Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani da Falmata, Dad dina kallon tsana yake min ina mamakin ya akayi ya dawo yau,

Katse min tunani yayi da fad'in uban wa ya miki ciki ??

Cikin razana da fargaba nace Dad mai.....

Tas tas ya saukemin Mari har biyu tare da fad'in kin cuceni Zainab, nida nake ma jama'a wa'azi , yau gidana shine y'ata ta ciki na tayi cikin shege.... Allah ya isa tsakani na dake Zainab kin cuceni, duk irin tarbiyan dana baki, jiya sanda ummi d'inki ta kirani tace in dawo gida babu lafiya, Banyi zaton wannan mummunan labarin zan Tarar ba.....

Cikin kuka na fara fad'in Wlh dad ba ciki gareni ba, kuma Wlh muje asibiti a duba, Niko saurayi ma ban dashi W.......

Tas Falmata itama ta sakar min wani gigitaccen Mari tare da fad'in shairi likita zata miki, mutuniyar banza, wlh kin cucemu kaf zuri'ar mu babu wacce ta taba Abun kunya sai ke

Cikin kuka nace ummi Kema shaida ce banda K......

Tayi sauri ta katseni tare da fad'in Yimin shuru munafuka

Dad dina shidai shuru yayi inda Falmata take ta kalaman batanci akai na tare da fad'in na d'auko musu Abun kunya yanzu taya zasu kalla mutane da wannan abun nawa..... Falmata ta kalli dad dina babu ko tsoro tace naji kayi shuru kaman kana jin tsoran yi mata magana gwara ka yanke hukunci tun Kafin mu kasa fita

Dad dina yace in fad'i uban da yayi min ciki.

Ina tamai rantsuwa akan ba ciki gareni ba, dan dai nidai nasan ban taba kwanciya da kowa ba nida ko maza ban kulawa taya zan samu ciki, sai dai in a ruwa nasha.... Da sauri nace Dad Wlh hala a ruwa nasha d...... Falmata ta saki shewa tare da fad'in a ubanki gashi nan da yake gabanki kika sha...... Ko tsoran dad batai ba ta dinga zaginshi Wai shine ya dauremin gindi ai yana nunamin so ya d'auki dukiya masu yawa Yaban ba dole Inbi maza ba..... Kuka nake Sosai tare da takaici na tabbata Falmata Nada wani mummunan Abu a kaina tun sanda Dad dina yace tun jiya ta kirashi akan ya dawo, toh ni kuma yau Dr tazo ta dubani kenan tasan wani abu ko ince ita ta kullamin shairi..... Tsawan da Dad dina yamin yasa na dawo cikin hankalina da hayyacina yace na baki nan da zuwa gobe ki fad'amin wanda yayi miki Inba haka ba za kiga fishina y'ar iska fuuuuuu ya fita...... Wannan itace mummunan Kalman dana taba ji Dad ya fad'a tunda nazo duniya kuma ba'a kan kowa ya fad'a ba sai a kaina, Kalman tayi min ciwo, nidai nasan namiji ko hannuna bai taba ri'kewa ba balle ince toh taya na samu ciki kwata kwata na kasa ganewa..... Ina dai nan zaune inda nake ina kuka saiga Falmata ta shigo tazo gab dani Tana fad'in Zainab kiban had'in Kai Indai kina son Dad d'inki ya yafe miki.....

Wani irin kallo na Mata tare da fad'in da in aikata abunda kike bukata gara dad ya yankani d'anya ya soya Naman jiki na, akan in aikata wannan mummunan aikin wanda Manzon Allah ya tsine ma masuyi.....

Tace haba zainab sau d'aya kawai za muyi in mukayi sai mu tuba....

Zainab tace tir lallai tabewa da Asara sun tabbata a kanki, lallai irinku ne wanda ake cewa kuna fita daka addini baku Sani ba......

D'aura hannunta tayi akan nonona da sauri na wanka mata Mari Wanda dai dai lokacin dad dina ya dawo d'akin ganin na mareta yasa ya fara salati tare da fad'in munanan kalamai a kaina wanda zan iya rantsuwa sune suka bini harya kaini inda nake yanzu domin bakin iyaye dafi ne, sai yasa koda wasa karka taba aibanta d'anka domin addu'an iyaye kaman takobi take da kaifi..... Dad yaci gaba da fad'in daka yau bani bake bazan zauna da wannan abun kunyar ba, wlh saboda ke bazan fasa fita cikin al'umma ba , sannan harda marin ummi d'inki lallai wata rana Nima zaki mareni,

Kuka nake Sosai domin jin maganan dad nake Wlh kaman bashi yake fad'ansu ba, mutum Mai tawakkali, da ilimi yau shine yake nuna da yaji kunyar duniya gwara ya rabu dani har abada, duk irin sonda yake min ban taba tunanin zai min haka ba, yau koda cikin gareni dagaske ina tunanin dad dina zai d'auka a matsayin kaddara amma gashi anyi min shairi ya yarda

Gashi matarshi sai zugashi takeyi shi kuma yana k'ara hawa yana aibanta ni......

Ranan cikin dare mahaifina yace in bar mishi gidanshi tunda naki fad'an uban da yayi min ciki, ina kuka inata rantsuwa akan banda ciki, inma ciki ne Toh a ruwa nasha, har al'qur'ani na d'auko na dafa akan ban taba saduwa dako wani namiji ba amma dad dina baiko saurareni ba, cikin kuka nace Dad na tabbata abunda kake min yanzu kana yinshi ne cikin rashin bincike, dad kafi kowa sanin wacece ni, kafi kowa sanin abunda zan aikata yau Dad koda ciki gareni ina tunanin zaka d'auka a matsayin kaddara....

Cikin murya irin ta fushi yace fita kibar min gida y'ar iska karuwa......

Lallai wannan Kalman ta dad'e tana Yimin ciwo Sosai har yau inna tuna ina kuka

Mahaifina ya'ki amsan kaddarata saboda Kar yaji kunyar duniya ace y'ar babban malami tayi cikin shege, duk da a lokacin ban San inada ciki ba dagaske.....

Tafiya nake cikin dare komai ban samu na d'auka ba, daka ni sai kayan jiki na, wata babban mota na gani ta lodo wasu kwalaye na samu na shige duk da ban San inda za suba kawai Ina burin inbar garin abuja dan nasan motar wani gari zata, ban dad'e da shiga ba motar ta tashi kaman ni suke jira...... Aiko mukai ta tafiya...... Munyi tafiya Sosai Kafin motar ta tsaya inda na samu na fito na ganni a wani waje kaman kasuwa duk da darene ga mata birjit, cikina naji ya fara ciwo Sosai tare dajin wani abu kaman hanjin cikina zai fita, da sauri nayi wani wajan benci na zauna inata juyi ji nayi wani abu kaman ruwa na fita daka jiki na, ina dubawa naga jini Sosai ga wani irin ciwon ciki inaji Sosai, muryan wani naji a kaina yana fad'in na shiga uku an fasa aurena Mai zan gani haka y'ar uwa??

Ganin na kasa magana alaman ina jin jiki yasa ya kamani yana fad'in oh ni hjy babba sai ku tashi ku kwaso ciki kuzo kusha maganin zubar da ciki kuyi ta juyi, sai a nan na tabbatar da ciki gareni kuma Bari Nayi domin anyi mana bayanin jinin al'ada a islamiyya kuma yanda wannan jinin yake zuba nasan bana al'ada bane, na shiga rud'ani Sosai tare da tunanin a Ina na sami ciki, naci kuka tare da takaicin wannan abun..... Wanna d'an daudun Mai suna hjy babba shine ya taimaka min harna warke na dawo normal Ina kwana a d'akinsa saiya koma d'akin abokanan sa y'an daudu...... Wannan shine silan komawa na gidan karuwai har na fad'a wannan mummunan harkan tunda banda wani abu da zanyi sai shi, sannan nakan je kofar gidan mahaifina ko in tura a ajiye Mai hotuna na da shigan banza dan in kuntata mishi sai dai ban sani ba koya gani ko bai gani ba oho, ina karuwanci ne saboda rasa mafita ko madafa iyayena sun koreni banda wani gata.... Komai ya fado min shi zanyi tunda banda mafita duk da ina aikata Abunne kaman dole sai dai banda wata hujja akai, amma na d'aura hujjata akan ina son in kuntata ma Dad dina, duk da wani zuwa da nayi na ajiye hoto naga gidan babu kowa , na tambaya akace sun tashi tun daka wannan ranan da naje naga gidanmu ban k'ara tunanin in koma Gida ba ko in nemi iyayena ba...... Dan Tsagaitawa tayi tana kuka tana rungume jikin Yarima taci gaba da fad'in Wlh Yarima Ina aikata zina amma Wlh harga Allah cikin raina Ina mamakin haka..... Had'uwa na dakai shine yasa na daina, gaba d'aya, Yarima Nasan had'uwa na dakai had'in Allah ne, na tabbata duk wannan Abun daya faru dani kaddarace Wanda har yanzu ban son wanda yamin ciki ba, Yarima dan Allah kaima karka juyamin baya kaman yanda dad dina yamin dan Allah Yarima.......

Yarima Aliyu dan janyeta yayi a jikinshi ya kura ma fuskanta ido na wani lokaci sannan ya fara murmushi tare da fad'in wow wow nice story I wish dat am a director in had'a film da wannan labarin naki Nasan zan samu kud'i, zainab I will never ever trust you again, komai zai fito daka bakinki karya ne, do you think dat I will believe you with dis ur fake story....... Har kina danganta kanki da babban malami kina fad'in shine dad d'inki?? Wani irin murmushi yayi tare da fad'in you always lies to me...... Bazan k'ara yarda dake ba in my lyf......

Tace Yarima am telling you the truth........

Yace truth?? Zainab komai naki karya ne, kina tunanin wannan labarin naki zai sa in yarda dake?? You are wrong, this is not the same Yarima dat trust you before, today wen I see d truth about you I have change.....

Cikin kuka tace Yarima Wlh gaskiya na fad'a maka harga Allah, Wannan shine gaskiyan labarin rayuwa ta......

Yace koda gaskiya ne....... I won't accept you as my wife...... Zaki zauna a nan a matsayin baiwa Mai min bauta...... I won't accept you macen da kowa ya Santa, but before in baki aikin ki dole in miki HIV test in gani May be kina dashi tunda anbi wancan anbi wancan so Kinga in kina dashi sai in San Kalan aikin daya dace in baki...... Zainab I will make sure to hurt you, saina hukunta ki yanda nan gaba bazaki k'ara yaudaran wani ba, you r lucky I make promise to my dad da yau sai kin bar gidan nan but you will live here as my servant, I hate to see your face, make sure to hide your face from me har sai na nemeki cheater, Yana fad'in haka ya ri'ke kirji dake faman mishi zafi ya fita tare da bar mata d'akin...... K'asa tayi tana kuka shikenan Yarima ya tsaneta duk da ta fad'a mishi gaskiyan ko ita wacece kuka ta saki mai ban tausayi......




Daka yanzu duk wacce take neman BARIKI NA FITO, daka farko taje ta duba Wattpad ko facebook page d'ina MARYAM OBAM NOVELS... Dan gskya daka yanzu babu wacce zan kara turamawa na gaji ga typing ga aikin ture ture haba Abun yamin yawa......







*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 21*







Lallai dama duk Wanda yabar Allah yana tare da tabewa da Asara, duk Wanda ya zabi sabama Allah, amma babu komai zan jure insha Allah, zan d'auki duk wani hukunci ukuba da Yarima zaiyi min...... Da sauri ta tuna da abunda habib ya Mata, lallai habib yaci amanarta rayuwa wanda ka yarda dashi shine mai cutanka...... D'auko wayanta tayi duk da dama Yarima ya canza mata layi gab da bikinsu Tana da number habib dana su haulat ...... Kiran habib tayi duk da lokacin wajan karfe biyar saura an kusa kiran sallah asuba..... Cikin muryan bacci ya d'auka daka gani baima ko duba sunan ba.....

Jin muryan bariki yasa habib fad'in harya koroki ne???

Tace habib kaci amanata Tana magana tana kuka, mai yasa kamin haka, duk irin yardan da nayi maka??? Abun ......

Yace dakata ki daina kaini jinsin da ba nawa ba Mlm,

Tace an kaika d'an daudun banza da hofi..... Maci Amana

Habib yace dakata bariki, miye zancan cin Amana?? Au dama bariki akwai Amana ne?? Toh gaskiya Indai haka kika d'auka bai kamata a dinga ce miki bariki ba, karki manta kud'i na fito bid'a, kuma da Farko Aina rufe miki sirrinki, da aka Biyani naira na dukan Naira har million biyar na fad'i gaskiya, sannan wacce taban tace in kira Yarima in fad'a mishi gaskiya, Kafin ki fad'a mishi, sannan ta tura mai hotunan ki da kikai da maza, da sim d'inta na kira kuma ta wayarta ta tura hotunan, dan haka aikin kud'i nayi, ke kina tunanin saboda in rufa miki asiri zanki amsar million biyar, haba bariki ai kin yaudari kanki, Bariki babu Amana ko yarda..... Da Farko na ri'ke miki amana daka baya kud'i yasa na canza, dan haka Kar kiga laifina.........

Bariki tace abunda Kamin insha Allah sai kaima anyi maka, kaida wacce kuka shirya hakan......

Habib yace Ina ja miki kunne ki daina kaini jinsin daba nawa ba, sannan Bari kiji ita wacce ta Biyani so tayi Yarima ya koroki ita ta aureki domin y'ar lesbians ce, bari in fad'a miki sunanta, sunanta hjy Umaima abunda yasa na fad'a miki koda Kema zaki Biyani ki nemeni dan ki rama, ko yaushe ina free Danni da kika ganni y'ar kasuwa ce ya k'arasa maganan tare dayin shewa ahayye....... Ita haulat da bata da k'ashin arziki Aida ita akaso ayi aikin ta Fara yima matar kwana kwana.....

Bariki kashe wayarta tayi domin bazata iya jin wannan tsinannan ba......

Kuka take Sosai wato hjy Umaima itace tayi komai tare da amfani da habib, toh taya tasan habib din?? Taya suka had'u?? Lallai haulat ya kamata taban amsa, kiran Layin haulat tayi bata d'aga ba, k'ara kira tayi harya kusa tsinkewa sannan haulat ta d'auka cikin muryan bacci.....

Da sauri Bariki tace haulat maina miki keda habib da hjy Umaima.....

Haulat da bacci ke idonta jin haka yasa ta tashi tare da cewa bariki, Kece?? Mai kike fad'a haka......

Nan Bariki ta bata Labarin abunda habib yayi mata

Haulat tace Bariki wlh Wlh ban San hjy Umaima zatai miki haka ba, da Farko dai taso taje wajan boka danta miki asiri ki yarda da ita, har nayi niyan taimaka mata a lokacin, sanda na dawo kaduna in zaki tuna wata rana Aina amshi wayarki?? Toh Ina cikin duba hotunan da nake turawa sai gashi an turo wani keda Alh madu tsirara, nan nima na tura, in baki mantaba data dinki a kunne take ranan, ganin na tura na Alh madu saina had'a dana wani da kika kwana a kirjinshi, ina gamawa na baki wayarki, dama Nayi magana da hjy babba akan Alh madu ya bashi aikin ya gano wa zaki aura, yace yana son in tayashi...... Jin haka saina kira hjy Umaima akan Kar taje wajan boka na bata labarin halinda kike ciki, akan auran da za kiyi akwai wanda yake son rusa auran, harda hotunan dana tura cikin wayarki ta bu'kaci in tura mata tunda na bata labari, nan na tura mata harda number din habib dan na fad'a mata shine yasan komai da kike shiryawa...... Bariki tun ranan da kikai min wa'azi tare da nasiha Wlh daka ranan naji jikina yayi sanyi tare dayin nadama, kuma harga Allah na cire hannuna daka son cutar dake, wlh bariki ban taba tunanin hjy Umaima zata nemi habib ba, dan tunda tamin magana nace tayi hakuri kawai ta bari kiyi aure in yaso daka baya sai ta nemeki, na fad'a mata hakan kawai danta kyaleki Ashe bata hakura ba, kai amma wannan matar ko y'ar iska amma karki damu bariki zan dau miki mataki Wlh, Shima kanshi Alh madu da kanshi ya kira hjy babba yace a daina maganan ya barki kawai.........

Bariki kashe wayan tayi bata taba tunanin hjy Umaima ko habib za suyi mata haka ba, lallai makashinka na tare dakai, ta yarda da habib amma yaci amanarta, lallai gaskiya habib ya fad'a bariki babu Amana, sannan komai kayi sai Anci amanarka Indai a bariki ne, jin kiran sallah asuba yasa ta tashi dakyar kanta kaman zai fashe da ciwo, toilet ta nufa dakyar tayi alwala, tazo tayi sallah......

Bayan ta idar gaba d'aya ta kasa bacci , ba komai take tunani ba sai irin matakin da Yarima zai d'auka wanda ta tabbata za taji jiki, dan murmushi tayi tare da fad'in indai wannan hukuncin da Yarima zaimin zaisa ya yafemin Zan jura, koda zaiyi ta azabtar da rayuwa na Indai Ina matsayin matarshi zan jure.... Kuka ta kuma saki tare da fad'in Yarima Ina maka son so, Sonka a jini na yake, zan amshi duk wani horarwa daka gareka...... Tashi tayi ta fita falo da niyan ta Fara aikin bauta daka yau,tana shiga taga Yarima kwance akan kujeran falon yana rawan sanyi, da sauri ta nufeshi cikin Tashin hankali idonshi a rufe kaman yana bacci amma ba bacci yakeyi ba........ Hannunta tasa akan goshin shi taji zafi Sosai.. Ido ya bud'e a hankali idonshi ya sauka akan Nata gaba d'aya kallon juna suke cikin ido...... Sunyi wajan minti uku suna kallon juna Kafin ta tashi da sauri taje ta samo ruwa da towel tasa towel din tare da matsewa, ta Fara k'okarin sama Yarima akai cikin murya irinta mara lfya yace don't you dare try to touch me.

Cikin kuka tace Yarima plz allow me to do it, you have a fever.....

Yana k'okarin yin magana tayi sauri tasa Mai towel din akai tana d'an matsa Mai, jin haka yasa ya kasa maganan da yake son yi.....

Amma cikin ranshi babu komai sai k'una tare da tuna hotunan da aka turomai bariki akan namiji tana kwance ga wani kuma yana tsirara ya ri'keta, da sauri yasa hannu ya ture ta.......


K'asa tayi ruwan dake kusa da ita ya zube, yace karki k'ara zuwa inda nake, I have told you, I hate to see your face....

Kuka take Sosai tare dayin nadama akan irin rayuwar data jefa kanta, dan kawai ta kuntata ma Dad d'inta, wanda inta mutu bata da wata hujja, lallai dama irin bala'in dake cikin zina harda rashin ganin k'imar mutum, sannan ba'a ganin darajan mazinaci Wanda gashi shine take gani yanzu, ta tabbata bata ga komai ba yanzu, sai nan gaba.....

Yarima ne ya daka mata tsawa cikin tsana tare da fad'in I said leave from here.

Jiki a sanyaye ta tashi tana kuka harta kusa shiga d'aki yace stop...... Cak ta tsaya

Yace zoki goge wannan ruwan, wa kika bari ya goge?? And make sure ki cire carpet dinnan dan ruwa ya tabashi shima, kije ki shanya a waje......

Kitchen ta nufa ta d'auko mopper ta Fara goge ruwan, carpet din yana da girma kasa d'auka tayi, duk abunda Zainab keyi Yarima na kwance yana kallonta, ganin bazata iya d'auka ba yasa tace Yarima cikin dashewan murya bazan iya d'aukan carpet dinba yayi min nauyi.....

Murmushi yayi tare da fad'in inda sex ne ai kina iya yi, harda kwanciya akan ko wani namiji kin iya, kindai iya karuwanci......

Ido ta lumshe domin maganan Yarima Aliyu ya dakar Mata zuciya, harga Allah Kalman daya fad'a ta iya karuwanci taji Kalman har cikin zuciyarta, tunda take ba'a taba ce mata karuwa ba tunda ta fito karuwanci Abun ya dameta, ita da takeso a dinga ma kiranta da bariki, amma yau shine rana na farko da aka ce ta kware da karuwanci Abun yayi mata ciwo.... Wani zazzafan hawaye ne ya zubo mata ganin in bata fitar da carpet dinba zaiyi ta fad'a mata magana sai yasa ta Fara k'okarin ta d'auki carpet din domin ta kaishi waje din, kaman yanda yace.... Fara ja tayi tana son tayi k'okarin ta d'auka tasa akai, santsin tiles din wajan dabai bushe ba ya di'beta zata Zame, gaba d'aya ta sadakar ta fad'i ji tayi an ri'keta, idonta dake rufe saboda tsoro ta Fara bud'ewa a hankali idonta ya sauka akan na Yarima da shima din ita yake kallo, sunyi wajan minti biyar a haka suna kallon juna , sannan ya d'agota gaba d'aya tare da fad'in stop making and excuse da zaki dinga sawa ina taba wannan kazamin jikin naki.....

Bata ce komai ba shima yana tsaye yana kallonta, kokarin d'aukan carpet din ta karayi......

Hannu yasa shima tare da kama mata duk da baya jin dad'in jikinshi , har kofar waje suka Kai ganin fadawa a wajan, gashi ko hijab balle Gyale bata saba sai dan kwalin dake kanta na jallabiya, yasa yace sake carpet din kibar nan....

Bata musa ba, dan in tayi magana zai iya yi mata ihu, ga fadawa kuma tana hangowa ita yanzu tsoran halin Yarima take, d'auke roban ruwan tayi takai kitchen ta fito kenan shima yana shigowa falon, kallonta yayi tare da kawar da idonshi daka kanta, daka ya kalleta sai ya tuna irin karyan da tamai, Ashe duk ba sonshi take ba, dan kud'i ta aureshi dan k'aramin tsaki yaja tare da wucewa d'akin da yake matsayin nashi danya kwanta yabar ganinta domin wani irin tukukin ba'kin ciki yake cika shi tare da mamaki Wai itace take da wannan munanan halin.....

Gimbiya zinatu Tana farkawa ko sallah batai ba ta doka ma gimbiya Amina kira.......

D'auka gimbiya Amina tayi tare da fad'in zinatu lafiya da asuba, badai Yarima bane ya miki wani abu??

Tace ko d'aya labari na kira in baki da dumi duminsa

Gimbiya Amina tace bani inji kodai Yarima ya Kori Matar daya aura ne??

Gimbiya zinatu tace kusan haka, nan taba gimbiya Amina Labarin abunda Ya faru.....

Gimbiya Amina tace Kai amma wannan labarin yamin dad'i wlh, toh kodai ya sameta a bule ne?? Hala ba budurwa bace an gama cinyeta a waje, shine yaci yaji kofa a bud'e shine nasan yasa lokaci d'aya ya tsaneta, amma labarin nan yasa ni nishad'i.... Su Yarima manya shidai Mata duk ba virgin....

Dariya suka saki su duka, gimbiya zinatu tace ni tunani sunyi min yawa wlh, na farko dai bamu tabbatar ko virgin bace ko akasin haka, kinga bamu da tabbas and sanda yake kwance ita taje tayi magana dashi, har Dr yana cewa tare da taimakon ta, yasa zuciyarshi ta Fara harbawa.... Wlh am compose

Gimbiya Amina tace haba zinatu karki sama kanki tunani, ke dama miye burinki badai Yarima yafi sonki bane, koma ya saki matar daya aura??

Zinatu tace eh shine burina My love

Gimbiya Amina tace toh ki cire tunanin komai, na kusa zuwa Zaria din insha Allah, zamu shirya komai, yanda zata bar gidan gaba d'aya.......

Yarima koda ya shiga d'aki kasa bacci yayi sai juyi yake, gashi kirjinshi na mishi mugun zafi, ga zazzabin har yanzu yana ji, zainab ta gama dani, ta cuceni, but zan rama abunda tamin Wanda nan gaba zata kiyayi yaudaran wasu.....





******
Farhan ya kammala karatu inda ya taso da maganan auranshi da haulat, nan hjy habiba ta tasar da balli akan bai isa ba, babu yanda mijinta baiyi ba akan ta fad'a mishi dalilin rashin yarda amma ta kasa bashi amsa, dan haka yace dole sai farhan ya auri haulat......

Haulat tana d'an waya da Bariki kuma tana neman shawaran bariki duk da bako da yaushe bariki take d'aukan wayanta ba, wata waya da sukayi Bariki taba ma haulat shawaran ta fad'ama farhan gaskiyan lamarin abunda suke ciki ita da mum dinshi in yana Sonta may be ya aureta inko baya Sonta sai su hakura, inda bariki ta fad'ama Haulat ita gashi karyan da tama Yarima gashi tana shan wuya yana nuna mata tsana a fili, haulat ta d'auki shawaran bariki.

Farhan yazo kaduna inda suka had'u da haulat kaman yanda bariki ta fad'a mata haka ta fad'ama farhan, nan da nan idonshi ya kad'e yayi ja, baiko tsaya sauraranta ba yayi gaba abunsa....... Koda haulat ta kira bariki tana fad'a mata bariki tace aiki godema Allah da kika fad'a mishi Indai har so gaskiya ne zai dawo, sannan zunubin da kika aikata keda mum dinshi Kinga saiku nemi gafaran Allah tunda kince min kin daina yanzu ,

Bariki taci gaba

Please Login or Register in order to submit comment