Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take.



*ASALIN LABARI*



Yau litinin ce tun asuba Farha ta tashi tayi wanka ta shirya domin zuwa makaranta 7:24am ta gama shirinta tsaf ta fito gaishe da iyayen nata tayi ta miqe zata fita Ummah tace “bakici abinci ba zaki tafi" yatsina fuska tayi tace “kin manta yau litinin azumi nakeyi" tana fadin haka ta juya ta fice a qofar gdan suka hadu da qawarta Binta suka rankaya suka tafi.


A hanya take bawa Binta labarin abinda ya faru jiya dafe qirji Binta tayi tace “Allah ya taimakeki Farha kin tako saa wlh har Sarki Hafeez da kansa yace yanason auranki gsky nayi miki murna ke nimafa da zaayimin aurennan wlh so nakeyi” tsaki taja tace “qyale tsinanne wlh na tsaneshi baki ganshi ba jiyafa da naganshi ido da ido a gdanmu wani garnaqeqe dashi wlh qirar samudawan farko ne dashi wannan matarsa ta shiga uku aini wlh tsoronsa zankeji idan ya tsaya a gabana saifa ajera irina goma sannan zasu taba kansa” dariya Binta tayi ita kuma ta daure fuska tace “wato dariya ma nake baki ko?” dariyar dake cinta ta guntse tace “to ai kece da abin dariya Wai garnaqeqe koma dai ya yake kinsan babu fashi tunda ya furta saiya aiwatar ni bama wannan ba Farha karatunki fah keme burin zama Dr?” idanunta ne ya kawo ruwa cikin sanyin murya tace “ai guduwa zanyi a nemeni a rasa kamar yanda Samiran gdan Ali me dawaki tayi kinga ai kowa ya ma huta ko?” kallonta tayi da sauri daidai lkcn da suka shiga cikin makarantar tace



“Tabdi kinaso kema ki batawa kanki dasu Baffa suna kenan a rinqa cewa dake karuwa yarinya idan ma kin gudu bazaki tsira ba wasune a banza zasu lalata maki rayuwa garama ki tsaya ki auri Sarki ko ba komai zaake kiranki QUEEN FARHA matar sarki kuma muma ma dangwali arziki hange fada daga nesa ya kau tunda kina cikin gdan sarauta muma dole wata rana mu shiga kuma fah bakisan want abuba shifa Sarki Hafeez ance duk sati a makkah yake sallar juma'a....” nuna Binta takeyi da hanu tana dariya har saida takai qasa tsayawa Binta tayi sororo tana kallonta ganin ta janye hanunta daga kanta tana nuna want guri yasata saurin kallon inda take nunawa,



Qululuuuuu cikin Binta ya bayar ganin tawagar fadawan da suke nufosu sauke idonta tayi akan shugaban zugar sanye yake da jar alqabba da jan nadi komai na jikinsa jane hatta kwagirin hanunsa, qasa tayi da idonta cike da mugun tsoron ganin ya tsaya kusa da qafafun Farhan da har yanzu bata daina dariya ba, jikin Binta har bari yake jira kawai take taga dogaran sun rufesu da duka amma ga mamakinta sai taga ya rusuna ya sanya gaya hanunsa ya dagota duk da idanunsa cikin baqin glass suke amma kowa dake gurin yasan ita yake kallo, sake kallonsa tayi harda yin dage saboda ta kalleshi sosai kuma fashewa tayi da dariya cikin dariyar qeta tace.


“Ai ni bantaba addu'a Allah bai karba ba wlg jiya nayi addu'ar Allah yasa ka makance ka kuturce ka gur.......” tsawa dogaran suka buga mata wadda tasata wata muguwar razana ta fada jikinsa ta shige cikin alqabbarsa tana cukuikuiyeshi tana fadin “Allah ya isana ban yafeba da kukasa cikina ya qulle da muryoyinku masu kamada duro eh din an fada Sarkin naku ya gurgunce idan da wanda ya isa yazo da tabani a jikin wannan basamudai yaga yanda zai zama gari yanz.....” sake qanqameshi tayi ganin wani dogari ya zaburo yana ihu yana cewa.



“Allah yaja kwanan sarkin duniya fushin Mai martaba ya tabbata akan mara kunyar yarinyar nan...” shigewa ta kuwayi tsakanin qafafunsa ta tsuguna tana fadin “wayyoh! shikenan zasu kasheni da yar service wayyoh!! Wayyoh Baffana” baisan lkcn da murmushi ya qwace masa ba, daga masa hanu yayi da sauri ya dakatar dashi zubewa yayi a qasa yana buga kansa da kasa yana fadin “tuba nake adalin Sarki mai zamani haqiqa ni bawanka ne me tuba da neman yafiyarka Allah ya taimaki Mai martaba sarkin talakawa”


Damqar hanunta yayi da qarfi har saida qashin hanun yayi qara ya fizgeta ya nufi staffroom din principal din makarantar doransa suna binsa yana shiga ya watsata ciki ya juya yayi tafiyarsa, hanunta take karkadawa tana hawaye tana murguda baki saida yayi nisa ta dago ta kalli inda yake tace “mugu kawai Allah ya isan wanda bashi da qirar samudawa yasin da nima basamudiya ce da rangwashi daya zanyi maka na huda kanka qwaqwalwar ka ta tarwatse ta watse” shidai principal din bai kulata ba harta gama kukanta da ihun hanunta zai cire ta tashi zata fita har taje bakin qofa ta juyo tace “kuma wlh saina fadaka da Sarki nace daya kawoni ko sannu bakace min ba kuma dole mutum yacemin QUEEN FARHA MATAR SARKI HAFEEZ ehee ko mutum yayi ta aikinsa” miqewa yayi ya zari bulala ta diba a guje ta shiga Class dinsu ta shige qarqashin bancinsu.

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*





🅿3⃣



Ta jima a qasa a zaune tanaci gaba da kukanta tana matsa hanunta da yakeya yimata zugi shigowar malamin da zaiyi musu darasi ne yasa Rahmah leqawa tace “sai ki fito in kinga dama malam ya shigo” daqyar ta fito ta zauna har yanzu idanunta hawaye yake fitarwa, aiki ya samu mata ranar ko break bata fitaba kasancewar azumi takeyi amma bawai azumin ne ya hanata fita ba wai hanunta ne ya karye🤣 badan hakaba dako tsokana saita fita tayi sai qarfe biyu suke tashi lkcn da suka tashi suka fito suna tafe anata hira amma banda ita kowa mamaki yake yanda akayi jikin ta qaura yayi la'asar da wuri haka.


Binta ce da tasan komai ta dubeta tace “amma mutumin nan mugune kinga yanda hanunki yayi ja kuwa anya ba gdan madora zamu wucce ba” matse qwallar idonta tayi tace “qyaleshi macuci aini dayasan muguntar da zaiyimin kenan dama bari yayi wadannan wahalallun dogarawan nasa suka kasheni kuma wlh bazan yafeba bashi yaci Allah saina rama saina tsige masa gashin hammatarsa da daidai” dariya ce takecin Binta amma babu halin yi tasan yanzu zata sauke kwandon jarabarta akanta haka suka rabu kowacce ta shiga gdansu saida ta tsaya a soro ta qara qaqalo kuka sannan ta shiga gdan tana shiga ta cire Jakarta ta ajiye ta fada gado taci gaba da kukanta tanata zabga Allah ya isanta, baby wanda ta samu ya kulata saboda sunsan halinta rarrashin ma baji takeba idan tanajin iskancinta da haka bacci ya kwasheta.



Bata farka ba sai qarfe uku da rabi tana tashi ta shiga wanka ta fito ta zura uniform din islamiyyar ta ta dauki qur'aninta da sauran littatafanta zata fita taji Baffa ya kirata daga dakinsa juyawa tayi ta shiga murmushi tayi tace “Lahh Baffa ai bansan kananan ba na dauka kana kasuwa" fuskarsa babu yabo babu fallasa yace mata “aa ina gda daga Giyyade na dawo yanzu akan mgnr auranki wakilan Mai martaba sunje sun sami su Baffanku Jafaru da Balaji sunyi mgn har sun bayar da dukiyar auranki shanu hamsin da sadaki dubu hamsin kamar yanda Baffanki Jafaru ya yanke musu” dagowa tayi da idonta da ya ciko da qwallah tace “wai dama da gaske kukeyi Baffa aure zakuyimin Baffa kaifa kake cewa ni yarinya ce kuma ma duk a qawaye na Salman gdan Hadi me raqumi kawai akayiwa aure gsky ni aa Baffa bazan yarda ba mugu ne fah dazu qaryamin hanu yayi a makaranta danma nidin qashi dayane dani danayi bacci ya hade” harta gama shirmenta kallonta yakeyi saida yaji tayi shiru sannan yayi gyaran murya yace “koma dai menene haka zakiyi hqr dashi tunda shine zabin da Allah yayi miki kuma ya kafa maki dokoki yace daga yau bayason qara ganinki a waje saboda akwai barazana a cikin fitar zaa iya daukeki idan akasan kedin zai aura yace yaje makarantar bokonku yau sunyi mgn da principal dinku zaa zana miki jarabawa a cikin wadanda zasuyi jarabawa wannan shekarar in yaso idan kina raayin cigaba da karatun sai kici gaba a gdansa saboda haka kije ki cire uniform dinki yace anjima zai turo a daukeki zaa kaiki tallar da zasuyi dunkunanki su ganki”



Dagowa tayi zatayi mgn ya katseta ta hanyar daga mata hanu yace “umarni aka bani nima umarni nake baki tashi maza kije ki shirya” miqewa tayi a salube ta fita daga dakin tsayawa tayi a jikin dakin tana share hawaye tana cewa “Allah dai ya sakawa wanda aka zalumta kawai azzalumai masu ci da rawani shi ko kunya bayaji yanda yake kaya gudannan yace waini zai aura maji dai ma gani ai nasan yanda zanyi dakai”
Shigewa tayi dakin ta kwanta tare da Kiran almajirin da yakeyi musu aike tace yaje yace da Binta bazataje makarantar ba makiri algungumi yasa Baffanta ya hanata zuwa ko ina.



Da yammaci wajan misalin 05:37pm Baffanta ya kirata yace taje ana jiranta a waje, saida ta gama yauqinta sannan ta fita tsayawa tayi a qofar gdan nasu tana qarewa motar dake parking kalloh qirar Hunday baqa wulik har sheqi takeyi kamar an shafa mata mai jitayi an danna mata horn tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin ta fara takawa a yangance har ta qarasa jikin motar ta tsaya, bude mata akayi kamar bazata shigaba saj kuma ta tuna da kashedin da Baffa yayi mata, kama murfin tayi ta qarasa budeshi ta shiga ta zauna tare da rufowa tace “bismillahi Allah ka rabamu da yan gangan da gangancin qarya” juyowa tayi ta kalleshi tare da dafe qirjinta tace “na shiga uku dama kaine naga cewa kayi da Baffa na turowa zakayi a daukeni a kaini” lumshe idonsa yayi tare da dawo da kallonsa kanta ya zare glass din idonsa ya ajiye yanda ta zuba mishi ido tana qissima irin mutumin da zata kwatantashi dashi a jerin yan film din India ne yabashi damar zuba idanunsa cikin nata.


Da sauri ta dauke idonta tayi qasa da kanta cikin rawar jiki da muryar tsoro tace“ni ka daina kallona da idonka gsky ni banason sa ido” ya jima yana kallonta cike da mamaki wato shine ma yasa mata idon kenan, lasar lips dinsa yayi tare da yima motar key yayi ribas suka bar unguwar suna tafi tana addu'a saboda gaba daya a tsorace take gaban wata Plaza yayi parking ya dauki wayarsa ya kira wata number “Yeah” kawai taji yace ya ajiye wayar ya kwantar da kansa a saman kujera inda ita kuma take satar kallonsa ganinta take wata yar tsakuwa a kusa dashi, qwanqwasa qofar motar akayi batare daya dago kansa ba ya bude mata qofar yace “kije ki dawo” yanda yayi mgnr ne yasata saurin kallonsa “wato ita kanta mgnr ma dole yakeyinta” hanunsa ya daga tare da nuna mata waje ta zura qafafunta qasa ta fita suka jera da wata mata da alamun itace tazo tafiya da ita suka shiga cikin Plazar rarraba ido takeyi ta kalli nan ta kalli can ji tayi an dafata ance.



“Ranki ya dade ana mgn” juyawa tayi ta nufi inda ake kiran nata kasancewar gurin duk mata ne yasa ta saki jikinta aka gwadata sosai sannan matar data shigo da ita ta kuma kama hanunta suka nufi wani bangaren daban nan kuma bangaren gyaran gashine da wankin qafa da gyaran farce mamakine ya cikata ta tsaya tana kallon ikon Allah ji tayi matar tace “Ranki ya dade idan ba damuwa ki zauna a tsefe miki kanki” zaro ido tayi waje tace “kam bala'i tabdi yasin aa damuwa ma qatotuwa toni bari kiji tunda nake kosu Rahama basu taba tsefemin kaina ba Ummah ce take tsefemin balle naba wasu da bansan su waye ba su tabamin kaina”


Murmushi tayi tace “kiyi hqr umarnin Mai martaba ne wannan saboda haka dole ki bari ayi miki" zatayi mgn tace “aa ranki ya dade hakan fah zaayi” haushine yasata cizge dankwalin kanta tace “nifa kaina a tsefe yake ma dan kuji" dukkansu saida sukayi dariya wacce taji an Kira da Manah tace “gaki da gashi ranki ya dade nicema zan wanke miki kan muje ai yanzu zaa gama miki” babu yanda zatayi saboda taga sun fara kawo mata rainin hankali shiyasa tabita suka nufi wani guri na musamman gefe kuma wani qasan gurin glass ne ruwa da wasu qananun kifaye tarwada suna yawo a ciki rintse idonta tayi tana salati murmushi Manah tayi tace ga guri zauna mu jefi tsuntsu biyu da hoge daya tsugunawa tayi ta cire wasu yan robobi a jikin glass din daidai qafar Farha wata a gurin ta taso ta dauko wani Mai zata shafa mata a qafarta tayi saurin janyewa tace “to ita kuma qafar me zaayi mata?" Kallonta Manah tayi tace “zaa shafa miki wannan manne sai ki zurata cikin ruwannan maana wanketa zaayi sai ayi miki lalle”


Qurawa ruwan ido tayi tana ganin kifayen da suketa wutsil² ta kalli Manah tace “kuma a cikin ruwannan?" Daga mata kai tayi numfashi Farha ta sauke tace “kuma da wadannan kifayen a ciki?” sake daga mata kai tayi, murmushi tayi tace “aa wlh banaso ku barshi idan naje gda zan wanke da soson gogewa ni qafata ma bata faso bata kaushi wannan ma ai salon jawa kai jafa'i ne to kuma yanzu idan suka gutsire min qafa sai nace me?” dariya sosai sukeyi mata daya cikin ma'aikatan gurin ta sanya qafarta a ciki taga yanda kifayen suka taso suka yanyame qafar tata suna lasa sai kuwa ta zunduma ihu tana ja da baya, daqyar suka shawo kanta ta bari akayi mata wani wankin qafar daban amma fir taqi yarda da wannan na kifayen.


Amma fir taqi yarda da lallen shima tace ita bataso dole suka qyaleta Manah ce ta sake rakata ta bude mata motar ta shiga yaja suka juya suka fita daga Plazar ba gida sukayi ba wani guri ya kuma nufa wannan karonma bai fita ba wayar ya kuma kira wani mutum ya fito ya russuna ya kwashi gaisuwa sannan ya bude bayan motar ya ajiye ledar dake hanunsa ya juya ya tafi yaja motar Suma suka tafi, cike ta mamakin lamarinsa shi bakinsa ko tsami bayayi tunda suka taho bataji yayi mgn ba saida Eh ko Aa tabe baki tayi tace “Allah dai ya kyauta bama dole mutum yayita hawaba mgn ma bazaayi ba saikace kurma nifa natsani mutum mai girman kai wlh yo akwai wani sarki ne a duniya bayan Allah sarautar ma...”damqar da yayiwa hanunta ne yasata hadiye mgnr tana fadin “wayyoh Allah zai qarasa kasheni aini dama nasan badan Allah ka daukoni daga gdanmu ba wayyoh kayi hqr jijiyar da qashin duka sun karye” bai saki hanun nata ba kuma baiyi mata mgn ba har yayi parking daidai qofar gdan yanayin parking takai hannunta zata bude yayi saurin danna mata key tare da finciko ta ta fada jikinsa ya damqin gashinta da daya hanunsa yaja da qarfi, qara ta saki tana jijjiga masa kan mgn takesonyi amma ta kasa sai hawayen da take zubarwa bai saketa ba saida yaga ta jigata tukunna ya sakar mata kan nata tare da bude mata qofar ta fita da sauri har tana faduwa zagayawa tayi daidai inda yake zaune fuskarta sharkaf da hawaye tace “Allah ya sakamin mugu kawa...” motsawa yayi kamar zai bude murfin motar ta kwasa da gudu ta shige cikin gdan murmushi yayi tare da Kiran wani yaro ya bashi ledar da suka karbo yace yakai mata ciki.



Tana shiga ta fada dakinsu ta fada saman katifa tasa kuka tana fadin “wlh duk abinda kayimin bashine akwai ranar dazan rama don bazan taba yafe maka ba kaci banza mugu kawai” shigowar yaronne dakin yasata dagowa ta haushi da masifa tace “munafiki ubanme kazo yimin anan" cikin tsoro yaron ya miqa mata ledar yace “wani ne a waje yace na kawo miki” fuzgar ledar tayi tace “mugu kawai ai wlh bazan mayar masa ba yaci banza” tana mgnr tana zazzage ledar tarkacen turaruka ne sai kwalin biscuits da chocolate sai wata qaramar ledar aciki ta daukota itama ta bude kwali ta gani a ciki ta zaro kwalin tana dubawa Rahmah ce ta shigo ta kalleta tace “ina kikaje ne" turo baki gaba tayi tana bude kwalin tace “yawo naje munafukai masu zuwa lahira da qoqon dambu to mijina ne yazo mukaje yakaini wai aka gwadani harda wankemin kai akayi kuma aka wankemin qafa kingani ma" ta fada tana daga mata qafar hanu tasa ta shafa tace “lahhh kinji yanda qafarki tayi laushi Farha wannan kuma menene a wannan kwalin?"


Miqa mata tayi tace “nima bansaniba mugu kawai har yanzu kaina zafi yakeyi...” maganar ce ta maqale ganin abinda Rahmah ta zaro a cikin kwalin da sauri ta miqa hanu tayi ta fusga tana qare mata kallo waya ce sabuwa dal qirar I phone 7+ tsalle tayi ta rungume Rahmah tana dariya tace “yehh nima na zama babbar yarinya na faso gari wlh zan tsula tsiyata son raina nima sai na rama rashin mutuncin da Zainab Shattima tayimin kwanaki akan wayarta" dariya Rahmah tayi tace kedai a ramuwa zaki qare Farha ki tashi kije ki dauko abincin ki a kitchen” yatsina fuska tayi tace “tabdi ai na daina cin abu me nauyi ni yanzu kinsan ance matan manya basacin abu me nauyi daga cake sai ice cream sandwiches da bugger and sweet cheeks chocolate something let that dai kindai gane ai” dariya sosai Rahmah takeyi harda riqe ciki wato ita gaba daya ma bata fahimci abunda ake nufi da auran ba saida ta qama dariyarta sannan tace


“Waike Farhanah idanma anyi miki auran me zakije kirinqayi a gdan mijin naki?" Dariya tayi harda tafa hanu tace “lallai ma kin rainani to bari kiji na lissafo miki zanke girki wanke² shara kula da dakuna na da wanke bandakuna sannan zanke gyara shimfidar mijina kamar yanda malam Nuhu yace mana nifah baki sani ba cewa zanyi da Baffa kada ya siyamin gado iya katifa ta isheni saboda qatoto ne mijinnawa sannan katifa biyu zaa siyamin tawa da tasa yawwa kuma yace zanci gaba da karatuna a gdansa” murmushi Rahmah tayi tace “kinsan wani abu idan fah akayi maki aure yarinya mijinki zai iya taba ko ina a jikinki kuma zai iyayin komai dake yarinya”


Juya mata baya tayi ta kwanta tace “keni fah koma me akeyi zan iya indai ba dambe bane keko damben ne da cizo da yaqushi zan qwaci kaina” dariya Rahmah tayi tace “aa babu batun dambe a wannan harka soyayya ce zaa shata madararta bare ke da kike da abun badawa" dariya sukayi dukkansu sukaci gaba da hirarsu har bacci ya daukesu, da safe tana gani suka shirya suka tafi makarantar amma banda ita tanaji tana gani saidai ta kwanta tayita bacci tama manta da wata waya tunda ta mayar da ita kwalin ta ajiye bata kuma bi ta kanta ba, tun saura kwana hudu aka fara shirye² a gdan nasu yan qauyensu duk sunzo gdan ya cika sosai.


A gdan sarautar ma haka abin yake shagali akeyi sosai qofar fada ta kacame kilisa aketayi a tsakanin gdan sarki da filin sukuwa baqi sun cika garin sosai inda aka qawata lungu da saqo na gdan sarautar daga gdan sarautar aka tura mai gyaran jikin amarya take gyara Farha biki fah yayi biki gari yadau harami ranar alhamis ne yakama zaayi kamu qaton Hall ne na gani a fada aka ware musamman saboda kamun sai qarfe bakwai na dare motoci sukazo suka dauki amaren zuwa gurin da zaayi kamun saida aka takura mata sannan ta yarda suka tafi goma da rabi suka gama bidi'o'insu injita da fada aka kuma dawo dasu gida suna zuwa ta cire rigarta tayi jifa da ita ta daura zani tace “haba dan masifa a qaqabawa mutun riga sai cizona takeyi yasin bazan qara sanyata ba ranar juma'a sukayi traditional day shima ba qarya an kashe daloli wajan shirya komai sudai bangaren amarya saidai ace musu zaaje guri kaza zaayi kaza saboda abun na masu garinne asabar ce ta kama ranar da zaa daura auren tun safe data fahimci da gaske dai auran zaayi mata take kuka har qarfe biyu aka daura auran a masallacin fada daurin auren da ya kafa tarihi me tarin yawa a garin Bauchi saboda ko auran Sarki Hafeez na farko bai nuna farin cikinsa kamar wannan ba da wanda ya isa da wanda bai isaba a wannan rana miqa masa hanu yake su gaisa lamarin dayake baiwa kowa mamaki da yawan mutane abinda suke ayyanawa a ransu lallai so gamon jinine shikuma duk girman kansa da izzar mulkinsa Farhanah ce tayi masa duk cikar garin Bauchi, ga wadanda sukasanta kenan wadanda basusanta ba kuma suna cewa ita kuwa wace wannan me saa data saqalo rayuwar Isasshen Sarkin da baya ragawa kowa.




*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers.)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com




🅿4⃣



02:00pm aka daura auran 3:30pm jerin gwanon motocin daukan amaryar sukazo tare da kawo kayan lefe kayane na gani a fada babu qarya an zuba naira cikin lefen Farha iyakar ganin me kallo bazai iya qididdige adadin kayan dake cikin akwatunan lefen ba sarqoqi kawai da aka zuba mata na gold sunkai bakwai hakanan badan an gama ganiba aka fito da ita sanye cikin Alqabba milk colour tayi kyau matuqa kamar dama ahlin abun kanta qasa tanata sharbar kukanta wanda ta yini aikinsa Ummah ce ta riqe hannunta har turakar Baffanta ta tsuguna daidai qafarsa tana qarawa kukanta sauti wai don yaji tausayinta yace yafasa aurar da ita, dago kanta yayi da hanunsa yana girgiza mata kai yace.


“Kiyi hqr Farhanah bawai don bama sonki zamu bayar dake a tafi dake ba aa saidon babu yanda zamuyi haka Allah ya tsara mana tun farko kece zaki riga yan uwanki tafiya dakin mijinki Farha banason jayayya da lamarin ubangiji shiyasa na yarda da aurannan naki amma nasan akwai manufa a cikinsa duk da manufarsa ba haramtacciyar manufa bace amma naso ace ba kece wacce kika zama sirrin manufarsa ba kiyi hqr kiyiwa mijinki biyayya kuma ki zauna da kowa lfy kinga dai yanda Allah yayi dake kin taso gdanku daga ke sai yan uwanki da baku zarta shidda ba gaba daya gdanku mutum tara ne yanzu kuma zaki koma babban gda da yake dauke da mutane sama da dari kuma kowanne da halinsa kowanne da iyayensa saboda haka dole ki nutsu ki gyara takunki karkice zaki tafi da shirman nan naki gdan sarauta zakisha wahalar rayuwar cikinsa kuma karkice zaki dauki girman kai da izza irinta makusanta Sarauta zakiyi baqin jini kuma zaki fuskanci wulaqanci da gori ki tsaya iyakar huruminki na mata babu ruwanki da duk wani abu daya shafi sarauta idan kikayi haka zaki zauna lfy da kowa”


Numfashi yaja tare da sakin kanta yace “tashi kije suna jiranki Allah yayi miki albarka ba kareki daga sharri da makircin gdan sarautar garinnan” kama hanunta Ummah ta kumayi ta fita da ita har tsakar gdan ta damqata hanun Jakadiyyah kamo hanun Rahmah tayi ta rungume ta suka fita dukkansu suna kuka, baa dauki wasu mutane da yawaba mutun shidda ne manya sai yan uwanta guda biyu da qawarta Binta suka shiga motocin suka nufi gidan sarautar tun kafin su qarasa ta fara jiyo bushe²

Please Login or Register in order to submit comment