Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kade² sake lafewa tayi a jikin Rahmah tanaci gaba da rera kukanta Jakadiyyar da tausayin uwar dakin nata ya cikata ta rinqa bata hqr tana lallashinta har suka qarasa batayi shiru ba.


Motocin ne sukayi parking a harabar gdan da yake gari guda kowa ya fito sannan aka bude mata qofar suka fito ita ce qarshen fitowa tana fitowar aka dora saman wata farar godiya sunata kide² su da waqoqinsu har suka isa wata babbar qofa aka bude musu suna shiga bayi da barori sukayita zubewa suna kwasar gaisuwa har suka isa wata qofar nanma aka bude suka shiga sauketa akayi daga kan godiyar Jakadiyyar ta sake riqe hanunta suka shiga parlourn tare da sallamarsu parlourn cike yake da mutane aka farayi mata marhabin wata mata ce ta taso ta riqo hanun Farhan tanayi mata sannu da zuwa bata gane komai itadai taji anyi qasa da ita ta russuna sai kuma taji an dafa kanta muryar dattijuwa taji tace “barkanki da zuwa gdan nan matsayi matar Mai martaba Hafeez Farhanah Allah yayi muku albarka ki saki jikinki nan gdanku ne ki daukeni kamar mahaifiyarki kiyi duk abinda zakiyi a gdanku nanma gdane kinji, Hajjah ku kaita sauran bangarorin ta gaishesu”


Sake fita sukayi suka shiga apartment din Hajiya Sogiji suka kwashi gaisuwa babu wata fuska a gurin wadanda suke dakin saboda haka basu dadeba suka nufi part din Hajiya Kilishi nan ne Farhanah taga gata da riritawa anan part din aka barta yan uwan nata sukayi musu sallama suka tafi lkcn shidda da rabi ta wucce yammata biyu ne a bangaren Asiya da Nadiya sune suka sata a gaba sunata yi mata hira da dauke mata kewa amma taki sakin jikinta sai kuka takeyi dariya sukeyi mata wadda aka ambata da Nadiyyar ce ta ruqo hanunta tace “wlh Yaya ya more yarinya qarama danyen jini zai bare a leda ina tausaya miki Farha” dariya Asiya tayi tace “nifah kawai tunda na ganta nake ayyana yanda karon zai kasance yanda Yaya Hafeez yake Masha Allah ga tsayi ga qauri Allah idan ya rufeta bazaa hangota ba ko kadan”



Sake qarawa kukanta sauti tayi tace “nidai na roqeku kuyimin shiru banason wannan mgnr” kwashewa sukayi da dariya sukace “zakiyi bayani ne da harda Chinese sai kinyi nidai zan taimaka da ruwan zafi...” toshe kunnenta tayi tana girgiza musu kai ganin tana neman tayar musu da iskoki ne yasasu sauya ragamar zancen, suka farayi mata bayanin kowa a gdan musamman part's ukun da aka kaita sukace na farko da aka fara kaita shine na surukarta mahaifiyar Sarki Hafeez ita ake Kira da Fulani Hajjah itace babbar yarta sai Hafeez sai Asiya ita kuma Sogiji itama da yayanta biyu Hasheem da Umaima ita kuma Hajiya Kilishi tanada ya daya Nadiya.


Ruqo hanunta Asiya tayi tace “zaki fahimci komai a hankali zakuma muyi qoqarin sanar dake wasu abubuwan Aunty Farha kedai kawai ki shiryawa rayuwa a rikitaccen gdan da wanda yake wajensa baya hango tarin matsalolin da suke cikinsa babban abin damuwata gareki shine kishiyarki Gimbiya Amna batada kirki gata da bala'in kishi yanzu haka rikici suke tukawa da Mijinku saboda batasanma da mgnr auran da zaiyi ba sai yau da safe saboda haka dole ki nutsu ki shiryawa tunkarar qalubale uku mijinki kishiyarki da kuma cikin gdannan musamman Hajiya Sogiji koda wasa karki taba sakin jiki dasu...” mgnr tace ta maqale saboda ganin dawowar Hajiya Kilishi da wata mata tare da Hajjah.



Ruwan wanka suka hada mata sukace taje tayi wankan shiga tayi toilet din ta jima tana qare masa kallo kafin ta fara wankan ruwan kamar ruwan madarar turare zallah haka shima sabulun bayan tayi wankan ta dauro sabon towel din da Hajiya ta Kilishi ta bata ta fito matar da suka shigo da Hajjah itace ta bude wata jaka ta dauko wanu Mai ta rinqa matsa mata tana fada mata inda zata shafa harta gama mulke jikinta dashi qamshinsa ya cika dakin ta kuma dauko wani tace ta shafa shima ta shafa sannan ta zauna Hajjah ce ta kama gashinta ta gyara matashi tsaf sannan ta daureshi da band aka shafa mata powder tare dasa mata White lips brexia da pant suka bata ta karba ta koma bathroom din tasaka sannan ta sake fitowa Farha akwai baiwar dukiyarsu ta fulani a qirjinta Wanda suke tsaye cak kamar dashe, wata maroon din rigar bacci matar ta miqa mata tace tasa batayi musuba ta zura rigar ta sauka har gwiwarta murmushi Hajjah tayi ganin mugun kyaun da yarinyar tayi babban abida yake burgeta rashin tsoronta wata Alqabba suka Dora mata rufaffiya itama maroon Mai maballi har qasa wani flat din takalmi suka bata tasa a qafarta shima maroon tayi bala'in kyau qarshe barin turare sukayi mata kamar hauka tadau wani mugun kyau da qamshi miqewa Hajiya Kilishi tayi ta fita bata jima ba suka dawo da Jakadiyyar gdan Sarkin.



Ruqo hanunta Hajiya Kilishi tayi ta damqashi ana Jakadiyyar tace “to Ummah ga amana nan kindai ganta kinga yarintar ta ki zama idonta kuma kunnenta sannan ki rinqa qoqarin nusassheta tare da yi mata bayanin abubuwan da suka shige mata duhu kada ki munafurceta bani nabaki amanar nan ba Mai martaba ne saboda kowa ya gani duk girman gdannan da mutanen dake gdannan bai amince ya tura kowa ya dauko masa matarsa ba saike” jinjina kai tayi tace “nayi gdy na qara Hajiya Allah yaja kwana ya qara lfy" murmushi tayi tace “ki rakata gurin mijinta dare yayi nisa Allah yasa muji alkhairi Farha Allah ya kankaro miki darajarki data Mijinki daya kasa samu tun auran farko”amsawa duk wadanda ke dakin sukayi da amin.. itadai Farhcikin maganganun su babu abinda ta fahimta.


Kama hanunta tayi har suka fito harabar gdan mota tagani a tsaye askarawa sun kewayeta bude mata akayi suka shiga driven yaja suka tafi a hankali suke tafe har suka isa wani katafaran bangare wanda ya gaji da haduwa ko ina dake gdan haskene ya gauraye gdan bude musu get akayi suka shiga sukayi parking suka fito har yanzu hanunta na cikin na Jakadiyyar bayi sunata zubewa suna kwasar gaisuwa abinda yafi bata mamaki shine duk Wanda ya zube saitaji yace “barka da isowa masarautar sarkin sarakuna adalin Sarki Hafeez barka da zuwa uwar sarkin gobe cikon farin cikin shugabanmu” kalaman mugun daure mata kai sukeyi, bangare uku ne a gdan biyu maka maka dayan kuma madaidaici amma shima ba qarami bane shine a tsakiya da an kafa qaton hoton zane na Sarki Hafeez a jiki an rubuta (KING HAFEEZ || ) shi kansa rubutun da ruwan gold akayisa sai daukan ido yakeyi da alamun dai gurin mallakinsa ne sai dayan bangaren daman an rubuta PRINCESS AMNA shima da manyan kalmomi akayi rubutun alamar da take nuna bangaren matarsa ne shikuma na hagun an rubuta QUEEN FARHA alamar da take nuna nanne bangaren Farhanan, wani gabjejen dogari ne yazo ya zube a gabanta yace “tuba nake ya shugabata na cika umarnin Mai martaba ne ” Jakadiyya ce ta miqa masa hanu ya bata mukullin apartment din ta bude suka shiga suna shiga Jakadiyyar tasa ce “Allah ya taimakeki nan shine bangarenki zanso ki kwanta ki huta amma hakan bazai samu ba saboda dokar masarauta yau dole kiyi kwanan turakar Mijinki”


Gaban Farha ya yanke ya fadi ta dago da sauri ta kalli Jakadiyya tace“turaka fah kikace wacce turaka inane turakar me zanyi a can?” murmushi tayi tace “bazan iya baki amsa ba lkc ne zaisa ki fahimci haka” sake kama hanunta tayi ta nufi wata qofa ta danna qararrawar sau biyu sannan taga wani blue din haske alamar an bata damar shiga murdawa tayi suka shiga tare da sallamarta yana kwance saman wani kushin yayi matashin kai da tumtum gabansa cike da tarkacen kayan abinci da kayan marmari da alamun na musamman ne idanunsa qur akan amaryar tasa yanajin wani sabon farin ciki yana gusar masa da baqin cikin da yake ciki, sannu a hankali har suka iso gabanshi durqushewa Jakadiyyar Ummah tayi tace “tuba nake ya shugabana wannan ya farune sakamakon jinkiri da aka samu wajan shirya Sarauniya amma bazaa qaraba ayimin aikin gafara” jinjina kansa yayi tare da nuna mata hanya harta juya zata fita yayi gyaran murya ta sake zubewa tace “takunka salamun kwanciyarka salamun adalin Sarki mai duniya” tashi yayi zaune ya sanya hanunsa cikin aljihunsa ya zaro wani abu a qunshe cikin takarda ya miqa mata tasa hanu ta karba tana zuba gdy tare da kirari, shi mutumne meson a yabeshi a kurantashi amma yau baya buqatar wannan soyake kawai yaga fuskar Farha a gabansa yaji irin kurinta na yau saboda haka ya nuna mata hanya ta miqe kanta a qasa tace “kwana lfy cikin salama da amincin Allah ya shugaban talakawa baya goya marayu uban kowa gatan kowa shugaban Jakadiyya Ummah Mijin Sarauniya Farhanah uwar Yariman gobe" idan tayi masa wannan kirarin dadi yakeji tana fita taja qofar ya danna mata password tare da zuba mata ido tana durqushe a inda Jakadiyya ta durqusa tun farko kanta a qasa saida ya qare mata kallo kafin ya miqe ya qarasa gabanta ya zauna tare da sanya hanunsa ya dago kanta, ga mamakinsa sai yaga hawaye sharkaf a fuskarta duk ta dame fuskar dashi tausayinta ne yadan darsu kadan a zuciyarsa ya sake sakin tsaddadan smelling dinsa wanda ya qarawa kyakkyawar face dinsa kyau da kwarjini daidai lkcn ta bude idonta tun isowarsa gurin ta zuba idonta cikin rikitaccen idonsa wanda duk girman mace kuma duk qanqantar ta bata iya jure kallon cikinsa, itama lumshe idonta tayi tana jiran taji abinda zaiyi mata.


Saukar lallausan tafin hanunsa taji a saman fuskarta yasa yatsansa yana share mata hawayen a hankali kuma a nutse sannan a mulkance ya bude bakinsa yace “baayimin kuka a fadata saboda haka ki kiyaye" saurin jijjiga masa kai tayi tare da motsa dan qaramin bakinta kamar zatayi mgn, ajiyar zuciya ya fuzgo tare da damqo hannunta cikin nashi yana qara qare mata kallo miqewa yayi ya dagota yana riqe da hanunta har suka qarasa inda ya tashi ya zaunar da ita shima ya zauna daf da ita saukar numfashinsa da takeji ne yasa tsoronta qaruwa ta fara matsawa a dabarance ita a tunaninta kada ya gane ji tayi ya ruqota tare da janyota jikinsa ya hadata da jikinsa sosai bakinsa yasa daidai kunnenta yace “yau ba ranar fada bace ranar shiri ce ni na daina fada koda yake kince bazaki yafemin ba tarani kikeyi saboda haka na baki wuqa na baki nama ni yau nine kedin kece ni ki yanki duk inda yayi miki a jikina” turo baki tayi gaba zatayi masa tsiwa yayi sauri dora hanunsa akan bakinta yace “duk kalma daya da irin hukuncinta saboda haka ki kiyaye" yanda yake magana cikin izzah yasata shiga taitayinta dauke hanunsa yayi daga bakinta ya bude wata warmer yace “kitashi ki daibi abinda kikeso kici banason musu banason gardama saboda haka ki kiyaye” ajiyar numfashi tayi ta miqe zumbur jikinta na rawa ta koma gefe ta tsaya tace.


“Bazanci badin haka kawai na qoshi don qeta ace bazan fadaba Allah bazanci ba saidai ka kasheni kuma bazan kiyaye badin ko a lahira aka kafa mani wannan dokokin ai nasan aljanna ce akeson yimin qwalele don babi zanyi ba...” bata ankara da tahowarsa ba juyowa tayi ta ganshi qerere a kanta ta ihu tasa ta kwasa da gudu tayi baya fadawa tayi dakin akwai isasshen filin yin wasan tsere saboda haka yabita a nutse har takai qarshe ta maqale a jikin bango tana karkarwa, qarasowa yayi gabanta ya sanya hanunsa yayi mata waigi ta dago kanta taga yanda yayi mata rumfa tace “wayyoh na shiga ukuna ka rufeni banashan iska...” matseta yayi a jikin bangon sosai kamar zai shigar da ita ciki kanta a qirjinsa kuka ta saka masa da taji matsar tayi yawa dan sassauta mata yayi ya sanya hanunsa ya fara balle maballin alqabbar ta riqe hanunsa cikin kuka tace “ni banason haka ka bari me zaka gani a jikina idan ba salon kwartancinka ba ai dama daga ganin girmanka zakayi mugunta idan ka kasheni ai ka huta kowama ya huta...."


Sunkuyowa yayi yayi kissing kuncinta tare da dora hanunsa saman lips dinta yace “babu laifi hakanma idan nayi kwantoncin ma ai ba laifi bane tunda kawomin ke akayi nayi duk abinda nakesonyi dake wlh badan inajin tausayinki ba dana gwada miki salon tawa muguntar da kike yawan ambata tunda na fahimci son gani kikeyi amma duk da haka bazakici banza ba...” yana fadin haka ya sunkuceta ya nufi wani guri da ita ihu take tana zille² da dukansa a qirji tana kiran “ni ka saukeni Allah banason irin haka dama ashe kaima haka kake shiyasa kake wani lumlumshe ido na iskanci Allah idan baka saukeni ba saina cijek..." Wata qofa ya shiga ya jefata a saman tangamen gadonsa ya kashe fitila yace “ ya isa haka oya maza kwanta banasan surutu kiyimin shiru" bargo taja tana haki ta rufa tace “eh dai naji kuma kada a sake a hawomin nan ni banason shisshigi da neman ismun” murmushi yayi ya nufi wata qofa ya bude ya shiga tayi tunanin dakinsa ya shiga tayi dariya tace “matsoraci kawai ashe izzar taka ta qaryace akai abinda kake tsoro toba dolema kaji tsorona ba yanzu shekarata 16 nasan idan na qara hudu sai nayi kamar kai kuma irin abincin da kakeci nima shi zankeci na zama katuwar basamudiya irinnka yanda bazake cin zalina ba idanma kaci zanke ramawa" da haka bacci ya dauketa yana fitowa yaga tayi bacci ya bude blanket din ya leqa fuskarta yayi murmushi, mai ya shafa a hanunsa da qafafunsa da sauran jikinsa ya zura doguwar rigar bacci me laushi ya raba ya kwata a gefenta ya janyota a hankali ya hadata da jikinsa tare da yi musu addu'a ya rufesu shima bai jima ba baccin ya daukeshi saboda dare yaye lkcn 1:30am....







*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻





*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿5⃣



Da asuba tana farkawa ta fara kokawar qwacewa amma ya riqeta gam ganin bazata iya qwacewar bane yasata lafewa a jikin nasa ta qura masa ido tana kallon fuskarsa da dan siririn sajensa sai sumarsa data kwanta luf a kansa ta kwanto gaban goshinsa sak ta fulanin asali tabe baki tayi tace “ba laifi kanada dan kyau kadan" duk abinda takeyi yanajinta saboda ya rigata farkawa batayi zatoba taji yace “kuma na fiki kyau ba" saurin rufe idonta tayi tana dariya tace “lahh ashe wayo kayimin idonka biyu to Allah baka da kyau ma subutar bakic...” dora hanunsa yayi saman lips dinta yace“oh gud kedai bakya gajiya da surutu tashi ki tafi dakinki kiyi wanka kiyi alwala ki sallah” langwabar dakai gefe tayi tayi masa kalar tausayi tace “ni bansan dakinba kawai data shigo dani nan dakin ta kawoni” miqewa yayi yana miqa ya nufi qofar dakin yace “taso na taimaka miki na rakaki” miqewa tayi tabi bayansa suka fita daga dakin suka ratsa parlourn nasa da ta rinqabi da kallo a fili tace “bakaji ba" tsayawa yayi yana kallonta tayi dariya tace “aa bafa wani abu zance ba dama cewa zanyi dole kayi girman kai wannan aljanna da kake ciki" dariya ta bashi amma dake miskili ne sai murmushi yayi yaci gaba da tafiya tana biye dashi har sukazo bakin qofar kasancewar parlour biyune a part din nasa ya bude qofar tunaninta waje zasu fita amma sai taga sun sake shiga wani parlourn shima me masifar kyau tsayawa tayi cak ta bude baki tana kallon parlourn tare da shafa bangonsa da yaketa kyalkyali ajiyar zuciya ta sauke ya murda wata kofa ta bude ya juyo.


Hangota yayi acan nesa a tsaye yayi tsaki tare da duba agogo yace “kizo na nuna miki na tafi masallaci kin tsaya kina shirme" takowa tayi da gudu² sauri² ta tsaya a gabansa ya kama hanunta suka shiga wani dan madaidaicin parlour ne wanda babu komai a cikinsa sai carpet babba daya kusa cinye rabin parlourn sai tumtum manya guda takwas da ka ajiye ko wacce kusurwa daya hudu kuma a tsakiya kalar maroon da baqi sai wata qatuwar TV ta bango amma bata qarasa girman ta parlour da suka baro ba gefe kuma dinning ne sai wata qofa a kusa da dinning din da alamun kitchen ne da store juya idonta tayi wani bangaran da taga wasu qofofin guda biyu hanu yasa ya bude daya ya shiga itama tabi bayansa dakine qaton gaske kamar a qasar turawa gadone tangameme kamar na turakarsa komai da komai iri daya ne sai wadroop bango guda ta dressing mirror shima ya cinye wani bangon an jera kayan shafa dana kwalliya akai sai drowers din gadon da dressing chair ko wanne a muhallinsa wata qofa ya nufa ya bude ya shiga bai jima ba ya fito ya kalleta kamar zaiyi mata mgn sai kuma ya fasa ya fice.



Tabe baki tayi tace “kaji dashi ciwon ajali a dan yatsa" shigewa tayi toilet din itama tayo alwala tace “hmn wai nayi wanka yanzu tab yasin bayi zanyi ba sai anjima" sallah ta tayar daidai lkcn da taji masallacin fada suma sun tayar bayan ta idar ta zauna tanata azkar dinta har lkcn da gari ya fara haske ta fara jiyo motsin mutane a harabar gdan tananan zaune taji ana dannan qararrawar dakin miqewa tayi sanye da hijjab dinta ta nufi qofar ta bude Jakadiyya Ummah ta gani tsaye jikin qofar ta russuna tace “tashinki lfy shugabata gaba salamun baya salamun da fatan alkhairi" itama qasa tayi tace “ina kwana" saurin dagota tayi tace “na tuba ranki shi dade ki gafarce ni kada kiyimin ta abinci na idan Mai martaba ya gani sawa zaiyi a koreni" sakin baki tayi tana kallonta har tayi shiru sannan tace “saboda na tsuguna na gaisheki din zai koreki ai naga kinyi jika dani" murmushi tayi tace “ranki ya dade ai tsarin masarauta ba haka yakeba ranki ya dade duk girman indai bawane kaine zaka risinawa mutum duk qanqantar sa indai yanada jibi da gdan sarauta” gwauron numfashi ta ajiye tace “tabdi Allah ya kyauta"juyawa tayi ta shige ciki ita kuma tace “yanzu me kike buqata a kawo miki na rabawa kowa aikinsa sun fara sai me gyaran dakinki itace ban kawo ba saboda nayi tunanin baki tashi ba” yatsina fuska tayi tace “babu komai idanma ina buqata zanyi da kaina yanzu bacci nakeson komawa” risinawa tayi tace “na gde ranki shi dade tashinki lfy" tana fadin haka ta juya ta tafi ita kuma ta koma ta kwanta baccinta me dadi ya dauketa bata farka ba sai goma da rabi tana tashi ta fada bathroom ta sakarwa kanta ruwa tayi wanka ta fito daure da towel tana tsane jikinta ajiyeshi tayi ta fara dauko mayuka tana dubawa fara shafawa tayi saida ta gama ta gyara fuskarta tayi kwalliyarta ta fesa turare ta dauki wata super Holland baqa tasa dinkin riga da siket sun zauna das a jikinta ta daura dankwalin ta simple ta ciro takalmi baqi flat tasa a qafarta tare da sanya sarqa da dankunne na baqin dutsan diamond tayi masifar kyau shigar ta fito da asalin quruciyarta abin baa cewa komai agogo ta daura ta zura zobe ta kalli kanta a mudubi tayi murmushi tace “Yes Queen Farha” dariya tayiwa kanta ta bude qofar dakin ta taka a nutse har cikin parlourn tunda ta fito taga kowa ya qame kallonsu takeyi sororo tana takawa harta qarasa dinning din ta zauna bisa jagorancin Jakadiyya Ummah ta zauna masu hidimar abinci suka fara zubewa suka kwashi gaisuwa sannan sauran hadimai sunata kwasar gaisuwa itadai bata amsawa sai Jakadiyya Ummah ce take sallamarsu hada mata abincin suka rinqayi dakatar dasu tayi tace “nifa ya isheni” rusunawa sukayi suna neman afuwarta murmushi tayi tace “waiku komai anan laifi ne tabdi kuna cikin wani hali” taja cup din tea din ta fara sha saida tasha me isarta sannan tadan taba farfesun yan shilan sannan ta miqe ta koma ta kwanta a saman tumtum din tare da kunna kallo shigowar yan matan biyu ne yasata miqewa tayi tsalle suka rungume juna kallonta Nadiya tayi tace “aa meye hakan Aunty Farha lallai ma Yayannan dan rainin hankali ne wato baiyi miki komai ba aikuwa wlh akwai chakwakiya saboda su Hajiya Sogiji suna can suna jiran a fito da qyalle” dariya tayi tace “me kenan wanne irin qyalle kuma zaa fita dashi?”



Murmushi Asiya tayi tace “wata shegiyar al'ada ce ta gdannan duk yarinyar da akayiwa aure ko aka auro kwananta na farko a gdan mijinta sai an fito da zanin gadon an nunawa duniya Wai takai budurcinta ga mijinta ko bata kaiba, wannan matsalar itace take damun Mai martaba saboda a auransa na farko da safe da aka koma baa samu wata shaida da take nuna Gimbiya Amna ta kawo budurcinta gareshi ba nan akayita yamadidin zance abun yaso ya zama matsala daqyar Marigayi Mai martaba mahaifinmu ya tsawatar maganar ta lafa amma abin yana zuciyar Hajiya Sogiji da Gimbiya Amna saboda ita Gimbiya Amna yar yayar Hajiya Sogiji ce wannan dalilin yasa tunda abin ya faru suke gaba da kowa a gdannan damma Yaya yana takawa matarsa birki bata samu yadda takeso a gurinsa ba gata da masifar kishi ko bayi mata taga Yaya yana bawa umarni sai taho fushi dashi wannan dalilin yasa yaqi sanar da ita zaiyi aure sai ranar daurin auren aikuwa tun jiya take hauka har yau jiya ma cewa da ita yayi idan ta sake ta fito taje inda aka saukeki a bakin auranta so saboda son da take masa yasa bata zoba”


Ajiyar numfashi Farha tayi tace “tabdi iska tana wahal dame kayan kara toni aida yabarta tazo wlh rotse zanyi mata irin wanda nayima motarsa shi kansa mijin nata tsoron bala'i na yake bare wata ita karan kada miya” dariya sukayi suka zauna sukaci gaba da hirarsu sunata bata labarin abubuwan da suke faruwa cewa tayi “hmm ita Hajiya Sogijin nan bata sanni ba shiyasa nifa babu ruwana duk wanda yayi mini kan kara na itace nake masa” ranar yini sukayi suna hirarsu sai yamma liqis sannan sukayi mata sallama sukace zasu tafi binsu tayi suka nufi bangaren Surukan nata a parlour suka tarar da Hajiya fulani nan suka gaisa suka rashe sunata hira Farha nata bawa Hajiya labari tana dariya har lbrn haduwarta da Hafeez din ta bata suka rinqa dariya kamar cikinsu zaiyi ciwo Hajiya tace “kina da abin dariya yata shiyasa lkc daya Hafeez ya rikicemin yace aure zaiyi cikin sati daya” haka sukaita hirarsu har dare ya fara nisa ta fara jin bacci suka miqe suka nufi bangaren Hajiya Kilishi cewa sukayi ta shiga ta gaida Hajiya Sogiji amma fir taqi a daidai qofar Hajiya Sogijin sukayi karo da Amna kasancewar gdan tarwai yake tamkar rana dukkansu jada baya sukayi ita nata na tsoron jin ta buge mutum ne ita kuma Amna na tsananin mamaki ne ganin Hoton zanen data dade tana gani a turakar mijinta yau gashi gabanta a zahiri dafe qirji tayi tare da nuna Farha da yatsa tace.



“Wa...wace wannan meye ya kawota gdannan?” dariya Nadiyya tayi tace “yar uwarki ce maana amaryar Mai martaba ce” matsawa tayi da sauri kusa da Farha tana nunata da yatsa tana wani irin mugun huci shaqota tayi tana jijjiga ta tana cewa “ina qaryane wlh qaryane ace wannan itace kishiyata wannan ma ai abin kunya ne na nuna yarinyar nan nace itace matsayin matar da aka auromin matsayin kishiya shima Mai martaban yasan qarya yake, dama saboda dake ne mijina ya canzamin saboda dake ya juyamin baya saboda dake yakemin duk wulaqancin da yakemin a gdannan nayi tunanin

Please Login or Register in order to submit comment