Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

awon gaba dashi.
Ajiyar zuciya ta Saki jin rufe kofar shi Addu'a tayi ta shafa nan bcci yayi awon gaba da ita ko motsi batayi saikace gawa



Sai wurin karfe uku na Dare unguwan tayi tsit bakajin motsin komai saboda Dare daya tsala Ustaziya aka ajiye a Wata bakar mota tasha tint baki sidik bakin Saurayin ta datake jida shi mai suna mahuta shiya dawo da ita dukda tanada su dayawa but ajin mahuta daban ne shiyasa duk Wanda ya Santa a harkan yake mata kirari da suna *Ajin hutu* ita kuma ta amsa *Sai hutu* cikin zumbulelan hijab dinta Saurayin ya maidata bayan sun raba Daren nasu cikin kazantacciyar hanya kudi ya cika mata taf a Jakarta Wanda bata wani Abun Arziki sai gyaran jiki da magungunan mata mahaukata masu shegen tsada da kudin halal ne tabbas data ajiye kadarori masu tarin yawa dukda account dinta shake yake da kudi Dan bata Karamar harka, amma dayake abun sai a hankali a banza suke karewa, saitin kunnan shi takai bakin ta tareda cizon shi kadan a kunnan tana lasa, *"ka goge mun hadda ta tayau mahuta* mai kakeso incema su malam idan suka Sani tilawa? Kice musu ajin hutu kikaje, yafadi yana Kara jawota, ture shi tayi sanin idan ta biye mishi wasan zai Kara chanza salo, rufe kofar motar tayi tareda lekowa ta window motar ta furta, *sai hutu* gida ta shiga ta Danna musu sakata a hankali inda Allah kadai ke tsare iyayan nata daga barayi da masu yankan kai Dan wani zubin gafda asuba ake direta kuma basa taba Sanin tadawo bata dawo ba sudai sunsan tatafi hadda, wuce dakin iyayen tayi sai zuba munshari sukeyi hankali kwance dakinta ta shiga tana Dan rangaji Dan bata gama matsewa ba, karamin bayin ta dake dakin ta shiga ta watsa ruwa ita kanta tasan tashi takeyi saboda tsaro, tafito tabi lafiyar gado babu sallah bare salati dama sallar ta ganin ido takeyi tafi ganewa ta jerosu lokaci daya direct kamar na kwana biyu haka.



*More comments more pages*


Mr's Rumah ceπŸ’…πŸ»
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?*πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€

*Written by Anty Mamie*

*Ina matukar jin dadin comments dinku na Sani nishadi tareda karamun karfin Typing ashe haka AK keda bakin jiniπŸ˜‚ Dan Allah ayi mishi A hankali babu ruwana idan kuka hadu da fushin Aisha. Anty Mamie's Novel Group 1and 2 ina yinku sosai sosai😍 godiya mai tarin yawa fans Dina Wanda na Sani dama Wanda ban Sani ba ana tare.πŸ˜πŸ‘ŒπŸ»*

*Dedicated to Sister husnah*


6


Washe gari yakama ranar Wednesday hakan yasa halima ta tashi dakyar wurin 6:30 domin shirin zuwa makarantar Boko a lokacin SS3 take suna shirin jarabawar karshe kuma tana gama secondary school tabbas Aure babansu zai mata kassncewar basa karatu mai zurfi na Boko.

A' gurguje🀨
*Wacece halima?*

Isma'el Wanda akafi Sani da Malam liman shine mahaifin halima tareda Ma'haifiyarta Raliya wacce suke kira Mama, dukkan su yan Asalin kauyan Rano ne dake jahar kano Auren zumunci ne tsakanin iyayan nasu Wanda a tarihin gidan nasu tun kaka da kakanni masana Addini ne gaba da baya Allah yabasu ilimin Addini sosai abun saiya Zama kamar gado hakan yasa suke Auratayya tsakanin su, Malam liman na zaune a unguwan sabon gari cikin garin Kaduna ne tareda iyalan shi cikin rufin asirin Allah dukda bawata sana'a yakeyi ba I'lla iyaka duk juma'a manyan masu kudi dayan kasuwa suna daukar karatun Dare a wurinshi anan babban masallacin unguwan nasu bayan sallar isha'e kuma yana samun Alheri sosai daga wurin nasu sannan shine limamin unguwan duk Wata matsala inta taso a sabon gari tohfa shawarar Malam liman ake dauka kaf unguwan ana ganin mutuncin shi fiyeda kima, Allah ya azurta shida yara hudu rak a duniya maza biyu mata biyu, Aliyu shine Babba Wanda Dan kasuwa ne yana Aure da iyalan shi a Kano kuma yana taimaka ma iyayan nashi sosai da sosai, sai tasi'u shine na biyu Wanda yake zaune a Kano tareda Dan'uwan nashi yana taimaka mishi a kasuwancin nashi, sai Rumaisa'u itace ta Uku tana Aure anan garin Kaduna yaron ta daya rak malamin islamiyyar su ta aura, sai Auta halima wacce burin iyayanta kaf yakare a kanta yayinda suke mata soyyar da batada adadi kasancewar tun tashin ta takeda kwakwalwa sosai Ga natsuwa batada Abokin fada ko kadan ga hakuri kamar damo uwa uba sunan mahaifiyar Malam liman gareta kaf unguwan babu yarinya Abun kwatance irin halima hakan yasa dayawa ma basusan ainihin sunan taba saidai *USTAZIYA* saboda natsuwa da kamun kanta Wani abun Al'ajabi kaf unguwan babu wacce za'a nuna ace wai kawar halima ce batada kawa ko daya a unguwan saidai Abokan karatun ta a makaranta, idan akwai matsala daya a rayuwar gidan nasu toh bai wuce yanda basa lura da rayuwar halima ba dukda ita kadai ce a gabansu suna ganin tunda Allah yabata natsuwa har kwatance akeyi da ita tohfa basuda sauran tarbiyyar dazasu bata shiyasa duk abunda tayi daidai ne babu maice mata komai tun tana shekara goma a duniya ta sauke Alkur'ani mai girma yayinda tasha lashe manyan gasa tareda kyaututtuka masu yawan gske a fannin Addini dukda haka tana zuwa makarantar domin Karo karatu akan manya manyan littatafan Addini amma saida Dare kasancewar da rana batada lokaci saboda makarantar Boko daganan kuma zata tsaya lesion, tun halima Nada shekara sha'uku ta rikice tafara harka da kawayen banza yan karya data hadu dasu a makarantar boko dukda babu abunda take Sha'awa kamar rayuwar yanci da wayewa amma ganin gidan data fito shiyasa bata fito da kudirin nata a fili ba tanaso tasan duniya duniya ma tasanta, halima Nada shekara sha'hudu a duniya tafara kananan shaye shaye harda zuwa club makarantar ma ta rage zuwa sai jefi jefi Kota fito saidai ta biya gidan kawayan nata yan'club suyita shaye shaye tareda baccin asara, Mahuta shine saurayin daya kara budema halima ido sosai, sun hadu a sanadiyyar yawan ganinta dayakeyi a club nan danan yakasa danne maitarsa a fili ganin yasamu swt 14 yaita bibiyarta ganin bata Dade a harkar ba yakara samun kuzarin bude mata ido yanaso ya Raine ta tahada komai dayake bukata shine Wanda yafara kawarma da halima budurcin ta tun tana shekara sha hudu a duniya inda bata damu ba ganin ya mallaka mata duk wani jin dadin Rayuwa har gida yabata itada kawayen ta Wanda yake a GRA madaidaicin gida ne inda shida Abokan shi ke zuwa suna holewar su a gidan kawayan nata dayake korarru ne a gidan iyayan nasu, feenah da meenah, shiyasa suka tare a gidan din'din'din yayinda leema kuwa bcci kawai ke dawoda ita gidan iyayan ta, dukda haka babu Wanda ya farga da kazantar da takeyi harta iyayan nata saboda komai da taku takeyin sa.


Mahuta Dan gata ne gaba da baya irin sangartattun yaran yan siyasa Wanda babu kwaba babu tsangwama kusan duk abunda yakeyi wurin babanshi ya gada barewa bazatai gudu danta yayi rarrafe ba baban shi babban mazinaci ne hakan yasa shima ya haifi magaji a zina babu abunda basu mallaka maiba najin dadin Rayuwa dukda baban nashi yana samun labarin ta'asar da yaronsa keyi jefi jefi amma bai damu ba ganin hakan shine wayewa, mahuta bakaramin manemin mata bane kuma Dan kwaya domin baya kananan shaye shaye har cocaine sha yakeyi.




*Mr's Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*

*Yah Allah ka zaunar mana da kasarmu lfyπŸ‘πŸ»kaduna people how market?🀣ya gajiyar zaman gida? Wannan doka mun gaji da ita😭 ya Allah ka dauwamar mana da kwanciyar hankali a kasar muπŸ‘πŸ».*


*Dedicated to sister Husnah*


8


ko lekawa dakin su meenah da suketa ramokon bcci batayi ba dayan dakin tasa makulli tabude ta shiga kassncewar two bedroom flat ne sai katotan parlor a tsakiya tareda toilet Uku, kowane daki da toilet sai daya a parlon ko'ina tsaf tsaf gwanin ban Sha'awa yasha furniture's ba laifi gidan baida wani hayaniya, dakinda yake mallakinta ta shiga saboda babu mai shigar mata nan take sauke mahuta da sauran samarin ta yayinda dayan dakin kuma mallakin su meenah ne.
Cire kayan jikinta tayi batabar komai ba saidan pant da bra ta bararraje tafara sharara munshari.



Kiran sallar asuba neya farkar da Zainab duk nauyin bccin da takeyi tohfa ana fara kiran farko cikin ikon Allah saita tashi, nan ta Mike tayi salla tana zaune a wurin tana lazumi har gari yafara haske sannan tashiga bayi tayi wanka, kwalin plaster dinda ke garkame akan madubin dakin ta bude tareda daukan guda biyu, ta manna daya a goshin ta daya sace amma yabar karamin ciwo, daya kuma a gefen bakinta ta manna, blue material Mara nauyi ta dauko wacce akai mata simple dinkin doguwar Riga ba hayaniya simple make-up tayi tareda feshe jikinta da turare nan tafito Ras abunta dinkin ya amshe ta sosai dukda Zainab masha Allah kamar yanda AK yace she fat for back she fat for front tohfa haka yake a cike take taf tareda taimakon shafaffen cikinta dake tona asirin kyawun halittarta ya kwanta ya lafe kamar ba hanji a ciki, irin dogayan matan nanan ne amma ba fara bace bakuma baka sidik ba black beauty ce skin dinta mai tsada tanada kyau mai tsayawa a rai hmmmm *'nasan zakuso kuji wacece Zainab ku cigaba da kasancewa da Yar mutan katsinawa*


Saida ta kyara ko'ina na cikin gidan dukda girman gidan amma yauda gobe tasaba bata wani ganin wahalar hakan kasancewar tun Dare ta wanke kwanukan da akai Amfani dasu tareda goge kitchen din, hakan yasa turaren wuta kawai tasa ko'ina yadau kamshi masha Allah, ragowar ferfesun jiya ta dumama tareda Juyewa a cooler sai sandwich datayi tareda dafa ruwan tea Wanda Yaji kayan kamshi kan dinning ta jera komai da komai cikin rawan jiki tafito makeken harabar gidan nasu wurin jerun motocin AK ta nufa guda Uku masu kyau, 'dattijon mai gadin gidan nasu ne ya matso wurinta tana hango shi ta gaishe shi nan ya Amsa mata cikeda fara'a da mamakin ranarda zata daina wankema AK motoci kusan shekara Uku Abu yakici yaki cinyewa ba karamin tausaya mata yakeyi ba hakan yasa har Addu'a yake mata Allah yakawo mata karshe wahala wurin uban gidan nashi, a iya sanin shi baitaba jin AK ya dagama wani murya ba kokuma ya zagi wani sai matarshi hakan yasa yake cikeda zumudin San jin tarihin rayuwar su dukansu idan da Hali, sanin babu halin shiyasa ya hakura yaja kafarshi tareda komawa bakin aikinsa, 'motocin ta shiga wankewa sauri sauri gudun fitowar shi, hakan yasa tagama dawuri ta wanke su duka tas tareda gogesu ciki da waje a gajiye take lis ko wankin motocin wani katon aiki ne sanin ko kura yagani cikin motar tohfa ta shiga Uku, tana gamawa ta dauki abun gyaran flowers ta nufi flowers dinda ke zagaye da gidan nasu, dukda ada akwai masu aikin gyaran flowers din harda mai wanke mai motan tun farkon Auran suya sallame su duka a cewarsa kudinsa ya huta an kawo mishi jakar mai Aiki, cike da sabo da kwarewa tashiga gyarawa tagama komai nan ta hau sharar tsakar gidan nasu dakyar ta gama saboda girman gidan, shiganta cikin gidan yayi daidai da fitowar shi daga dakin shi sanye da dakakken suite milk color yasha necktie black da zanan milk ya tsuke fuskar nan a murtuke dukda haka yayi matukar yin kyau gawani bakin gashi daya zagaye fuskar nashi hakan yakara fito da madarar kyan shi, dogon Namiji ne fari tas Tubarkallah masha Allah, shagala tayi da kallon Sa kaunarsa na Kara ruruwa a ruhinta ji take kamar tayi tsalle ta makalkale shi, ganin batada niyyar daina kallon nashi yasa shi watsa mata Wata shegiyar harara a cewarshi kada ta shafa mai bad luck da sanyin safiya, russunawa tayi tana gaishe shi, 'ina kwana ka tashi lafiya? Kamar kullum wuceta yayi kamar tana magana da dutse kallon dining yayi yaga ta jera abinci kotakan abincin baibi ba, dama baci yakeyi ba sai ranarda tayi matukar Sa'a idan kuma batayi ba wani sabon tashin hankali ne, duk Randa tayi gigin mai tayin abinci kuwa a jikinta yake Juyewa duk zafin shi.
Tanajin fitar shi gidan a gurguje tashiga daki Kara gyara jikinta tayi tareda chanza kaya duk sun takura ta, ta matse cikin kananan kaya gajeran wando jins blue da farar vest, masha Allah ita kanta tasan Allah ya kawata surar ta, shiyasa ta dinga fuskantar matsaloli ada saboda hakan kan dining ta nufa nanta kwasa girkin ta yayinda ta koshi daki ta koma ta zumbula dogon hijab sauran abincin ta juye awani cooler Wanda yake mallakin mai gadi ne, mika mai tayi tadawo tareda kunna TV takamo Arewa24 kwantawa tayi akan doguwar kujera tanata kallo har wurin 11 taji tsamin jikinta ya dame ta baya mata dadi ko kadan, tashar ta chanza aikuwa ta kama Wata tashar wakan turawa sai karkada jiki sukeyi, nan danan ta Mike wai itama zata gwada kozata danji karfi karfi a jikin nata idanta jijjiga jinin jikin ta dukda maganin datasha a banza, rawan ta shigayi tana botsarewa sai bankare bankare takeyi tana juya cikin ta kamar yanda taga sunayi , tayi Akalla kusan minti 10 cikin nishadin data dade batayi ba ganin takoma saikace yarinya yar shekara sha Tara, karan Abu taji hakan yasa ta waigo da sauri abun mamaki AK tagani tsaye kamar gunki ya sankare yana Kare mata kallo ko kyaftawa bayayi baki a bude aikuwa a 360 tabar wurin tareda garkama makulli a dakin nata, wayarshi daya Saki ya kalla a kasa domin tunda tafara rawan ya shigo da niyyar Amsa waya haryasa a kunne yanaji ana mai magana cikin wayar amma yakasa tabuka komai............yanzu abun Aisha harya kaiga haka? Tuno wani littafin sanin sirrin mata daya taba karantawa idan bai manta ba malamin cewa yayi duk macen datake yawan mika ko bankarewa toh tana cikin tsananin bukatar Namiji, *Innalillahi wa inna ilaihir raji'un* ya furta cikin sanyin jiki.


*Shin wakesan yasan labarin ma'auratan nan masu ban Al'ajabi?* duk maiso ya daga hannuπŸ’πŸ»β€β™€




*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


7


Bakaramin San halima mahuta keyi ba inda ya kudira a Ranshi idan lokacin auren shi yayi zai iya Rayuwa da ita dukda yakai munzulin auren amma a cewarshi bayaso ya tsufa abunda ya lura Aure na saurin tsufar da mutum tun bare idan yafara Tara yara gara nanda kamar shekara 45 ya daure yayi, suko iyayan shi ko'a kwalar rigar su Dan suma American style sukeyi basa takura ma yaro a cewar su rayuwar shice yanada yancin yin komai, duk cikin bebs dinshi bai hada leemah da kowa ba a cewarshi saboda tana nishadantar dashi yanda ya kamata, kullum jinta yakeyi zamzam ko kadan bata sakaci da maganin mata hakan yasa yake mata duk abunda takeso gudun kada ta naima a waje abunda baisani ba Yammata irin halima basuda Alkawarin rike saurayi daya tunda zata iyama iyayanta basaja shi awa? yanda cikin takun ta take kula Gayu sosai tareda basu kanta jinta takeyi bazata taba Rayuwa da namiji guda daya a rayuwar taba saboda karfin Sha'awar da takeda shi hakan yasa kullum saita samu mai debe mata kewa inda take abunta cikin kwarewa tareda taimakon maganin Hana daukar ciki, tunda tataba yin ciki kusan sau biyu dakyar tasha inda a lokacin Mamarta keta zuzuta yanda tayi haske dakara cika aiko nan ta sanarda mahuta sukaje asibiti aka burge shi bakaramin wahala tasha ba hakan yasa aka daure mata bakin mahaifa, dayake Allah ba'a mai wayau saiga wani Alamar cikin a jikinta a lokacin su meenah ne suka farga cikeda tashin hankali suka koma Asibiti Ashe mahaifar budewa tayi ba karamin wahala tasha ba inda har jinya saida tayi a gida amma ankasa ganewa mama tadage da dafa mata huntu da ararrabi a cewarsu shawara ce taimata mugun kamu hakan yasa duk Wata saitaje an duba lafiyarta a Asibiti saboda ba kowani maganin planning ke amsarta ba shiyasa yakara cika ta dam dam harta fara losing shape ba tareda ta farga ba.
Halima tana cikin jerin mata masu matsaikacin tsawo itaba gajera ba bakuma doguwa ba, tanada haske farace amma ba Sol dinnan ba dirin jikinta ma babu laifi saidai batada cikar kirji sannan basuyi Kanana sosai ba, yar madaidaiciya yayinda hancin ta Dan daidai yadan bude kadan baiyi tsini sosai ba saidan karamin bakin ta tareda ido masu Dan girma, baza'a kirata mummuna ba tanada kyau mai sanyi, tareda zubin halitta mai kyau saidai kan nan nata ne toh masha Allah kamar kwallon goribaπŸ˜•a takaice dai irin gashin sister Husnah gareta🀣🀭 amma tareda taimakon karin gashi wanda dorawa kawai takeyi akai bata yarda aimata kitson shi saboda tsaro shima tana gama abunda zatayi take tunbuke shi saidai kan nata dukda bawani gashi a tsaftace yake zaka ganshi Ras da kitso maiban Sha'awa kwarjinin ta shike Sa manyan Gayu ke mutukar kaunarta duk kankantar ka indai zaka zube mata kudi toh babu abunda zai hanata budema kafa a takaice dai *The definition of halima is fake*


*Cigaban labari*


Shiryawa tayi cikin kayan makarantar nata doguwar Riga wacce tadan haura kugun ta da dogon wandon har kasa sky blue sai hijab dinta iya guiwa fari tas takalmin gida tasa flat a cewarta tunda karatun WAEC sukeyi ba'a takura musu daka ganta kaga student fuskarta babu kwalliya I'lla pawder da man baki Mara kala dukda haka tayi kyau ba laifi, wurin 7:30 tafito dauke da Karamar jaka Wanda katon littafi guda dayane a ciki shima dandai daukan nashi yazama dole ne, iyayan ta tasamu zaune a matsaikacin parlor dinsu Wanda babu komai a ciki sai ledar tsakar daki a gefe daya kuma katon dirowa ne shake da littattafai kala kala na Addini ko'ina tsaf gwanin ban Sha'awa suna zaune akan tabarma da Alama Karin safe sukeyi, dukawa tayi ta gaishe da iyayan nata cikin faraa suka Amsa mata, 'uwata ya karatu? Yakuma haddar taki? Duk inda kike da matsala wurin rashin fahimta ki gayamun sai inkara doraki akai, inji Malam liman, Toh Abba insha Allah bama Wata Matsala, "toh toh yayi haka akeso aita dagewa shi ilimi da kike gani kogi ne sai gaba zakiga amfanin shi maza zauna ki karya ki hanzarta kada ki makara ya fadi yayinda da kanshi ya tsiyaya mata koko cikin kofin dake hannun shi da Alama ko gama sha baiyi ba tura mata yayi gabanta harda ledan kosan daya siyo musu na Kari, mamanta ce ta turo mata wani kwanon Samira ta ajiye gabanta, dumamen tuwon dawa ne miyar kubewa danya sai tururi yakeyi, 'maza ki hada da wannan saboda kiji nauyi nauyi tunda keda dawowa sai shida na yamma, 'a'a mama kosan maya isheni tafadi tana shan koko cikin natsuwa, dari biyu babanta ya mika mata dari Na abun hawa dari kuma kozata siya wani Abu darana saboda yinwa gashi zata tsaya lesson din WAEC, 'baba kabarshi Wanda kabani jiya da daddare ma yananan tafadi , a'a uwata hada duka aikin chanchanci komai gurina babu abunda bazan iya miki ba dakyar ta Amsa Naira dari wacce tace kudin mota zatayi dashi, 'mikewa tayi cikin natsuwa tabar gidan a'daidaita ta nema drop ta dauka basu zame ko'ina ba sai gidansu na isa kaita Wanda yake a U/rimi GRA rabonta dawata shegiyar Boko harta manta a cewarta babu abunda kudi bazai siyan mata ba kuma tana dasu, hakan yasa harta biya ansamu Wanda zaimata komai da komai da sunanta batareda ciwon kai ba. tana isa mai'gadin su dayake zaune kofar gidan sanin cewa daidai lokacin take zuwa, gaishe ta yahau yi Kota kanshi batabi ba 'kada abar kowa ya shigo batareda ambaka izinin yin hakan Ba, tafadi yayinda tashiga cikin gidan, batajin zata iya tarban baki da safe saita huta domin bccine sosai a idon nata.





*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?*
πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€

*Written by Anty Mamie*

*Gskia sai jiya na tabbatar da masoyan littafin nan Nada yawa fiyeda tsammani na wayata har daukewa takeyi saboda ruwan comments da Addu'a a gareni nayi matukar farinciki tareda mamakin yanda kuka karbe shida hannu biyu biyu, bazan daina fadi ba comments dinku nasani matukar nishadi tareda karfin typing, Godiya mai tarin yawa Ga makaranta😍😍*
Sorry nayi mistake a last page inda zansa Sunan Aisha nasa Zainab, Afuwan typing error ne.

*Dedicated to sister Husnah*


9

*Shin wacece Aisha? Wanene kuma AK?*

Ya'u shine Mahaifin Aisha tareda mahaifiyarta Ramata Asalin yan cirani ne daga Damagaram dake jahar Nijar, inda suka shigo Nigeria lokacin da yaransu biyu, namiji da yar'karamar yarinya mace wacce mahaifiyarta Ramata ke rike da ita a hannu, a lokacin bazata wuce shekara biyu a duniya ba, namijin suna kiransa da garbati, yayinda macen suke cemata shatu, Sanye suke da bakaken kayan buzaye yayinda sukasha nadi a kansu daka gansu kaga bakin haure, daga Ya'u har Ramata irin dogayen buzayen nanne sosai wankan tarwada kyawawa Tubarkallah, yayinda cikin ikon Allah suka sauka garin Kaduna a unguwan shanu kai tsaye gidan mai unguwa sukayi inda suka gayamai kudirin suna San fara sana'a yanda zasu tallafa rayuwar su, cikin ikon Allah mai unguwn yabasu daki daya Wanda ke zauran cikin gidajan shina unguwan aiko ba karamin murna suka dinga yiba tareda godiya da Addu'a a gareshi, dakin karami ne baida girma sai window kwaya daya rak, inda Allah ya taimake su zauran nada dan fadi hakan yasa Ramata keyin sanwa a lungun zauran, yayinda suka hada bayi da mutanan dake cikin gidan dukda gidan bawani Babba bane dakuna Uku ne a cikin gidan sai bayi guda daya da kitchen dinda kowa ke Amfani dashi, batareda bata lokaci ba Ya'u ya kafa Karamar teburin shayi a gaba da gidan nasu nan danan yafara Tara customer's bakaramin ciniki yakeyi ba darana kuma saiya kasa rake duk anan wurin yayinda Garbati ke tayashi Zama a lokacin yanada shekara goma a duniya akwai tazarar shekara takwas tsakanin shida Aisha, Ramata kuwa baa barta a baya ba, wankau tafara a cikin gida, itama babu laifi tana samu hakan yasa tace barita gwada shiga cikin gidajan masu kudin unguwan kila zata Dace su dauketa wani aikin, cikin ikon Allah nan saman layin su sosai inda gidaje masu kyau suke nanta tunkara duk gidan data shiga bata dacewa harta fara gajiya ga zafin rana Ga Aisha dake bayanta sai kuka take tsalawa, ganin sauran wani gida daya Wanda yafi duk Wanda take zuwa tsaruwa tana shirin komawa gida hakanan tace bari ta gwada sa'ar ta, tun daga kofar gidan mai gadin gidan ya dakatar da ita, 'hajiya lafiya? Yana Kare mata kallo sama da kasa, kafun takaiga bashi Amsa sukaji karan horn din mota Alamar masu gidan ne suka dawo, matsawa tayi gefe tareda rusunawa, koda suka shigo hajiyar gidan ce dayara guda biyu tareda ita, babban shekaransa goma sha biyar mai suna Abdulkareem yayinda dayan bazai wuce sha'daya ba, shikuma Abdulhakeem kallo daya zakai musu kaga kallar kamarsu da mamar tasu wacce take fara kar, 'a'a lafiya? Wacece wanchan? Hajiyar ta tambaya tareda nuna Ramata daketa zuba zufa cikin tsakiyar rana, Kafun mai gadin yabata Amsa ta karaso tareda Kara dukawa gaban hajiyar tana gaishe ta, 'amsawa tayi cikin sakin fuska, 'hajiya Dan girman Allah ki taimakeni kibani aikin yi, ta furta cikin rawar murya, achan kasan layinku gidanmu yake Mijina ne mai saida shayi da rake a kasan layi, 'shigo mu shiga ciki hajiyar ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.

A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta

Please Login or Register in order to submit comment