umarni ko shawara duk abunda kace min a matsayin umarni yake a wajena.... Abba kayi hakuri a kullum nafi son kaban umarni domin Ina Mai biyayya ga duk wani abunda kacemin

Mai martaba yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka masu yi maka biyayya

Yarima ya amsa da Ameen Abba,

Mai martaba yace yarinyar y'ar inace????

Yace Abba a cikin kaduna suke, a u/kanawa ,sannan Abba mahaifinta bamai karfi bane....

Mai martaba yace babu damuwa, ya tarbiyan gidan yake??

Yace Abba Alhmdlh gidan akwai tarbiya domin yarinyar yau kwana hud'u data sauke AL'QUR'ANI Mai girma kuma hadda....

Mai martaba yace Alhmdlh, lallai gidan akwai tarbiya, Allah yasa na tsoran Allah ne sannan duk Wanda yake da ilimin addini yaji dad'in duniya da lahira zai iya zama da kowa, dukiya ko mukami bashi bane Abun dubawa tarbiya itace Abun dubawa, kaje zansa Ayi bincike akan gidansu......

Yarima tashi yayi yana mai yima mahaifin nashi godiya sannan ya fita cikin murna yana K'ara godema Allah da har mahaifinshi ya yarda yanzu tunda Mai martaba ya amince toh ya Gama samun Zainab insha Allah, lallai Allah Abun godiya bai taba tunanin zai samu amincewan mahaifin nashi cikin sauri haka ba...... Gefenshi ya nufa na da, koda ya shiga rufewa yayi tare da nufa bedroom dinshi ya fara kallon hotunan Zainab din, Wanda ya zana, tunani ya farayi Mai Zainab take son fad'a mishi wanda take tsoron fad'a??? Kodai in tambayi habib?? Nop bai kamata ba ita ya kamata ta fad'amin koma miye, and d way yanda take kuka yana nunamin abunda take son fad'a Kaman ya shafi rayuwanta? Toh mai take son fad'amin ido ya lumshe yana tunani..... Na farko dai bata da wani aibu balle yace ga abunda take kokarin fad'amai, to Mai Zainab take boyemai??....... Kai ban tunanin abun serious ne inda serious ne data fad'amin.... Wata zuciyar tace mishi kaika sani ko nauyin Abunne yasa ta kasa fad'ama? And kuma Inba serious bane mai yasa take kuka haka in tayi kokarin fad'a Mai? Ganin duk iya tunanin da yayi ya kasa gano komai yasa ya cire abun a ranshi tare da fad'in koma miye Indai Mai muhimmanci ne zai sani, yanzu dai ya kamata in mata surprise inje in ganta....

Bariki na kwance taji ana mata nocking, tashi tayi ta bud'e kofar da sauri ta saki kara tare da rungume haulat Tana fad'in mutanan abuja sai yau, ko waya babu.....

Dariya haulat tayi tare da fad'in kiyi hakuri bariki Wlh wayata ce ta fad'i bani da number d'inki yanzu, sai yasa ina dira kaduna Wajanki na fara zuwa Kinga ko d'akina banje na ajiye akwati ba nazo Wajanki.....

Bariki tace shigo mana

Haulat shiga tayi tare da zama tana fad'in Kai nasha abuja

Bariki tace gashi kin kara kyau da k'iba kaman bake ba, kai zama waje d'aya yayi

Murmushi Haulat tayi tare da fad'in dan bani wayarki in tura hotuna na tare da number d'inki, banda pic dina dake ko d'aya a phone dina

Bariki mi'ka mata wayar tayi tare da fad'in yunwa nake ji wlh Bari in duba habib

Haulat tace ok, haulat ta d'auki abunda take so cikin wayar bariki, sannan tayi murna da abunda ta samu a game da bariki din......

Bariki bata dad'e Sosai ba ta dawo, cikin d'akin tare da fad'in habib ya cika yawo kaman yaci kafan Kare.... D'aukan iPhone dinta tayi ta Fara kiran habib harya tsinke bai d'auka ba......

Haulat tace ashe kinyi iPhone ga Samsung ga iPhone gskiya bariki kina jin dad'i.... Tashi haulat tayi tare da mi'ka ma bariki wayarta Tana fad'in Bari inje inyi wanka in huta anjima nazo

Bariki tace ok but nima zanyi tafiya sai dai munyi waya

Haulat tace ok tana murmushi ta fita

Bariki ganin data dinta a bud'e yasa ta shiga whatsapp da message keta faman shigowa ganin Alh madu ya mata message yasa ta bud'e nashi ganin hotunan daya d'aukesu tayi, tsaki taja tare da shiga gallery ta goge dan in an turo Mata hoto shida kanshi yake bud'ewa bata rufe ba, harda na Hon salis duk ta goge su Wanda ya tura mata kwanaki, duk wani hoto data d'auka wanda bai dace ba ta goge a cikin wayarta...... Kiran Alh madu ne ya shigo cikin wayarta kaman Karta d'auka saita tuna da hotunan daya turo Mata Wanda hakan ya tabbatar mata yana son Mata wani tuggu sai yasa ta d'auka tare da fad'in lafiya?

Dariya yayi tare da fad'in hotunan sun d'auku da kyau koh?

Tace tir da hali irin naka

Yace na baki awa biyu kizo inda nake ko yanzu ki ganki a internet ansa hotunan da mukayi kuma da fuskan wani ba nawa ba danna biya kud'i anyi min aikin , babu wanda zai gane an canza fuskan domin kwararru sukamin aikin kuma ba y'an kasar nan bane.....

Bariki k'asa tayi tana hawaye wayar ta sulale a hannunta......









~MARYAM OBAM~
[8/24, 9:32 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 10*






Kuka take Sosai tare da nadaman fadawarta bariki, wanda ita da kanta tana mamakin yanda har ta fad'a wannan mummunan harkan, yanzu kenan kowa zai iyayi mata barazana kenan? Duk yanda taso ta kimtsa kanta sai an gwadayi mata barazana?...... Share hawayenta tayi lokaci d'aya ta saki murmushi tare da shiga toilet tayi wanka tasa dogon wando da hijab, sannan ta d'auki akwatinta ta fita, u/kanawa ta Fara zuwa ta ajiye, bata sami abbanta na Bariki ba sai ummanta na bariki dan haka tace mata bari taje ta dawo.

Bariki direct gidan Alh madu ta nufa, bayan ta karasa ta sallami mai keke sannan ta shiga cikin gidan Kai tsaye....

A falo taga Alh madu

Ganin bariki ta shigo yasa ya tashi yana fad'in dama Nasan zaki zo, nasan dole kizo.....

Bariki ta dakatar dashi tare da fad'in Zanzo for sure, gani nazo Mai kake bukata??

Yace ke nake bukata tare da d'aga mata gira.

Bariki tace ni kake bukata??.... Wani irin dariya ta saki lokaci d'aya kuma ta gimtse fuska tare da fad'in amma wasa kakeyi koh?? ..... Ina tunanin ka manta wacece bariki shi yasa kake kokarin Sani abunda Banyi niya ba.... Kasan Mai yasa nazo???.... Kai a tunaninka saboda ina tsoran ka tura hotona a internet yasa nazo? Never.... Karka manta bariki ake kirana miye danka watsa hotona a internet?? Miye a ciki? Kai a tunaninka dan kasa hotona a internet zanji wani abu?? Dariya ta saki tare da fad'in u r wrong duk yarinyar data baro gidan iyayenta ta fito tana zaman kanta kai a tunaninka dan kasa hotanta da namiji tsirara zata damu??? Aini Idan kasa aka watsa a internet plz kasa a had'a da number dina May be in sami Mai babban ayaba ba irin naka ba na Wasan yara, SANATA ALH MADU..... kana son buga wasa dani tunda ka Fara sai mun buga..... Karka manta bariki ba y'ar Siyasa bace, bariki ba Sanata bace bariki bamai mukami bace..... Face karuwa Mai zaman kanta wacce take aikata komai dan ta sami duniya..... Yau Idan ka d'aura hotona a internet koda ace nice banda kaya a jikina suna zaka samamin zaka sa in sami yawan masoya masu son sex dani, Kaga may be Turai ma su kirani susa inyi blue film a Biyani..... But amma abunda nake tsoro shine inkai ka rasa kujeranka na Sanata........

Da sauri yace enough don't you dare say something like that in your life again in front of me......

Dariya tayi tace why?? I thought mulkin farar hula muke kowa Nada y'anci koka manta ne??? Ba nazo wani dogon surutu bane ko turanci ba..... Am hare to warning you, ka fita harka na ,nasha ko d'an Siyasa kaman distinguish senator yana da tunani da basira, ashe ba haka bane..... Oh na tuna abun ya had'e da tsufa dariya ta saki mai sauti sannan tace ga kuma son duniya.... Wlh harna tausaya ma al'umar da kake wakilta basu San tsohon banza suka tura...... Tas ya wanke fuskanta da Mari tare da Jefata kan kujeran falon

Bariki tace u slap me?? Kara mata wani Marin yayi.... Yazo zai kara mata wani tayi wuf ta ri'ke hannun amma karfin mace dana miji ba d'aya ba ya kwace hannunshi tare daja mata hannu yayi bedroom dinshi da ita, yana shiga ya Jefata kan gadon d'akin..... Sannan ya kalleta yana wani huci kaman wanda yayi aikin karfi..... Yace zan nuna miki ni tsohon banza ne, zan ajiyeki a nan har karshen rayuwarki inyi ta cinki sai dai ki mutu y'ar iska kawai.....

Dariyan da bariki ta saki ne, shine yasa ya kura mata ido, tace amma kayi hauka koh?? Ina tunanin Bayan tsufa da toshewan basira ka Fara tabuwa, Bari kaji Kafin inzo inda kake saida na shirya ma, ka d'auka haka kawai Zanzo ba tare da wani shiri ba???? Toh inma haka kake tunani Toh ka daina...... Karka manta dazu ka kirani duk abunda ka fad'a nayi recording, sannan ka turamin ainiyin hotan da ka d'aukemu nida kai, Kaga in kasa an canza wancan zan karyata ta hanyar tura Wanda ka turamin wanda fuskanka ne akai tare da tura recording din da nayi kake ta surutai akan kasa a canza fuska...... D'an shuru tayi tare da kallonshi ganin yanda ya d'an tsorata yasa taci gaba da fad'in Kaga in nasa nawa Nima k'imarka da siyasan ka ya zube...... Madu ina son ka sani bana son bata maka suna amma kana ingizani, are you not are shame, nace na daina harka da maza aure zanyi amma kana son dole saina ci gaba dayi, inaso ka sani daka yau shine rana ta karshe da zaka sake yunkurin shiga al'amari na, zan iya fasa auran da zanyi kaifa zaka iya yarda ka rasa kujeranka???..... Ganin Alh madu ya kasa cewa komai yasa ta Fara kokarin fita har takai bakin kofa ta tsaya tare da waigowa tace ina maka fatan shiriya domin mutuwa ci take kaman rana, a shekarunka yanzu babu abunda ya dace dakai sai istigfari domin neman gafaran Allah dan an bata y'ay'an mutane da dama, kaima ka jira Kaga abunda za'ayi ma naka da yardan Allah...... Fuuuuu ta fita tabar gidan, tafiya take tana kuka a kafa tare da takaicin tsintar kanta da tayi cikin wannan kazamar harkan, amma ta d'anji dad'i tunda yanzu ta tabbata Alh madu bazai K'ara Mata barazana ba akan rayuwarta dama shine matsalanta..... Yanzu Abu d'aya zan fuskanta shine Idan Yarima yasan gaskiya shima zanyi komai yanda ya dace ta hanyar fad'amai da fahimtar dashi komai...

Bayan fitan bariki Alh madu murmushi yayi wanda nidai ban gane na miye ba, na mamaki ne? kona nadama ne? kona shirin wani tuggu ne? oho ...... Koma dai miye zamu gani in yaji gargadin bariki ko kuma zai sake bibiyarta

Bariki tana zuwa kofar gidansu na u/kanawa ta hango motar Yarima a fake, wanda shi d'aya yazo..... Mamaki abun ya bata Toh Mai yasa bai kirata ba, kuma wayarta na hannunta, tace may be yanzu yazo...... Gaba tayi tazo zata wuce cikin gidan tayi kaman bata ganshi ba, shima yana kallonta baice mata komai ba harta shige cikin gidan..... Murmushi Yarima yayi tare da d'aukan wayarshi ya tura mata message kamar haka......

Ko in tafi ne???

Bariki ganin message dinshi yasa tayi dariya tare da fitowa waje ta sameshi inda yake bud'e motar tayi ta shiga

Kallonta yayi tare da fad'in kina ganina kika wuce

Tace Yarima yaushe na ganka??

Murmushi yayi tare da fad'in my princess inafa kallonki, harda wani kawar dakai Kalan baki ganni ba

Tace Yarima nidai naga mota amma ban San Waye a ciki ba, ko kana son inyita kallon maza ne ??

Bai san lokacin da yayi dariya ba, tare da fad'in koda yaushe kin San hanyar da zaki Kare kanki...

Shuru tayi tana tunanin I wish Yarima yasan gaskiya ya fara sona, hawaye ne ya gangaro mata a ido da sauri tasa hannu ta goge dan karya gani tare da d'ago kanta taga koya gani.... Kur taga yana kallonta...... Da sauri tayi k'asa da kanta

Yarima Aliyu yace Zainab a kullum nazo Wajanki kina Sani fargaba, Wai Mai kike boyemin ne?? Kina sani tunani Kala Kala plz tell me Mai yake damunki banso ki barni cikin duhu.....

Kuka ta farayi tare da fad'in Yarima tunda nake ban taba jin son kowa ba sai Kai, ina jin tsoran abunda zai faru in kasan gaskiyan al'amarin da nake boye maka....... Karan wayan Yarima ne ya Katseta

D'aukan wayan Yarima yayi ganin Sunan waziri ne, ji nayi Yarima yana fad'in ok gani nan zuwa, har kun karaso?.... Kashe wayan yayi tare da kallon zainab yace Bari inje in dawo yanzu.

Bariki tace ok tare da fad'in saika dawo sannan ta fara kokarin fita daka motar.....

Hannunta ya ri'ke tare da fad'in haka zaki fita Fuskanki yana hawaye??..... Janyota yayi jikinsa tare da goge mata hawayen fuskanta yace plz my princess kibar wannan kukan yanzu zan dawo sai muyi magana Kinji?

Kaita d'aga Mai alaman eh.

Murmushi yayi tare da fad'in dat my girl, inna dawo zan fad'a miki albishir

Murmushi tayi tare da fad'in saika dawo sannan ta fita.

Yarima direct u/sarki ya nufa inda Zai had'u dasu waziri a nuna mishi filin da Mai martaba ya bashi sannan suje asibitin shi y'an jarida su d'auka domin a tallata asibitin duk da Yarima baiso hakan ba, amma waziri yace ayi tunda yace zai Fara aiki na wata uku kyauta akan matsalolin mata tunda shi likitan mata ne, ta gidan tv da radio mutane za suji marasa karfi su zo..... Asibitin ba Yarima kadai bane zaiyi aiki a cikinsa ba harda wasu likitoci na fanni daban daban......

Bariki bayan ta shiga cikin gida, ummanta tace Zainab Yadai har Yarima din ya tafi?

Tace eh amma zai dawo.... Wai har yanzu habib bai zoba? Tun dazu yake cemin yana hanya.....

Sallaman habib dinne yasa tayi shuru ya shigo yana gafaran ku dai masu gida

Shiga d'akin dasu bariki suke yayi yana fad'in in shigo ko in jira a kimtsa....

Bariki tsaki taja Tana fad'in Asara, bayan ka shigo din kake tambaya koka shig......

Waige ya farayi yana duba dawa bariki take magana, yaga babu wani namiji a wajan yace ke dawa kuma?? Naga banga ko wani namiji a nan ba

Bariki tace dakai nake mana...

Yace Wlh bariki zan miki rashin mutunci miye wani ka? Mai yakai mace jinsin maza, gskya banso yana maganan yana hura hanci Kalan ranshi ya baci.....

Umman bariki ta Karya babu abunda take sai dariya, tace Zainab gskya bakya kyautawa taya zaki dinga kiranta dana miji Bayan kin San macece y'ar uwarmu....

Habib yace fad'a mata dai

Bariki dariya tayi tare da fad'in ni bama wannan ba kawata kina ji??

Habib yace kunne aike ji

Bariki bashi Labarin yanda sukayi da Yarima tayi Kafin yace zaije ya dawo, taci gaba da fad'in Wlh Ina son fad'a mishi gaskiya Kinga sai muyi aurenmu lafiya ba tare da matsala ba.....

Habib gyara zama yayi yace lallai Bariki, ban taba sanin baki da wayau ba sai yau. Ke kina tunanin in kika fad'ama Yarima gaskiya zai aureki?? Kin bashi iyayen karya tare da Labarin karya ke kina tunanin duk son da yake miki zai yarda ya aureki? Karki manta kina fad'amin yanda yake kyaman mace mazinaciya, sannan kike gigin son fad'a Mai gskya? Toh inma shi Yariman ya yarda ya aureki kina tunanin iyayenshi zasu yarda??? Bariki kin San Gidan sarauta kuwa?? Shawaran da zan baki shine kiyi shuru da bakinki kiyi yanda kika tsara in an d'aura aure kya fad'a mishi gaskiya tunda naga kina mishi son tsakani da Allah kuma naga kina son zaman auren, kuma nasan bazai sakeki ba tunda ya aureki kuma basa saki..... Yau inda bakya sonshi Kinje gidan da wani manufa ne sai kice mai fyad'e aka miki, amma tunda son gaskiya kike Mai saiki fad'a mishi gaskiyan koke wacece.

Mahaifiyar bariki ta Karya, tace bariki gaskiyan habiba ne, wlh Indai kika fad'a mishi gaskiya zaki iya rasashi kuma na har abada, gidan sarauta zasu iya yarda su rasa d'ansu akan ace ya auro musu karuwa domin abun kunya ne, ki duba kiga su ko aure kayi a gidan sarauta sai Anga jini shine kin Kai budurci... Bayan bako wace mace ke jini ba kuma budurwa ce

Habib ya tabe baki tare da fad'in nidai Allah yasa ina d'aya daka cikin mata masu zubar da jinin, Kar insha gorin miji .... Dan mazan nan ba mutunci garesu ba.....🤣🤣🤣🤣

Bariki tace toh kuna ganin inna aureshi na fad'a mishi zai hakura dani?

Habib yace insha Allah, dole ma ya zauna dake tunda bada gardi ya kamaki ba, ai yanda kikaji dad'i al'adan gidan basa saki, sai an kamaka da gardi kuma kince kin tuba.....kuma na tabbata koda yayi fushi zai sauko tunda ya aureki zaki san hanyar da zaki janyo hankalinsa ma dole ya sauko, domin ya sami. santaleliyan yarinya son kowa k'in Wanda ya rasa...... Toh Bari dai mu gani bariki zata fad'ama Yarima inya dawo koko ta d'auki shawaran habib au🤭 Anty habiba.....




*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 11*








Dariya bariki tayi tare da fad'in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh ban son inga ya shiga wani hali, bazan iya jura ba, ina sonshi da yawa.....

Habib yace Toh fah, yau Ina ganin bariki.... Toh yanzu dai Mai kika yanke....??

Bariki tace abunda kuka fad'amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d'aura aurenmu aka kaini ranan zan fad'ama Yarima gaskiya.....

Habib shewa ya saki tare da fad'in Aiko ki tabbatar kin fad'a mishi tun Kafin ya shiga yaji ya shige zirif kaman bakin gate.....

Bariki duka takai ma habib iya karfinta tare da fad'in rafi ne ba gate ba

Habib ya ri'ke wajan da takai Mai duka yana fad'in na shiga uku zata kassarani..... Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu ki takarkare iya karfinki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba......

Bariki tace andai yi Asara

Habib yace ke kikaga Asara bani ba

Umman bariki tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu sai su kaimu gaba....

Habib yace gaskiyanki domin naga matar can d'akin ta kusa daku Tana min wani kallo wanda ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci in cire kaya mu daku Dan ban son iskanci....

Suna cikin haka Yarima ya kirata tare da fad'in baby come out Ina waje.....

Tashi tayi tana fad'in bari inje inga Yarima na.

Habib yace oh kunga salo a gayas....

Fita tayi tana fad'in kaji dashi.....

Motarshi ta nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud'e motar ta shigo ciki tare dayin sallama....

Amsawa yayi tare da fad'in my princess na gaji, tunanin driving nakeyi in zan koma Gida.....

Kallonshi tayi tare da fad'in ko in tu'ka ka, in kaika gida??

Yace dakin taimaka min kuwa

Dariya tayi tare da fad'in kaman dagaske....

Yace dagaske nake mana Kinga Idan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa....

Hannu tasa tare da rufe fuskanta tana dariya

Yarima kiran sunanta yayi da Zainab.....

Da sauri ta d'ago ta kalleshi domin jin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai muhimmanci.... Wanda yake bukatar natsuwanta

Yace d'azu kina son Yimin magana Ina jinki yanzu....

Murmushi tayi tare da fad'in Yarima a kullum Ina tsoran fad'a maka cewa ni dakai bamu dace ba, saboda kai ka fito gidan girma ni kuma ba y'ar kowa bace ina tsoran auranka domin gudun wulakanci irin na mas......

Da sauri yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad'in enough, dama duk wannan nonsense din kike son fad'amin shine kike d'agamin hankali?..... D'an tsaki yayi alaman jin haushi tare da kawar da kanshi gefe.....

Ganin ranshi ya baci yayi banza da ita, yasa ta d'ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri, ban San zakai fushi ba.....

Katseta yayi da fad'in Zainab ban taba tunanin zaki dinga irin wannan tunanin ba.... And kina ma sona kuwa????.....

Da sauri ta kalleshi tare da fad'in Yarima baki bazai iya fad'in irin sonda nake maka ba, how I wish in bud'e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka..... Yarima Ina Sonka yanda baka zato duk wani jini dake gudana a jikina yana gudana ne da Sonka I..... Da sauri tayi shuru ganin yana kallonta.....

Jin tayi shuru yasa ya ru'ko mata hannu tare da fad'in Zainab are you sure akan abunda kika fad'a??

Kai ta d'aga Mai alaman eh

Wani irin murmushi ya saki cikin jin dad'i, tare da fad'in nace zan baki albishir d'azu right?

Tace eh

Hannunta ya saki tare da fad'in ina goran albishir din???

Dariya tayi tare da fad'in zan baka in naji albishir din

Dariya yayi tare da fad'in promise?

Tace yes I promise....

Yayi murmushi tare da fad'in mai martaba ya amince da maganan aurena dake.... But at first yace in Bari nan gaba tunda ban dad'e dayin aure ba.... Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra'ayi ba yace za'a turo gidanku ayi magana d'azu waziri yake fad'amin May be cikin week dinnan a turo......

Bariki gaba d'aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba d'aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai....

Ganin tayi shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad'in lafiya kuwa my princess? Kodai you are not happy ne dan za'a turo??

Da sauri tace a'a am so much happy tare da sakin murmushi....

Ganin ta saki jiki yasa Yarima jin dad'i sun dad'e suna fira sannan Yarima yace Zai tafi tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a ciki ba....

Amsa tayi tare da fad'in ngd

Hancinta yaja tare da fad'in sai munyi magana.....

Tace OK tare da fita tayi cikin gida,.... Tana shiga habib ya amsa ledan tare da fad'in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa nakeji tun safe babu abunda naci....

Su turare ne Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud'i a ciki.... Habib d'aukan kud'in yayi dubu d'aya d'aya bandir biyu, dubu d'ari biyu kenan..... Yace Kai Yarima akwai kyautar girma....

Uwar bariki ta Karya tace ai gidan sarauta ya fito dole ya dinga kyautar girma.... Domin da suji kunya gwara dukiyarsu ta k'are....

Bariki kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad'in mai kuke cine Wai??

Ummanta tace abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya...

Bariki tace toh yanzu tunda nazo inyi sati d'aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib tayi tare da fad'in muje muyi cefane mu dawo......





********
Tsakanin haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da kalamai masu dad'i da kwantar da zuciya...... Sai dai abu d'aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar Hjy habiba ta yarda d'anta ya aureta ..... Sai dai

Please Login or Register in order to submit comment