Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muni kaman kacin wanda yasha zobo. Maman Abd Shakur 😘



mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 67 TO 69KAINE SIRRI NA 77to87 →
KAINE SIRRI NA 70 to 76
Posted on July 14, 2016 by mamanshakur
​[7/12, 18:21] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
70

Ganin jikin sojan damai gadin yay sanyi jin maganar datayi yasa ta mike tsaye tana kakkabe bayan zaninta” zaku nunamin dakin jikata ko saina sa Barraq ya koreku inya dawo?” Da hannu security ya nuna mata part din ta wuce abinta.
Bude part din keda wuya Duduwa ta kwalalo ido “aljannar duniya,wanan daula wlh dole kifita daga ciki Rufaida” katuwar tv bangon dake aiki ta kurama ido, ganin mutane kaman zasu fito. kalle kalle tafara da tabe tabe, tunawa ana jiranta yasa ta fara waige waige neman kofar uwar daka. tafiya tafara takaraso asalin tafkeken falon ganin kaman mutum a chukuikuye cikin bargo akan kujera yasa ta yaye bargon ahankali. ganin kamar fuskar Rufaida kaman kuma ba itaba yasa ta tottafa miyau a hanunta ta malka a idanunta ta dirza kafin ta kara kallon fuskar Rufaida,tabbas itace amma ya akayi mayyar nan tai kyau haka??tai kiba??ahankali ta kama hanunta ta duba tafin hanunta, salati ta buga “Hasbunallahu! yanzu yarnan ciki gareki,cikin shege Rufaida?” hannuwanta ta dunkule guda biyu iya karfinta ta sakinma Rufaida dake bacci nushi aciki tus! Rufaida dake bacci tasaki ihun wahala ahh! Wayyo cikina Mummy” ta tashi zaune ta rike cikinta tana kada kafa saboda azaba. Kaman a mafarki taji muryar Duduwa tace”dan kan ubanki tashi ki tattara kayanki mutafi kauye, tunda zaman karuwan ci kike, hakanan dan kija Allah yajefani a jahannama kinzo kina zama da namiji har ciki yamiki” Rufaida da idanunta ke juyawa saboda azaba ta kokarta takai dubanta ga kafan Duduwa ahaka har takai dubanta ga fuskarta batasan lokacin data zube akasa jikinta na rawa tace”ina kwana Duduwa” Duduwa tasaki shewa” lalle Rufaida, da namiji kike zama ko?” Rufaida ta girgiza kai duk jikinta na rawa, ta fashe da kuka” wlh bada namiji nake zamaba, dan Allah Duduwa kiyakuri karki daken bazan karaba ” Duduwa tai dariya “ai idan banci ubankiba, ba sunana Duduwa diyar mai mandiri jikar mujittpa ba, sainai miki lilis sanan zaki tattara kayanki mu koma kauye ” wiwi Rufaida tafashe da kuka cikinta da maranta na wani irin juyawan azaba da ciwo. Duduwa ta cire gyalen jikinta taci dammara dashi tanabin Rufaida tana ja baya tana kuka “dan Allah kiya kuri Duduwa, dan girman Allah, wlh zan biki amma karki daken wlh banison duka plz”. Duduwa ta kifa mata mari a fuska” yimin shiru kama bakin kidena min ihu kafin arnayen chan suji su shigo” Rufaida ta rike bakin ta tana kuka sosai jijiyo yin kanta sun fito radau, saboda kuka da tsoro zaka iya ganin yanda kirjinta ke bugawa da sauri fat-fat-fat. “Waya miki ciki?” Duduwa ta tambaya a masifan ce. Rufaida ta zaro ido tana kallon Duduwa bata gane maganar datake ba Duduwa tasa kafa ta take kafar Rufaida. Rufaida ta fasa ihu ta rike baki Duduwa tace” oya yi magana waya miki ciki?” Cikin kuka Rufaida tace “wlh wlh wlh Duduwa banda ciki, kalli cikina,baiyi girma ba” hannu biyu Duduwa tasa ta ture Rufaida tafadi akan tiles tasaki karan wahala da kuka, alokacin taji abu mai dumi nabin kafanta cikin karamar murya tace “dan darajar Allah Duduwa kidena dukana, zan mutu wlh,banason duka,kiya kuri”. “oya tashi ki hado kayanki mutafi” Duduwa ta fada tanamai tura kan Rufaida. Rufaida takasa tashi. Duduwa ta daka mata tsawa “tashi nace! Da rarrafe Rufaida ta tashi Duduwa na biye da ita tahau bene tafara tafiya jin kafafunta sun rike yasa ta tsugunna tafara Jan jiki da kyar tanabin benen Duduwa na lura da jinin dakebin jikinta taji dadi bazan taba bari ki haifama bature masu kudi yaroba. a tsiyace zaki mutu shegiya yar tsuntuwa. ahaka sukakai daki Rufaida tadau akwati tafara diban duk kayan da idanunta dake juyawa sukaga tana lodawa a akwati harya cika ta rufe Duduwa tace “bazaki sauriba ko saina ballaki ki”. tafashe da kuka cikin dashasshiyar muryar ta tace “dan Allah karki daken Duduwa” ahaka suka fito tanajan jiki suka sauko kasa Duduwa tai gaba wurin kofa ta juyo taga Rufaida tsaye tana kuka ahankali Rufaida tace “Duduwa indan kirashi nafada mai? ?wlh inbaki yardaba nafasa ” maganar ta mugun batama Duduwa rai “ah lalle yarinya nikike fadama zaki kira wanda yamiki cikin shegen nan” ta kama wuyar rigar rufaida ta jijjiga ta Rufaida taji wasu abubuwa masu dumi sunabin kafarta, idanunta suka fara juyawa da kyar tace “Duduwa zan mutu, ki dena dan Allah” daga hannun da Duduwa tayi zata daki Rufaida taji an bude kofa. Maman Abd Shakur 😘

[7/12, 22:53] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
71

Barraq ya tsaya chak yana kallon jinin daya gani a stairs,da Rufaida dake hannun Duduwa tana numfashi kamar wacce taga mutuwa. Duduwa na ganin Barraq tsaf ta ganeshi, jiki na rawa ta saki Rufaida. Rufaida tai baya zata fadi da sauri Barraq yay gudu ya tareda tafado jikinshi,ya rungumeta kafin ya daura kanta akan cinyarshi yana shafa kanta, yama kasa magana saboda yanda zuciyar shi ke mugun tafarfasa, idanunshi da fuskarshi harma da kunnenshi sunyi bala’in ja,abunku da farin mutum. dago kanshi yayi ya kalli Duduwa saida dan guntun fitsari ya zubo mata saboda tsorata dashi datayi dan gani tayi idanunshi kaman jini,gabaki daya fuskarshi tai ja juyawa Duduwa tayi zata fita tana neman kofar daya shigo da ita dakin bata ankaraba taga kofunan da windunan falon sun kulle da kansu, Duduwa tajuyo a rude tace” kabude min kofa, zan fita natafi kauye, kabude min nace”. bai ce kalaba ya dauko wayarshi yakira wata number ahankali yace “I need ambulance” sanan ya katse wayan ya ijiye. kan Rufaida ya shafa zuciyar shi na mugun kuna da tafasa, ahankali ya kai hanunshi kasanta yaji har alokacin jini na zuba ,jijjiyoyin kanshi ne suka kara tsattsowa ya matse Rufaida a jikinshi,cikin fushin yake kokarin tunanin meke sata bleeding bayan yasan tana salla. “are yhu pregnant Rufaida? ?”tambayar ta fado ranshi. Tunowa da news din daya kalla jiya ana hira da wata Dr hartake fadin alamomin mace nata ciki yasa ya lula duniyar tunani. tun na farkon nan Rufaida bata kara fashin salla ba,ga zazzabin safe, ga yawan bacci, ga selecting abinci,and kirjinta were far too full kwanakin nan ahankali yace”u are pregnant with my own baby Rufaida,my child” ganin yanda take bleeding yasa yace “and matar nan ta zubar min da cikina,u killed my baby” ya kalli Duduwa” waya baki izinin tabamin matata har kika kashemin da, waye? ?” Duduwa da takarasa sakin sauran fitsarin ta rike labule gam da hannu, jikinta na rawa” yo uban wayace ka sacemin jika,ka tambayi izinina kafin ka tafi da itane? bazan taba bari ta haifi shege ba, saisa na daki cikinta da hannayena biyun nan, dan ta mutu cikin ma ya mutu” Barraq jikinshi yafara rawa ya kwantar da Rufaida akasa “kece zaki mutu yanzu ba matata ba” taku biyu ya kaishi gaban Duduwa wacce ta daga murya ta tsala ihu tana neman taimako “wayyo Allah, zai kasheni, ayi taimako zai kashe kakar matarshi” Barraq ya daga hannu zai wanketa da mari kenan yaji muryan Dad yace “Barraq! Chak ya tsayar da hannun batare daya kai fuskar Duduwa data make a labule ba, kuma bai sauke hanunba,Amma tai sauri takarasa inda Rufaida ke kwance tafashe da kuka “Wlh hukuma ce zata rabamu dake”. Dad yakarasa wurin ya kama kafadar Barraq ya matsa da karfi “dan ranka yabaci bazaisa kai abunda bai kamata ba,idan rai yabaci hankali karya gushe! maizaka daka a jikin tsohuwar nan da akalla tai clocking 80 years?wot will yhu archive?and kakar matar ka for dat matter!,Kul!Ahir gareka ya Barraq karka fara kadaga hannu wataran kace zaka daki wacce ta isa ta haifeka, koma wanda ya girmeka,ba tarbiya bace, dan haka za’ama iyayenka kaima wataran, no matter wot she did ka barta da halinta, duniya nada fadi and Allah subhanahu wata ala never sleep. Yana ganin komi”. Sakin kafadar Barraq yay Ya kalli Duduwa yace “Mama tafi abunki” Barraq ya kalli Dad afusace “wot are saying Dad?dis woman killed my unborn child Dad,my Baby!she have to pay for her crime Dad”. John! Joseph! Yakirasu dawani irin muryar zaki, suka shigo dakin da sauri ta kofar kitchen, ya nuna musu Duduwa” lock her up! Da sauri sukazo zasu kama Duduwa Dad hana”let her go” alokacin Amma tasa baki tace “akulle ta, koma wacece she must pay for her crime, ku tafi da ita ku kulle ta cus wot she did is unforgivable “. Dad baice komiba saidai taku biyu dayayi yakaishi gaban Duduwa ya mika hannu ya riketa, Duduwa data mugun rudewa bata tabajin tsoro irin nayau ba arayuwar ta, tabishi luuu ya kai ta har kofar gida sanan yaciro dubu goma ya bata yay murmushi manya yace “mungode hajiya,kome kikama Rufaida kin isane saisai, Allah kaiki lpy” Jikin Duduwa yay sanyi ta karbi kudin tajuya tana tafiya ahankali tana waigen Alh( Dad). Tare da motar ambulance Dad ya shigo, Barraq na tsaye inda Dad ya barshi zuciyar shi tai baki, ahankali Amma ke maimaita mai kalmar La ilaha illallah. Daukar Rufaida akayi akasata akan wata yar gado aka samata oxygen a hanci sanan aka gungurata aka fitar, Barraq dayaki kallon Dad saboda fushin dayake ya kalli Amma yace “Amma zanyi baki daga Lagos any minute from now,Dan Allah ki tsaya idan sun iso entertain them,if they insist zasu ganni ki kawosu hospital”. Amma tamika mishi tissue ganin hawaye nabin idonshi. Tace “take it easy Barraq komi zai dawo normal I promise” bai ce komiba yajuya yafita da sauri ya shiga motar ambulance din ya rike hanun Rufaida gam hawaye na sintiri a kumatun shi masu zafi. aka wangale gate suka fita,dad ya shiga motarshi ya bisu abaya akabar Amma kadai a gidan. Ko minti 15 ba ayi da fitar motar ambulance dinba wata hadaddiyar Benz baka har walkiya take ta shigo gidan. Magidancin Alhaji ya fito dauke da yaro tareda matarshi data zagaya ta bude baya ta ciro stroller sanan ta karbi kakkyawan yaron ta saka cikin stroller. Ta kalli mijinta tace”Ragadada maigida nakaina” yace”naam Ragadada uwar gida takaina” wlh naji wani iri dana taka kasar gidanan why??”. Maman Abd Shakur😘

[7/13, 08:50] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
72

Dad na shiga gida wata arniyar bakar mota ta paka a gaban Duduwa a guje, da sauri Duduwa taja baya tana haki tazaci Barraq ne yazo harbeta. aka bude mata kofa ta shiga da kyar ta zauna ta jawo kofar ta rufe. cikin bacin rai ta cikin motar tace “ina Rufaida?Ya aka kare? Naga shigan motar Barraq, sanan naga shigar motar gidansu kaman ta Dad dinshi maiya faru??” Duduwa ta gyara zama “nai miki aikin dayafi na komar da Rufaida kauye, ciki gareta kuma saida na zubar da cikin”. “Wot!ciki??Har Barraq yama yarinyar nan ciki?Maiya gani ajikinta? Maitake dashi?? Yanzu ya aka kare??” Duduwa ta gytsuri goro “Barraq yakusa kasheni dayaga jini na zuba daga jikin matarzhi, amma babanshi ne ya taimaken, dan abunda namata hala ita kanta Rufaida bazata rayuba, mutuwar ta nakeso dan ita takashemin yara”. Nana ta sauke ajiyar zuciya da tattausan murmushi” good tsohuwa,kinyi kokari” Nana ta kunna motar tace “muje nabiyaki, gobe PA zai maidake kauye”. Suna cikin tafiya amota DUduwa ta kalli Nana nayan sakanni kafin tace “ke ciki gareki,kuma danyen ciki” Nana tai wani irin take burki akan hanya Duduwa tafasa ihu” wlh ban shirya mutuwa ba”. Nana tace”nikeda ciki??To saidai inko a ruwa nasha, Alhaji na tun wata hudu dasuka wuce yatafi US ban kara hada jikina da wani ba,ke bamani da ciki”. Duduwa tai shewa” hala kam dai a ruwan kikasha dan ciki gareki yarinya”. Nana ta gangara motar zuwa gefen hanya hankalinta atashe” towa yamin ciki??kodai danaje club aka ban maganin bacci nasha akamin??” Chan wani bangaren zuciyarta yace”sama’ila mai gadi! Shikadai nai tarayya dashi,randa Barraq yaban chocolate dinan. Ihu tayi wayyo Allah na!wlh bazan taba daukan cikin mai gadi ba Allah kyauta” tacigaba da sumbatu Duduwa na cin goro tana kallonta. A Bangaren su Alhaji Amma ta wadata su da abun ciye ciye sunci suka kumayi addu’a Allah ya tsayar da cikin. Suka karbi address din asibitin sukace gobe da yamma zasuje su gaida Barraq da mara lafiyan sanan suka tafi. Amma sai kallon karamin yaron hanunsu take yanda fuskarshi tai mugun kama dana Rufaida Allah mai iko da iya sarrafa hallita daban-daban,kala-kala. Har karfe 9:00pm likito ci basu fito ba,Barraq na zaune nesa da Dad da Amma wace bata dade da zuwa ba,Dad yay yunkurin magana da Barraq amma dazaran yazo Barraq saiya tashi yabar wurin. ahankali Dad yace”kadade bakai irin fushinan ba Barraq!mutum daya ne zai iya kwantar ma da hankali. Yajuya yafita daga haraban asibitin. Sai wuraren 10:30 likita yafito Barraq ya tashi likita yace “Barrister muje office” Barraq yabi bayanshi kirjinshi na bugawa, Dad da Amma ma haka likita ya zauna ya nunama Barraq wuri ya zauna, ya girgiza kai Dad ya zauna da Amma Barraq ya tsaya yana kallon Dr da rinannun idanunshi. Dr ya gyara zama” sakamakon dukan da akama matarka a ciki,da kuma tsorata datayi wanda kowa yasani tsoro in not good for a pregnant woman munyi mata hotuna a ciki da…” Barraq ya dafe kanshi “let’s skip d talk and cut to the chase,menene condition din matata yanzu??” Dr yadanyi shiru kafin yace”we tried our possible best muyi saving baby ka hakan ya gagara,am sorry Barrister Barraq cikin matar ka ya zube! Barraq ya kalli Dr da rinannun idanunshi kafin ya rike kujera ya tsugunna ganin zai fadi. Dad ya taso ya bubbuga bayanshi “is ok son,kaya kuri,ka dauki ranannan a matsayin jarabawa” Barraq yakai kusan minti 5 ahaka kafin ya janye hanun Dad daga kafadarshi ya tashi ya kalli Dr ahankali yace “can I see her” Dr yace “of course u can” yajuya da kyar yafita daga Dakin Dad zai bishi Amma ta rikeshi “Alhaji barshi Barraq needs to be alone now” Dr ya karbe da hakane ku barshi ya duba matarshi. Barraq ya shiga dakin ya maida kofar ya rufe ahankali yakarasa gaban gadon da Rufaida take, ya tsaya yana kallonta tai haske sosai tana numfashi kadan kadan, jan kujera yayi ya zauna ahankali ya daura hanunshi kan cikinta, muryarshi ta dishe,takuma yi rauni, ya runtse idonshi gam yana shafa cikin da hannu, hawaye nabin kumatun shi “we lost our baby my Rufaida,we lost our Baby”. Ganin yakasa controlling hawayen yasa ya nemi hanunta ya rike gam ya sumbace su”get well soon My Rufaida,I luv yhu soo very much”. Sakin hanunta yayi ya kifa kanshi akan gadon yarasa mekemai dadi. Jin anshafa mai kai yasa ya dago kanshi ganin Mummy shi idanunta sunyi jaa yasa ya rungumeta da sauri kukan dabaisan daga ina yazoba yasake shi da karfi,Mum ta shafa bayanshi “is ok son,be strong “ahankali ta zaunar dashi kan kujera ta rike kumatun shi da hannayeta ta share mai hawaye,ta sumbaci goshin shi. Gilashin idonshi ta zaro ta chusa hannu a Jakarta ta ciro clean tissue ta share hawayen jiki sanan ta maida mai idonshi. “How did yhu get here Mum?”ya tambaya ahankali Nuna mai agogo tayi yaga karfe 2:30 na dare,” is a long story son, we will talk about that tomorrow. Just sleep,get some rest, cuz u need its”. zaiyi magana tace”shii”ta zauna akan gado ta daura kanshi akan cinyarta ta, Barraq ya rike hanunta daya gam yana sauke ajiyan zuciya, yayinda ta daura dayan hannunta akaan Rufaida tana shafa gashinta kadan kadan. Maman Abd Shakur😘

[7/14, 10:55] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
73

Da asuba yafita yay salla a masallacin dake wajen private asibitin. bayan ya dawo ya tarar da Mum zaune kan dadduma ta idar danata sallan. Ya gaidata ta amsa kafin ya duka ya sumbaci goshin Rufaida ahankali yace “morning Baby na” bude kofa akayi aka shigo Dr ne dawayan su nurses suka bukaci abasu wuri suduba Rufaida atare Mum da Barraq suka fita. Fitar su keda wuya suka tarar da Dad awajen wurin ciki ciki Barraq ya gaidashi “morning Dad” bai jira amsar shiba ya bar wurin da sauri. Dan Restaurant dake wajen asibitin ya shiga ya zauna waitress tazo ta tabambaye shi maiyake so,da kyar yace”coffee” yana zaune yana jiran coffee dabaima jin zai iya shaba yaga Mum da Dad sun shigo wajenshi sukazo sukaja kujeru biyu suka zauna. da sauri Barraq ya tashi zaibar wajen Mum tai magana “koma ka zauna” yakoma ya zauna “Saboda Baban ka yahana ka kadaki tsohuwar dat is old enough ta haifeni shine kake fushi dashi?Haba son haka na tarbiyan tar dakai?” Barraq ya girgiza kai “am not angry Mum,Bana fushi,kawai abun yamin ciwo ne yanda Daddy yabar matar data kashemin da walkout from my house free,yamin ciwo sosai,I want justice to be serve,I wanted to interrogate her,yanda zansan wanda ya nuna mata gidana,cus dat old woman bazata iya kawo kanta Abuja ba,someone must be behind all dis,someone dat hate me and Rufaida,koma wanene I want dem to pay,I want dem to pay Dad,banason Rufaida to face any more problem in her life,she is under my custody” ya karasa maganan muryarshi na rawa sosai, Dad ya daura hanunshi akan na Barraq “komi ya wuce son, babu wanda ya isa ya cutar dakai ko amfanar dakai a duniyanan sai ubangijin ka yaso yakuma basu iko, dat is d fact! Komi ya faru ne saboda tun fil azal Allah ya kaddara hakan,ina tare da Amma securities dinka suka kirani wai sunata kiran number ka akashe I have to come something is wrong, sunji kukan Rufaida,na tambaye su tana tareda wanine sukace min eh kakarta tazo. inajin haka namike tsaye arude nakashe wayan nadau car keys Amma tabi bayana muna zuwa mukaga kofa a kulle shine mukabi ta kofar baya ta kitchen. Naga kana shirin dukanta which is wrong,Barraq learn to forgive and forget kome tayi itada Allah yawuce,nakifa jin zafin abunda tama yata, nafika son jikana data kashe,amma Allah daya bamu shizai sake bamu wani” Ya shafa kumatun Barraq” ka manta da zancen tsohuwar nan and be happy my son, Allah zai bani wani jikan very soon” Mum tace “Ameen” yayinda Barraq yace”I luv yhu Dad”,Dad yace”luv u too son,Allah maka albarka”. Tare sukasha coffee sai labari dad da Mum ke bashi naban dariya saboda yadan sake hakan yafaru yadan sake kadan suka tashi suka koma cikin asibiti. Karfe 4:10 na yamma Dad da Mum da Amma ne adakin Rufaida, Suna hira sama sama,Dr yace musu jikin da sauki halama ta farka yau. yayinda Barraq yafita haraban asibitin shigo da bakinshi na legas dan sun dan bata. Shigowa asibitin sukayi sukai parking a inda aka tanada na parking, Barraq yakara so wajen da waya a hanunshi yana murmushi anatse. fitowa sukayi daga motar,Barraq ya karbi karamin yaron daga hannun matar yana murmushi “Umma ina yini” ta amsa a fara’ance, ya juya ya mikama Alh hannu suka gaisa “Barrister yamai jiki?hope taji sauki”. “Alhamdulillah sir taji sauki, unfortunately we lost d baby” Alh da Umma suka nuna damuwar su sukaima addu’a “Allah kawo rayayye,Allah sa mai ceton kune ” Barraq yay M urmushin dayafi kuka ciwo ya rike hanun karamin baby dake tsalle a jikinshi yana kokarin ciremai gilashin idonshi yace”Ameen Nagode” sai kallon yaron hanunshi yake yaga kamar yaron dana Rufaida ya baci. Amma ta bude bayan motar ta dauko wata katuwar ledar shopping din da Alh yamusu tabisu abaya. Barraq yasa hannu ya bude kofar dakin da Rufaida ke kwance “Bismillah sir” ya shiga ciki dauke da yaron, Alh da Hj na biye dashi Barraq yace”Mum, Dad meet my client d one I told yhu about, wanda yarshi tabace almost 2years a…” Karrraras! karan zubewar abu wanda har saida yaron hanun Barraq ya firgita yasa Barraq kasa karasa maganar shi ya juyo da sauri yaga Alh da Umma suna kallon Rufaida, yayinda Umma ta daga hannu ta dake rawa ta nuna Rufaida tace”Ru..r..Ru…fai. ..”bata karasa kiran sunan ba tai baya luuu zata fadi.

Please Login or Register in order to submit comment