Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 65 to 66

Angama duk wani Shirin shiga kotu Aunty Bahijjat kuwa har yanzu tana asibiti sabida jikin ta babu qarfi sosai ga matsanancin bugun zuciya datake fama dashi yau takama safiyar litinin kuma ayau ne za'a shiga kotu misalin 10 adede wannan lokacin Aunty Bahijjat Maher yad'akkota daga asibiti zuwa gida cikin parlour Ammin suka shiga zaunar da ita yayi sannan yafuskanceta sosai yace

" Aunty Bahijjat kinga yau zamu shiga kotu amatsayina name kareki wato lawyer ki inaso kinatsu Kuma kiyi tunani sosai kisanar dani wane abune baby tafiso wanda kullum setacishi sannan kisakeyin tunani lokacin da kikeyin abincin da zakikai ma baby babu Wanda yashigo cikin gidan ki sannan lokacin da kika kaima baby abincin tare dasuwa take " shiru Aunty Bahijjat tayi nawani lokaci sannan tace

" Abinda baby take matuqar so Wanda kullum setasha shi shine yoghurt dadyn ta yake siya mata su dayawa amma a wannan ranar babu dan har kuka taso yimana dataga babu haquri dadyn ta yashiga bata adede wannan lokacin ne Ayna tashigo itad'in 'yar qanwar Mahaifiyar shi ce dah itace akaso ya aura amma seyaqi ya aure ni itace ta tacigaba da lallashin baby sannan taduqa tanayimata magana qasa qasa wadda mu Kam bamusan maitace mataba dariya mukaga baby tayi alokacin ne Kuma baby take cemin yau nice zan kai Mata abinci a Skul nayi mamaki sosai sabida tunda nafarayin rashin lafiya konace zanje kaimata abinci setace a a bataso Momyn ta tasha wahala amma a ranar seta nemi hakan bayan dadyn ta yatafi kaita muka zauna tareda Ayna a parlour munayin hira cikin mutunci abinda banta'ba samuba wajan Ayna kullum cikin masifa takeyimin idan har tazo cikin gidan harara kuwa ba'ayin magana har zuwa lokacin da nashiga kitchen danyima baby abinci ko kad'an ayna batasamin hannuba har nagama nashiga wanka kafin nafito Ayna tashigo cikin bedroom d'ina tacemin ita zata tafi sabida ankirata yanzu tanada baqo "

Kasancewar inacikin toilet babu halin yimata magana koda nafito tuni tafita nagama shiryawa natafi kaima baby abinci alokacin ne tacemin Momy yanzu Aunty Ayna tatafi kuma kafin taqarasa akashiga kad'a musu qaraurawar shiga masallaci hakanne yasaka bataqarasa min zancen ba nadawo gida Saraki iya abinda nasani kenan wallahi banice nakashe baby ba bansaka komiba cikin abincin ta Ina matuqar son baby kamar rai na Saraki kataimakeni banason duniya tazargeni akan kisan baby Saraki katabbatar ma duniya ni Mai qaunar baby ce bazan iya kashe taba karka bari kowa yad'auki son danikeyima baby amatsayin yaudara Dan Allah Saraki kaji "

Taqarashe fad'ar hakan cikin tsananin kuka dubanta Maher yayi sosai yace " karki damu tun yanzu nagane inda wannan kullin yadosa Kuma nayi imanin bakece kika kashe baby ba Kuma iname tabbatar miki cewa wannan shari'ar cikin sauri zamugamata tashi kici abinci sannan kidaure karkiyi kuka a cikin kotu sannan karki sake kiyi rantsuwa ko kice wallahi kaza ko kin rantse da Allah bakebace a a sannan karki sake kicanza magana duk irin tambayoyin da Barrister Jamil zaiyi Miki kibashi amsa Kai tsaye Kar kiyi inda inda ko kwana kinji namiki alqawarin babu Mai tsareki kinji kiyi sauri kigama ni zanje gidan Akeey Zaffar yanzu akwai wani abunda nikeson tabbatar wa "

Daga haka Maher yafita kalaman Maher yasaka Aunty Bahijjat jin karfin zuciya tashi tayi tayi abinda Maher yace misalin 9:40 suka Isa kotu kaf zuri'ar Sarki Zaid sun iso cikin kotu hadda mama amman banda Kaka shikam yanacan yanayimusu addu'a cikin murmushi barrister Jamil yanufi gurin Maher sallama yayi mishi ya amsa sannan yadubeshi yace

" Barrister Maher barka dazuwa wannan kotu nadad'e Ina matuqar son Allah yahad'a ni dakai cikin shari'a 1 nakashe maka wannan qwarin gyuwar taka a wannan shari'ar ne zansaka mahaifin ka da Mahaifiyar ka da duk wani d'an uwa naka suyi tur dazaman ka lawyer karka manta kaifa ada kata'bayin ciwon hauka "

Cikin matuqar fusata Maher yadube shi amma seyayi saurin tausar zuciyar shi murmushi yayi yace " Barrister Jamil kenan lalle kuwa zanshiga cikin wannan shari'ar cikin rashin hankalin yadda babu uban daya'isa ya'iya dakatar dani yazama dole kowane barrister yaji tsorana cikin qasata dama banta'ba tsayawa shari'a cikin qasar nan ba yazama dole najijjiga kowa tun azaman farko barrister Jamil kasani wadda zan tsayawa shari'a ayau itad'in rayuwata ce Kuma Ina matuqar son Rayiwata kaga kenan zan jajurce wajan kwatar rayuwata sannan abu nagama nikam banta'ba tsayawa shari'a mai matuqar sauqi irin wannan ba ganinta nikeyi tamkar wasan yara Allah yabamu sa'a Barrister Jamil mushiga kotu ko time yayi "

Daga haka Maher yajuya yashiga kotu kotu tayi tsit alqalin shari'a yashigo kowa yamiqe bayan yazauna kowa yazauna akayi tsit Aunty Bahijjat tana tsaye wajan tsayuwar masu lefi duban Maher tayi shima kallonta yayi yasaki murmushi hakan yasa Aunty Bahijjat tasakejin natsuwa cikin zuciyar ta miqama Alqali kud'in bayanan shari'ar akayi kamar haka " yau 10 gawatan February misalin 10:00 am za'afara sauraran shiri'a a tsakanin ACP Kabir da Gimbiya Bahijjat Zaid abisa zargin ta da kashe Baby wato Yar mijinta wadda take hannun ta matsayin 'yah Allah ya bayyana gaskiya "

Daga haka yamiqa ma Alqalin ta'kardun sannan yazauna dubawa Alqali yayi sannan yad'ago kanshi yace " kotu tanason kowaye lawyer yagabatar da kanshi " Barrister Jamil yafara miqewa sabida sune wa'inda suka shigar da qarara yace " sunana Barrister Jamil lawyer government nine lawyer mai jagorantar masu qara " yakoma yazauna sannan Maher yami'ke gaisuwa yakai sannan yace " Sunana Barrister Maher Zaid nine lawyer maikare wadda ake tuhuma " jinjina kai Alqali yayi cikin zuciyar shi yace nagode ma Allah dakadawo qasarka Barrister Maher muna matuqar son irin ku cikin qasar nan bayan wasu 'yan rubuce rubuce barrister Jamil yamiqe yace Ina son nayima Gimbiya Bahijjat wasu tambayoyi idan kotu tabani dama " kotu tabaka dama " cewar Alqali fitowa Barrister Jamil yayi ya'isa gurin Bahijjat yadubaita sosai abinda yabashi mamaki seyaganta cikin dakewa murmushi yayi yace

" Gimbiya Bahijjat zanso naji shin a wannan ranar waye yadafa abincin da baby taci daga abincin safe har zuwa nadare ? " Cikin qarfin gyuwa tace " nice " jinjina Kai yayi sannan yasake cewa " anbamu cikakkiyar sheda akan cewa bakaice kike kaimata abinci zuwa Skul ba amma wannan ranar sekikaje da kanki kika kaimata kenan a wannan ranar kikayi niyyar kasheta kuma kikayi nasara " Objection yamai sari'a yakamata Barrister Jamil yacanza salon tabbayoyin shi yadena jinginama gimbiya Bahijjat lefin kisan kai tsaye har yanzu zargine babu tabbaci nagode yamai sari'a " duban Barrister Jamil Alqali yayi yace " qorafi yakar'bu barrister Jamil akiyaye " nagode mai Sari'a gimbiya Bahijjat zaki iya sanar dani shekarun ki nawa a gidan Zaffar wato mijin ki mahaifin baby kenan ? " 6 yrs kenan " amma duk tsayin lokaci baki kota'ba samun cikiba se ayanzu dakike d'auke da cikin 2 months ko ? " Eh hakane " jinjina Kai Barrister Jamil yayi sannan yace

" Yamai girma mai Sari'a inaso wannan kotu Mai adalci tayi duba da wannan lamarin sosai tsayin 6 yrs gimbiya Bahijjat bata ta'ba yin Koda 'bari bane see wannan lokacin tasamu cikin ganin haka yasata kashe baby sabida yazama yaranta ne kawai zasu iya mallakar dukiyar Zaffar sannan a wannan ranar ita tayi abincin da baby taci Kuma da kanta takai Mata zuwa Skul sannan cikakken doctor yayi bincike sosai yatabbatar mana cewa baby gubace taci kuma gubar zata iya d'aukar kimanin 2 hours ko 3 hours kafin takashe mutun misalin 2 Gimbiya Bahijjat takaima baby abinci Skul sannan baby tadawo gida misalin 5 tana dawowa tace ga garunkunan lissafin da doctor yayi mata yayi dede da awannin da Gimbiya Bahijjat takaima baby abinci 2 zuwa 5 3 hours kenan sannan munyi bincike cikin Skul d'in su kaf an tabbatar mana cewa baby batacin abincin kowa Kuma bata amsar wani abu taci haka halinta yake akwai tabbacin babu abinda taci a wannan ranar se abincin gidansu wanda gimbiya Bahijjat tadafa da wannan qwararan hujjojin nike roqon wannan kotu mai daraja data gaggauta yankema gimbiya Bahijjat hukunci tunda shedu sunfito fili cewa itace tayi wannan kisan ga takardar gwajin doctor " miqawa yayi akabama Alqali " amsa yayi yaduba sannan yayi rubutu yad'ago yace " kotu tana buqatar Barrister Maher yafito yagabatar danashi hujjojin " tashi Barrister Maher yayi yace

" Nagode yamai sari'a gaban Gimbiya Bahijjat yanufa yatsaya sannan yadubeta sosai yace " gimbiya Bahijjat Zaid inaso kiyima kotu cikakken bayani akan irin yadda kika d'auki baby cikin zuciyar ki ? " cikin sanyin murya tafara dacewa "

" Ina matuqar son baby inajinta tamkar nice nahaifeta dukda bansamu haihauwa ba amma banji damuwaba sabida inatare da baby kosau 1 banta'ba jin a raina cewa akwai banbanci akan abinda zan haifa da baby ba Ina tsananin son baby "

Jinjina Kai Barrister Maher yayi sannan yace " Masha Allah gimbiya Bahijjat a ranar dakika yima baby wannan abincin shin akwai wanda yatayaki ko Kuma akwai Wanda yashigo gidan a ranar ? "

" Babu wanda yatayani amma Ayna tazo gidan a wannan ranar har bayan nagama ma baby abinci nashiga wanka tananan amma kafin nafito tacemin tatafi "

Jinjina Kai Barrister Maher yayi sannan yajuya yadubi Alqali yace " yamai girma mai Sari'a inaso kotu tabani damar nayima ACP Kabir wasu tambayoyi " kotu tabaka dama ACP Kabir yafito kotu tanason ganin shi " tashi ACP Kabir yayi yafito bayan yatsaya Barrister Maher yadubeshi yace " ACP Kabir kafin faruwar wannan lamarin yaya dangantakarku take kaida Zaffar ? "

Kai tsaye ACP Kabir yace " abokinane Kuma amini sabida nabashi dukkan wata yardata shima Kuma haka inazuwa gidan shi shima yanazuwa nawa a ranar da baby tarasuma Ina gidan " jinjina Kai Barrister Maher yayi sannan yace

" Kenan zaka iya fahimtar yaya Gimbiya Bahijjat tad'auki baby ? "

" Qware kuwa sabida naji matuqar mamaki danaji cewa ba gimbiya Bahijjat bace ta haifi baby sabida irin tsaquwar dake tsakanin su irin ta 'yah da uwa ne har baby tarasu batasan ba gimbiya Bahijjat bace ta haifeta baby tafison Gimbiya Bahijjat sosai akan dadyn ta na tabbatar dahakan sabida agaban idona da kunnuwana nashajin tana fad'in haka kuma tana aykata wasu abubuwan masu Kama dahakan "

Murmushi barrister Maher yayi yace " to ranar da abin yafaru tunda kana gidan a wannan lokacin wane irin hali kaga gimbiya Bahijjat tashiga Kuma Yaya kad'auki lamarin ? "

Ajiyar zuciya ACP Kabir yasauke sannan yace " gaskiya tashiga cikin tananin tashin hankali Wanda yasata zubda hawaye masu yawa sannan gaskiya ni kaina nayi mamakin hakan kuma nashiga wata tantama amma kasancewar babu wata alama datake nuna ba itace tasaka gubar ba yasa dole tanacikin zargi" murmushi Barrister Maher yasakeyi sannan yace kenan kana tantamar cewa gimbiya Bahijjat ba itace ta kashe baby ba ? " Eh kusan haka shiyasa muka kawo lamarin gaban kotu dan fiddo Mai lefi "

" Juyowa barrister Maher yayi yace yamai sari'a idan kotu tabani dama inason yima Zaffar wasu tambayoyi wato mahaifin baby " duban Barrister Jamil Alqali yayi yace " barrister Jamil ko kanada tambayoyin dazakayima ACP Kabir ? " Miqewa barrister Jamil yayi yace " babu yamai shari'a " ACP Kabir zaka iya komawa kazauna kotu tana buqatar ganin mahaifin baby " tasowa Akeey Zaffar yayi yazo yatsaya duban shi barrister Maher yayi yace

" Zaffar kaji duk bayanin gimbiya Bahijjat dana ACP Kabir shin gaskiya ne ko akasin hakan ? " share hawayen fuskar shi Akeey Zaffar yayi yace " tabbas gaskiya ne Kuma Ni banyarda cewa uwa zata iya kashe 'yar taba idan baby batada lafiya kwana kuka gimbiya Bahijjat takeyi Bata ta'ba samun natsuwa se taga tasamu lafiya sannan take samun natsuwa gaskiya bazata iya kashe baby ba sabida tana matuqar kaunar ta tamkar itace Mahaifiyar ta " jinjina Kai yayi sannan yasake duban Alqali yace " yamai sari'a idan kotu tabani dama inason akiramin Ayna dan yimata wasu tambayoyi "

Gyara gilashin shi yayi sannan yace " barrister Jamil kanada tambayoyin dazakayima Zaffar ? " Akwai yamai sari'a " to kotu tana sauraranka " Zaffar tayaya kasan cewa gaskiya ne gimbiya Bahijjat tanason baby sosai kasanfa babu wanda yasan abinda ke zuciyar duk wani d'an Adam se Allah kasani ko iya fatan bakinta akwai son yake baikai zuciya ba sannan maiyasa kace bazata iya kashe baby ba ? "

Cikin takaici Akeey Zaffar yace tsayin 6 yrs yaci nagane wane irin so Bahijjat takema baby sannan sotari idan nafita nakan tsaya nad'inga sauraran irin hirarsu sannan kasan yaro shi Babu ruwan shi Kai tsaye yake fad'in abinda yake cikin zuciyar shi idan danni Bahijjat take nunama baby so to ay Ina tafiya nabarsu idan nason gaskiya bane idan bana wajan zatayima baby duk abinda taga dama ko sau 1 baby Bata ta'ba cemin Bahijjat tayimata wani abu nacutarwaba sannan baby kullum tanacikin walwala da farinciki wannan yasa na tabbatar dacewa soyayyar gaskiya Bahijjat takeyima baby sannan idan baby tana rashin lafiya Bahijjat tana zubda hawaye Kuma tarasa natsuwarta Wanda yakasance Yana zubda hawaye Kuma yarud'e akan wani idan bashida lafiya kenan Yaya zai kasance idan yamutu balle ace shine zai iya kasheshi wannan bazai yiwuba "

Ajiyar zuciya barrister Jamil yasauke yace " nagode yamai sari'a iya tambayoyin dazanyima Zaffar kenan " daga haka yakoma yazauna tsayin lokaci Alqali yanayin rubutu sannan yace kotu tana buqatar ganin Ayna Habib agabanta " cikin sanyin jiki Ayna tafito ta tsaya dubanta Barrister Maher yayi cikin tamke fuska sannan yasaka hannu cikin aljihun wandanshi yaciro robar yoghurt dasaura aciki yace

" Kafin nace komi ga sauran yoghurt din dakikabama baby kafin 5 minutes tak dazuwan gimbiya Bahijjat Skul d'in bansan maiyasa kika yarda sauran ba bankumasan maiyasa baki Bata shi dukaba kila kema kinason shane to amma bansan ko fasa Sha kikayiba Kika jefar amma yanzu kifara riqe abinki tambayoyin dazan miki shine zai bamakowa amsar wa'innan abubuwan "

" Objection yamai sari'a " barrister Jamil qorafi bai karbuba Barrister Maher cigaba " wani irin murmushi Maher yasakar ma barrister Jamil

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_ πŸ‘ŒπŸ»πŸ€πŸ»πŸ₯°
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 67 to 68

Mai da duban shi Maher yayi sosai yace " Ayna ada bakay shiri da Gimbiya Bahijjat sabida tayi miki kutse ma'ana ta auri wanda kike mutuwar so ki aura amma segashi kwatsam kinje gidan cikin sakin fuska harma Kika taya gimbiya Bahijjat Hira wanine yayi miki nasiha Kika gane abinda kikeyi badede bane ko Kuma wani kud'irin nakine yakaiki ? "

" Ihh ihhh dama dama kawai de naga hakan baidace bane tunda tsayin shekaru bashida niyyar auran nawa shine nahaqura "

Jinjina Kai Barrister Maher yayi yace " nafaminta to maiyasa kikacema baby tacema Momyn ta wato gimbiya Bahijjat takai mata abinci a ranar ? "

Zaro ido Ayna tayi tajuya tadubi Barrister Jamil rumtse ido yayi cikin matuqar razana dajin tambayar da Maher yayi dan Kam batayi tunanin wani yaji wannan FURUCIN ba hakane Ayna babu wanda yaji akwai de tsabar qwarewar aykine irin na Maher tunda kinyima baby magana a qasaqasa shine yake kyautata zaton hakan Kika fad'a to amma marar gaskiya ko cikin ruwa gumi yakeyi bari muji wace amsa Ayna zatabama Barrister Maher cikin rud'ewa darawar baki tace

" Am hakanan kawai nace haka " kenan babu wani dalili ? " d'aga mishi Kai tayi alamar eh murmushi Barrister Maher yasake saki sannan yace " to bayan gimbiya Bahijjat tagama ma baby abinci tashiga wanka maiye yakaiki cikin kitchen d'in ? ko gubar kikaje zubawa shiyasa Kika bar gidan bakijira fitowar gimbiya Bahijjat daga toilet ba ? "

Objection yamai sari'a yakamata Barrister Maher yadena jinginama Ayna lefin dabata aykataba " Barrister Jamil qorafi bai karbuba duk tambayoyin da Barrister Maher yakeyi akan hanya suke cigaba Barrister Maher " cigama Barrister Maher yayi " kotu tana sauraranki " wata irin zufa tafara karyo mata cikin sanyin jiki tace

" Eh nashiga kitchen amma ruwa kawai nasha Kuma dalilin dayasa natafi inada wani uzuri ne na gaggawa "

" Idan nacinka dede uzurin zuwa Skul kaima baby wannan yoghurt din ne ko ? " Girgiza kai tayi tace " a a ni banje Skul d'in su baby ba " kin tabbata ? " Jinjina Kai tayi sake tamke fuska Maher yayi sosai sannan yajuya yace

" Yamai sari'a Ayna ta tabbatar ma kotu cewa ita bataje Skul d'in su baby ba a wannan ranar to nikuma inada qwaqqwarar hujjar dazata tabbatar makowa cewa taje Skul d'in wani bawan Allah Wanda yabuqaci da a boye sunan shi sabida kudin fuskantar barazana yad'auki video Ayna alokacin dataje cikin Skul d'in sabida yadda yaga yanayin ta yasa yaji bai yarda da itaba video yana cikin wayata ayanzu haka zan miqomaka yamai sari'a a kunna makowa yagani miqawa yayi akabama Alqali hayaniya kotu tad'auka tsawatar wa Alqali yayi sannan kowa yayi shiru aka kawo abu aka kunna

tun lokacin da Ayna tafito daga mota har zuwa lokacin da tabama baby yoghurt da hannunta bayan tarage tajuyo dashi tana sakin murmushi bayan tafito daga cikin Skul d'in tajefar da sauran yoghurt din tashiga mota tajata aguje " hayaniya kotu tad'auka sosai itako Ayna sosai tarikice Aunty Bahijjat kuwa kuka tasake saki da qyar Alqali yasamu akayi shiru sannan Barrister Maher yasake maida duban shi kan Ayna yace

" Kince bakije Skul d'in ba sekuma gaki kowa ya tabbatar da kinje yanzu kotu tanason sanin a Ina kikasaka gubar cikin abincin ko cikin yoghurt d'in ? " Cikin kuka Ayna tace nifa wallahi bansan komiba itace tace nasiyamata yoghurt shine nasiya nakai mata " ok hakane ? " yanzu idan har kin tabbatar babu komi cikin wannan yoghurt d'in to kishanye sauran gashi nan " ayni banashan yoghurt idan nasha amai yake sakani " ayko yazama dole Kisha dan tabbatar da babu guba acikin shi "

Objection yamai sari'a " tace batashan yoghurt yana qoqarin tursasata akan doke tasha " Barrister Jamil qorafi bai kar'buba yazama dole Ayna nasha wannan yoghurt d'in kotafadin gaskiya " cikin sanyayyar gyuwa Barrister Jamil yakoma yazauna kuka Ayna tasaki tace

" Bazan iya Shan wannan yoghurt d'in ba " dubanta Barrister Maher yayi sosai yace " to sabida mai ? " sake fashewa dakuka tayi tace " sabida idan nasha mutuwa zanyi " sabida mai ? " Sabida akwai guba acikin shi amma Allah nima bansan waye yabayarba nide ankirani da boyayyar number akabani aykin sabida inajin haushin Gimbiya Bahijjat yasa na amsa amma wallahi ni bansan baby zata iya mutuwa ba idan tasha " kina nufin bakison ko wayeba sabida mugun Sha Shanci da hauka irin naki to yanzu gashi komawaye yatsomaki ciki " yamai sari'a Ina roqon wannan kotu mai alfarma data wanke gimbiya Bahijjat agaban kowa tunda ayanzu kotu ta tabbatar batada lefi sannan Ina roqon abada umarnin bamu gawar baby danyi mata sutura sannan a qarshe inaso kotu tad'age wannan shari'ar zuwa wani lokaci yadda zamu binciko duk wani mai hannu cikin wannan kisan nagode yamai sari'a "

D'aga haka Barrister Maher yakoma yazauna bayan 'yan rubuce rubuce Alqali yace

" Bisaga qwararan hujjoji da kotu tasaurara ta tabbatar cewa gimbiya Bahijjat batada lefi dan haka kotu ta wanketa sannan tana bata haquri akan sakata cikin damuwa da akayi sannan Kuma kotu tanama gimbiya Bahijjat gaisuwar rashin 'yarta Nuratu Zaffar wato baby Allah yayi mata rahama sannan kotu zatatsare Ayna har zuwa lokacin da za'a tabbatar cewa dagaske sata akayi sannan kotu tana umartar ACP Kabir da yayi jagora abada gawar baby ayimata sutura sannan ayi qwaqqwarar bincike agano gaskiyar abinda Ayna tafad'a azama nagama wannan kotu tad'age wannan shari'ar zuwa 13 ga wannan watan 13 February kooooooootuuuuuuuu "

Aguje gimbiya Bahijjat tarugo ta rungumai Maher wani irin kuka take saki Wanda batasan wane iri bane Kama hannun ta yayi suka fita Ammin da Umma Sarki Zaid da su Aunty suka nufi Maher taruwa sukayi suka d'agashi sama suna murna adede lokacin Zaffar ya iso kama hannun Gimbiya Bahijjat yayi yace

" Nagode ma Allah dama niyi

Please Login or Register in order to submit comment