Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin shi har rawa yakeyi nan danan yafara hada zufa gashin jikin shi a Mike cikin tashin hankali, kulle fuskarta takeyi Dan yagama kashe mata ido da hasken wayarsa bata gani, Dan girman Allah ku Taimake ni zasu kashe ni a taimaka, aaaa.....isha ya furta tareda mikewa da sauri har yana dafa bango, muryarsa dataji ne tadan Mike zaune cikin maye dakyar dukda bata gane komai Amma taga gefen fuskar shi, Yaya, kaine? Yaya ka tafi dani daganan yaya bana gani sosai kaina zai cire.. Virus kuwa ikon Allah suke gani sai a lokacin suka gane AK cikin takaici ya kalleta, yaya? Ina yayan yayan ubanwa? Kin sanni ne? In taimake ki? Uban waya kawo kinan? Kwartayan da suka fito dake lokacin nan su maidaki Dan ubanki ni kikaba Goran gayyatar Dana gayyato miki su nan? Zare mata ido yakeyi kwalla na zuba a idon shida yagama rinewa, harya juya zai tafi ya waigo tareda kallon su virus, kuyi hakuri da katse ku danayi ku cigaba da abunda kukeyi, juyawa yayi baiko waigo ba, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, AK kada ka tafi ka rufamin Asiri AK! AK!! Zasu keta mun haddi AK!!! Aaaaaaaaaaa





*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniyaπŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah.*


12



Kafun kace kwabo mutane sun yanyame zauran gidan, nan aka damki ya'u dukanshi sukeyi Kota ina matasan unguwan, suna cewa duk iskancin su bazasu taba naiman jinin suba karshan iskanci yakare uba ya nema yarsa ya'u tuni yadan dawo hankalin Sa saboda bugun daya kesha jini ta hanci ta baki babu kyan gani kanshi a fashe duk jikin shi ciwo, 'wlh na dauka Ramata ce, Allah na tuba shegiya, shegiyyaaa giya giya Allah ya tsine miki yar iska ta kassarani Allah ka dauki raina Dan girman Allah ku kashe ni banda Amfani nadauka Mamarta ce taya zan naima abunda na Haifa? Bantaba zina ba ya za'ai infara akan diyar cikina? Allah ka shiga tsakanina da giya kaimana hisabi Kin gama dani kinji dadi giyaaaaaaaa, Babu Wanda ya saurare shi, Ramata kuwa kirjinta ta dafe nanta sulale kasa sharaf, matan makota ne suka suturta ma Aisha jiki dukda ba'a tsirara take ba nan aka Kara rikicewa a tunanin su mutuwa Aishar tayi danko motsi batayi, ruwa aka shiga watsa musu yayinda Ramata taja Ajiyar zuciya mai karfi Aisha kuwa ko Alamar motsi batayi ba, Auta bilki kuwa tana manne da bango kamar mutum mutumi itama ruwan sanyin aka shiga yayyafa mata domin batada banbanci da wacce ta suma, ana haka ne Garbati ya karaso a rikice dagashi sai gajeran wando saboda rudewa, dakyar aka iya bambare ya'u daga hannun matasa, nan Abokanan garbati suka shiga lallaba su, kememe sukace sai sun kashe shi mutumin da akace an ganshi turmi da tabarya shida diyar cikin Sa ina maganar sassauci? Karku raina mana hankali mana malam, cikin dabara Abokanan garbati sukaja hankalin su da sunan bada hakuri yayinda Garbati yaja ya'u batareda sun Ankara ba saboda garin yayi duf kowa da tuchlight yake rike, ya'u kuwa babu abunda yakeyi sai tsine ma giya da cha-cha tareda yima kanshi Allah wadaran sai a lokacin yasan illar shaye shaye wato duk abunda musulunci zai Hana toh bakaramin Rahama bane a garemu muddun zaka kusance shi kuwa sai Allah ya nunama kyakyawan jarabawa akan haka, Allah ya tsine miki giya, kabarsu su kashe ni, 'suna barin wurin Virus ya karaso da abokansa yan Sara suka harda fetur da taya wai zasu kona ya'u bakaramin takaicin rashin samun Sa sukayi ba, yayinda wasu sukace a fito musu da Aisha, nan virus yace su kyale ta batada laifi, Laifin baban ne dayake mata mugunta hartaki yin Aure Ashe shike kwasar romon tunda budurwa ce su barta kawai, a zuciyar shi kuwa wani kudiri ne na daban akan hakan dayayi tunda yaga Aisha da underwear yasa ma Ranshi koda gawarta cefa saiya dandana.


Watsewa akayi babu Wanda yabi takan Ramata da yaranta kowa ya koma gida ana ruruta abunda ya faru dama Wanda bai faru ba kowada kalar labarin Sa akan lamarin, dakyar bilki ta tattaro jarumtar ta yayinda ta dibo ruwa a Roba da tsumma taita shafama Ramata da Aisha a jiki saboda rashin mafitan abun yi shiyasa tace bari ta gwada kila a Dace, Saida gari yafara wayewa Ramata ta farfado nan akai jugum jugum Aisha kuwa babu ko Alama, saida tayi yini daya Sannan aka samu kanta, babu mai iya magana cikin su kamar kurame yayinda zaman gida yagama Auran dukansu babu mai iya leka waje, unguwa kuwa anyi gulma harta takashi🀭 a'haka Rayuwa ta kasance musu babu labarin ya'u babu kuma Wanda yadamu yasani cikinsu bare ya tambaya ko maganar basu Kara tadowa ba, hidimar gidan garbati ne ya dauka gaba daya harta gidansu AK Ramata ta daina zuwa inda Mamie ta tako takanas tazo musu jaje rareda Alkairi mai yawa inda Alhaji muktar ma yabada kudi masu yawa akan abasu.


Aisha kuwa saida aka dade sannan tafara fita hijab dogo har kasa take sawa kamar da nan za'ai ta mata habaici da gori a unguwan, nan aka Sa mata suna *Ustaziya ko Yar'duniya* yayinda ta dauki kaddarar tada hannu biyu bata taba tankawa ba makaranta daina zuwa tayi Boko da islamiyya akan dole inda ko Kare baya naiman ta samari kuwa ko'yan iskan ma sun daina zuwa a cewarsu ita kakarsu ce a bariki dakyar da sidin goshi mai unguwa yabarsu sukara Zama tareda kashedi mai girma idan makamancin hakan yakara faruwa za'a hukunta su tareda koransu gaba daya, sanarwa yabada duk Wanda yaga ya'u a unguwar azo a gaya mai baice kowa ya dauki hukunci a hannu ba.









Mr's Sadik rumahπŸ’…πŸ»
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*

*Written by Anty Mamie*

*Masu cewa idan wani Abu yasamu Aisha saisun kwanta asibiti kusha kurumin ku domin a iya chemist kawai zaku tsaya.πŸ˜‚*

*Dan Allah ku dinga mun uziri idan banyi posting dawuri ba, kullum banayin kasa da page biyu har Uku inayi, kunsan halin yauda kullum ba koda yaushe mutum keda lokaci ba Ga hidimar gida damai gida, a dinga mana uziri.*


*Dedicated to sister Husnah*


14



Kai meye haku kukeyi? Inji virus yayinda yaga sauran yaranshi na zura wando, baibi takan suba ya dumfare ta babu komai a jikin shi, hankade shi daya daga cikin su yayi, oga Ashe baka gane ba, wani shegen ne zai ganmu a haka yace mu cigaba? Eye? Tarko nefa kagane mana eyeh haba baba, kasan yanda yarinyar nan suke da gidan su yaron nan AK harfa hawaye nagani a idonshi, Na Ukun ma ya amasa, 'Alkur'an nima na ankare kai, kwalawa zai kwaso mana yayinda yagama Tara mana jama'a kawai eh yanee, dakyar suka iya lallaba shi tareda janye virus da takaici ya kusa kashe shi badan yaso ba amma tabbas AK tarko ya hada musu, nifa yasin yasin tsaf dazata Aure ni zan yarda yarinyar akwai maiko yasin yafadi yana zura wandon shi, kaga Karamar kasa da Arzikin man fetur yasin kirarin irin matan nan kenan, Allah yabamu kudi muci babbar Giwa, Suna Allah ya isa suka watse a wurin yayinda suka dauki dari Uku da hamsin dinda tayar a kasa a cewarsu ko sigari Sa sha su rage zafi.
Aisha kuwa wani bcci mai karfi yayi awon gaba da ita, inda su Ramata ganin shirun bana karewa bane tace bari tabi sahu taga ko lafiya, gidan wankin tayi inda suka shaida mata Aisha tabar gidan tuni harta Amsa kudin wankin, cikin mugun tashin hankali taita duba lungu lungu sako sako babu ko tsoro, "hmmm wani Abun sai mama" cikin ikon Allah hartazo inda Aishar take yashe a kasa bcci takeyi harda munshari dalilin abunda ta shaka, salati tasaki babu halin ihu yanzun nan Sai akara fassara su da gagarumar sharri, kan Aisha ta Dora akan cinyarta tana kuka mai fitarda karamin sauti, jikin ta tashiga dubawa saida ta duba komai tsaf sannan tasaki Ajiyar zuciya, barin wurin tayi gudu gudu tareda amso pure water awani shago mai sanyi aiko ta dinga bulbula mata dakyar Aisha ta iya bude ido cikin maye a'haka ta tallabo ta suka Mike tana layi Kamata sosai Ramata tayi a jikinta a haka sukayi har gida cikin ikon Allah layin babu kowa babu Wanda ya farga, ba'a samu kan Aisha ba sai washe gari inda taita sujadar godema Allah da bata wulakanta ba, babu abun takaici GA diya mace irin zubarda budurci a titi koda Ramata tasamu labarin abunda yafaru saidai bata gaya musu zuwan AK wurin ba, mikewa tayi tareda rantsuwar za'ayi ta takare rashin gata ba hauka bane saidai subar unguwan, dakyar Aisha da Bilkisu suka lallashe ta ko garbati bai sani ba ganin ba karamin tashin hankali za'a kwasa ba, tunda Allah na Tareda mai gskia bawa bazai taba gujema jarabawar shiba idan sunbar nan suje ina? Inda zasu wayasan gobe? Wayasan abunda zai faru??
Ta hakura tareda sharadin babu inda Aishar zata Kara zuwa Abu daya zai fitar da ita daga gidan nan shine Aure insha Allah gashi kuma yana matsowa.

Musa yazo batareda boye boye yayinda Ramata ta turashi wurin mai unguwa a cewarta shine mai bada Auran Aisha, baiko nuna damuwa da hakan ba yayinda yace bai damuda sanin komai game dasu ba sun tsaida magana akan zai mata kayan fitar biki ne kawai banda lefe a cewarshi tunda ba kayan daki zata zoda shiba zaisa abunda baza'a rasa ba a dakin amma kada su cika buri, Basu damuda hakan ba sudai burin su ace Aisha na dakin mijinta dukda yace tareda iyalin Sa zai hadata, ita kanta Aishar bata damuba ganinta babu abunda zaikara sata farinciki a duniyar ta tun dataga AK dukda bawani ganinshi tayi ba gaba daya takasa sukuni ko kadan bataga Laifin shiba I'lla haushin kanta dataji daya risketa a haka shine takaicin ta, wani maganadisun soyyar shice ke fusgarta zuwa Gare shi a karo da dama tasha yunkurin kodai ta bishi gida taimai bayani ne? Sanin Ramata bazata taba barin ta fita ba hakan yasa ta rame sosai kullum tana cikin kwalla da tunanin kada yaimata fassara Allah yasa baya fushi da ita 'inda a barayin AK kuwa baida damuwa harkokin shi kawai yakeyi ya tattara ta gefe guda ya watsar komai suna Aisha ya tsana a halin yanzu.


Angama komai na Auran Aisha Ramata da garbati sun danyi bajinta ba laifi inda Ramata tasiya zanin gado guda biyu masu saukin kudi tareda risho da kula biyu masu kyau da samiru su cups da jugs da plates harda ledan tsakar daki, da kujeran tsugune, kaya dai ba laifi na fitar kunyar uwa a cewarsu basa mika ta haka gaya ba saikace daga sama ta diru, ya'u kuwa shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu.







*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*

*Anty Mamie's Novel GroupπŸŽ€1πŸŽ€2 tareda Ustaziya fans group ina mika gaisuwa ta, ana Tare.🀝🏻*



*Dedicated to sister Husnah*


15



Mai unguwa yayi farinciki sosai tun bare yanda aka Dora shi akan komai hakan yasa aka yanke ma Musa sadaki dubu talatin bayan an kwana biyu suka kawo kayan Sa rana nan akasa sati biyu masu zuwa tunda babu wani shirin da za'ai, kati aka buga mai saukin kudi akaita rabawa duk Wanda yagani saiya tofa Albarkacin bakinsa wasu na tayata murna wasu na mamakin Wanda Ze aureta a cewarsu munafuntar shi akayi wasu na ko sadaka basa so kowadai da abunda yake fadi, Ramata ta kaima mamie kati mai yawa da alewa nata Dana Alhaji aikuwa ba karamin murna mamie tayi ba baki yaki rufuwa nan taita Kara kwantar mada Ramata hankali tareda Alkawarin suma zasu bada gudunmawa mai yawa a Auran ita da Alhajin, ana haka AK ya shigo gidan daga wurin business dinshi yadawo tunda yayi sallama yaga Ramata dauke kai yayi harda juyawa, Kiranshi mamie tayi badan yaso hakan ba fuska a daure yaje, 'baka gane Ramata ba mamar Aisha wacce ka tambaya kwanaki? 'Ina wuni ban gane taba yafadi yana shirin juyawa, 'katin Auran Aisha aka kawo Aishar ka zoka gani nanda sati biyu....... Aishar babanta dai yafadi yayinda yadawo ba kunya yasa hannu ya dauki katin, kallon shi sukeyi daga Mamie har Ramata dataji wani iri a Ranta, 'Allah sarki bawan Allah, Virus zata Aura koh? Koda yake banga Alama ba su kansu maza yan iska suna neman ma yaransu uwa tagari lallai wannan ya dauko kaikayi ina fatan dai sunje Asibiti anyi gwajin kanjamau dukda maganin shi kyauta ne, 'AK wani irin iskanci ne wannan? Inji Mamie ko kadan bataji dadin Abunda yayi ba, mai nayi Mamie daga fadin gaskiya? Konayi karya ne? Yafadi yana ware hannuwa, Aisha fa nace wacce ka raina kafun tafiyar ka.....au Karuwa zaki cemun zanfi ganewa wannan Yar'iskan? Tsawa Yaji an daka mai ta bayanshi Alhaji muktar neya dawo, subhanallah Abdulkareem musulmi kake kira da munanan suna haka? Mai akai maka daga dawowa kasar? Ashe bakada hankali ban Sani ba? Mikewa Ramata tayi ido cikeda kwalla dakyar ta iya Jan kafarta batako bi takan Mamie dake bata hakuri ba tabar wurin cikin kunar zuci tareda tunanin Laifin da sukai ma duniya Tai musu daurin talala, AK kuwa daki ya shiga yayinda wani sabon tsanar Aisha ya shige shi ji yake kaf duniya baida na biyun ta a makiyi a dalilinta Mamie da Daddy kemai ihu a dalilin mai fuska biyu Yar'duniya yafadi 'gaban madubin dake manne a dakin ya tsaya yana kallon kanshi kamar zai hango Aishar a ciki.

Ramata kuwa babu Wanda taba labarin Abunda yafaru tabarma zuciyarta a ganinta fadin shi baida wani Amfani.


*Rana bata karya*


*Kai kubani kidan Amarya da Ango a sama kowa ya shirya kwaso shoki gobe nefaaaaπŸ‘―πŸΌβ€β™€πŸ’ƒπŸ½*


Sorry for d short page am occupied yau shiyasa.




*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*



16



Daddy ne zaune a parlor shida AK misalin karfe Tara da Rabi na Dare bayan sungama fira, Dadyn ya gyara Zama Alamar akwai magana a bakin shi yayinda ya kalla AK din, 'Abdulkareem , ya kirashi tareda kallon shi, 'naam dady ya Amsa hankalin shi gaba daya nakan baban nashi sanin daddy baya kiran sunan shi saida kwakwaran dalili, 'shawara ce nakeso inbaka inda hali, idan yama toh saidai muce Alhmdlh domin zanfi kowa jin dadin hakan, 'ina jinka dady yafadi tareda gyara zaman shi sosai hankalin shi akan daddyn, 'gyaran murya Alhaji muktar yayi sannan yafara magana, 'akwai yarinyar aminina business partner Dina duk Wanda ya sanni toh yasan Alhaji dan'juma mutumin kirki ne kuma mai Amana hakan yasa tuntuni na Dade dama Sha'awar baban diyarsa saboda yarda da tarbiyyan gidan danayi idan Allah ya kaimu kaje ka dubata idan tamaka harna masa magana akan zakazo kuga juna domin Kara dankon zumunci da kasuwancin namu kuma harma yafini farinciki da hakan.......'Daddy, AK ya katse shi daga maganar da yakeyi, 'ina jinka
Inji Alhaji muktar dukda baiji dadin katse shin dayayi yana magana, 'Kaimun gafara Daddy wlh tallahi batayi mun ba bana Santa Dan Allah a hadata dawani, yafadi kai tsaye bako kunya dajin nauyin mahaifin nashi 'kasan tane? Alhaji muktar yafadi cikin mamakin AK, kaje ko ganinta kayi mana, 'ban Santa ba daddy basai na ganta ba amma bata yimun ba koda naje zan Amince ne bada San zuciyata ba,
'Toh!
Toh!!
Toh!!!
Hakan yayi kyau, inji Alhaji muktar cikin rashin jin dadin Abunda AK yaimai, kanada wacce kakeso ne? Saika kawota da gaggawa niba mutumin banza bane ace shekaru nata jamaka sa'annin ka sai haihuwa suke tunda kadawo muke maka maganar Aure mai kake cemana? Lokaci kake jira koh? Toh mun gaji da Zama cikin lokacin ka, wacece wacce kakeso??
'Cikin rikicewa ganin yanda Alhaji muktar yadau maganar da zafi ba kamar yanda yayi tsammani ba sai zufa yake hadawa a zaune.....'dakai nakeyi fa inane gidansu suwaye iyayanta cikin satin nan nakeso aje gidan nasu, 'damaaaa damaa Wata ce bamu gama daidaitawa ba tukunna, yafadi cikin rawar murya, 'mttsssew Abdulkareem tashi kabani guri, naga Alama nazama Abokin wasanka ance kakawo mata kaki anbaka mata a gidan mutunci kace bakaso shin auren ne bakaso koko isa dakai ne bamuyi ba? Zakasha mamaki jeka jeka shikenan, mikewa yayi jikin shi a sanyaye yabar wurin dukya rasa maike damun shi wai ina matan suke ne? Ance akwaisu a gari sosai shi yar yanzu bai gansu bafa ya akeso yayi??


Alhaji muktar neke shirin zuwa Office dukda baicika zuwa ranan juma'a ba ko zaije baya zuwa dawuri amma tun safiyar ranar ya tashi ya shirya dawuri Mamie ceta shigo dakin cikeda mamaki, Daddyn su Abdul badai fita zakayi ba? 'Kaji mai idonki yagani idan ba fita zanyi ba mainene amfanin babbar rigar Dana Sa? Bafa nasan tambayar rainin wayau, 'Allah yabaka hakuri gani nayi yau juma'a ai sai bayan an sauko masallaci kake Fita gashi yaune daurin Auren diyar Ramata na dauka zakaje, 'auu kinga ko shaf na manta wlh Wasu baki mukeda su zasu zo daga Lagos zamuyi meeting dasu tuntuni Nike jiran kiransu saboda yau zasu toso da sassafe, karan kiran wayar shine ya tsaida shi yayinda ya dauki wayar dake kan kago cikin hanzari ya juya harshan turanci, yayi minti Uku a wayar ya katse cikin takaici sai masifa yake, 'ina amfanin rashin cika Alkawari kun tsaida mutane Dan iskanci kuce kun daga sai ranan Monday? Kaji fa, akin banza, 'ya akayi kuma mai gidana wake tabo munkai yaune inji Mamie datake shirin samai hula akan shi, 'maida ai nama Fasa fitan anyi canceling meeting din sai Monday insha Allah, yafadi tareda cire babban rigar shi, Anjima naje wurin daurin Auran ko lada na samu.


Misalin karfe daya babban masallacin unguwan ya cika makil babu masaka tsinke yayinda aka idar da sallar juma'a ana shirin daurin Aura saidai mai? Babu ango babu Alamar shi babu waliyan Ango nanfa akaita kananan surutu, a gefe daya ya'u ke zaune jikinshi manne Dana mai unguwa kassncewar tunda bikin ya matso yaita tura garbati wurin mai anguwa naiman Alfarman halartar daurin Auran diyarshi tareda Alkawarin ana daurawa baza'a Kara ganin shiba, dakyar da sudin goshi mai unguwa ya lallashi matasan unguwan akan subashi damar shigowa yau daya rak koba komai Auran diyarsa ake, yasha fararan kaya harda babban Riga sai washe baki yakeyi cikeda farinciki saikace shine angon, tunda akaga babu wani dangin ango bare angon aiko ya'u yaita hada zufa harda cire hular kanshi yana fifita dukya jike babban Riga, 'Musa ne ya shigo masallacin cikin hadin gambiza sanye da wandon farin shadda tasha guga sai Wata bakar kodaddiyar T-shirt baza ido yakeyi sai zage zage yakeyi aikuwa charaf idon shiya sauka kan ya'u daya kara makure jikin mai'anguwa, 'munafukin Allah ta'ala wato ni zaka Aurama diyarka daka gama kwakule ta saida ka tande ta tsaf zaka kawo mun tallar Auran ta? Macucu mazinaci tir duk iskancin ka ace sai kayi da diyar cikinka? Billahillazi ko balarabiya ce sai andawo da kudina tundaga kan taro zuwa sisi na bazaiyi ciwon kaiba yafadi yayinda yake nade kafar wandon shi kafun a Ankara harya shako wuyan babbar rigar ya'u ya hadashi da bango yakai masa naushi a baki, 'banda rainin hankali karuwar zaka aura mun duk mazan unguwan nan sungama saninta akace, mutane ke bashi hakuri yaki sakin ya'u a cewarsa sai an maido mai da komai saikace Wanda ya kashe kudin Arziki babu yanda baayi dashi ba kememe yaki sakin wuyan ya'u daya Kara makurewa, ya'u kuwa kunyar duniya tagama rufe shi ji yakeyi kamar kasa ta bude ya shiga kokuma Allah ya dauki Ranshi a lokacin wannan abun kunyar damai yayi kama? Dawani ido zai Kara kallan iyalin Sa a karo na biyu yakara tarwatse musu Rayuwa a dalilin gyaran dayake tunanin yayi, 'Alhaji muktar neya Mike yayinda ya tunkari wurin rike hannun Musa dake wuyan ya'u yayi, bawan Allah kaima Allah ka sake shi, wannan ai tozarci ne, fisabilillah saboda masifa ya fadar Ma yarinya ko'ince jarabawa saikuma taki auruwa? Haba jama'a ku tayani ganin lamarin nan idan ba'a Aurarda da ita ba karuwa barnar zatayi kadauki hakan akan zakayi sadakatul jari'a hakan ya kamata aima irinsu bawai Asa musu karan tsana ba da tsinuwar dake Kara dulmiyar da doran kasa bawai a dinga gudun suba Allah kadai yasan yawan ladan dazaka Sa.......''dakata dalla Malam gafara kafun in hadaku duka in tumurmusa rainin wayau kana nufin in Aure ta dukda ubanta ke cinta komai kake nufi? Toh billahillazi babu Dan iskan daya isa ya cuceni da dadin baki waikai zakai mun wa'azin bogi uban waya hanaka yin sadakatul jari'ar kai? Komu matsiyata akeso mu dinga yinta muna Auran yara karuwai idan kanaso ka burge ba haka zakayi ba saika Mike kawai a daura dakai ko mai gadin gidan ka ka Kara masa yakarasa ragowar ubanta dawata wa'azin ka Mara ma'ana sannu limamin madina kabar ganin ana kaunarka kanaso ka Kara siyan soyyar mutane da dadin baki, dalla kauce bani wuri ba maganan matsayi akeyi anan ba, 'Alhaji muktar Ranshi yayi mutukar baci ganin yanda Musa ya kwance mai zani a tsakiyar kasuwa duk girman shida daraja shida mutane keyi, abun takaici wasu burgesu Musa yayi yayinda dayawa ke dariya da ganin wautan Alhajin, cikin sanyin jiki yaje yaja hannun liman tareda makwabtan dake jikin gidan shi mutum biyu gefe suka koma cikin minti kadan liman yafara magana a lasifika,toh jama'a Alhmdlh ina cikeda farinciki tareda Kara ma Allah godiya akan lamarin daya faru yanzu wani baya taba Auran matar wani, duk a gyara Zama Dan Allah a kimtsa za'a daura Aure....'da uban wa? Inji musa, badai dani ba? Babu Wanda yabashi Amsa I'lla iyaka sadakin shida aka mika mishi dubu talatin chif, nan yaita washe baki yayinda ya zauna bako kunya harda lankwashe kafa cikin yan kallo shima yanaso ya kashe kwarkwatar idonsa, ya'u kuwa da garbati sakin baki da hanci sukayi, nanda nan jama'ar wurin suka shaida Auran *Abdulkareem muktar tareda Aisha Ya'u* akan sadaki Naira dubu hamsin nan take Alhaji muktar ya kirgo su tsaf makwabtan shi sune waliyan Ango sumai unguwa kuma waliyan Amarya duk Wanda ke cikin masallacin ba karamin mamaki yayi ba, ya'u kuwa hawaye kebin idon shi wani nabin wani yatashi jiki na rawa har inda Alhaji muktar yake zaune zubewa yayi hade da rike kafafun shi duka biyun sai bude baki yakeyi amma yakasa magana sai hawaye kawai, damke kafan Alhajin yayi sosai sai nishi da numfashi yakeyi idon shiya kafe a sama, dif ya zube a wurin zuciyar shi ta buga lokaci daya baiko motsa ba nan akayi kanshi ana salati, 'Vairus kuwa baiso haka ba domin kadan yake jira yace a daura Auran dashi dama Addu'ar shi daya Aisha tayi kwantai yaga samu yaga rashi.




*Mr's Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniyaπŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*


*Yah Rabbi duk inda na zaga duk inda na leka kowa Ustaziya harna rasa bakin Magana, waya kona amsata babu iyaka messages kuwa na mutane har wayata na daukewa, shin ta ina zan fara muku? Gskia mutum Rahama ne, nagode da Addu'ar ku a gareni masoya, Ustaziya fans group kuna Sani nishadi Mara iyaka comments dinku na jiya naci dariya, godiya gaduk masoyan Ustaziya makwaftan Aisha ina gaisuwa da kawayan ta tace ace muku adaina kushe mata Angon ta hakanan take san abunta.πŸ™πŸΌπŸ˜*


*Dedicated to sister Husnah Amarya*


17


Kan Ya'u akayi ina rai yayi halinsa tuni nan aka dauki kabbara Allah sarki ya'u ashe yanada rabon ganin Auran diyarsa Allah ya dauki Ransa a wurin daurin Auran yar'sa, jama'a nata jimamin lamarin tun bare jarumtar da Alhaji muktar yayi, liman yabada sanarwa da la'asar za'ai mai salla akai shi makwancin shi nan danan wani yaro ya ruga gida batareda bata lokaci ba Amarya taci kwalliyar ta babu laifi tayi kyau tasha lallan gargajiya inda babu wasu yan biki masu yawa sai makwaftar da gulma ce yakawo su harda masu kawo

Please Login or Register in order to submit comment