Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 27 to 28

Sha tafarayi setaji yanayin ruwan yacanza saurin cire robar ruwan tayi daga bakinta tasake dubawa jitayi cikinta yafara d'aukar zafi zaro ido tayi dandanan tarud'e tafara salati kafin wani lokaci tuni cikinta yafarayin wani irin mugun ciwo miqewa tayi zata fito amma ina kasawa tayi cikin tana neman kasayin magana yasa tasaki ihun Kiran Maher sede Kuma shi yayi nisa cikin bacci shiko doctor yanaji amma yayi banza se murmushi kawai yakeyi sosai Iftahal tasake sakin kuka tana fad'in " Maher dan Allah kazo mutuwa zanyi kazo kafin namutu kacemin kana matuqar son wannan babyn dan Allah Prince " tasake qwala kiran kamar cikin mafarki yafarajin Kiran Iftahal

Ahankali yabud'e idonshi sakejin kiran yayi cikin kuka tashi yayi zaune jikin shi duk babu 'karfi sabida baccin bai isheshi ba jiyayi tace " wallahi Prince idan narasa taimakon ka a wannan lokacin mutuwa zanyi shikenan zanmutu batare da Abbana yayafe min ba nashiga 3 "

Cikin sauri Maher yamiqe yafito yana sakkowa qasa yaga doctor zaune a parlour cikin mamaki yatsaya cikin zuciyar shi yace " kode kunnuwanane da dagaske ne ayda doctor yaji dakuma yakirani hmm wannan ciwon nawa kullum sake saban abubuwa yakeyi " juyawa yayi zaikoma dede lokacin yaji muryar ta cikin galabaita tace " Prince dan Allah katashi a wannan baccin kazo gareni kafin namutu "

Cikin sauri Maher yajuyo ya'idasa sakkowa saurin miqewa doctor yayi ganin Maher kallon mamaki yayi mishi sabida yasan wannan allurar bazatabar shi tashi yanzuba Koda kuwa tabarshi yatashi bazai iya fitowaba sabida gaba d'aya ga'bo'bin shi zasu kasance babu qarfi cikin rawar murya doctor yace " Prince lafiya kuwa ? " Wani irin kallo Maher yayi mishi yanufi bedroom d'in Iftahal yana shiga yaci karo da ita kwance saman carpet tariqe cikinta cikin sauri yaqarasa gareta ya tallafota da qyar tad'aga idanta takalleshi tace " dan Allah kakani asibiti " daga haka takasa qaracewa komi cikin razana da furgicin halin daya ganta yayi saurin surarta yafito da ita ganin haka yasa doctor saurin miqewa yanufo yace " Yaya meke faruwa ? " Muje kwantar da ita saman cushion naduba muga maiye matsalar ahankali Iftahal tace " a a Prince nayi imanin shine yasamin guba cikin ruwan danasha seyake yakasheni karka bari yadubani kakeni asibiti dan Allah " cikin yaran Araf take fad'amishi duk wannan shiko doctor baisan abinda takecewa ba wani irin mugun kallon yawatsamishi yace

" Niba sakare bane dazan yarda wani qato yata'bamin mata " daga haka yanufi hanyar fita dasauri yana qwala kiran Shanwul cikin sauri Shanwul yahayo saman karo yaci dasu cikin tsawa Maher yace " jeka tada mota " aguje Shanwul yajuya kafin su sakko tuni Shanwul yatada mota suna sakkowa akabude musu qofar motar suka shiga Shanwul yaja aguje sosai jikin Iftahal yayi sanyi addu'a kawai takeyi shiko Maher yakasa d'auke idan shi daga kanta ahankali tace " Prince Abba na dan Allah Koda namutu kasashi yayafemin wayyo Allah Ummina " kamo hannun ta yayi cikin tausayawa yace

" Babu abinda zai sameki kinji zakiga yafiyar su in sha Allah " suna isa aka amsheta cikin gaggawa aka shiga da ita hana kowa shiga sukayi amma Ina Maher yaqi dole suka barshi tsayin lokaci suna binciken matsalar sannan suka gane qwayar datasha allurori suka shiga yimata shigo wani doctor yayi hannun shi riqeda allura zaiyimata maher yayi saurin riqe hannun shi yace " namiji baya saka hannun shi saman jikin matata bama doctor Sera ko doctor Alina tayi mata sannan kafita "

Ganin babu alamar wasa afuskar Maher yasa doctor yamiqa allurar yafita tsayin lokaci sannan doctor Sera tadubi Maher tace

" Guba madam tasha Kuma mai matuqar had'ari sede anyi sa'a kad'an tasha kuma ankawota asibiti cikin lokaci gashi tanada ciki Allah yatsare su daga ita har babyn yanzu zatayi bacci sosai idan tatashi zatayi amai sosai daga nan zata koma dede "

Jinjina Kai kawai Maher yayi Amma maganar babyn datayi yasashi jin 'bacin rai sabida yatsani tuna wannan kalmar wani irin kallo yayi mata yaja tsaki afili yace " Ni tayaya zan amshi wannan babyn inada tabbacin banida alaqa dashi Iftiih!!! bari kitashi sekin sanar dani uban wannan cikin Kota halin yaya inada masifar kishi sabida haka bazan iya zama dakeba dama can babu niyyar hakan cikin zuciya ta "

Shiko Shanwul dake waje Yana ganin fitar doctor yabita har office bayan tazauna yace " doctor maike damun Gimbiyar mu ? " duban shi tayi tace " kaje kuyi magana da Prince " murmushi yayi yace " hmmm kinsanfa halin Prince sare basanar dani zaiyiba " shiru Doctor Sera tayi sannan tasanar dashi komi sabida tasan shine Wanda Prince yayar da dashi dan ta sanar dashi babu wata matsala sosai yafurgita dajin maganar guba amma dayaji matun ciki seyaji wani irin farinciki musamman da akace yananan cikin babu abinda yafaru dashi amma yashiga tunanin tayaya tasamu guba fita yayi daga office d'in cikin zuciyar shi yace lalle kuwa gimbiya kina buqatar kulawa sosai ciro wayar shi yayi yashiga Kiran layin Ammin bugu 3 tad'aga tana d'agawa Shanwul yagaidata cikin girmamawa yace

" Allah yaqara miki lafiya dama Gimbiya ce babu lafiya muna asibiti ayanzu haka " cikin tashin hankali Ammin tace " lafiya Shanwul badai Saraki ne yayi mata wani abu ba bayan ciwon shi yatashi ?" murmushi Shanwul yasaki Mai sauti yace " a a ranki yadad'e hasalima tun zuwan gimbiya cikin gidan Prince ciwon shi yarage tashi sosai yanzu de doctor tace am gimbiya tana d'auke da ciki am ma ana munkusa samun baby "

Wani irin farinciki Ammin taji wanda takasa banbance kalarshi da yanayin sa cikin yanayin muryar tsananin farinciki tace " yau d'in nan zan shirya tahowa USA Sabida Gimbiya tana buqatar kulawar uwa Shanwul wannan babban albishir dakayimin kanada babbar tukuyci dan haka nabaka dama kafad'i duk abinda kake so cikin fad'in duniyar nan nukuma zanyi makashi kayi tunanin shi kafin zuwana "

Tana gama wayar tadubi aunty Bahijjat dake gefanta cikin farinciki tasanar da ita wani irin ihun farinciki Aunty Bahijjat tasaki dede lokacin Zaffar yashigo ganin shi yasa Aunty Bahijjat fita cikin sauri part d'in mama tanufa cikin farinciki

Tofa wannan irin murna haka gaskiya Iftahal tawani 'bangaran FURUCIN!!! ki Al'kairi ne

Semun had'u zuwa dare danjin yadda wannan masarautar zata kasance shin ko Maher zai yarda yasanar wa Ammin cewa cikin nashine ko itama zai cemata banashi bane

ALLAH YASADAMU ZUWA DARE 8:30 pm Nagode

Comments please

_Marmyn Zarah ce_ πŸ‘ŒπŸ»πŸ˜˜
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 29 to 30

Tana shiga ta tafad'a jikin mama tanafad'in" Kaka yau abinda kike farki yatabbata tabbas Sarakin mu yasamu lafiya " saurin duban ta mama tayi tace " dagaske kikeyi Bahijjat ? " Rungumai ta Bahijjat tayi cikin farinciki tace " kusan haka mama wani albishir zanyi miki amma tukuycin Abu 1 nikeso shine kisaka baki Ammin taje dani USA " " murmushi mama tayi tace

" Idan har albishr d'in yacancanci wannan tukuycin to babu makawa zuwa dake USA " murmushin jin dad'i Bahijjat tayi tace " ayko yakai mama kinaji matar Saraki tanada juna 2 " saurin kallonta mama tayi tace " ke Bahijjat banason irin wannan zolayar " murmushi Bahijjat tasake saki tace wallahi mama ba zolaya bane kima tambayi Ammi yanzu akayi waya cewar tanada juna 2 tanama asibiti " mi'kewa mama tayi tace " ayko idan hakane nima yazama dole naje inda suke " zaro ido Bahijjat tayi tace

" Kije Kuma mama to wazakibar ma jinyar wannan tsohon ? " duban hanyar bedroom mama tayi tace " kumafa hakane Bahijjat babu yadda za'ayi nabarshi babu ni kusadashi kya amma nayi matuqar farinciki daba karatu takeyiba da nan zansa adawo da ita dankam zatafi samun kulawa " d'aukar wayar ta mama tayi cikin sauri tashiga Kiran wayar maimartaba shiko adede wannan lokacin suna hanyar zuwa airport dan dawowa gida Yana d'agawa mama tasanar dashi wannan batun

Wani irin farinciki yaji marar misali sannan yace " mama ay inaga daga nan zanwuce USA inason ganin Iftahal naga halin datake ciki " murmushi mama tayi tace " a a Zaid kadawo gida tukun kabari mata suje kasanfa babu kowa akan kujerar ka tayaya zaka barta har tsawon kwanaki kabari a kwaina 2 sekaje yanzu de kakira kaji Yaya jikin nata "

Amsawa yayi cikin girmamawa sannan yakashe wayar bayan mama tagama yin wayar tadubi Bahijjat tace kije kawai kiyi shiri dake za'a dan inada tabbacin Zaki kulamin da ita " murmushi jin dad'i Bahijjat tayi tace " Sosai makuwa Kaka " daga haka tafita part d'in Ammin takoma bata ciki tana wajan Umma sunataya juna murna Zaffar ne kawai cikin parlour gaban shi ancikashi dakayan motsa baki amma ko 1 bai ta'baba ganin shi yasa Bahijjat saurin natsuwa cikin zuciyar ta tace " ashe wannan uban yan miskilancin yanana zama tayi daga gefan shi tace

" Barka dazuwa " bai kalli gefan datakeba yace " yauwa ya kike " lafiya Lau Ina baby na ? " tana wajan Momy " yabata amsa ataqaice miqewa yayi yace " nizan koma sabida Ammin tace dole senaje USA zuwa gobe in Sha Allah " jin hakan yasa Bahijjat saurin cewa " am nima Kaka tace dani za'a " d'aga kafad'a yayi daga haka yajuya zaifita cikin sanyin murya tace " Allah yakaika gida lafiya " amin yace " yafita kafin wani lokaci cikin wannan babbar masarautar tad'auka da bayanin cikin Iftahal kowa sefaman farinciki yakeyi itako hjy Himla batanan batasan maike faruwaba

USA

Wajan 6pm Iftahal tafarka ahankali tashiga bud'e idonta tasaukesu kan Maher shiko jinginar da kanshi yayi jikin kujerar dayake zaune yana tunanin yadda akayi su Abbee sukasan batun cikin Iftahal gashi sun hanashi sakat dakiran waga hakan yasashi kashe wayar gaba d'aya Yun qurawa tayi ahankali amma kafin tatashi tafarayin yunqurin amai jin hakan yasa Maher dawowa daga duniyar tunanin nashi saurin tashi yayi yariqeta amma Ina kafin wani lokaci tuni tafara wankeshi da amai

Wani irin baqinciki Maher yaji cikin fusata yace 'batamin Kaya dakyau kinajin sauqi sekin wankesu dakanki Babu Wanda zai wanke mikish sake duban jikin shi yayi se a lokacin yalura bakayan dayasaka bane cikin mamaki yace tayaya hakan tafaru

Comments please

_Marmyn Zarah ce_ πŸ‘ŒπŸ»πŸ₯°πŸ˜˜
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 31 to 32

Yana sake kallonta bata iya bashi amsaba sebayan tagama kwara aman tace " kayi mamaki lokacin dakaga wasu kaya jikin ka ba wa'inda ka kwanta dasuba amma mamaki kawai kayi bakace a a bawasu bane ko bakace bakai bane " amma ni kacemin bakai bane bakuma zai yiyuba lokacin daka cire imani karabani da abinda yafi komi daraja agun kowace mace Ina kaba haquri Ina kuka amma baka saurareni ba seda kacimma burinka akaina har kayi sanadin samuwar gudan jinin ka cikin jikina amma kajuya baya kanuna bakasan hakanba haba Prince tunda nasanka nasan waye Kai Allah yasani ban ta'ba suffantaka ayadda kake tunani ba nasan lalurace bawai rashin hankali ba kamar yadda kake tunanin na d'auka ko kusa kalli wuyana Prince ji yadda kajimin ciwo har yanzu yagagara warkewa dubi yatsan hannuna kusan kwana 4 kenan yana a kumbure se azabar ciwo ka kalli fuskata da kyau har yanzu akwai shacin marin ka ajiki amma ko sau 1 bakata'ba duba irin illar dakayimin ba ko katambayeni kullum iqirarin ka shine bakason mace bakason duk wata ma'amala da ita to tayaya zan iya sanar dakai abinda yafaru bayan kasakamin tsoran ka cikin zuciya ta kaf cikin gidan ka akwai CCTV camera amma ko sau 1 bakata'ba duba abinda yake faruwaba cikin gidan kenan babu amfanin saka CCTV d'in Kai ne kayi sanadin rabuwata da iyayena amma ko tausayina bakaji maiye haka Prince idan baka duba kasan wanda yasamin guba ba to wallahi zannemi gubar dakaina nasha gara namutu da wannan baqincikin yau idan na tsallake gobe fa ? dan nayi imanin idan baka Kama Wanda yasaba gobema za'a sake sakawa kayi tunanin Prince nikam nazomaka da dukkan alkairi " taqarashe fad'ara hakan cikin tsananin kuka Mai qona zuciya

Sosai jikin Maher yayi sanyi dajin kalaman Iftahal Kuma sunyi masifar ratsa zuciyar shi sosai ya fuskanceta yace " naji Kuma zan bincika amma idan har ta tabbata wannan cikin nawane to bana buqatar shi zansa acire shi dan bazan iya da hayaniyar yaroba dan kinsan banason hayaniya idan ma kinsashi cikin ranki to gara ki gaggauta cire shi sannan tabbas nasan akwai CCTV camera amma banason dubata sabida natsani kallon halin da nike kasancewa idan ciwona yatashi amma yau yazama dole naduba zanje gida nadawo yanzu "

Daga haka yafita cikin sauri yana fita doctor Sera tashiga sannu tashigayima Iftahal sannan tasaka aka gyara gurin rumtse idon ta Iftahal tayi afili tace " bazan iya zubda ciki ba dan bansan abinda Allah yake shirin baniba banaso nazama maiyin butulci gurin Allah sede kayi duk abinda zakayi Prince amma bazan iya zubda wannan cikin ba

Maher Yana Isa gida yanufi saman shi wani room yashiga yana shiga ya kunna Computers d'in ciki cikin bedroom d'in shi yafara duba abubuwan dasuka faru tun daga ranar da Iftahal tashigo gidan yana zuwa dede gurin da tafara shiga bedroom d'in shi lokacin da ciwon shi yatashi har kwanciyar dasukayi saman bed yanayimata abu tamkar yaro da shaqarar dayayi mata dafe kan shi yayi amma baiga ya kusancetaba dawoda binciken yayi qasa cikin bedroom d'in ta nanfa yaga duk abin da yafaru tashi yayi cikin zafin rai yature Computer gefanshi tafad'i tafashe cikin tsananin zafin rai yace " wannan ne ni tabbas jikin nawane Amma akwai banbancin ruhi babu yadda za'ayi na amshi wannan cikin "

Har zai fita sekuma yakoma cigaba dadubawa yayi yaga zuwanta cikin bedroom d'in shi nad'azu sannan yaga yadda suka kasance dashi wanda yake iqirarin bashi bane sosai zuciyar Maher takeyin muguwar tafasa bayan shigarta bedroom d'in yaduba idon shi yagane mishi doctor yana saka qwayar cikin ruwa hakan yasashi komawa yaduba camera cikin bedroom d'in shi amma babu komi camera ma bata ayki tashi yayi yashiga watsi dakayan cikin room d'in duk yagama yanke hannu da glass sakkowa qasa yayi yanufi bedroom d'in da doctor yake zama amma Babu kowa duban shi yakai kan Camera dakin amma seyaganta afashe komawa saman yayi aguje cikin zafin rai yabud'e wordrop yawatso kayan ciki azafafe yashiga cire kayan yatsanza wasu yafita tun kafin lenta takaishi qasa yashiga Kiran securitys yana sakkowa sukayi saurin isowa gabanshi cikin zafin rai da fusata yace

" Yau she doctor yafita ? " amsa sukabashi da kafin shigowar ka babu jimawa " cikin d'aga murya yace " inaso kukawomin shi nanda 1 hour Yana gama fad'ar hakan yace " atadamin mota " duban juna suka cikin sauri d'aya yace " ranka shi dad'e ay tare kuka fita da Shanwul d'in " wata irin tsawa Maher yadaka musu dafad'in " dole se Shanwul ne kawai zaiyi driving d'ina ? " Jin haka yasa wani soja saurin nufar mota yabud'e shiga Maher yayi yace " Asibitin su Sera idan kawuce 15 minutes bamu isaba to bakin aykinka jin haka yasa shi taka mota aguje wayar shi yaciro yadanna Kira ana d'agawa yace " Uncle inaso adakatar da tashin kowane jirgi a yau sannan abaza jami'ai duk inda Doctor darman yake akawomin shi " daga haka yakashe Kiran

A asibiti kuwa bayan fitar Maher Shanwul yashigo ciki amma abin mamaki seganin doctor darman yayi yashiga hanyar room d'in da Iftahal take yanufa Kai tsaye yashiga ji Shanwul yayi zuciyar shi bata kwanta ba hakan yasashi bin bayanshi yana shiga Iftahal tayi saurin bud'e ido ganin doctor darman yasata zaro ido murmushi yasakar mata yace

" Ay har yanzu baki tsiraba Kinga wannan allurar yanzu zata kaiki kiyama ke mai miji ko ? to kinguji allurar a gida zaki sameta cikin Asibitin kamo hannun ta yayi daqarfin tsiya zeyi mata allurar Shanwul yashigo tureshi yayi daqarfin tsiya yafad'i tare da allurar saurin tashi doctor yayi yashaqo wuyan Shanwul sosai yashaqure shi ganin hakan yasa Iftahal fasha ihu Wanda seda ko Ina na cikin Asibitin yad'auka Kuma dede lokacin motar Maher tatsaya jin hakan yasa doctor sakin Shanwul yafito aguje cikin sauri aka bishi Maher Yana fitowa daga mota yaga doctor darman yafito aguje cikin zafin nama yabishi tareda sauran ma aykatan asibitin cikin sa'a Maher yashaqo wuyan shi wani irin duka yashiga yimai tako Ina jama'ar suna isowa doctor yazame rigar saman shi datsiya yasakar ma Maher yasake rugawa amma kafin yayi nishi sukaji qarar harbin bindiga kafin wani lokaci doctor yabaje matatce aqasa duba sukakai kan motar data wuce tagaban shi nanko idansu yagane musu Wanda yayi kisan riqe da bindiga cikin mota amma kafin su yunqura tuni motar ta'bace saman titi sabida irin mugun gudun datayi

Dede lakacin jami'ai suka iso amma Koda suka d'aga doctor tuni yamutu sabida tsakiyar kanshi bullet d'in yashiga seda yafasa qwaqwalwar kanshi wani irin ihu Maher yasaki yashiga fad'in " wallahi idan baku nemo Wanda yayi wannan kisanba duk Sena kashe ku Sena kasheku " ganin hakan yasa aka riqeshi cikin zafin rai yawatsar dasu yajuya afusace kai tsaye yashiga cikin Asibitin room d'in da Iftahal take yashiga ganin doctor Sera yayi kan Shanwul daketa faman tari sabida muguwar shaqarar dayasha duban Iftahal yayi ganin hawaye yayi saman fuskar ta sha'be sha'be qoqarin seta muryarshi yayi yace

" Fatan Babu abinda yayi miki ? " d'aga mushi Kai tayi dan bazata iya yin magana ba sabida har yanzu zuciyar ta bugawa takeyi taga mutuwa kusa badan Shanwul ba dayanzu tazama labari kallon doctor Sera yayi yace yanzu zamubar wannan asibitin sabida bashida tsari babu tsaro tunda har za'abar Mai lefi yashigo yayi yunqurin kisa Kuma idan baku gyaraba senayi duk yadda zanyi naga anrufe wannan asibitin zamu tafi yanzu Kya dinga zuwa gida kina dubata amma kisani wallahi idan matata tamutu ko wani abu yasameta sanadin

Please Login or Register in order to submit comment