Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawa yayinda hawaye daya nabin daya a idonta....'yauwa sannan kana sakin Aishar ni zanyi sadakatul jari'ar da ita insha Allah bazaku maidani karamin mutumin banza ba dattijon banza Wanda bai isada gidanshi ba kunji na rantse muku, AK kuwa mutuwar tsaye yayi cikeda takaicin Daddy Anya daddy ne kuwa? Idan shine kuma maiya same daddy a'yau? Daddy na shirin barin wurin mamie ta fada a kirjin shi tareda sakin kuka mai cin rai, Ashe zaka iya Rayuwa batare dani ba? Ashe akwai Ranarda ko'a mafarki Zaka iya dangantani da kishiya? Wlh ban zuga AK ba harga Allah mijina babu abunda yarinyar nan ta taba mun Allah yabasu zaman lfy tunda abun yazama haka wlh kowa ya gyara Auran shi bazan bari Aurena ya mutu ba saboda na wani, 'dariya taso taba daddy dakyar ya iya gimtse dariyar Sa, 'haba mamie wlh an cutar dani kada kimun haka, inji AK dayake tunkaran iyayan nashi, 'wlh Abdulkareem kowa yaje ya gyara Auran shi bazan koma gida yin zawarci da tsufa naba bayan haka inasan tsohon mijina ban hadashi da komai ba a duniya dukda ina sanku banda kamarku amma sanku bai isa ya kashe mun Aure naba tareda rugujemun soyyar shekara Arba'en danayi ba, Kara Rungume ta Daddy yayi a jikin Sa cikeda kaunar matar tashi, Yauwa yanzu ne bilkin shi tadawo bilki amma da dukta rikice an birkita mishi mata, Sakinta yayi yayinda ya tunkari dakinsa, 'Dadyn su Abdul na tuba Dan Allah kayi hakuri mai gidana, tafadi harda daga muryar ta, baiko waiwayo ba bayaso ya nuna mata ya sauko dawuri saiya Dan Kara gasata nan gaba bazata Kara jayayya da hukuncin saba, 'AK barin wurin yayi yayinda ya shiga dakinsa da hanzari ko ganin Gabansa baiyi sosai cikin minti Uku yafito da karamar jakar kaya a hannun Sa, 'Yau saika haifi da'mai bakin ciki? Inji Mamie tana kallon AK na saukowa daga steps, 'ina Zaka? Muddun ka dauki hukunci akan Yarinyar nan bazan taba yafe maka ba Abdulkareem kaji na gayama wlh Aure da ita kasama ranka kamar kafara ne mutu ka raba kaida ita muddun ina numfashi idan ba haka ba kuwa bazan yafe maka ba, Aure baifi Aure ba, 'tuni AK yabar gidan cikin motarsa kamar zai tashi sama kanshi kuwa kamar zai fashe tuni zazzabi da ciwon kai mai zafi ya rufe shi dakyar ya iya karasawa 17th hotel tareda kama daki na kwana uku, cikin rawan sanyi ya zube akan gadon dakin kuka ya fashe da karfi kamar mace yana dukan gadon a hankali, 'why Aisha? Why cikin mata maiyasa saike? Maiyasa kika koya mun muguwar tsanarki? Maiyasa? Dukda na guji rayuwarki maiyasa kika sake shiga duniyata tareda zaban Rayuwa dani? Kin cutar dani Aisha wlh bazan yafe miki ba bani kadai zan rayu da bakin ciki ba dukanmu mun rasa abunda mukeso daga rana tayau dukanmu zamu rayu cikin kunci wlh zan dandana Miki kunci kwatankwacin Wanda kika Sani a ciki, maiyasa zanga Aibun ki? 'Yah Rabbi ka sassauta min Aisha a cikin zuciyata, ka rage mun ita ta dameni, kuka yakeyi yana rawan sanyi jikin shi kuwa kamar garwashin wuta saboda zafin zazzabi.

Mamie kuwa wanka ta dauka tareda tsara girki mai matukar dadi cikin gaggawa ada ta kudiri niyyar babu Wanda zaici abincin Dare a gidan saboda Auran AK harsai an mata abunda takeso shiyasa tun kafun daddy ya farga batayi girki ranar ba ta shiga cikin hanzari tayi, Abdulhakeem kuwa yana makaranta achan Egypt gidan babu kowa sai masu aiki da Mijinta hakan yasa ta tunkari dakin shi domin Kara lallashin Sa sai kamshi take zubawa mai tsayawa arai.




Washe gari kuwa karfe goman safe ta shirya cikin shiga ta Alfarma yayinda itada masu aikinta dake dauke da manya manyan kuloli shake da Abincin sadaka Wanda tun daran jiya tasasu dafawa da asuban farin yau, Abinci ne mai rai da lafiya haka aka daddauki kulolin da kwalayan lemuna da ruwan gora katon katon kai tsaye gidan Rasuwa suka nufa hakan datayi ba karamin Kara soyyar ta yayi a zuciyar Alhaji muktar nanda nan tausayin matarshi ya shige shi ganin yanda take matukar tsoran rabuwa dashi, 'Cikeda mamaki Ramata ta tarbe su hannu biyu biyu a kasan Ranta kuwa taji dadi sosai sai a lokacin hankalinta yadan kwanta kwana tayi da tunanin yanda Rayuwar marainiyar yar'ta zai kasance a gidan Alhaji muktar tareda kallan da Mamie zatai musu, samun kanta tayi da washe baki hadeda godema Allah a fili, mikewa Aisha tayi tana gaishe da mamie har kasa ta tsuguna cikeda kunya zata bar dakin Mamie ta rike hannun ta tareda zaunar da ita kusa da inda take, 'gaisuwa Tai musu na rashin da sukayi sosai itada ja'maar gidan ta sannan tace musu Alhaji muktar yace akara musu gaisuwa mika ma Ramata Envelope tayi cikeda kudi a cewarta Alhaji muktar neyace abata, kememe Ramata taki Amsa da ada ne Amsa zatayi amma yanzu bataso suga kwadayin su tunda anzama sirikai kada ace sun siyarda yar'su, dakyar da sudin goshi aka samu Ramata ta Amsa harsaida mutane sukasa baki a cewarsu ta Amsa a matsayin sadaka ba'a maida kyauta, nan yan'unguwa akaita shigowa kwasar abinci mai raida lafiya tunda sukaga shigan kayatattun kulolin Abinci da Hajiya bilki nan akaita shigowa har babu wurin Zama kamar an bada sanarwan jama'a, Mamie tayi minti ashirin a gidan yayinda ta Mike zata tafi, riko hannun Aisha tayi tace ta biyo ta zasuyi magana, kiran Ramatan tayi har waje suka shiga bayan motan ta saboda jama'a dake wucewa, 'Aisha kokuma ince diyata tunda yanzu anzama daya, Dan Allah ki gani kiki gani, duk abunda zai shiga tsakanin kida AK kiyi hakuri kada ki biye mishi ki daure kuba Mara da' kunya Yanzu kowa jira yake aga yanda zakuyi kada ki biye mishi duk abunda zai miki kiyi hakuri kodan saboda ni kinji diyata? Harda rikema Aisha Hannu wacce kunyar duniya tagama rufeta, duk abunda ke damunki ki gayamun ki daukeni a matsayin uwa keda AK mutu ka raba insha Allah nanta roki Ramata Alfarman Kara tausasa Aishar inda sukaita godiyar jin dadin Abunda hajiya Bilkisu tayi nan duka bakin cikin Ramata ya yaye koba komai Aisha tayi dacen surukai ta fannin AK mai sauki ne dama ganin yanda AK din ya tsani Aishar da furicin dayayi a gabanta babu ko kunyar ta a matsayin Mahaifiyar Aishar shike hanata sukuni.

Aishi kuwa dukta kosa ayi sadakan bakwai akaita gidan mijinta masoyinta ji takeyi kamar ace ta tashi ta naimo shi ta bishi, gawata azabar soyyar shida ta Mike mata kullum cikin murmushi zaka ganta batada damuwa ko kadan Yanzu ko bcci takeyi sunan AK take kira mafarkin AK babu Wanda batayi harsai Ramata ta girgiza ta ko bilki, abun yafara damun Ramata inda cikin takaici tafara tankama Aisha, Kidai yi a hankali wlh ba baki nai miki ba muddin kika nunamai soyyar nan zaki sha bakar wahala ace ayi mace ba kunya wannan wace irin Rayuwa ce kika daukan ma kanki dakon soyyar wahala? 'Ummah wlh yayi AK na sona kila fiyeda yanda nake sanshi, 'haka ya gaya miki? Yaushe kika ganshi? Koko sako ya aiko miki na soyyar taki? Kidai yi a hankali banasan hauka da rashin kamun kai, 'Idan Ramata tayi furucin nan Haushi Aishar keji sosai, hakan yasa tafara lallaba Auta bilki akan ta leka mata kofar gidansu AK ko zatagan shi tanaso taga ko yana lfy kwana biyu tarasa sukuni tanasan sanin lafiyar mijinta? Kai tsaye bilki tace mata bazata jeba aiko nan taita dukan bikin cikin takaici, 'wlh Anty kozaki kashe nine babu inda zanje ni wlh haushi yake bani ma ace ko gaisuwa yakasa zuwa yayi mana sirikin shiya rasu haba Dan Allah, 'ke mai kika Sani? Gaisuwa banda Wanda mamarshi taxo tayi a madadin shi? Harfa masu Aikin gidan su sunzo mana gaisuwa da tarin Alheri mai yawa, 'Ramata dake girki a zaure tashi tayi cikeda takaicin Aishar shiga dakin tayi mafici ta dauka ta buga ma Aishar, sannu dadi miji saikije gidan nasu ki bishi, fitar min a daki Mara kunya Kifa kiyaye ni Aisha wlh ranki zai baci akan yaron nan, turo baki Aishar tayi tana gunguni, mutum da mijinsa sai a hanashi jin yanda yake? Gskia baai mata Adalci gara tayi tayi tabar musu gidansu.


Alhaji muktar neya sauko daga dakin shi misalin karfe sha'biyu na rana yana shirin fita, kwalama Mamie dake kitchen tareda yan aiki suna girki kira yayi, 'amsawa tayi hadeda shigowa parlon nasu Zama kusa dashi tayi, Dadyn su Abdul harka shirya Ashe, 'Eh zan Dan fita nisa zanyi sai yamma zan dawo insha Allah, Allah ya dawo dakai lfy mai'gidana Angona ni kadai ta furta cikin murmushi, mikewa yayi sannan ya kalleta, 'danki bai dawo daga gudun hijirar dayayi bane? 'Uhm bari kawai lamarin AK sai a hankali wlh haryau babu labarin shi mamaki yake bani sati daya babu shi Anya Alhaji ko za'a bada cigiyar sane? Duka wayoyinsa a kashe office ma yadaina zuwa, 'bawata cigiyar katon Saurayin dazan bada yanda ya dauki kafa yabar gida toh zai dawo da kafarsa, idan yadawo kice ya gaggauta barin mun gidana nima, Ga mukullin gida na Wanda ke Malali GRA ba'a Dade da kammalawa ba ki bashi ya tarkata yanasa yanasa chan zasu zauna kafun in kai masa matarshi insha Allah.





*Mr's Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*

*Alhmdlh nadawo nagode da Addu'ar ku masoya, Gskia banyi niyyan posting yauba but Alkawarin danayi shiyasa kuka jini masu kirana suji lfy ina godiya sosai😍, Zaku cigaba dajina insha Allah daga yanzu*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


19



Ak kwance yake akan gadon dakin hotel dinda yakama a yanzu gadon baida banbanci Dana asibi saboda tun daga ranar daya sauka a dakin ciwo yaita yi kamar bazai kai labari ba family doctor dinsu yakira nan aka Dora mai ruwa babu yanda likitan baiyi akan zaifi samun kulawa a Asibiti Sam yaki yarda yayinda yaima doctor din kashedi mai tsauri akan bayasan iyayanshi Susan inda yake harsai sun neme shi, kimanin kwana Tara kenan yana kwance a dakin dukya fige ya rame sai uban farin daya Kara likitan ne atare dashi yayinda yagama zarkada masa Allurar karshe daya gama Amsa a ranan kashedi yaimasa akan yarage tunani domin yana gafda kamuwa da ciwon zuciya banda hawan jinin dayake dashi a halin yanzu, godiya yaima doctor din nan yafara hada yanasa yanasa a cewarsa ko mutuwa zaiyi gara ya mutu a gaban iyayan shi ba'a dakin hotel ba dukda bawai ya yafe musu cutarshi da sukayi bane😑aa zaidai koma ne kila a yanzu sunyi nadama sun kuma San zafin rashin Sa a kusa dasu, misalin karfe Tara na Dare ya shigo falon nasu yayinda yake tafiya kamar Wanda kwai ya fashe ma aciki hannun shi rikeda jakar gudun hijirar Sa, Daddy da Mamie na zaune a parlor suna kallo cikin nishadi kallo daya zakai musu ka tabbata basuda damuwa, sallamar sane yadawo dasu nan Mamie ta Mike da sauri ta tarbe shi tana salatin ganin yanda ya rame shiko gogan Kara murtuke fuska yayi adole fa anmai laifi, wani irin ciwo kayi haka ka ganka kuwa? daddy kuwa kallo daya yaimasa ya kauda idonshi ya cigaba da kallon shi, 'Ciwo kayi ne AK ka ganka kuwa? Kanaso ka halaka kanka akan abunda bai taka Kara ya karye bako? Tafadi rikeda hannun shi har bakin kujerun parlorn kememe yaki Zama a kujerar, 'yanaga kadawo dawuri? Koko sauran kayan ka kazo kwasa? Aida bakaxo ba saika yi waya idan yaso maba bireba yakawo maka sauran kayan inji Alhaji muktar yayinda ko kallon AK baiyi ba, shiko wani takaici yakara turnuke shi ganin iyayan shi sun daina sanshi da tausayin shi duk akan wata shegiyar Aisha, 'dukda haka bata baci ba zan yarda kayi kwanan karshe a cikin gidana, naba mamarka makullin daya daga cikin gidajena kaje chan ka zauna insha Allah nakusan kawo maka iyalin ka, 'nifa banda kudin dazan iya zuba kaya a cikin gidan, inji AK
Cikeda mamaki Mamie ta kalle shi wai AK ne baida kudi, 'Karka damu ai ninaga zan iya nasa muku duk wani abunda zaku bukata a matsayina na Uban Amarya uban Ango kuda akaima Auran gata? Lefenka ma ake hadawa bana bukatar ko kwandalar ka, ahtoh daddy yafadi yayinda AK ya wuce daki kai tsaye cikin takaici.


AK ya tare a dankareran gidan su Wanda ya hadu ya hadu ya hadu harya gaji da haduwa, gidan ba gidan sama bane four bedroom ne manya manya sai katotan parlor Guda daya a tsakiyar dakunan yayinda kowane daki yanada bayi harda parlor kowani daki saida a zuba furniture's hadaddu parlor kuwa Royal kujeru ne har set biyu sky blue da Orange, sai barayin dinnin dinda aka kewaye shida transparent glass komai na wurin white ne gskia dady ba karamin kudi ya zuba a gidan ba, hmmmm sai Wanda yagani bari inyi shiru kada ace zan zuba karya🀭.


Mamie ce ta aika gidansu Aisha aka amso measurements din kayan ta da size din takalmi da undis nan aka hada mata lefen ta mai rai da lafiya akwati set daya yayinda aka dinka kayan ciki sosai bayan an kwana biyu Mamie da kanta tazo da direba inda ta dauki Aishar basu zame ko'ina ba sai babban boutique English wears taita jidan ma Aishar a cewarta so takeyi ta rikita AK tanaso taga yazo ya durkusa yana musu godiya akan aura mishi Aishar da akayi kunya ta cika Aishar inda take ji kamar ta nutse a kasa, kaya ne naban mamaki masu daukar hankali ko kunya Mamie bataji ba nanta dinga gayama Aishar kissar mallake miji cikin dabara saikace ba sirikarka ba, itako Aishar jinta takeyi a sama duniyar ta fes, tun daga ranar Kullum da safe zatazo ta dauke ta takaita wurin gyaran jiki na amare, hmmmm Allah sarki Naira, cikin kwanaki Uku kachal Aisha tayi masifar kyau naban mamaki tayi fresh color dinta yakara fitowa gashin nan ba'a magana yayinda akaita dura mata maganin mata a zuciyar Mamie kuwa sotake AK yayi har kukan Agwagwa Ranan 1st 9ytπŸ˜‰oooh su Mamie iyayan Zamani, ranar karshe Kunshi akakai Aisha akai mata baki daja, hmmmmmm Kara gyara mata kanta akayi inda Mamie ta hadata da turaruka masu matukar kyau da motsa Sha'awa, sai wurin la'asar suka dawo nan take shaida ma Ramata akan daddy zaizo karfe Tara na Dare shi da kanshi zaikai Amarya dakin ta ba'a bukatar yan rakiya idan yaso bayan an kwana biyu sai aje aga daki, Hmmmm zo kuga bakin Aisha har saida yakusa yagewa saboda murnar zata kwana da masoyin ta ayau, tunda yamma Ramata ta hada mata ruwan wanka na turare kala kala, nanfa Aisha abun naima yasamu taita durzan fatan jikin ta a cewarta ayau zata fara hada jiki da Rabin Ranta muradin ta AK, shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu yayinda Ramata take shirin binta bayin sugani ko wani wabu yafaru ne ko nakuda takeyi ai ya isa ace ta haihu Yanzu inji Ramata, haba har ana shirin shin sallar Isha'e, Aisha kuwa badan taso ba ta fito kassncewar ruwan yakare kuma fatar jikinta yafara zafi durza yasha bana kadan ba, 'harara Ramata tabita dashi, aina zaci bcci kikayi a bayin, Kota kansu batabi ba tafara kwalliya mai daukar hankali tana rera wakar soyya cikin nishadi.

"So bai karewaaaa
"So bai chanzawa aaa
"Wanda nake kauna "da'eman fa bazai "chanza baa gani gaka, harda rufe fuska a dole tanaba kanta kunya, bilki kuwa daga uhmm sai uhm uhm, suna ganin ikon Allah, turare taita sawa kala kala saida bilki ta kwace kwalbar a hannun ta, nan tasaka wani dankareran red lase dinda yagaji da haduwa cikin kayan lefenta Mamie ta bata dazu tace shi zatasa idan za'a kaita, lefenta tuni ankai mata gidanta ko ganin shi basuyi ba a cewar Mamie Sa gani achan gidan, wow bilki ke cewa ita kanta yayar Tata tamata ba kadan ba ko makiyin ki wlh Anty Aisha idan yaganki saiyace shegiya amma fa tayi kyau, mayafin kayan tasa Wanda keda digo digon baki tareda flat shoes tasha dankunne ta sarka da zobe harda agogo da warwaro sak Amaryar masu kudi sunan da bilki tasa mata kenan a lokacin, 'Ramata da garbati sai santin ta sukeyi saikace ba ita ba lallai kudi sunyi, nan sukaita mata nasiha da fada mai shiga zuciyar mai sauraro inda Ramata keta kukan rabuwa da murnar Aurarda Aisha, itako Aishar batama San sunayi ba dukta kosa daddy yazo inda Rabin fadan dasuke mata ke shiga kunnan ta ya fita ta dayan kunnan jefi jefi tana Satan kallon agogo wurin karfe Tara saura, maiya tsaida Daddy? Itafa takosa akaita taga mijinta, 'toh Kidai rike maraicin ki kinsan wacece ke basai na tuna miki ba mu talakawa ne lis bamuda gata saina Allah, ke ai ko ba,ai miki fada ba ya isa kima kanki ganin irin Rayuwar da mukeyi har a unguwan nan, hakuri Aisha, Hakuri bazan daina maimaita miki ba, kiyi hakuri, girgiza kai kawai takeyi cikin mayafi sai a lokacin ne ta matso jaririn kwallar rabuwa da yan'uwanta bilki kuwa kuka takeyi kamar zata suma saika rantse itace Amaryar dukta kankame Aisha, aikowa akayi daddy yazo daukar ta, inda dakyar garbati ya sashi shigowa suka gaisa sama sama da Ramata daketa zuba godiya da kuka, rike hannun ta bilki tayi inda ta bude mata bayan motan ta zauna yayinda daddy ke zaune gaban mota shida driver dinshi, Inda akace bilki zata kawo mata kayan da akai mata anan zuwa jibi insha Allah,motar na tashi ta tsinci kanta da muguwar faduwar gaba tareda fargaban yanda daren nasu nayau zai kasance itafa tsoro takeji Allah yasa AK ya bita a hankali saboda tataba ji Wata yar'islamiyyar su tana bada labarin 1st 9yt dinta idan tace har saida ta suma, hmmmm nan takara rikicewa tana Addu'ar Allah yasa mijinta yabita a hankali.



Bakaramin rikitata gidan nata yayi ba ko'a duniyar mafarki bata taba gani da zuwa irin gidan nan Wanda harya gaji da haduwa ba bare kuma ace nata ne, ooh Allah kenan Dare daya yakanyi Bature, da Addu'a ta shiga gidan kamar yanda Ramata ta umarce ta, wani sanyi AC neya ratsa su yayinda gogan ke kwance nashe nashe yana shan madarar shanu mai kyau cikin kwanciyar hankali yake kallon American movie dinshi sanye da kananan kayan shan iska su matukar yimai kyau, mikewa yayi tareda gaishe da daddy cikin fa'raa da murna kamar bashi ba, shi kanshi daddy yayi mutukar mamakin sauyin AK, kodai ya dangana ne? Inji daddy, idan ma bai dangana ba dole zaiyi kuwa, a zuciyar shi yake fadi yayinda AK da Aisha ke zaune a kasa daddy nakan kujera, nasiha yayi musu mai shiga jiki tun bare AK yaita tausasa shi har saidaga karshe yatashi ya Mike tareda kallon Aisha, 'zan aiko miki da waya na tambayi mamarku tace bakida waya zansa miki number na a ciki, zan dinga jin yanayin zaman naku ko kallon banza yaimiki Wanda zuciyar ki bata amince dashi ba kiyi gaggawan sanar dani, Allah yaimiki Albarka yabaku zu'ri'a dayyiba, kaikuma ina jiranka ka aiko min da gawarta domin yanzu mun Riga Munsa kafar wando daya ni dakai, 'subhanallah daddy Dan Allah kayi hakuri nayi nadamar abunda naimuku kaida Mamie insha Allah babu Wanda zaiji kanmu katayani ba Mamie hakuri idan an kwana biyu zamuzo sai in Kara bata hakurin, cikin jin dadi Dady yace, 'a'a kuyi zaman ku kada kaje ko'ina ku huta Sannan kuzo, fita daddy yayi yayinda AK yatafi mai rakiya, tunda suka fita takara gyara mayafin kanta a cewarta angon ta ne zai yaye mata kamar yanda akeyi a Al'adance, shiko AK tun shigowar ta parlon turaren ta yagama susuta shi wani irin turare ne wannan? Kai waya bata? Gskia kamshin shi yamasa jiki a mace ya shiga parlon.




*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah*



20



Tanajin motsin shigowar Sa takara natsuwa dakin shiya wuce kai tsaye Kota kanta baibi ba, inda shiru shiru babu ango babu labarin Ango kafarta harta fara tsamin gajiyar Zama gawata yinwa datake ji rabonta da abinci tun rana saboda zumudi batama wani ci sosai ba a cewarta yau zataci kazar amarci, har karfe sha'daya darabi shiru tana zaune a wuri daya inda sai a lokacin hankalinta yakara tashi toh kodai ya manta an kawo mishi Amaryar sane? Gashi taga yakara mata wani masifar kyau dukda ta cikin mayafi ta kalle shi, shiko gogan yana kwance nashe nashe akan gado sai chatting yakeyi a Facebook tareda frnds dinshi hankali kwance inda kamshin turaran ta daya shaka duk yabi ya hanashi sukuni, tsaki yaja a karo ba adadi tareda mikewa, gskia dole in nema matar mutunci in Aura mutum shi kadai kullum Ga Sha'awa hakurina yafara karewa shekara talatin da biyu ba wasa ba, ya furta parlon ya wuce ta inda ya dinga bin wutan gidan yana kashe wa haryazo kanna parlon, kashe kayan kallo yayi harya kashe wutan parlon ta Mike ganin baisan da halittar taba, 'Yaya AK, tafadi cikin hanzari ta Mike,Yaya..tasamu kanta dajin nauyin shi inda lokaci daya ya tsaya yana Kare mata kallo hadeda kunna wutan parlon, 'ya akayi? Menene? Jarabarki ta motsa ne?? Ooooh ba haka kikai tsammani bako? Kin saba jin namiji kwance akan cinyarki wace irin Amarya ce wannan? Banda iskanci harkin fara nema na uwar mai zan miki Wanda ba'a taba miki ba? Look bari in kankara miki warning na farko yafadi yana nunata da yatsa, nidai ba mazinaci bane asalima ko yatsar Wata macen ban taba rikewa ba ma'ana ni tsarkakekke ne tas Alhmdlh, sannan ni bantaba cin diyar Wata ba, duk Randa kika Kara mun magana kiyi kuka da kanki kada kisake kiyima kanki wani kallo na daban a cikin gidan nan, kisama ranki kinzo a lokacin bayi, rayuwar bauta zakiyi idan nace miki yar'aiki toh kinsamu promotion, noooo noooo ke baiwace black monkey kawai wawiya mazinaciya mai fuska biyu simi simi kamar mutuniyar Arziki idonshi harya fara rinewa yayinda Aisha kafarta Sam takasa daukarta hawaye daya nabin dayan jikinta na wani irin rawa yayinda zufa yagama wanke ta dukda sanyin AC, takowa yayi har gabanta murmushi kwance akan fuskar shi wuyanta ya shako hadeda dago kanta yana mata kallon kiyayyah, congratulations na tayaki murnar samun namiji Irina Wanda babu kamarsa amma kamar yanda zaki fara ganin babu kamana a mugunta, congratulations daga rana tayau kunyi bankwana da farinciki a duniyar ki, ina tayaki murnar sabuwar rayuwar bauta, kakari tafara cikeda azaba nan yayi wurgi da ita kan glass cup dinda yagama shan fresh milk bakaramin bugewa tayi a kanta ba, juyawa yayi sannan yakara dawowa, 'Akwai mai gadi na dattijon Aziki ina neman Alfarman kada ki bata tsohon mutane domin mijin marigayiya ne ance kefa jarabar taki har tsofaffi baki bari ba, kiyimun Alfarma iskancin ki ya tsaya a waje banda yan aikina wlh wlh zan iya kashe ki har lahira Randa na kamaki dawani a gidan nan, sannan inada masu bama flowers ruwa damai wanke mun mota, congratulations a dalilin ki kinsa sun rasa aikin su bazan barki da gattin samari masu jini a Jika a cikin gida ba kamar naba kura Ajiyar nama ne, 'kanshi yadaga Alamar yana tunani chan yadawo ya tsuguna yadago fuskarta da hawaye yagama wankewa, 'bazan taba baki damar kizama karuwar gida ba kada kazantar zunibin kiya halakamu baki daya, idan jarabar kita motsa kinsan inda zaki GA kwartayan ki, Wuceta yayi hadeda rufe bedroom dinshi harda Sa mukulli a cewarshi kada taimasa fyade tunda ankawo ta cikin maza babu abunda bazata iya ba.

Anan ta kwanta kanta dukya kulle tarasa abun yi inda sai wurin biyun Dare ta Mike taci kuka harta gode Allah taita shiga sauran dakunan harta gane dakin ta saboda ganin hadaddun akwatunan lefen ta, komai na dakin dark purple ne yayi matukar kyau amma Sam bai burge taba Yanzu dama ba Auran soyya tayi ba? Mai AK ke nufi?? Dukda taji matukar takaicin abunda yaimata amma soyyar shi nanan daram dam a zuciyar ta.

Tun daga ranar tafara aikin bauta a gidan, AK ya kori matasa masu gyara gidan a cewarsa ankawo kura cikin garkin nama kudin

Please Login or Register in order to submit comment