Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne yasata sake shigewa katifar taci gaba da kukanta can taji an daina bugun wayarta ta dauki qara dauka tayi daqyar tace “hel hello Momy" “to" ta kuma cewa sannan ta tashi saman gadon ta bude mata qofar janyota tayi jikinta tace “kiyi hqr wauta ce irinta Yayanku amma nayi masa mgn bazai qaraba babu maiyi miki dole a qyaleki har Allah ya kawo miki wanda kike jira” ajiyar zuciya tayi tace “na gde Momy Allah ya qara girma" amsawa tayi da amin taja hanunta suka fito parlourn bayanan ya fita don haka ta saki jikinta sukaci abinci.


Lkc yanata turawa sababbin qalu-bale suna qara shigowa rayuwarta zamanta a cikin gdan Alh Usman ita da danta sai son barka cikin shekara goma sha biyar dinnan bata da wata matsala saita mutanen da suke damunta a lkcn ne sarki ya gama secondary School.
Yau takama asabar saboda haka yana tare da Uncle Nasir tun safe saida suka gama yawonsu sannan suka nufi guesthouse house din Prince Hafeez a zaune suka tarar dashi saman center carpet din dake parlourn ya hada kai da gwiwa yana tunani da sauri Sarki ya qarasa ya dago kansa hawaye ya gani sharkaf a fuskarsa hanu yasa ya rungume yaron kukansa ya qara qarfi shima Sarki fashewa yayi da kukan idan duk sanda yaganshi a cikin irin wannan yanayin shima sai yaji ya shiga damuwa jin qaunar abokin Uncle nasa yakeyi a cikin jininsa a hankali ya rinqa bubbuga bayan yaron da zummar rarrashin shi kansa Nasir baisan sanda hawayen tausayin mutane uku ya zubo masa ba yana tausayawa King Hafeez saboda yasan ciwon son matarsa da kuma kewar rashin haihuwa sune suke cin zuciyarsa ga dukiya har dukiya an tara babu masu cinta saidai yayita rabarwa talakawa da bitalmali matar daya data rage masa ya saketa babu gaira babu dalili wannan wacce irin rayuwa ya zabawa kansa ta kadaici oho duk inda kabi a gdan ya rubuceshi da sunan matacciyar matarsa ( I LOVE MY FARHA I MISS YOU MY QUEEN R.I.P LATE WIFE MISS YOU LOVELY WIFE)
Abinda zakayita gani kenan a duk inda kasa qafarka a gdan.


Dagowa Sarki yasa hanunsa ya fara sharewa King Hafeez hawayensa cikin rawar murya yace “meyasa kullum zan hadu dakai cikin damuwa zanganka Dady meyasa bazaka bar rayuwarka ta hutaba meyasa kaima ka hana kanka kwanciyar hankali kamar Momy na kullum itama Momy na saina ganta tana kuka ta rungume wani tsohon hoto idan na tambayeta waye a jikin hoton sai tacemin itama batasonshi ba amma tanajin sonsa a zuciyarta ina tausayawa Momy na kaima kuma ina tausayin ka Daddy ku taimakeni ku daina damuwarnan wlh kona tafi karatun da kace zaka turani Rasha bazan iyayi ba saboda zanke tuna nabaro mahaifiyata cikin damuwa sannan kaida ka daukeni matsayin kake sona da burin ganin rayuwata ta inganta kaima kana cikin damuwa Daddy inasonka inajinka a cikin jinina inajin dama ba babana ne mahaifina ba dama kaine inajin dama zan iya dauke kaddararku kaida Momyna ta zama tawa inason ganinki cikin farin ciki Daddy plz ka daina Daddy ka daina...."
Ya qarasa mgnr yana qara rungume King Hafeez shima rungume yaron yayi qamqam a jikinsa yana matso wasu sabbin hawayen masu zafin gaska ya bude bakinsa yace “inda zan iya cire Queen Farha a zuciyata da tuni na cire kodan na samawa tawa rayuwar sauqi amma na kasa Abdallah Queen Farha ta tafi da rayuwata nima gangar jikina kawai tabarmin Abdallah kuka biyu nakeyi kullum a rayuwata na rashin matata farin cikina dana rashin dana dake cikinta da nasan idan na fita daga gda Farha fita zatayi taje tayi hatsari wlh ranar daban fita ba dana zauna ta mutu a hanuna naga gawarta na tabbatar data mutu yanzu gashi dai nasan ta mutu amma kullum mafarkin ganinta nakeyi kullum nemanta nakeyi a duniya da zanga koda me kamarta ne tabbas zance Farha tace ta dawo...”


Yana mgn yana kuka mecin zuciya tashi Nasir yayi ya matso zai janye Sarki daga jikinsa yayi saurin riqe yaron yace “kabarni dashi Nasir inajinsa a cikin jinina qaunar Abdallah daga indallahi take wlh bantaba jin qaunar wani da a duniya kamar yanda nakeson Abdallah ba Nasir ka taimakeni ka barmin Abdallah na nunawa duniya shi a matsayin dana don Allah”
Hawaye Nasir ya share yace “da ace nina haifi Abdallah da babu abinda zaisa na kasa bakashi amma kash ba dana bane kuma mahaifiyar sa itama shi kadai ta mallaka matsayin da taqi aure bare ta haifi wani mutane dayawa sunason auran Hanah ciki harda ni amma taqi yarda kullum zancenta mijinta ita zataci gaba da rayuwa har ta tadda inda mijinta yake kullum mgnrta irin takace Hafeez yaron nan shine sanyi idaniyarta shi take gani taji dadi idan ka rabata dashi na tabbata saita shiga halin da yafi wanda kake ciki kai saboda ita ta haifa kai kuwa baka haifa ba naka zai zama da sauqi zaka fita juriya da dangana"


Kwantar da kansa yayi saman wuyan Sarki yace “haka ne amma Ina neman alfarmar abarshi dani a ransa kada ta rabani dashi kallonsa kadai yana samin nutsuwa” yana fadin haka ya miqe ya shiga dakinsa ya fada bathroom yayi wanka ya shirya idanunsa sunyi ja sosai saboda kukan da yaci saboda haka ya dauki baqin glass yasa ya fito kama hanun Abdallah yayi ya shigar dashi wani daki yace “saboda kai nasa aka gyara dakinnan ka shiga kayi wanka ka canza kaya akwai kaya a wadroop nakane sunfi kala hamsin ka zabi wanda kakeso kasa kazo ka rakani Emergration office inason ayi maka passport nanda kwana takwas zaka tafi kamai dakai kayi karatu kaji yarona" tsalle yayi ya rungume shi yayi kissing kuncinsa yace “yess farin uba I love it” ya fada tare da jinjina masa ya sakeshi ya fada bathroom din ya fara wankan yana fitowa ya shirya cikin wani yadi fari kalar wanda yaga King Hafeez din yasaka ya fito yana dariya suma dariyar sukayi Nasir ne yace “lallai wannan wariyar launin fata taku ta kai inda takai wato sai kukayi anko ni kuma ko oho ko?" Maqalewa yayi jikin King Hafeez yace “to kaima ai sai kayi da yayanka Nima nida Daddy na mukayi” murmushi Hafeez yayi ya sanya cump ya fara taje masa sumarsa yace “gskyrka yarona amma sumar nan asketa zaayi yau”


Da haka suka fice suna tafe suna tattana abinda ya shafi asibitocinsu har suka isa inda zasu akayi musu duk abinda zaayi musu sannan suka wucce asibitin yauma kamar kullum suna zuwa akace ita kuma Hanah ta fita King Hafeez yana mamakin sabanin da sukeyi da Hanah kullum zai shigo asibitin zaace ta fita ko tashiga emergency room ko tana Teather room kullum a haka suke samada shekara bakwai din da take aiki a qarqashin asibitinsa.





Please Comments
Share and Vote





*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻


*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿1⃣4⃣



Saida ya shiga cikin asibitin ya duba duk wani abu daya kamata ya duba hanunsa yana riqe dana Sarki har suka gama ya shiga office dinsa suka zauna inda Nasir ya nufi wani bangare na asibitin domin duba wani patient sun dan jima suna hira da Sarki yana tambayarsa abubuwan da yake buqata shikuma yaron yana fada masa saboda harga Allah Sarki jin King Hafeez yakeyi kamar mahaifinsa.


Shigowar Nasir ce tasasu miqewa suka fita Nasir ne ya dubesa yace “wato King Hafeez Hanah ce take neman dauko mana wani risky a cikin sana'armu wani bawan Allah ne yake fama da wani irin ciwon zuciya wanda yasa wani bangare na zuciyar tasa ya wuje yake fitar da wani baqin jini da ruwa me wari duk yanda zaayi dashi tun a garinsu Zamfara anyi amma abin yaci tura har Kano teaching hospital aka turashi qarshe suka rubuta mishi takarda zuwa wani asibiti dake Hydrabat saboda aiki zuciyarsa take buqata kuma baa taba irin aikin anan qasa 9ja ba, amma da yake itadin yar rigima ce ta karbeshi tace su zasuyi aikin a cikin asibitin su har hukumar kiyaye lfy ta one millions health ta turo takarda akan cewa kada muyi gangancin yin aikin da manyan asibitocin qasa suka kasayi qarshe itama ta rubuta musu cewa tabada rayuwarta da duk abinda ta mallaka fansa ga iyalansa indai ya mutu ta sanadin sakacinmu wajan aikin da zaayi masa wannan abu yana damuna"


Murmushi King Hafeez yayi yace “ai baa riqewa yaro garma Nasir tunda tace zata iya jagorantar aikin mu barta kuma da babu mai koyo da gwanaye sun jima da qarewa suma inda zaa kaishi din qarshe zakayi mamaki idan nace maka yarane masu koyan aiki zaa bari dashi suyi masa kuma ya miqe idan bama daukan irin wadannan risky din to tabbas bazamu taba ci gaba ba a rayuwar aikinmu" yana kaiwa nan ya juya ya kalli Sarki da yaketa cin cheesen sa yace “ ka qarfafawa mahaifiyar ka gwuiwa akan kyakkyawan qudurinta nikuma nayi alqawarin duk abinda ake buqata wajan aikin zan kawoshi cikin qanqanin lkc kace tayomin list na komai ta baka ka kawomin ka rabuda matsoracin uncle dinnan naka kaji kayi jajircewa irinta Momynka da Daddynka kaji yarona”


Jinjina kai sarki yayi da confidence dinsa yace “yess lovely father I love it" dariya sukayi dukkansu daidai lkcn da sukayi parking suka fito suka shiga cikin parlourn Momy ce kawai a zaune a ciki Farha na dakinta Maryam na gdan mijinta harda yaranta biyu zama yayi suka gaisa Sarki ne ya matsa daidai kunnen King Hafeez yace “Daddy nasan bakasan Momy na ba bari na kira maka ita ku gaisa ko?” murmushi yayi yace “na gde lovely Son" miqewa yayi ya shiga dakin ya tarar tana wanka juyawa yayi yace “Daddy Momy is bathing" ajiyar zuciya yayi ajiyar numfashi yayi yace “wala aibi boy Momynka bataso na ganta amma nasan komai girman gona akwai kunyar qarshe idan dai muna raye wataran zamu hadu” yana fadin haka ya miqe yayi kissing lips din dannasa yace “kayi bacci cikin aminci My lovely Son ka isarmin da gaisuwar qarfafa gwiwa ta wa Momynka zanje gda na kwanta gobe zan tafi Bauchi" shima kissing dinsa yayi suka rungume juna sannan sukayiwa juna bye ya fice da sauri ya hau motarsa ya tafi zuciyarsa cike da ciwo yanzu Farhansa tana raye da yanzu dansu ko yarsu tayi kamar Abdallah wasu hawaye ya share a idonsa yana qarajin tsanar Amnah da Hajiya Sogiji a ransa tabbas badan muguwar baqar zuciyarsu da baqin kishinsu ba da tuni shima babane da yanzu yana tare da Farhansa tana lailayashi tana shayar dashi salon soyayyarta da kulawarta gareshi” irin wadannan tunane tunanen sune suke hana King Hafeez kwanciyar hankali, yana zuwa gda ya shige dakinsa ya fada saman gadonsa ya janyo hoton Farha daya ajiye saman bedsat drower dinsa ya rungume ya kuma sakin wani sabon kuka me ciwo.



A bangaren Farha kuwa tana fitowa ta tarar da dannata kwance saman gado yanata aikin kuka matsawa tayi ta juyo dashi tace “haba My lovely Son me kuma ya faru haka har zuciyar Momy take zubar da hawaye?” ture hanunta yayi yace “ni babu ruwana dake tunda kike gudun Daddy na kullum idan yazo gdannan saiki buya bakyason ku hadu Momy meyasa hakane?”
Murmushi tayi tace “yanzu akan dan wannan abin zaayi fushi dani Sarki to kayi hqr watarana zamu hadu badaga ni bane Allah ne yake kawo sabanin tashi maza kaje ka hadomin tea a kitchen zanyi wani binkice banason musu banason surutu” miqewa yayi ya fita yana bubbuga qafa shi a dole tayi masa laifi bata kulashi ba taci gaba da abinda takeyi tasan ba kawo Mata tea din zaiyi ba saboda ta bata masa rai akan wannan mutumin daya qwallafa ransa akansa.
Zama tayi taci gaba da bincikenta sai dare sosai ta gama sannan ta fita ta ci abinci ta dawo tayi brush ta kwanta zuwa yanzu kadaici ya fara damunta sosai shekarunta sun fara nauyi 32 years ai tayi hqr shekara sha biyar babu namiji gsky ya kamata tayi wani abu miji takeso sosai.


Da wannan tunanin bacci ya dauketa washe gari da wuri ta tafi asibiti saboda tunanin patient dinta jiya ya hanata sakat tana zuwa ta dubashi ta bashi magunguna kasancewar komai ita takeyi masa da kanta sai yamma liqis ta fito daga asibitin ta nufi gdan tana shiga ta fada kitchen ta dafa Indomie ta nufi dakinta taci sannan tayi wanka ta kuma fita zuwa gdan Maryam acan Yaya Nasir ya sameta tayi kicin² taqi ko kallonsa dariya yayi ya lakace mata hanci yace “yi hqr maida wuqar yar qanwata dama General manager ne yace na isar da gaisuwar sa gareki sannan yace yana qarfafa miki gwiwa akan abinda kika daukowa kanki sannan yace kiyi list na abubuwan da ake buqata idan zai tafi Rasha kai Sarki saiya taho dasu" murmushi tayi ta bude handbag dinta ta dauko wata takarda ta bashi sannan taci gaba da hirarta da wasa da yaran Maryam ganin babu fuskane yasashi miqewa ya tafi tabisa da harara tare da jan qaramin tsaki dariya Maryam tayi tace “nidai Ina mamakin wannan soyayya taku da Yaya Hanah kawai ki yarda ayi kema kya samu Mai sosa miki gurin nan dan nasan yanzu ba qaramin susa yakeso ba” ajiyar zuciya tayi ta share hawayen da suka gangaro mata tace “Sister bazaki gane ba wlh bani naqi aure ba shine ya qini saboda na kasa koyawa kaina son wani da namiji a duniya sai mutum daya shikuma bansan inda zan nemoshi ba Maryam ya zanyi da rayuwata haka Allah ya tsaramin Maryam" bude jakarta tayi ta zaro wani tsohon hoton kati ta miqawa Maryam tace “wannan shine farin cikina Maryam shi nakeso shi zuciya ta take kwadayi amma na rasa gane inda zanganshi wlh Maryam har shiryawa nakeyi takanas na fita domin nemansa na kasa ganinshi" ta rufe bakinta daidai lkcn da Maryam ta karbi hoton.


Wata zabura Maryam tayi ta miqe tare da zaro ido waje tace “King Hafeez Hanah King Hafeez kikeso meye alaqarki dashi ina kika samu tsohon hotonnan nasa tun yana saurayi?" Itama miqewa tayi tana yiwa Maryam kallon tuhuma tace “su..sunansa kenan Maryam ina kika sanshi Maryam ina zan ganshi Maryam ki taimakeni hqr na ya qare game da bawan Allan nan bansanshi amma inajin qaunarsa a cikin jinina” sake riqota Maryam tayi tace “ina kika samu hoton Hanah tabbas wannan hoton King Hafeez ne abokin Yaya Nasir wanda yake da rukunin asibitocin QUEEN FARHA CONSULTANCY HOSPITAL, Hanah a qarqashin sa kike aiki wannan hoton dadadden hotone King Hafeez ya daukeshi ne lkcn farin cikinsa na tare dashi ba yanzu da shekarunsa sukayi nauyi ba kuma ya rasa farin cikinsa Hanah dole akwai dalilin da yasa kika sami wannan tsohon hoton ina kika sameshi Hanah?"


Girgiza kanta tayi tace “wlh iyakar gsky kenan Maryam bansan Ina na sameshi ba kawai nidai na ganshi a gurina ne tare da mahaifi na dana taba nuna muku” shiru Maryam tayi tana jinjina lamarin miqewa tayi ta dauki wayarta ta kira number Yaya Nasir ta fada masa abinda yake faruwa, cikin tashin hankali ya juyo ya dawo gdan yana shigowa ya tarar da ita zaune a qasa ta kifa kanta da kujera tanata gursheqen kuka hoton ya dauka ya zubawa ido shakka babu King Hafeez ne a jiki tun yana saurayi ba yanzu da girma ya fara shigo masa ba tsuguwa yayi a gabanta yace “meye alaqarki dashi Hanah Ina kika samu hotonsa?" Cikin kuka tace “sama da shekara sha biyar nake tare da hoton nan duk iyakar tunanina nason nasan matsayinsa a gurina na kasa tunawa kawai nidai abinda na sani yanayimin kama da dana Abdallah” kansa ne yayi wata muguwar sarawa a tsorace yake furta “ya haka me hakan yake nufi to kodai shine yayi miki fyade har kika samu cikin Abdallah shiyasa shima yakeyi masa so irin na da da mahaifi? Kai aa wannan qaryane nasani King Hafeez bashi da lfyr da zai iya bawa kowacce mace ciki to kodai dan uwanki ne Hanah meye alaqarki dashi?"


Ya fada da qarfi yana qara matsarta tanaja da baya karo yayi da center table ya fadi hakan ya bata damar surar jakarta ta key din motarta ta fice da gudu kafin ya taso har taja motar da mahaukacin gudu tayi waje tanayin parking ta fito ta shiga gdan a guje daidai lkcn da shima yayi parking biyota yayi a sukwane ta fada jikin Momy ta qanqame ta tana sake sakin wani sabon kuka me cin zuciya fincikota yayi da qarfi ya hadata da bango ya shaqeta kamar wani zararrare yace “wlh saikin fadamin alaqarki dashi kona kasheki na kashe banza Hanah meye nayi miki da zaki sakamin alkhairi da sharri meye aibina da zaki qini ki so abokina sai kin fadamin alaqarki dashi na rantse da Allah...” kyawawan maruka yaji guda biyu a kuncinsa ya saketa da sauri ya juya Daddy ne tsaye a kansu ya qara kai masa wani marin ya kauce da sauri, nunashi yayi da yatsa yace.


“Baka da hankali ne Nasir kasheta zakayi ko anaso dole ne tace batasonka da aure to dole ne ko hakan da kakeyi mata shine zaisa ta soka?” juyowa yayi ya kalli Daddy yace “amma Daddy da bata sona kuma saita rasa wanda zataso sai abokina King Hafeez fah Daddy meye hadinta dashi ina ta samu tsohon hotonsa tun yana saurayi ni tambayar danakeyi mata kenan kuma ita nakeso ta amsamin” Daddy da kansa ya gama kullewa ya kalleta ya juyo ya kalleshi ya kai dubansa ga Maryam dake shigowa yanzu matsowa tayi ta miqa masa hoton tare da basu lbrn duk abinda ya faru da abinda Farha tace tanaji game da King Hafeez, zama Daddy yayi dafe da kansa yana ambaton sunan Allah itama Momy abin ya girmi tunaninta kallon Farha takeyi kawai data keta gursheqen kuka matsawa tayi gaban Daddy ta ruqo qafarsa tace “ku yarda dani Daddy wlh bansan komai game dashi ba nidai kawai na tsinci hotonsa a cikin kayana tare dana mahaifina dana taba nuna muku abinda yasa ban nuna muku shiba saboda bansan meye alaqata dashi ba amma nasani tabbas yana kama da dana Abdallah duk sanda na kalli hoton na kalli Abdallah sai naga kamar mutum daya ne Daddy bansan ya akayi na fara sonsa ba kawai nidai na tsinci kaina ne a qaunarsa inajin kamar idan babushi bazan iya ci gaba da rayuwa ba”


“Aikuwa zaki mutu kiyi mushe Hanah saboda tabbas son maso wani kikeyi King Hafeez babu wata ya mace a duniya dake gabansa sai Farha tsohuwar matarsa data mutu samada shekaru goma sha biyar kullum ita yakewa kuka saboda ita ya kasa zama da matarsa ya saketa yake zaune shi kadai saboda ita ya kasa qara aure kullum mafarki yakeyi zata dawo gareshi bayan yasan duk wanda ya mutu baya dawowa amma so ya makantar dashi ya kasa ganewa Hanah kiyi gaggawar cireshi a ranki ki karbeni a matsayin mijinki nafi kowa sanin darajarki kuma nafi kowa tausayinki plz” yanda yake mgnr ne yasata qarawa kukanta sauti tana girgiza masa kai,



Daidai lkcn Sarki ya shigo da gudu yana tsallen murna da ihunsa ganin yanda sukayi jigum jigum yasashi saita nutsuwarshi ya matsa kusa da Momynsa ya ruqo hannunta yace “Momy meye yasaki kuka?" daukan hoton yayi ya zuba masa ido cikin rawar murya yace “Da...ddy Mom..my wal..lahi Daddy nane wannan...” daidai lkcn shima King Hafeez ya sawo kai cikin parlourn da ledoji niqi² a hannayensa yana cewa “kaga sokon yaro ka gudo kabar Daddynka da dakon kay....” mgnr ce ta maqale jikinsa ya dauki rawa ya saki kayan hanunsa a kidime ya daga hanunsa da yake rawa ya bude bakinsa da kyar yace “Qu...een Far..hanah ke...ce dama baki mutu ba...” miqewa itama tayi ta zuba masa ido tana wani irin hawaye ta fara tafiya da sassarfa zuwa inda yake shima takowa yakeyi har suka hade a tsakiyar parlourn ya cafkota da sauri ya hadata da qirjinsa ya matseta yana cewa “mafarki nakeyi Farhanah ko gaske ne kece a gabana Queen dama kina ra....” bai iya qarasawaba saboda wani jiri daya dabeshi ya yanke jiki ya fadi sumamme amma duk da haka tana maqale a qirjinsa ta saki wani kuka me gunji ta janye jikinta daqyar cikin muryar tashin hankali tace “ya sanni shima Momy shima ashe ya sanni wlh nasanshi sosai amma nakasa tuna inda na sanshi Daddy ku taimakeni kada ya mutu shine rayuwata plz Daddy” miqewa tayi da sauri ta janyo hanun Daddy da Yaya Nasir tana kuka tanayi musu magiyar kada ya mutu Sarki ne ya matsa ya rungume shi yana kuka me tsima zuciya yana cewa “kada kayi mana haka Daddy kada ka mutu ka barni don Allah Momy na ma ta sanka ka tashi Daddy ka tashi ni katashi nace Daddy....”






Please Comments
Share and Vote





*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻


*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com


Ina gdy masoyana wadanda sunka kirani domin dubani da wadanda sukayimin text da wadanda suka turomin ta wtsp dama wadanda basu sami damar yimin ko daya ba sukayimin addu'a.

Na gde!
Na gde!!
Na gde!!!
Allah ya qara zumunci🙏🏻



🅿1⃣5⃣



Daddy ne ya dauko ruwa a frigde ya bude ya tsiyaya a hanunsa ya fara shafawa King Hafeez a fuskarsa har suka samu ya fara sauke ajiyar zuciya ya bude idonsa qir a kanta itama shi take kallo tabbas tasan fuskarsa baa hoto ba a zahiri amma takasa tuna inda tasanshi, miqewa yayi ya zauna tare da sake sanya hannayensa ya ruqo nata ta matsa kusa dashi har numfashinsu na bugun na juna suna qarewa juna kallon, hawayene suka kwace a fuskar King Hafeez ya sake matsarta sosai yace


“Wai da gaske kece a gabana Farhana ke nake gani meyasa akacemin kin mutu bayan kina raye meyasa kika gudu kika barni cikin mawuyacin hali Farha meyesa Farha ina cikina dake jikinki Queen Abdallah shine dana don Allah kicemin shine kada kice bashi bane plz Queen ya akayi hakan ta faru....?” ya qarasa mgnr cikin shaqewar numfashi, kallonsa takeyi har yanzu tanason tunano inda ta sanshi da inda kalamansa suka dosa amma ta kasa kawar da kanta tayi tare da miqewa zatabar gurin yayi saurin sake kamota ta dawo ta fada jikinsa ya matseta a qirjinsa yace “bazanyi sakacin da zaki sake yimin nisa ba Farha” wayarsa ya zaro a aljihunsa ya danna wata number cikin rawar murya yace “ Baffa naga Farhanah a Kaduna” sauke wayar yayi ya sake kiran wata number ya kuma cewa “Hajiya farin cikina ya dawo naga Queen dita a Kaduna" kashe wayar yayi ya fara sunsunar wuyanta kamar wani bunsuru abinda yabawa kowa dake parlourn kunya kenan musamman Sarki da yake kusa dasu yanason gasqata abinda yake faruwa dasu.


Gyaran muryar da Daddy yayi shine ya dawo da King Hafeez cikin hayyacinsa saboda gaba daya ya susuce baimasan me yakeyi ba, zubawa Daddy ido yayi hakanne ya bata damar qwacewa daga ruqon tsaurin da yayi mata ta matsa kusa da Momy ta zauna Maryam ma ta zauna kusa da ita miqewa KING HAFEEZ yayi ya matsa kusa Farhan tashi Maryam tayi ta bashi guri saboda ta lura kamar baa cikin hayyacinsa yakeba zama ya kumayi kusa da ita ya dora kansa a kafadarta ya

Please Login or Register in order to submit comment