Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata san yanda akayi Abun ya sameta ba.....

Gimbiya zinatu kam tana shiga gefenta wa'ka ta kunna Tana ta rawa cikin jin dad'i, tare da fad'in first night ya zama ranan ba'kin ciki dariya ta saki cikin jin dad'i...

Koda su Yarima Aliyu suka Iso gida, cewa yayi zai nufi gefen Zainab, duk da mum taso ya bita amma ya'ki, mum bata sa komai a ranta ba, ita a tunaninta da taji yace zashi wajan Zainab, sai tayi tunani ko abunda yayi mata d'azu yake son bata hakuri, sannan a mota ta fad'a mishi abunda Dr sukace inda badan Zainab dinba toh da zai iya mutuwa..... Fadawa na k'okarin rikeshi yace Nop ku barni, zan iya, tafiya yake dakyar harya shiga cikin falon bai ganta ba

Mum ganin ya shiga yasa itama ta wuce

Yarima bedroom dinshi yayi inda tun Kafin ya k'arasa yake jin sautin kukanta, bud'e kofar bedroom din yayi ya ganta a k'asa tana rasgan kuka a hankali cikin murya irin na marasa lafiya wanda yake jin jiki yace wannan ba kuka kike yiba..

Jin muryan Yarima yasa tayi sauri ta tashi, tare da kallonshi tana mamakin ya akayi ya dawo......

Yarima Aliyu idonshi na kanta yana mata wani irin kallo Mai Kama da I hate you, yace Zainab oh sorry Bariki......

Jin ya kirata da Bariki yasa zuciyarta ta tsinke gaba d'aya, abunda take zargi shine ya faru an fad'ama Yarima.......

Katse mata tunani yayi da fad'in how dare you....... Shuru yayi cikin kunan rai hawaye na zuba a idonshi...... Yace kin cuce ni, kin yaudareni, and ina asibiti kin kuma bina har ana fad'in da badan keba dana mutu, Mai yasa kika zo?? Mai yasa ban mutu ba, I wish da mutuwa nayi da Nasan zanga irin wannan ranan, you play with my feelings you all lies to me, you cheat me, kin maida iyayena yara kinyi wasa dasu......

Da sauri tace dan Allah Yarima ka saur......

Yace keep quiet, don't try to say anything, let me speak you cheater......

Bariki kuka take Sosai

Yarima Aliyu yaci gaba da fad'in do you think I will trust you again?? You break my trust, dan shuru yayi sannan yaci gaba da fad'in Zainab I love you from d bottom of my hrt, why are hidden your secret with me??.......

Tana kokarin yin magana yace I said don't try to speak keep your mouth shut, I don't want to listen to ol your lies again,

Bariki kuka take na farko ga Tashin hankalin halinda mijinta ke ciki, gashi ya hanata yin magana

Yarima Aliyu yace but you don't cheat me, you cheat your self, Zainab I was shock to see your pictures with different men's, ido ya rufe yana hawaye domin takaicin abunda yake fad'a ji yake kaman zuciyarshi zata buga, I never expect dat from you, Zainab mai yasa kika bata rayuwanki nawa kike samu? mai kike ji,? mai yasa kika yaudareni,? mai yasa kika boyemin gaskiyan ko ke wacece,? Zainab how old are you kwata kwata da zaki bata rayuwanki just for money?? Mai kika samu Mai kika tara ??

Da sauri tace Yarima plz ka saurareni dan Allah tana maganan tana kuka....

Yace I don't want to listen to ol your lies, komai naki karya ne your love your affection is ol a lies......

Shuru yayi hawaye na zuba daka idonshi Abun gwanin tausayiπŸ’” sanna yaci gaba da fad'in you break d trust dat I have for you, Zainab kwata kwata shekaranki nawa?? Har kin San ki samu iyayen Karya, ki aurar da kanki da kanki, you fool us, mai kika d'auki aure??? Do you think dat marriage is a joke?? Zainab I truly love but I won't accept you d way you are.....

Ihun data saki Tana bashi hakuri akan ya tsaya ya saurareta tayi mishi bayani akan duk wanda ya fad'a yayi ne danya had'asu......

Yace Yimin shuru, Habib zai miki karya ne?

Cikin razana tace habib.....

Yarima yace eh habib call me and tell me everything ol your plan...... Zainab I feel so sad when I hear d truth about you..... Nayi takaici you never love me habib told me you marry me only for money...... Shuru yayi yana hawaye can yaci gaba da fad'in kin aureni dan ki sami kud'i bakya sona Wanda kike so yayi rejecting d'inki sai yasa kika aureni danki nuna mishi kina da Wanda suka fishi..... After dat he send me your pictures matsawa yayi kusa da ita ya d'auki wayarshi ya fara dannawa nuna mata yayi yace Waye wannan hotunan tane da Alh madu, gashi tsirara ya ri'keta, sai kuma wanda tayi da Hon salis...... Yarima yace have you seen it?? Ok shima wannan it ol a lies ko shima wannan so ake a had'amu?? Jefa wayan yayi a K'asa ta fashe...... Idonshi ya rine yayi ja, ga zuciyarshi dake faman tafarfasa kirjinshi na mishi zafi........ Yace you betrayed me, who did I harm to deserve ol this punishment...... Ban kasance mazina ciba, ban taba sanadin lalacewan wata ba, why matar dana aura kowa ya Santa.......

Bariki kuka take Sosai tare da tunanin irin cin amanan da habib yayi mata, lallai don't trust anyone in life,...... Bakinta na rawa ta Fara fad'in Yarima Nasan ni Mai laifi ce a gareka dan Allah kaban dama just once I need to exp......

Yace I won't give you any chance to tell me another lies, karyan da kikayi min baya ya isa...... My heart only beat for you..... Tun a mafarki na Fara sonki, but you never love me, you hurt me alot...... You marry me for money not for love...... Ok even I, I won't accept you as my wife..... You will live here as my servant har karshen rayuwarki zaki zama mai min bauta, and I will make sure to hurt you d same as you did to me, nd I promise to hurt you, keda duk Wanda kukai wannan abun sai Nayi punishing naku, I will make sure to make you regret knowing me in ur lyf........

Da sauri ta matsa kusa dashi tare da kokarin tabashi ya daka mata tsawa tare da fad'in don't you dare try to touch me.... Karki k'ara yunkurin tabani da wannan kazamin jikin naki......

K'asa tayi da giwowinta Tana kuka tare da fad'in Yarima call me wit wat ever name you like, I deserve it, Yarima just once plz ka saurareni plz.....

Yarima yace do you think zan kara sauraran wannan karyan naki?? Harda cemin kin sauke Al'qur'ani, Wat a funny, kin dai yi hadda a bin maza.....

Tace Yarima iz true na sauke al'qur'ani tun I was 11yrs plz Yarima allow me to speak......... Hmmmmmm bari dai muga ko zai bata daman fad'a mishi ko ita wacece πŸ™†




*Plz kuyi manage I have a headache na gaji da typing din, comments dinku yasa nace bari in takura kaina inyi muku posting, ina matukar yinku Sosai da Sosai*








~MARYAM OBAM~







[9/4, 7:56 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 19*







D'an shuru yayi kanshi na k'asa yana zubar da hawaye, yana son Zainab yana mata tsantsar so, but da yasan haka take daya ro'ki mutuwa, daya ro'ki Allah ya d'auki rayuwarshi da yasan zaiga irin wannan mummunan ranan........

Jin yayi shuru yasa ta Fara fad'in Yarim......

Yace I said keep quiet, I don't want to listen to you.... Zainab even at once kin taba tunanin irin yanda zanji in nasan gaskiya a kanki???...... Kin taba tunanin ya iyayena zasu d'auki abun in suka San koke wacece??..... Zainab mai kika d'auki rayuwa?? Mai yasa kikai wasa da feelings dina?? You don't love me...... Wani hawaye mai zafi ya zubo Mai sannan yaci gaba da fad'in, tunda bakya sona Mai yasa kika aureni, Zainab inda kin fad'amin bakya sona tun Farko kud'i kike so, I will give you d money dat you want..... Basai kin yaudareni ba kin aure ni b.....

Kafin ya k'arasa abunda yake son fad'a ta Fara matsawa kusa dashi, daka mata tsawa yayi tare da fad'in karki zo inda nake..... Tari ya farayi Sosai......

Da sauri ta nufeshi tare da rik'eshi Tana buga mishi baya a hankali, tana kuka ta Fara fad'in Yarima I knw dat I have lies to you, na boye maka koni wacece Nasan wannan gaskiya ne, but Yarima abunda aka fad'a maka Akan son da nake maka karya ne..... Yarima you are my life, Yarima I love you, I can't live without you...... Tsagaitawa yayi da tarin da yakeyi tare da kallon idonta itama idonta nakan nashi...... Taci gaba da fad'in Yarima sonda nake maka shine yasa na boye maka koni wacece, saboda ban son in rasaka....... Yarima in zaka tuna nasha kuka ina son fad'ama wani abu, sometimes wani abu ya shigo koka katseni.... Yarima I try to tell you who I am but whenever I try to tell you wani abu saiya shigo, and habib yana fad'amin Indai na gaya maka gaskiyan who I am you will hate me and leave me..... Yarima sonda nake maka bazan iya juran rashinka ba..... Yarima Wlh Ina Sonka Ina Sonka, how I wish in bud'e maka zuciyata Kaga irin sonda nake maka..... Yarima plz ka amshi kaddara ta karka juya min baya kaman yanda mahaifina yayi min, Wlh Yarima Idan ka juya min baya zan iya mutuwa...... Jin haka Yarima Aliyu yayi sauri ya rungumeta dukansu kuka Yarima hawaye ita kuma kuka mai sauti....... Bariki tana rungume a jikin Yarima Aliyu ta Fara fad'in Yarima........

Ni d'aya mahaifina ya haifa......

Nice y'ar mahaifina ta Farko kuma tun daka kaina bai k'ara samun haiyuwa ba, tun ina y'ar shekara Goma mum dina ta rasu, lokacin na shiga gararin rayuwa, gaba d'aya na tsani komai dake duniya .

Mahaifina babban malami ne a k'asa nan wanda kowa ya sanshi bama kasar nan ba harta kasashen duniya, mahaifina malami ne mai sani Sosai sannan d'an kasuwa ne wanda yayi fice Sunan mahaifina sheik musa monguno...... Dan maiduguri ne, sunyi auren soyayya da mahaifiyata tun a k'asar misra suka had'u lokacin sunje karatu mum dita y'ar Sokoto ce soyayya Mai karfi ya shiga har takai da aure..... Tunda mum dina ta rasu mahaifina bai kara tunanin yin aure ba, shi yaci gaba da kula dani har Nayi hadda na sauke al'qur'ani da sauran littafai lokacin ina shekara shad'aya a duniya..... Ina karatun boko komai nawa dad dina yake min tare da taimakon Mai aikin mum dina wata tsohuwa Wanda na dauketa kaman kakata nake kiranta da Ummaa,

Dangin mahaifina sun dameshi akan ya k'ara aure, domin zamanshi haka bamai yihuwa bane, ya nuna musu babu tsarin k'ara aure a ranshi, domin bai yarda yayi aure ya bada ri'kona wajan matar daya aura ba, domin yana matukar jin tausayi na, ya nuna musu Ummaa na kula dani baya bukatar ya auri wata mata, koda zaiyi aure yace saiya aurar dani shine zai samu nutsuwa......

Haka dai suka barshi Ina shekara shabiyar a duniya Ummaa ta rasu 😭😭, naji mutuwar Ummaa Ina tunanin Nafi jin Nata akan sanda naji mutuwar mum dina, har saida na kwanta a asibiti, a lokacin na k'ara yarda ba mutuwa akema kuka ba, shakuwa ce da Sabo akema kuka, haka na k'ara fad'awa cikin gararin rayuwa tare da kadaici, mahaifina yana matukar jin tausayina Sosai.....

Bayan rasuwan Ummaa family din dad dina suka k'ara taso mishi da maganan aure, wannan karan basu mishi da wasa ba, kusan duka y'an uwanshi suka had'u harda mamanshi wato kakata tunda mahaifinshi ya dad'e da rasuwa, dole yasa ya amince ganin yanda suka nuna fishinsu akan ya k'ara aure........ Wata y'ar uwarshi aka aura Mai Mai suna Falmata wacce mijinta ya rasu ya bar mata yara biyu Mata, ganin abbana yana da kud'i yasa akace zai iya ri'ke yaran dan haka tare aka kawota da yaran, gidan dad dina dake Abuja.

Falmata Tana nuna min so Sosai, bata Bari koda kud'a ya tabani, mahaifina yana jin dad'in hakan, sannan komai zai mana tare yake mana da Kananan yaranta, haka dai rayuwa taci gaba dad dina wata rana ya d'aukeni mukaje bank aka bud'emin account, gaba d'aya kud'in da mum dina ta bari aka samin kud'i masu uban yawa a lokacin kusan 20mil banda kadarori data bari tare da gidan gona Wanda kullum cikin samun kud'i ake, komai na mum dina dad dina yace cikin account dina za'a dinga sawa.... Na nuna ma dad dina daya Bari a wajanshi amma yace a'a in ri'ke hakki nane........ Mahaifina yana nuna min tsantsar so Sosai har baya iya boye son da yakemin gaban kowa kullum magananshi ni tare da fad'in irin tausayi na da yake ji......... Dad dina yana yawan zuwa gari gari wa'azi da kasashe, ganin matarshi Tana kula dani yasa ya yarda yake tafiya yabar mata ni....


Lokacin da nake shekara Goma sha bakwai komai nawa Ya fito, kyau diri Kirjina komai nawa dai tubarkallah, Falmata duk kawayenta kana kallonsu zaka gane y'an duniya ne, sannan basa zuwa gidan sai dad dina baya k'asar........

Wata rana Ina d'aki na fito daka wanka daka ni sai towel, ina zaune ina shafa mai saiga Falmata ta shigo, da sauri na tashi Ina kokarin in d'auko abu in rufe jikina A Kai rashin Sa'a towel din ya fad'i, gaba d'aya idon Falmata na kaina, da sauri na shige towel na rufe Ina kuka domin naji kunya Sosai ranan

Ranan dai a d'aki na wuni banko le'ko ba

Washegari na fito da yake lokacin ina zana waec kuma ranan shine paper na karshe na fito zani skul cikin jin kunya, saiga Falmata tazo ta ri'ke min hannu tare da fad'in haba zainab, mai yasa tun jiya kika k'i fitowa nifa mamanki ce kiyi hakuri dana shigo ba tare dayi miki nocking ba, tunda ta ri'ke min hannu sai wani murmurzawa take kaman filo ta ri'ke, ganin zanyi lati gashi tana ta wani shafa min hannu yasa nace ummi zanyi lati.

Murmushi tayi tare da fad'in muje in rakaki mota, har mota mukaje ta sani tare da fad'ama driver ya kaini a hankali

Tun daka ranan Indai Falmata zata min Abu saita tabani ban taba zarginta da wani abu ba, duk tunani na tanayi ne saboda in saki jiki da ita, domin tunda Abun nan ya faru nake jin kunyanta Sosai, haka zatai taja na da fira ni gashi ban cika son magana ba......

Wata rana dad dina yaje saudiya umra ,ina d'aki ina karanta wani hadith daka ni sai kayan bacci a jiki na, kawai Falmata ta fad'o d'akin dama kwana biyu ban cika bari muna had'uwa ba inma mun had'u nesa nesa nake da ita domin ban son yanda take yawan tabani..... Ganin ta shigo d'akin yasa na tashi tsaye domin taban tsoro irin kallon da take min..... Nufoni tayi tana y'ar murmushi tare da fad'in baki bacci ba har yanzu?

D'an murmushi nayi tare da fad'in eh ummi.

Matsowa tayi gab dani tare da min wani irin kallo da yasa gabana ya fara fad'i....

Tace Zainab nazo ne muyi wata magana wacce nake fatan zaki amince min??

Cikin rawar baki nace eh ummi insha Allah

Shafamin fuska tayi tare da fad'in yauwa my daughter

D'an ja baya nayi kad'an

Murmushi tayi tare da matsowa kusa dani ta janyoni jikinta ta rungume har ina jiyo sautin ajiyan zuciyarta, a hankali tace Zainab plz ina son ni dake mu dinga biya ma juna bukata, Wlh sonki ya kamani dan Allah ki yarda kiban had'in Kai.....

Da sauri na fara kokarin tureta amma na kasa domin tayi min ru'ko Sosai, bakinta take kokarin kaiwa nawa ina kuka ina tureta har Allah yaban Sa'a na cije ta a hannu da sauri ta sakeni, na shige toilet na rufe, kuka nake Sosai tare da tsoro da mamaki, dama ummi tana yin mad'igo Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, ranan na tsorata Sosai tare da k'ara jin tsoran duniya..... Tunawa da irin azaban da Allah ya tanadar ma masu yin mad'igo sannan zamanin annabi ludu an kifa duniya saboda luwadi da mad'igo, yau shine ummi take aikatawa...... Tunawa tayi da sanda malaminsu yake musu wa'azi akan masu aikata mad'igo ko luwadi...... Inda yace



Mad'igo ko luwadi babban zunubi ne a musulunci, wanda za'a iya cewa Idan aka cire shirka, da kafirci to yana iya biyo baya.......

Sannan hukuncin wannan mummunan aikin luwadi ko mad'igo yana kusan dai daine da mutumin daya zagi Manzon Allah..... Kuma Kun San hukuncin Wanda ya zagi Manzon Allah.....

Manzon Allah (S A W) yace

Mafi girman abunda yake jin tsioranshi akan Al'ummata shine aikin mutanan Annabi LUD....

mai nene aikin mutanan Annabi LUD??...... shine luwadi da mad'igo Allah ya tsare.....

A wani hadisi so uku ajere Manzon Allah yana tsinema Wanda yake aikata irin aikin mutanan Annabi LUD.....

Manzon Allah (S A W) Yace....

*ALLAH YA TSINEMA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINEWA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINEMA WANDA YAKE AIKATA AIKIN IRIN MUTANAN ANNABI LUD*
Asara da tabewa ta gama tabbata akan mutumin da Manzon Allah ya jera Mai tsumuwa har guda uku akanshi.😭😭😭

Sannan Manzon Allah yace.... Duk Wanda kuka samesu suna aikata irin aikin mutanan Annabi LUD to kukashe maiyi da wanda akeyi dashi

Sai dai a cikin hadisai ana samun rauni da wanda bai inganta ba.......

Sannan malamin mu ya kara dacewa duk mai aikata luwadi ko mad'igo hukuncin shi Indai aka kamasu wasu sunce........

A jefesu wasu kuma sunce a k'ona su, wasu kuma sunce a sami bene ginin gidan sama wanda yafi tsawo a jefo su aita musu haka har sai Sun mutu😭😭😭😭😭 Wlh muji tsoran Allah, y'an mata da samari kunji wannan babban laifi ne wlh masuyi ku tuba 😭😭😭😭


Bariki kuka take Sosai tare da tsoran Falmata lallai Asara da tabewa ya tabbata akanta aikata lesbians, kuka take Sosai tare da burin Dad dinta ya dawo ta fad'a Mai......




*May be anjima inyi muku wani ko gobe da safe*








~MARYAM OBAM~
[9/4, 8:37 AM] Hayat: *BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 20*




*WARNING: DUK WACCE TAKE GROUP DINA, DAKA YAU DUK WACCE TA K'ARA TURO NOVELS DIN DA AKACE NA KUD'I NE WLH ZAN CIRETA KO WACECE, NAGA WASU ABUN NASU YANA YAWA, ANCE NA KUD'I NE NA KUD'I NE, IN BAZAKA BIYA BA KARKA KARANTA SAI KACE DOLE, NIDAI NA FAD'A DUK WACCE TA K'ARA TURA NOVELS DIN DA AKASA NA SIYAR WANE CIKIN GROUP DINA WLH SAI NA CIRETA😑*





Rannan saboda tsoro a toilet na kwana, koda asuba yayi da lambo na bud'e kofar toilet din naga bata nan, naje nasa ma kofata key,... Tun daka ranan ban cika fitowa ba, wata rana naje kitchen Zan d'iba abinci sai gata ta shigo nan gabana ya fara fad'i amma sai naji Abu daban, inda ta Fara bani hakuri Wai Wlh shaidan ne ba halinta bane, ita bata haka kaza da kaza tsautsayi ne wlh kunyan had'a ido takeyi dani, dan Allah in rufa Mata asiri Kar in fad'ama kowa....... Ganin harda kuka sai taban tausayi tare da fad'in Ummi ki nemi gafaran Allah akan ya k'ara kareki daka fad'awa halaka, sannan babu wanda zan fad'ama wa, tunda har kin gane kinyi kuskure..... Nan tai tamin godiya.......

Tun daka ranan na daina shige mata, dama ba wani shige mata din nakeyi ba, sai dai ita ce ke k'okarin jana a jiki......

Wata rana naje kitchen d'iban abinci, harna d'iba na fito naga Ummi a falo ita da wata kawarta na gaida kawar wacce ta kuramin ido kaman tsohuwar mayya,, ummi tace zainab Nayi coconut juice yana fridge Nasan kina so.....

Nace eh ummi tare da komawa kitchen na d'auko a cikin fridge, d'akina na shiga na fara cin abinci na, cikin kwanciyan hankali, nasha juice dina tunda ga lokacin ban San inda kaina yake ba, tun wajan karfe biyu na rana, nidai na farka wajan karfe goma na Safiya gabana Nata zugi kaman ansa min Reza an jimin ciwo, kafana duk ciwo suke min kaman anyi dambe dani, jiki na duk tsami, dakyar na tashi nayi toilet dan in samu inyi tsarki da ruwan zafi ko zanji sauki daka zugin da nakeji, bayan na shiga toilet Wanda ban Lura ba kawai naga jini na bimin kafana...... Abun yaban tsoro ya kuma bani mamaki nasan dai bana al'ada sau biyu a wata kuma baifi kwana Goma dana Gama ba, abun ya dauremin Kai, amma tunda nayi wanka tare da gasa wajan, nasa pad, na fito ina tafiya dakyar.....

Abunda Yaban mamaki shine yanda naga pad din bai baci ba, tunawa da nayi ance al'ada yakan Zoma mace tako wani siga, wannan abun ne yasa na basar duk da ban taba yin irinsa ba, ganin jinin baizo ba yasa nayi wanka na fara sallah

Lokacin da dad dina ya dawo daka saudiya baiko nemeni ba, gaba d'aya tunda ya dawo ya canza daka irin kulawan da yake min, da Farko Ina mamaki amma daka baya saina Fara tunanin aiki sunyi mishi yawa, gashi ina son mishi maganan karatu na, domin ni saudiya nake son zuwa karatu ban son inyi a k'asar nan...... Wata rana naje d'akinshi na sameshi akan maganan karatu na, ya nuna bai yarda inje wata k'asa karatu ba, nai k'okarin in nuna mishi irin burina na son zuwa can fad'a ya bini dashi abunda bai taba min ba a rayuwa, kuka nasa ganin haka Ya fara rarrshi na akan inyi hakuri baya son yayi nisa dani ne, haka yaita rarrashi na, duk da ina Lura da irin canza min din da yayi Sosai.......

Wani Tashin hankali da damuwa daya rufeni shine rashin ganin al'ada dina harna wata biyu, ga nonona suyi ta faman min zugi da rad'adi, gashi sun k'ara girma na k'ara wani haske ....... Gashi gaba d'aya turare na da nake masifar so naji suna min wani irin wari, gaba d'aya na zubar nace hala sunyi expire ne, nasa driver yaje ya siyomin wasu irinsu ,shima dai naji warin yakeyi, abun bada ka nan ya tsaya ba nida bani da wani cin abinci Sosai amma minti Goma na fara jin yunwa gashi ci kaman jaka...... Duk wannan abunda ake ciki Dad dina baya k'asar yana Ghana.

Wata rana na fito ina zazzabi shima dakyar na fito na nufi kitchen dan naji yunwa na neman kasheni, ina zuwa falo Nayi d'akina da gudu Ina amai domin warin turaren wutan da aka sa a falon ji nayi kaman warin jaba...... Ina cikin amai saiga ummi da kawarta sun shigo suna fad'in sannu maike damunki bari in kira Dr, ban damu ba dama ina da bukatar ince a kira family Dr dinmu ta dubani domin dad baya Bari maza na dubamu...... Dr tazo tana tamin tambayoyi ina bata amsa Kai tsaye tace bari ta d'iba jini na, na mi'ka mata hannu na ta d'iba, tace zata koma tayi gwaji inta gwada ta gani zata Aiko da magani.....

Bayan Dr ta fita na koma na kwanta ina jiran a kawo min magani, ina cikin bacci naji an bugo min kofa da karfi, tashi nayi inga ko Waye dad na

Please Login or Register in order to submit comment