Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maman Abd Shakur😘

[7/14, 21:07] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
74

Alh ya rike mata hannu da sauri, Dad yatashi daga kan sofan dayake Alh ya daurata akai, kowa ya mike tsaye,Amma ta dauko goran Eva water mai sanyi ta mikama Alh ya bude yaba Umma tasha kadan tana Nuna Rufaida da hannu. Barraq dake dauke da yaron su a hannu ya juya dan ganin abunda Umma ke nunawa ganin Rufaida yasa ya dawo da kallonshi garesu a natse yace”Umma itace matata Rufaida,mesa kike nunata?” Alh ya mike tsaye ya share dan guntun hawayen idonshi”itace Rufaida dana fadama case dinmu akanta,wlh yarmu ce! Rufaida yar muce! Dad, Barraq,Amma da Mum suka hada baki alokaci daya sukace “what?! Umma ta daga kai cikin kuka ta kallesu tace “wlh yarmu ce,Rufaida baby na,i missed u” ta tashi zataje wurin gadon Barraq ya tsaya agaban ta “don’t touch my wife Ma,imma turoku akayi kutafi,inma set up ne to it won’t work,cuz Rufaida iyayen ta sun mutu, a minna parents dinta suke aiki amma asalin su yan kauyen gujungun ne na jahar jigawa, gini yafado ma iyayen ta ,nida kaina naje na karbo kudin da Gov. Sukaba duk family da ginin yafado musu,so yhu guys should cut d drama,I respect yhu alot Alh,ku barmin matata tahuta,why soo much hate??kowa yatashi Rufaida, everything Rufaida, wani laifi yar yarinyar nan tayi dat deserves all dis wahala?? Yhu guys should get out of dis hospital before I call security”. Ya mikama Alh yaron. Umma ta tsugunna tafashe da kuka sosai Alh yace”wlh wlh Barraq yarmu ce,itace Rufaida damuke ta nema”. Barraq cikin daga murna yace”I know is all a setup,idan itace Rufaida ku maisa baka taba nunamin hoton taba duk zuwana gidanku? “Alh yay shiru yakasa magana ga yarshi amma ana karyata shi, da kyar ya tattaro karfinshi yace”dan girman Allah ka yarda damu Barraq, wlh yarmu ce,ban taba tunanin nunama hoton taba but look inada hoton Rufaida a cellphone dina” Barraq yace” I don’t want to see, just get out of dis hospital now” Idanun Barraq yay ja dan duk atunanin shi wata kullalliyar aka kullo. Umma takara fashewa da kuka takama kafar Mum tace”Hajiya wlh yarmu ce,Rufaida nace, kice yabar mu muganta”. Mum ta girgiza kai “Hajiya batar fuska kikayi,Rufaida nan iyayen ta sun rasu, dan Allah kutafi murabu ta arziki inma turoku akayi mun gane bazaiyi aiki ba kutafi” Umma taki tashi, Alh yaki matsawa yaron hanunshi na kuka sai alokacin Dad yay magana “Alh wanan ba itace Rufaida kuba, kutafi kafin akira security bamuson tashin hankali”. Barraq ya daga murya yana kiran security! Security! Umma takara kecewa da kuka yaron hanun Alh ya fashe da kuka, hayaniyan dayacika dakin da koke-koke yasa Rufaida tafara motsi, kafafun ta suka fara rawa ahankali tace”wayyo Mummy,Uncle B Duduwa “da sauri kowa ya juyo inda take Barraq yakarasa wajen da sauri yarike hanunta ahankali yace”Baby ni ne, open ur eyes” ahankali ta bude ido tana ganin Barraq ta kankameshi tana kuka sosai “zata dakeni,plz kace karta daken Uncle B, banason duka ” Barraq ya cireta daga jikinshi yasa hannu ya share mata fuska yace”Hey!calm down,look nikadai ne sai Mummy da Daddy dakuma Amma,babu wanda zai dakeki,bazan kara bari acutar dakeba” da kyar ta iya maimaita abinda yace saboda zafin dataji cikinta namata tace”Mummy?” Barraq ya girgiza Mata kai” yes!mummy tazo tun jiya” matsawa gefe yayi Mum ta bayyana agaban ta tana murmushi,Rufaida ta bude ma Mum hannu tanason ta rungume ta, da sauri Mum ta rungumeta. Sai alokacin idanun Rufaida ya sauka kan wata yar mata a tsugunne idanunta hawaye shabe shabe,sai kallonta take da wani mutume yana dauke da yaro shima sai kallonta yake. ta dago da kanta daga jikin Mum tana kallon mutanen dabatasaniba, Mum da kowa na dakin yabi Rufaida da kallo. Umma ahankali takara matsowa jikin gadon ta daga hannu tana kokarin taba Rufaida da sauri Rufaida ta shige jikin Mum tadanyi ihu “Mummy wacece wanan?maisa take kuka?maisa itada wanchan suke kallona? ” kafin Mum tai magana Umma tarigata tace”Rufaida nine Mummy ki, Umma,kin manta ni Rufaida? ” Umma ta tashi da sauri tariko hanun Alh tace “kinga ga Daddy ki shima kin mantashi??” Rufaida ta girgiza kai “nidai kidena kuka,Ga Mummy na nan,asalin Amma na da Abba na sun rasu”idanunta yakawo kwalla Barraq yace”look sir kufita daga dakin nan,kunga bata da lpy,kundai ji tafadi muku da bakinta bata sanku ba”. Saida aka kira security sanan Alh da Umma sukabar asibitin. Da kyar Alh ya kwantar ma da Umma hankali yace”Alhamdulillah ma munganta,mun kuma san tana hannu nagari masuji da ita,masu sonta,matsalar da tambayar daya ce tak! maisa Rufaida ta manta damu??Maisa? “. Maman Abd Shakur😘

[7/14, 23:04] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
75

Da kyar suka kai hotel din dasuka sauka, Abba yakira kanninshi dasuke kano ya sanar dasu anga Rufaida,amma anhana su ita, kowa yahau murna, sukai alkawarin zasuzo gobe da sassafe Abujan, ayita a waje dole suji daga garesu. Yakira amintaccen mai gadinshi dayake yanada makullin gida yace ya shiga dakin Rufaida ya bude wardrobe dinta ya kwaso albums din hotunonin su duka da kayan makaran tarta da jakar makaran tarta yahada su waje daya gobe zai turo wani abokinshi akaishi Airport yazo Abuja yarike katin zaben shi dan zaa tambaya. Mai gadi ya amsa da to Alhj ya shiga gida yahada komi tsaf dan shirin zuwa Abuja gobe sai murna yake zai shiga jirgin sama. Yau Babbar rana ce ga Alh,Umma da yan uwan su harda mai gadi. Misalin sha biyu na rana kowa ya iso daduk all evidence da shaidun da suka nuna cewa Rufaida yarsu ce. Manyan motoci biyu suka cika aka tafi asibitin dashi. Koda suka isa ba’a barsu sun shiga ba wai ba visiting hour bane. suna tsaye saiga Dad yazo zai wuce Alh yamai magana ya tsaya suka gaisa sanan sukaja Dad gefe daya tiryan tiryan yayan Alh yama Dad bayanin komi tareda nuna mishi hotunan Rufaida tun tana karama har girmanta. Da kyar suka samu Dad ya yarda dasu saida shima tashi tambayar daya ce “maisa Rufaida ta manta dasu,maisa ta manta da iyayen ta? ” Sai alokacin kanin Alh yay magana yace”inaga aljanu ko sammu ne suka shafi Rufaida, dan mutum baya manta iyayenshi haka inbadai matsalar kwakwalwa yasamu ba,nataho da magani da addu’oin dazan mata in sha Allah zamuji gaskiyar abun,komi zai warware”. Dad yace “shi kenan bari nakira muku Barraq,saina nemi sallama wurin likita dan mutafi gida ayi komi achan”. Sukaima Dad godiya sosai. Dad ya shiga dakin ya tarar da Barraq naba Rufaida tea tana sha ahankali Mum na bandaki,Amma ta tafi gida yomusu abinci da sauri Rufaida ta kawar dakai ganin Daddy ya shigo murmushi dad yayi ya kalli Barraq “ana nemanka awaje son” Barraq ya amsa da to. Dad ya juya yafita yacigaba dabama Rufaida tea,ture cup din tayi tadan ya mutse fuska “am okey” Barraq ya ajiye tea agefe “saina miki dure tunda bakicin abinci yanzu”. tashi yayi daga kan gadon ya tsugunno yama goshin ta kiss “I luv yhu Baby na” ya juya zai fita harya bude kofa ya tsaya yana kulle boturan rigarshi yaji muryar Rufaida tace”Uncle B” da sauri ya kalleta “Naam Baby na” hannuwan ta tarufe fuskarta dashi”I love you” kulle ido yayi ya bude,kafin yasa hannu ya mintsili kanshi so ba mafarki yakeba Ahankali yace “mekika ce??” Tajuyar dakai tana murmushi Mum tafito daga bayi tsayawa yayi agaban kofa yana kallonta Mum na zama agadon Rufaida ta tashi da kyar ta rungume Mum fuskarta na kallon Barraq ta bude baki ta Furta mai I love you, lips dinta ya karanta yagane abunda tafada. fita yay daga dakin yana M urmushin da saida duka hakoranzhi suka bayyana. Koda yaga su Alh ne yajuya zai koma “Umma tace dan girman Allah Barr ka tsaya” bai musu ba ya tsaya, ahankali kowa ya gabatar mai da iya gaskiyar su da hotunan, yakuma kara ganin kaman da Rufaida tayi da Rayyan kaninta but still yace “Alh mu shiga asibitin nan ayi DNA test,Dad dake karaso wa yace”Son shiga mota mutafi gida”Barraq ya juya yaga Amma riqe da Rufaida dake tafiya da kyar Barraq yace”But Dad…”Dad ya katseshi “No but Barraq,is time to know d actual Truth,is time dazamu san maisa dat old woman hate Rufaida sosai,less go” kowa ya shiga mota Rufaida na jikin Mum tana numfashi da kyar ita yanzu tsoron mutane take bana wasaba. Maman Abd Shakur😘

[7/14, 23:15] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRINA* 76



Babban falon Daddy aka sauke bakin. Dad,Mummy,Amma,Barraq,sai Rufaida daya rike mata hannu gam kamar zata gudu. Bangaren su Alh kuwa daga shi sai Umma,sai Babban wanshi,da kannenshi biyu da mai gadi agefe. Ba abunda sukeyi sai kallon Rufaida. Rufaida ta rike hanun Barraq gam kaman za’a saceta. Dad ya kalli kanin Alh yace”Bismillah” Mutumin ya kalli Rufaida yace “zo,Al Qur’ani mai girma zan karanta akanki” Rufaida ta rike Barraq gam tana kuka,Barraq yakara riketa shima bayason taje danshi bai yarda da abinda zasuyi ba. Dad ya kalli Rufaida yace”Daugther na” ta kalleshi yace “jeki”. Da taimakon Barraq ta iya tashi yakaita gaban malam ya zaunar da ita, sanan ya koma wurinshi ya zauna mutumin yay isti’aza da basmala cikin kira’a mai dadi, cikin kuka Rufaida tace “Dan Allah tsaya,wlh ni banason karatunan dakake min, yana tadamin da hankali” mutumin yacigaba batare daya saurareta ba. Rufaida takara fashewa da kuka tana mikama Barraq hannu jikinta ko ina na rawa, Barraq yay kaman zai tashi Dad ya ballamai harara, yakoma ya zauna karatu yay karatu ayoyin Allah sun soma ratsa kan Rufaida ahankali ta sulale ta kwanta akasa flat idanunta suka kankance, Barraq ya zabura ya tashi Mum ta zaunar dashi ta rikemai hannu. mutumin ya kalli su Dad “dama nace da abunda akama yarinyar nan,sammu ne yanzu kuma zan karyashi da izinin Allah, sammun zai koma kan wanda yamata” kowa yay shiru mutumin ya dauko jakarshi ya dibi garin tafarnuwa dawani bakin magani da garin habbatus sauda ya hada yasama Rufaida abaki, ya diga ruwan zamzam so uku abakinta yahade mata bakin ya rufe ya matse hancinta nadan sakanni saida yaga tahadiye sanan ya saketa “Rufaida! Rufaida! Rufaida! Ki mantasu arayuwar ki! Ki manta Abban ki da Umman ki, ki shiga duniya karku sake haduwa…”Barraq ya mike”Dad do something I hate all dis stuff,wot is he doing to her? Wot is she saying?” Dad ya nunamai kujera alamun ya zauna yako zauna. Chan kuma saita shiru. Tana buga kanta akasa sosai Barraq ganin bazai iya juran ganiba ya chusa kanshi a tsakakanin kafafunshi yana goge hawaye. Dakin yay shiru Rufaida ta dena abinda takeyi. Mutumin ya cigaba da rera karatun Al Qur’ani a gefenta. Tadau minti talatin ahaka kafin ta bude idanunta ta kalli saman dakin. Saikuma ta zabura tamike tsaye har saida mutanen dakin suka tsorata, tadanyi kara ta rike cikinta”auch” idanunta arufe tace “Umma gari yay haske baki tashen daga bacci ba,uh cikina na ciwo,banasom nai lattin school munada test yau” da sauri Barraq ya daga kanshi ya kalleta. Barraq yataso yazo kusa da ita”Baby na are yhu ok?Dr yace cikin zai rage miki ciwo nan da gobe” ahankali ta cire hanun daga cikinta ta bude idonta ahankali tana kokarin ganin fuskar husky muryar dayay mata magana yanzun nan. Sauke idonta datayi akan wani kakkyawan bature,ga gashin baturai,ga wani hadaddan farin gilashi a idonshi yana mata murmushi yasa ta juya tana karema mutanen dakin kallo,waige waige tafara hango Umman ta datayi akan kujeran karshe rike da karamin yaro yasa tajuya da sauri tana rike da cikinta takarasa wurin tafada jikin Umma tariketa gam tana kuka, Umma ma kuka. Da karfi tace”Umma kalli-kalli”tace “auch Umma cikina ciwo yake” sanan ta nuna Barraq,Mummy,Daddy da Amma “Umma suwaye wayanan turawan?” Barraq ya zaro ido yana kallon ta, yatako zuwa gaban kujeran datake ahankali yace”Rufaida ” murguda mai baki tayi ta kalli Abban ta tace “Abba wai waye wanan baturen? Baffa a ina kuka samo turawa?”. Maman Abd Shakur😘



mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 70 to 76KAINE SIRRI NA 88 TO D END →
KAINE SIRRI NA 77to87
Posted on July 25, 2016 by mamanshakur
​[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
77

Kafin Umma tabama Rufaida amsa takara jeho wata tambayar “Umma maisa naga duk sunsa gilas?Umma daga ina zukazo? “Tafadi maganar tana kallon fuskar Mum. Umma takasa magana tarasa maizata yi awanan gaban farin cikin ganin yarta,harta tunasu ko bakin cikin ta manta wayanda suka taimaketa, ciki harda abin kaunar ta,mijinta. Umma takara kecewa da kuka, Alh yay jarumtar yin magana ta hanyar kallon kanin nashi yace”Young malam meke faruwa? ?explain kasamu aduhu? Maisa ta manta mutanen dasuka taimaketa da mijinta?” Mutumin ya gyara zama yace”yaya amma Rufaida sammu ta manta iyayen ta gabaki daya,da rayuwar ta nada,ta shiga duniya kaman yanda kukaji tafada dazu, duk wani Rayuwa datayi bayan ta bar gidanku tayishi ne bata cikin asalin hankalin ta,tana cikin sammu,saisa ta manta su,amma zata tunasu nan bada jimawa ba,tashin ta yanzu taganine kaman daga bacci ta tashi,rayuwar datayi kaman mafarki ne,sai ahankali zata dinga tunasu kadan kadan,kubata lokaci zata warke duk zata tunaku,wanan bawata babbar matsala bace” Rufaida data kwantar da kanta ajikin Umma ahankali tace “maganar wa Baffa yakeyi Umma?” Umma tadan shafa kanta “zan fada miki anjima”. Sai alokacin Mum tai magana “nakasa gane dis whole thing,suyawe iyayen Rufaida dahar suka mutu?ita Duduwa data kira kanta kakar Rufaida who is she then??a ina suka san Rufaida?”. Dad yay gyaran murya” d only person dat can answer that question is Duduwa! Barraq cikin fushi yace”babu wacce zai kira matar nan gidanan, juyamin kwakwalwar mata sukayi ,dey did something to her” yakama kwalar malamin “mekama Rufaida?”kowa na falon ya mike tsaye Dad ya rike hannu Barraq “son let him go,ka sakeshi,ba abunda yama Daugther,I said let him go” da kyar Barraq ya sakeshi idanunshi sunyi ja Dad ya zaunar dashi yadawo yana bama malamin hakuri wanda ya nuna bakomi. Dad yakoma kan Barraq yana mai fada”nasha fadama idan rai ya baci kar hankali ya gushe,idan kai tunanin komi everything make sense zaiyu yaron Duduwa ya tsinci Rufaida ya dauketa saisa ma Duduwa hate her soo much,understand and get it once rayuwar da daugther tayi damu tayishi ne kaman amafarki,she will remember us amma ba yanzu ba” Barraq yay shiru ya daura kanshi akan cinyar shi,yarasa mezaiyi yaji dadi,zuciyarshi na mugun zafi,kanshi kaman an zuba garwashi” Karan wayar dayaji yasa ya dago kanshi ahankali suka hada ido da Rufaida harara ta balla mishi saboda taji haushin yanda ya shake baffan ta. Jin maganar Alh yasa kallon yakoma kanshi arude yace”garin yaya?ganinan dawowa,kuhadu ku kamata a kulle yanda bazata fitaba” ya katse wayar tashin hankali ya bayyanah karara a fuskarshi Umma ta fara tambaya “lafiya Alh?” Share gumin kanshi yayi yace “mai gadin gidan hajara(kishiyar Umma) yakirani wai Hajara ta haukace, tafito sai raye raye take tana cire kaya tana kiran Rufaida,ankasa kamata dole natafi Abuja yanzu” ya kalli Dad yace”Alh dan Allah inason keban cewa da yan uwana da Rufaida Alh” Dad ya washe baki “to ba matsala”. Yatashi Mum da Amma sukai gaba Barraq yaki matsawa daidai danan da chan Dad ya rike hanunshi suka fita daga dakin. Alh ya fuskanci yayan shi yace”yaya inaso ku saurare ni, munga Rufaida shine kuma abunda muketa addu’a akai ko?”Suka amsa da haka ne. “Amma da muka ganta mun tarar da ita a matsayin matar aure, kuma ga miji salihi mai taimako ga tausayi maikuma sonta”, tashi yayi ya matsa kusa da Umma dake kallonshi ya rike hanunta “abunda nake shirin fada nasan zaimiki wuyan yi, amma inaso ki duba mutuncin mutanen nan, dakuma abunda sukama yarmu na nuna mata so,kulawa,suka aurar da ita ga miji nagari” yadanja numfashi kafin yacigaba”Alhamdulillah mun godema Allah daya bayyana mana yarmu, dudda Rufaida bata tunasu ba bazaisa mutafi da itaba,bata karkashin mu yanzu,tana karkashin mijin ta, hukuncina shine zamu barta anan mutafi madinga zuwa dubata” yakarasa maganar yana kallon Umma dake hawaye. Ahankali ta girgiza mai kai,”na yarda da abunda kace na amince,bazamu taba karbar Rufaida daga hannun Barraq ba” ya kalli Yayan shi shima ya nuna amince warshi. Kowa na dakin ya nuna amincewar shi. Alamu Alh yay ma Umma da ido. Umma ta share hawayen ta tajuya ta kalli Rufaida tarike mata hannu tace”Baben Mama” Rufaida ta kalleta Umma tace”inaso ki zauna a gidanan da wayanan turawan zamuje gida Anty ki batada lpy zamu kaita asibiti kinji” Rufaida ta lankwasa kai”Uhm Uhm Umma nidai bazan zauna dasuba, bana sonsu banason gidan,inason naje school gobe tunda nariga nai latti yau ” Umma ta mikama Alh Rayyan dayay bacci ta juyo ta fuskanci Rufaida tace “Bebin mama inaso ki saurare ni kiji abunda zan fadan miki,…”Umma tafadin ma Rufaida komi,kan Rufaida yay chaji kalma daya kwakwalwar ta yafi rikewa “ke matar aure ce!matar Barraq!. Kanta ta chusa a cinya tafara rafka uban kuka bana wasaba, “wlh bazan yardaba,Allah bana sonshi, mutumin daya shake wuyan Baffa yanzu nan wlh bana sonshi,nibazan zaunaba, kuzan bi muje gidan mu”. Yayan Alh yatashi yazo gabanta yace”Rufaida! Ya daga mata tsawa,jikinta yafara rawa dantana mugun tsoron Baffa Yaya yacika fada,ga fushi.”idan naji kin kara cewa bakison Barraq saina karyaki,young Malam yace zaki tuna komi so dolenki ki zauna dasu,yanda kika zauna dasu da haka zaki zauna dasu yanzu,shashanci banza kawai, yanzu bamu da iko dake sai yanda mijinki yace, muba butulu bane da zamu goya miki baya ba,bazamu taba godema mutanen nan tahanyar tafiya dakeba kinajina” ta dagakai da sauri tana zaro ido. ya kalli mai gadi yace”kirasu mungama” mai gadi yafita dan kiransu. Maman Abd Shakur 😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
78

Shigowa su Dad sukayi kowa yanemi wuri ya zauna Barraq idanunshi nakan Rufaida dayaga tana kuka sosai kaman yay magana saikuma yay shiru ya dukar da kanshi akasa. Alh yay gyaran murya yace “Alh zamutafi” da sauri Barraq ya dago kanshi ya kalli Alh. Alh ya sakinma Barraq tattausan murmushi kafin ya juya ga Dad yace”mun gode da kula da yarmu dakukayi da zaba mata miji nagari dakukayi nagode Alh. Babbar gaisuwata da fatan alheri gareka Barr Allah yakara daukaka ka yabaka zuri’a nagari, nagode da bama yata so da kulawa”. Barraq ya sadda kanshi kasa,Alh ya cigaba “ga Rufaida nan, in sha Allah zamu dinga zuwa dubata,Allah ya saka muku da alheri” ya juya ya kalli Rufaida yace “kima mijinki da iyayenki biyayya, inhar aka kawomin karanki saina saba miki kinajina ko?” Ta gyada kai tana share hawaye. Dad yay magana “bazaku tafi da ita tadan zauna daku ba?munsan kuna bukatar yarku itama haka,abun zai mata yawa ta warke kuma tacigaba da zama da wayanda batasani ba” Alh yay murmushi “tasan ku, saitana zama daku dinne ai zata tunaku,yanzu bata karkashin mu tana karkashin inuwar auren Barraq ne, haka Allah ya kaddara, mun gode kwarai,”ya kalli mum yace mun gode ma ya kalli Amma yace mun gode ma Umma da su Baffa suka goggode musu kafin kowa ya mike tsaye zasu tafi duk suka tashi Rufaida tarike zanin Umma tana kuka “ni wlh kidawo,banason gidanan,zan biku” Umma ta shafa kanta “banace zan dawo ba? kiyakuri kinji Baby na” Rufaida ta make kafada tana kuka. cikin Bacin Rai Baffa sarkin masifa ya daka mata tsawa “yimana shiru kafin nafasa bakinan,sake ta” bakinta tarike tana hawaye, Ya kalli Barraq yace”kaita daki tasha maganin ta tai bacci, bata gama warkewa ba bata bukatan all dis stress”. Ahankali Barraq yatako inda take ya mika mata hannu make kafada tayi da Baffa yamata wani mugun kallo batasan sanda tabashi ba tana tafiya ahankali suka fita daga dakin part dinshi yakaita yabude suka shiga. sukama su Alh sukabar gidan Dad dasu Amma suka dawo ciki kowa yana mamakin abunda yafaru yau. Suna shiga dakin ta fizge hanunta tana turo baki”kuma ni mutum yasake ni tunda dai ba hanunshi ya rike ba” Ta nemi kujera ta zauna ahankali tana cije lebe. Barraq baice komi ba saidan Murmushin dayayi aranshi yace so real Rufaida nada masifa O God save me!. Fita yayi daga dakin yatafi bangaren Amma yaganta tareda Mum yace”Mummy ina magungunan ta?” Mum ta dauko tabashi ya juya zai fita takirashi Son ya dawo “kabi Daugther ahankali, kayi hakuri dakome zatayi kaji, karka bata mata rai, kadaiga batada lpy anjima zan shigo naganta” ya juya yafita koda ya shiga dakin ya tarar da ita a zaune tadena sai kumbure kumburen datakeyi. ya dauko goran ruwan faro da maganin daya kamata tasha ya ballo ya mika mata “sha maganin ki Baby na”ta kalleshi ta ballamai harara “ni bazan shaba malam, kumani kabani kayan sawana zanyi wanka na chanza kayan nan” yadade tsaye yana kallon yanda take murguda mai baki. Tsugunnawa yayi agabanta yace”naji but plz take it and drink,baki da lafiya” “ance baza ashaba,wai ni dole ne wlh niba ruwana da mutum, wai mijina ne, aibani nace inaso ba, nigidan mu zaka kaini gobe ehe” tana karasa maganan tabi ta gefenshi tayi hanyar wata kofa data gani,tasa hannu ta bude tabi wurin takara ganin wani kofa ta bude taga bedroom takarasa shiga dakin tanemi bakin gado ta zauna da kyar. Ta sauke ajiyan zuciya tana shafa cikinta “wai meyasa cikina ke ciwo?wayyo zapi wlh” tafada araunane. zip din rigarta ta zage, ta cire rigar daga jikinta dan

Please Login or Register in order to submit comment