Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinyar ba domin y'ar iska ce....... Ganin yanda babanshi ya dage, sai yaron Ya daina musu komai dama iyayen ba masu karfi bane, yaron ke musu komai tunda yana aiki,...... Toh Kunga irin matsalolin dake faruwa, a sanda naji wannan labarin Nayi takaici Sosai, ai iyaye iyaye ne, yaka mata mu dinga hakuri dasu, mu muna ganin mune akan dai dai, haka suma suke gani sune akan dai dai, in kayi hakuri kabi umarnin su, kasan kwana nawa za suyi a duniyar?? Koko saika rasa su zaka Fara kuka dayin dana sani?? Wlh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai basa raye, sai munyi hakuri da iyayenmu sau da yawa kana ganin abunda yake dai dai kuma kowa yasan dai dai ne amma su sai suce sam, in mutum ya duba Aida basa haka, yanzu harda girma daya kamasu sai yasa suke irin haka, Idan mutum yana girma tunaninshi yana kara canzawa...... Idan har yaro yana tuna haka ya kamata ya dinga hakuri da iyayenshi, sannan abunda kama iyayenka kaima haka naka za suyi maka shairi ko khairan, sannan Indai kai burinka kuntata ma iyaye bazaka taba ganin haske ba a rayuwa..

Mum tace hakane, Allah yasa mu dace

Mai martaba ya amsa da Ameen, tare da fad'in zan tura aje a nema masa auran yarinyar cikin satin nan insha Allah, saiku Fara shiri

Mum tayi y'ar murmushi tare da fad'in Allah ya bada Sa'a zamma Yarima albishir

Dariya Mai martaba yayi tare da fad'in dan nema ba, Ashe tun a mafarki yake ganin yarinyar ikon Allah.

Mum tace Wlh nima nayi mamaki, Allah dai yasa abokiyar zama ce.

Mai martaba yace lallai soyayyarsu had'in Allah ne, duk Wanda yace zai shiga tsakani akwai matsala

Mum tace hakane, tayu rabo ne na kusa tsakani sai yasa ya kasa hakuri, kuma rabo na kisa

Mai martaba yace hakane, Allah ya shige mana gaba.....



Mai martaba yasa an tura gidansu bariki, inda su waziri suka je, kuma babu laifi su waziri Sun yaba da irin gidan tarbiyan da bariki ta fito, domin tunda Yarima ya fad'a mata ranan da za suzo bariki ta hayo wasu mutum biyu Sunan sune y'an uwan mahaifinta, sannan duk ta tsara musu yanda za suyi.

Koda waziri yayi maganan sadaki akan nawa zasu yanke

D'aya daka cikin kawun Bariki na karya yace dubu hamsin ya isa, domin karancin sadaki shine albarkan aure,

Waziri yaji dad'i Sosai domin ya gano gidan mutunci Yarima yake neman aure sannan ba masu kwadayin abun duniya bane, duk da ya gansu talakawa kuma ko yanzu a sauron gidan suke zaune, Ma'ana a zaure.

Nan take Waliyan Yarima suka biya sadaki, dubu hamsin tare da K'ara million d'aya suka ce wannan kaman matsayin kyautatawa ne, tunda iya abunda suka yanke shine na sadakin,

Dakyar iyayen bariki suka amshi kud'in, domin cikin mutanan Yarima sunce gidan sarauta in sun bada Abu dole ake amsa, ba'a miyar musu. Sannan an tsaida rana nan da wata biyu

Nan dai akayi addu'a tare da tashi kowa Ya wuce.....

Cikin Wanda sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma'ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi magana Mai Kyau akan gidansu bariki 🤔 ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take?? Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za muji zamu gani....

Koda su waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad'a mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad'amai sai dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan, kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad'in sai dai abunda ya kara burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun duniya

Mai martaba yaji dad'i Sosai, tare da fad'in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su koma, wannan kyauta ce daka gareni

Waziri yace an gama godiya suke .

Bariki bayan magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan, nan suka bata kud'in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu. Tafiya sukayi suna godiya.

Kallon abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau

Yace Sosai kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had'asu, ina tsoran ranan da asiri zai tonu

Bariki tace karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.

Yace dakyau tare da fad'in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure

Bariki tace dagaske kakeyi?

Yace dagaske nake Wlh

Bariki tace Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu ai zan had'a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada

Yace ina godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne

Dariya bariki tayi tare da fad'in wannan haka yake.

Yarima Aliyu yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta sameshi a mota

Yarima kallonta yayi cikin jin dad'i tare da fad'in amaryata

Murmushi tayi cikin jin kunya tare da gaidashi

Amsawa yayi tare daja mata hanci, yace am so happy today

Kallonshi tayi tare da fad'in happy for wht?

Yace soon zaki zama tawa ..... Oh na manta kin ma riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki...

Murmushi kawai tayi

Yarima yace yaushe za muje kiga gininki?

Tace a'a basai Naje ba,

Yace toh ni ina son kije ki gani , ya za'ayi kenan??

Tace zan tambayi Umma inta amince sai muje

Murmushi yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??

Tace kaman me??

Yace event din da za'ayi

Shuru tayi tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su fad'ama Yarima gskya Kafin ita ta fad'amai, kai gskya a'a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi'a.....

Kamo hannunta yayi tare da fad'in, a'a ya kamata muyi koda Abu d'aya ne, muyi dinner, inaga zaifi

Tace toh amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta'ki yarda da maganansa.....

Kallonta yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud'i Kisai irin kayan da kike so, duk da za'a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki K'ara da irin naki choice din .

Bariki ido ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada dama Ayi mishi.

Sunyi fira akan in zai dawo zai Kawo Mata kud'i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata sallama ya tafi ..... Toh andai ce duk abunda akace an yishi had'e da karya komai daren dad'ewa gskya zata bayyana, zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa........




*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 16*






Bariki gida tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi tace Umma.....

Amsawa tayi da fad'in ya akayi? Yau dai Kedai shar

Bariki tayi dariya, tare da fad'in ina son miki magana Allah yasa zaki amince....

Umma din tace name fah.?

Bariki tace akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga zaifi muku.

Umma tace aure? Dawa Rufamin asiri, barni inyi abunda ya kawo ni.

Bariki tace kin fiso ki zauna babu aure??

Tace a'a ina so inyi mana inna samu dai dai ni

Bariki tace gashi kin samu

Dariya tayi tare da fad'in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had'awa??

Bariki tace shiya Aiko ni inyi miki magana, kuma naga Wlh auran shiya dace daku.

Tace hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, saiki fad'a mishi na amince

Bariki tace Alhmdlh, amma dan Allah Ayi bikin Kafin aurena..... Nan dai sukai ta tattaunawa suna cikin fira habib ya fad'o kaman an jefoshi

Bariki tace miye haka ko sallama babu

Tsaki yayi tare da fita ya tsaya a kofar d'aki yana gafaranku dai masu d'aki, tare da kuso Kai.....

Bariki tace wannan ne sallama??? Ai b....

Yace dakata Mlm, nifa ban gane miki ba, tunda Yarima ya fara soyayya dake kika koma wata iri iri, in ke kin zama ustaziya ni barni yanda nake.....

Bariki tace Allah ya shirya, ni bama wannan ba zauna kaji.....

Kallon tara saura kwata ya watsa ma bariki, sannan yace wlh Ina gab da in Tsiga miki rashin mutunci, Idan kina kaini jinsin da ba nawa ba.....

Tace Allah ya baki hakuri, zauna dan Allah

Zama yayi yana bud'e hanci wai shi a dole ranshi a bace yake

Bariki tace iyayen Yarima sun Aiko har Sun tafi

Yace haba dan Allah?? Gud'a ya saki tare da fad'in inama inada duwawu babba dana tashi nayi rawa da duwaiya guda d'aya....

Bariki dariya tayi tare da fad'a ma habib yanda aka yanke bikin nan da wata biyu

Habib yace Wlh bariki ban San mai yasa ba, ina sonki da Yarima,...

Bariki tayi dariya tace ngd kawata, nan suka shiga tsara yanda za'a gudanar da bikin da yanda za'a samo kawayen Haya duk habib yace abar komai a wajanshi......

Sannan maganan gyaran jiki irinsu dilka, maganin Mata bariki tace y'ar Maiduguri take So,da yar Sokoto

Suma habib yace duk zai Kawo, cikin satin nan dan a Fara , sunyi magana Sosai inda tabi habib suka je maraban jos domin ta Fara had'a kayanta wanda take bukata wanda bata so kuma ta bayar.....

Koda suka je sunga haulat ita da Hjy babba suna magana, ganin bariki yasa haulat ta nufi bariki Tana fad'in Indai za'aga wannan kina wajan.....

Habib yace Wlh Haulat zan miki bura uba, ban so

Tabe baki Haulat tayi tana bashi hakuri,

bariki kam wajan hjy babba ta nufa tana fad'in haka hjyta har yanzu fushin ake dani?.

Hjy babba yace kyaji dashi, ni Kinga karki batamin rai yanzu da yamman nan

Bariki tace haba hjyta kiyi hakuri mana

Hjy babba yace Wlh bariki kina bani mamaki, da kyanki da kuruciyarki da lafiyanki, amma kice zaki aure, keda ake rububinki haba bariki

Bariki tace hjyta adai yi hakuri

Hjy babba yace ya wuce yana tabe baki

Bariki tace godiya nake tare dayin gaba ta nufi d'akinta.....

Tana cikin had'a kaya haulat tazo, ganin bariki nata aikin had'a kaya yasa haulat tace badai bikin yazo ba??

Bariki tace eh Wlh, Kinga wata biyu aka sa, gwara in fara had'a kaya, in kyautar dana kyautar wa inbar na Bari

Haulat tace hakane, ni har yanzu ba'a fad'amin dan wani gari bane ko sunanshi

Bariki tace saurin Mai kike ki jira koma Waye zaki gansa in lokaci yayi

Haulat tace Allah ya kaimu, nan ta Fara taya bariki had'a kaya, haulat ta d'auko wata Leda nan kayan suka zube dan ledan ya fashe, Aiko ayabar roba suka fito...... Haulat d'auka ta farayi taga har guda biyar tace bariki dama kina dasu?? Ah ba banza ba kika daina harka da maza ba, ashe kina da abunda yake d'ibe miki sha'awa

Bariki kai ta girgiza tare da cema haulat ki d'auka duka na baki, ni ban taba amfani dashi ba, yanda aka bansu haka na ajiyesu dan banda abunda za suyi min

Haulat ta dinga godiya tare da fad'in amma wanda ya baki yasan kina son babban ayaba tunda harya baki....

Bariki tace Alh madu Yaban dan iskan tsoho, ci gaba da had'a kayanta tayi harta gama taba haulat kyautan kayanta da yawa.

Haulat tana ta mata godiya duk yanda haulat taso bariki ta fad'a mata wa zata aura amma bariki ta'ki Tadai fad'a mata dan gidan sarauta ne, abunda kawai bariki ta fad'a mata kenan..........





A kwana a tashi babu wuya wajan uban giji, bariki ta gama istabra'i, sannan iyayenta sunyi aure, mai martaba ya siya musu Gida Mai kyau 4bedroom a u/kanawa inda anan iyayen nata na Bariki suka tare, sannan bariki tace ta bar musu gidan halak malak, domin suna Mata aiki yanda ya dace, bariki ta K'ara kyau da haske domin ana mata gyaran jiki Sosai.....

Yau bikin bariki da Yarima baifi kwana Goma ba, Yarima yanzu ba kullum yake zuwa wajanta ba, domin aiki sunyi mishi yawa, ga hidiman biki, gana asibiti ga fitinar zinatu, abubuwa sunyi mishi yawa Sosai..... Yana office ya Gama duba patient yaji yana bukatar ganin Zainab dinshi dan haka ya tashi ya nufi gidansu, wanda yanzu in yazo ciki yake shiga dan akwai falon ba'ki a gidan, kiran Zainab din yayi yace ta sameshi a waje basai y'a shigo ba.

Fita tayi inda ta sameshi a mota ta bud'e ta shiga tare da gaidashi

Mai makon ya amsa sai yace Kai my princess Kinga yanda kike K'ara kyau kuwa?? Gskya ana gyaramin ke dakyau,

Murmushi tayi cikin jin kunya sannan tace Kai Yarima wani kyau nake karawa?? Tayi maganan a shagwabance

Yace Zona nuna miki tare da janyota jikinshi, wani irin kamshi ne ya daki hancinshi Wanda tunda ta shigo yake ji, amma daya janyota jikinshi sai yaji kamshin ya fito Sosai, gaba d'aya yaji jikinshi ya fara weak domin kamshin turaren yasa jikinshi ya fara yin sanyi..... Itama ta gefenta wani iri take ji domin maganin da ake bata ya tsumata Tana matukar bukatar namiji amma babu yanda ta iya dole sai mijinta Bayan tayi aure, gashi yanzu Yarima yana son tada mata bala'i.... Yarima Aliyu hura mata iska yayi a fuska da sauri ta d'ago suka had'a ido peck yakai mata a goshi tare da furta I love you my princess

Da sauri ta lumshe ido

Ganin haka yasa Yarima ya kura mata ido yana kallonta tare dajin wani irin mugun sonta na K'ara shiganshi.... Jin shuru yasa ta bud'e ido a hankali idonta ya sauka cikin kwayar idonshi da yake kallon nata idon..... Dukansu wani irin yanayi mai wuyan misaltuwa suka shiga....... Karan wayar Yarima yasa ya saketa ta tashi da sauri daka jikin nashi ta koma ta zauna dakyau..... Daukan wayan yayi ya duba, ganin mai kiran yasa bai d'auka ba, zinatu ce......

Bariki kam gaba d'aya ta birkice, dan dan tabata dinnan da Yarima yayi har tana jin zuban ruwa a cikin pant dinta, lallai ya kamata Yarima ya rage zuwa, ko kuma ya daina tabata.... Domin Indai hakan zaici gaba da faruwa zata sha wuya, ido ta lumshe tasan ba komai yake sata yawan sha'awa ba sai maganin da take sha, wacce y'ar Sokoto take bata.....

Yarima ne ya Katse Mata tunani da fad'in, my princess zan gudu, bata sim yayi guda d'aya tare da cewa ta cire nata, baya son ta kara amfani dashi.....

Amsa tayi, tace toh dama tun tuni take da burin canza layi, amma tana tsoran Kar Yarima yace Mai yasa, yanzu tunda ya kawo mata, hankali kwance, sannan ya bata check na 3mil yace a K'ara gyaran jiki domin naga suna gyaramin ke dakyau......

Tace Yarima kafa ban kud'i cikin kwanakin nan, kaban a kalla wajan 7mil kace in siya kayan akwati, kuma gashi kace May be gidanku su Kawo nasu gobe ko jibi, kai kamin gashi gidanku zasu kawo, ga kud'i kuma kana karamin, gskya abun yayi yawa, ka barshi.....

Bata fuska yayi tare da fad'in in kin ciro kud'in ki zubar a bola tare da ajiye mata check din a jiki.....

Ganin yanda ya bata fuska, yasa tace Yarima kayi hakuri, wlh ba haka bane, naga hidimar tayi yawa ne Sosai, Kaga y......

Yace enough, komai na miki, kin can Canta inyi miki shi, and karki manta am your husband to be, waya kamata inyi ma Abu Inba keba?? In my life ban taba kyauta ko wani abuba a nuna ba'a soba sai ke..

Da sauri tace kayi hakuri plz na tuba, ngd Allah ya saka da alkhairi....

Jin ta fad'i haka yasa yaji dad'i..... Ba komai yasa Yarima ya bata wannan kud'in ba, sai sanin da yayi ba masu hali bane su, and y'an uwanshi zasu Kawo akwati, ance ana bada kud'i, sai yasa ya bata wannan kud'in dan iyayenta su bada tukwici... Ajiyan zuciya yayi tare da fad'in zan tafi sai munyi waya,

Tace OK

Yace kin dai ki zuwa kiga gidanki koh?

Tace Yarima saurin Mai kakeyi?? Ka Bari har a kaini mana

Murmushi yayi domin kin amincewanta yasa ya kara yarda damai tarbiya da kuma kamun kai zai aura, sabanin matan yanzu da suka lalace suke ganin haka shine wayewa, tab kunji Yarima shi'a dole zai aura ustaziya🤣

Sallama ya Mata sannan ya wuce......

Bariki gida ta shiga jiki a sanyaye lallai Yarima yana matukar sonta da yawa, hawaye ne ya gangaro daka idonta, tare da tausayin kanta yanda zai dauketa in yasan ko ita wacece......

Anata shirin biki musamman ta gefen ango, domin dai ita amarya rufa rufa take ma auran ba kowa bane ya sani, sai dai zargi da wasu sukeyi......

Ranan da za'a kawo akwati saida bariki da habib sukai hayan mata guda biyar, An kawo akwati guda ishirin da hud'u, dozen biyu kenan, kaya ne makil na Kece raini masu tsadan gaske..... Ganin yawan kayan yasa umman bariki taga 1mil yayi kad'an dan haka ta sami bariki dake boye cikin wani d'aki, tace ya kamata a K'ara kud'in nan Kinga uban kayan kuwa? Bariki kara 1mil tayi ya zama 2mil, nan aka basu kud'in tukwici, tare da abun ciye ciye da aka tanadar musu, bayan sun fito sis din Yarima Fatima tace Kai ance yarinyar talakawa ne amma har da bata 2mil, Aini ban d'auka zasu bada koda dubu d'ari ba, dariya sukayi sannan aka canza firan,

Bayan sun tafi bariki ta fito tana kallon kayan, itama Abun ya bata mamaki ganin kaya masu uban yawa da tsadan gaske, yanzu ga akwati ishirin da hudu, gashi kudin da Yarima ya bata itama ta siya guda sha biyu, duka talatin da shida.....

Ummanta ta bariki tace Kai gskya ki gode Allah y'ar nan, Yaron nan yana sonki Sosai, ji uban kaya sannan kayan d'aki yace baya bukatar komai, kai Kinji dad'i wlh

Bariki murmushi kawai tayi jiki a sanyaye, domin sai yanzu ta Fara jin tsoran abunda take kullawa na auren bariki, da tana ganin abun kaman wasa, amma tunda har taga akwati yau an kawo ta tabbatar Abun dagaske ne, d'aki tayi ta Fara rusgan kuka tare da fargaban abunda zai biyo baya..... Hmmm Allah ya kyauta dai zan iya cewa

Biki ya kan Kama amma amarya bata cikin nutsuwa kullum tana cikin fargaba, harta rame saboda damuwa, kullum bata da wani aiki sai kuka tare da K'ara tsanar rayuwar bariki........ Tana cikin wannan kukan Yarima ya kirata, da sauri ta seta kanta dan Kar ya gane sannan ta d'auka...

Gaidashi tayi

Amsawa yayi tare da fad'in ya naji muryanki haka??

Da sauri tace mura nakeyi Yarima

Yace toh fah, Allah ya sawake zan Aiko miki da magani.

Tace nasha tun dazu

Yace OK, toh ya shirye shirye?

Tace Alhamdullilah

Yace za'a Aiko miki da kayan da zaki saka a dinner sannan masu makeup za suzo suyi miki ranan, lil sis taban sa'ko in fad'a miki

Bariki tace ok Allah ya kaimu

Ya amsa da Ameen, sun d'an taba fira Kafin sukai sallama.....

Yana ajiye wayar gimbiya zinatu ta shigo, Tana fad'in yanzu Yarima saboda cin fuska a cikin gidan nawa kake waya da wacce zaka aura??? Kuka ta fashe dashi tare da fad'in haba Yarima Wlh kana cimin fuska da yawa maina maka haka da kake Yimin wannan abun??

Ganin yanda take kuka sai yaji ta bashi tausayi, rarrashinta ya farayi.....

Gimbiya zinatu ji take kaman ta tureshi Dan tsabagen kishi, Allah ya sani da badan gimbiya Amina tana kokarin hanata wani Abun ba da Wlh babu abunda zai hana tayi ma Yarima mugun tujara, amma Gimbiya Amina tace tayi hakuri ta Bari Ayi auran zata nema Mata mafita, yarda da gimbiya Amina da tayi shine yasa har take dan jurewa, amma ji take kaman zata mutu dan kishin Yarima take Sosai, bata son ganin ko wace mace kusa dashi......


Toh biki ya rage saura kwana biyu, inda a yau za'a gudanar da dinner, bariki da habib sunyi hayan kawaye Wanda sune kawayen amarya, cikin kawayen harda haulat da khairat, zuwan haulat gidan iyayen bariki yasa ta gane yanda bariki ta shirya auranta, ta gano tayi amfani da iyayen bariki, haulat ta kalli bariki tace gskya kinyi dabara, nima Ina tunanin haka zamma farhan, in samo iyayen bariki

Bariki ganin Haulat ta gano komai, yasa tace inko za kiji shawarata karki Fara yin aure da iyayen bariki, gwara ki koma Gida wajan danginki

Haulat tace Hmmm kedai kawai Ayi sha'ani,

Anyi ma amarya makeup na Kece raini, tayi mugun bala'in yin kyau, gaba d'aya makeup din da aka mata yasa ta canza, ta kara mugun kyau dama yaya balle an kara da wanka, an shiryata cikin wani tsaddan material Mai Kama da less anyi mishi dinkin doguwar riga, k'asan kuma anyishi da fad'i kaman weeding gown, an saka mata head maroon kayanta kuma golden, ba karamin kyau tayi ba, kawayenta kuma sunsa kaya red head golden, ba karamin kyau bariki tayi ba, da kawayenta, 7 dai dai aka turo motoci dan d'aukan amarya da kawayenta zuwa wajan dinner da za'ayi a cikin garin kaduna, duk y'an uwan ango suna kaduna, an d'auki amarya an nufi hall da ita, inda motarsu na zuwa na ango yazo, dan haka Yarima ya fito ya nufi motar da Zainab ke ciki, Yarima daya ganta ido ya kara bud'ewa ganin irin kyau data K'ara kaman ba ita ba, dama yasan tana da kyau gashi anyi mata makeup, lokaci d'aya kuma sai yaji yana kishin ta shiga Ayi ta kallonta, ya dad'e a motar yana nazari akan baiso ta shiga.....

Itama ta gefen amarya fargaba take, karta shiga taga Wanda ta sani, asiri ya tonu.....

Jin Yarima shuru yasa usman yazo yana buga glass din motar

Bud'ewa Yarima yayi tare da fad'in Usman gskya aje abama mutane hakuri, an fasa wannan dinner din, suci abinci kawai su wuce

Usman yace Yarima. Kasan Mai kake fad'a kuwa?? Plz Yarima ku fito mu shiga

Yarima yace kasan inna fad'a magana bana canzawa koh??

Usman shuru yayi yana nazari can yace dan Allah Yarima kayi hakuri ka duba girman Allah karka bamu kunya......

Yarima ya dakatar dashi da fad'in am telling you kayi abunda nace, wannan umarni ne.... Karan wayanshi yasa ya d'auka ganin lil sis

Yana d'auka tace Bros ku shigo mana kowa na jira, dan Allah kuyi sauri

Yace sis am sorry bazan zo ba, kuba mutane hakuri .....

Tace what? Tare da tashi ta fito waje dan taji dakyau, hango usman tayi da Yarima a tsaye da sauri ta nufesu, tana fad'in bros miye haka plz kuzo ku shiga....

Zaiyi magana tace plz koso kake ace akwai matsala ne??

Yace let people say what ever, nidai bazan shiga wannan wajan ba.

Hafsat tace bros akan wani dalili?

Yace ban son ayita Kalle min Mata, inada kishin iyali na

Hafsat hannu ta d'aura a Kai, alaman takaici, danta d'auka wani abune akayi mishi da yasa yace bazai shiga ba, motar da bariki take Hafsat ta nufa, sai gata ta fito

Ganin amarya a waje yasa Yarima ya fara yima Hafsat fad'an Mai yasa zata fito mishi da mata....

Hafsat

Please Login or Register in order to submit comment