Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne

Mai martaba shuru yayi cikin jimami da takaici, Amma babu yanda ya iya, wannan abunda ya sameshi kaddara ce.

Yace hafsat gashi Umar ya rasu, yanzu kina tunanin zaki sami wanda zai aureki, Bayan kin bata rayuwarki?

Sheik musa monguno yace mai martaba, yanzu ka gama bayani akan hakuri da dangana, da kuma d'aukan kaddara, kayi hakuri, ka cinye wannan kaddaran taka kaima.

Mai martaba yace hakane, Allah yasa mu dace, zan nemi iyayen umar din muyi magana dasu

Kallon gimbiya zinatu yayi sannan yace zinatu kinyi matukar bani mamaki, kin San bala'in dake cikin aikata mad'igo kuwa? Bariki kiji daka aikata mad'igo gara kayi zina duk da shima babban bala'i har gwara mai aikata zina akan mad'igo Bari kiji illar dake cikin zina kawai Kafin muzo wajan mad'igo

Mai zina mace da namiji akace ayi musu bulala d'ari, kuma kada aji tausayinsu akan bin hukuncin Allah, Indai kayi imani da Allah da Ranar lahira, sannan ana son jama'a mumunai su halarci azabar da za'ayi musu, wannan in saurayi da budurwa ne wanda basu da aure.

Masu aure kuma mace kona miji jifa ne.

Manzon Allah (S A W) Yace:
Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina sai an cire mishi imani... Wa'iyazubillah yanzu Idan kana aikatawa Allah ya d'auki rayuwar mutum kunga ya mutu a kafiri Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, yarima yasa mu dace .

Yace zina ta had'a dukkan sharri gaba d'aya, zina bala'i ce babba, tana haifar da bala'i Mai girma, Tana sa rashin tsoran Allah, tare da haifar da cututtuka da mutuwar zuciya, Tana sa zuciyar mutum tayi ba'ki da tsatsa ,tana sa mutum kullum ya jishi cikin damuwa da rashin kwanciyan hankali, sannan tana haifar da talauci, da zubewar mutunci, mazinaci dukiyarshi bata albarka, saboda kullum yana neman mata yana basu, Suma matan basa iya tara dukiyar saboda suna ganin wani zai basu, a haka za suyi ta zama har su daina samu, kowa ya'ki taimakon su.

Manzon Allah ( S A W) Yace mutum bakwai Allah ya tsine musu, kuma bazai kallesu da rahma ba ranan Al'Qiyama zaice musu ku shiga wuta Innalillahi'wa inna ilaihirajiun..

Mai yin zina da dabbobi
Mai yin luwadi da mad'igo
Wanda akeyi dashi
Mai yin zina da uwa
Sannan kuma yayi da y'arta
Mai yin wasa da al'aurarta
Ko maiyin wasa da gabansa
Masturbation kenan

Zinatu cikin kuka ta Fara fad'in Wlh shekaran jiya na fara wannan mummunan abun, da masturbation nakeyi Ashe shima babban laifi ne, wayyo Allah na tuba

Mai martaba yace
Yana d'aya daka cikin laifukan da mutanan Annabi LUD suka aikata, sannan an ruwaita duk maiyin haka Indai harya mutu bai tuba ba zai tashi ranan alkiyama hannayenshi d'auke da ciki

Yarima Aliyu yace Abba sannan duk maniyin da aka fitar dashi da gangan baya fita gaba d'aya wanda ya rage saiya daskare ma mutum cikin mara, sannan yana sa rashin haiyuwa wannan daskareren maniyin yana kashe kwayoyin hallita daga jikin namiji ko mace, sannan likitoci sun k'ara fadada bincike akan hakan yana haifar da mugayen cutuka kamar haka
Saurin yin realising mutum nan da nan yaji ya Kawo, Yana saka raunin ido, mutum Idan yanayi zai iya rasa idonshi har abada, yana sa mutum yawan mantuwa, raunin al'aura, wannan y'ana d'aya daka cikin abunda masu wasa da yatsa ko masu aikata mad'igo yake haifar wa, bance duka ba sai yasa yanzu mata yawanci suke fama da rashin haiyuwa, wata ita lokaci ne baiyi ba, wata kuma tana aikata mad'igo Wanda maniyin daya fita sauran ya daskare mata a jiki, Abba tunda na Fara aiki a asibiti Ina had'uwa da abubuwan al'ajabi da dama sai dai muce Allah ya shirya ya ganar damu hanyar gaskiya.

Mai martaba yace zinatu ana son bawa koda yace ya tuba, yayi tuba na tsakani da Allah yanda bazai K'ara aikata wannan mummunan aikin ba

Allah gafurul rahim ne, Allah mai yafiya ne ga bayinsa, Allah yana son bayinsa masu tuba.

Zinatu ta kalli Yarima tace dan Allah Yarima kamin rai karka ce zaka rabu dani, wlh Ina Sonka, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, Yarima Ina Sonka dan Allah kayi hakuri.

Yarima Aliyu shuru yayi yana nazari, can yace zinatu Allah ya sani bazan iya zama ina kallonki da wannan abun ba, domin duk macen da zatai sha'awar mace y'ar uwarta, Toh kallon hoto take ma mijinta

Da sauri mum tace Aliyu kayi hakuri ka d'auki komai yazo maka a matsayin kaddara, lallai Kaga jarabawa, Allah yasa daka wannan sai jin dad'i,.

Yarima Aliyu wani hawaye ne mai zafi ya fito mishi tare da fad'in ya zanyi mum? Babu yanda zanyi tawa kaddaran kenan sai hakuri, Allah ya bani ikon cinyewa, zan zauna da Mata na zan basu dama na biyu, Indai zan yafe ma d'aya dole In yafe ma d'aya, amma daka ranan da suka k'ara aikata wani aiki irin wanda sukayi, bazan iya d'auka ba, amma d.....

Shuru yayi yana kallon Bariki yace mum dole In k'ara aure,

Da sauri Bariki ta taso ta nufeshi tare da fad'in Wlh ban yarda ba, tama manta suwaye a falon saida taji dariyan su sannan taji kunya tare da barin falon da sauri, ganin harda gudu takeyi yasa Yarima yabi bayanta da sauri Karta illata mishi unborn child dinshi, dan yaga kaman ta manta tana da ciki, kuma ance tana bukatan bed rest, shine take wannan gudun.

Bata tsaya ba sai cikin gefenta, a bedroom ya sameta ta kwanta akan gado tana sauke nishi, d'agota yayi tare da fara fad'a kin manta bake d'aya bace Zainab har kike wannan gudun.

Kuka ta sakar mishi da karfi tare da ihu Tana fad'in na shiga uku.....










~MARYAM OBAM~
[9/11, 11:22 AM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*








~MARYAM OBAM~





~MARYAM OBAM~



*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 28*




*LAST PAGE*🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚




Ido ya 'kura mata yana kallonta, ganin yana kallonta ya'ki cewa komai yasa ta k'ara sakin wani ihun tana kuka, zama yayi akan kujeran bedroom din dake d'akin, yana kallonta yana murmushi.

Ganin haka yasa ta Fara fad'in bazaka bani hakuri ba? Bazaka ce inyi shuru ba? Sai kuma ta k'ara sakin kuka, ganin har yanzu bai taso ba yasa taci gaba da kukan tana fad'in Dad d'ina zanbi in tafi tunda an gaji dani.....

Yarima ri'ke kirjinshi yayi tare da d'an sakin k'ara, da sauri ta k'arasa wajanshi cikin tashin hankali, tana fad'in Yarima maiya sameka? Har yanzu yana maka ciwo ne,? Gaba d'aya ta rud'e Sosai, tace bari in kawo maka ruwa, tana k'okarin tashi ya kamo hannunta, tare da janyota jikinshi ya kashe mata ido tare da fad'in how far?..

Dukan wasa takai Mai, a hankali yace ah banda lafiya fah.

D'aure fuska tayi tare da fad'in Yarima Mai yasa kake min haka? Kaga yanda hankalina ya tashi kuwa? Nasha dagaske kana jin zafi plz karka k'aramin irin wannan Wasan plz Yarima.

Murmushi yayi tare da fad'in ina son sanin wani abu ne, and kuma na sani yanzu

A hankali tace mai kake son sani?..

Murmushi yayi tare da fad'in kina tsoran kiganni cikin damuwa ko ciwo, taya zaki iya barina? Ai nasan bazaki iyaba

Murmushi tayi tare da fad'in Yarima koda na minti d'aya bazan iya barinka ba, sai dai Inba mutuwa bace ta rabamu ta k'arasa maganan tare da zubar da hawaye.

Yarima Aliyu goge mata fuska yayi tare da fad'in, koda mutuwa zata zo, nafi son ta Fara d'auka na

Zainab tace Yarima kana tunanin inka tafi niya Zan kasance, nafi son mu mutu tare, rungumeta yayi tare da fad'in I love you

Lokaci d'aya tace Yarima

Yace ina ji my princess

Tace maganan k'arin aurenka Wlh zuciya na zai buga

Dariya yayi tare da fad'in inya buga zan baki magani

Tace Yarima dagaske nake fah

Yace keda Nasan ba wani sona kike ba, gwara in auro y'ar budurwa yar shekara Goma sha d'aya......

Kuka ta saki tare da fad'in dama Nasan abunda ke ranka, kana son samun budurwa, Yarima kaddara ce ta fad'amin, na rasa budurcina ba tare da sani naba dama Nasan dole kayi sha'aw..... Hannunshi yasa ya toshe mata baki, idonshi na cikin nata yace kina magana ko tsayawa ki huta bakya yi, za tayi magana ya k'ara rufe Mata baki tare da fad'in dnt say anything my princess, ku biyu kun isheni rayuwa, ina dake wace mace Zan kalla balle inyi tunanin aurota, wasa nake miki Yarima naku ne ku biyu.

Wani irin murmushi ta saki mai d'auke da farin ciki, Hancinta yaja tare da fad'in oya muje in miki wanka sai ki kwanta kin San yanzu an baki bed rest, so komai bazaki dinga yiba sai dai ayi miki, Kafin jikin ki yayi kwari, matsawa yayi kusa da kunnanta yace nima Ina bukatar matata but baby d'ina ya hana, dole in hakura har sai kinyi sati biyu, amma gskya zan cutu da yawa.

Zainab uhm kawai tace tare da nufa toilet da sauri yabi bayanta yana fad'in bazan bari kiyi wanka da kanki ba, kar a tabamin lafiyan baby.





***********
Ranan da habib ya tafi duk inda yake tunanin Bariki zata je, yaje amma bai ganta ba, dan haka dole yasa ya koma domin yace May be bata shigo kaduna bane, amma yasan dole ta dawo tunda bata da kowa a zaria, tunda anyi mata saki uku, da sauri ya d'auki waya ya kira wanda ya bashi labari inda ya k'ara shaida ma habib Zainab tabar gidan.

Koda Hjy Umaima ta kira ya fad'a mata bariki bata dawo kaduna ba, tace tana ganin zata shigo kaduna din da kanta sai su nemo ta, ikon Allah kunji jaraba.

Hjy habiba tayi mugun shiga damuwa domin harta rame Sosai, d'anta gaba d'aya ya tsaneta, wanda a halin yanzu ta gwammaci daya auro haulat wacce ta gama sanin sirrinta ta kuma ta cita, ace yau d'anta ya aurota wannan babban abun kunya da Tashin hankali da kwamacala Ina zata kaishi, dan haka ta yanke mijinta yana dawowa zata Sanar mishi.

Kaman yanda hjy habiba ta yanke ranan da mijinta ya dawo daka tafiya, saida ta Bari lokacin kwanciya ta shiga d'akin mijin Nata da rigan bacci inda ta sameshi yana danna system, zama tayi a kusa dashi.

Yace lafiya kuwa, yau naga gaba d'aya kaman baki da lafiya, wai Mai ke faruwa ne??

Hjy habiba hawaye ne ke zuban Mata a fuska tare da shesshe'kar kuka, ta Fara fad'in dan Allah ka yafemin Wlh Ina tsoran Sanar dakai abunda na aikata, na cuci kaina da kaina

Jin haka gaba d'aya hankalinshi ya dawo kanta, yana kallonta tare da fad'in habiba maiya faru?

Tace ina son kamin kyakyawan fahimta, na kasance Ina cin amanarka cikin kuka take maganan

Jin abunda ta fad'a da sauri yasa ya tashi yana mata wani irin kallo, cikin kuka taci gaba da fad'a mishi irin abubuwan data aikata, tun sanda take neman maza harta dawo hulda da Mata.

Innalillahi'wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, zama yayi tare da zabga tagumi, alaman yama rasa abunda zaice mata, baka jin sautin komai saina 'karan Ac da kuma sautin kukan hjy habiba, saida yayi wajan minti Goma Kafin ya d'ago ya fara magana kaman haka, lallai zina mugun alkaba'i daka shirka zina zai biyo baya cikin manyan laifuka, sai yasa Allah (S W A) Yace kada ku kusanceta, saboda munin laifinta, sai yasa akace Idan Matar aure tayi zina kona mijin auren da yayi zina hukuncin jifa ne a kansu, idan kuma saurayi ko budurwa tayi zina a musu bulala d'ari.

Bayan kinyi zina kin had'a da mad'igo, har d'anki ya kamaki, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, kin aikata zunubi mafi girma y.......

Cikin kuka tace dan Allah ka yafemin, ko Allah Idan mukayi laifi muka tuba yana yafe mana, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, sannan ni mace ce ina da bukata tare da sha'awa, yau rabon daka kulani wani abu ya shiga tsakaninmu harna manta, burina bawai Inci abinci bane ko sutura a'a ina da bukatar hakki na, tunda Nima mutum ce, da farko Ina zaune dakai saboda kana da dukiya Kar ince ka rabu dani ban San wanda zan aura ba, ganin ban son in rasaka yasa na Fara aikata zina, ganin zaka iya kamani yasa na Fara neman mata yanda koda kazo Kaga mace bazaka zargeni ba Dan Allah ka yafemin.

Jikinshi yayi sanyi lallai shima yana da laifi Sosai, ko yace shine mai laifi ma gaba d'aya, yau zai iya cewa rabon da yayi wani abu da ita yakai wajan Wata biyu ko fiye da hakan ma, lallai shine mai laifi babba, bawai kaba mace kud'i ko wani Abun jin dad'in rayuwa ba, tana da bukata, babu abunda nasa sai business da neman kud'i, bani can k'asar yau bani can, bani da lokacin iyalina Kai gaba d'aya nine ma Mai laifin, jikinshi yayi sanyi Sosai, duk da yasan shi ba wani tabuka Abun arziki yake a gado ba, amma yasan inda yana biya mata bukata koda yaushe bazatai marmarin wani ba, ko kad'an. Kallon hjy habiba yayi tare da fad'in na yafe miki duniya da lahira, sai kiyi tayin istigfari tare da neman gafaran uban giji, domin kofofin tuba a bud'e take ga wanda suka tuba, Allah mai gafara ne ga bayinsa Indai sunyi tuban tsakani da Allah.

Sannan maganan auran farhan da haulat babu fashi sai ki Fara shiri, wannan shine hukuncin Mai sabon Allah, gashi Allah ya jarabci d'anki da yarinyar da kukai lalata da ita.

Hjy habiba kuka take Sosai, lallai tasan wannan jarabta ne, da wani ido zasu dinga kallon juna ita da sirikar tata? Kai kai kai matar d'anta Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, lallai taga ishara, amma babu yanda zanyi dole In amshi kaddara domin bijire ma Abun in Allah yasa akwai rabo Zan iya rasa raina akai, bai kamata inyi jayayya da abunda uban giji ya tsara ba.

Hjy habiba ta amince Ayi auran farhan da haulat, Amma kullum tana cikin tunani irin kallon da zasu dinga yima juna

Hjy Umaima ce kwance ita da jamcy, suna ta faman cin juna, tare da tsotse tsotsen iskancin su, Bayan sun gama ta kalli jamcy, tace Kai kin tsallake Rijiya da baya, jamcy tace ai yaron hjy habiba ko dan iska, sai yasa ni yanzu inba keba bana yarda Inbi ko wace mace gida, sai dai ta Kama mana hotel, wayan hjy Umaima ne yayi k'ara d'auka tayi taga habib ne, ban San mai yace mata ba, naji tace dagaske Bariki ta koma gidan mijinta? Ban San amsan daya bata ba, naji tace ka tabbata malamin aikinshi nayi? Toh karka damu gobe da safe zan tawo kaduna.

Kaman yanda hjy Umaima ta tsara zuwa kaduna hakan ya faru, ita da jamcy suka Kama hanya, aiko sun zo wajan jere wata babban mota ta bugi nasu, nan motarsu ta Fara kifawa tana juyawa, motar ta bugi wani dutse ta tsaya a wajan, nan mutane aka taru tare da kiran police da ambulance, aka fara k'okarin ciro su hjy Umaima, amma koda aka ciro su hjy Umaima rai yayi halinshi, driver dinma shima Allah ya mishi rasuwa, jamcy ce take numfashi itama rai a hannun Allah, ko Kafin su k'arasa asibitin itama Allah yayi mata rasuwa, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, kai rayuwa ba komai bace, hjy Umaima ta fito da niyan shairi zata wajan boka, zata ta aikata shirka, gashi Allah ya amshi rayuwarta, ba tare data nemi gafaran Allah akan laifin data aikata ba, kai duniya ba komai bace, sai dai Allah gafurul rahim ne, ba'a shiga tsakaninshi da bayinshi, Allah kasa mu cika da imani yasa muyi kyakyawan karshe.

Lokaci kad'an labarin rasuwan hjy Umaima ya bazu ko ina, hjy habiba taci kuka Sosai, koda labari ya riski habib budan bakinshi yace za'a sha kwairi domin an aikata Abun tsiya, Hmmmm Allah ya kyauta, mutuwa dai ance wa'azi ce, Amma habib ko alaman nadama babu ko tausayawa alaman yayi nisa.

An fara hidiman bikin haulat da farhan, Zainab taso taje amma Yarima ya hanata, dole ta hakura, anyi bikin farhan da haulat lafiya inda suka tare a sabon gidansu, haulat tana bama hjy habiba girma Sosai, hjy habiba tun tana d'ari d'ari harta dan saki jiki, sai dai abunda suka aikata kullum yana damunta Hmmmm Allah yasa mu dace, wannan abun kunyar har Ina





********
Bayan wata shida Hafsat ta haifi d'anta namiji santalele Mai kyau, wani ikon Allah Sai yaron yayi sak babanshi Umar, ranan hafsat taci kuka sanda taga yaron, iyayen umar suma sunci kuka, nan aka ma yaro huduba da Umar sunan babanshi.

Yarima Aliyu sun tare a gidansu na kaduna, Cikin Zainab yayi girma haiyuwa yau ko gobe, tana zaune a falo daka ita sai wata doguwar riga irin ta roba dinnan domin kayanta basa shigarta, irin rigan da take sawa yanzu kenan, kanta babu d'ankwali, tasa kankana a gaba tana ta sha, daka gani cikinta ya cika amma sha takeyi tana nishi kaman dole, Yarima ne ya shigo cikin falon kallonta yayi ya girgiza kai yanda take tusa kankana din, d'auke plate din yayi yana fad'in oh my princess ki barshi haka mana,

Tace Yarima plz ka bani insha, yace Nop ya isa haka, d'agota yayi tare da fad'in bari in gaisa da baby d'ina, tsugunnawa yayi tare dasa kunnenshi a cikinta, dariya ta saki Tana kallonshi

Lokaci d'aya ya fara magana hello baby, is ur Dad, wen r you coming to d world?

Bariki dariya tayi tare daja baya tana k'okarin zama, lokaci d'aya ta saki kara mai sauti tare da ri'ke cikinta, da sauri Yarima ya nufeta, ganin yanda takeyi yasa ya nufeta da sauri tare da ri'keta, kamata yayi suka fita yasa ta a mota, dai dai lokacin zinatu ta shigo gidan ganin haka itama ta fito daka mota ta bisu, direct asibitin Yarima suka nufa, suna zuwa akai labour room da ita, Yarima saboda sauri ko kayan haiyuwa ba'a d'auko ba, dole zinatu ce ta koma ta d'auko, Yarima shi kadai Ya shiga ansar haiyuwar Princess dinshi, ganin yanda take ihu da kuka ya kasa tabuka komai, dole fita yayi ya kira wata Dr akan ta amshi haiyuwar Zainab dinshi domin bazai iya juran ganinta Tana wannan halin ba,.

Cikin minti 30 da fitan Yarima bariki ta sintibo d'anta namiji kyakyawa kaman Yarima Aliyu, sai dai farin na Bariki ya d'auko, nan aka gyara yaro da Mai jego, Yarima tunda yaji ihun jariri yasan ta haiyu amma ya kasa shiga saboda tsoro, hahahaha kunji Yarima fah shida yake ansan haiyuwar wasu amma ya kasa amsar na his princess saboda tausayi .

Saida Dr ta fito tana fad'in congratulations Dr Aliyu matarka ta haifi baby boy, saboda murna da sauri zinatu ta rungume Yarima Aliyu, tare da sakinshi lokaci d'aya, tun Kafin Yarima ya shiga zintau ta shiga Tana taya Zainab murna tare da d'aukan baby tace Kai lyk father lyk son, Shigowan Yarima Aliyu yasa ta mi'ka mishi Yaron tare da fita danta basu daman magana, Yarima kallon yaron yayi tare da fad'in Masha Allah, lokaci d'aya ya nufi gadon da Bariki take kwance hannunta ya kamo tare da fad'in sannu my princess, ganin bata kulashi ba yasa ya tashi yaje ya kwantar da baby din, tare da dawowa, yace my princess talk to me, d'agota yayi tare da zaunar da ita hawaye ta Fara, ganin haka Yarima ya rud'e ya fara tambaya lafiya? Tace Yarima gaskiya bazan kara haiyuwa ba, nasha wuya, maganan da tayi yaba Yarima dariya, suna cikin haka saiga mum da hafsat Sun zo, Yarima saida Ya gansu yama tuna bai kira ya fad'a musu ba, mum tace wato saida aka haiyu shine aka kiramu koh? Hafsat d'aukan baby din tayi tare da fad'in wow kaman bros, Zinatu ce ta kira su mum, nan itama mum ta d'auki baby din, suna cikin haka saiga Fatima yayar Yarima tazo itama, Bariki kam kunya take taji, Yarima kam gashi Abu kad'an ya janyota jikinshi ga mum a wajan, ta rasa yanda zata mishi yabar tabata dariyan Ya'ke kawai takeyi,ga zinatu itama ta shigo, ganin babu wani matsala da yamma suka dawo gida, inda Mum tace a ZARIA za'ayi taron suna, dan haka suka had'a kaya suka nufi Zaria

Shirin suna akeyi Sosai inda ranan suna Yaro yaci Sunan Mai martaba Murtala, suna kiranshi da Anan, Zainab ta samu kyauta Sosai, ga wanda babanta yayi mata gana Mai martaba gana mum,ga Wanda matar babanta tayi mata domin ya auri kanwar waziri, Mai suna aysha matar Mai hankali dason addini ba irin Falmata ba, kuma har yanzu dad din Bariki yana ri'ke da yaran Falmata, domin yace uwarsu ce ta mishi Abu basu ba, zinatu itama tayi ma bariki kyauta Sosai an kashe naira a sunan, saida Bariki tayi arba'in Kafin mum ta yarda ta koma kaduna, Bayan anyi mata gyara Sosai

Bayan hafsat ta yaye d'anta iyayen umar suka ro'ka alfarman a basu ri'kon Yaron, hafsat bata soba, amma mai martaba ya amince haka aka tafi da yaron, Mum kullum addu'arta Allah yaba hafsat mijin aure, ana cikin haka Usman yace yana son aurenta, wanda dama tun tuni yana Sonta, mum tafi kowa murna, haka aka fara hidiman biki, inda y'an uwa da abokanan arziki suka hallara, gaba d'aya y'an uwan Yarima Mata sun zo rukayya, salamatu, Fatima, inda suke ta gyara y'ar kanwar tasu, biki akeyi na Kece raini, Yarima ya hana bariki sakat dan haka ta kashe wayoyinta, gaba d'aya

Yau za'ayi dinner din bikin hafsat Washe gari a d'aura aure, Bariki tayi mugun kyau, bata yarda tabi Yarima ba, dan gaba d'aya boye boye ta dinga mishi, domin kayanda tasa ta tabbata inya ganta sai yace ta canza, saboda tsabagen kishi irin na Yarima, motar su Fatima ta shiga suka nufi hall din, inda an tsara hall din manyan mutane duk sun hallara, wayar Fatima ce tayi k'ara ta d'auka, Bayan ta kashe ta kalli bariki da Anan yake ta faman Mata rigima Wanda tuni Bariki ta yaye shi saboda da kanshi ya daina shan nono,, tace Zainab Yarima yace kije waje yana jiranki, tashi tayi ita da d'anta suka fita, ganin mutum tayi a gabanta ba kowa bane sai Alh madu, da sauri tayi baya saboda tsoro, Alh madu yace Zainab nazo in tayaki murna sannan in gode miki, wlh tun sanda kikai k'okarin cewa zaki watsa hotona, tun daka lokacin na tuba na daina abunda nake aikatawa na gane duniya ba komai bace, kuma naji tsoran Allah, mutum kaman ni yanzu babu abun daya dace dani sai dai inyi ta istigfari tare da gyara lahira ta, ngd miki Allah ya baki zaman lfya keda mijinki, mi'ko hannu yayi yana ma Anan wasa, shiko yaron dariya yayi tayi Alh madu wucewa yayi, Zainab hango motar Yarima tayi inda ta nufi motar koda taje bud'e gidan gaba tayi ta shiga, tana shiga yaja motar da gudu, bai tsaya ko inaba sai fada gefenshi Nada Wanda suke shida Zainab din ya shiga itama binshi tayi, suna shiga ya kalleta tare da fad'in har abada duk macen da tasan tayi rayuwar Bariki bazata taba canzawa ba, lallai yau kin nuna min koke wacece , mutumin dana ganshi tsirara yana manne dake shine kike magana dashi, Zainab why? Nayi hakuri na cire komai saboda ina sonki but what did you do now? Zainab gwara sonki ya kasheni da in zauna dake kina cin amana ta, amsan Yaronshi yayi tare da fad'in kije ki tafi bana bukatar ki a rayuwata

Cikin kuka tace shikenan Yarima Zan tafi naji zan tafi, amma ina son kaji wannan Kafin in tafi recording din maganan alh madu tasa mishi, tare da fad'in sanda ya fara magana na kunna recording a wayana dan nayi tunanin kana kallon mu, amma babu damuwa tunda Yarima baka yarda dani ba, zan tafi Allah yasa wannan hukuncin daka yanke ya

Please Login or Register in order to submit comment