Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kasan carpet yazuba black tea d'in shi wanda yasha kayan had'i yafara Sha sosai yaji yayi mai dad'i sosai Iftahal da Ammin sund'ad'e suna waya daganan sukayi sallama Koda Iftahal tasauka 'kasan carpet tuni Maher yafaracin abincin sosai yasha black tea d'in dan Kam saura kad'an yashanye kallonshi kawai Iftahal takeyi yadda taga yana lumshe ido kamar Mai baccin tashi yayi yanufi samanshi batare dayace komiba cikin sauri tami'ke tabi bayanshi tana shiga taga bashi a parlour cikin sauri tashiga bedroom d'in

Dur'kushe taganshi hanyar toilet da alama yakasa 'karasawa cikin toilet d'in ne wani irin amai yafarayi cikin matu'kar gigita ta'isa gareshi ri'keshi tayi tsayin lokaci yanayin wannan aman ba'ki 'kirin ga yau'ki dagani kasan wannan aman akwai wani mugun abun da Maher yake amayarwa cikin wata irin murya yace " Iftiih!!!! kibar nan wajan inaji kamar ciwona zaitashi kifita nace kar nakuma illataki " kuka Iftahal tasaki tace bazan iya ba kaifa mijina ne Koda zaka kasheni bazan iya tafiya nabarka ba " wata irin tsawa yadaka mata " Nace kifita kifita Iftiih!!!!! Please dan Allah banaso kimutu yanzu "

Cikin rawar jiki Iftahal tami'ke tafaraja baya amma kafin takai kofar taga Maher yami'ke wata irin dariya yasaki cikin waga irin murya wadda dagaji batashi bace yace " hhhhhhhhh wato ma har yafarajin tausayin ki koooooo ? wato keeee Mai taurin Kai kinfara karyamana shiri ko to kisani yau Zaki mutuuu kinsan wannan wane irin abune kikasashi yake amayarwa to to wannan abun seda muka d'auki shekaru muna shiryashi muka sharya dashi shine kikeso ki'bata Mana komi ko to kafin kigama lalata mana shiri bari nakaiki inda ba'a dawowa " daga haka yayi kanta wani irin bugun zuciya matsananci Iftahal tashiga ji kafin ya iso gareta tuni zufa tawanke duk ilahirin jikin ta

Comments please

_Marmyn Zarah_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 19 to 20

Wani irin yawu Mai kauri da d'aci Iftahal tahad'iye cikin darqewar murya tace " Allahumma rahamataka arju'u falatakilni ilanafsi d'arfatan aynun wa'aslihu shi'ani kullahu la'ilaha illa anta " kamar haka tacigaba dayin addu'o'i neman tsari da neman kariya daga dukkan abin cutarwa yana isowa gareta yasha'kure wuyan ta yajefata saman bed yasake nufarta gadan gadan cigaba tayi dayin addu'o'i yanasake nufota tatofa mishi wata irin 'kara yasaki yana fad'in " kin kasheni lalle kam kijira dawowata idan nawarke anan gaba nasha alwashin sena kasheki idan nadawo banza kawai " daga haka yafad'o saman bed d'in kamar matacce cigaba tayi dayin addu'o'i tana tofa mishi kamar 20 minutes yatashi zaune duban ta yayi sosai yanayimata wani irin kallo babu zato taji yajawota jikin shi manna mata kiss yayi yace " My wife nagodema Allah dabaki mutuba naje kawo ruwa nasamiki kitashi sekuma bangankiba dan Allah karki sake tafiya kibar ni " jin wannan sunan da maganganun shi yasa Iftahal tagane wannan ba Maher bane Saraki ne sauke ajiyar zuciya tayi tace

" Yauwa Saraki dan Allah kaceci rayuwa ta kasa Maher yasan cewa yarabani da budurci na da Kai da Maher duk abu 1 ne dan Allah Saraki kacece ni inajin tsoro kar Maher yazargeni Kar yayi tunanin wani ne nakaima kaina Kum....... " Wata irin tsawa Saraki yasakar mata cikin fushi yace " My wife banason kisakeyimin maganar wani ni bansan wani Maher ba kisani ni duniya ta daban shima duniyar shi daban babu wanda nasani cikin duniya ta se ke My wife karki sakeyimin maganar wani Maher kenan ma akwai wani Wanda kike so Kuma kike ma'amala dashi ko my wife kisani wallahi zan iya yin kisa akan ki sabida Ina tsananin son ki Kuma inada matu'kar kishi " sake jawota yayi jikin shi ya sassau ta murya yace " dan Allah My Wife kisoni kamar yadda nike sonki "

Tureshi daga jikin ta Iftahal tayi cikin kuka tace " dakai da Maher duka abu d'aya ne Saraki maqiya ne kawai suka raba 'kwa'kwalwar ku gida biyu shiyasa babu wanda yasan wani cikin ku babu wanda yasan mai d'aya yakeyi Saraki amma kass shi Maher yafika zama zahiri dan shi kowa yasani Kai kuwa ni kad'ai nasanka nafison Maher yasan cewa shine yayi min fayd'ey jiya dan Allah Saraki kasanar dashi " ta'karashe fad'ar hakan cikin kuka sosai Saraki yafusata yace " wato akan wani kike zubdamin hawayenki lalle kowaye wannan yacancanta nayime hukunci Mai tsanani da inada dama dana tarwatsa tashi 'kwa'kwalwar nahuta My Wife kirabu da wancan Maher d'in zan baki farinciki Kuma zan baki rayuwa mai cikeda farinciki My Wife dan Allah kimanta dashi "

Cikin damuwa Iftahal tace " tayaya zaka iya bani duk abinda nike buqata Saraki kaida bakasan kankaba bakuma kasan iyayen kaba sannan bakasan dalilin zuwan ka USA ba bakuma kasan tayaya ka aure niba kaga kuwa shi Maher yasan duka wannan kaga kenan shine zahiri kuma shine yafi cancanta dayasan ya amshi budurci na " dan Allah kasanar dashi "

Babu zato kawai seganin shi tayi yana kuka cikin kuka yace " gaskiya ne duk bansan wannan ba My Wife kafin zuwanki banaganin kowa cikin wannan gidan seni 1 amma segaki alokacin inajina kamar yaro 'karami bana sanin jiya ko yau bansan Yaya ma rayuwar takeba bana iya banbance komi ko sunana bansaniba seda kikazo Kika bani suna bansan cewa ni bayaro bane se ajiya kikasa nasan cewa ni babba ne dan Allah My Wife kisanar dani komi amma kimanta da Maher nafishi sonki "

Sosai jikin Iftahal yayi sanyi cikin damuwa tace to naji amma Kai tayaya zandinga ganinka aduk lokacin danike son hakan se zuwon Maher yatashi sannan Kai 'kwa'kwalwar ka take cigaba dayin ayki kasanar dani yadda zandinga ganinka duk lokacin danaso amma batare da tashin ciwon Maher ba " shiru Saraki yayi kamar Mai nazari kafin yayi magana wani haske yashigo cikin bedroom d'in cikin sauri Saraki yayi baya itama Iftahal haka addu'a Iftahal tashigayi kafin wani lokaci wannan hasken yarikid'e yakoma mutun dattijo dubansu yayi yayi murmushi sannan yace

" _barka da 'kokarin Iftahal gaskiya najinjina miki nine wanda nasanar da Shanwul duk abinda yake faruwa akan Maher yanzuma zansanar dake wasu abubuwan amma kafin Nan kice Saraki yayi bacci cikin zafin rai Saraki yace " babu baccin dazanyi wato nayi bacci kasamu damar cutar da ita ko to wallahi baka isaba idan kaga kacutar da ita to sede idan kasheni kayi " murmushi tsohon yayi yace to ay kokanaso ko bakaso sekayi wannan baccin daga haka yahura mishi iska kafin wani lokaci tuni Saraki yabaje sosai Iftahal taji zuciyar ta tadake duban wannan Tsohon tayi shima yadubeta yace

" _Yarinya inamai sake sanar dake daki jajurce sosai sabida akwai 'kalubale dayawa akan zamanki da Maher sannan dole zakisamu rud'ani akan Maher dole zakiga kamar kinarayuwa da mutun 2 ne bayan Kuma 1 ne sekinyi ha'kuri kimaida maher kamar su 2 ne kamar yadda Kike kiran wannan Saraki to kibarshi ahaka Kuma kiyi rayuwa dashi mai kyau sabida anan gaba idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e zai iya tuna yadda kikayi rayuwa dashi a wannan lokacin duk wani abu dakike shakkar shi ko kike ganin baki'iya sanar dashi to duk zesani idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e amma ayanzu dole ki daukesu tamkar daban daban kiyi rayuwa da shi akowane yanayi yake aduk lokacin dakike so yajuya kamar yadda kike so to zan baki wata addu'a dakinyita danufin Maher kike so yajuya ko Saraki shi kenan zai juya amma daga lokacin da yasamu lafiya shikenan ni nabarki lafiya idan natafi kita'bashi zai tashi amma Saraki ba Maher ba Maher Yana bu'katar hutu sosai sannan kiyi duk yadda zakiyi kihana doctor yimai wannan allurar dazeyi idan yadawo Kuma wannan karon bada Sarki Zaid zezoba sabida shi zashi Nigeria wajan iyayen ki_

Daga haka yabata addu'o'i sosai sannan yatafi sosai Iftahal take jinjina wannan lamarin tayaya zatadinga rayuwa da mutu 1 amatsayin 2 sosai lamarin yake bata mamaki had'ida matu'kar d'aure Kai sannan tayaya zata iya hana doctor yin wannan allurar ? tsayin lokaci tanayin wannan tunanin sannan tajuya tadubi Saraki dake kwance kamar maiyin bacci cikin jin d'adi cikin rawar hannu tata'bashi kamar wanda aka furgita yatashi afurgice saurin jawota jikinshi yayi yana dube dubai zuwa can yasauke ajiyar yace

" My Wife babu abinda yayi miki ko ? " Murmushin 'karfin hali tayi tace " babu abinda yayi min kwantar da hankalin ka " sake rungumai ta yayi cikin sanyin murya yace " mu kwanta ko My Wife am dama dama dama " kallon shi tayi cikin mamaki tace " dama Mai sanar dani mana " sake kallon ta yayi yace " dama inaso musakeyin wannan abun ne najiya " zaro ido Iftahal tayi sabida sosai tafurgita dan kam bata manta irin azabar datashaba 'kokarin kwace jikin ta daga nashi tashigayi amma Ina yamatseta sosai cikin raunin murya tace " haba Saraki dan Allah kabarni banfa warke daga jinyar daka sakaniba Kuma banaso Maher yagane abinda yafaru dani sabida banida amsar bashi kaga kenan zansamu matsala

Afusace yaturata tafad'a saman bed d'in yabita cikin hassala yace " banace karki sakeyimin maganar wani Maher ba nine mijinki nahar abada Allah idan Kika sake yimin maganar wancan sena tarwatsa tashi 'kwa'kwalwar nahuta daga haka yake bakinshi cikin nata yafara kissing d'inta kuka Iftahal tafarayi sabida yadda taji jikinshi yafarayin rawa hannun shi yad'aura saman breast d'in ta jin shasshekar kukanta yasa Saraki dakatawa cikin muryar lallashi yace

" Haba my wife meye Kuma nayin Kuma tonaji nabarki shikenan amma gobe zakibani ? Saurin d'aga mishi Kai tayi sake sumbatar lips d'inta yayi sannan yaja musu blanket sosai yarungumai ta cikin 'kirjinshi cikin sanyin murya yace

" My wife ina tsananin sonki amma zuciyata tanayin zafi idan naji kin ambaci wancan Maher d'in nine mijin ki bashiba dan haka daga yau babuke babu shi kinji my Wife cikin shagwa'ba tace " Ina ay dama ni Babu ruwana dashi Kai ne Mai sakarmin fuska Kuma Kai ne mai furtamin kalmar soyayya nima Ina matu'kar son ka Saraki na " sake matseta yayi cikin jikinshi sabida dad'i ahaka har bacci yayi gaba dasu sosai Iftahal tayi bacci Mai dad'i cikin wannan daran Kiran sallar asalatu yafarkar da Iftahal kallon fuskar Saraki tayi sefaman Shan bacci yakeyi sosai takejin dad'in kallon shi murmushi tasaki tace " Allah sarki Saraki na yanzu zakabar ni nida wannan uban miskilancin " daga haka tayi addu'o'i da wannan tsohon yace tayi

Babu jimawa Maher yabud'e idonshi ahankali suka sauka kan kyakkyawar fuskar Iftahal saurin janye jikinshi yayi daga nata tamke fuska yayi sosai yace " waye yasaki hawamin saman bed ? " Murmushi Iftahal tasaki tace katambayi kanka Mana Prince Kai da kanka kajawoni Kuma bakaga yadda karungumeni ba ? " tsaki yaja afusace yace " banason shashancin daga yau Kar in sake ganin hakan " cikin d'an damuwa Iftahal tace " to amma naga umarnin Ammin ne hakan tace karmu raba gurin kwanciya " banza Maher yayi da ita yasauka daga bed d'in seda yake bakin 'kofar toilet yace " hakane umarnin Ammin ne amma Kinga wannan cushion d'in to anan zakidinga kwanciya " har yad'aga qafarshi zai shiga sekuma yatsaya yace " waye ya kwashe aman dake gurin nan ? " saurin duban gurin tayi tabbas Babu komi agurin Kuma iya saninta bata kwashe shi ba sosai Iftahal tayi matu'kar razana amma cikin in ina tace nice " tsaki Maher yaja yace " Wai banace babu ruwanki cikin lalurataba Kinga Iftiih!!!!! banaso kina saka kanki cikin wannan lamarin ki kiyaye tashi kibar bedroom d'in nan "

Saurin sauka Iftahal tayi tafita sabida tsananin tsoro dan Kam tafurgita sosai tana sakkowa tanufi bedroom d'in ta abinda tagani yasata saurin jabawa gaba d'aya ancanza tsarin kayan bedroom d'in aguje tafito tana kwalama Maher Kira cikin sauri yafito kogama alwala baiyiba kasa magana tayi senuna mai hanyar bedroom datayi Kai tsaye yanufi bedroom yashiga dube dube yashigayi amma baiga komiba Kuma Shirin kayan yakoma yadda yake ahankali Iftahal tale'ka amma setaga yadda Shirin yake tunda haka yake wani irin kallo Maher yayi mata yaja tsaki yabar bedroom d'in

Comment please

_Marmny Zarah Ce_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 21 to 22

Tsayawa tayi tana nazarin lamarin amma cikin matu'kar tsoro take tsayin lokaci tana tsaye tana karanto addu'a sannan tashiga ciki darajar addu'a yasa Iftahal taji zuciyar ta tadake sosai Kai tsaye tanufi toilet tayo alwala tafito salla tatada kafin Kiran sallar asuba sosai Iftahal takeyin addu'a akan wannan lamarin Allah yayi mata jagora

Egypt

Bayan dawowar Sarki Zaid da Sarauniya Batol mama takira Sarki Zaid Babu jira ya amsa kiran Mahaifiyar tashi yana shiga parlour ya taradda hjy Himla da d'anta Abdul bayan yazauna yagaida mama sukuma suka gaidashi ygara zama mama tayi tace " Zaid abinda yasa nakiraka bawani abu bane maganace akan Abdul yana son auran Bahijjat kuma ni nayarda da wannan auran sosai Sarki Zaid yaji babu dad'i sabida dan Kam yasan halin Abdul bayaji tako Ina gaskiya bayason wannan auran to amma yaya zaiyi bazai iya yima Mahaifiyar shi musuba babu yadda zaiyi dole yadubi mama yace " to Mama tunda kinason hakan Allah yasa hakan shine mafi alkairi " murmushi mama tayi tace Allah yayi maka albarka Amin yace yami'ke yafita murmushi hjy Himla tayi shiko Abdul mi'kewa yayi yafita fuskar shi d'auke da murmushi part d'in Ammin yanufa sabida yasan Bahijjat tanacan yana shiga yasameta zaune akan cushion tana latsa wayar ta Zama yayi kusada ita afurgice tadube shi cikin fad'a tace

" Maiye haka Yaya Abdul Babu ko sallama wallahi ni Kam kabani tsoro " tamke fuska yayi yace " to banyi niyyar yin sallamar ba jawota yayi tafad'o jikin shi babu zato rungumai ta yayi sosai yakawo bakinshi dede kunnanta yace " zuwa nayi nasanar dake cewa Maimartaba Zaid yabani auran ki kinga kenan daga yau zakifara yimin biyayya " cikin zafin rai tatura shi tadube shi tace Allah yatsari gatari dasaran shuka wallahi dana aure ka gara namutu babu aure kasani Ni Bahijjat ba irin matar kabace "

Murmushi yayi yasake matsowa kusada ita babu zato taji ya wanketa da mari mai matu'kar zafi 'kara tasaki hakan yasa Ammin fitowa ganin Abdul agaban Bahijjat itakuma tadafe kuncinta yasa Ammin tafahimci abinda Abdul yayi ma Bahijjat cikin fad'a tace " haba Abdul maiye haka da girmanka kake cin zalin 'kanwar ka idan wani abu tayimaka ay seka sanar dani nayi mata fad'a ko " murmushi Abdul yayi yace " Babu ruwan ki Ammi tsakanin mata da miji ne Kinga babu buqatar sanar dake " daga haka yajuya yafita yana sakin shi'umin murmushi bin shi Ammin tayi da kallo tana jinjina rashin kunyar Abdul juyawa Bahijjat tayi cikin kuka tarungume Ammi tace " Ammi dan Allah karku bari a auramin wannan azzalumin kingani tun yanzu yafara nuna muguwar d'abi'arshi Ammi dan Allah " dede lokacin Zaffar yashigo shi d'ah ne ga yayan Ammin tsayin 5 yrs kenan da yin auran shi amma kas lokacin haihuwar matar shi tafari Allan yayi mata rasuwa bayan tahaifi kyakkyawar yarinya Mai Kama da ita tun daga wannan lokacin Zaffar yarufe shafin wata mace bashida abin dubawa se 'yarshi wato baby wadda taci sunan Mahaifiyar ta yad'auki dukkan lokacin shi da kulawar shi yabama yarinyar shine yakeyi mata komi yaqi bakowa ita duk da cikin yan'uwan shi dayawa sun nuna sunaso ciki hadda Ammi kimanin shekarun baby 4 kenan akwai wayo gurin baby sosai wannan kenan

Yana shiga yadubi Ammi yadubi Bahijjat dake kuka sama yayi sannan ya gaida Ammin gaidashi Bahijjat tayi sannan tabar gurin takoma qaramin parlour bayan fitar Bahijjat Ammi tadubi Zaffar tace " lalle ashe yau zamusha ruwan sama cikin garinnan Zaffar yau cikin gidan nan ? anya kuwa shine bagizo idanuna sukeyiba ?" d'an murmushi Zaffar yayi yace " nine Ammin bagizo bane " hmmm " Ammin tace sabida mamaki sannan tace " lalle de kam amma Ina baby yau naganka babu ita murmushi yayi yace " ay baby angirma tana Skul nima yau Ina hutu banje Hospital ba shiyasa 'kila se zuwa yamma " dede lokacin Bahijjat takawo ma Zaffar abun motsa baki da lemon bayan ta aje tajuya hira Ammin da Zaffar suka shigayi zuwa can Ammin tace

" Wai nikam Zaffar yaya batun aure ne ? kasani zamanka hakafa bazai yiyu ba Zaffar idan kaqi yin wani auran tofa kamar baka yadda da qaddarar da Allah yad'aura maka bane Zaffar kad'aure kayi aure kodan baby dole tana buqatar samun kulawa daga mace sannan kullum tanayimaka kukan Ina Momy kaga idan kayi aure baby zatabar kukan rashin Momyn tata Dan Allah Zaffar " ajiyar zuciya yayi sannan yace

" Ammin bawai na'kiyin aure bane sabida kasa yarda da qaddara a a Ammin sedan bazan iya sake son wata 'ya mace ba Ammin banaso nayi aure amma yazama nakasa sauke haqqin matar sabida gaskiya tunda Nuratu tarasu narufe zuciya ta na kulle idanuna daga kowace irin mace ayanzu babu abinda nike kallo naji dad'i kamar baby kuyi ha'kuri Ammin bazan iya sake saka wata mace cikin zuciya ta ba zanjira har namutu naje natadda matata Nuratu ina roqon Allah yahad'a mu cikin gidan aljanna tare "

Ajiyar zuciya Ammin tasauke tace " amin ya Allah amma Zaffar amatsayina na qanwar Mahaifiyar ka ina roqon wata alfarma kuma banaso kayi musu idan har na'isa Zaffar inaso ka auri 'yata Bahijjat " saurin dubanta yayi sannan yadubi hanyar da Bahijjat tabi bayan takawo mishi abun motsa baki bud'e baki yayi zaiyi magana Ammin tace " karkace komi ni zanji da komi Zaffar dan Allah karkace a a tabbas zakasamu tsananin kulawa agun Bahijjat Kuma daga lokacin da Bahijjat tashiga gidan ka baby tabar kukan rashin Mahaifiya idan har dagaskene bakason damuwar baby balle kukanta to kasamar mata da wata Mahaifiyar wacce zata maye mata gurbin tata Mahaifiyar "

Iska Zaffar yafesar yace " shi kenan Ammin amma fa banajin zanso Bahijjat zanyine dan ke Kuma dan baby amma badan ra'ayin kainaba " sosai Ammin taji dad'in hakan tashi yayi yayimata sallama yafita Kiran Bahijjat tayi cikin sanyin jiki Bahijjat tafito tariga duk taji komi zama tayi kusada Ammin cikin wani irin yanayi murya a raunane tace " Ammin Abbee yariga ya amsa cewa Abdul zan aura Kuma Ammin Zaffar basona yakeyiba inajin tsoron auran Wanda bana gabanshi " jawota Ammin tayi jikinta tace

" Kwantar da hankalin ki Bahijjat nasan Zaffar zesoki Kuma zakiji dad'in zama dashi sannan maganar auran ki da Abdul abune mai sau'ki wajan warware shi amma idan Kika sanar da Saraki cewa bakison Abdul ke Zaffar kike so tonasan zeyima mama magana Kuma kinsan yadda mama takeson Saraki duk abinda yakeso zatayimai Babu musu bari zankirashi dakaina muyi magana dalilin dayasa nace ki auri Zaffar idan babu maganar auran wani tofa babu mafita kuma badan Zaffar yana matsayin d'ah agareniba nake son ki aure shi a a kyawun halin shi da kamalar shi tasa nike miki shi'awar auran shi dakuma gujema auran Abdul " murmushin farinciki Bahijjat tasaki sosai taji dad'in abinda Ammin tace amma tana tunanin yadda zatayi zaman aure da Zaffar dan tasan halin Zaffar danuna halin ko in kula damutun

Bayan Bahijjat tatashi Ammin takira Saraki take sanar da shi suna gama waya Saraki yakira mama magana yayi mata a takaice " _mama barka da yau fatan kina lfy naji kince maganar auran aunty Bahijjat to amma mama ni yanzu bankai matsayin asanar daniba ? kema kinyarda ni marar hankalin ne mama ? komade Yaya kuka d'auka ni amatsayina na shaqiqin Aunty Bahijjat tuni nariga nayima akeey Zaffar al'kawarin auran Aunty Bahijjat Kuma itama nasanar da ita kuma ta amince dama jira nikeyi Abbee yazo nasanar dashi

Please Login or Register in order to submit comment