Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakyar da sudin goshi daddy ya Amince amma da sharadin babu hannun su a ciki tunda ya dage sai yayi Auran suna ganin hakan kamar cima Aisha fuska zaiyi daga maganar haihuwa saiya zo musu da batun Karin Aure, saida akakai ruwa rana sannan suka amince inda ya tabbatar musu bazai taba tozarta Aisha ba, babu abunda zai Chanza a Auran
Dazai Kara nan hankalin Mamie yadan kwanta, Ankai kudin gaisuwa tareda kayan Sa rana inda ba'a ja bikin ba Wata Daya akasa a cewar AK yanaso ayi da wuri harga Allah Sha'awa na neman yimasa illah inda duk abunda akeyi Aisha batasan wainar da ake toyawa ba.


Kawayan leemah su meenah kuwa koda suka samu labari suka kuma kyalla ido sukaga AK nanfa hankali ya tashi ganin yanda Leemah tayi musu fintinkau a bariki dukda sun rigata shiga Amma tafisu cin riba uwa uba zata Auri babbar harka, tsananin barikin su saida iyayan su suka koresu a gida inda suke zaune darajarta sukeci kasancewar gidan na mahuta, gashi kuma akan idonsu zata Auri handsome young milonia sukuma fa? Sukare a duniya? Inaaaa nanfa hassada mai zafi ya darsu a zuciyar su inda ta rokesu bataso mahuta yasan da Auran da zatayi suka Amsa mata akan ana Tare bazasu gaya masa ba.




Amarya fa sai lakuce lakuce da banke banke da like like takeyi kullum cikin hayakin HQ take saikace yar'bori maganin mata kuwa sha take kamar hauka daga karshe saida yasata zawo saboda shan haukan da takeyi Anty zakwai kuwa ta kuke ta dage tun daga Maiduguri tazo hada leemah inda tai mata masauki a dakinta na isa kaita, kudi sosai tasamu wurin mahuta inda ya sakin mata Aljihu ganin ta chanza test da harta fara sire mishi ta bude dayawa amma yanzu dayaji sabon sinadari nan ya ware Aljihu, Wata kawarta ce Deejah bariki tabata shawara akan zata Rakata asibiti a dinke ta tsaf kamar kwarya yanda ko AK na aiki da Aljanu bazai taba gane ta bude ba, nan kuwa leemah tayi matukar farinciki San AK take kamar hauka nan takara sakinma mahuta jiki ya kwashi gara aikuwa tasamu yanda takeso kudi yabata sosai ba tareda bata lokaci ba suka nufi asibi inda saida aka kankare fatar wurin aka goge, subhanallah Karamar tiyata akai mata a wurin *"hattara mata wani sabon bala'e daya shigo kenan yanzu mace saitaje Asibiti Yammata harda matan Aure akan a dinki su tsaf ko kunya babu ku wage jiki da sunan gyara haka za'ai ta dinke ku saikace buhun masara kai jama'a waiduk kan da'namijiπŸ˜• hmm Wata kotayi a banza wlh kozai chanza miki na lokaci kadan ne zaki Kara budewa ke kenan kin dinga zuwa ana miki dinki kenan? Saikace wacce ta haihu? Shi namijin maiya dinke kokuma mai yakeyi domin samun gamsuwar ki? Wlh wani ko magani bazai taba Shaba domin burgeki amma duk kudinki yagama karewa akan maganin mataπŸ€¦πŸ»β€β™€karshe su nakasa miki mahaifa GA cancer datai yawa a mata yanzu, subhanallah wata ma yanzu tana samun ciki yana shiga Wata tara zataje asibiti ta kwanta aimata operation tun bata fara nakuda ba wai ita tayi dabara bataso ta bude ita uwar sisi da gayu maisan gamsar da namijin da bazakiyi bajinta ba ko tsoran lafiyar ta batayi, Allah yasa mu daceπŸ™*



Rabonda Aisha tasa AK a ido an kwana biyu tun tana boyema ganin shi harta daina kwata kwata baya Zama a gida inda kayan abincin su yayi kasa sosai tanaso taimasa magana batasan ta yanda zata fara ba, dukda shike duba komai zaiba yaron aikin shi kudi ya siyo duk abunda ake bukata saidai taga an jera mata su a kitchen, tana zaune sanye da Pakistan Riga da wando, wandon pencil rigar ma batada wani tsawo pink mai kyau tasha ado sai zuba kamshi takeyi kanta daure da karamin rober band, shigowa parlon yayi yana waya da leemah cikin nishadi dukda daga wurinta yake amma ka'eda ne yana barin gunta zata kira shi suyita waya harya kai gida yauma hakan ne, burki yadan ja cikin mamakin ganin Aisha zaune a parlor tana kallo harga Allah rabonda yasata a ido ya manta dukda yaga tadan rame amma kuma takara kyau, 'matar so just a minute I will call you, kashe wayar yayi 'A'a su Ustazai ne Ashe kunyi wuyar gani, yafadi cekeda zolaya inda saida tayi mamakin shi wai yau itace yake zolaya, tunda Allah yasa mun hadu yau wlh Sam nama manta dake a gidan, cut the story short, yauwa next week insha Allah za'a kawo mun matar so, Amarya kuma uwargida ta swt 18 Asalin Ustaziya diyar mutunci diyar malamai da kamala kimtsatiya kamila, hafiza, malama bawai a suna ba nooo, uwa uba uwa ga yarana insha Allah, farincikin AK ina fatan zaki bita sau da kafa saboda gudun shiga matsala a wurina? Biyya dole ce gara ki kwantar da hankalinki zaki karu da ita yauda gobe na tabbata zata saki a hanya kema kidanyi hankali, yafadi yana dariyar keta, kallon shi tayi daga sama har kasa dariya ciki ciki, 'heeeyeeeeah Allah tafadi yayinda ta tafa hannu duka biyun, sannu namiji, Sannu Ango kasha kamshi lallai ka cika namiji Gwarzo ai abunda ya kamata kayi tuntuni kenan Allah yakawo matar so, Allah yakara kauna tsakanin kada matar so, Allah kuma yakara Soyyah, mikewa tayi yayinda takara kallon shi shekeke, daga kai har matarka bakwa gabana gara tun kafun ta karaso kaja mata kunne ka ajiye rikakkiyar Yar'duniya billahillazi ta shiga gonata nan zaku Kara tantance banbancin diyar malamai da diyar mai'shayi yar duniya ubanta zataci ni baka gabana daga kai har ita, akwai lokacin da nake jira yanayi zan cikama rigata iska inbar muku gidan Soyyah kukara soyewa, Allah ya sanya Alkairi ango mai jiran gado, daki ta nufa tana tafiya tana juya mazauni harda yar Karamar waka,

'Ga ango Na Amarya,
"Inaaa Ango Na Amarya,
" Kai sai ango Na Amarya.

yayinda yabita da kallo baki bude samun kanshi yayi dajin takaicin maganar datayi saiyaji Auran yadan sire mishi ko kadan ba haka yaso tayi ba aiya dauka shake shi zatayi tana rokon shi kada yaimata kishiya ta tuba inda zai shuka mata Rashin mutunci sosai Lallai kodan kishin da mata keyi Aisha bata masa kishiya fa yace zaimata muguwar yarinya maiya mata a Rayuwa Wanda takasa nuna jinjirin kishi akan Sa? Wace irin kiyayya ce haka? Ada idan zai tuna ai tana matukar sansa dama so na chanzawa? Ikon Allah, Kodan kukan da mata keyi baiga Alamar tanada niyyar yiba.

Tana shiga daki ta kulle da makulli toshe bakinta tayi nan bakin kofa ta zube tareda fashewa da kuka mai kona zuciya.






*Mrs Saddiq Rumah πŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie*


*Gobe bazan samu daman typing ba saboda wani babban uzirin dake gabana.*


*Dedicated to sister Husnah.*




29


Tayi kuka tayi tayi harta gode Allah, harga Allah taji ciwo kishiya da ciwo koba komai ita macece sannan cikin soyyar AK ta rayu dukda batajin shi kamar da amma wani zazzafan kishin shine ya kamata ganin zai fara sanin Wata mace kafun ita dukda ta cire rai akanshi amma samun kanta tayi cikin matukar kishin hakan cikin Daren ta kira bilki tareda gaya mata abunda ke faruwa inda taita kwantar mata da hankali yayinda ta shaida mata zatazo idan gari ya waye, da ciwon kai mai zafi tareda zazzabi ta kwana inda duk yanda taso ta raya daran da Rokon Allah hakan ya faskara jikinta ba abunda yakeyi sai rawa inda kirjinta kamar zai fashe a'haka daran nata ya kasance gogan kuwa dakinshi ya shiga jikin shi yayi sanyi leemah ceta kirashi a waya yayinda ya kasa dauka kashe wayar yayi gaba daya ya cillar da ita gefe kwata kwata bayajin dadin jikinsa, shirye shirye nata wakana AK yakara dagewa wurin gyaran gidanshi dukda babu abunda gidan ke bukata amma saida ya chanza furniture's din gidan kaf banda na dakin Aisha harta kitchen bai bari ba kasancewar kitchen din kwaya daya tak shiyasa Aisha taci darajar gyaran dazaiyi yanzu ne zaiyi Aure kudi yake kashewa bana wasa ba, babu yanda Malam liman baiyi ba Sam AK yace baya bukatar ko Allura kobai Auri leemah ba shimai iya mata kayan daki ne darajar Malam din a wurinsa, hmmm gida fa ba'a magana komai ya dauka har barayin mai'gadi saida aka gyara lefe yake hadawa bana wasa ba akwati dai'dai har dozin tareda manya manyan jakar fata guda biyu yakama goma sha'hudu kenan wani abun da gayya yakeyi saboda ya kular da Aisha amma Kota kanshi batabi aikuwa ya kulu ganin Mamie da Daddy ko Allura basu bashi ba shiyasa yace zaima kanshi abunda ba'a tunani, fadin haduwar da lefen daya hada yayi hmmmm bata baki ne babu ne kawai babu a ciki ango nata rawar kai Aisha kuwa da taimakon bilki ta kwantar da hankalinta yayinda Mamie ke Kara tausasa ta, a wannan karan ma Mamie tadau aniyar gyara Aisha a cewarta bataso abar diyarta a baya inda Aisha har tausayin Mamie takeji ganin Wanda akeyi domin shi baima San anayi ba sai Asarar kudi ake amma hakanan takeshe koba komai zatai fresh maganin mata ne natural na itatuwa ba masu illah ba.


Amarya leemah ce zaune a gaban likita sai kuka takeyi kamar Ranta zai fita jin bayanin dayai mata, lallai ba karamin sakaci da ganganci ta tafka ba tafi kowa sanin maganin planing bai cika karban taba hakan yasa take taka'tsantsan every month tana zuwa ana duba ta, gafda zata haduda AK ya kamata taje medical check up amma taki haduwa da AK ya Kara mantar mata da tunanin ta, su meenah ke Kara lallashin ta, 'please beb this is not the end of ur life remember, za'a samu mafita insha Allah ki kwantar da hankalinki please......what mafita? taya? Kinji mai doctor yace kuwa? Am two months pregnant fa yake gayamun can u imagine why ooooh why sai yanzu bikina sauran kwana Uku ya zanyi ni diyar Malam, doctor please do something duk maganin zubar da cikin daka bani yakiyi sai bakar wahala da galabaita nakeyi iyayena duk tunanin jimamin barin gida ke Sani jinya kwana biyu ni kadai nasan azabar da nake sha how can I be so stupid, tafadi tareda rushewa da kuka harda majina, Wyyooo future husband Dina wyyooo mijina wyyyooo burina wyyyooo Naira mafarki na, GOD ka rufamun Asiri taya zanfara tunkarar Gidan miji da cikin wani mahuta ka cuceni maiyasa na baka kaina,ooooh bariki Alalen gero gashi yauta kwabe dani 'look hajiya please ku natsu munsha gaya miki jininki Nada mutukar karfi yadace ki dinga zuwa ana duba ki jefi jefi and kinga yanzu Babu abunda bamuyi ba akan cikin nan ya zube yaki uwa uba kinje anmiki dinki Wanda babu yanda zamu Sa karfen dazai markade cikin a cikinki sai mun kwance dinkin da akai miki idan kin yarda fine.....noooo bikina saura kwana Uku idan aka budeni maizan kaima mijina kenan? Taya za'a Kara budeni bayan har yanzu ban gama hadewa ba har yanzu ina kan jinya ne Taya zan fara mishi bayani? Look hajiya shawara ya rage naki idan kun tsaida magana daya zaku iya dawowa namu aiki ne.
Ficewa doctor yayi yabasu wuri ganin suna bata mishi lokaci wurin awa daya ana magana daya, dakyar meenah suka tasa keyarta suka koma gidansu domin samun mafita leemah kuwa sai yanzu tafara ganin illar bariki Ga miji har miji amma tama kanta makeken bakin fenti a Rayuwa inda meenah kuwa sunfi kowa matukar murnar faruwar hakan, mahuta suka nema a waya tareda yimishi bayanin komai da komai har Auran da zatayi harda cikin shi datake so ta zubar takasa, Ranshi yayi mugun baci inda babu macen datai mishi yaudara irin nata, he can't believe Aure zatayi nanda kwana Uku and take kawo masa kanta ko kunya take cewa tana sanshi for all the hidimar da yake mata menene baya mata? Mai Wanda zata Aura ya fishi dashi? Mai zai bata Wanda shi bai taba bata ba? zai nuna mata ita Karamar yar'bariki ce kuma zaiga shegen likitan dazai cire mata cikin shi za'ayi karamin yaki akan cikin nan ko duniya zata tashi bazai yarda ta cire ba, bawai Dan yanaso ba nooo fansa zai dauka da cikin nata wazaiji kunya idan duniya tasani a tsakanin shida ita?
'Leemah kuwa tuni ta sallami Anty zakwai a cewarta yanzu bata zaki takeyi ba mafita take nema inda mama taita ko'dah kyau dinda leemah takara tayi haske sosai skin dinta sai kyalli yakeyi duk a tunanin ta gyaran Amaran datace tana zuwa kawarta na mata shiya maida ta haka, wani Asibitin suka chanza idan suka samu wani doctor ya amince zai burge cikin amma koda za'a bude ta Dan kadan ne nanma hankalinta bai kwanta ba idan an bude ta tayi yaya da 1st 9yt? Hakura tayi yayinda tace idan sun gama shan Amarcin su zatazo a cire cikin Kota halin yaya gudun tonuwar asirin ta kada ta haifi katon bakwaini.


Ankai lefe saidai muce masha Allah Allah yaba Amarya da Ango zaman lfy da kwanciya hankali har saida Malam liman yayi fada akan uban lefen da aka kawo inda dakyar ya Amsa a cewarsa ba siyarda diyarsa zaiyi ba yayinda akai ma masu kai lefen tarba ta musamman tareda sha'tara na arziki, Mamie kuwa ba yabo
Ba fallasa itama ta yaba inda da kanta taima Aisha kayan fitan biki masu zafi kala goma duka an dinka su AK kuwa dubu hamsin ya ajiye ma Aisha cikin Wata farar takarda wacce yayi rubutu a ciki ya ajiye kan kujera a cewarsa yabata ne sadaka tasa ma auransu Albarka tunda satin farinciki zasu shiga bayasan hayaniya da kowa itama tasamu nasa kati, da taki daukar kudin yayinda ta kira bilki a Waya ta shaida mata, bilki ce tasata dauka karfi da Yaji a cewarta raba mugu da makami ibada, inda Aishar tace bazata ci ko sisin saba aikuwa bilki taxo ta Amsa kudin yayinda tayi kasuwa fitunannun kayan bcci da shegun kananan kaya ta siyo mata fadin haduwar su bata baki ne a cewarta sune bomb na farko da yayar Tata zata Dana ma ango Da Amarya a cikin gidansu saita saka Aisha ta ruguje musu tunani da natsuwar su kaf saita sasu sun rasa kwanciyar hankalin su insha Allah muddin tana raye karyan iskanci AK yakeyi waya gaya mishi ana Jada mace? Macen ma cikakkiya irin Aisha mai kayan aiki komai Yaji masha Allah.



*Mrs Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Fan's Dina farinciki na, murmushi na hakika ina ganin zallar Soyyah kuma yau naga ninkin shi a wurinku Allah yasa ku cigaba da kasancewa dani ko'bayan na gama novel, banaso kusoni Dan novel Dina, A'a please kusoni a Mamie dina.*😍naso inbaku kyautar page dinnan saidai kasheπŸ€¦πŸ»β€β™€ novel dinnan gaba daya sadaukarwa ne Ga kanwata *Husnah*😍 dukda haka kusani ina yinku wlh.πŸ˜πŸ’ž



*Written by Anty Mamie.*




*Dedicated to sister Husnah.*



30




Amarya ansha lalle tareda gyaran kai babu laifi
Shirye shiryen biki ba kama kafan yaro ta kowani barayi shiri akeyi inda Ranar juma'a dinbun jama'a suka shaida daurin Auran Abdulkareem muktar tareda Amaryar Sa Halima daurin Auran daya samu halartar manya manyan malamai da kusoshin gwamnati har'yan kasuwa ba'a barsu a baya ba, tun a wurin daurin Auran akaita rabon manya manyan ledoji masu dauke da hadaddun Abincin da Ango yabada kwangilar ayi, Duk inda AK ya gilma wasa shi akeyi sanye yakeda manyan kaya farare tas Riga da wando da malum malum yasha aiki da golden zare hmm iya haduwa ya hadu sai murmushin yake yakeyi shi kanshi baisan maiyasa tunda aka daura Auran gabanshi ke faduwa ba, gidan Amarya kuwa hausawa sukace Abu namu maganin a kwabe muπŸ‘―πŸΌβ€β™€ Walima gangariya Akayi wa'azi kuwa ba'a magana inda manya manyan malamai mata sukaita fadakarwa gameda zaman Aure Amarya kuwa tana zaune a gefe cikin kawayan ta jefi jefi tasha katon hijab yayinda su meenah keta kaiwa da kawowa sune kirjin biki, shigowar text message taji wayarta duk a zatonta Angon tane Wanda taita kira a karo ba adadi amma yaki dauka dukta shiga damuwa.

Number mahuta ne nanda nan ta bude

*Congratulations Amaryar shagali, gskia kin iya zabe wato ko'a cikin mazan Auren saida kika zaba kika darje naga ango ba karya yayi ya cika namiji harna mishi Addu'ar zaman lfy yayinda muka gaisa a wurin daurin Auran naku, da Alama anjima zan kai mishi ziyara na musamman tareda labari mai dadi harda gudunmawar Auran naku zan hada in bashi, hmmmm kina nufin da cikina zakije gidan wani ya turmushe ki? A wannan Karon kinyi karya wlh wlh San cikina nakeyi idan har wani Abu yasamu cikina zaki tabbatar dani tantiri ne kallon ki kawai nakeyi inga karyan duniyancin ki nabaki nanda Minti Goma sha biyar idan baki sameni a dakina ba, hmmm ki saurari jin labari mai kayatarwa tareda girgiza jama'a A gidan TV anjima da daddare sannan kada ki manta ki ajiye Redio a kusa domin sauraran program din Inda ranka zakiji labarin Diyar malamai budurwa mai Aure da cikin shege, hahahaa.*


Hijab din jikinta ta shiga girgizawa rufa dukya rufeta, innalillahi na shiga Uku ni halima yayinda ta Mike tsaye, Kallo ne ya koma kan Amaryar da Akema wa'azi a cikin mutane, 'lfy? Maiya faru? Nan kallo ya koma kanta Ashe a fili tayi maganar, Antyn tace tajata gefe inda take tambayar ta dalili, cewa tayi babu komai Wata kawarta ce aka turo mata text akan ta rasu, toh'ai Addu'a ya kamata kiyi duk kin tada mana da hankali, wucewa Antyn tayi inda ta shaida ma masu tambayan dalilin salatin Amarya, Meena ne suka jata lungu inda tana kuka take shaida musu Abunda yafaru wani munafukin ya gayama mahuta tanada cikin shi kuma yaki fita, wani munafukin ne ya gaya mishi Auran ta?,Dan girman Allah ku nema mun haryar fita Kota Katanga ne wlh mahuta zai iyayin fiyeda haka wyyooo ni kaina taya zan fara? Ya zanyi? Kuka takeyi inda taita kiran mahuta yaki daukan wayar text taita mishi babu reply inda daga karshe ta Amsa wayar meena ta kirashi aiko ya dauka, "yanzu ni zaka tozarta cikin sha'shakar kuka take magana hannu daya akan kirjin ta, duk soyyar Dana gwada maka? Kada ka manta fa kaika fara Sani na,....eh kuma kika yaudareni kika Auri wanina ba munafuka Karamar yar'bariki, 'kasan har duniya ta tashi bazan taba ba wani namiji irin zumar Dana baka ba ya kamata inci koda darajar wannan ne a gunka, 'lashe bakin shi yashiga yi tuno irin Roman daya kwasa dukda Yanzu bayajin irinshi a tareda ita, murmushi yayi tuno gskia ta fadi, 'dakyar da sudin goshi suka bashi hakuri itada su meenah tareda Alkawarin nanda kwana biyu zatazo gareshi, 'idan ma bakizo ba wlh wlh zaki ganni a gidan naki, kina nufin zaki bashi kanki cikina fa? 'Nooo Babu abunda zai shiga tsakanin mu nama Alkawari saboda inada ciwon da bai gama warkewa ba, 'Shegiya leemah, shikenan saimun hadu sai nazo yafadi tareda kashe waya yana dariyar mugunta.



Misalin karfe Tara na Dare yan'daukan Amarya sukazo inda Abokan AK sukaita kwasar su Amarya tasha fada ba laifi sai kuka takeyi za'a rabu dasu Malam dakyar aka banbare ta daga jikin su malam inda aka kaita gidanta daya gaji da haduwa, nan su meenah suka Kara kulewa harda kwallar takaicin daular da leemah ta shigo babu Wanda baiyi santin gidan ba Addu'a kuwa sunsha shi, an damkar Amanar Amarya a hannun uwargida Aisha wacce bata gayyaci kowa ba sai kanwarta bilki datai ta kwantar mata da hankali inda da hannu biyu biyu ta Amsa bilki na tayata sai washe baki sukeyi nan akaita yabon Aisha ba karamin rudewa Leemah dasu meenah harda dangin amarya sukayi ba ganin surar Aisha Cikakkiyar buzuwa komai Yaji mai diri kyakyawa black beauty, sanye take dawani danyan leshi kalar ruwan kwai da mint green bilki tamata kwalliya na Musamman irinnan amare kannan yasha daurin gwggwaro anbude gashinta ta tsakiya ga kananan kitso an yarfa mata gashin nan masha Allah kunshi hannu da kafa Jan lalle a tafin kafa sai zuba kamshi takeyi nesa ba kusa ba tafi Amarya kyau nan aka fara kananan gulma wasu na cewa idan banda jarabar namiji Yanada mace irin wannan Auran mai zai Kara kuma? Leemah hankalin ta yagama tashi inda su meenah keta dariyar mugunta a zuciya a fili kuwa lallashin ta sukeyi a cewarsu da baya Santa da bazai aurota ba ai yasan da matar tashi, kowa ya watse Leemah ta tasa keyar su meenah akan babu mai kwana mata a gida dole taji dumin jikin mijinta yau, badan sunso ba suka tafi suna mata Allah ya isa ta hanasu Dana gadon da za'ai bidiri akai.


Sai karfe goma da Rabi Ango ya shigo indai kai tsaye dakin Amarya ya nufa hannun shi dauke da manyan ledoji kasancewar ya Hana kowa rako shi inda akaita mishi tsiya, kwance ya tadda ta tsakiyar gado kaiba dankwali baiji dadin ganinta haka ba shida yake tunanin zai ganta da lullube ya yaye da kanshi, sallah ya umarceta suyi kai tsaye ta shaida masa batada tsarki yadanji takaici yaso yasan zakin mace ayau nan sukayi Addu'a sosai ya ciyarda ita taci ba laifi, gassar kaza ce sai yogot inda kai tsaye ta shiga wanka jiki na rawa ganin irin kyau dinda AK yakara mata nan wani mugun kwadayi ya motsa mata amma ya zatayi? Nan gani nan hange, shigar kayan bcci tayi kallo daya yaimata ya kauda kai ganin ko kadan bata kaima rabin tunanin shiba yanda kasan Agwagwa haka surar jikinta yadawo ba shape ba komai ga cikinta yadan tura kadan kamar karamin tunbi, samun kanshi yayi dajin haushin ganinta a hakan ko kadan bata burge shiba tunowa da surar jikin Aisha hakan yasa shi mikewa tareda Jan karamin tsaki yabar dakin, Jiki a sanyaye takoma gefen gado hadeda buga uban tagumi,mai hakan ke nufi? Daga kallo daya a first 9yt saikuma tsaki? Tayi tunanin zai tashi ya rungume tane ya rikice kamar yanda sauran samarin ta keyi, dakin shi ya shiga inda yayi wankan tareda chanza kaya zuciyarsa na azalzala masa yanaso yayi tozali da Aisha yanaso yaga halinda take ciki kodai tana kukan kishi ne? Murmushi yasamu kanshi dayi sanye da kayan bcci ya doshi dakin ta inda a karo da dama yake tunanin shiga, bude kofa tayi da niyyar zuwa kitchen zata ajiye Kofunan da akai Amfani dasu sanye take cikin hadaddiyar rigar bcci tayi matukar kyau, Jada baya tayi wyyoo Allah, harga Allah taji tsoran ganin mutum tsaye a bakin kofa, gefensa ta ratsa zata wuce inda zuciyarta ke suya ganin shida kayan bcci, 'tare hanya yayi, nanma takara yunkurin wucewa yakara tarewa, 'Malam wai lfy? Tafadi cikin harara, 'nazo kisama Aurena Albarka ne yafadi murmushi a fuskarsa samun kanshi yayi da farincikin ganinta tun bare yau tamishi kyau fiyeda koyaushe, jikinta kawai yake kallo ji yakeyi kamar ya ganta kwance a kirjin shi ....'Allah sanya Alkairi, tafadi yayinda ta wuceshi, tsayawa yayi anan harta fito daga kitchen din takara wuceshi inda ta buga kofarta tareda Danna key, Dakin leemah ya shiga da gudu inda har'saida taji tsoro ganin yanda ya shigo kamar maibin wani Abu, ledar kajin daya shigo ya dauka dama kaji Uku ya siyoma leemah sauran biyun ya dauka hadeda juice dinda suka rage, 'lfy kuwa ango Na ina kuma zaka? Baibi ta kanta ba dakin Aisha yakoma inda yahau buga kofar da karfi, tsaki taja yayinda takara Jan bargon ta hawaye daya nabin daya azababben kishi ke damunta, ganin baida niyyar dainawa harya fara kiran sunanta hakan yasata mikewa a hatsile, Malam wai lfy? Tafadi yayinda ta bude kofar Konaci ban biya bane? Hannu daya rike a kugunta tana girgiza jiki cikin masifa ji take kamar ta kifa masa Mari, 'Aisha kuka kikeyi? Kukan kishi na? Ji idonki laaaa wlh na kamaki hawaye ne, goge idonta tayi bataso yaga kukanta ba harga Allah ta manta kuka takeyi da bata bude kofar ba, 'mtsww lfy nace bccin ma baza'a barni inyi ba? Ina kabar matar so tazo taja mijinta, AK harda

Please Login or Register in order to submit comment