Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yakara jefo mata wani tambayan, ta girgiza kai alamun eh. mika mata byro da memo yayi “rubutamin inda iyayenki suke” kallonshi tayi ta kalli memo dayake mika mata da fararen hanunshi, kasa karba tayi, ganin haka yasa ya ajiye mata akan cinya “oya rubutamin na Karanta” ahankali tadau memo tafara rubutu kaman haka
“Abba na da umma na sun ra..
Kasa karasawa tayi ta kifa kanta a book din tafara kuka dan mutuwar takara dawo mata, tashi yayi ya daga kanta ya zari memo ya karanta sanan ya kalleta yace “sun rasu??” Dagamai kai tayi cikin kuka, yakara jefo wani tambayan “ance wani gida ya rushe mutane sun mutu dayawa kune,iyayenki na cikine?” Da sauri ta girgiza mai kai, “dis morning naji a news ana neman wai young lady iyayenta sun mutu amma ita an nemeta an rasa,cos gamnati nason bata tallafi,kece yarinyar?” Ta girgiza kai cikin kuka, dafe kanshi yadanyi sanan ya zauna akan gadon ya dago kanta yakai hanunshi ya share mata hawayen “is OK,in sha Allah nai alkawarin I will help yhu kinji” ta dagamai kai tareda matsawa baya. “Kinada yan uw… Bai karasa maganan ba saboda jin ana knocking, bada izinin shigowa yay Johnson ya shigo Sir kanada bakuwa? Yace waye? Is Nana sir” dan karamin tsaki yayi yace ina zuwa ”

Baikara cewa komiba, yay shiru tadan kalleshi taga kaman ranshi abace yake hakan yasa takara makewa a jikin gadon, kusan minti 5 sanan ya mike ya kalleta idan kinason zuwa waje kisha iska dakina shine agaban naki ki shigo kifada min zansa akaiki yajuya yafita.

Shiga dakinshi yayi ya mugun daure fuska ganin wacce ke tsaye cikin wani arnen kaya wanda dashi gwara babu, kakkyawar budurwa ce ajin karshe,tana zaune kan gadonshi.
“u again! Nana maiya kawoki wurina? Nafada miki stay away 4rm me”Fari tayi da ido ta langabar dakai “haba My B,maisa kakemin wulakanci dan kaga kanada kyau na mutu a kanka,ina sonka?” Tsaki yay yadafe kanshi kafin yadago yace “kitashi ki fita, get out kafin nakira securities su fitarmin dake” kada kai tayi “ok shikenan inkasan wata bakasan wataba, kakosan wacece mac.. “I said get out Nana” ya daka mata razanan nan tsawa batare da yabari ta gama magana ba. mikewa tsaye tayi tana kadamai jiki da kayan dasuka mugun matseta, matsawa gefe yayi dan ta wuce, saida tazo daidai kusa dashi cikin kyaftawan ido batare daya luraba yaji ta zare glass din idonshi, tasa cikin jaka da sauri takoma gefe tana dariya.

Cikin fushi yace “kiban glas dina,wai wot is ur problem Nana” “ai wlh My B kafin nabar dakinan saina tabbatar nadau cikinka Kota yayane sai Inga idan ka isa kace bazaka aureniba bancin inada cikin ka” ahankali yake daga kafa yana mika hannu kokarin shi shine ya gano saitin datake magana, dariya tayi ciki ciki ta koma gefe tana cire kayan jikinta.

Masu karatu makaho ne wai?ko matsalan ido gareshi?

Maman Abd Shakur😘
[4/28, 9:51 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

7
Ya dakamata tsawa Nana! “Kiban glass kafin na saba miki wlh,nace kiba..”bai karasa maganan ba saboda jin bakinta acikin nashi tana wani shasshafa bayanshi, jikinshi yaji yamutu yakasa tureta, yakasa aiwatar da komi. yana kokarin magana takara tusa harshenta cikin nashi…

Ahankali take tura kofan dakin tanadan hawaye, yatsanta na jini saboda yankewan datayi da nail cutter dabata taba ganin irinshiba. Shiganta dakin keda wuya tasaki wani razanannen ihu wanda saida yasasu firgicewa Nana tasakeshi da sauri tana kokarin jawo abu tarufe jikinta, ihu tacigaba dayi ta kukkulle ido dan ita bata taba ganin mace ba kaya a jikinta ba. Nana takoma baya dan kallon aljana take mata dan bataji alaman shigowan mutum ba saidai ihu, Barraq ne yadan tattaro karfin magana yace “ban eyeglasses dina” da sauri Nana ta dauko jakanta taciro glass din jikinta na rawa ta sakamai a hannu, sawa yayi yajuyo yana kallon yanda take ihu ta kulle idanu tsugunawa a gabanta yayi yace” lafiya ” Kara fasa ihu tayi tana cukuikuye hijabin jikinta tana Kara matsawa jikin garu, ganin kaman ta zare yasa ya juyo da kanshi ya kalli Nana datake tsaye tana kallonsu kauda kanshi yay yace “malama kisa kaya kificemin daga daki,believe me inna dawo na ganki u will see my other part” ya tashi ya dagata chak yafita da ita daga dakin, Kara kurma ihu tayi tana wunsula kafa ya bude dakinta ya wurgata kan gado tacigaba da ihu. ” keep quiet! Ya dakamata tsawa Idanunshi sukai jajir “one more ihu saina zaneki wlh, spoiled brat” ya fice daga dakin tareda bugo kofan yakoma dakinshi dancin uban Nana, saidai yaga batanan tariga ta tafi, zama yay gefen gado ya zaro taba ya kunna yafara zuka saida yasha Kara 4 sanan yaji bacin ran dayake ciki yaragu, bayi ya shiga yakarayin wani wanka yasake kaya.

Wayanshi tayi Kara ganin sunan mai kiran yasa ya dau wayan da sauri tareda zama akan kujera.
” Barrister Barraq! I just got ur email, so yanzu yarinyar natare dakai?” Ya amsa “eh tana tareda ni,u can come over ka ganta,badai tagama warkewa bane,tunda tamin bayani itace wacce parent dinta suka rasu shine nace is better na sanar daku dan adaina nemanta,but plan dina sir zan riketa I will train her and sponsor her education, inajinta kaman sister na,zanyi signing everything gobe inmun hadu a Court, tadawo under my custody,mace ce abu kadan ne zai iya lalata mata rayuwa,idan ban dauketaba bansan ina gawmnati zata turataba,orphanage?gidan marayu? Who knows, zan dauketa kawai” dayan yace “ok,I trust yhu Barisster, nasan u will take good care of her,come over later ka karbi kudin da government yabata” Barisster yadan yamutse fuska “no need of dat sir inada enough money dazan kula da ita” Minister yace “but still gawmnati yabata,kazo ka karban mata is her right” Barisster yace “ok,anjima zanzo na karba, thank yhu sir,I appreciate”
Tashi yayi yadau 1st aid box yafito ya wuce dakinta ganinta yay zaune kan gadon, tana ganinshi taja baya, baice mata komiba dan yasan yanda taganshi da Nana ne yajawo haka, “ban yatsan” Kalmar daya fada kenan, ahankali ta mika mishi tana matsar kwalla sai alokacin yagama karamin ciwone, yadan wanke jinin sanan yace “dena kukan ki kwanta kiyi bacci” kwanciya tayi ta lumshe ido shikuma yakoma kan sofa ya zauna yana karanta newspaper.

Ajiye newspaper yayi ya dafe kanshi yana cije lips, kwata kwata ya rasa natsuwarshi,Nana ta dagulamai lissafi tsaki yayi yazaro taba daga aljihun rigan dayasa ya kunna yafara zuka. Jin warin taba yasa ta bude ido ta juyo da kanta da kalleshi gabanta yay mummunan faduwa ganin yanda yakeshan taba, lumshe ido tayi tana maganan zuci na shiga uku,wlh bazan kwana anan ba yau,gwara na koma wurin Duduwa koda kasheni zatayi, wanan mutumin dan iskane, malam ma yace Annabi yahana zaman mace tareda namijin daba muharraminta ba a wurin daya. wayyo umma na maisa kuka mutu? Yanzu waye zaitaba rikeni?? hawaye take sharewa tana tausayin rayuwar ta, jin anbude kofa yasa ta juyo da kanta taga fita yayi.
Daki yakoma ya chanza kaya zuwa suit mai ruwon toka ya fashe jikinshi da turare yafita yaja mota zuwa gidan Minister.

kallon kujeran daya tashi tayi taga wallet dinshi akan kujeran daya tashi, ahankali ta mike tsaye tana gyara hijabin jikinta takarasa wurin wallet din ta dauka hanunta na rawa budewa tayi taga yan dubu dubu ne sababbi hannu ta rawa yafara da kyar ta iyakai hannu ta zaro dubu daya guda biyu ta maida ta ajiye jikinta na rawa tajuya tafita daga dakin da gudu, waige-waige tafara dan batasan hanyaba bene ta hango tai gudu tabi benen har ta sauka kasa tafito compound din sai alokacin tagane hotel ne danga sunan anrubuta Barraq’s aroyal hotel. Saidai inda tafito taga bangarene daban da fannin hotel din, gate tabi tafita da gudu tana share hawaye “dan Allah kayakuri, in sha Allah zan biyaka kudinka,wlh bana sata,niba barauniya bace, bazan iya zama da dan iskaba” takara gudu dan taji anfara kiraye kirayen mangariba, tana kaiwa titi ta tare adaidaita ta shiga wuf yace “malama ina za’a kaiki?”tace “tashan shiga mota”.

🖌KAINE SIRRI NA🖌

8
Isansu tasha keda wuya tabiya mai adaidaita kudinshi dari biyu, sanan ta shiga motan daizai kaita garin Jigawa! Ta biya kudi 1500.
Kuka sosai take acikin mota tana tuna farkon ranan dasuka zo daga kauyen gunjugu itada Abba da Umma zuwa nan garin Minna, wai yanzu shikenan Abba da Umma sun tafi? Duniyar kenan cewar wani bangaren zuciyar ta,addua kawai zaki dinga musu. matar dake gefenta tace “lpy baiwar Allah kike kuka?ko tsoron tafiyan dare kike?” Girgiza kai tayi tace “a’a Mama kaina ke ciwo”, “Allah sarki Allah sawake, ya sunanki?” Cewar matar, lumshe ido tayi tabude sanan tace sunana “RUFAIDA”!.

Maman Abd Shakur😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 1 TO 8KAINE SIRRI NA 11 to 13 →
KAINE SIRRI NA 9 &10
Posted on April 29, 2016 by mamanshakur
[4/29, 8:37 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

9
Wuraren karfe 11:30 na dare ya dawo, Solomon yakira ya kwaso mishi kayan cikin motan,katon ganamasgo ne wanda naira miliyan 2 ke ciki,wanda gwamnati yabata sai katoton akwati daya biya super market yayo mata shopping kaya nasawa da dama dakuma hijabai manya tunda ya lura ita ustaziya ce, saikuma dan kayan ciye ciye daya siyo mata,murna sosai yake dan gobe bayan yadawo daga Court zai koma Abuja, visa zai mata yakaita Russia wurin Mum,tana mugun son yara,shikadai ta haifa dan yama sanar da ita yasamo mata yarinya,iyayenta sun mutu,mamarshi tanata murna zata samu yarda zata kula da ita. zai kaita wurin Mum tai makaranta a wurin.. maganan Solomon ya katse mai tunani “sir dakinka zankai kayan kona madam?”da murmushi akan fuskanshi yace “shigar dasu dakinta ka ajiye, idan nai wanka zan shiga wurin”, ya wuce dakinshi yayinda shi Solomon ya bude dakinta ya ajiye kayan a gefen gado bai damu da rashin ganinta ba dan yazaci tana bandaki ne yafito ya mayar da kofan yarufe yatafi wurin kwananshi.

Bayan ya gama wanka,ya sanya pyjamas din bacci ya kalli agogo lokacin yaja dare yariga yaraba, dan alokacin 12 na dare yadan gota, tunanin dayayi nacewa yanzu haka tadade dayin bacci yasa kawai yaja bargo yay baccinshi gobe da safe kafin sutafi Abuja yamata bayani.

Karfe hudu na asuba tai musu a tashan garin Jigawa,sauka tayi sukai sallama da matan,tace” to Rufaida Allah Kara hada fuskokin mu,mijina yazo daukana”ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsa “to Mama Allah kaiki lpy,agaida yara”. Tasamu tadan zauna akan wani kujera da aka tanadarma masu tafiya bacci yadan dibeta sai Wuraren 5 na safiya sanan ta tashi taje jikin wani dan masallaci dataga mutane ta dibi ruwa tai alwala sanan takoma Chan gefe guda tai sallolin da ake binta,sanan tai ra’atanil fajir saitai sallan asuba.

Karfe shida ta shiga motan dazaikaita kauyen GUJUNGU itakadai ne aciki ta biya dari biyu kudin mota. tai shiru kaman marainiya tana kallon mutanen wurin dasuke Shan koko da kosai,kaman taje ta roka saboda yunwar dake cin cikinta hakanan ta daure sai Wuraren 8:30 motar ya cika sukadau hanyar kauyen gujungu.

Bayan yagama al’adunshi na safe,ya fito cikin 3quater dayar short sleeve dinshi fara fat yana rike da karamin kofin coffee ya tura kofan dakinta ya shiga,ganin bai gantaba yasa yakoma kan kujera yay crossing legs yana Shan cofee a nishadan ce, yadau remote ya kunna TV bango,atunaninshi tana bayi, ajiye cup din coffee yayi akan stool din gefen kujeran ya kalli agogon hanunshi almost 15 min da shigowan shi batafito daga bayi ba kuma baimaji alamun saukan ruwa a bayin ba. Tashi yayi da sauri ya tsaya a gaban kofan bayin ya kwankwasa ” Hi sister kina ciki?” Yaji shiru da sauri ya bude bayin yaga babu kowa aciki, a rude yasaki kofan bayin ya juyo sai alokacin idonunshi suka sauka kan wallet dinshi daya gani a bude wasu ID dinshima akasa sun zube karasawa yayi yadaga ya mammaida ya kulle sanan ya fita zuwa kasa dakinsu Johnson ya tambaye su kunga yarinya na? Kowa yace a’a,yace “Solomon jiya dakaje ajiye kayan nan baka ganta acikiba?” Yace “no sir,babu ita I thought tana bayi saisa ina ajiyewa na fito na kulle kofan”, Barr yace”God! I pray yarinyar nan ba guduwa tayiba” yakarasa wurin securities masu tsoron gate ya tambayesu wanda ke duty jiya yace “Sir jiya duk Wanda suka shigo hotel dinan dawayan da suka fita babu wacce tasa hijabi,sai wata yarinya black beauty haka sir,batada kiba sosai, kuma batada tsawo sosai,quite sure naga daga part dinka tafito da gudu,she was crying self lokacin datafita”.

Barr Barraq yace” damn it,wot is your problem mandawari?,kaga karaman yarinya tafito daga part dina tana kuka baka tsayar da itaba”,yakara dakamai tsawa “Kaine a duty ranan Dana kawo yarinyar nan wurin nan,u saw lokacin dasu Johnson ke shigar da ita ciki,but duda haka u let her go”, mandawari jikinshi na rawa yace “sorry sir,a gafarceni,wlh ranan ba kalli fuskanta da kyau bane” ya kalleshi da jajayen idonshi yace “u no nothing akan job dinka,so just pack ur things nd go, nakore ka” yajuya yakoma ciki Johnson da Solomon suka rufamai baya,mandawari yafashe da kuka ya zube akasa “dan Allah kayakuri sir,wlh bazan Kara kuskure hakaba” ko juyowa baiyiba daki yakoma ya dauko car keys,ya fito ya shiga yaja motan da bala’in gudu yana zukan taba yabar hotel din.

Maman Abd Shakur😘
[4/29, 8:37 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

10
A daidai kauyen gujungu aka sauketa,ta sauka tana tunanin uban tafiyan dazatayi kafin takai cikin kauyen, a hankali take daga kafa take tafiya tana Kara kallon kauyen rabonta da kauyen kusan wata shidda kenan, cikin sa’a taga mai amalan ken data Sani abokin Abba ta tsayar “Baba ina wuni” tafada tana murmushi Kara kallonta yayi yana goge idanu “wanake gani? Rufaidatu ce?” “Eh Baba nine”, ya sauri yace” a hayo, hayo mana, hannu Rufaidatu” tahau kan amalan ke,ya shau dama jakunan bulala suka fara tafiya, sanan yace”Rufaida ya hakuri? munji Malam Musa,da Asiya sun rasu daga bakin Duduwa,dan hargarin nan wasu polisawa sukazo ana nemanki,aka kuma sanar damu rasuwan iyayenki ta hanyar rushewan gini”. Hawaye ya cika mata ido “Alhamdulillah Baba” yace” Amma Rufaida maiyasa ki kara dawowa kinsan yanda Duduwa ta tsaneki,duk yanadaga cikin abunda yasa Musa marigayi ya Tattraku yabar kauyen daku saboda jaraban mahaifiyar shi Duduwa” cikin kuka tace “Baba banda kowa, sai Duduwan dole na dawo koda kasheni zatayi”, girgiza kanshi yayi yace”hakane Rufaida karki damu Allah natare dake,ki dage da addu’a Allah ya dauraki akanta ” tace” to Baba nagode”.

Haka suka dinga fira sama sama harsuka shigo cikin kauyen. Kauyene sosai, ko ina yara da yanmata anci atampa daban riga daban dan kwali daban ga dige dige a fuskannan sai kallonta suke dan basu ganetaba tasha hijabi abinda basu saba ganin yan matan garin na sawaba, a kofar gidan Duduwa ya sauke ta, ta sauka amma tasami kanta da kasa shiga gidan saboda tsoron Duduwa, kuka tafashe dashi sosai tana yarfe hannu, Baba ya tausaya mata yace” Rufaida ki shiga da bissmillah Allah na tare dake kinji yata karkiji tsoro” ta goge Hawayen wasu na zubowa tace “to Baba nagode”

Bude buhu kofar gidan tayi ta shiga ahankali tana tafiya a zauren, kunenta suka juyo muryan Duduwa na rera waka”Ladi mai kidan kwarya aja kida asha dadi …ari, kai anata sabon daa wayake ta tsohon da.. Ari, saidai munafukai su kalleni Niko ai inada nerori ..Ari, Alhakumu aljanna kubari infadi da hillanci.. Ari”

Hawayen idonta ta share, jikinta na rawa, ahankali ta rera sallama “Assalamu alaykum”

Maman Abd Shakur😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 9 &10KAINE SIRRI NA 14 to 16 →
KAINE SIRRI NA 11 to 13
Posted on April 30, 2016 by mamanshakur
[4/30, 10:47 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

11
Duduwa ta bude zip din lalitar jikinta ta zaro yar guntuwar goronta ta Balla sanan ta amsa”waalaika salamu,higo” ta shigo cikin gidan jikinta na rawa “Duduwa ina wuni”, da sauri Duduwa ta ijiye tabaryan hannunta ta mike tsaye baki abude tana kallon Rufaida, ” bakar mayya mekika dawoyi? Kindawo kasheni ne nima? Kin kashe Dana Musa da matarsa Asiya shine yanzu kika biyoni nima ki kashe” Rufaida ta tsaya tana share kwalla tace “wlh banina kashe suba Duduwa,gini ne yafado akansu” da sauri Duduwa tace “to dan ubanki juya kibar gidana,dama ai duniya kika shiga ki koma Chan inda kika fito ki barmin gida,Alhamdulillah dama Wanda ya kawoki ya mutu dan haka babu Wanda ya isa yanzu yahana ni koranki, wuce kibarmin gida” kuka tafashe dashi sosai tazo dagudu ta tsugunna agaban Duduwa ta dan Allah Duduwa karki koreni babu inda zani banda kowa wlh” ta hankada ta”,sakenmin kafa, da Chan dakika shiga duniya dawakike tare,kina gidan karuwai ko?” ta girgiza kai tace “A’a, dan Allah Duduwa kibarni na zauna”, Duduwa ta turata da kafa ta fadi “dan ubanki tashi ki barmin gida bazan iya zama da karuwa irinki ba, nizaki rainama wayau kafin a haifeki da shekaru dari nake duniya,daga ganin yanda kikai danya danya dinan kinwaniyi huras(fresh) cikin shegema gareki” ta finciki tabaryan datake daka fura dashi tace “tashi ki barmin gida” da gudu ta mike tayi hanyar fita tana kuka kaman za’a zare ranta, Duduwa takoma tacigaba da dakanta tana sauraran yanda Rufaida ke banka uban kuka, kome ta tuna sainaji tace “Faida” da sauri Rufaida dake kuka a zauren tace “naam” Duduwa tace “yaki” ta shigo, “dau tulu kije ki dibomin ruwa a rafin,idan kin gama ciccika randunan saikije ki gyara bukkan Chan shine dakinki” ta nuna mata wani bukkan Kara,da ake ajiye tumakai aciki da.

Murmushi tadanyi saboda dadin Allah ya daurata kan Duduwa zata yarda ta zauna,”bazaki wuce ki dauki tulu ki tafi ba shegiya mai kama da ifiritu”cewar Duduwa, da sauri taje kusa da kitchen tadau tulu ta juya zata tafi Duduwa tace “zonan” taje gaban Duduwa tana dar dar,mekuma tayi?
wukar dake gefen Duduwa ta dauka saida Rufaida taji tsoro Duduwa tasa wukan ta kyasta hijabin dake jikinta tundaga sama har kasa tana masifa “da da wanan shegen kimar(dogon hijabi) dinan zaki fita, shegiya rubabbiya, bakisan aurar dake zanyiba,kinwani sa wanan abun wazaiga jikin naki haryaso,wlh duk randa nakara ganin kinsa kimar kin fita saina kusa kasheki da duka,wuce daki zakiga wani tsumma danake goge kasa ki dauka kisa ki cire wanan na jikinki,anjima idan dillaliya tazo na siyar nasamu kudin saro sabuwar gyara”.

Ranta baiso ba,dan taso ta dinga tuna mutumin daya taimaketa ta hanyar ganin wanan doguwan rigan mai kyau kullum,chanza kayan tayi tasa tsumman da Duduwa tace sai warima suke hakanan tafito tadau tulun tace “Duduwa natafi” ko kallonta Duduwa batayi ba kirga fura take. Tajuya tafita tana tafiya ahankali, daga gidansu zuwa rafi badai nisaba,dan kusan karshen kauyen rafin yake.

Maman Abd Shakur😘
[4/30, 11:03 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

12
Barr Barraq babu inda baije ba agarin Minna neman taba,hatta inda ya tsinceta saida yaje,ranshi yabaci iya baci,yanzun ina taje? Ina ta shiga? Ga dukiyarta a hanunshi yazaiyi da ita? yunwa yasa ya kalli agogo yaga karfe 4 na rana a bakin wani masallaci ya paka yay salla sanan yabiya wani eatery yasai meat pie da Vita milk, dawowa mota yayi ya zauna ya dauko meat pie din zaici jiyayi ya tsani meat pie din yay wurgi dashi ta glass din mota, ya kunna taba kawai yaja motan yay gaba hotel yakoma su Johnson namishi magana ko kulasu baiyiba ya wuce dakinshi ya fada kan gado. Saikuma ya tashi yadauko wani karan taban yasha sanan yadanji bacin ran yaragu. wani dan abu naga ya danna a gefen gadonshi saiga Solomon ya shigo ahankali yace “kiramin P.A” ba adadeba PA ya shigo, Barr ya kalleshi yace “PA inaso kaje banki ka bude new account ka zubamin wanan kudin aciki,gobe ne zamu koma Abuja, bazamu iya komawa yauba” PA ya amsa da to yadau Ghana masgon da yaga Barr na nunamishi yafita daga dakin, tashi yayi yawuce yay wanka.

Sai Wuraren issha tagama cika randunan da Duduwa tace ta cika,ta gaji iya gajiya taje zata dibi ruwa taje tai wanka taga Duduwa ta haskota da tocula ” mezaki min da ruwa?”da sauri ta rufe randar tace”dama wanka zanyi” Duduwa cike da masifa tace” akace miki wanan ruwan na wankan ki neko,shegiya mai kama da ifiritu,idan zakiyi wanka kinsan hanyar rafi kuwuce kije ki debo,ruwan nan bana amfanin ki bane” ta tashi daga wurin tadau buta tai alwala, kallon dakin Duduwa tayi taga bata falo alamun tana uwar daka, da sauri taje dakin mamarta kafin subar kauyen ta shiga da kyar ta lalubo wani yamutsartsen hijabi hakanan tasa tai salla sanan tacire tafito ta zauna abakin kofan Duduwa tai shiru. gyangyadi na daukan ta saboda gajiyar datayi. Kwal taji anbuga mata wani abu abaya da sauri ta tashi tana Sosa wurin saboda azabar zafin dataji, Duduwa tace “wanan kazamtacciyar jikinki zaki wani kwantamin a tsaftatacciyar bakin kofana mayya, yi Chan” ta nuna mata gaban bukkanta,tajuya tana Sosa wurin da Duduwa tabuge ta tana kuka,”zonan! Duduwa ta daka mata tsawa “ungo”,Tamika mata ragowan tuwon dataci tarage,da sauri ta karba tareda fadin “nagode Duduwa”, taje gaban bukkanta ta zauna taci ko koshi batayi ba amma bata damuba tunda tama samu Tabata, ta tashi zataje tasha ruwa,harta bude randa Duduwa ta haskota da tocula “wlh inkika tabamin ruwa sainaci kan ubanki,kona alwala Dana bari kikayi shima dan ubangiji zakima ibada wuce kibar wurinan ki shige dakinki kiyi bacci”.

Da sauri ta shiga bukkan, ta zauna ta baki-bakin kofa,dan cikin bukkan duhu bata ganin komi,gashi kauyen ba wuta,tsoro takeji na bala’i. a zaunen tafara bacci sama-sama jin kaman kwaro nabin jikinta yasa tasaki ihun bala’i tafito tsakar gidan tana ihu, da sauri Duduwa tafito daga dakinta tana Kara gyara daurin zani ta daura mata dundu abaya tace ” shegiya bakar mayya,to wlh Kinyi kadan kihanani bacci, lpy kikemin ihu?” Da kuka tace “Duduwa kwaro kebin jikina wlh” Hannunta Duduwa taja ta haska dakin da tocula duk kyankyasai na bayi kebin kashin ragunan wurin,Rufaida takara ihu tarike Duduwa tace “kingansu kk Duduwa” Duduwa ta hankadata ciki,ta jawo kofan bukan ta rufe tana masifa “dan ubanki su cinyeki,Allah sama ki mutu kaman yanda kika kashemin Dana da matarshi”, ta ciro kwado daga lalitar jikinta tasa tajuyo tanajinta tana ihu amma ko das bataji arantaba, saima masifar data cigaba dayi “Marigayi Musa bakajin magana, kawai ka tsinto yarinya ka tsinto jaraba,gashinan ta hanani yin bacci,to wlh duk maitarta Ni bata isa ta lasheni ba, yanda kika kashemin da Ni da wahala zan aikaki barzahu” tahau yar gadon bunun ta ta kwanta,tana korafi.

Maman Abd Shakur😘
[4/30, 12:17 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

13
Rufaida dataga ihu da jijjiga kofa bazai fisheta ba saita make ajikin kofan tama kasa hawaye,Umma tafado ranta,””lokacin kafin Abba yasamu aiki subar kauye suje Minna Duduwa ta taba kulleta a wanan dakin lokacin tun ragunan ma naciki,haka Abba da Umma suka roketa amma taki budeta,Umma tadaga haka saitazo ta tsaya a bakin kofan tace Rufaida ki dinga fadin A’uzubikalimatillahi tammat min kulli sha’in ma kalaq” tunawa da addu’a da Umma takoya mata yasa tafarayi ahaka har bacci ya kwasheta Wuraren karfe 1 na dare batare dataji kwaro yahau jikinta ba ko wani abu ya cijetaba.

Karfe 5 na asuba taji an zaulamata zabori a cinya, a firgice ta mike tsaye taga Duduwa ce, tace”Ina kwana Duduwa ” Duduwa ta kalleta shekeke tace” karuwa,watoma yanzu baccin karuwai kikemin a gidako? Bacci

Please Login or Register in order to submit comment