Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake sakin sabon kuka me narkar da zuciya haka kawai taji zuciyarta ta karye itama ta saki kukan janyota ya sakeyi jikinsa yana shafa bayanta a hankali yanason yayi mgn amma ya kasa daqyar ya iya hada kalmomi yace.


“Sun cutar damu Farha an cutar da rayuwata an rabani da farin cikina da kwanciyar hankali na sama da shekara goma sha biyar kawai akan wani rudun duniya Farha meyasa Amnah tayimin haka me nayi mata data cutar dani haka na rufa mata asiri ita ta tonamin nawa na share Mata hawayenta ita ta zama sanadin zubar nawa hawayen na sanyata farin ciki ita ta sanyani baqin ciki meyasa amma ta zama butulu mai saka khairi da sharri Allah ya isana Amnah kin cutar dani bazan taba yafe miki ba Amnah...” dago kanta tayi ta kalleshi ido cikin ido tace “ya akayi kasan sunana? Wacece Amnah? Metayi maka? Kaidin waye meye alaqata dakai dana kasa mantawa dakai?”


Zuba mata ido yayi yana mamakin furucinta Daddy ne ya katse shirun da cewa “nima tambayar da nakeson yimaka kenan Mai martaba kada meye alaqarka da Farhanah?" Kallon Daddy yayi cikin hawaye ya sauka ya zame qasa yace
“Matata ce ta sunnah Daddy idan baka manta ba shekaru 16 baya nazo Kaduna gurin Nasir na kawo masa katin gayyatar daurin aurena wanda zanyi a karo na biyu to Farhanah itace matar dana aura munyi zaman lfy so da aminci kafin lkcn da qaddara tasa Farha tayimin nisa lkcn da abin ya faru tana dauke da tsohon cikina a jikinta..." Nan ya kwashe komai ya fada musu kana ya dora da cewa.


“Nasir yasani na shiga mayuwacin hali wanda har yanzu shine yake dawainiya da rayuwata Daddy lkcn da Farha ta bata iyakar binkice Media da hukumomin tsaro babu irin wanda bamuyi ba amma babu nasara qarshe ma aka tabbatar mani da a ranar da taje tasha motar Jos ta hau kuma motar tayi accident mutanen ciki sun qone babu wanda ya rayu hakanne yasa na fidda tsammani da sake ganin Farha amma zuciyata taqi yarda Farha ta mutu duk inda kasani a qasarnan dama maqotan qasashe babu inda banjeba kozan ganta amma shiru wannan dalilin yasa nima na susuce na zama kamar zararre wlh badan qarfin addu'ar da Hajiya ta da mahaifin Farha suka duqufa yimin ba da tuni na zama mahaukaci na gaske haka shekaru sukayita tafiya na zama wani iri niba namiji ba niba mace ba tun lkcn da Queen ta bata muka fara takun saqa da matata Amnah takasa hqr da yanayin da nake ciki ta manta cewa duk duniya burina bai shige Farha da cikin jikinta ba tasha fadamin nida Farha saidai idan ana aure a lahira muyi lkcn da Farha ta shekara uku da bata lkcn ne Nasir yazomin da mgnr Abdallah tunda ya fara bani lbrn yaron naji ina tsananin qaunarsa qauna irinta jini a kuma daidai lkcn ne ya turamin picks din yaron nikuma na nunawa Amnah tana ganinshi tahau bala'i wai wata nayiwa ciki ta haifamin dan shege ita kuma nakasa yimata ciki ai garama da Farha ta bata kumadai duk tsiyata da baqin cikina saidai nayi tunda shege baya gadon sarauta.


Munsha rikici da Amnah duk yanda zan wayar mata dakai taqi ganewa qarshe ta hadani da mahaifiyata Hajiya da taga hoton yaron itama cewa tayi dole akwai abinda yake akwai tsakanina da Abdallah wannan kamar dake tsakanina dashi ba iyakar ta halitta bace kamace ta jini naso mahaifiyata ta fahimceni amma yaqi qarshe sai tace tunda abin nawa iskanci ne ba lalura bace to dole tabani wata uku nayima Amnah ciki idan ba haka ba saita fiddani cikin yayanta, lamarin daya tayarmin da hankali harna fara tunanin anya kuwa Hajiya ita kadaice a cikin hayyacinta take kuwa? Banida amsa saboda haka nabada qaimi na dage akan saina yiwa Amnah ciki bisa sonbin umarnin mahaifiyata amma Ina abun ya faskara saboda bani nake bayarwa ba Allah ne har wata uku ta cika komai ya qara lalace min Hajiya tayi fushi me tsanani dani Amnah kuma ta sami damar rainani ban isa nayi mata mgn ba saitace min dalla karka takuramin sullutu kawai a haka gaka kamar namijin gaske amma empty kake baka da ruwan bada haihuwa saina jaraba wannan abu yana yimin ciwo sosai amma babu yanda zanyi.


Muna tsaka da wannan rigimar kuma wata ta bullo na dade dajin lbrn Amnah tana lesbian amma ban tabbatar ba kuma ban yarda ba saboda bantaba gani nasan dai tana yawan baqi mata to a wannan lkcn saboda rainin daya shiga tsakaninmu saita daina shakkata ta fara fito da halinta, ranar wata asabar ban fita ba ina part dina maqale da hoton Farha ina shafa tudun cikinta ina kuka kawai sai naji zuciyata tana rayamin na Kira Amnah banyi tunanin komai ba na kirata amma bata dagaba kira yafi nawa miqewa nayi jikina babu qwari na nufi part dinta ina shiga naga bayin dake sashin sunata yimin kallon tsoro amma basu da damar dakatar dani harna dangana da qofar wlh da nasan abinda zanje na tarar kenan da bazan qarasa ba ina bude qofan na shiga ina kiran sunanta yan mata ne guda biyu a saman Amnah sunata tsotseta gefe ga wani namiji shima yana qwaqular gabanta hankali na ya tashi matuqa nayi wani irin qara ganin wai matata ce a wannan halin bayan qarar ban iyayin komai ba saboda zubewa nayi a gurin nidai farkawa nayi naganni a asibiti yayata Hajjah da qanina Hasheem suna jinyata amma babu matata Amnah a gurin wasu hawayen nadamar sanin Amnah suka zubomin gana kewar rashin matata me tsoron Allah Hajjah ce ta matso ta riqo hanuna itama idonta na zubar da hawaye tace “kayi hqr Hafeez komai yayi farko to tabbas watarana qarshensa zaizo wlh Hajiyanmu baa cikin hayyacinta takeba” shima Hasheem matsowa yayi yace “insha Allah Yaya asirinsu zai tonu koma su waye sukeyi maka wannan mugun abin ni na tabbatar matarka ba mutuwa tayi ba inaji a jikina yana raye Yaya da zakaji shawara ta ka saki Amnah ka huta kaima ka samu sauqi kaji da matsala daya" “karka soma mukaji an fada daga bayanmu juyawa mukayi dukkanmu da mamakin me mgnr kawai sai mukaga Hajiyan mu ce hanu tasa ta dauke Hasheem da mari tace “laanannen Allah meson raba sunnar ma'aiki Amnah ba yayarka bace ne Hasheem? Wai ba yayarka bace Amnah? Na dauka yar yayar uwarka ce amma kakeyi mata wannan mugun fatan to bari kaji Amnah bazatayi zawarci ina rayeba wannan dan qaramin kuskuren kawai dan tayi baqi bata sanar dashi ba sai ace ya saketa? To bari kuji Amnah zama daram a gidan Hafeez indai nice na haifeshi kaikuma kake zaremin idanu to wlh da wasa ka kuskura ka saki Amnah saina tsine maka sau dari sallamamme na lura tunda wannan makirar matar taka ta mutu ka susuce saboda ta gama dakai na tabbata da kasan inda kabarinta yake da zuwa zakakeyi kana haqota kana kwanciya da ita tunda babu wacce ta iya sai ita babu mace me dadi da ni'ima sai ita saboda ta kawo maka budurcin qarya ai munsan komai Amnah ta fadamin kaza ka yanka ka cakuda jinin da maniyyinka ka zuba a zanin gadon kawai saboda son ace ita ta iya wawa kawai"


Tana fadin haka ta juya ta fice ta barni da kukan zuciya dana fili wlh bana jure duk wani rashin mutunci akan Farha saboda itace farin cikina, Daddy inaji ina gani haka naci gaba da zama da amma duk zaman namu bame dadi bane saboda na tsaneta babu wani abu da yake shiga tsakanina da ita qwanqwaminta nakeji sosai na tsani fasiqin mutum a rayuwata, haka mukaci gaba da rayuwa da ita wata rikitacciyar rayuwa mara tagomashin farin ciki kullum da sabon abinda zata bullo dashi gaba daya ban yarda da ita ba gashi hqrna ya qare kullum azumi nakeyi don cirewa kaina damuwa da sha'awa.


Wata rana Ina kwance a dakina nakai azumi harna fara bacci naji an bude qofa an shigo na bude idona na zubashi a kanta ta zauna kusa dani nayi saurin janye jikina kawai saita samin kuka tana yimin magiyar nayi hqr na yafe mata ta daina duk abinda takeyi ta tuba, Daddy Allah yasamin rauni akan lamarin ya mace musamman wacce take qarqashina ko kadan banason digar hawayen mace da wannan Amnah tayi nasara akaina har wani abu ya shiga tsakanina da ita amma duk da haka saida nayi amfani da comdom don kiyaye lfy ta sati biyu da haka Amnah ta fara rashin lfy likita na kira gda ya dubata gwajin farko aka tabbatar min da Amnah tanada shigar ciki wata biyu zabura nayi na miqe ina kallon likitan ina kallon Amnah da taketa murmushi nace Dr wata biyu ko sati biyu? Dagowa yayi zaiyi mgn tayi saurin daga masa hanu tace “wata biyu ne Hafeez nasan dashi abinda yasa ban fada maka ba saboda inason bakashi a matsayi surprise ne jeka Dr mun gde" juyawa likitan yayi ya fita bayan tayi masa kyauta me tsoka likitan yana fita nayi kukan kura na damqeta na shaqeta idanunta sukayo waje Ina jijjigata Ina fadin ta fadamin cikin uban waye?


Shigowar Hajiya Sogiji ne ya ankarar dani barnar da nake shirin yi saboda Amnah ta daina numfashi sakinta nayi ta fadi na nufi Sogiji na nunata da yatsa nace “ Wlh Hajiya bazan yarda ba ta nemawa shegen danta uba amma ba cikina bane banida wata alaqa dashi ita ta sani” Ina fadin haka na fice na koma dakina ina shiga na zube a qasa ina dafe da kaina ina kiran sunan Allah tare da maimaita kalmar “ innanillahi wa innah ilaihir raji'un” na dauki lkc a haka batare da nasan me nake tunani ba ji nayi ana buga qofar dakin da qarfi kamar zaa balleta na miqe da sauri na bude ban gama tantance waye ba naji an daukeni da wani gigitaccen mari, baya nayi da sauri tare da dago kaina Hajiyata ce ta shigo dakin tare da daukan duk abinda yazo hanunta tana jifana dashi tana cewa “ashe kai mahaukaci ne Hafeez bansani ka karbi dan shege wanda kayi cikinsa a titi amma halattace wanda uwarsa take cikin gdan ka matsayin matarka kace bakaso ba naka bane to tunda kace bane fadamin ubansa nace ka fadamin ubansa bayan kai?"







Please Comments
Share and Vote





*UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻



*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


www.fauzahtasiu41@gmail.com





🅿1⃣6⃣



Hajiya na mgn tana qara nufoni har nakai qarshen dakin sannan itama ta tsaya durqushewa nayi na daga hanuna sama ina roqon Hajiya nace “na roqeki don girman Allah ki tsaya ki fahimceni Hajiya wlh tallahi cikin jikin Amnah ba cikina bane bansan inda ta samoshi ba nidai iyakar sanina munfi shekara wani abu bai shiga tsakanin mu ba sai sati biyu da suka wucce cikin jikinta kuma ance wata biyu...” wani kyakkyawan jifa Hajiya takaimin da wani kofin glass tayi nasarar samuna a fuska take jini ya balle min nayi saurin dafe gurin a hasale ta kuma cewa “kadan ka fara gani Hafeez indai akan Amnah ne kuma ciki kamar yanda ka karbi wancen shegen tsinannan yaron naka na kwararo dole shima ka karbeshi domin mu shi mukasani shine Yariman Bauchi kallon banza kasake ya shiga tsakaninka da baiwar Allah Amnah a bakacin nono na da kasha Hafeez na yafeka duniya da lahira balle kuma baqar mgn shashasha kawai wanda baisan abinda yake masa ciwo ba nidai wlh nayi asarar haihuwa” juyawa tayi ta fice nikuma na bita da kallo hawaye nabin fuskata ina tambayar kaina “anya kuwa wannan Hajiya ta ce iyakar sanina Hajiya ta me jin tausayi nace dason farin cikina amma yau komai ya canza har tana iqirarin yafeni cikin yayanta akan abinda nasan iyakar gsky kenan”


Inanan cikin dakina har saida nayi kwanaki uku ban fita ba komai a ciki nakeyi hankalina yayi qololuwar tashi kukana ta zama biyu kukan rashin salihar matata da rashin halattacen dana dana qwallafa raina da burina akansu sannan ga kukan wannan muguwar qaddarar data shigo rayuwata waini Hafeez nine matata ta sunna take dauke da cikin daba nawa ba kuma a cikin gdana kuma dole inaji ina gani aka liqamin shi babu yanda zanyi, miqewa nayi a fusace nace ina wlh bazai taba yuwuwa ba dole nadau mataki bazan iya zama baqin cikin Amnah ya kasheni ba, wanka na shiga na fito na shirya cikin qananan kaya na dauki wata qaramar jaka na shiga tattare duk wasu muhimman takardu na na karatuna dana kadarorina dake ciki da wajen qasarnan na zuba a ciki na debe komai da nasan me amfani ne a gurina sannan na bude bangaren Farha na dauke mata gwala-gwalanta da takardun karatunta da hotunan bikinmu gaba daya da duk wani abu da nasan yanada amfani na sake zubasu a wata jakar na fita nasa a cikin mota naja na fice daga gdan sarautar.



Kai tsaye nan Kaduna nan nufo saida na shigo cikin garin na kama hotel sannan na kira Nasir na sanar dashi Ina cikin garin bai wani bata lkc ba sai gashi yazo tun daga nesa nake kallon ayar Allah shima yaron kafeni yayi da ido sakin hanun Nasir yayi ya nufoni da gudu ya riqe qafafuna duk nauyin da zuciyata tayi sai naji ya kau farin ciki ya mamayeta nasa hanu na dagoshi ina juyawa dashi yana ta dariya nima inayi dakatar da tawa dariyar nayi na zuba mishi ido inason tuno yanayin dariyarsa da tawa takemin kama, shima daina dariyar yayi ya kwantar da kansa a kafadata yana sauke ajiyar zuciya har muka shiga dakin da na kama muka zauna na kwantar da shi a cinyata nayi kissing nashi nace masa My Son yada kallo?" Dariya yayi ya sauka daga cinyata ya fara wasansa muna tattaunawa da Nasir amma hankalina yanakan Abdallah har muka gama Nasir yakai hanu zai daukeshi yaqi ya maqaleni da qyar mukayi masa wayo ya yarda suka tafi tundaga wannan lkcn nakejin so da qaunar Abdallah a cikin jinina kuma nakejinsa tamkar wata tsoka ta jikina har kawo wannan lkcn Daddy bayan barowata Bauchi abubuwa da dama sun faru wasu na san zasu faru wasu kuma da wasa bantaba kawowa zasu faru ba.


Watana tara a nan cikin garin Kaduna a wannan lkcn ne na gina asibitin Queen Farha consultancy hospital inda na dauki manyan ma'aikata a kuma daidai wannan lkcn ne naji yakamata na waiwayi gda naga wainar da ake toyawa shigar dare nayi cikin garin Bauchi saboda haka babu wanda yasan da zuwa na kai tsaye bangare na na nufa abin dana gani ya kada hanta ta da hanjina Amnah ce a cikin dakin kwance itada qanin mahaifina Waziri Iliyasu gefenta ga jaririyar data haifa nan kwance a gadon jariran dake gefe juyawa kaina ya farayi daqyar na dafe bango nayi qarfin halin kunna light din da zata wadata dakin da haske zumbur suka miqe dukkansu tsarara babu komai a jikinsu maimakon ganina yasa su razana aa saima daukan boxes dinsa da yayi ya saka ita kuma ta koma ta kwanta a gadon ya nufoni gadan² yana zuwa ya shaqoni yana huci yana fadin “meye ya shigo dakai turakata munafikin Allah ta'ala meye ya kawoka dakin da nake kebewa da matana?” mamaki ne ya cikani nasa hanuna na cire hanunsa nace “matanka kake cewa ko Iliyasu? Ashe Amnah ma matarka ce kenan? Kayi hqr bansan cewa mace tana auran namiji sama da daya ba daban shigo muku a wannan lkcn ba...”


Ban ida rufe bakina ba ya daga hanu zai mareni na riqe hanunsa ina girgiza masa kai nace “gangancin da zakayi qwaya daya tak a rayuwarka shine fitar da hanunka ka taba jikina nasamu lbrn komai da kakeyi a masarautar nan saboda bananan to ka sani kuma ka rubuta ka ajiye da sannu zaku girbe abinda kuke shukawa” Ina fada masa haka na juya na fice daga dakin na nufi part din Farha na bude na shiga dakin duk da qurar dake part din haka na fada saman gadon na kwanta inata juyi zuciyata na tafasa tanayimin wani irin zafi dana rasa wanne irine ranarta ta qarshe da Farha ta rinqa dawomin a wannan dare nayi kukan daban tabayin irinsa ba da safe labari ya cika fada cewa Mai martaba ya dawo tun ina ciki na rinqa jiyo hayaniyar mutane daqyar na tashi nayi wanka na fita ina fita wasu manyan fadawa na suka nufoni suka dagani suna fadin “takawarka lfy dan waliyin Allah haqiqa munyi rashin adalin Sarki Allah yaja kwananka fada dama qasar Bauchi tayi kukan rashinka da fadawarta hanun azzaluman bayi tabbas bayan tafiyarka gaskiya ta bayyana anyi yunwa halin kowa ya fito kuma walqiya akayi me qarfi mukaga munafukai a rana Allah ya qara maka lfy Hajiya Mai babban daki kullum sai tayi kukan rashinka hakan yar yana neman haifar mata da wani ciwon ka fara zuwa ta ganka kafin zaman fada" suna saukeni na keta tsakiyar mutanen na nufi bangaren Hajiya ina shiga ita kuma tana shirin fitowa da gudu ta nufoni ta rungume ni tana wani irin kuka dana kasa gane wanne irine na farin cikine kona baqin ciki shafani take tana qara cusa kanta a qirjina tana fadin “kaine kaine da gaske Hafeez kana raye basu kashemin kaiba Allah na gde maka daka tsaratar min da yaronnan daga kaidin mugayen mutanen nan Hafeez ina ka shiga kamanta da tsohuwarka da jama'arka Allah babu abinda zancewa Shugaban malaman fada Mal Usman Giyyade mahaifin Farha sai gdy"

Tana mgnr tana shafa qirjina wasu hawayene masu zafi suka zubomin na durqushe a gabanta na saki kuka nace “kiyi hqr ki gafarce ni Hajiya wlh bazan iya jure baqin cikin ganin matata Amnah da cikin daba nawa ba shiyasa na yanke shawarar barin qasar Bauchi baki daya amma yanzu gani na dawo kiyi min umarni da duk abinda kike ganin shine daidai nayi alqawarin zanyi biyayya a gareki" itama durqushewa tayi ta kamo hanuna tace “So nake a yanzu basai anjima ba kayiwa Amnah saki uku kyawawa sannan kasa a koreta daga garin Bauchi ita da Baffanku Waziri Iliyasu wannan shine umarni na qarshe da nake fatan baka a rayuwata Hafeez” dama wannan ranar nake jira don haka yanke take na kira magatakardar fada nasa ya rubutawa Amnah saki uku tare da umartarsa yasa a hada mata kayanta itada Waziri Iliyasu a fitar dasu daga qasar Bauchi gabadaya haka kuwa akayi cikin qanqanin lkc aka aiwatar da abinda na fada.


Dagowa nayi na kalli Hajiya nace “Hajiya saime kuma kikeson nayi miki” murmushi tayi tace “nayi haihuwar albarka Hafeezu Allah yayi maka albarka ya dawo maka da farin cikinka Hafeez Allah ya baka zuri'ar da zasu zama gatanka anan gaba Hafeez nayi nadama da danasanin abubuwan da nayi maka har sukaja kayi fushi dani ka tafi ka barni cikin tsaka mai wuya bayan tafiyarka nice nake kula da lamuran Amnah duk wani abu da zaa fadamin game da ita bana yarda nasha zuwa domin duba lfyr cikin da na qwallafa raina akai ina ganinshi kamar kai amma idan naje saina tarar da ita da mata suna harkokinsu bantaba damuwa ba saboda an kashemin zuciya kai tafi² har ta fara shigo da maza sau yafi goma ina zuwa ina tarar da ita da Waziri Iliyasu suna ha'intarka a lkcn ne na fara damuwa na kira uwarta Hajiya Sogiji nayi mata mgn aikuwa sai ta hauni da fada har tana cewa wai ai gara Amnah da qanin mahaifinka take harkarta kaikuma fah wa yasanma wanne jinsin ka ajiye kake badalarka da ita har kayi mata ciki ta haifa maka dan dakan kuka kacika duniya da hotunanka dashi kana fakewa da cewa wai tsananin kamace kawai bayan ga jininka nan yana gudana a jikin yaron, har cemin tayi kamar yanda kake da da a bayan fage to itama Amnah da bakason ta samu saita samu kuma Allah ya dubeta ya bata dan baqin ciki saidai ya mutu wai dani dakai din babu yanda zamuyi da ita, ban sake magana ba kawai saina duqufa addu'a da fatan Allah ya dawomin dakai kazo kaga yanda komai ya lalace a masarautar ka kwatsam bayan wani dan lkc sai Amnah ta fara naquda muna kaita asibiti ta haifo yarta mace me kama da Waziri Iliyasu hasken fatarne kawai na Amnah aikuwa magana ta rinqa zagawa a fada da wajenta cewa yafa ba taka bace ta Waziri Iliyasu ce domin damacan tun kafin kabar qasar Bauchi shine farkan Amnah tun zamanin Farha duk ranar da kake tare da Farha to ranar ita kuma tana tare da Waziri Iliyasu wannan abu ya daki zuciyata data yan uwanka musamman Hasheem da Umaima shi Hasheem yana mamakin yanda abubuwan sukayi tsanani haka inda ita kuma Umaima take kuka tana fadin ai duk abinda ya faru kitimurmurar mahaifiyarsu ce Hajiya Sogiji.


Bayan komai ya lafa mun zubawa sarautar Allah ido wata ranar juma'a data kama ana gobe sunan yar da Amnah ta haifa muna zaune a parlour nida yayarka Hajjah da Hajiya Kilishi da Hasheem da sauran yan daka kawai saiga Umaima ta fada tana wani irin kuka tana cewa “ innanillahi wa innah ilaihir raji'un La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin Hajiya sune wlh sune ashe sune sukayiwa Aunty Farha kurciya ta bata tabar Yaya saboda kada ta haifi Yariman Bauchi ashe sune Hajiya sune suka shiga tsakaninki da Mai martaba suka sanya miki tsanarsa dajin haushinsa sune suka sake kada Mai martaba duniya saboda su dafe dukiyarsa ta hanyar cikin jikin yaya Amnah wanda bashida wata alaqa dashi ashe Waziri Iliyasu shine uban yarinyar nan da yaya Amnah ta haifa wlh da gaske nakeyi Hajiya mun shiga ukunmu Hajiya tayi nisa a shirka ta bata Allah dama ba Hajiyan muce ta haifemu ba haqqin rai...” yarinyar tana fadin haka ta yanke jiki ta fadi tana wani irin kuka mecin zuciya.


Dukkanmu kanmu kullewa yayi da mamakin wannan al'amari daqyar Hasheem ya miqe yana kuka ya fita ya nufi bangaren mahaifiyar tasu yana shiga ya rufe Amnah da duka kamar Allah ya aikoshi bayaji baya gani Hajiya Sogiji tayi yunqurin hanashi bisa tsautsayi ya bigeta ta fadi a sume mu da muke shigowa muka nufeta muka dagata aka fice da ita akabar Amnah kwance cikin jini muna zuwa aka shiga da ita emergency aka tabbatar mana da tasamu shanyewar barin jiki wlh Hafeez tundaga wannan lkcn gda ya dada rikicewa Amnah ta samu goyan bayan farkanta da yake iqirarin tun ka mutu yanzu shine Sarki suke tsula tsiyarsu son ransu babu mece musu donme, tunda Hajiya Sogiji ta kwanta ciwo Amnah bata taba zuwa ta dubata ba idanma akayi mata mgn sai tace ita bai shafeta ba yayanta sune dolenta ba itaba haka akaci gaba da cakudawa har kawo yanzu da Allah ya dawomin dakai" hawaye na share me zafin gaske wannan wacce irin musiba ce me Farha tayi musu haka mena tare musu da suka rabani da farin cikina?" Tabbas badan Hajiya tasa na saki Amnah ba dasai na kasheta har lahira kuma har yazu inada wannan burin a raina.


Bayan Hajiya ta gama bani lbr ta qara riqe hannuna tace “ Hafeez ina zaka samomin wannan yaron wlh kullum da qaunarsa nake kwana nake tashi ka karboshi mu rikeshi idan da halima ka yanta uwarsa ka aureta ku daina wannan qazamar rayuwar don Allah kaji” sunkuyar da kaina nayi qasa ina share hawayena nace “wlh Azeem Hajiya bansan mahaifiyar yaronnan ba ban taba ganin mahaifiyar Abdallah ba kiyi believing dina iyakar abinda na sani Abdallah maraya ne mahaifinsa ya mutu tun kafin a haifeshi sannan dane ga qanwar Momy mahaifiyar abokina Nasir mutumin Kadunan nan da mukayi karatu

Please Login or Register in order to submit comment