Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da taimakon likita suka sashi a motar likitan Aisha da Ak na baya kanshi akan cinyarta sai girgizashi takeyi, kada ka tafi idan katafi basuda asara ni sukaima asara ya zanyi Yaya AK kafi kowa sanin kaine farincikina Dan Allah ka kasance dani wlh bazan gujeka ba koda zaka dinga dukana kada ka mutu, kwantar da hankalinki madam bazai mutuba insha Allah inji Doctor daketa zuba gudu a titi, Kai tsaye dakin Emergency akayi dashi Dakyar aka Hana Aisha shiga wacce tagaji dacin kuka harta gaji.

"Baki na bude ni Mamie ganin yanda Aisha ta bankeni harsai Dana kai kasa a kokarina nabinsu Asibiti domin dauko muku rihoto inaji ina gani aka badeni da kura suka barni tsaye nida baba mai'gadi, kokarin shiga gidan nakeyi tsawa mai'gadi ya dakamun, 'toh uwar gulma masu gidan basanan mai zaki musu a gida kuma?Sakata yasa yabarni cikeda takaici na watsar da Alkalamina nayi cikin fushi 'muma mijinnan munada shi bare a karya mishi ni a banza😑da gudu nayi wurin My RumahπŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€naga kowa nashi yasani.




*Mrs Saddiq Rumah πŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah*



34




Bakaramin artabu akasha wurin daidaituwar numfashin nasa inda saida aka kwasa mintuna mai yawa sannan Aka samu nasarar numfashin Sa Kiran su Mamie Aisha tayi tana kuka ta shaida musu suna asibiti batareda bata lokaci ba Mamie da Daddy harda Abdulhakeem suka rankayo Auta bilki ma ba'a barta a baya ba Ramata kuwa cewa tayi zatazo da yamma duba jikin nashi, aikin lallashi bilki ta shigayi inda Aisha ke makale jikin Mamie yayinda take musu bayanin iya abunda tasani salati suka dauka gaba daya daddy na girgiza kanshi cikin takaici, maganin shi kenan ai duk Wanda baijin Maganar iyayanshi taya yake tunanin ganin mai kyau a rayuwar Sa yara ana nuna muku gabas kuna yamma tafi kyau Wanda baiyi sharar masallaci ba wlh harta tasha zaiyi ina amfanin irin wannan? "Haba Alhaji haba Alhaji kadaina yin furucin nan shin bawa na wuce kaddarar sane? Mudauki haka akan shine jarabawarsa Saimu rakashi da Addu'a tareda nasarar cinyewa, tausasa daddy Mamie keyi ganin yanda Abun yaimasa ciwo sosai ita kanta Mamie tausayin dan'nata neya gama rufeta doctor neya katse musu jimamin da sukeyi yana share zufa da farin hankacif cikeda gaisuwa yake sanarda daddy akan zaiyi mgn dashi a Office inda hali, binshi daddy yayi nan likita yafara bayani, " duk mai imani yakamata ya tausayama AK halinda yake ciki Wanda komai yafaru akan idona saidai muce Alhmdlh Allah ya takaita munyi iyakar kokarinmu wurin dawoda numfashinsa dake kokawa sanadiyyar bakin cikin dayake ciki Wanda zuciyarsa tafara kumbura da taimakon ubangiji tunda bayin mu bane Alhmdlh komai yana shirin dawowa daidai Dan Allah Alhaji arage bata masa rai kassncewar Sa mai zurfin cikin gaske shiyasa Ciwon yayi saurin tasiri a gareshi yanada damuwa tattare dashi ku taimaka mana dashi kanshi wurin kwantar masa da hankali tareda dauwamar da murmushi a gareshi, godiya daddy yayi cikeda tausayin AK.


Tunda mahuta ya figi mota bai zame ko'ina ba sai gidan iyayanshi inda tun'da mai'gadi ya bude mishi kofa ya watsama su meenah kallon banza wadanda suke cikeda gulmar sanjin abunda yafaru amma ganinshi a halin nan yasasu tsuke bakinsu dukda ba hakan sukaso ba amma ko banza sun huce haushi tunda sunsan bakaramin bomb Aka tadar a gidanba tabbas yakuma tashida dakin hutu.......uwar mai kukemun a mota kananan yan'iska ko bina gidan iyayena zakuyin? Jiki na rawa ganin yana shirin huce haushi akansu suka shafama kansu lfy inda Meenah ta leko da kanta ta windon motar, "dan Allah kabamu na mota wlh bamu fitoda jaka ba.......idan banci ubanda ya haifeku ba shege nake, kokarin bude motarshi yakeyi a kufule tuni suka kama gabansu ganin yana shirin musu tijara da sanyin safiya suna tafiya suna tikar dariyar murna harda hawayan farinciki inda basuda burin daya wuce na ganin leemah tareda sanin halinda take ciki.

Mahuta na layi kanshi kamar zai fashe mommy sane da daddy suna karyawa a dinning section ihu momnyn Sa tasaki ganin shalele na shirin faduwa fuska jini da majina da gudu suka tashi har'rige rigen rikeshi sukeyi itada daddyn Sa inda babanshi yaita kunduma manya manyan Ashar tareda rantsuwar daukan fansa akan duk Wanda keda hannu akan abunda akaima dan'sa likitoci yashiga kira saikace Wanda yarasa kafafu inda yakira commissioner of police tareda lauyoyi manya guda biyu a cewarsa suzo akwai katon tashin hankali a gidansa yanaso yayi shari'a dawasu daga yau har'igiya tayi rara, 'batareda wani kunya ba mahuta ya gayama iyayanshi duk abunda yafaru cikin sha'gwaba nan mommy takara kulewa, 'matsiyata suba abun farinciki bane ace Dan lele kamarka yama diyarsu ciki ita mijin nata ai abun yayi murna ne jininka na Rayuwa a gidanshi akan dan'karamin abunnan ne zasu nakasaka harda cire hakori saikace Wanda yaima Yammata dubu ciki muba matsiyata bane idan bamasan cikin sai a burge idan munaso kuma dandai rai daya jal sai'a dauko masu aiki suyita kulada babyn mukayima wasu banza bare namu tsiyar rashin wayewa kenan ina ranar dakikanci? wlh wlh bazan yarda ba harta iyayan yarinyar sai munyi sha'ria dasu akanka aka farama mata ciki? Koko dole kayi mata har'tayi cikin?......'Mamie mijinta fa Babba ne daga gani shima Dan babban gida ne ina ganin kawai abar case dinnan abari ta haifo mun bby na kawai dukda ban shirya Zama tsoho ba but zanyi hakan a matsayin daukar fansa inbata sunan iyayanta diyar manyan malamai cefa.....'kaci gidanku, daddy yaimasa dakuwa, kana nufin sun bugi banza kenan?

Leemah kuwa kamar mahaukaciya tadawo duk inda ta gilma sai kallonta akeyi wasu najin kyamar ta wasu na tausaya mata chan gabada unguwar sosai ta tsaya a cewarta kada AK ya biyota dakyar tasamu napep dinda ya dauketa yayinda ya kaita gidanta na Isa kaita, fitowa tayi tashiga buga gate din mai'gadin gidan ya bude saida tabashi tsoro..........haaaajjiiya.....kece kuwa? Kodai bake bace? Subhanallah hatsari kikayi abun babu kyan gani wlh, 'banasan surutu karamin munafuki sallami mai a'daidaita kakuma kulle mun gidana......'isowar su meenah neya katse mata maganar ta yayinda suka fito suna salatin ganin ta a haka cikin munafunci ransu yayi fari kar' kamar audiga, "ubanwa yayi miki haka kinga fuskarki kuwa saikace zombie, meenah tafadi tana shirin shafa fuskar leemah, kul kada ki kuskura munafukin hannunki ya sauka a jikina Algunguma butulu maciya Amana wadanda basusan mutunci da Arziki ba matsiyata....'haba dakin hutu mai yayi zafi haka yanzu dai dan Allah bani kudi mu sallami mai abun hawannan, kudinda ubanku yabani ajiya? Tafadi tareda bude idonta dayayi suntum dakyar take iya ganinsu, Kallan mai'gadin sukayi, sallame su Dan Allah sai binmu sukeyi da ido, yana shirin basu kudi leemah ta buga masa tsawa, su kakema aiki koni? Wlh muddin kabiya kudinnan kamar ka yanki takardar barin aikinka a gidannan ne, oooh hajiya kuyima Allah kuyi hakuri har mutane sunfara kallan ku, 'kuma kada kabar kowace yar'iska shigan mun gida tunda gidan bana uban mutum bane, zuciya taja meenah jin Abunda leemah kecewa, ke gidan na uban naki ne mai dattin hula?
'Dukda bana ubana bane amma da sunana aka siyeshi sannan nikeda mallakin shi Baku ba, dama ance tsintacciyar mage bata mage.....aiko
nan suka damko leemah suka hau jibgarta dama a kule suke da ita kafun kace kwabo jama'a ancika akansu layi ya kaure da tikar dambe dakyar aka kwaci leemah a hannun su wacce da ana suma hamsin tabbas da tayishi a yau, yan unguwar ne suka raba dakyar masu napep kuwa cewa sukayi sunyafe kudin domin rabonda suga damben mata Wanda ya kayatar dasu irin wannan tun yarinta, nan yan'unguwa aka shiga zaginsu meenah kassncewar ansan gidan karuwai ne gidan amma ganin manyan masu kudi sun daure musu gindi kowa yakasa magana ganin yau dama tasamu hakan yasa akai musu chaa akai ana tsine musu harda masu dukansu tareda jama mai'gadi kunne duk wacce yabari tashiga gidan saisun gona gidan da mutanan gidan sungaji da zunubin da ake cika musu unguwa dashi, kuka su meenah sukeyi inda suke roko abarsu sushiga koda wayarsu ne su dauka gasuda uban kudi a gidan Ga motoci dankara dankara, kememe aka rakasu da duka sukabar layin kaya duk'ya yage kamar mahaukata takaicin su babu mai waya bare su kira Alhazawan samarin su, kuka sukeyi tareda tsine ma leemah a cewarsu ta shafama rayuwarsu bakin fenti ina suka dosa? Suba dangin iya barena Abba a garin kaduna dama barikice takawo Alkawarin zuwa gidansu leemah sukayi domin warwarema iyayanta halinda take ciki.
'Leemah kuwa tana kwance da alamar wani suman tayi wani makwafcin sune ya tausaya mata inda shida matasa guda biyu suka dauketa zuwa asibiti cikin gaggawa aka amshe ta babu kyan gani yayinda aka gyara mata cikinta da azaba yasashi komawa gefen mahaifa amma bai zube ba, azaba iya azaba tasha inda ta gwammace dama mutuwa tayi nan wadanda suka kawota sukayi wucewarsu.




Sai'chanda yamma AK ya farka inda yayi ramuwar sallolin da ake binshi ba laifi jikin nashi yayi kyau Sannan yaga gata wurin dangi kowa jidashi yakeyi tareda kwantar masa da hankali Aisha kuwa tana gefe daya tarasa sukuni babu ko kunya AK ke kallanta tareda tarin nadamar Abubuwan dayayi mata abaya cikeda Alkawarin neman gafararta ya yarda zaiyi Rayuwa da ita a'haka ya Amince yanzu baya bukatar swt 18 kokuma budurci matarshi yake bukata da soyyar ta duk runtse saiya lallaba abarsa, 'mikewa yayi gaban daddy dasu Ramata daki yacika yayi makil inda babu kunya kai tsaye ya dosa Aisha wacce ke zaune kusada Mamie cikin mamaki yasaki kuka tareda Dora kanshi akan cinyar Aisha nan kallo yakoma kanshi ganin katon Allah na rasgar kuka A'gaban matarshi, 'Mamie na cuceta na cuce kaina hakika Aisha bazata yafemun ba shiyasa nake naiman Alfarmar neman yafitarta a gabanku daddy Dan Allah kasa baki tanajin kunyar ka na cutarda matata wlh banida abunda nakeso samada Aisha wlh Mamie kinfi kowa sanin yanda nayi rainon soyyar Aisha tun kafun inbar kasarnan da soyyar ta natashi nakuma rayu Mamie duk abunda nayi soyyar ta ce sila, Santa ne sanadi da bakin kishin ta ku rokamun matata please Mamie har'dukan Aisha inayi......rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai, bataso yayi bakinjini a idon yan'uwanta ga mahaifiyarta a wurin ga wanta garbati bawai hakan na nufin ta yafe masa bane a'a ko kadan saiyaji kwatankwacin azabar da tasha dukda ko'a haka tabarshi tasan ya gasu burinta taga wannan ranan, rananda AK zai tsuguna akan kafarsa yana kuka tareda neman gafararta, zata iya shiryawa dashi sukuma bazasu taba daina mishi kallon ba har'abada darajarshi bazata dawo a idonshi ba, kuka takeyi kamar Ranta zai fita, 'bawani uziri yaya AK bakada uziri baka sona kada kawani fake da soyya ta, Rungumeta yayi tsam a jikinsa tareda Kara fashewa da kuka.....'my Eesha bakisan sirrin dake zuciyata ba kinsan yanda nakeji duk Randa nasaki kuka kuwa........'gyaran murya Alhaji muktar yayi tareda kallansu, 'yanzu dai bare mufita mubar muku Asibitin tunda ka nuna matarka kakeso tayi jinyarka ana mana korada Hali babu ko kunya kuke rungume rungume a gabanmu harda kukan soyya, 'hajiya tashi mu wuce saiya gaya mata sirrin zuciyar tasa baza'ai rashin kunyar nan a gabana ba idan kuma zaki tsaya kallan dramar soyya toh Nina tafi saimun hadu a gida, fita Daddy yayi Ramata tabi bayanshi da garbati cikeda kunya Aisha tayi tayi AK ya saketa rantsewa yayi akan bazai saketa ba sai Mamie tabata hakuri harda rikema Mamie gefen zani inda Aisha keta kukan abun kunyar da AK kemata gaban surukai saikace yara. Mamie kuwa murmushi takeyi ganin sababbin Romeo and Juliet a gabanta.







Mrs Sadik Rumah πŸ’…πŸ»
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie.*



*Dedicated to Sister husnah*



35



Mikewa takesan yi Amma ya'hanata wai saitace ta yafe mishi inda Mamie cikeda dariya take tayashi ba Aisha hakuri dukda batasan abunda ke tsakanin suba amma ya zatayi? Ya hanata koda motsi ne cewa tayi ta hakura ganin idon Mamie gakuma kunyar yanda ya kankameta koba komai Mamie bata chanchanci musu a wurinta ba hakan yasa Mamie mikewa tareda janye mayafinta yayinda taimusu fada sama sama wucewa tayi sanin daddy na jiranta a waje inda Aisha tafito Rakata nan Mamie ta dinga janta a jiki tareda nuna mata akan takula da Mijinta wannan wata sabuwar damace Allah yabata idan laifi yaimata duk mace mai aji basaita gayama mijinta yamata laifiba zai gane Laifin Sa cikin hikima da dabara ake komai a'haka sukayi sallama inda tabi daddy Wanda yaketa mamakin karfin Hali da rashin kunyar AK saikace ba shine yagama ihun bayasan Aisha oooh yaran yanzu basuda kunya yaro anama gata kakasa ganewa kadan ma kagani, inji dady yafadi yana murmushi. AK kuwa sabuwar sha'gwaba yake xubama Aisha kamar yaron goye ita abunma kunya yake bata gaba daya bata sakan masa fuska inda yakicin Abinci wai itace zata bashi a baki sai shege mata yakeyi ita kuwa cikin rashin sabo sai janyewa takeyi bataso tabashi fuska harga Allah tana matukar kaunar mijinta amma bata shirya Amsar'sa a yanzu ba saiya gane kuransa tukunna nan gaba yasan darajarda takeda shi.



Commissioner of police ne zaune gaban sanata inda Yaketa bashi hakuri tareda Alkawarin daukan mataki cikin gaggawa nan sanata ya Saki bakin Aljihu saboda komai yatafi daidai zai iya yafe komai banda cima iyalinsa fuska, mahuta kuwa azaba yakesha kanshi kamar ya fashe likita ya duba lafiyarsa tareda Dora shi akan magunguna bayi yashiga yadade yana gasa jikinsa bakaramin bugu yaci a hannun AK ba nan yashafa maganin zafi duka jikin nasa inda yaci abincin da mommy ta tasashi a gaba shayi kawai yasha saboda bakin nashi dake mishi azaba magani yasha nan yaita bccin wahala.


Kai tsaye su meenah gidansu leemah sukaje inda Mama ta tarbesu hannu biyu biyu Cikeda mamakin ganin yanayin su babu Alamar mutunci kaya a yage kamar an kwato su daga bakin kura yayinda yayyan leemah maza wadanda ke Kano sunanan da iyalansu tun biki basu koma ba gida yacika gwanin ban Sha'awa Malam liman nanan shima cikin daki take shirin jansu su kimtsa jikinsu amma suka nuna bashine ya kawosu ba,nan kowa yafara tambayan lafiya kallo daya zakai musu kasan basa cikin natsuwa, izinin Zama Malam liman yabasu ba musu suka zauna aka basu ruwan sanyi sukasha saida Malam ya tursasa musu cin abinci nan sukaci kadan badan sunso hakan ba dukda suna tareda uban yinwa amma kwarjini Malam din yake musu basa iya Musa mishi, bayanin Abunda ya kawosu suka farayi tiryan tiryan inda kafun meenah tarufe bakinta taji saukan murfin kwanon'sha Wanda mama ta buga mata tana huci, ooooh bakin ciki kukema diyata ganin tayi Aure a gidan Arziki cikeda kwanciyr hankali shine saboda fitsara kuka wanke kafafunku ba kunya kukema diyata Dana dage wurin bata tarbiyya kazafi wlh mai rabani daku sai Allah, sirikanta mata ke riketa inda duk abunda ta rarumo take jifansu Meenah dashi Malam liman kuwa tunda suka fara magana baice komai ba har zuwa yanzo inda ya tsawatarma mama dakyar ta natsu tana kuka tareda Allah ya isan sharrin da akaima diyarta, kallon su meenah yayi inda yabasu umarnin su cigaba da bayani meenah kuwa duk a tsorace take baki na zuban jini cikeda azaba take shirin barin gidan inda yayyin leemah suka dakatar da ita, feenah ce takarasa bayanin tana kuka ganin tashin hankali da suka jefa kansu daga wayewar garin yau, ana hakane Motocin yan'sanda suka dinga Dira a kofar gidan saikace sansanin yaki inda batareda bata lokaci ba akayi musu sallama damai gidan wasu rikeda bindigogi cikin sanyin jiki Malam liman da yayyin leemah suka fita waje inda kai tsaye aka tasa keyar su a cewarsu saisun fitoda yar'su da sirikinsu dasuka boye sakamakon sunje gidan AK mai'gadi ya shaida musu bakowa a gidan shiyasa sukazo nan a tunanin su Malam dinne yaboye AK da leemah, Salati Malam yadinga nanatawa tareda kiran sunan Allah yayinda jiri ke dibarsa nan unguwa ta cika makil inda matasa da dattawan unguwan sukace indai suna raye bazasu bari aci mutuncin Malam ba hayayyakoma yan'sandan sukayi ganin ba sarki sai Allah haka yasa suka hakura Malam yashiga daya daga cikin motar matasan unguwan da suka shirya binsu domin ganin yanda zata kasance cikeda tashin hankali mama take inda kukan da takeyi tuni ya tsaya tama rasa abunda zatayi taji dadi a Ranta.



Rikici akayi sosai a station sunan Allah kawai Malam ke kira jin Laifin da ake zargin AK dashi wato na cirema yaron sanata Wanda Saurayin leemah ne a sakamakon yaje duba Ajiyar cikinsa dake jikinta, dariya ma maganar tabama jama'ar wurin Abu saikace wasan yara taya mace da Auranta kuma ace tanada cikin wani? inda kassncewar babu kwakwaran shaida akan abunda ake zargin suda shi hakan yasa sanata yace a sakesu kai tsaye kotu za'akai karar saiyaji dalilin da zaisa a cirema danshi hakori, isarsu gida yayi daidai da kiran wayar Mama da aketayi inda dakyar ta iya amsawa Asibitin da leemah takene suka tasata gaba akan saita bada number wani nata an kira babu yanda batayi ba sukace indai zata biya kudin Asibitin ba matsala zata iya tafiya ganin batada kosisi kuma batada Wanda zata kira yabata gashi tabar wayarta a gidan AK tun daran 1st 9yt bareta kira samarinta hakan yasa badan taso ba tabada number Mamarta nan aka kira mama aka shaida mata tazo asibi ana nemanta cikin gaggawa tazoda kudin biyan AAsibiti cikin gaggawa itada sirikanta mata biyu suka shirya zuwa Asibitin shigowarsu malam yasa aka rankaya gaba daya inda kai tsaye aka nuna musu dakinda leemah ke ciki nan cikeda tashin hankali da tarin tambayoyi mama ke kallon leemah da halittar ta tagama chanzawa duk Wanda ya Santa ada bazai iya ganeta ba wasu dayawa musawa sukayi akan ba ita bace mama kuwa kallon ta takeyi batako kyafta ido sanadiyyan bayanin da likita yaimusu akan cikinda ke jikin leemah harna Wata Uku.





*Mr's Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*

*Alhamdullah Allah ya dawo dani kamar yanda naimuku Alkawari, gobe nasoyin posting amma messages dinku da yawan kiranda nake samu dole kujini yau saboda kada a kashe mun batir din waya, lol😜 masoyana Naga sakonin fatan Alkairi da Addu'a godiya nakeyi Allah ya barmu tare.*

*Dedicated to sister Husnah*

36

Kuka leemah keyi ganin yanda mamanta ke kallon ta babu ko kyafta ido, tun tana shirin jin saukan duka har'abun yafara bata tsoro, saida mama ta dauki minti biyar tana kallon ta inda akaita 'kallon kallo a dakin sautin kukan leemah kawai ke tashi sannan ta bude bakinta dayake mata nauyi, 'menene Laifin mu a matsayin muna iyayanki? Ilimi koko gatan da muka baki? Ciki kikayi kodai mafarki nakeyi? Diyata? Ni? Jinita dayin cikin Shege......Dan Allah mama kiyi hakuri kaddara ce,.....kaddara? Wace irin kaddara ce wannan data sauko tsakiyar gidan malamai? Durkushewa tayi kasa tareda ware duka muryarta tana kuka tana bugun kirjinta tareda Rokan Allah ya dauki Ranta akan ganin bakin ranan nan diyar cikinta hafiza wacce suka ginata akan ilimi da tarbiyya ita keda cikin Wata Uku ko sati daya batayi ba dayin Aure, kuka mama keyi inda Malam liman ke manne jikin bango sai kallon matar tasa yakeyi da diyarsa kamar TV babban dansa ne da jama'ar da sukazo tare ke shirin tabashi da niyyan lallashi yayinda ya dakatar dasu da hannun da Alamar su barshi kawai duk Wanda ke wurin saiya tausayama Malam da hawaye daya kebin daya a fuskarsa karona farko a tarihin rayuwar malamin da suka ganshi a yanayin nan wurin Mama yakarasa tareda tsugunnawa ya Tallabota jikinsa yayinda suka Mike domin shirin barin dakin suna gafda fita akaga idon mama ya kafe sama kumfa na fita ta bakinta jikinta na rawa kamar an jona mata wutan lantarki wani ihu leemah tasaka yayinda ta nufi wurin Maman tana kuka tana girgiza ta tuni likitoci suka dauketa da gaggawa inda babban wansu ya rufe leemah da duka tako'ina yana kuka harda majina yana mata Allah ya isa, kallon su Malam liman keyi yana durkushe kafun a Ankara shima ya zube bakinshi dauke da salati nan asibiti aka rikice da surutai yaran Malam liman ne duka Ukun suka taruma leemah da duka ta ko'ina Alkawari sukai saisun kashe ta tunda tayi sanadiyyan kashe musu iyaye bazasu barta ba, dakyar aka kwata leemah a hannun su wacce ko motsi batayi jini sai ambaliya yakeyi ta kasanta Asibiti ya cika makil kowa na ganin abun Al'ajabi kassncewar Malam liman sananne hakan yasa harda yan'jaridu da TV stations anata kokawan daukan labarai, cikin hanzari aka karayin gaba da leemah inda saida tarasa hakora Uku biyu a saman baki daya a kasa ta gefe duk yanda akaso ankasa daidaita numfashnta inda ake shirin sakata a coma.

AK kuwa gaba daya chanzawa yayi yayinda abun yafara ba Aisha tsoro ganin dama AK ya iya magana haka, kwana daya yayi a Asibitin dakyar Wanda daran jiya yadamu Aisha da roko da magiya akan tayafe mishi ganin duk abunda yake mata bai hanata jinyar shiba dukda babu yanda baiyi da ita akan ta kwanta akan gado ba amma kememe taki inda ta raya daran nata wurin Rokan Allah akan ya daidaita rayuwarta ko'itama zata samu jin dadi tun AK na kallonta Yayinda take burge shi har bcci yayi awon gaba dashi, washe gari Dagewa yayi akan bazaici abinci ba wai hannun shina ciwo a cewarsa mahuta ya bugan masa hannu sosai yanama tunanin har'yayi targade hannun yayi tsami inda Aisha baki bude take mamakin yanda Yaya AK ya kware a karya idan bata mance ba baima ba mahuta damar dukansa ba amma ji yanda yake gilma karya babu ko kunya, kiri kiri yakicin Abinci dukda yanajin yinwa a cewarsa indai Eesha bata bashi a baki ba tohfa saidai ya mutu da yinwa ko jiyama haka yayi inda madara kawai yasha Aisha kuwa ta murzama idonta toka dukda Tausayin shida takeji bataso yasamu weakness dinta, ana cikin haka ne kaninshi Abdulhakeem ya shigo inda AK yahade rai tareda kunkuni, "wai nayau ma kawai baza'a bar mutum ya sake da iyalinsa ba? Mtseww, Zama Hakeem yayi tareda murmushi, Daddy ne yace inzo in kwana dakai a Asibiti Anty ta koma gida itama ta huta.......ka kwana dawa? Badai niba? Wace Antyn? Badai my Eesha ba? Yafadi fuska a hade kamar zai mangare Hakeem, Allah ya kyauta in kwana da katon kato a daki daya bayan inada matata wacce zata kula dani, my Eesha ko bakyaso ki samu ladan jinyar mijinki ne? Ya fadi murmushi akan fuskarsa, mikewa Aisha tayi yayinda tajawo hijab dinta tareda shirin tafiya dukda tanaso ta kasance da Mijinta, kallon Hakeem tayi, 'yauwa ka bashi Abinci a baki yace bazai iya Amfani da hannunsa ba Nina tafi saida safe, 'wait Wait Hakeem ya furta cikeda dariya yana tafa hannu tareda nuna AK da yatsa, Badai Bros kike nufi zanba abinci a baki ba tsofai tsofai dashi? Nooooo it can't be possible kuna wasa ne wlh bazanba wani kato abinci a baki ba look ki ciyarda mijinki, 'nine katon? AK ya Tambaya sounding so serious fuska a harde, " am sorry bro but u and ur wife are very funny, 'Nina tafi Aisha ta furta tana shirin bude kofa inda AK yayi wani mugun tsalle daya tareda damko ta saikace bashi ke jinya ba, rungume ta yayi sosai da hannuwa duka biyu ta baya har'saida tasaki yar'kara sai kokarin kwace jikinta takeyi ina yaki barinta ihu tafarayi kasa kasa tana bubbuga kafarta cikin shagwaba, Kallon Hakeem yayi Wanda yasaki baki da hanci yana kallo da mamakin salon yayan nashi, toh magulmata sai abamu wuri koh jeka waje ka nemo mun lemun bawo mai zaki, 'Allah ya Baku hakuri ni ina zan iya kallon abun kunyar nan? Dama fita zanyi ko'bakace ba yafadi yayinda ya Mike, but Bros wannan uban lemun fa? Yafadi tareda nuna tarin lemun zakin dake jibge a gefe daya, 'look Malam basu nakeso ba kana bata mana lokaci, ko kunya baiji ba ya juyo da Aisha tana fuskantar Sa

Please Login or Register in order to submit comment