Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeji, gajeren hawaye daya zubo yadan goge sanan ya Danna key zai tada motar ya dago kanshi yana kallon titi. hango Barr Barraq yayi a tsakiyar titi yana dogara sanda ga motoci sun taho da gudunsu dayake express road ce, da gudu yafito daga motarshi ya fanfala da gudu ya bude muryarshi yace “B stay still,just stay where u are,am coming” yama motocin dasukai layi alamun su wuce duk suka wuce sanan ya shiga cikin titin,kamo hannun Barraq yayi suka tsallako sanan yama Barraq dake fadin Muzzamil kaine muryan ka naji, kakkyawan runguma Muzzamil yabashi tareda fadin is Me,I missed yhu B”.

Maman Abd Shakur😘
[5/4, 9:06 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

23
Suka kankame juna daga baya Muzzamil ya sakeshi yace “bari nakira Dad” ba’afi minti 20 da fadama Dad ba suka zo wurin shida polisawa,Dad yazo inda suke tsaye ya rungume Barraq tareda fadin”Alhamdulillah, Alhamdulillah,my little champion is safe and sound ” Barraq yay murmushi da kyar ya iya furta “Dad am hungry, yunwa nakeji sosai wlh”Dad yace” muje kaci abinci” yajuyo ya sallami poliswan tareda basu kudi mai yawa ya dawo ya shiga motar Muzzamil yajasu sai cikin garin Jigawa state,anguwar GRA suka sauke Dad suka fara saukewa a wajen daurin Auren,Muzzamil yace “Dad musai munje mun shirya zamu zo,nasanma Kawu yariga ya karbi auren”
Dad yace “ok nidazaran angama daurin auren zan tafi inada meeting” yabude jakar dake hanunshi yaciro wani dan karamin akwati yasama Barraq a hannu yace “your eyeglasses son,take good care of yourself” Dad din Muzzamil yakaraso wurin yanamishi magana yayinda Muzzamil yaja motar da sauri dan yasan fada Dad zaimai suka tafi hotel dinsu.

Dakin Muzzamil suka shiga, sai alokacin yabude akwatin yaciro glass din yasa, ahankali ya furta “Alhamdulillah” Muzzamil dake gefenshi yay murmushi yace”Ala kulli hal”zama Barraq yay akan gado, tashi yayi yace “Men yimin order din abinci,bari nai wanka” yawuce bathroom.

Fitowa yayi daure da towel daure a kwankwaso sai aranan nakare mai kallo,namiji ne kakkaura,fari tass yake jajjir kana ganinshi kasan yahada jini da turawa,yanada yawan gashi ajiki, ga gashin kanshi mai yawa baki sidik,lips dinshi Jane sosai idonunshi manya ne,amma kwayar idon wani irin blue ne, yanada tsayi jikinshi a mummurde.
Zama yayi yadau coffee dake gefen abincin da aka kawo mishi ya shanye tass sanan ya dauko Basmatic rice da aka dafadashi da cactus da green beans, yadanci badayawa ba sanan ya tura gefe Muzzamil yafito daure da towel shima Barraq kalleshi yace”ina kayan dazan sa?” Muzzamil yabude wardrobe ya dauko mai shadda fara iri daya datashi ya bashi Barraq ya kallai yace but… Muzzamil da sauri yatareshi yace”I know nasani,B bayason manyan kaya but kasamana just 4 today kaji” Barr Barraq yay murmushi ya tashi yasa kayan sunmai mugun kyau. Karfe 12:30 suka gama shiryawa,Muzzamil yace” B munyi mugun latti,maybe ma anriga ankai baby na,cos I arrange everything dazaran an daura aure za’a tafi da ita saboda cocktail night dazamuyi a Abj by 8 nadare” yadanyi murmushi “but lemmi call just to confirm”. Yakira Yusuf ya dauka yace”ango hope anga B?mu gamunan a hanya zamu wuce da amarya Abuja” Muzzamil yace”thanks Yusuf, gashinan tareda ni, muma yanzu zamu zamu taho muhadu later just handle everything”, sukai sallama da Yusuf ya katse wayan.

Yan kayayyakinshi na hotel din ya tattara yakai car,sanan yay settling bill yadawo daki yasamu Barraq zaune kan kujera ya lumshe idanu. dafashi dayaji anyi yasa ya bude ido yana kallon Muzzamil, Muzzamil yace”meke damunka,why all d sudden thinking?Tundazu na lura da hakan?”
Lumshe ido yayi ya bude sanan yatashi yajuya ma Muzammil baya ahankali yace “Muzammil kwana daya kacal nayi tareda ita,bansan taba bansan kamanintaba,but all I can tell u is,am in luv with Rufaida, ina sonta,nd is time to save d luv of my life” yana karasa fadin hakan yay sauri yabude kofa yafita,Muzammil ya mike tsaye cikeda mamakin abokin nashi Barraq in luv? Ahankali yace”abun mamaki” da sauri yabishi yatarar dashi a zaune a mota kanshi nakan kujera ya lumshe ido Muzammil ya zagayo ya zauna a mazaunin direba ya kunna motan sanan yakalli Barraq yace “ina mukayi B?” Barr Barraq ya kalli Muzzamil da dan gajeren murmushi yace”kauyen daka daukoni shinake so ka kaini,idan muna kan hanya I will tell yhu everything about her life” sanan yay sauri ya juyar da kanshi ganin Muzzamil na neman mishi dariya. Ya kadakai kawai yatada mota aranshi yace Barraq in luv,hmm wot a surprise!.

Maman Abd Shakur😘
[5/4, 9:24 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

24
Ganin boyewan datayi akan bishiya bashi zaisa yau afasa jefeta ba yasa ta sauko daga kan bishiyar mangoron tana kuka na fitan hankali da tulunta a hannu, tafiya take kowa na kauyen ana nunata ana cewa “ga wacce za’a jefe a kofar gidan mai gari anjima,ankamata da namiji suna lalata,namijin ma bature fa” ko kallon mazan da suke magana batayi ba saidai ma takara fashewa da kuka tawuce gida shiga gidan tayi da sallaman ta takarasa tsakar gida ganin Duduwa dawasu kattan maza su uku,Duduwa na zaune akasa suko suna tsaye bakake dasu hakan yasa tasaki tulun akasa,batasan lokacin da wani zazzafan fitsari ya tsiyayo yabi cinyar ta zuwa kasa ba.

Duduwa ta taso tazo gabanta tace “aikuwa gaskiyar su laminde,gako rigar maza nan ajikin ta, wlh yau saikin kusa mutuwa saboda azaba Rufaida” taja hanunta Rufaida tafara tittirjewa tana ihu dan “Allah Duduwa karki kaini gurinsu, mezasu min?” tana ihu haka Duduwa tadinga janta akasa ta kukkuje,Duduwa ta jefata tsakiyar mazan tace”Mujittafa gatanan ka daketa,kaimata bulala dari, kadaki bashin gyadar ka data batar, sanan kushiga daki dukanku kuyi duk abunda kukaga dama da ita,dama ai tadawo karuwa inkunga damama dukanku Ku ukun Ku afka mata a lokaci daya ba matsala ta bace”. Mujittafa yasa hannu yadaga Rufaida tsaye dake kuka sosai yana karemata kallo sama da kasa da wararran bakin nan nashi da ba hakoran gaba yace”ahh Duduwa ai wlh bama saina daketa ba,kawai afka mata kadai idan nayi nabar miki bashin gyadar ” Duduwa da sauri ta mike kaman mahaukaciya tace”ninace kuyi mata bulala dari,maza takebi” da sauri ta shiga daki taciro sharbebiyan dorunar ta mai baki 4 da wayan wuta tahadesu ta nannade tana mikama Mujittafa tace “gashi kacimin ubanta yanda bazata Kara neman mazaba” Rufaida tafasa ihu ta kankame jikinta tana kuka.
Mujittafa yace”haba Duduwa saikace ba jikarki ba zakice azaneta da wanan doruna haka”Duduwa ta nuna kirjinta” Ni Ni nace kadaketa da ita,kuma Rufaida ba jikata bace ban hada jini da itaba,yar tsuntuwace, asiri nake rufamata danama bari ta zauna Dani ina bata abinci,Ku cimin ubanta kuma kasheta Ni banda asara, kumata bulala dari sanan Ku wurgata bukka Ku afakama bunsurar” Mujittafa yakara washe jajayen hakoran yace “kwantar da hankalin ki Duduwa dole mu ladaptar da shegiyar da duka,sanan dukanku mu afka mata mu yagata,yanda bazata Kara marmarin bin mazaba”, Duduwa takara gyara daurin zani tace “yauwa haka nakeso” ta nuna sauran mazan tace “Ku dagata kujumai ita yamata dari abaya”.

Rufaida na ihu, kururuwa, kuka,shesheka, haka suka dauketa, daya ya rike hannuwanta dayan kuma kafafunta suka juyata, Duduwa tasama Mujittafa dorinar a hannu tace “yauwa cimin ubanta”. Mujittafa iya karfinshi ya zaula mata daya abaya, ihu Rufaida tasaki tawani bankare kaman zata fadi akasa saboda azaba, Duduwa tace” kuriketa da kyau yar yarinyar nan tafi karfin kune?,kaikuma Mujittafa haka ake dukan mazinaciya budurwa yimata da karfi”. Mujittafa yakara daddagewa yakara zubama Rufaida abaya Wanda saida rigan Barr Barraq ya barke ta baya, masu karatu Ni kaina kasa daurewa nayi nafito daga gidan dan duba wai har yanzu su Barraq basu isobane???.

Paka motan sukayi ahanya Barraq yaga wata yar yarinya dauke da tulu zata wuce yace”dan Allah baiwar Allah inane gidan Duduwa? ” yarinyar tajuyo tace $Chan cikin kauye ne” Muzammil yace “zaki iya shiga mota ki kaimu?” Da sauri ta bashe baki “eh,eh wlh zan kaiku, zaku Sani a gaban mota?” Muzammil yace “eh muje” da sauri taje tana bubbuga kofan ita adole zata bude Muzammil ya bude mata ta shiga ya kulle sukaja motar tana nuna musu hanya har kofar gidan Duduwa, yarinyar tace “ga gidan nan”, Barraq ya dago kanshi kirjinshi yace Dumm ganin yanda yan mata da matasa suka taru a kofar gidan ana leken cikin gidan, ahankali suke tafiya yarinyar na gaba suka kukkusa mutane dake kallonsu. tunkafin sukai ga zauren sukejin ihu Wanda yasa jikin Barr yafara rawa dan yagane ihun Rufaida ne, muryan Duduwa sukaji tana yauwa hamsin kenan, kai Mujittafa wanan na hamsin din bai shigeta ba,da karfi sosai zakayi sai ansake Mujittafa ya zuba mata daya lafiyayya Rufaida bakajin ihunta saboda muryarta ta dishe gabaki daya da sauri suka shiga gidan,aiko mutanen kofar gidan suka biyosu, jikin Barr yahau rawa ganin yanda kattai suka tale Rufaida suna duka ya kalli Duduwa, yarinyar data rakosu tace “ga Duduwa Chan ga Rufaida nan ana duka”, dunkule hannu Barr yayi Muzammil ya rikeshi amma ina ya fizge jikinshi yakarasa wurin dawani irin mugun zuciya Mujittafa ya daga dorinar zai shaulama Rufaida yaji an shakemai wuya,Barraq ya shakemai wuya da karfi kanshi na girgizawa tsabagen fushi, Mujittafa ko motsin kirki baya iyayi, Duduwa tazo tana rikemai hannu” Malan kai waye, mutum na hukunta jikata kazo ka shakemai wuya?” Hannu daya Barr yasa ya ingiza Duduwa ta zube a wurin, suko wayanda suka rike Rufaida suna ganin bature ya shigo ya shake wuyan Mujittafa suka saki Rufaida akasa suka arce aguje, Ganin Barr na shirin kisa yasa Muzzamil yazo yace “B control ur temper, just let him go” da kyar ya fizge hannun Barraq daga wuyan Mujittafa, Barraq ya fizge hannunshi daga hannun Muzammil yahau dukan Mujittafa Kota ina yana buga kanshi da bango hawaye na zuba daga idonshi, Muzzamil ya fizgoshi ya rikemai kafada yana jijjigashi “B I said is OK,control ur anger,Les just take her to hospital” Barr yasa hannu ya goge Hawayen idonshi yaje gaban Rufaida dake akife jini yabata bayanta, duka rigar ta farfashe saboda duka, ya dauketa chak ya daurata kan cinyarshi ya rungume ta sosai ya lumshe ido,hawaye yakara gangaro wa daga idanunshi.

ya mike ya dagata kaman tsintsiya a hanunshi yay hanyar fita da sauri Duduwa ta tashi kaman mahaukaciya tana dukan bayanshi” ina zaka kaimin jika? wayyo jama’a kutaresu masu Satan yara ne” haka suka fita daga gidan babu Wanda yay gigin zuwa inda suke, ya shiga bayan mota har alokacin yana rungume da ita,Muzammil ya rufe kofan yakoma gaba ya zauna sanan yatada motar, kalma daya Barraq ya iya fadi”kaisauri mu kaita asibiti,bata numfashi “.

Maman Abd Shakur😘


mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 21 to 24KAINE SIRRI NA 34 to 37 →
KAINE SIRRI NA 25 to 33
Posted on May 12, 2016 by mamanshakur
[5/6, 9:51 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

25
Wani asibiti dasuka gani a hanyar barin garin Jigawa suka tsaya,Barraq ya dauko ta suka shiga ciki, kin dubata sukayi waisai suntaho tareda police dakuma record din abunda yafaru dahar aka mata wanan mugun dukan. fitowa sukayi Barraq ya shigar da ita baya,ya kwantar da ita a kife saboda yanda bayan ke jini,ya kalli Muzzamil yace”mutafi Abuja kawai,zan kira family Doctor dinmu ” yakoma gaba ya zauna Muzzammil ya tada motar suka dau hanyar Abuja.

Wuraren 5 na yamma suka isa Abuja yace ma Muzammil” just kaini gida,kaisai kawuce kasan friends dinmu na nemanka yanzu” Muzammil ya saukeshi akatafaran harabar gidansu Barraq yadan mishi murmushi yace” thanks for everything, katafi they need you more than I” Muzammil ya kada mishi kai kawai Barraq ya fito ya bude kofar baya yasa hannu ya dauketa yay side dinshi da ita, ahankali ya kwantar da ita kan gado, yacire tazarcen dake jikinshi yafito daga bedroom din yafita daga dakin zuwa dakin Amma, da sallama ya shiga, Amma ta amsamai da murmushi tace”ahh mutanen biki har an dawo” yay murmushi yace “eh amma”, yadan Sosa kai yace”emm Amma dama damuna mota nakira Dr Faruk nacemai muhadu a gida yazone?” Amma tadanyi dariya tace”oh,tsufa yasoma kamani,abunda fa zan fadama kenan, yazo dazu yanama falon baki” Barraq yace “ok ina auta?” Amma tace “auta tatafi islamiyya” yace “ok”.

yajuya zai fita Amma tace “kaine bakada lpy?incedai ba nama kaci dayawa ba?” Ya girgiza kai tareda fadin “no Amma bani bane” yasakai yafita daga dakin, dakin baki yaje yasamu Dr Faruk a wajen suka gaisa sanan yace “muje ka ganta”. yana gaba Dr Faruk na baye dashi,har bangaren shi, bedroom yabude suka shiga kwance take rubda ciki saidai fuskarta na kallon hanyar kofa, mamaki yahana Barraq magana saidai yadaga hannu yana nunata,da kyar bakinshi ya iya furta “Ku..kur..ma! Dama kece Rufaida??” danshi kwata kwata sai yanzu ya lura dama fuskanta,sai yanzu ya kalli fuskarta. Dr Faruk dake bayanshi yace”lpy Barr naga ka tsaya ne” Barr yadan girgiza kai tareda fadin no,shigo kaduba bayan ya matsa ma Dr Faruk yakaraso cikin dakin Barr ya jingina da bango yay shiru yana mamaki to maizai sa farkon haduwarshi da Rufaida tamai karya? Maganan Dr Faruk yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula yace”amm Barr zan samu light shimi haka da karamin bowl” Barr yace “eh,I think so”. yafita zuwa shashin Amma kitchen ya shiga ya dauko karamin bowl saiya wuce dakin auta, wani Babban akwati daya kawomata lokacin dayaje Russia ya dauko ya bude wani shimi na mata mara nauyi mai dan girma ya dauko yafito daga dakin yakoma shashin shi, ya shiga bedroom din yabama Dr Faruk ya karba,almakashi Dr yasa ya yaga rigan dake jikinta daga sama zuwa kasa ta baya, bayanta gabaki daya ya bayyana, duk tabon bulala sai fitar da jini suje, Dr Faruk yajuyo ya kalli Barr yace”dis is child abuse, waye ya daketa haka 4godsake?”Barr yay folding hannu a kirji ya sauke ajiyan zuciya ahankali yace”her Grandma, labarin nada tsawo” Dr Faruk ya girgiza kai kawai yabude jaka ya ciro wayansu gora guda biyu da allurai biyu ya yanko auduga da almakashi ya tsoma audugar a cikin ruwowin daya hada a bowl sanan yakai bayanta yadaura kan ciwon ihu tasaki tareda kama zanin gadon da karfi tana shure shure da kafa, Barr ya lumshe ido, ganin bazai iya daurewa ba yasa yafita daga dakin ya zauna akan kujera ya dafe kanshi yana huci, jiyake kaman ya dauke mata ciwon.

Maman Abd Shakur😘
[5/6, 10:06 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

26
Fitowar Dr yasa ya dago kanshi ya kallai tareda fadin “hw far Dr?akwai any ciwo?” Dr Faruk yace “no any ciwo,kawai yarinyar na bukatan hutu tareda abinci mai kyau,yanzu tana bacci zata iya farkawa yau, hala kuma sai gobe ko jibi ma self,cus nabata allurai dazasu sa jikinta yay relax” Barr yace “to thank you” yamikamai hannu sukai sallama yatafi. fadawa kan kujera yayi tareda fadin “why Rufaida? Maisa kikaimin karya? Duda kin ganni a kauyen Ku baki taba nuna kinsani ba”, da sauri yace “to kodai shine d reason y take yawan cemin inada kirki? Ko saisa ta taimake ni cus nima nataba taimakon ta?” Ahankali ya furta yess hakane yanzu na samamma tambayata amsa. Dan murmushi yayi yace “in sha Allah wahalar ki takare,is a promise Rufaida, saina share miki hawaye, iyayenki dakika rasa saina maye gurbinsu” lumshe ido yayi tareda gyara kwanciya akan lumtsatsiyar kujeran yadaura hannu kan zuciyar shi saikuma yarufe ido da sauri yanadan murmushi daban gane maanar shiba.
Ringing din dayar wayarshi daya bari a gida yasa ya mike a kasalance ya jawo wayar dake kan center table,ganin sunar daya bayyana a screen yasa yay murmushi ya dauka harda daga kafa yace” mana!I missed yhu” daga dayan bangaren naji matar da yaren turenci tace” my baby I missed you ya kk?” Yay murmushi yace “mee too mummy ya jikin ki? Hope kina zuwa check up dinki?” Tace “yes ina zuwa”. bayan sunyi dan maganganunsu na da da uwa sanan ta magana cike da damuwa tace ” son har Yanzu bakaga yarinyar dakace zaka kawomin ba,nagaji da zama nikadai no grandson, no in-law, inason wani dazan kula dashi and pamper with luv”murmushi yayi yace”Mummy na ganta,but batada lpy”arude ta tambayi maiya sameta? ya sanar da ita komi kan Rufaida, kuka sosai Mum din Barraq tai a waya da kyar ta iyayin shiru sanan tace”son I beg yhu duk yanda zakayi kayi kamata visa yau tomorrow ka kawomin ita,I need to shower her with my luv,zan zame mata uwa data rasa,banga Rufaida ba amma inason Rufaida, banga Rufaida ba amma Rufaida tadawo yata,just try son, ka kawomin ita gobe,I need to take good care of her” ajiyar zuciya yayi sanan yace”ok mummy, in sha Allah gobe zankawota” sukai sallama ya katse wayan sanan yatashi ya shiga Bathroom yay wanka anan bayin falon,yawuce bedroom dan dauko kayan dazaisa yatafi yaga ko zai iya samarmata visa, bude kofa yayi adaidai lokacin tana fadin “Umma tsuntsun,zai kamani,wayyo Umma yana Jana yana bina”.. Da sauri yakarasa cikin dakin ya tsugunna agaban gadon yana hura mata iska a fuska tareda shafa zufan daya gani a goshinta,ya saka hanunshi cikin nata yana kallon fuskarta dayay fayau, gashi gashin gefen fuskarta sun kwanta lub tai wani irin simple kyau, ahankali yakai bakinshi kan goshin ta ya sunbaci goshin tareda sa hannu ya share wurin yana murmushi yana kallon fuskarta yace” wani tsuntsu ke damun min baby na? Koma wani tsuntsu ne just go, yabarmin baby na tai bacci” ahankali yaga ta sauke ajiyar zuciya tacigaba da bacci tareda kankame hanunshi sosai.

Maman Abd Shakur😘
[5/10, 5:55 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

27
Ahankali ya zame hanunshi daga nata yadau kayan dazaisa yafita daga dakin yaje falo ya shirya tsaf ya fesa turare, sanan yadawo dakin ya tsaya a gaban gadon yana kallon ta hanunshi ya zura cikin aljihu ya dauko wayarshi ya tsugunna ya dauketa hoto yana mai murmushi ahankali yace”sleeping beauty, maybe I can use it as her passport”. yadau car keys yafita daga dakin.
******
Bayan kwana biyu.

Yau takama litinin,fitowarshi daga kotu kenan shida PA,sai murmushi yake,kokari press suke suga sunmai yan tambayoyi danyau ya kayar da Babban mai saida miyagun kwayoyi,yatona mishi asiri shida mukarraban sa inda aka kaisu gidan yari amma baida lokacin amsasu dan tafiya gareshi yau. Tun kafin yakai wurin mota aka budemai ya shiga da sauri yana duba agogon hanunshi tareda dafe kai”Lord! Nakusa lattin flight to Russia ” ya kalli bodyguard dake tuki yace” kai sauri 5 flight dinmu zai tashi and dis is already 4:00pm”.
Suna isa gida yafito daga mota, yana cikin sauri yaje dakinshi yaji an fado bayanshi ana “uncle B oyoyo”, juyota yayi yana murmushi yaja kunnen ta “auta bakiji ko”, tadanyi Kara ya sake kunen, rikemai hannu tayi suka cigaba da tafiya tana bashi labarin school yau, saida yakai bakin kofa ya tsaya. auta ta kalleshi, yay mata murmushi yace “yauwa Auta oya tafi kinji anjima zanzo, ki gaida Amma” ta noke wuya tana murmushi. yadan daure fuska tareda fadin “tafi mana”tai zuru-zuru tana kallonshi tace” uncle B kullum kullum yanzu baka bari nashiga dakin ka why? Abu kake boyemin ko?amma ai kace ni kawarka ce ko? Kuma ina fadama all my secrets” tabashi tausayi dakuma dariya yadan rage tsawo tareda sa hannu ya share dan guntun hawayen daya zubo a idonta yana murmushi ya girgiza kai yace “kinsan banason kuka ko?” Ta dagamai kai, yace” ok, ai mun riga mun kulla fadama juna secret, banason ki shiga dakinne cus is too dirty, kuma nasan bakison datti ai,oya tafi anjima zansa a gyara sainakira kizo kinji” Ta girgiza kai tareda juyawa dan tafiya shikuma ya bude kofa ya shiga dakin.

Auta na ganin ya shiga tajuyo tana dariya,”ai wlh sainaga yanda dakin Uncle B yay datti,dama Amma tace dakinshi baya datti wai yanada tsafta, yau sainaga dattin dayayi ” tasa hannu ta bude dakin a ahankali ta shiga, ganin bataga datti a falon ba yasa tai dariya tareda kwafa, tayi hanyar bedroom dinshi tasa hannu ta bude kofan a hankali dan karyaji motsinta, ganin mace a kan gadon Uncle B bayanta a bude duk shaidan bulala dasukai wani iri ba kyan gani ga gashin kanta duksun barbasu akan gadon hakan yasa Auta tasaki ihu tareda kankame jikinta.

Maman Abd Shakur😘
[5/10, 6:19 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

28
Da sauri B yafito daga bathroom yana kallon auta dake ihu, jikinta yahau rawa ganinshi rai abace,yana tsaye inda yake yace mata “zonan” kuka tasa sosai dan tasan yau saita gane kurenta, tafara sharban hawaye tana “yakuri Uncle B, wlh zan dinga jin magana, bazan karaba dan Allah karka daken”, fizgo hanunta yayi takara fasa ihu tana” kayakuri,plz-plz-plz!” tausayi tabashi sosai,hakan yasa yafasa dukanta yace “wuce kitafi kafin na bata miki rai” juyawa tayi ba musu tafara tafiya hartakai kofa tasake juyowa tana kallonshi yace “what?” tace “Uncle B batada lafiya ne?”Tai maganan tana nuna Rufaida dake kan gado, daga mata kai yayi shima tareda kallon Rufaida dako numfashin kirki batayi, Auta ta girgiza kai “Allah sarki,Uncle indan je intabata?” Ya dade yana nazarin ta kafin ya daga mata kai, da sauri auta taje gaban gadon ta tsugunna ta kama hannun Rufaida tana kuka ahankali saboda yanda taji tabata tausayi sosai tasake juyowa ta kalli B tace”Uncle B baka kaita asibiti ba,ciwonta nata jini,kaga yama bata zanin gadon,ka kira mata Dr Faruk,wlh ina sonta Uncle ” Barr yakaraso wurin shima ya tsugunna yakama dayan hanun Rufaida yarike sanan yace”banason nasake kiranshi dan banason kowa yagane tana gidanan, yau zan kaita wurin Mummy a Russia, za’a kaita asibiti achan” .

Yasake kallon Auta dake kallon Rufaida tana hawaye,tana hura iska akan ciwon yace “Auta”, tajuyo ta kallai yace” karki fadama Amma kinga Mara lafiya adakina, is our little secret kinji?” Tasa hannunta a harshe tareda fadin “I promise uncle “. ya shafa kanta tareda fadin “good Gurl, kinsan wheelchair din Daddy dayay amfani dashi lokacin da baida lafiya?” Ta girgiza kai da sauri tace “eh nasani,ai yanama cikin store dinmu nan Amma ta ajiye” yace “yauwa jeki dauko min” tafita da gudu kafin ta shigo yagama shiryawa, tana shigowa da wheelchair din ta ajiye tazo kusadashi ta tsaya tace “Uncle yanzu zaku tafi airport? ” yace “eh”, ta kalli Rufaida sanan ta kalleshi tace “but ai wanan kayan jikinta sun baci da blood, ka chanza mata wasu” yadan tabe fuska yace”auta Ni ban iya samata kayaba, abarta ahaka kawai intaje wurin Mommy tasa mata” yay maganan kaman wani Yaro ,auta tace “laaa nidai na iya, bari na dauko mata wayanan kayan dakasiyomin manyan nan, Wanda sukamin yawa”, kafin yay magana harta fita daga dakin da gudu ko minti biyu batayiba ta dawo dauke da wani Jan dogon sket da shimi baki very light, saidan karamin hijabi da bathroom slippers mai kyau baki shima.
Ta ajiye kayan kan gado Uncle B ya matso kusa da ita yace “auta keda Amma kesa miki kaya balle har ki iya sama wani?” Buga kafa tayi a kasa tace “ai wlh na iya,ni kawai dagamin ita ta zauna saina sa mata” yay kwafa tareda fadin “ok”, ya dawo kan gadon ya dago Rufaida ahankali ya zaunar da ita akan jikinshi yace “oya samata”, Auta ta tsaya agabansu tana kallon fuskarshi yace “what again?” Tace “to Uncle baka rufe idoba, ba Amma na tace babu kyau babban namiji ya kalli jikin wata ba…” bata karasa maganar ba ya kulle ido da sauri. Auta tasa hannu tacire shimin dake jikinta da, ta samata Wanda ta dauko,sanan tace “nagama saura sket” ya kwantar da ita duk idonshi arufe Auta tasamata sket,tasa mata karamin bakin hijab, da slippers sanan tace “to bude idonka kagani”ya bude ya kalleta yaga tamai kyau Sosai murmushi yayi ya

Please Login or Register in order to submit comment