Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

danko yakeyi gashi yayi kauri, saida tabari yasha iska sannan ta tace inda ta dauko Karamar robar ruwan zamzam ta bude tareda juyewa a ciki, fridge shima ta saka, Yar'shilan kazarta ta dauko shima farfesun hadin ridi da nonan rakumi tayi inda tana gamawa ta juye a plate suka koma parlor abunda ta yini ci kenan yinin ranan hmmmm kafun yamma kuwa🤪baa magana abun sai Wanda yagani🙈har tsoran yanda ta dinga naso takeyi inda bilki taimata hadin dilka taita gurje mata ilahirin jikinta, gashin kanta ma baa barshi a baya ba, yini sukayi cur suna Abu daya inda Aisha kejin kanta babu abunda wata amaryar zata nuna mata a'yau sai wurin karfe shida ta shiga wanka yayinda ruwan wankan nata yasha hade haden hadaddun turare masu sirrin kamshi harda hadin ruwan lalle a ciki, sabulun kanshi hadi na musamman yasha lokaci ta dauka sosai inda ta dinga durza fatarta kamar zata chanza brush kuwa saida takusa kararda macline din bayin, oooh su Aisha abun nema yasamu🤣 tana gama wankan bilki ta miko mata kaskon turaran tsugunne wanda magic chacole ne ta kunna kasancewar babu garwashi a gidan botikin fenti tasaka kaskon a ciki inda bilki ta zuba mata garin turaren tsugune na mai'duguri Mai matukar kamshi zama tayi akan bokitin inda akasa bargo aka rufe ta dumi na ratsa duk wani lungu na jikinta tanayi tanashan hadin tsumin datayi saida takusa minti Ashirin akai sannan ta Mike inda bilki tagama turara mata wasu hadaddun fitinannun kananan kaya tareda rigar baccin dazatasa anjima harta pantis dinda zatasa saida aka turara mata da kumasa shi kanshi pant din aka diga mishi turaran miski Mai matukar kamshi nanta zauna ta tsara Kwalliya inda kowani lungu na jikinta da kalar turaran da aka shafa mishi, bilk kuwa tana ihu harta hango yanda Ak zaiyi kukan Agwagwa🦆 Sai zuzuta Kyau da Aisha tayi take, sanye takeda Purple slik short gown Mara hannu Mai budadden kirji kadan ya saukan mata kugu kyawawan cinyoyinta sai kyalli sukeyi gashin nan yasha gyara shima an kamashi da karamin ribom Mai kyau ya sauka ta baya lips dinnan sai kyalli yakeyi ba janbaki tasa ba man baki tasa Mai matukar kyau dadan ratsin pink pink a ciki, hmmmmm fadin haduwar da Eeshar Ak tayi baa magana, sai wuraran karfe takwas saura na dare Ak ya shigo kasancewar Daddy yasashi wani aiki shiyasa bai shigo da wuri ba Wanda dama hakan su Aisha sukeso yanda zasu shirya a hankali, tun daga bakin gate yakejin wani masifar kamshi na tashi a cikin gidan nashi hakan yasa sauri sauri yakarasa cikin gidan idan yana bude kofa Aisha tafito daga daki cikin takunta na kasaita sai juya jikinta take a natse kugun nan kam hmmm baa magana, ledar dake rike a hannun shiya sake Wanda takeaway ne yaimusu da gasssar kaza, da hanzari ya rungume Matar tashi yana ihu, wowww African Beauty I can't believe this Angle is my wife, dagata yayi yana jujjuya parlon da ita batareda bata lokaci ba yahada bakinsu tare shan bakinta yakeyi cikin kwarewa da zalama kamshinta dukya rikitashi yagama fita hayyacin shi, bilki ceta fito ganinsu a haka kunya taji inda take musu sallama Aisha ce take kokarin kwatar jikinta ganin zuwan bilkin gogan kuwa baimasan duniyar dayake ciki ba sai kankame matarsa yake karayi, 'Dakyar ta kwata kanta a jikinshi, Hubby bilki nanan fa please ka tsaya, oooh Eeasha wacece bilki kuma? Yafadi with his red eyes sai lumshesu yakeyi, "Ni bilki zan wuce saida safe sabon Ango, " kallonta AK yayi shi wlh yama manta wata bilki, oooh dama baki tafi ba Ashe, toh saida safe mai'gadi zai kaiki gida mun gide....."aa Mai gadi kuma? Tafadi tana dariyar yanda ya rikice, "ooh Ina nufin saida safe yafadi tareda Jan matarshi zasu shiga daki Aisha na turjewa duk kunyar kanwarta takeji, " meye haka Eeasha mijin ki yadawo ko ruwa kya bani, "but Yaya kabari muyi sallama da ita mana, look banasan musu tayi miki uziri mana yinwa nakeji muje ki zuba mun abinci, but Kabar ledar a parlor ai....datse kofar bedroom dinshi yayi batareda bata lokaci ba ya cigaba da abunda yakeyi Eeasha kinyi masifar kyau am going insane kamshinki zai kasheni, abunda yake furtawa kenan biki kuwa tafa hannu takeyi kunya dukta isheta tama kasa magana tsallake ledar da Ak ya zubar tayi inda taja musu kofar parlon su tareda Alkawarin bazata kara kaiwa dare a gidan yayar tataba daga yau bare taga abun kunya taga alamar Ak baisan wata kunya ba.


Dakyar Ak ya sararama Aisha yayinda ta zuba mishi abinci yadan tsakura sai hadin dabinon data wuni sha ta zuba masa nan yaita zuba santi, a'daddafe dakyar yabari karfe goma yayi inda ya watsa ruwa sama sama cikin kayan Bcci milk color riga da wando Aisha kuwa tsoro yagama rufeta ganin haukan da Ak ketayi tun ba'aje ko'inaba yagama rikicewa ita kanta a takure take tana bukatar mijinta hakan yasa takasa ko motsin kirki inda ya shigo batareda bata lokaci ba ya rage hasken wutan dakin yayinda ya kunna na Bcci, 'Hubby tun yanzu zamu kwanta? 11 fa muke Bcci, 'karki damu yau dawuri zamu kwanta Bcci nakeji toh Bari inje in chanza kaya, tafadi jiki na rawa harta kai bakin kofa tana shirin budewa, 'my Eeasha basaikin wani chanza kaya ba please kizo, 'waigowa tayi cikeda fargaba, yanzu zan dawo Ina zuwa tana fita ko tsakiyar parlon bata kaiba taji anyi sama da ita, Daukarta yayi batareda Yaji nauyin taba, "naga saiwani jamin aji kikeyi kinaso ki manna mun hauka, yafadi tareda direta a'tsakiyar Gado inda yaimata rumfa da faffadar kirjin shi ya shiga aika mata da zafafan sakonnin da suka fara kwance mata da dukwani tunaninta a duniyarta dukansu bakaramin fita hayyacinsu sukayi ba Ak kuwa tun ba'aje ko'ina ba tunda yafara sarrafa jikin Aisha ya dinga ihu kadan kadan kusan awa daya suna buga hot romance a lokacin da zaka tambayesu sunayan su tabbas bazasu Iya tunawa ba, ganin abun bamai karewa bane yasa na lallaba tareda barin musu dakin da sai nishi sukeyi duk kunya ma tagama cikani wlh🙈, parlor nakoma na zuba tagumi inaso Inga abunda zai turema buzu nadi batareda bata lokaci ba naji Ak na salati Wanda saida ya furgitani, "Innaa...lillahi, ya salam, Wyyooo Mamie na, Aisha Aiiiiishaaa meye haka?
Meye haka Aisha? " ita kuwa kuka kawai takeyi harda magiya tun muryarta na fita cikin tashin hankali harna daina jinta...........
"Zaki kasheni Aisha,
Ihu yakeyi sai kiran sunan Aisha yakeyi kamar Wanda zaa zarema rai😕nifa sunsani a tsaka Mai wuya kamarya zata kashe shi? Damai zata kashe shi?🙁










*Mr's Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*



*Written by Anty Mamie*

*Kuyi hakuri kwana biyu kun jini shiru, wlh Hidima namun yawa da weekend ne shiyasa but karku damu askin yazo gaban goshi insha Allah.*



*Dedicated to sister Husna*



41


Ba karamin rikicewa Ak yayi ba inda ya dinga kiran sunan Allah sai misalin dayan dare yasamu natsuwa inda ya kwanta gefe yana maida numfashin gajiya yama rasa abunyi yarasa tunanin dazaiyi cikin kankanin lokaci zazzabi Mai zafin gaske ya rufe shi inda yajawo Aisha jikinshi A ranshi kuwa zuba mata Addu'a kawai yakeyi yama rasa bakin magana, rufesu yayi da bargo yanda yakejin kanshi ko wutan dakin bazai Iya kunnawa ba saboda Mazarin da jikinshi keyi kafun lokaci kadan Bcci yayi gaba dashi sai munshari yake bugawa yayinda ya kankame jikin Aisha yana sauke ajiyar zuci tuni Bcci yayi gaba dashi kiran sallar Asuban farko yatashi sakamakon nishin da Aisha ke fitarwa na wahala Wanda yakeji sama sama a kunnan shi da hanzari ya Mike tareda kunna wutan dakin da gudu ya karasa wurinta ya shiga jijjigata, "na shiga uku my Eeasha subhanallah, rungumeta yayi kam jikinsa dake rawa da zafi yana kuka kamar karamin yaro sai hakuri yake bata, "bana cikin natsuwata har yanzu nakasa tuno komai kaina ya kulle am a very bad parson Aisha ki yafema mijinki na cuceki, kwance take a jikinshi sai lumshe idon wahala takeyi tana jin maganar nashi sama sama, " I can't believe u r still a vargin wowww my Eeasha a vargin that's my dreams coming true yah rabbi yah Allah Kaine Mai maida Impossible To be possible am confused, sumbatu ya cigaba dayi yana kuka daka ganshi baya cikin natsuwar sa inda lokaci daya ya jawo wayarsa dake bedside dukda haka kan Aisha na rungume a jikinshi sai faman lailaya mata yakeyi yana hawaye likitan shi yakira cikin daran inda wayar taita Kara tana katsewa har kusan sau biyar harya gama cire ran zaa amsa wayar yafara tunanin kodai Mamie zai kira tazo ta dawo mishi da Eeashar sa daidai? Muryar doc dince ta katse shi cikin magagin Bcci, "Doc wlh she is a vargin and I hurt her soo badly ooh how can I be soo stupid nayi zargin innocent jewel Dina, oooh Allah na shiga uku please ya zanyi idonta a lumshe yake tun dazu tana nishi help me please my wife is in pain and becox of my stupidity why? How comes? She is a vargin wlh wlh Nina fara saninta I can't believe what am seeing......." Carm down Sir please ka kwantar da hankalinka sir kaimun bayani yanda zan gane and who is a vargin? Tsawa Ak ya daka mishi kamar zai fasa wayar, "Who Else if not my wife u stupid Moran malam just tell me abunda zanyi banasan gulma, " sorry sir, taimaka mata zakayi ka gasa mata jikinta sannan ka kimtsa ta kakawo mana ita asibiti zanma likitan mata bayani zaai mata duk abunda yadace, "shikenan abunda zanyi? Ya tambaya murya na rawa
" yes sir shikenan kafun inzo anjima....dif ya katse wayar shi tareda jifa da ita nan ya Mike cikin kwarin jiki ya shiga yin duk abunda likitan yasashi, yanayi dukkansu suna kwallar azaba Aisha nayin hawayan radadin zafin datake ji shikuma yanayin hawayan radadin zafin dayasata tareda Dana sanin duk abunda yaimata a baya yafi kowa sanin matarshi shiya fara budeta koda cikin hauka yake yasan ayau shiya amshe budurcin Aisha, nan yaita rasgar kuka harda majina yana rokonta gafara yana mata wanka itako Aisha idonta a lumshe yake ta kanta takeyi, Cikin kankanin lokaci ya kaita asibiti inda batareda wani bayani ba aka Amshe ta sanin zuwan nasu kai tsaye Aka fara bata kulawar daya dace inda Ak ya karata yanda yaje mata batareda sanin budurwa bace yadauka inrinsu leemah ne zuruf zai shige🤣, sai safa da marwa yakeyi hannu duka biyu akai dagashi sai dogon wando da farar singlate duk Wanda yazo wucewa saiya kalle shi ganin yanda yake rasgar kuka kamar tsohon bayairabe inda wani likita yazo gilmawa harya wuce yadawo tareda dafa kafadar Ak ganin yanda babban saurayi ke hawaye, sannu bawan Allah Dan Allah ka kwantar da hankalinka irin wannan kuka saikace ba namiji ba? Da alama madam na labour ne Addu'a zakai mata ba kuka ba Allah ya raba lafiya, "kallon mutumin yakeyi ji yakeyi kamar ya watsa masa mari kozai huce takaici, shi kanshi likitan ganin irin kallon da Ak yake masa shiya sa yawuce da sauri kada ya
huce a kanshi.
Aisha kuwa bakaramin wahala Tasha ba inda likitan dake dubata tayi masifa da fada sai kumfar baki takeyi bakaramin haushin Ak takeji ba wannan ai rashin hankali ne ko makaho ne bai kamata yasa miki karfi haka ba ko kinmai gardama ne? Ta tambayi Aishar da batada niyyar bata amsa, dakin hutu aka kaita tareda Kara mata ledan ruwa da alluran Bcci.

Kafun gari yawaye harya kirasu Mamie dasu bilki yan'uwa yaita kira Eeashar sana Asibiti priceless Jewel batada lafiya batareda tunanin dalilin dazai gaya musu ba, aikuwa nansu Mamie da brother Hakeem sukazo harda bilki wacce Hakeem yacema Mamie su biya su dauko ta Ramata kuwa cewa tayi basai taxo ba Adduar ta ya wadatar batareda bata lokaci ba Mamie ta tambayi abunda yasamu Aishar Ak kuwa da gaskiar shi yake shirin yima Mamie dalla dalla inda bilki ta farga tayi saurin katse shi,........" Wlh maleria ne yasata gaba jiya danaxo haka na barta jikin sai a hankali Ashe jikin nata yayi tsanani bayan tafiyata, "Adduar samun sauki sukai mata inda bilkin tayi hakan ne saboda surutun da mamakin da zaai shekara uku da Aure sai a lokacin ma'auratan suka San junansu it will look somehow, "Ammah bro duk ciwon sister neya rikitaka kazo asibiti babu ko riga? Sai a lokacin Ak ya kalla jikinshi inda kunya tagama kamashi yiyinda Mamie ta kalleshi tana girgiza kanta, " Allah ya shirya ka Ak dannaga alama kana gafda fara hauka, wucewa dakin da Aisha ke bccin hutu tayi bilki kuwa sanin Abunda yafaru da yayar tata bakaramin tausaya mata tayi ba inda suka koma gefe daya itada hakeem sai fira sukeyi kallo daya zakai musu ka faminci zallar soyyah a idonsu, "hmmmm wata sabuwa da Alama jinin buzaye yagama mallake gidan Alhaji Muktar👯🏼‍♀

Mota Ak yakoma inda yakira PA dinshi tareda shaida masa yataho masa da sabuwar riga yana asibiti yazo kuma zai Aikeshi wani wuri.


Takarda ya zaro da biro a jikin motarshi inda yafara rubutu kamar haka.

*Ni Abdulkareem Muktar na saki Munafuka makira muguwa Shegiya macucuya Kuma Azzaluma Halima Mai fuska biyu, Saki uku nida ita har abada Kuma Allah ya isa tagama dani Bankuma yafe ba.*

Nade takardar yayi inda abubuwa suka dinga dawo masa dai'dai cikin lokaci kadan naga ya yaga takaddar tunowa dayayi da darajar malam liman a wurinsa nagartaccen dattijo Wanda baida kwadayin duniya da abunda ke cikinta idan banda haka saiyayi sha'ria da halima saboda tagama masa rami a rayuwa Amma ya dauki hakan a matsayin jarabawa tareda hakkin Aisha,
Wata takaddar ya dauko inda yakara rubutu kamar haka.

*N Abdulkariem na datse dukkan igiyar Auren dake tsakanina da halima na saketa saki uku a dalilin cin amanar Aurena datayi.*


Mikama PA dinshi yayi tareda bashi izinin kaiwa gidansu leemah inda saida Aisha tayi kusan sati daya a asibiti gatan duniyar nan ta ganshi a wurin Ak makale mata soyyah kuwa hmmm kamar ya kashe kanshi bakaramin soyyah suke sha'ba hakuri kuwa ta sha'shi inda yaita mamakin yanda yasameta a vargin nanta warware masa komai Addua sukaita ma ya'u inda ya kudiri aniyar duk Wanda yakara jin yakira matarshi da makamancin sunan Ustaziya ko Yar'duniya kowaye kuwa saiyayi sha'ria dashi kuma zai fito ya nunama duniya shikadai ne namijin dayasan ta sai inda karfin shi yakare akan hakan, koda aka sallami Aisha Kyautar 1st 9yt dinta na musamman na jiranta inda yasai musu dankareriyar motoci guda biyu hadaddu shida ita na Aisha fara tas a cewarsa saboda rayuwar shida ta haska shiyasa yaimata kyautar farin mota, tashi kuma milk color inda ya biya musu kujerar hajji itada family ta gaba daya su garbati Mai rake za'a zama Alhaji a cewarsa it is the little he can do ganin baida wata hanyar faranta mata zai cigaba da wanke mata bakincikin daya dasa mata da karfin shi dakuma dukiyar shi koda zai zauna baida ko'sisi a duniya zai kararda komai akan Priceless Jewel dinshi tattali na musamman yake bata kamar zai maidata cikin shi.

Halima saida takusan kwasan wata daya sannan aka sallameta tayi baki tarame ta kode saikace Mai ciwon kanja'mau inda tun kafun akai ko'ina tayi nadama matuka iyayanta gaba daya basa bin ta kanta inda mamarta bata amsa koda gaisuwar ta ko kallon inda take batayi malam liman kuwa kullum cikin wa'azi yake mata a cewarsa hannunka bazai rube ba ka yanke dukda abun namasa ciwo Amma bazai bar sanrai yasa yayi aikin jahilci ba, gaba daya aikin gidan ita keyi babu yanda malam bai lallashi mama akan ta dinga sassauta mata ba hakan yasa Maman ta tattara halima da malam din dukansu ta watsar a cewarta da tanada wurin zuwa babu abunda zaisa ta zauna gida daya da halima taga Alamar malam dinne ke daure mata gindi Inda kullum halima na kunshe a daki kamar daddawa duniya tamata zafi danma Allah ya taimake ta cikin baya bata wahala ko kofar gida tayi Alkawarin bata Kara fita koda malam yabata takardar sakinda Ak ya aiko mata ranan tawuni kuka kamar ranta zai fita ganin yanda tacuci kanta da rayuwarta Allah yamata gata babu abunda tarasa San zuciya yasa tama Allah butulci Ina ranar bariki? Duk ribar da mutum zai samu a bariki na lokaci kadan ne yayinda zai karasa sauran Rayuwarsa cikeda nadama wacce batada amfani tanaji tana gani tayi asarar nagartaccen miji har abada, mahuta kuwa bishasha kawai yake zubawa inda neman mantan shiya ninku saikace Wanda akaima baki kowace kareda doki binta yakeyi abun yazama mishi jaraba saidai muce Allah ya kyauta yakuma hanemu da aikin danasani Mara amfani.

Aisha fa tama rasa bakin godiya saidai hawayen farinciki ganin yanda mijinta ke rurutata takara godema Allah daya tsare mata budurcin ta tabbas duk macen datayi asarar budurcinta a titi wlh wlh tayi asarar babban farinciki da kwanciyar hankali a gidan auranta bawata daraja da zatayi matukar Mijin yagane duk sanda yake miki babu inda auranku zekai koma Auran yayi tasiri wlh sai an samu zargi tareda wasi wasi a zaman.

"Misalin karfe goma na dare Ana sati daya daidai da daran 1st 9yt dinsu bayan tagama kimtsawa tadau wanka sai kamshi takeyi kamar koda yaushe wayarta ce tayi Kara *King of hrt* shine sunanda yafito baro baro akan fuskar wayar tata batareda bata lokaci ba ta amsa tana faman zuba mishi kirari tana wasa Mijin nata kamar yanda ta saba, sanar mata yayi ta sameshi dakin shi Wanda anan ne akayi sha'galin😜 batareda bata lokaci ba dama a shirye take tunda yamma ta hada hadaddan hadi na musamman, danyan zogale ta gyara da madarar pick na ruwa ta markada tareda zuba masa Zuma Mai kyau akai shita wuni sha dukda baida dadi a baki Amma biyan bukata yafi dogon buri, Alkawari tayi koda duk kwanan duniya Ak zai dinga karata Ana dinketa Bazata taba guje ma shinfidar shiba, duk halinda take ciki Alkawari tayi bazata taba hanashi kanta ba zata juri komai saboda king of hrt, she is Ever Ready, yes a shirye take da faranta mishi koda hakan na nufin Ajalin ta, tana bude kofar dakin sanye da hadaddun kayan Bcci red cikin takun kasaita yayinda take mamakin abunda ya boye Mijin nata tun dazu bai makale mataba kamar yanda yasaba, batasan sanda tasaki ihun dadi ba tsalle tayi tareda rungume mijin nata tarasa awace duniya zata sakashi ganin yanda.............😜
Saimun hadu a next page Wanda zai zama second to the last insha Allah👯🏼‍♀










*Mr's Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*



*Written by Anty Mamie.*



*Dedicated to Sister Husna*


42



Aka kawata dakin da rose flowers masu ban sha'awa na masoya saman gadon yasha red bedsheet masu matukar kyau an zuba flowers jajaye gwanin ban sha'awa yayinda aka watsa multicolors balam balam Mai hrt shape ta'koina har zuwa kasan dakin Wanda ke dauke da karamin table dauke da madaidaicin Hadaddan red cake da rubutun, *"Happy One week Anvasary"* tareda hotonsu a jiki Wanda ya matsa mata suka dauka sanda take jinya a asibiti dukda babu Kwalliya fuskarta hoton yayi kyau sosai kanta nakan kafadar shi yayinda shikuma yake kallon fuskarta daya tallabo da dayan hannun sa gefe daya kuma Kwalbar Hadaddan champagne ne tareda red glass cups dogaye guda biyu, wani cool music ke tashi a hankali cikin wakan sanannan mawakin nan black American "Akon a wakarshi Mai taken " Am so lonely " cikin sauti Mai natsuwa da ratsa jiki "bin dakin tayi da kallo inda lokaci daya ya sunkuce ta tareda direta tsakiyar gadon dayasha gyara sai dariya sukeyi yana mata chakulkuli saida suka dauki minti biyar sannan ya dakata yayinda ta kalleshi cikeda mamaki, "king of hrt wai yaushe kayi duk wadannan abun? And na menene? Bakinsu ya hada wuri daya yana bata wani irin sako Mai wuyar fassara saida suka dawo hankalin su sannan ya rike hannun ta har zuwa wurin cake din tareda mika mata yar'karamar wuka red, " bismillah nakosa inci cake dinnan dear feed ur hubby please, "but cake din mainene? Na Anvasary din sati daya da first 9yt dinmu ne idan zaki tuna tundaga ranan bamu Kara kwana a dakin nan ba saidai inbiki dakinki saboda jinyar da kikeyi, " tugunnawa yayi a gabanta kamar karamin yaro sanye yakeda wando 3quater fari tareda red armless riga Mai daukeda rubutun, *Give me Another special place in ur hrt* a gaban rigar Wanda rubutun ya kasance fari, "shiyasa a karona biyu nakara gayyatarki dakina Wanda banaso ki dinga tunowa da komai sai ire iren abubuwannan just our happy moments, Mr's Abdulkareem congratulations because am All urs sai yanda kikai dani babu boka ba malam kin gama mallakeni yanzu dai ki ciyarda mijinki, yafadi yana chuno mata baki, Cikin wata sabuwar duniyar farinciki ta Lula yayinda ta yanka cake din Wanda ya kasance chocolate and red velvet cake sai hadiye miyau takeyi tareda gutsoro madaidaici tana shirin dorawa akan karamin Tea plate ta hango wani Jan Abu namata kyalli tacikin cake din, hannu tasa tareda turawa tsakiyar cake din dauko Hadaddan karamin case ne Mai kamada gidan dan'kunne tana budewa tayi ido biyu da kyawawan zobuna guda biyu sai kyalli sukeyi tareda daukar ido na mace Dana miji cikeda mamaki ta maida kallon ta ga AK Wanda ya kashe mata ido daya yana zuba murmushi, Rike hannunta na dama yayi tareda Amsar zoben ya zaro na macen Dan siriri Mara hayaniya saika saka ido sosai a zoben zakaga Harafin A&A Wanda aka rubuta da ruwan gold, yatsar hannunta na biyu ya rike inda ya kalleta with a serious look, " My Eeasha I know I made a mistake a baya banyi Alkawarin bazan Kara bata miki raiba Amma nayi miki Alkawarin hawayan idonki bazai Kara zuba ba a dalilina namiki Alkawarin duk hawayan dazai fito idonki a gidana insha Allah zanyi iyakan kokarina Inga ya kasance na farinciki sannan zanyi iyakan kokarina wurin faranta miki da dukkan Abunda nake dashi, kasancewar bikin mu baayi wani shagalin da zamu dinga tunowa dashi ba kasancewar abubuwan da suka faru ada cikin rashin Sani shiyasa na hada miki yar'karamar dinner nidake a dakinmu Mai tarin tarihi da farinciki inaso ki manta da abunda yafaru a baya ki rike ranar yau a zuciyarki wacce Ranar yaune zai zama Ranar da zamu dinga Celebration akai, My wife, please kikara bani dama a karona biyu insake taka rawa a rayuwar ki, zura mata zoben yayi a tsintsiyar hannun ta Wanda ba karamin kyau yayi mata ba yayinda ya rike hannun tareda sumbatar shi, a daran masoyan sun Kara lulawa sabuwar duniyar ma'aurata Mai tarin natuwa tareda tsayawa a'rai saidai muce Asuba tagari Eeashar AK💃🏽.



*Bayan wata Shida.*


Leemah ce keta mutsu mutsu gwanin ban tausayi dukta bushe ta jeme tayi baki tarame ga uban ciki, tun tana daurewa tana nishi da kuka kasa kasa harta galabaita ita kadai a daki da Alama nakuda takeyi bakaramin wahala tasha ba taci kuka harta gode Allah yayinda mama batasan Abunda ke faruwa ba kasancewar bata shiga harkarta gaba daya, Addua takeyi Allah ya dauki ranta kozata huta da azabar da take ciki inda takasa jurewa ta kwallama Maman kira cikin kukan azaba tana rokon yafiyar iyayan nata tareda nadamar abunda ta aikata, cikin hanzari mamar ta karasa dakin saida ta tausayama halinda taga diyar tata bakaramin azaba take sha'ba, wurin malam ta garzaya tareda amso rubutun nakuda Wanda yadade a ajiye, dakyar tasamu halima yasha kadan saboda tanasha tana dawoda rubutun ne ganin anata Abu daya har yanzu babu Alamar haihuwa hakan yasa malam ya dauko shatan keke napep aka sakata a ciki batasan inda kanta yakeba Allah ya taimaka unguwar babu mutane a lokacin babu Wanda ya farga da abunda ke faruwa, cikin ikon Allah Ana gafda isa asibitin halima tasaki wani uban ihu Wanda harta Mai napep din saida ya tsorata batareda bata lokaci ba Ashe yaron ne yayi mugun karata inda jariri ya sumbulo

Please Login or Register in order to submit comment