Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka yagani amma baniba idanhar alhaki ne yafarabin Alhaji tokam baimaga komiba zanyi jinyarshi nawasu lokuta shima sabida darajar aure amma idan naga abin bana qare bane tofa zan tattara inawa inawa nayi gaba "

A cikin masarautar Sarki Zaid kuwa adede lokacin da Alhaji Tukur yafad'i adede lokacin Abba yatashi wato Kaka cikin mamaki yami'ke tsaye yashiga zagaya cikin bedroom d'in kukan farinciki yasaki yadubi gabas yayima Allah sujuda yadad'e yanayin addu'o'i sannan yamiqe yafito parlour cikin mamaki Mama da Hjy Himla da Umma suka shiga kallon shi tamkar a mafarki tashi mama tayi taje ta rungumo shi sannan ta tabbatar da gaskene kukan farinciki tasaki Suma su Umma tashi sukayi suna sakin nasu kukan farincikin cikin sauri Umma tafita part d'in Sarki Zaid tanufa tasanar dashi takoma part d'in Ammin maimartaba aguje yarugo wajan ganin mahaifin nashi hakama Maher da Ammin dakuma Iftahal amma ita takasayin gudu sabida cikin jikinta dogarawa ma kafin wani lokaci tunin part d'in yaciga da jama'a

Tsayin lokaci ana taya jaje sannan Kaka yashiga karanto addu'a had'ida sake miqama Allah godiya sannan yashiga tambayar ankai su Bahijjat dakunansu aka tabbatar mishi dacewa ankaisu babu jimawa duban Maher yayi yazo zonan Saraki na Ina matar taka kuzo naji diminku nasamuku taku albarkar " kama hannun Iftahal Maher yayi suka isa gaban Kaka rungumai su yayi yashiga saka musu albarka cikin farinciki bayan nan yadubi Hjy Himla yace

" Ke ina wannan Sha Sha Shan d'an naki yanatsu kuwa ? koda yake babu alama sabida tunda nakwanta banganshi yashiga gaidaniba ko sau 1 hakan ya tabbatar min dacewa har yanzu bashida hankali " tamke fuska hjy Himla tayi duban Kaka Maher yayi yace " tabbas kuwa Kaka nima nasheda wannan rashin hankalin nashi d'azu nakamashi yanaqoqarin yima Aunty Bahijjat fyad'e shine nayimai duka nasa aka rufeshi kafin ayimai hukun da anan gaba bazai sakeba agaban Mahaifiyar tashi akayi " zaro ido Hjy Himla tayi tace

" Kajimin munafukin yaro to ni bansan komi ba tun d'azu nike neman Abdul ashe kaine kasa aka rufemin yaro to wallahi kayi gaggawar sawa abud'e shi dan wallahi nasan Abdul bazai aykata hakan ba " sosai Maher yayi mamakin FURUCIN hjy Himla kafin yayi magana kaka yadakamata tsawa dafad'in

" Yimin shiru Himla tabbas Abdul zai iya aykata hakan dan nasan halin shi balle yanajin haushin an hanashi auran Bahijjat Kuma nasan Saraki ba zeyimai qazafiba ribar mai zaici idan yayi ma Abdul qazafin fyad'e kinsan kuwa hukuncin wanda yayi yunqurin fayd'e ? to abune mai qirma hakan yasa zansa ayimai hukunci irin wanda agobe ko ance yasake baze yiba dan haka nabada umarnin gobe dasafe afito da Abdul gaban kowa afad'i irin lefin dayayi sannan a kwaramai ruwan sanyi atubemai riga azaneshi da wannan zabgegiyar bulalar bulala 505 "

Jin haka yasa Hjy Himla miqewa cikin 'bacin rai tace " gaskiya Abba idan akayimin haka toni wallahi ba'amin adalciba dama ni kam nalura antsaneni dagani har d'ana cikin masarautar nan dan haka idan har akayima Addul wannan wulaqancin to zan tattara nida d'ana mubar mugu masarautar gaba d'aya tun....... " Kafin taqarasa Sarki Zaid yatashi yasauke mata marika guda 2 cikin fusata yace

" Kishiga cikin hankalin ki Himla kokin manta waye kike gayama wannan banzar maganar atunanina Koda akan kuskure Abba yayanke ma Abdul hukunci bazakiyi magana ba amma segashi akanma dede kike gayama mahaifin ki irin wannan gaskiya kisakeyin tunani " cikin 'bacin rai sosai Abba yace " barta Zaid ta isane tanunamin d'anta yafi ubanta dan haka duk inda Zaki kije amma wannan hukuncin babu fashi " duban Maher tayi cikin tsananin 'bacin rai tace " kayi nasara amma kasani wallahi senasaka kayi mugun baq'in ciki fiye danawa kasan wannan Kai d'an gold ko ? duk abinda kazartar ya zartu ko hmmm to wallahi zakusha mamaki har ita Bahijjat din kaja mata " daga haka tafita afusace

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 57 to 58

Sosai ran mama yayi matu'kar 'baci d'an kam batayi tunanin Himla zata iya furta irin wannan maganganun ba sallamar taron Kaka yayi sabida yadda ranshi ya'baci sosai Iftahal tashiga mamakin hjy Himla to mai take nufi dasetasashi yayi baqin ciki fiye da wanda tayi haka taita wannan tunanin har suka Isa part d'in su bayan sun zauna tadubi Maher tace " My blood nifa maganar Hajiya tasaka hankalina tashi sabida ko kad'an banason wani abu yata'bamin kai " murmushi yayi yasake jawota jikin shi yace " haba my Sonahh 'bacin rai ne kawai babu abinda zata iya yimin kimacire wannan cikin ranki Allah shine zai cigaba da karemu akan dukkan maqiyanmu kece kike tunasar dani kullum cewa addu'a itace babban magamin mumini nakumasan tabbas hakane to mukam mun riqe addu'a duk abinda kikaga yasamemu to karkice addu'a batayi tasiriba a a qarfin qaddarar muce haka amma sanadin addu'a zakiga koma maiye yazo cikin sauqi kin my Sonahh kicire wannan cikin ranki kinji kinsan banason damuwar ki " murmushi Iftahal tayi had'ida jinjina mishi kai

Washegari kamar yadda Kaka yace hakan kuwa yafaru agaban duk jama'an cikin masarautar akayima Addul wannan bulalun tun yana ihu har yagagarayi Hjy Himla kasa zama tayi agun hakama su Ammin Iftahal ma qinzuwa tayi bayan angama aka kamashi aka kaishi part d'in Mahaifiyar shi dubanshi tayi idanunta cike tab dahawaye tace " Abdul nayimaka alqawarin saka Maher cikin tananin ba'kin ciki kamar yadda yasakamu nida Kai Kuma ayau zamubar cikin masarautar Nan zamukoma gidan mu Wanda mahaifin ka yabarmana kayi haquri kaji " nishi kawai Abdul yakesaki sabida azaba babu jimawa doctor yayi sallama cikin part d'in duban shi hjy Himla tayi tace " Kai kumafa a gayyar wa ? " sosai doctor yayi mamaki amma seyace " mama ce takirani tace nazo naduba Abdul " wata irin tsawa Hjy Himla tayi wadda tasaka doctor saurin jabaya

" Bana buqata kayi gaggawar fita daga wannan part d'in tun kafin nawulaqantaka " ganin haka yasa doctor saurin juyawa yafita yana jinjina irin masifar hjy Himla koda yasanar da mama sosai taji babu dad'i akan abinda hjy Himla tayi sallamar doctor tayi yayi tafiyar shi bayan fitar doctor ko 1 hour su Hjy Himla basu sakeyi ba suka fito tareda kayan sakawar su kawai se key d'in motar datasiyama Abdul da kud'in ta amma duk wani abu dayashafi nacikin masarautar ne ko Wanda Kaka yasiya Mata ko mama ko Sarki Zaid bata d'auki koda tsunkeba cikin sauri aka sanar da Sarki Zaid fitowar su tashi yayi yafito cikin mamaki dakatar da dogarawa yayi ya'isa inda take cikin mamaki yace

" Haba Himla maiye haka kike shirin aykatawa ? idan kikayi hakan kenan kin nuna ke d'anki yafi karfin hukunci kenan ko ? yanzu idan kikayi hakan kinanufin Abba da mama harma damu zamuji dad'in hakan ? yafakamata kisakeyin tunani wannan badede bane " wata irin harara tasakar mishi taza tsaki takama hannun Abdul sukabar gurin suna shiga mota tatadata tajata aguje dagudu dogarawan bakin get suka bud'e mata sabida sunga babu alamar zata saurara Koda aka sanar da Kaka cewa yayi shi Kam bazaice tadawoba tunda babu wanda yayi mata lefi hukuncine anyi ko gobe yaqara se anyimai hukunci sosai kowa kam baiji dad'in abin ba amma tunda Kaka yace abarta to yazama dole surabu da ita

A 'bangaran Amarya Bahijjat kuwa ko kad'an Akeey Zaffar bai saurara mataba sabida dama cikin matuqar matsuwa yake sannan ayanzu yanajin son Bahijjat sosai cikin ranshi abinda bai ta'ba tunanin zesake bama wata mace ba segashi zuciyar shi tasake amsar soyayyar wata akaro na 2 kwance Bahijjat tace saman kyakkyawan bed d'in ta sabida duk jikinta ciwo kawai yakeyi aguje baby tashigo hayewa saman bed d'in tayi tafad'a saman jikin Bahijjat tace

" Momy na yau ke zakimin wanka dama nace duk ranan da Momy na tadawo to dady yadenamin wanka se Momy na Kuma Momy ko naraba idan dady yakaini Skul kekuma seki d'akkoni idan muka tashi ko Momy " murmushi Aunty Bahijjat tayi lokaci d'aya taji tsananin son yarinyar tamkar itace tahaifeta dede lokacin Akeey Zaffar yashigo dubansu yayi yasaki murmushi yace " iyye wato baby yau batani kikeyiba ko wato kinga Momy ko ? to zomuje ayi wanka karki makara " sake kwanciya tayi jikin Aunty Bahijjat tace " a a ni Momy zatayi min " murmushi yayi yaqaraso bakin bed din Zama yayi yajawo babyn zuwa jikin shi yace " naji Momy zatayi miki amma ba yauba kibar Momy tahuta batada lafiya "

Kuka Baby tasaka tace " Momy kice ciwon yadawo jikina banaso kinayin rashin lafiya " sosai Aunty Bahijjat tayi mamakin wayo irin na baby hakan yasata tashi zaune cikin dabara ta sakko daga bed d'in kama hannun baby tayi tace " kinga natashi lafiya ta lau kinji muje ko " maqale qafad'a baby tayi tace " sede ki d'aukeni sabida shima Dady daukata yakeyi yakaini cikin toilet yamin wanka " murmushi Aunty Bahijjat tayi tad'auketa suka shiga toilet binsu da kallo Akeey Zaffar yayi cikin farinciki da soyayya

Tun daga wannan lokacin Aunty Bahijjat take bama baby tsananin kulawa idan bakasaniba bazakace ba itace ta haifetaba itakam babyn batasan hakanba domin dama batasan Mahaifiyar tata tarasuba ta d'auka tabbas Aunty Bahijjat itace Mahaifiyar tata yadda Aunty Bahijjat kekula da baby yasa Akeey Zaffar tsananin son Aunty Bahijjat jiyakeyi kamar yabud'e cikin zuciyar shi yasakata sabida tsananin so

2 weeks su Maher sukayi suka koma USA sosai su Ammin sukaji kamar karsu tafi to amma yaya zasuyi tunda basu kammala nasu karatun ba an had'asu da wasu hadiman dan kulada Iftahal sosai haka sukabar Egypt cikeda kewar su Ammin itako hjy Himla tunda tatafi har yau babu wanda yasakejin duriyar ta

Bayan wasu watatni cikin Iftahal yashigo cikin watan haihuwa dole Ammin takoma USA tazauna sabida kulada Iftahal sosai zakayi mamaki idan ka kalli irin girman cikin Iftahal Aunty Bahijjat kuwa har yanzu batada ciki izuwa yanzu baby tana yawan damunta akan tanason qani matar Yaya Ibrahim itama cikin nata yagirma itama Aunty Shukura ayanzu tana d'auke da cikin Wata hudu a bangaran Alhaji Tukur kuwa har yanzu Yana kwance cikin halin rayuwa ko muwa kashe dukiyar tashi kawai akeyi amma shiru kakeji

To Alhamdulillah ala kulli halin Ina matuqar godiya agareku masoyana πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ har naga idon 😳 besty da maman Baffa kai hajjo nifa bance book yaqareba kukuma sauran fans mai zakuce naga kun tamke fuska tokushi kurumin ku akwai saura yanzu akafara wasan πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜œπŸ˜œ

Ayau safiyar asabar Iftahal tatashi da ciwon naquda tun tana daurewa har takasa Ammin talura da halin datake ciki shiko Maher yanajin haka yashiga cikin rud'ewa babu jira aka nufi asibiti da Iftahal cikin sauri doctors suka rufa kanta babu abinda Iftahal keyi se addu'a tun tanayi anaji har yakaiga takomayi cikin zuciyar ta sabida bakin nata yayi nauyi shiko Maher yakasa barin qofar room d'in hakama Ammin da Shanwul abu kamar wasa har dare Iftahal bata haihuba sosai hankalin Maher da Ammin yayi matuqar tashi har washe gari shiru kakeji sosai Iftahal tayi matuqar galabaita amma har kwanaki 2 kenan Iftahal taba haihuba shiga cikin room d'in Maher yayi cikin fad'a damatuqar tashin hankali yadubi doctor yace

" Gaskiya zan canzama matata asibiti kwana 2 fa kenan kunbar min ita sefaman Shan wahala takeyi to banga anfanin zuwa asibitin ba " dafashi Ammin tayi cikin sanyin murya tace " kayi haquri Saraki Koda wani asibiti mukaje tofa dole se Allah yakawo haihuwar nan kaqara haquri kacigaba dayin addu'a " wasu irin hawaye masu zafi sosai suka shiga gangarowa daga cikin idanun Maher qarasawa yayi bakin bed d'in yakamo hannun Iftahal yasaka cikin nashi d'ayan hannun yad'aura saman cikinta cikin raunin murya yace

" Haba kaiko wannan babyn dan Allah kafito ko Momyn taka tahuta haba my baby please dan Allah Ina roqonka kafito kabar wahalarmin da Mata dan Allah " ahankali Iftahal tace " My blood dan Allah kakiramin Abbana kace yazo yayafemin mutuwa zanyi My blood bazan iya ba Ina gab dakasawa dan Allah kakiramin shi " cikin sauri Maher yaciro wayar shi yana fad'in bazaki mutu kibarniba Sonahh in sha Allah zamu rayu tare kiran wayar yayi bugu 3 Abba yad'aga baijira Abban yafarayin magana ba yace " Abba dan Allah kataimaka kazo USA Iftahal tana asibiti kwana 2 kenan tana naquda amma har yanzu shiru tace kazo dan Allah kuma tana neman yafiyar ka nida kaina zanbiya kud'in jirginku Kai da Ummi dan Allah Abba kazo "

Cikin da kakkiyar murya Abba yace " bana buqatar kud'in jirgin ka " sekuma muryar tashi tayi rauni sosai yacigaba dacewa " nine yakamata nabiya kud'in jirgi dan zuwa wajan 'yata muna hanya in sha Allah samata wayar a kunne cikin rawar hannu Maher yasama Iftahal wayar a kunne cikin sanyin murya Abba yace " kwantar da hankalin ki Iftahal in sha Allah zaki haihuwa lafiya inanan zuwa nida Ummin ku sannan Iftahal nayafe miki duniya da lahira gamunan zuwa gareki cikeda tsananin soyayya fiye da dah mijin ki Yaya gaskiya Iftahal Ina matuqar son ki 'yata "

Wani irin numfashi Iftahal taja tace " Alhamdulillah " daga haka tace ga garunkunan 😳😳😳😭😭😭

Wai ashe cema Maher tayi ga wayar kanan " πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜œhar naga idon wasu πŸ˜‚πŸ˜œ wannan numfashina da Iftahal taja yasata sakin wayar tafad'i sanadin ciwon dayataso fiye da dah cikin sauri doctor Sera tayo kanta ayfa abu seyafi dah cema Maher da Ammin sukayi sufita wani irin kallo Maher yayima doctor hakan yasa dole tarabu dashi fasowar kan baby yasa Iftahal sakin salati sabida azaba cikin hukuncin Allah babyn yafito had'ida tsanyara kuka zaro ido Maher yayi yadubi babyn yadubi Iftahal saurin shafa kan Iftahal yayi yana fad'in mashi Allah amma seyaji takamo hannun shi da 'karfi kukan wani babyn yaji saurin duban doctor yayi kafin yayi magana tayimai nuni da hannu ✌🏻sake maida duban shi yayi kan Iftahal wata irin zufa yaga tawanke fuskar ta tamkar an watsa mata ruwa d'ayan hannun nashi yasaka ya tallafo fuskar ta saurin fizge kanta tayi tace " Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuuunn Hasbunallahu wani'imalwakil Al hayyu lu qayyum " tasaki wani irin nishi sega wani babyn 😳 cikin rawar baki Maher yace " wani Kuma doctor 3 fa ke...... " Kafin yarufe baki doctor tace gama wani nan 4 kenan "

Maher maisan sanda yafashe da kukaba amma yarasa kukan mai yakeyi kukan tausayin halin da Iftahal take ciki yakeyi ko kukan farincikin zuwan babys d'in shi 4 duniya jin kukan babys fiye da 1 yasa Ammin shigowa duban Iftahal dake kwance tayi tadubi Maher sannan tadubi inda jariran suke tace " gimbiya Saraki wa'incan babys d'in duka...... " kafin taqarasa Maher yace duka nawane Ammin duka yara 4 Alhamdulillah ala kulli halin tsarki yatabbata ga ubangijin halitta Allah kayimin kautar da duk duniya babu Wanda ya'isa yabani se Kai Kuma babu wanda ya'isa ya amsa se Kai Allah Ina godiya agareka marar adadi "

Saurin nufar gurin jariran Ammin tayi wani sassanyan kallo tabisu dashi sannan tashiga duba jinsin su sassanyan ajiyar zuciya tasauke tace " Saraki duka 2 Allah yahad'a mana 2 maza 2 mata Alhamdulillah Allah kenan mai kauta da qari ko yanzu namutu Allah yacikamin burina d'ah d'aya yazamarmin gari Allah karayamana wa'innan yara bisa sunna kasa suzama masu tsoran Allah masoya manzon Allah masuyima addinin Allah hidima Allah kawadatasu da lafiya da farincikin rayuwa Ameen ya Allah kabama dukkan musulmi mai nema ya Allah darajar Annabinmu Muhammad S.A.W "

Itako Iftahal samasama takejin su sabida ta galabaita sosai dubata doctors sukashigayi suko yara tsala kuka kawai sukeyi alamar lafiya suke wasu har sunkai hannu baki mazan kenan kunsan maza dacin tsiya tarwar suka bud'e idanunsu addu'a Ammin tashiga yimusu tana shafa musu cikin sanyin murya Iftahal tace " My blood kaje kaima kayima babys addu'a idan kagama kukan " dubanta yayi yasaki qayatatcen murmushi yace " ga Ammin can ni Ina nan senaga my Sonahh takoma normal " murmushi tayi tace " kaifa yanzu ubane suna buqatar d'aya daga cikin mu kaje kabar doctor sudubani nakoma normal kamar yadda kakeso kacema babys d'ina inayimusu maraba dazuwa sabuwar duniya


Comments please πŸ‘πŸ»

_Marmyn Zarah Ce_ πŸ₯°πŸ€πŸ»πŸ‘ŒπŸ»πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 59 to 60

seda Iftahal tasake kwana cikin Asibitin sannan akabasu sallama kafin wani lokaci labarin haihauwar Iftahal yabazu ko ina Umma tanaji tace ay Ina itakam se USA su Abba kuwa jigin safe sukabiyo kafin wani lokaci tuni baqi sunfara sauka su Uncle kuwa tun kafin subaro Asibitin sukaje jama'a kuwa wasuma ba'asan suba amma sunzo ganin yan 4 Iftahal labarin haihuwar Iftahal ya iske Hjy Himla zaune take amma seda tami'ke tadaji cewar Iftahal ta haifi yara 4 wata irin ajiyar zuciya tasauke tace " yara 4 hmmm lalle yau kowa Yana cikin farinciki amma bandani dasannu zansaka kowa cikin tashin hankali " duban Abdul tayi dake gefanta tace " Abdul zanje USA barkar haihuwar Iftahal " murmushi yayi yace " tayay Momy bayan ayanzu mun manta dasu Suma sun manta damu karki manta tunda mukataho babu d'aya daga cikin su wanda yazo yace muyi haquri mukoma nide aganina karkije Momy sabida idan kikaje komi zai iya faruwa mubarsu kamar yadda muka kudurta " shiru Hjy Himla tayi tace kumafa hakane da wani shiri nike qullawa to amma yanzu katunasar dani idan naje na aywatar dawani abu to tabbas za'a zargeni tunda kowa yasan akwai takun saqa tsakanina da Saraki "

Jinjina Kai Abdul yayi yace " kingani kenan yauwa Momy mahaifin Lubna yacemin naturo iyayena sekiyima su Abba magana kinga kenan nakusa zama hamshaqin attajiri tunda dama sunce senayi aure zasubani dukiyata da mahaifina yabarmin Momy nankusa zan taka duk wani wanda naga dama amma abin haushina 1 har yanzu banida matsayin taka Saraki " duban shi Hjy Himla tayi tasaki ajiyar zuciya tace " hakane Sabida shi yariga yahad'a komi amma akwai wanda zamu had'a qarfi dashi wajan quntatama duk wani makusancin Saraki shine Alhaji Tukur " tsaki Abdul yayi yace " haba Momy wannan maikamada gawan tsayin watanni Yana kwance babu lafiya tayaya zamusamu abinda mukeso agun shi ? " Murmushi Hjy Himla tayi tace

" Yaro kenan ay seyatashi zamuyi komi Kuma yana gaf datashi sabida ayanzu haka munfitar dashi zuwa qasar daza'a yimai ayki yatashi " murmushi Abdul yayi yace " aha lalle zuciyata takusa warkewa daga baqin cikin danike ciki " dafashi hjy Himla tayi tace " qware kuwa "

Aunty Bahijjat zaune saman cushion ta d'aura baby saman cinyarta fuskarta d'auke da murmushi sanad'in jin haihauwar Iftahal jitake kamar tatashi sama taganta a USA yanzu sallama Akeey Zaffar yayi yashigo dubansu yayi yasaki murmushi yace " kaga uwa da 'yarta duk lokacin danashigo inajin farinciki marar misali musamman idan naga uwa da yarta agu d'aya Ina godiya ga Allah daya mallakamin wannan family Alhamdulillah " kafin Aunty Bahijjat tayi magana abokin Akeey Zaffar dake tsaye bakin qofar yashigo sallama yayi sannan yace " kabarni inatafaman tsayuwa kadage sefaman zuba kakeyi bakada niyyar yimin iso tonashigo Amarya kigafarceni "

Murmushi Aunty Bahijjat tayi shima Akeey Zaffar haka sannan yace " yi haquri ga guri zauna kasan duk mutumin dayasamu kyakkyawan family to idan yashigo gida mantawa yakeyi dakowa my dear wannan abokinane bamujima tare sosaiba shiyasa bakisanshi ba shidin police ne mataimakin Comishinan 'yan Sanda nanan munhadune sakamakon yarinyar shi dayakawo Hospital d'ina sunan shi Kabir Kabir yaude gaka cikin gidana " murmushi Aunty Bahijjat tayi suka gaisa sannan tamiqe taje kawome abun motsa baki binta Baby tayi aguje murmushi Kabir yayi yace

" Lalle baby kamar bakiga dady ba kinbi Momy " murmushi Akeey Zaffar yayi yace " hmmm inde baby ce bazata zaunaba sede idan Momyn tata tana wajan " jinjina kai Kabir yayi yace " to amma Zaffar

Please Login or Register in order to submit comment