Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba yayiwa mutum mai daraja irinka kyau kaji?" Ajiyar zuciya yayi ya sake hadeta da jikinsa jiyake kamar ya raba jikinsa ya shigar da ita yace “Queen kukanma kansa yakeyi ina cikin farin cikin da babu abinda ya kamaceshi sai kukan baby bushara akayimin yau ni Hafeez nima na kusa zama uba ta dalilin ki zanyi sanadin zuwan wani duniya Farha am very happy Queen na kusa zama uba nima kin kusa haifamin baby Farha cikina ke gareki ya zanyi na nunawa Allah gdy ta idan banyi kuka ba” qanqameshi tayi ta saki kukan itama tanajin qaunar mijin nata na huda jininta tana shiga Sarki Hafeez dabanne a cikin maza ya iya kula da mace da nuna mata qauna, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta koma ta kwanta tana shassheqar kuka sake matsawa yayi ya riqo hanunta yace “why you crying Queen?" Lumshe idonta tayi ya rinqa zagaye idon nata da hanunsa har yakai bakinta yasa hanunsa cikin bakinta ta rinqa tsotsa a hankali yanajin wani dadi, sake tambayar ta yayi dalilin kukanta a kasalance ta kalleshi tace “kawai naji nima ya kamata nayi kukane saboda kasancewata wadda Allah ya zaba na zama uwa ga yayan Sarkinmu Hafeez a lkcn da duniya bata taba zataba amma ya akayi haka Mai martaba nifah bantayin haila ba kuma malamanmu sunce sai mace tana haila sannan take haihuwa” murmushi yayi yana kallonta har tayi shiru sannan yace “sa'ata ce a haka cikin watan da zaki fara period na sanki qwan da zan mutu ya fita a matsayin jinin haila saiya koma a matsayin da kinsan alfarmar da nake nema a gurinki?" Kada masa kai tayi alamar aa yayi murmushi yace “ki kulamin da kanki da dana dake jikinki kinji?" Daga masa kai tayi alamar eh yayi murmushi yace “I love you so much" dariya tayi ta rufe idonta shima yayi dariyar yace zakiyi bayani ne yarinya" miqewa yayi ya dagota yace tunda babyna ya hanamu yin dinner mu tashi mu tafi gdanmu mu huta" yafa mata mayafinta yayi ya rungumo ta jikinsa saboda ya lura bata da qarfi a jikinta kamar ma jiri takeyi suka fito nan fah mutane suka rinqa tasowa sunayi masa Congress yanata washe baki yana amsawa cike da murna har suka isa gurin motarsu suka shiga driven yaja suka tafi gda.


Suna zuwa ta kwanta saboda hajijiyar da takeji shima shigowa yayi ya kwanta kusa da ita ya janyota jikinsa yana shafa cikinta yanajin wani farin ciki a ransa wayarsa ya dauka ya kira Hajiya bugu biyu ta daga suka gaisa yake fada mata samuwar cikin qwarai tayi murna tayiwa Allah gdy sannan ta bashi shawarwari sosai na yanda zai kula da ita yaji dadi yayi gdy suna shirin aje wayar Asiya ta fusge tace “Yaya kace da Aunty Farha ta haifa mana kyakkyawan yaro me kama da ita don Allah yaushe ma zaku dawo wlh part dinku zan dawo muyi rainon babynmu tare" murmushi yayi ya kashe wayarsa saboda shirmen Asiya yayi yawa lkcn daya gama wayar har tayi bacci baiyi qoqarin tashinta ba ya shiga bathroom yayi wanka ya rage qarfin A.C dakin ya kwanta tare daja musu blanket bayan yayi musu addu'a.


Saida suka qara wata uku a birnin London suna rainon cikinsu baya barinta ko wanka tayi da kanta komai shine yakeyi mata hatta abinci bai yarda taci da kanta ba lkcn da cikin ya shiga wata na hudu ne ya fara fitowa aka fara ganinsa masifar ji yakeyi da cikin ko bacci zaiyi hanunsa yanakan cikinta shi kadai zai zauna yayita mgn da abinda ke cikinta itadai saidai tayi dariya kawai, abinda yafi burgeshi da Farha yanda ta saki jiki dashi take nuna masa kulawarta da bashi duk abinda yakeso lamarin daya qara ninka girman matsayinta a gurinsa.


Watan cikin Farha biyar suka fara shirin komawa qasarsu Farha tayi wani fitinannan kyau haske da qiba sannan ta qara wani kwarjini na musamman ta cika sosai, ranar da suka dira a 9ja motocin gdan sarauta sukazo tarbarsu harda mataimakin governor a tawagar suka rinqa gaisawa da mutane kafin su shiga mota aka jasu zuwa gdan sarautar qofar fada ta kacame da kide² da bushe² Mai martaba ya dawo suna tafe yana dagawa mutane hanu cike da farin ciki suna shiga akayi parking tare da shimfida musu abin takawa suka rinqa tafiya a hankali kamar bazasu takaba ana watsa masu fure tare dayi musu kirari itadai dole take irin wannan tafiyar isar don tayi bala'in gajiya yaso wuccewa ya huta amma babu dama dole saida suka shiga part din su Hajiya fulani da part din Hajiya Sogiji suka fara suna zaune itada Amnah da Umaima sai bayin da suka kewayesu anata zuba mulki suka shigo tunda suka shigo idon mutane ukun yake kanta musamman Amnah da take qara zaro idonta waje tanason gasqata abinda take gani, miqewa tayi da sauri ta zata nufi inda suke Hajiya Sogiji ta ruqota da qarfi ta koma ta zauna itama Hajiyan idonta nakan cikin Farha daya fara turawa duk da yabi jikinta amma hakan bai hanashi dan dagowa ba daga cikin alqabbar dake jikinta.


Kujera ya samu ya zauna ita kuma ta tsuguna a qasa saman carpet duk da baiso hakan ba saboda bayason tana abinda zata takura amma bai hanata ba ta qwace hanunta tace“sannu da gda Hajiya mun sameku lfy” wani yawu ta hadiya me daci tare da daga mata hanu tace “lfy" daga haka bata qara cewa komai taci gaba da taunar apple dinta juyawa tayi suka hada ido da Amnah da takeyi mata kallon qurullah miqewa yayi ya juya zai fita yace “ki taso muje" miqewa tayi tabi bayansa suka nufi bangaren Hajiya Kilishi tayi murna sosai da ganin Farha ta rungume ta tanata yimata sannu tana tambayarta jiki.


A bangaren Hajiya Sogiji kuwa suna fita ta dubi Amnah ta qudduma uwar ashariya tace “ciki? ciki fah nagani a jikin wannan makirar yarinyar Amnah bantan ubancan billahil azeem bata isaba dole ko sunaso ko basaso kece uwar Yariman masarautar nan ” kuka ta sake saki me gunji tana cewa gsky da sake Hajiya cin mutuncin yayi yawa yana sane ashe yaqi yimin ciki saboda ni ya tsaneni to wlh bazai yuwu ba dole ma asan yanda zaayi Hajiya tun farko kece kika ja mini wannan masifar tun lkcn da aka kawota gdannan nace mu dauki mataki amma kikace mu kyalesu kinada tabbacin bazai taba haihuwa ba yanzu ga irinta nan..." Ta qarashe mgnr cikin kuka kamota Hajiya Sogiji tayi tace “ki kwantar da hankalinki wlh nayi miki alqawarin bazan barki ki koka ba kamar yanda Hafeez yasaki kuka to shi saiya mutu yana kokawa kawo kunnenki kiji wani abu” miqa mata kunnen tayi sai kuma suka kwashe da dariya tare da tafawa.


Saida suka zauna sukayi dinner a bangaran Hajiya Kilishi sannan sukayi mata sallama suka tafi part dinsu an gyara mata komai tsaf tana zuwa kwanciya wanka tayi ta canza kayanta zuwa na bacci tayi sallah tayi azkar sannan ta koma ta haye gadonta ta lafe bayan ta kulle qofarta baccinta me dadi ya dauketa, shima bayan yayi wanka ya kwanta har ya fara bacci yaji ana danna qararrawar dakin remote din ya danna ya qofar ta bude saboda yariga yasan wacece me bugawar shigowa tayi ta zauna a gefen gadon jan blanket yayi ya rufe jikinsa, dubansa tayi tace “mgn nazo muyi dakai" sake shigewa yayi cikin bargon yace “ki adata mayi da safe yanzu bacci nakeji idan kin gama ki rufemin qofar na gaji da yawa bacci nakeji” haushi ne ya kamata tayi kamar ta miqe ta fita amma babu hali saboda tana buqatar kasancewa dashi sosai, shigewa tayi cikin bargon ta kwanta tare da tura masa qirjinta tasa masa kuka tace “tunda kayi aure ka watsar dani ka daina kulani rabonka da kusanta ta tun kafin ka fara neman auran munafukar yarinyar na...” daga mata hanu yayi yace “idan abun daya kawoki kenan to ki tashi ki ficemin dagani kullum saina fada miki ki rinqa iya bakinki akan Farha amma baki fahimta matata dana aureta saboda inasonta kuma matsayin ta ya dada daukaka itadin uwar yayana ce”


Shiru tayi masa saboda bazata iya jure wannan cin fuskar tashi ba itadai burinta ya biya mata buqata shigewa ta kumayi jikinsa yasan inda ta dosa saboda haka ya biye mata badon yanaso ba saidon sauke haqqinta dake kansa babban abinda yake damun Hafeez da Amnah bata damu da biyan buqatar sa ba indai tata ta biya shikenan ga rashin kula da ni'imar jikinta a cikin wata biyar dinnan da basa tare ya kamata ace tayi abinda zai manta kansa idan ya shigeta Farha ce kawai take yawo a zuciyarsa tunda ya aureta ranaku daidai ne baya kusantarta amma kullum ya shigeta sabuwa yake jinta gata da saurin daukan move daya dorata ta hau ta zauna harma ta fisa zaqewa sometimes idan yana tare da ita mantawa yake da yanada wata macen bayanta yau duk jinsa yake kamar wani mara lfy, wayarsa ya dauka ya rubuta mata dan gajeran saqo me cike da kalmomi masu kwantar da hankali lkcn itama ta farka juyi kawai take da tunanin mijin nata taji qarar saqon dubawa tayi ga mamakinta sai taga ashe shine murmushi tayi bayan ta karanta saqon itama ta rubuta masa amsa a gajarce ta tura masa ko minti daya baayi ba kiransa ya shigo wayarta ta daga da sauri tace “hello” ajiyar zuciya ya sauke yace “meye ya hanaki bacci My Queen?" A sanyaye tace “ kewarka Mai martaba yau jina nake cikin wani sabon yanayi na saba kwanciya tare dakai duk juyi da zanyi a jikina nakeyinsa amma yau saini sai pillow na kasa bacci wlh King Hafeez nakasa jurewa rashinka bansan jikina da zuciyata sunyi irin wannan mugun sabon dakai ba sai yau...” ta qarasa maganar cikin kuka


Hankalinsa ne ya tashi ya miqe da sauri yace “ya Salam ki daina kuka don Allah ganinan bari nazo nasaki bacci yanzu” bai jira cewarta ba ya miqe ya dauki boxes dinsa yasa ya leqa fuskar Amnah yaga kamar bacci takeyi baisan bakam tayi masa tanajinshi ba yayi murmushi tare da ja mata bargon ya bude qofar a hankali ya fita yana zuwa ya dannan qararrawar dakin tana zaune saman sallaya ta miqe ta bude masa shigowa yayi ya mayar da qofar ya janyota jikinsa ya hadata da qirjinsa suka sauke ajiyar zuciya lkc guda ya dagata cak ya dorata a gadon ya kwanta shima ya matseta a qirjinsa yana hura mata iska a kunnenta yana fuzgo numfashi daqyar ya dauki hannunta ya dora a kansa ta tura hanunta cikin sumarsa ruwa taji cikin sumarsa ta zare hannunta ta fara qoqarin zare jikinta qara matseta yayi yace “bacci nakeso kiyi Queen baby ya gaji yana buqatar hutu” ajiyar zuciya tayi tace“ruwa naji a kanka” shafo fuskarta yayi yace “yayarki ce ta sani wanka maza yi baccinki don Allah ina tausayinki da babyna” bata kumayi masa mgn ba ta kwanta luf a jikinsa zuciyarta na tafarfasa “ashe da gaske dama haka akeyi kamar yanda yake kwanciya da ita suyi wanka itama Amnah haka ya kwanta da ita?” wasu hawaye ne suka zubo mata masu zafi tayi saurin gogewa saboda bataso ya fahimta jitayi ya dagota ya juyar da ita ya hau samanta yasa harshensa yana lashe hawayen nata yace “kishi ko Farha kema kinada irin wannan kishin ashe Farha mene abin damuwar kinsani kece nakeso kece rayuwata kece farin cikina don Allah kada kema ki dauki wannan halin ku hanamin kwanciyar hankali plz Queen na roqeki”.......






Please Comments
Share and Vote






*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿🔟



Kuka ta saka masa tana qoqarin qwacewa a jikinsa amma ya riqeta ya dora mata dukkan nauyinsa ya hade bakinsu yana yi mata wani irin hot kiss yana qara zaqulo harshenta rintse idonta tayi ta dura masa yawu a baki duk dan ya saketa amma memakon hakan sai taji ya hadiye yaci gaba da tsotse mata bakin yasa hanunsa ya fara shafo nononta da ya qara wata muguwar cika numfashi yake saukewa da sauri yana qara matsa nipples dinta da suka miqe sunajin saqonsa daqyar ta iya qwacewa ta dira qasa tana mayar da numfashi sake biyota yayi ya qara matseta a bango yace “yau daya nayi missing dinki Queen help me pls...” ji sukayi ana dukan qofar kamar zaa balleta da sauri ta fincike daga hanunsa tace “don Allah ka taimakeni ka kyaleni wlh Allah na gaji babu kyau haramun ne....”



“Ku bude munafukai azzalumi Allah ya isa tsakanina dakai Hafeez wannan wanne irin wulaqanci ne da cin amana ka tsallakeni a daki ka dauko kwanana ka kawowa wata shegiya wlh Allah...” bude qofar yayi bai ankara ba tayi wuf ta fado dakin tayi kukan kura ta cafko Farha da take gefe ta shiga dukanta kamar Allah ya aikota tana qoqarin dukan cikinta ita kuma ta kare, da gudu ya qaraso ya finciketa yayi jifa da ita gefe ya qarasa ya dago Farha da taketa qoqarin tashi zaune jini ya gani a bakin Farha jikinsa ne ya dauki wata muguwar rawa ya juya ya fincike ta daga dakin yayi jifa da ita zuwa parlourn itama kanta ya hadu da tiles ya mayar da qofar ya rufe ya dago Farhan ya sanya hanunsa yana share mata jinin da hawayen qwacewa tayi daga jikinsa ta miqe da qyar zata shiga bandaki ya cafkota zubewa tayi a qasa ta saki sabon kuka tace “na roqeka don Allah ka taimakeni ka ficemin daga daki nan gaba kasheni zasuyi akanka Hafeez ka fita ka fice don girman Allah ka fice naceeeee"



Yanda take kukanne yasake tayar masa da hankali hanu yakai zai ruqota ta janye tana girgiza masa kai matsawa yayi gabanta yace “shikenan naji zan tafi kinga zo...zo ki kwanta wlh bazan iya bacci ba idan baki bacci ba” miqewa tayi ta shiga bathroom din ta kulle ta zauna taci gaba da kukanta bugun duniya yayi taqi bude masa magiya babu irin wacce baiyi mata amma tayi banza dashi duk ya susuce ya fita a hayyacinsa saboda tunda yake da ita basu taba samun sabani irin haka ba sai yau Amnah ta zame masa masifa saboda tsabar rashin adalci yanzu idan bai bawa Farha kulawa ba wa zai bawa? Badon ransa yaso ba haka ya fita daga dakin zuciyarsa na quna yana zuwa ya tarar Amnah tana zaune tanata gursheqen kuka bala'i ya hau surfa mata yana nuna mata girman kuskuren da tayi yace “yanzu kinje har part dinta kin daketa saboda haukan kishinki mezaisa ki daketa Amnah me zaisa ki dakarmin mata to wlh ki sani kuma ki rubuta ki ajiye duk abinda ya samu Queen da abinda yake cikinta billahil lazi La'ilaha illah huwa ki kuka da kanki kuma da wasa kika qara karambanin dukanta a bakin auranki saboda na lura ke mahaukaciya ce bakisan zuru ba shashasha kawai haka ake so a haukanki kinasona bakyason farin cikina to bari kiji na fada miki cikin jikin Queen shine cikon farin cikina saboda haka ki kiyaye"


Yana fadin haka ya haye gadon yayi kwanciyar sa yana doka uban tsaki yace “kuma tunda abun naki iskanci ne daga yau kwana daya zankeyi a bangaran kowacce saboda Farha ta fiki buqatata ita da abinda ke cikinta” yana fadin haka yayi shiru ya soma kiran wayar Farhanah tana ganin kiran nasa lkcn ta fito ta kulle dakinta ta haye saman gadon ta takure tanata aikin kuka tausayin kanta takeyi a cikin gdannan tun dazu da suka shiga part din Hajiya Sogiji jikinta yayi sanyi ta lura idan suka samu dama tsaf zasu kasheta saboda qarara take hangen qiyayyarta a qwayar idonsu, ranar da qyar bacci barawo ya saceta tana kallon kiransa taqi dagawa da asuba ma tanaji yana dannan ring belt din tanata qara tayi banza dashi saboda mugun haushinsa takeji gani take duk shine yaja mata wannan tsanar da yasan bai isa da matarsa ba meyasa ya aurota, data gajima da jin qarar saita tashi ta shiga bathroom ta hada ruwan wanka ta gasa jikinta duk da. Amnah batayi nasarar dukanta sosai ba amma jikinta ciwo yake musamman bayanta saida ta gasa jikinta sosai sannan ta fito tayi sallah ta zauna tayi azkar dinta ta koma ta kwanta sai takwas ta tashi ta sanya wata doguwar riga mara nauyi ta shafa powder kadan sannan ta nufi kitchen tana fitowa madu yimata hidima suka rinqa gaisheta tana amsawa tare da tambayarsu matsalolinsu wasu suka fada wasu kuma sukayi shiru ranar tayi musu rabon kudi bana wasa ba saboda ribarta da aka samu a Plazar ta tanada yawa tana kitchen din aminiyarta Binta ta kirata cikin murna ta daga suka gaisa take tambayar ta mutanen gda ta amsa mata da lfy tare da fada mata bikinta saura sati uku sannan ansa bikin yan uwanta Rahmah da Rahina sukuma saura wata daya da sati biyu tayi murna sosai tace “amma Baffa munyi waya dashi be fadamin ba?" Murmushi Binta tayi tace “ai yanda yaga Mai martaba yana yinki ne yasa yace bazai fada miki ba ki tashi hankalinki kice saiya dawo dake"



Murmushi tayi sukayi sallama ta ajiye wayar taci gaba da dama kunun cous-cous din bayan ta gama ta zuba a cup ta zuba madara da suger kadan ta dauko pepper soup din cow let din ta fito parlour ta zauna tare da kunna kayan kallon tanacin abincin tana kallo bayan tagama ta kwanta wata baiwa tazo ta debe kayan ta mayar kitchen daidai lkcn taji qamshin turarensa ya daki hancinta lumshe idonta tayi tanajin wani sabon bugun zuciya bataji isowarsa ba saiji tayi yasa hanunsa ya dago fuskarta suka hada ido ya sakar mata tsadaddan murmushin sa sanye yake cikin shigarshi ta alfarma da alamar fada zai tafi, qasa tayi da kanta saboda wani saqo da yake tura mata ta cikin idonta a kasalance tace “ barka da sfy Allah ya taimakeka" daure fuskarsa yayi kamar bai taba dariya ba ya sake dago kanta yace “kinyi bacci kuwa jiya?” kada masa kai tayi ya sauke ajiyar zuciya yace “amma nasan lkcn dana Kira wayarki bakiyi bacci ba meyesa baki daga kirana ba” shiru tayi masa ganin bazatace komai ba ya miqe yace “is ok ki shirya zanyima Shahid driven mgn ya kaiki gda ku gaisa da yamma zanzo na daukeki ki kulamin da kanki kinji inason baby na ya zama cikin aminci, ki gaida su Baffa” yana fadin haka yasakai ya fice yana fita taji an fara busa Algaita ana fadin “gyara kintsi dan waliyin Allah takawarka lfy sarkin sarakunan duniya dan sarki jikan sarki baban sarkin gobe Allah yaja kwana uban Yariman Bauchi jikan sarki Hafeez dan Sarki Hambali uban Sarki Hambali”


Kwafa tayi ta miqe ta nufi dakinta ta fara shirinta cike da farin ciki yau zataje gidansu taga iyayenta da yan uwanta shiri tayi bana wasaba tana gama shiryawa ta kira wata cikin bayinta tace take ta shirya tazo su tafi bata jima ba ta dawo ta riqe mata jaka da wayarta suka fito harabar gdan nan danan taga wasu mata sanye da uniform din security sun taso suna sara mata ajiyar zuciya tayi ta daga musu hanu wani namiji ya bude mata mota sabuwa dal qirar Land Gruiser da alamun itace wacce ya bata cikin kyautukanta na fansar budurcinta sauran mutanen dake gurin duk suka shiga sauran motocin Shahid yaja suka fita daga gdan sarautar anata daga mata hanu itadai murmushi takeyi tare da hawaye lkc daya saida suka fita cikin gdan suka dauki hanya abin mamaki sai taga sunbi wata hanyar daban ba wacce tasani a matsayin ta gdansu ba kamar bazatayi masa mgn ba dai sai kuma taga tafiyar tayi tsayi tace “ina zamune haka Shahid?” qasa yayi da kansa yace “Allah ya taimakeki ai sun matsa daga wannan gdan sun koma wani daban anan hayin Daudu” iska ta furzar batare da tace komai ba saboda batasan mene zatace ba sun danyi tafiya a unguwar sannan taji yanata horn a jikin wani get dago kanta tayi tana kallon ikon Allah har get man yazi o ya bude motocin suka shiga sukayi parking wadannan matan biyu suka fito tare da wasu maza masu irin uniform dinsu sune suka bude mata mota ta fito tana qarewa gdan kallo Baffanta taga ya bude wata qofa ya fito tana ganinsa ta saki wani ihu ta kwasa da gudu ta fada jikinsa tana dariya shima dariyar yakeyi yace “ho uwata har yanzu kinanan da halinki yanzu da kike irin wannan gudun baki tsoron lfyrki da abinda ke cikinki” qasa tayi da kanta a kunyace tace.


“Baffa na sameku lfy ina su Ummah da Mama ashe dama ansa bikin yan uwana baka fadamin ba?" Murmushi yayi ya lakace mata kumatu yace “sarkin tambaya muje cikin gdan saiki tambayeni sosai dariya tayi ta qara maqaleshi tace “Allah Baffa nayi kewarku da yawa dama Mai martaba yabarni na kwana tare daku” gani yayi surutunta bazai qareba yaja hanunta bayan sun gaisa da Ex-court din nata mazan sun juya sun tafi matan suka take musu baya suna shiga ta fara qwalawa iyayenta Kira “Ummah Mama ku fito gani nazo” fitowa sukayi suna murna Ummah tace “yar nema kin samu Mai martaba kin manta damu ko?” dariya tayi ta zame jikinta daga na Baffa ta zauna tare da cewa “washhh wlh ba haka bane kullum daku nake kwana jiya fah muka dawo banyi ma tunanin zai barni nazo ba sai gashi tun kafin na fada masa inason zuwa yace na shirya nazo" murmushi sukayi suka zauna kusa da ita tace“waini ya na ganku anan Ummah inasu Rahmah?” murmushi Ummah tayi tace “sun tafi fitar da ankon bikinsu" ajiyar numfashi tayi tace “baki amsamin dayar tambayar ba” kama hanunta tayi suka shiga daki Mama tanayi musu tsiya ta zaunar da ita a hankali tace “zauna a hankali karnayi barna Mai martaba yasa a daureni don nasan yanda ya kwallafa ransa akan cikinnan qaramin abune hakan a gurinsa, wato Farha bayan auranki da kwana daya wadda ta kama ranar da akayi bikin budurcinki a fada ranar ne Mai martaba yayima Baffanku kyautar wannan gdan da duk abinda ke cikinsa a washegari ya dage saida muka dawo cikinsa inda mukuma yayi mana kyautar kujerun Umarah da hajji yanzu haka munje Umarah mun gaida ma'aiki munyiwa Allah gdy daya sanya kika zama mabudin arziqinmu saura aikin hajji Wanda shima zamuje nanda wata hudu amma ni inaji hqr zanyi saboda lkcn yayi daidai dana haihuwarki in yaso mamanku tunda ita mahaifiya ce tana fullaci sai taje ni daga baya naje” tunda Ummah ta fara mgnr take sharar kwallah komai nata Mai martaba komai ta tambaya sai ace Mai martaba waishi kuwa wanne irin so yake Mata ne haka” kwanciya tayi a jikin Ummah ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta tabbas mijinta yana sonta amma mutane uku tak suna neman hanasu farin ciki abinda tayi masa jiya shine ya fado mata bata kyauta masa ba har shima ransa ya baci yayi fushi da ita da wannan tunanin su Rahmah da Rahina da Binta suka shigo aikuwa sukayi tsalle suka maqalqaleta suna dariya Mama ta shigo tace “nima ayi dani hirar mana” Ummah ce ta rinqa janyesu tana sallalami tace “yau naga hauka do Allah ku daga masa mata karku janyo mana jamgwan dan wlh akan cikinnan ba qaramin matsala zamu fuskanta ba” janyewa sukayi cike da mamaki Rahmah tace “wai cikine dake Aunty Farha?"


Dariya Farha tayi sosai tace “kunji munafuka wai Aunty Farha” dukkansu suka sheqe da dariya Rahmah tace “to ba dole na hqr da girman ba na baki tun ke kinyi aure auranma na masu garin sanban gashi

Please Login or Register in order to submit comment