Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko?” dagowa tayi tana qare masa kallo tace “ya zaayi na manta da mijina uban cikin jikina wanda ya karbi budurcina a gurina taya zan manta dakai Hafeez meyasa kakemin tambayar nan ne? Ko wani abu ya faru dani ne?” shafa cikinta tayi ta dago ta kalleshi da sauri ta zame jikinta daga nasa tace “ina cikin jikina Mai martaba?” shafa fuskarta yayi yace “saidai wani idan na ajiye yau amma wancan ya fito duniya har ya kusa zama magidanci” dago kanta tayi ya daga mata gira tare da dagata ya dorata a gadon yace “kiyi hqr mu kwanta nasan tambayoyin ki suna da safe kyayimin su kin gajiyar dani ina buqatar hutu” bata kuma yimasa mgn ba taja musu bargon tare dayi musu addu'a suka kwanta.


Sai 8:00am suka tashi shima bell din gdan ce ta tashesu ya bude idonsa tare da kallon window hasken daya ganine yasashi direwa da sauri yace “ya salam mun makara Queen tashi ko sallah bamuyi ba” bude idonta tayi ta saukesu a kansa tare dayin miqa shima miqar yayi daidai lkcn da aka sake dannan Ringbell din ya nufi qofar ya bude ya fita zuwa parlourn yana tambayar waye sake dannawa akayi ya murda key din ya bude ji yayi ya fado jikinsa yana ihu yana “oh Dad kayimin wayo ka daukemin Momy na kawai sai da safe nashiga dakinta naga batanan Dad ansha amarci ina Momy na wayyoh dadi Allah jina nake kamar wani daban ga Momy na a gdan Dad na” murmushi yayi yace “kacika yarinta My lovely Son wato ni kakema tsokana ko? to na fasa bawa Momyn taka qaninka tunda abin naka iya shegene zauna ka jirani yau makara mukayi" yana fada masa haka ya direshi a kujera ya nufi dakinsa baiyi tunanin yana bayansa ba saida ya shiga dakin yaji ya fasa ihu ya dire a saman gadon ya kwantar da kansa jikin Farha yace “wayyoh Momy ta Dad na inata missing dinki” kallonsa takeyi da rashin fahimta har ya sanya bakinsa saman kuncinta yayi kissing dinta yace “I love you My Mom jikinki zafi kamar bakida lfy” lumshe idonta tayi daidai lkcn da King Hafeez ya fito daure da towel a qugunsa yana tsane ruwa ya kalli Abdallah yace “kazo zaka dameta da surutunka bata da lfy to” bude idonta tayi suka hada ido da Abdallah tace “waye shidin Mai martaba?” juyowa yayi da sauri inda shima Abdallan ya juyo ya hadiye mgnr da yake shirin yi cike da matsanancin mamaki.....







Please Comments
Share and Vote






*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿1⃣9⃣



Shafa fuskarta yaron yayi yace “momy meye yake damunki da har zaisa ki manta danki qwaya daya tak da kika mallaka a duniya?” lumshe idonta tayi ta cire hanunsa daga fuskarta tace “Mai martaba kai nake tambaya waye wannan? Meye alaqarmu dashi?” takaici ne da mamaki ya hana King Hafeez mgn ya matsa ya bude wadroop ya dauko jallabiya yasa ya koma ya kamo hanun Sarki yace “qyale Momynka batada da lfy Son” hawaye ya share yace “kanaji fah Dad wai bafa ta ganeni ba dama uwa na manta danta?”


Kamashi yayi suka fita yana lallashinsa mota suka nufa ya dauko musu break din da Momy tace a kawo musu suka dawo yanayi masa bayanin halin da Momynsa take ciki yayi ajiyar zuciya suka zauna a parlourn sunata hirarsu, jin shiru basu dawo ba yasata miqewa ta shiga bathroom tayo wanka daidai lkcn King Hafeez ya shigo ya miqa mata kayanta saida ya taimaka mata tasa kayan ya riqo hanunta tana lafe a jikinsa har suka shigo parlourn ya isarta har dinning din suka fara breakfast din gabadaya hankalinta yanakansu yanda suke hira kamar dama tare suke ita mamakin kamarsa da yaron takeyi saida suka gama sannan ta sake tambayar King Hafeez waye Abdallah murmushi yayi yace “shine albarkar auranmu Queen saboda Abdallah aka rabani dake tsayin 15 years aka barni da kukan zuciya dana fili saboda shine akayimana duk abinda ya faru da a baya amma a yanzu ya zama tarihi Queen wannan shine amsar tambayar da kikayimin jiya da daddare shine abinda kika haifamin a cikin dake jikinki kinganshi dama a jiyan na fada miki shima ya kusan zama magidanci”


Murmushi ta fara saki tana kallon Abdallah tana share hawaye tasowa yayi ya fada jikinta suka rungume juna suna kuka me ban tausayi a hankali yace “yanzu kin tunani ko Mom Allah ya isanmu Mom duk sun juya miki tunaninki Mom bazan taba yafewa duk wanda yake da hanu a cutar min da iyayena ba sun sani kuka saboda rashin kasancewar ku tare har wasu ma cikin mutane suna cewa nidin shegene mara asali ashe Nima dane na sunnah me cikakken asali inasonku iyayena I love Mom and Dad” ya fada tare da rungume su suma dukkansu kukan sukeyi suna tausayin kansu sunajin ashe suma zasu kasance cikin wannan farin cikin, ranar haka suka yini nunawa junansu kulawa da tattalin juna cikin su ukun babu wanda yakeson dayansu ya motsa har gasa King Hafeez da Abdallah sukeyi wajan nuna mata kulawa shi Abdallah ya yarda Mom dinsa zazzabi takeyi shi kuma King Hafeez dake yasan shine yayi barnar pean relief kawai yake bata tare da wasu magunguna na kashe zugi.


Sai yamma Baffa da Daddy da sauran jama'ar gdan sukazo yanda suka tarar dasu saida sukaji kunya King Hafeez ne kawai a zaune Farha na kwance tana bacci a jikinsa Sarki ma yana kwance a daya bangaren yana ta zuba mawa mahaifin nasa surutu, Maryam ce ta qarasa kusa da ita ta zata tasheta da sauri King Hafeez ya dakatar da ita yace “ki taimakeni kada ki tasheta daqyar na samu tayi bacci batada lfy” yanda ya marairaice yanama Maryam din mgn yasu dukka suka kwashe da dariya shima dariyar yayi hakanne yasata tashi ta bude idonta tana binsu da kallo Baffa kawai ta gane ta yunqura ta tashi zaune tace “sannunku da zuwa Baffa dama kananan ashe zakazo baka fadamin ba kuma harda baqi ma Yaya Anass sannu da zuwa” kallon kallo Momy da Dad da Maryam da Nasir suka farayima juna sukayi murmushi tare da hamdala Daddy yace “alhmdllh hakan ma anyi nasara Hafeez me kayi mata ta dawo daidai da wuri haka?" Murmushi yayi ya shafa kansa yace “Daddy kenan ai nida Farha baa shiga yanzu matsalar da muke fama da ita kuma duk abinda ya faru 15 years dinnan baya ya goge a mind dinta bata iya tunawa dashi sai an tuna mata.


Ajiyar numfashi Baffa yayi yace “tunda wancan tunanin ya dawo shima zai dawo dama munzo ne muga ya kuka kwana kuma inason wuccewa Bauchi gobe idan Allah ya kaimu” yana fadar hakan ta miqe tanajan qafarta daqyar ta matsa jikin Baffa tace “don Allah meye yake faruwa danine Baffa nifa jina nake wata iri kamar wadda ta taba ciwon hauka” murmushi Baffa yayi ya zaunar da ita a kusa dashi ya shafa sumarta yace “ba daga ciwon hauka kika tashi ba Farhanah kawai dai kin samu gushewar tunani ne na tsayin shekaru goma sha biyar to yanzu kuma shine tunaninki na baya ya dawo kuma duk abubuwan da suka faru a cikin 15 years dinnan sun goge a qwaqwalwar ki amma insha Allah zasu dawo” nan ya zauna ya rinqa yimata bayanin kowa a gurin da irin gudummawar da yabawa rayuwarta miqewa tayi ta rungume su Momy tana kuka me ban tausayi tana cewa “kuyi hqr wlh nasan na sanku amma ban tuna inda na sanku ba Saida Baffa ya fadamin na gde Momy na gde Daddy Allah yabar qauna” shafa kanta Momy tayi tace babu komai my daughter Allah ya tsare mana ku ya kiyayeku daga kaidin maqiyanku Allah ya dawwamar da wannan qaunar taku da soyayya Allah yasa nanda wasu yan watanni mu dawo suna”


Dagowa tayi suka hada ido ya daga mata gira tare da amshewa da “amin Momy insha Allah hakance ma zata faru Son ya gaji da zama shi kadai qani yakeso ko My Son?” daga masa kai yayi yace “yess Dad kuma twince nakeso ma” dariya sukayi ita kuma ta matsa kusa da Maryam suka rungume juna suna kuka Maryam tana cewa “na dade Ina jiran zuwan wannan ranar da zan ganki cikin gdan mijinki Sister Hanah” qasa tayi da muryarta tace “da alamun ma har Ali yaga Ali ko?" Qasa Farha tayi da kanta tana dariya itama dariyar tayi tace “dama tsoffin masoya kuma mayunwata irinku ai babu wanda zai ragawa wani na sani muje kiga wani abu” tana fadin haka suka juya suka nufi wata qofa da alamun kitchen ne suna shiga suka tarar da kuku yanata aikin girkinsa zubewa yayi a qasa yana kwasar gaisuwa tayi murmushi tace “akwai baqi a parlour kakai musu ruwa da abin tabawa” hada kayan yayi ya fita sukuma suka fara tattaunawa Maryam ta fito mata da wasu sirrika ta bata tace “suna da kyau da tsadar gaske tun lkcn da Yaya Nasir ya nuna yana sonki na siye wasu saboda ke so da mgnr ta shiririce ma nayita ajiyarsu Ina jiran wannan ranar gata kuwa Allah ya kawota ki dage kiyi amfani dasu zakiji dadinsu sosai nasan saikin nema da kudinki don da ganin mijinki bazaiyi sauqi ba garama ki dage kafin ya gano wata" ajiyar zuciya tayi tace “ai yanzun ma yanada wata matar akwai princess Amnah”



Tsaki Maryam tayi tace “ke kina Ina sanda yabada lbrn rabuwarsu yanzu ke kadaice saboda haka ki shirya kulada mijinki ke daya ki zama jaruma wajan kula da duk abinda ya shafi rayuwarku Allah ya shige muku gaba” haka Maryam ta rinqa nuna mata abubuwan da yanda zatayi amfani dasu kafin suyi musu sallama su tafi Sarki ya dage kan shi dole sai yabi Baffa Bauchi dole suka qyaleshi yabisu akan Suma goben zasuzo suyi sallama da Baffa kuma idan sun huta zasu taho Bauchin suna tafiya ita ma ta miqe ta shige dakinta tayi wanka tasha magungunan ta tayi sallar magaruba da isha daidai lkcn ya shigo dakin ya tararta a kan sallaya tana azkar zama yayi a gefen gadon harta gama ta juyo ta kalleshi shima itan yake kallo sukayi murmushi a tare ta miqe ta cire hijjab din jikinta ta linke ta nufi jikin mudubi ta fara gyara gashinta bayan ta gama ta dauki turare ta shafa a jikinta ta raba ta gefensa ta kwanta ya hadiye yawun kwadayinsa ya kwanta a gefenta ya janyota jikinsa yana ajiyar zuciya yace “I Miss you My Heart long time Ina kewarki Ina zubar da hawaye akan rashinki My Queen wlh bazan taba yafewa duk wanda yayi silar nisantani dake ba”



Yana fadin hakan yana qara shigewa jikinta janyewa tayi ta koma ta kwanta ya sake matsota yace “ I hope matata jaruma ce me qoqarin sanyani farin ciki da sallama min jikinta a duk sanda na buqaceta tana iyakar yinta wajan ganin ta gusar min da qishirwa ta Queen ke kanki kinsan nayi qoqari bayan batanki da shekara bakwai muka rabu da Amnah kuma ko sanda muna taren nayi samada shekara biyu bama mu'amalantar juna in kika hada shekara tara da biyu zai baki kusan sha daya kenan kinga kuwa ai nayi qoqari a matsayi na namiji” yana fadin hakan yana matsawa jikinta kuka tasa masa tace “nidai ka qyaleni Abban Sarki wlh bazan iya ba na gaji jiya Pls ka tausayamin don Allah” ajiyar zuciya yayi ya janyota yace “shikenan na hqr mu kwanta muyi bacci” da wannan bacci ya dauketa shikuma ya nata juyi da haka baccin ya daukeshi sai asub ta farka tana shirin sauka ya ruqota yace “ki daure kiyimin wani abu kafin muyi sallah” tureshi tayi tace “Allah ka cika matsala Mai martaba anfa shiga masallaci don Allah” miqewa yayi yace “is ok muyi sallah tukunna a bani breakfast" batacew masa komai ba ta nufi bathroom wanka kawai tayi ta dauro alwala shima ya tashi ya shiga yayi sukayi sallah ta miqe da niyyar fita yasan nufinta saboda haka ya ruqo ta yace “hqr zakiyi dani fah Queen” turo baki gaba tayi ya dagata suka koma saman gadon daqyar ta qwaci kanta shima saida tasa masa kuka sannan ya qyaleta sukayi wanka suka fita dinning din sukayi breakfast sai sha daya suka nufi gdansu Momy lkcn Baffa ya shirya yana jiransu suna zuwa ya miqe sukayi sallama suka fita Sarki na daga mata hanu itama daga masa takeyi King Hafeez shine yakaisu airport ya juyo gdan ya dauketa suka tafi gdansu.





Please Comments
Share and Vote






*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿2⃣0⃣



Haka sukaci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin so da tattalin farin cikin junansu satinsu daya a Kaduna suka nufi Bauchi tana lafe a jikinsa har suka isa motar ta shiga gdan sarautar ta dago kanta daga jikinsa duk da an sakewa gidan fasali da tsari sosai amma bata kasa ganeshi ba ganinshi take kamar jiya ta barshi, sunayin parking aka bude musu qofofin shine ya fara fita sannan ita nan danan ido ya dawo kansu gdan ya rude da ihun murna tare da kabbara bayin mata sunata rugowa suna rungumeta itama ta saki jiki dasu tana hawaye suna rungume juna saida komai ya lafa sannan suka nufi part din surukar tata a hanya suka hadu da ita da jikanta sarki ta tafi da gudu ta rungume uwar mijin nata sai kukan da taketa qoqarin hadiye wa ya kwace mata itama Hajiyan kuka tasa tace “Farha ashe kina raye a duniya ashe da rabon zaku qara ganawa da Hafeez munyi kewanki tsayin shekaru Farha ashe kinanan keda jikalle na”


Itama kukan takeyi ta janye jikinta suka shiga ciki suka zauna sunata jajantawa juna Sarki ne ya dubi Momynsa da kakar tasa yayi dariya yace “wlh Dad nake hangowa sanda ya laluba yaji ba Mom....” daquwa Farha ta watsa masa shikuma King Hafeez ya zuba masa dundu a baya ya kwallah qara yace “wayyoh Hajiya kina kallonsu zasu sheqeni” murmushi tayi da riqo hanunsa ya dawo kusada ita tace “aiba qarya yayi ba ya kake sanda suka bata din ai kaima zaucewa kayi kaidin badan qarfin addu'a ba da tuni ka shiririce” murmushi yayi daidai lkcn Hajiya Kilishi ta shigo itama ta nuna murnarta da farin cikin ta sosai aka rinqa jere musu abinci kamar hauka da abinsha sukaci sukasha duk iyalan gdan Mai martaba sarki Hambali sun hallara harda Asiya da Nadiya da Umaimah harda Prince Hasheem da baima taba ganin Farhan ba ranar yini akayi ana shagali a gdan sarautar sai dare sosai King Hafeez ya dauke matarsa suka wucce part dinsu shi kansa part din a fashe shi an sake masa gini yanzu part daya ne qaton gaske saika shiga ciki ne zaka gane yanda tsarin gdan yake bangaren Farha parlour uku ne da dakuna uku kawanne an zuba furnitures yan gaske sai bangarensa me parlour biyu da daki daya sai wani daki wanda shima idan ka shigeshi parlour ne babba da aka qawatashi da kayan alatu sai daki biyu a ciki kai gdan ya tsaru sosai bangarenta ya rakata wanda ya cikashi da manyan pics dinsu tun na auransu suna shiga ya fara kiciniyar cire mata kayanta yace “ya kamata muyi wanka mu kwanta ko?"



Daga masa kai tayi suka shiga bathroom din sukayi wanka suka shirya tare suka kwanta, haka kwanaki sukayita shudewa sarki ya tafi Rasha karatunsa inda King Hafeez ya hana farha aikin asibiti babban asibitinsa dake Kaduna ya mallaka mata yace duk abinda zaike shigowa aljihunta zaike shiga hakanan ta hqr da aikin ta zauna zaman ci da kashi tunda haka ya zaba mata.
Wata daya wata biyu wata uku har duka suka doshi shekara babu wani bayani tun abin bai fara damun King Hafeez ba har ya fara damuwa duk lkcn da yaji tace tana period saiya kulle kansa a daki yayita kuka yana roqon Allah ya qara musu da ko dayane me albarka harma ya saduda ya mayar da hankalinsa kan tilon dannasu da yake tunanin qila shi kadaine rabonsu.



A cikin shekararsu ta biyu ne Allah ya azurtasu da samun qaruwa ita kanta batasan dashi ba kawai dai baccinta ya qaru saita yini tana bacci batare data gaji ba sannan takanji kwadayin wasu abubuwa da abaya basu dameta ba, yau litinin ce da wuri ta tashi ta hada musu break kasancewar tun dare ya fada mata yanason zuwa Abuja akan aikin wani sabon asibitin da yake ginawa batayi break din ba saboda cikinta da yake danyi mata ciwo tana kwance saman gado tana kallonsa ya gama shirinsa ya dauki laptop dinsa da wayoyinsa ya matso kusa da ita ya shafa fuskarta yace “zan tafi Queen” lumshe idonta tayi ta budesu a kansa tace “Allah ya kiyaye hanya ya tsare min kai” amsawa yayi da amin yace “yau bazan samu rakiyar bane” hanunsa ta ruqo tace “kayi hqr Allah yau kasala nakeji" murmushi yayi yace “dama ai kin dade da zama kasalalliya a ko inama ni wannan baccin ya fara yin yawa da rana a yini anayi da darenma kuma dana nemi haqqina a kama yimin rakin bacci akeji”


Yana wannan mitar ya fita ita kuma ta koma ta kwanta bacci me dadi ya dauketa tayi kusan awa biyu tana baccin taji zuciyarta da mararta na wata irin hautsinawa da sauri ta tashi zaune amma daqyar ta iya durowa daya gadon amai ya qwace mata gashi bataci komai ba sai ruwan tea saboda hakanne ta jigata sosai ga ciwon marar da ya addabeta kwanciya tayi a qasa gefen aman tanata murgususun ciwo har qarfinta ya ida qarewa sai yamma liqis Jakadiyya ta shigo itama saboda King Hafeez ya kira yace taje ta duba ne ta gano masa lfyrta shiru yana Kiran wayarta taqi dagawa, part dinta ta fara shiga bata ganta ba saboda haka ta nufi part dinsa tana kiran “ranki shi dade uwar gijiyata Mai martaba yanata Kiran...” mgnr ce ta maqale saboda yanayin data risketa cikin amai ido a juye kamar matacciya, salati tayi tare da nufarta da sauri tana kiran sunanta amma babu alamun zata amsa hakanne yasata fita da gudu ta nufi cikin gdan a gigice ta fadawa Hajiya Fulani cikin tashin hankali suka rankayo harda Kilishi suna zuwa suka gyarata ruwan da suka sanya mata a jikinta ne yasata farfado amma da ganinta kasan a jigace take Hajiya ce ta dauki wayarta ta kira King Hafeez din bugu biyu ya daga yace.



“He...hello Queen ya akayi ne Ina kikasa wayar...” katseshi Hajiya tayi tace ka turo mana likita cikin ma'aikatan ka akwai matsala Farha batada lfy” tana fada masa ya hau salati tare da cewa “qlau fah muka rabu Hajiya ciwon har yakai wanda bazata iya daga wayata ba?” katseshi Hajiya tayi da cewa “muma yanzu muka shigo akwai alamun ta jigata...” katseta yayi da cewa “ok ganinan Nima bari na kira Patrick yazo ya dubata” yana fadin haka ya kashe wayar ya miqe ya fita daga asibitin a hanya ya kira likitan ya bashi umarnin yaje ya duba matarsa.
Cikin abinda bai wucce 15 minutes ba Dr Patrick ya iso ya shiga cikin gdan a wani weell chair aka turata zuwa clinic din dake part din aka kwantar da ita a gadon ya daura mata drip kafin ya fara dubata yanayinta kawai ya gani yasan matsalar ta amma saboda gudun kokwanto saida ya debi jininta ya gwada yayi murmushi tare da saita na'urar scenning a cikinta ya fara dubawa nan ma dai sakamakon dayane ya dago yayi murmushi yace “ Allah ya raya Hajiya's Madam nada cigar baby wata uku" kabbara suka dauka tare da godiya ga Allah magunguna ya rubuta mata sannan ya kuma kallon Hajiya yace “a kula da cin abincin ta sosai baby yanason abinci saboda ya samu Energy sosai” amsa masa sukayi tare dayi masa gdy ya fita da takardar bai jima ba ya dawo da magungunan dayake abune na masu abun a parmercy dinsa aka debo shigowar Dr Patrick tayi daidai da shigowar motar da taje airport ta dauko kin Hafeez a qofar part din sukayi kacibis da Patrick yayi murmushi yace “Congrass Sir madam tanada sabon baby almost 3 mouth a gurin ya zube yayi wata doguwar sujjada Patrick ya saki baki yana kallonsa ganin bai dagoba ne yasashi sanya hanu ya dagoshi fadawa yayi jikin Patrick yace “Allah na gde maka ashe bayan Sarki zan sake haihuwa wayyoh Allah na Patrick na gde kaine mutum na biyu da kayimin wannan kyakkyawan albishir din dole ka karbi kyauta me kyau yanzu Ina Queen din take?”


Kama hanunsa yayi suka shiga dakin ya zame hanunsa ya qarasa kanta ya tsugunna yana kallonta yau daya duk ta rame ta dashe ta qara wani sabon haske ajiyar zuciya yayi ya sanya hanunsa ya shafa cikinta tare dakai bakinsa yayi kissing bayan ya dage rigarta a hankali yakai har zuwa bakinta ya fara tsotsa kamar alawa kunya ce tasa su Hajiya ficewa daga dakin saboda ta lura idonsa rufewa yakeyi idan yana tare da Farha jin dumin lips dinsa a saman natane yasata tura hannunta cikin sumarsa da take kwance luf kamar ta balarabe bude idonta tayi a hankali ta zubashi a cikin nasa yayi murmushi yace “kiyimin murna nayi namijin qoqarin sake ajiye qwaina a mahaifarki daqyar Sarki zai sami qani ko qanwa"






Please Comments
Share and Vote






*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿2⃣1⃣



Ajiyar numfashi tayi tare da murmushi me nuna farin cikin ta shima murmushin yayi ya sake ruqo hannunta yace “yanzu inane yake miki ciwo me kikeso kici?" Girgiza masa kai tayi alamun babu komai ya sake matsawa jikinta yace “ ok tashi muje ciki na sama miki abinda zakici" bai ida rufe bakinsa ba ya dagota suka fita yana riqe da ita har cikin parlourn ta ya kwantar da ita saman kujera ya nufi kitchen dauko mata cake da youghut ya dawo ya rinqa bata tanaci har taci ya isheta sannan ya dauketa suka shiga bathroom sukayi wanka ita ta kwanta shikuma ya dauki wayarsa ya fita dakinsa.


Tashin farko Abdallah ya kira ya fesa masa ya bawa Momyn sa ajiyar qaninsa ya kuwa saki ihun murna yace “kayimin daidai Dad Ina Momyn take?” murmushi yayi yace tana dakinta tana bacci sai da safe kwa gaisa” sunayin sallama ya kira mutanen Kaduna ya fesa musu suma sunyi murna sosai Maryam tace zatazo taga Farha da ciki itama ta rama tsiyar data rinqa yi mata,
Sunayin sallama ya nufi dakinta lkcn har tayi nisa a baccinta ya haye gadon ya janyota jikinsa ya rinqa shafata har saida yaji alamun

Please Login or Register in order to submit comment