Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dazu abbanta yakira baturen nan da Barraq. Ahankali Muryarta na rawa tace”Baba bature ne? ” Baba ya girgiza kai “eh jini biyu ne dai”Mamar shi yar rasha(Russia)babanshi dan Nigeria”. Rufaida ta tsala wani irin uban ihu tafashe da kuka tai hanyar part din Daddy yanda maza suka cika wajen yasa tajuyo takoma dakinsu tana kuka wardrobe ta bude taga suit baki daukowa tayi tasa ta daure wandon da dankwali saboda yamata yawa tasa necktie, rasa yanda zatayi da uban gashin ta yasa ta dauko wani facing cap data gani tasa ta dunkule gashin aciki tana kuka sosai”wlh saina ganka, saina kutsa cikin mazanan na ganka,dan Allah karka mutu” kara rike cikinta tayi dataga yakara motsi ta tashi da kyar tafito. Koda takaraso wurin taga an lullube abu da fararen kaya ansa amakara jiri tafara gani batasan lokacin data shiga cikin dandazon mazan nan ta dinga kutsawa har saida ta taba makarar ta rike gam tana kuka. Muzzammil dake hawaye ya juyo dan yaga me bugeshi garin kokarin kama makara. Ana saka makarar a mota Rufaida tariga kowa fadawa ciki ta chusa kanta a cinya tana kuka. Tadaiji mota natafiya wanda hakan yasa ta dago kanta ta kalli kowa Daddy kadai ta gane acikin mutanen Motar. Kuka tasake fashewa dashi sabo kafin ta zabura saboda motsin dataji cikinta nayi ta rike cikin gam tana kuka cikeda ihu tace”kadena min ciwo,wlh saina raka bature gidan gaskiya,inason shi,Allah ya jikan mijina ” kowa na motar ya zabura yana kallon mutumin da akaji da muryar mace, Dad yakai hannu ya cire hular gashin ta ya zuba akafada atare Dad da Muzzammil sukace “Rufaida! Kuka tasake fashewa dashi tana wani irin haki kaman zata mutu, ganin kowa na motar take biyu biyu ta hade hannayeta da kyar ta iya magana “Dad dan Allah karka koran zan bishi ne, idan kace a’a zan mut…”bata karasa maganan ba idanunta suka fara juyawa wani irin mugun jiri ya kwasheta ta sulale kwance a wurin hannunta daya ya sauka akan farin kyallen da Barraq ke ciki”. Dad yay salati Muzzammil yaza. ..” Muzzammil yace”Daddy look” ganin farin kyalle na motsi sosai yasa sauran mutanen cikin motar suka fara neman wurin guduwa. “Daddy budeshi, doguwar suma ce,he is alive! Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
83

Muzzammil yataya Dad suka ciroshi Dad ya warware kyallen jikinshi. Ahankali Baban muzzammil ya paka mota agefen titi sauran motoci da machina dake binsu abaya duk suka paka suna mamakin maiya tsayar da motar daya dauko gawa.
Daddin Muzzammil ya bude mota ya fito,Imam ma yafito suka zagayo baya,Muzzammil ya bude musu da sauri hawaye na kwarara a idonshi ahankali yace “Daddy da ranshi doguwar suma yayi,mutafi asibiti kawai” Dadin muzzammil yakai dubanshi ga Dadin Barraq dayasa Barraq a kirji yana hawaye sosai ahankali Barraq ya furta “Boo water,I need water” Dad ya dago kanshi da sauri yace”Muzzammil bamu ruwa ” kafin kace kwabo mutanen da suka zageye motar kowa yafara gudun nemo ruwa a shagunan dake kan hanya. Wani bawan Allah yasamu aka dinga pasin pasin goran ruwan faro saboda yanda jamaa suka taru har ya iso cikin motan muzzammil ya karba ya bude yabama Dad,Dad ya saka abakin Barraq da sauri yafara sha rabi na zuba akasa, Dadin Muzzammil ya gyara mai bakinshi ajikin ruwan yadan sha dadan yawa sanan Dad ya cire goran a bakinshi. ahankali Dad yace “mutafi asibitin”. Da kyar jama’a suka matsa ma Dadin Muzzammil da Imam suka fito suka shiga mota akaja, yayinda Muzzammil ya rufe kofa. Jama’a anata al’ajabin al amarin wato daguwar suma yayi. Aka koma mota wasu suka bisu wasu kuma suka juya gida tareda fatan Allah bashi lafiya. Karfe 10:30 P.M. suka isa Baban asibitin garin Abuja mai suna “Handsome Shakur Specialist Hospital” kwararun likita suka karbi Barraq da Rufaida da gaggawa. Anata yima Dad gaisuwar Allah bashi lpy mutane na tafiya. Muzzammil yasamu yadan kebe ya ciro wayarshi ganin kusan 35miss calls din Hafsat yasa yakirata da sauri yay mata bayanin abunda yafaru. labarin ya girgizata Muzzammil yace duk dare zai dawo tanuna mai bakomi,ya kula da abokinshi zuwa gobe yazo ya dauketa yakaita ta dubasu sukai sallama suka katse wayan. Yana gama wayan kiran Mum ya shigo wayarshi da sauri ya dauka Mum da muryarta ya dishe sosai tace”Muzzammil neman Daugther muke bamu ganta ba,kuyi sauri ku dawo” Muzzammil yay murmushi dimple dinshi suka bayyana “Mum kira Daddy danshi yakamata ya baki goodnews dinan” ya katse wayan yayi dailing number wani abokinshi ishak babban police ne,daya rike matsayin DpO yamai bayanin komi,DPO yace”gobe da safe zasuzo idan lokacin Barraq zai iya magana dole suyi magana dashi dan yamusu bayanin maiya kaishi gidan Nana,da sauran vital informations. Muzzammil yay godiya ya katse wayan tareda komawa cikin asibitin. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
85

Suna fitowa suka tarar da Amma da Muzzammil da Auta dake zaune kusa dashi yana lallashinta. Dad ya zauna Amma ta tambayeshi ya jikin murmushi ya sakar mata “cikin nanan bai zube ba,nakusa zama grandpa”.
Farin ciki ya lullube fuskarta. Mum ta zauna gefen Amma tace”any news akan son ?”Amma ta girgiza kai “har yanzu Dr bai fito yamana bayanin komi ba”. Mum ta rike kuncinta tana sauke ajiyan zuciya damuwa ya bayyana akan fuskarta. Amma ta dafa kafadarta “Hey!don’t worry,Barraq is a fighter zai warware,komi zai koma normal kaman da I promise” Mum ta daura hanunta akan na Amma ta lumshe ido”thank yhu Amma,tashi muje mu duba daugther” suka mike atare Mum ta bude dakin da Rufaida ke ciki suka shiga har alokacin tana bacci ana kara mata ruwa. Suka zazzauna. Dad ya dauko waya ya kira iyayen Rufaida ya sanar dasu komi daya faru bayan tafiyar su salati Alh yayi ya sanar da ubangiji yace”Allah yabashi lpy, in sha Allah zamuzo gobe mu dubasu”. Dad yace”no need kaida kakeda maras lafiya” Alh ya sauke ajiyar zuciyar yace”Akwai abunda ban fadama ba jiya bayan mun dawo,cikin haukar ta ta sanar mana ita tama Rufaida asiri ta manta damu ta shiga duniya, she’s paying for wot she did,baruwana da haukan ta ramin muguntar data hakane tafada ciki nida Umman Rufaida zamuzo gobe, Allah kara musu lafiya yasa kaffara ne ” Dad yace”Ameen”. Dad ya kalli Muzzammil yace”son kaje gida mana Daugther na nemanka ” Muzzammil ya girgiza kai “sai B yatashi zan tafi, Dad ina sapayan gilashin shi? ” Dad yadanyi shiru “baida wani sapayan gilass ,normally a eye clinic dinshi na India idan gilashin sukai expire yaje biyu suke bashi,so lokacin dayay hatsarin nan a kauyen Duduwa da bikin ka har gilas dinshi ya kone na tahomai da sapayan yasa,yanzu dole mu fitar dashi a duba idon achan kafin sumai gilashin dayay suiting idon a yanzu, but dat will be bayan ya warke ” Muzzammil ya sauke ajiyan zuciya “Allah sa muji alkhairi” Dad ya amsa da “Ameen “. Suna zaune a wurin DPO da wasu polisawa guda uku suka shigo Muzzammil na hangoshi ya tashi ya shigo dasu inda suke ya kalli Dad yace”Dad nakira sune saboda na fadin musu abunda Barraq yafada min da iya abinda nasani,dan duk wanda yayma Barraq abunan saina kulleshi” DPO ya mikama Dad hannu suka gaisa kafin su zazzauna. Ahankali Muzzammil yamusu bayanin komi tun lokacin dayake office Barraq ya kirashi, harya iso yaga Barraq cikin jini da abunda yafadan mishi. Dad yay mamaki yace”Nana?Nana dai dana sani? ” Muzzammil yace”Eh ita Dad” Dad yay shairu. DPO yay rubuce Rubuce kafin ya kalli Muzzammil da Dad yace”kiran sunayen mutanen nan uku da Barraq yayi acikin jini makes dem our suspects, PA,Duduwa da Nana. Cus muna bama irin maganan nan amfani sosai,but still zamu so ji daga bakin Barraq idan ya tashi. And zamu nemo Nana,Duduwa PA dan interrogating dinsu,zamu tafi yanzu zamu iya dawowa any time dan yimuku tambayoyi idan mun shiga duhu akan binciken”. Ya tashi yamika ma Dad da Muzzammil hannu suka gaisa. Muzzammil ya taka musu zuwa wajen asibiti suka shiga mitarsu,kafin ya dawo ciki ya zauna kusa da Dad. Wuraren 12 na rana likita yafito daga dakin da aka shigar da Barraq, saida ya wanke hannu da fuska sanan ya zo wirinsu yace”congratulations sir,Barraq is safe and sound,mutum daya kadai zai iya zuwa ganinshi for now,saidai patient din nata kiran sunan Rufaida Rufaida sometimes yace”Baby na I suggest akai mai me sunan ya ganta gaskiya” Dad ya washe baki yacema Dr “thank yhu sosai”, Dr yay murmushi yace “Sir akaima patient dina abunda yaketa kira plz”,Muzzammil yace”Sure,yanzu ma kuwa”. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
84

Karfe 6 na safe taima Mum da Amma harda Auta da fuskarta tai suntum ya kumbura saboda kuka a asibiti. Duk suna zaune Dad ya dauki Auta dake kuka yana lallashin ta wata likita tafito daga wani hadadden Daki. Tana sanye da farin coat data daura akan riga da wandon dake jikinta,hannayeta sanye da hand gloves,tasanya iD dinta a wuyanta da aka rubutu sunanta ajiki “Dr Rukayya Sadau”. Takaraso ta tsaya agaban su Dad tace”Ina iyayen Patient Rufaida? ” Dad ya mike da sauri tace”ku biyoni office ” Dad da Mum sukabi bayanta. Ta zauna su Dad suka zauna bude file din Rufaida tayi tana yan dube dube da karance karance. Kafin ta kalli Dad tace”Sir jiya kace bata dade dayin bari ba da ina tambayarka akanta?” Dad ya gyada kai “yes tai bari 2 days ago” “an mata wankin ciki ne bayan tai barin?” Dad ya girgiza kai”no,Doctor yace cikin yariga yafita basai anyiba, kawai mu dinga bata abinci mai kara jini ajiki da magungunan daya bamu” Dr Rookey Sadau tadanyi rubutu acikin file din kafin ta dago kanta ta kalli su Dad murmushi Kwance akan fuskarta tace”Cikin bai fita ba,sun tsayar da jinin da wuri,maybe saboda yanda tai bleeding din yasa basu gane da wuri cikin nanan ba,but cikin yarku nanan for now inhar zakubi kaidodin dazan baku ” Dad yama kasa magana saboda farin ciki Mum ce tai magana “menene kaidodin?” Dr Rookey tace”ku hanata daga any object ko abu mai nauyi,sanan any exercise irinsu tsalle-tsalle,guje-guje da dirke-dirke tadena yi saboda suna kawo zuban jini hakanan ko zubar ciki ma. zaku kiyaye abubuwan cinta tana yawan cin abinci mai kara jini sanan ta guji abinci mai siga sai shawarwarin dazan baku shine Mai ciki ta dinga yawan cin wake saboda yana karama yaron cikinta kaifin kwakwalwa sanan yana bama maiciki ruwan Nono sosai. Shan kankana yana gyara fatar yaro acikin ciki,kuma yana karama yaro kaifin kwakwalwa. Cin ganyen irinsu ugu da alayyahu yana kara jini ajikinsu,Sanan alokacin da mace keda ciki wanda ke yawan sata amai tadinga cin kwakwa (coconuts)da rake(sugar cane) yana rage yawan amai. And suna hana yaro ya dinga kurjaren zafi, wutar dare and d rest bayan an haifeshi,kuma suna rage ciwon nakuda. Cin dabino(Dates) strengthen the muscles of the uterus akarshen watan haihuwa. Kuma Yawan cin dabino yanasa mace ta bude ta cikin sauki batare da an karata ba a lokacin haihuwa. Cin dabino ga mai ciki dama wacce ta haihu yana karama ruwan Mama elements din da ake bukata na karama yaro lafiya da kariya daga kowace irin cuta. Sanan sai shawarwarin kula da yanayi (mood)din datake ciki. Yanada kyau mai ciki ta kasance cikin farin ciki kowani lokaci,ta kalli abu mai kyau,taji abu mai kyau,ta sha abu mai kyau,ta shaki kamshin abu mai kyau. Dan ko wani hali mai ciki ke ciki haka dan cikin ta ke ciki. Yanada kyau mai ciki ta nisanci bakin ciki ko bacin rai,sanan kartaji haucin kowa kota tsani wani abu,ko ta dinga bakin ciki dawani. Dan duk hali /yanayin damai ciki ke ciki yana affecting yaron cikin ta. Ta kalli Mum tace” Ma ko film din ban tsoro baaso mai ciki na kallo inhar suna bata tsoro irinsu vampires films,Horror films and d rest duk bai kamata ba. (It is important to have good feelings,good thoughts, and not to carry grudges,have fear of something or be unduly worried about something. A pregnant woman should remain calm,happy and should not be allowed to be over concerned and allow herself to be overtaken by grief. The thoughts you generate within urself will affect the kind of disposition the child will have. If u are sad and miserable the child will be equally affected. REMEMBER! it is the mother’s womb that is carrying the baby and that the baby is affected by whatever she is thinking, feeling, reading and listening to. It is better and advisable for a pregnant woman to keep a good company, to read good books. Example The Holy Qur’an.) likita tace “zaku iya tafiya sai jibi zamu sallameta dan 16prime ce,we need to monitor her” Dad da Mum sukai godiya suka fita. NOTE:Duk abunda nafada akan mai ciki yakama ta tayi hakane,gaskiya ne,Allah sa wasu su amfanu da my little ilimi, Ameen. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
86

Dr Rookie Dad yay ma bayanin komi babu bata lokaci tasa nurses suka gungura Rufaida zuwa dakin da Barraq yake batare da anbar su Dad sun shiga dakin ba.

Da kyar Barraq ya furta “My Rufaida kece?”Jin motsin dayayi a dakin Dr Rookie tai murmushi takama hanun Rufaida ta saka a cikin hanunshi tace”ga Ruffy dinka anan,bacci take,karkai magana da yawa cus of ur condition,take care” tajuya ta mayar musu da kofa tafita. ahankali Barraq ya murza hanunta tareda lumshe ido “get well soon Baby na,naso zan iya ganinki yanzu”yakai hanunta kan bakinshi ya sumbaci hanun ahaka bacci yay gaba da shi.
Washe gari akabar Su Dad suka shiga ganinsu har alokacin bata tashiba sai Barraq da idonshi biyu Mum ta rungume shi gam tana kuka Auta ma haka da kyar sukai shiru. Dr yabama Dad takardar transfer zuwa India saboda yimai gilash.
Karfe 12:Am na Rana Rufaida ta farka ahankali ta tashi zaune daga gadon da kyar tana yatmutse fuska. Kallon dakin tafara bataga kowaba,daga hanunta dazatayi da zumar sosa fuska taji kaman an riketa, da sauri ta juyo ganin Baturen da tasan ance yamutu yasa taji kanta yafara juyawa yayinda zuciyarta ke tashi tanajin wani irin amai na taso mata, bata ankara ba tafara kwara amai da bakomi ciki sai ruwa yellow Mum dake zaune wajen dakin tana karanta jarida ta ajiye a gefe ta shigo dakin da sauri ganin Rufaida na amai yasa takoma waje da gudu takira Dr. Dr da Nurses suka biyo bayan Mum aka shigo dakin daura Rufaida sukayi akan gado suka fita da ita zuwa dakinta. Barraq yace Mum maiya sami Rufaida? ?ta rike hanunshi Son karka damu amai ne kawai.

**********

Bayan sati biyu.

Zaune Rufaida take a falon Amma ta tasa dan wake agabanta tana kallo takasa ci ko kadan. Ta rame sosai tayi wani irin haske. Kirjin da baya ne kawai acike dam. Amma ta zauna kusa da ita tace”Rufaida kefa kika daman na miki dan wake kuma kin kici,ko kinfiso sai Auta ta dawo daga makaranta ta tasaki agaba tana kuka kafin kici?kin manta fadan da Umman ki da Abbanki suka miki jiyako?” Rufaida ta girgiza kai tana share hawaye “Amma ni bature nakeson gani,kunce yana raye amma ni ban ganshi ba,tun randa na ganshi a mafarki harna dinga Amai ban kara ganinshi ba” Amma tai murmushi “oya ci koda kadanne nabaki albishir mai dadi kiji” tadan kalli Amma,Amma ta gyada mata “trust me,I promise zakiji dadin news din,amma kifara ci dan rabonki da abinci tun jiya da daddare da Auta ta tasaki agaba kikaci yam balls,so kike bebin cikin ki ya rame? ” Rufaida ta girgiza kai tareda sa hannu aciki plate din tafara ci ahankali har taci rabin plate sanan ta kalli Amma nakoshi. Amma ta shafa kanta kafin ta mika mata maganin rana tasha da kyar sanan tace “Amma fadamin?” Amma tai murmushi “dazu kina bacci Dadin Auta yakira yace min yau zasu dawo dashi da Muzzammil da Barraq dinki ita kuma Mum zata wuce Russia dan tanada case a chan ana nemanta” cikin murna Rufaida ta rike hanun Amma tace”Amma wanan baturen shine Barraq ko,shine zai dawo? ” Amma ta gyada mata kai tana murmushi, murmushi Rufaida tasake yi tareda chusa kanta tana murmushi Amma tai dariya oya tashi ki dauko hijabin ki na kaikai Zee Hamza saloon wata yar katsina amiki gyaran jiki dana gashi da kunshi.
Karfe 5:00 na yamma suka dawo Rufaida sai sheki take fuskar nan tai kyau. Amma ta kaita part din Barraq tahada mata ruwan turare tai wanka dashi. Amma tace bari naje na duba abincin da Fauzeeya(yar aiki)ta hada. Ta wuce tafita. Rufaida tai wanka tafito ta zauna a gaban madubi tana kallon lallin da akamata dake burgeta. Ahankali tasake mikewa ta dauko wata katuwar handbag ta juye akan gado tana murmushi “Umma na nagode da kayan kwalliyan da kika kawomin” kwalliya tayi sosai tai kyau sanan tasake dauko katuwar jakar da Umma ta kawo mata taciro wani bakin 3quarter wando wanda da kadan ya wuce guiwa da Jan shimi armless anmai kwalliya da fulawowi bakake,saka kayan tayi ta chusa shimi cikin wandon (zanzaro)tadau wani kacha da yazo tare da wandon a matsayin belt ta zura ta kulle tareda sakinshi yabi gefen hip dinta ya kwanta. Zama tayi agaban madubi ta zira jan dan kunne karami yana walkina kaman Diamond tadau wani hair clip jajaye masu suffan kananun fulawowi ta jerasu agaban gashinta abin yay mata kyau sosai takara dawowa yarinya sak. murmushi tadan saki ta kalli madubin tai mai fari”toni kai madubi mena kallona?,ai dai ban cema inason bature ba “ta murguda baki”am just soo excited yau bature zai dawo” tasa tafukan hanunta ta rufe fuskarta “to uhm, uhm ai jiya da Umma tazo tace nadinga gayu,nai gayu sosai randa bature zai dawo” da sauri ta mike tsaye”laaa turare na da Umma tace nasa duk randa zai dawo” da sauri tasake bude jakar ta dauko wani dan karamin kwallba ta bude ta tsiyaya turare a hanunta ta murza ta shafe jikinta dashi tareda lumshe ido jin wani sassanyar kamshi na shiga jikinta. Jin ana kiran sallan mangari ba yasa ta shimfida dadduma tai salla takara gaggyara dakin ta wuce falo ta kwanta akan kujera tana kallon “Love is timeless” ko minti sha biyar batayi da fara kallon ba Bacci yay gaba da ita.
Suna fitowa daga bangaren ya kalleta ya shafo kanta”Auta na ki koma daki kije kiyi karatu, ba kince min gobe kunada exam ba?”Auta tadan zumburo baki “but Uncle B i missed yhu saisa nakeson na bika na kwana a part dinku” da kyar Barraq ya hadiye yawun daya taru a bakinshi yadan zaro ido”Okay Okay Auta naji amma yanzu kifara komawa part dinku revise ur book very well anjima saina zo mutafi ki kwana tareda mu “murmushi ya bayyana akan fuskar Auta tasaki Uncle B tajuya tace”to zanyi karatun sosai yanda bazan manta bako?” Barraq ya gyada kai good gurl tajuya takoma part dinsu. Yayinda Barraq yay murmushi yaja trolley hanunshi zuwa part dinshi. Ahankali ya bude kofar dakin wani sanyayyen ni’imantaccen kamshi ya ziyarci hancinta. Ya lumshe ido ya bude.
Maman Abd Shakur 😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*



87

Kafin ya daga kafa ya shiga falon ya maida kofa ya rufe. ware ido yayi hango abu mafi soyuwa agareshi kwance tana bacci cikin kwanciyan hankali. Karasa wa gaban kujeran yayi ya tsugunna yana kallon ta shimin ya zazzago yanda ta kwanta hakan yabashi daman ganin abunda yafiso gani, lumshe ido yayi da sauri jin wani irin shock nabin jinin shi. Ahankali yasa hannu ya shafa lallan dayaga an mata a hannu dan ya mugun burgeshi ga fatar ta yakara taushi ya daura hannu akan cikinta ya lumshe ido” My Baby Allah rayamin kai,baka taba gaisawa da Baban ka bako?”Yadan bude ido kadan “don’t worry yau dole na gaisa dakai” Ahankali ya dukar da bakinshi yakai saitin kunnen ta “My Rufaida ur Husby is back” turo baki tayi cikin barci takara muskuta wa cikin bacci. Barraq yakai ganinshi wurin abun dake kara tadamai hankali. Hanunta yadan daddaka ahankali”Baby na Baby na ” bude ido tayi kadan ta kalleshi ganin bature tsugunne agabanta yakara haske gashin kanshi ya kara kwanciya ga sabon farin gilashin da akamai yafi nada kyau da karbanshi yasa takarasa bude ido gabaki daya ta kalleshi murmushi ya sakar mata “tashi nine nadawo” tashi tayi zaune idanunta suka ciko da kwalla tana kallonshi “kaine ko yauma mafarki nakeyi?” Barraq yay murmushi “nine mintsile ni kiji” ya mike tsaye itama ta tashi takai hannu ta taba fuskarshi taji ta taba fuska kuka ya kufce mata Barraq ya bude hannu tafada kirjinshi tana kuka sosai,ya kwantar da kanshi a kan gashinta yana shakan kamshin dake neman sa hankalin shi ya gushe dago kanta tayi daga jikinshi ta zame jikinta daga nashi ta juya taji Barraq ya rike mata hannu”ina zaki? ” idanunta alumshe cikin karamar murya tace”fitsari nakeji sosai” saki ta yayi tajuya tana tafiyan ta mai daukan hankali daya kara birkita Barraq harta shiga bayin ya sauke ajiyan xuciya yafada kan kujera

Please Login or Register in order to submit comment