Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to amma ni bazance kucanza ra'ayin kuba amma idan kuka qi to tabbas kund'aukeni marar hankalin nabarku lafiya_ "

Kafin mama tasakecewa komi tuni Maher yakashe Kiran sosai hankalin mama yatashi tuni tasa aka kiramata maimartaba da hjy Himla da su Ammin Babu 'bata lokaci kowa ya hallara cikin parlour bayan kowa yazauna mama tadube su tace " ke Himla akan maganar auran Bahijjat da Abdul ayanzu Kam Babu ita kafin maganar Abdul tuni Saraki ya amshi maganar Zaffar wato d'an wan Batol se yanzu yake sanar dani Sabida haka Abdul yayi haquri yanemi wata mu aura me " wani irin farinciki kowa yaji amma banda hjy Himla data miqe tace

" Amma gaskiya mama hakan beyiba yanzu ace har Saraki yakai matsayin amsarma Bahijjat miji bacin matsayin qani yake gunta gaskiya idan akayi hakan babu adalci yaron da Babu tabbacin yana cikin hankalin shi yake sanar daku k...... " Ke Himla kishiga cikin hankalin ki Mahaifiyar tamu kike yima magana haka tobari kijj Saraki shine magajina duk da yake qarami cikin su to tamkar shine babba sabida shine namiji idan bana guri shine jagoran su dan haka yanada cikakkiyar damar za'bama Bahijjat miji dukda tana matsayin Aunty shi sannan daga yau karki sake fad'in kalmar hauka akan Saraki Shiba hauka yakeyiba lalurace Allah yasaukar mishi Kuma in sha Allah tazo 'karshe mama Ina godiya agareku dakuka babbatar ma Saraki cewa ya Isa dakoma cikin masarautar nan Ammin Saraki kisanar da Zaffar na amince yaturo magabatan shi "

Daga haka Sarki Zaid yafita Ammin da Umma Suma sallama sukayima mama suka bar parlour itako hjy Himla afusace tabar parlour tana shiga cikin parlour ta tad'auki wayarta takira bokan ta yanad'agawa tace " boka akwai matsala fa wannan banzan Saraki yana lalata min komi dan Allah kasheshi nike buqata tuntuni amma kakasa haba boka gaskiya nagaji idan bazaka iyaba to kasanar dani nacanza guri " dariya boka yasaki sannan yace " haba hjy Himla karki bani kunya Mana komi yakusa zuwa qarshe yanzu matsalar mu wannan matar tashice bamu iya yimata komi sabida tanatare da addu'a akoda yaushe Kuma ayanzu haka tafara shayer dashi addu'ar Kuma yafara samun sau'ki amma yanzu matakin dana d'auka shine zamu gigita ta tahanyar bata tsoro zamusa adinga furgitata sosai ta yarda dole zatabar gidan ki saurara kiji Nan kusa zatabar gidan Maher "

Ajiyar zuciya hjy Himla tayi sannan tace " to naji amma inaso kalalata auran Bahijjat da Zaffar da'ake Shirin qullawa " dariya yabushe da ita sannan yace " angama kisaurari ayki kawai amma inajiran ganin saqon Kaya masu nauyi " tsaki hjy Himla taja tace " yaushe na ayko akakawo maka kud'i to kasani inajiran naga ayki yaci kafin nasake ayko dawasu kayan " daga haka takashe wayar "

Zama tayi kan cushion tana huci dede lokacin Abdul yashigo ganin yadda ran Mahaifiyar tashi yake a hatashe yasa Abdul dakatawa tambayar ta yashigayi cikin fushi Abdul yace " Mom wallahi tunda aka hanani auran Bahijjat sena lalata mata rayuwa wallahi senasata taje gidan mijin batare da budurci ba tuni nike kwad'ayin surar jikin Bahijjat Mom zasunan ni suka hana auran Bahijjat " murmushin mugunta hjy Himla tayi tace " kayi duk abinda kake ganin zaisaka kahuce my son " murmushi yasaki yace " zanyi kuwa Mom

USA

Akwana atashi babu wuya ayau ne doctor yake kan hanyar zuwa USA Abbee Kuma yasaka a Nigeria abubuwa dayawa sunfaru kafin wannan lokacin sosai Iftahal tayi muguwar rama sabida ko abinci bata iyaci hatta ruwa idan zatasha inba tayi addui ba seyakoma kamar jini duk tagama furgicewa yauma kamar kullum hankalin ta cikin Matu'kar tashe yake Sabida tayi duk tunanin dayakamata amma tarasa yadda zatayi wajan hana doctor yin wannan allurar shigowar Maher yasa Iftahal saurin zaunawa isowa yayi yazauna kan cushion ciro sigari yayi yakunna yafarasha kallonshi Iftahal tashigayi sosai tanajin matu'kar tausayin shi da tsananin qaunar shi cikin zuciyar ta d'an dubanta yayi se'alokacin yaga tayi wata irin muguwar rama sosai yaji mamakin hakan a hankali yadubeta yace

" Iftiih!!!! meye dalilin ramarki nalura bakison cin aminci sannan kinsan nace idan har kinason nayi miki abinda kike so to yazama dole ki kwantar da hankalin ki amma bakiji magana taba " cikin raunin murya Iftahal tace " bahaka bane Prince kusan 1 week kenan banajin dad'in jikina shine kawai amma Babu wata damuwa " jinjina Kai yayi sannan yamiqe yace " tashi muje Asibiti " daga haka yanufi hanyar fita cikin sanyin jiki tamiqe dan Babu yadda zatayi tabbas batajin dad'in jikinta to amma batason zuwa asibiti d'an tsayawa tayi tace " am Prince nifa banason zuwa asibiti nan naji sauqi sosai " wata irin harara yasakar mata dole tashiga bedroom ta d'akko gyalenta tana fitowa yawatsa mata wani irin kallo yace " bana buqatar shigar banza " duban mayafin tayi ba qarami bane Kuma yarufe mata jiki sosai " dole takoma ta d'akko hijab tafito suka fita

Nigeria

Sarki Zaid da waziri da liman suka sauka Nigeria cikin babban birnin tarayya wato Abuja basusha wahala ba wajan Isa gidan Alhaji Ishaq wato minister kud'i sosai akayimusu tarba tamusamman bayan sunhuta suka zauna cikin ke'bantaccen parlour duban Alhaji Ishaq Sarki Zaid yayi sannan yace " Alhaji kasan daga Egypt muke tun zuwanmu amma zansake sanar dake sunana Zaid Irfan wato Sarkin qasar Egypt ayanzu nine mahaifin Maher wato mijin 'yarka Iftahal Alhaji nataso daga Egypt ne har nan Nigeria dan baka ha'kuri akan abinda Maher yayi shine yakeda lefi ba Iftahal ba sabida ita FURUCI!!!! tayi bada niyar yin aure ba amma FURUCIN!!!! yazama dalilin auran su to mud'auka wannan abun daga Allan ne tunda kaga hakan tafaru to Allah kad'ai yasan dalilin haka iname baka ha'kuri Kuma Ina taya Iftahal da Maher roqon ka akan kayafe musu dan Allah musamman Iftahal kasan fushin iyaye akan 'ya'yan su babbar matsalace dan Allah kayi ha'kuri sannan ayanzu inajiran duk wani bayani akan yadda kuke shirya naku auran zamubi dukkan wata al'ada taku aure de anriga anyi duk mubar wa Allah ikon shi "

Mi'kewa Alhaji Ishaq yayi sannan yace " nayi farincikin zuwanku hakan yasa na tabbatar kai Sarki ne Mai adalci cikin masarautar ka tunda har ka it's tasowa daga Egypt zuwa Nigeria akan bani ha'kuri dakuma neman yafiya nagode sosai amma sede wani abu 1 ni banayin magana nacanza bazan iya maida Iftahal matsayin 'yataba nariga nayafeta gareku nikam banida wata 'ya maisuna Iftahal kusani nayafe mata Amma bana bu'katar sake ganinta arayuwata har abada nagode sosai Maimartaba inatayaka munar samun qaruwar wata 'yar wato Iftahal " mi'kewa Saraki Zaid yayi yace " nagode sosai daga yafe mata Kuma nayi matu'kar farinciki dabani 'yah mai hankali da tarbiyya irin Iftahal muzamu koma fatan alkairi ga sadakin Iftahal Nan " saurin juyowa Alhaji yayi yace banida alaqa da sadakin 'yar daba tawaba dan haka bana bu'katar ganin su " sake Sarki Zaid yayi yafita waziri ne yad'akko kud'in suka fito hotel suka nufa Sarki Zaid sosai yashiga damuwa akan yadda Alhaji Ishaq yayi fushi da Iftahal

USA

Suna Isa asibiti doctor Sera tayima Iftahal tambayoyi sosai bayan haka aka d'ibi jininta akashiga gwadawa bayan wani lokaci doctor Sera tadawo zama tayi tadubi Maher da Iftahal tayi murmushi tace " Prince ina tayaka murna gimbiya tanada ciki tsawon 5 weeks " cikin matu'kar mamaki Maher yadubi Iftahal zaro ido tayi tadafe qirjinta tsayin lokaci yakasa denayimata kallon mamaki itakuma takasa cewa komi kuma takasa d'auke idon ta daga kanshi juyawa yayi yafita afusace batare dayace komiba


Comments please

_Marmny Zarah_ 🀝🏻πŸ₯°
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 23 to 24

Cikin matu'kar razana Iftahal tadubi Doctor Sera tace " doctor wai dagaske cikine dani ? " sake tabbatar mata doctor tayi sosai hankalin Iftahal yatashi d'an dedeta natsuwar ta tayi sannan tace

" Am doctor kibani allurar bacci idan naje gida zanyima Prince sabida bayasamun bacci sosai tambayoyi doctor tashiga yimata sosai sannan tabata cikin mutuwar jiki Iftahal tafito Koda tafito babu ko alamar Maher agurin sosai hankalin ta yasake tashi tunanin mafita tashigayi amma tarasa wasu irin hawaye masu zafi taji suna sakkowa daga cikin idanunta tsayin lokaci tarasa abinyi isowar wata mota tasa Iftahal d'an ja baya cikin sauri Shanwul yafito yanufo inda take ganin tana zubda hawaye yasa Shanwul saurin cewa " gimbiya lfy ? " Saurin share jawayen nata tayi sannan tace " lfy Lau kaina yakeyin ciwo " jinjina Kai yayi badan ya gamsuba cikin girmamawa yace " Prince ne yace nazo nad'aukeki amma nayi mamakin haka sabida naga shima gida yayi " d'an murmushin ya'ke Iftahal tayi tace " kajika sekace bakasan halin Prince ba dubani akatsaya yi shine yace shi bazai tsayaba " jinjina Kai Shanwul yayi kafin yace wani abu Iftahal tanufi mota dan batason sakeyin wata magana cikin sauri Shanwul yabu'de mata motar tashiga a cikin motar Iftahal tahad'a wannan allurar cikin sirinji bayan tagama tadubi Shanwul tace

" Doctor ya iso kuwa ? " Cikin sauri yace tun bayan fitar ku babu jimawa jin haka yasa Iftahal saurin cewa dan Allah kayi sauri ka kaini gida " jin haka yasa Shanwul sake taka mota suna isa tafito cikin sauri tanufi ciki tana shiga tahangi doctor yana neman jijiya zeyimai allurar cikin sauri ta'karasa fige allurar tayi saurin juyowa doctor yayi shikuma Maher yami'ke wani irin kallo yashiga yimata saurin dedeta kanta tayi tace

" Haba Prince kasanfa nace maka daga yanzu nice wadda zandinga yima allura tunda kasan abunda nike karanta kenan amma shine kaqi jirana ? "

Rai 'bace Maher yace " bashi allurar nan tun kafin ranki ya'baci " ganin yadda yahad'e fuska yasa Iftahal miqa mishi tajuya tabar gurin tana shiga bedroom tasauke ajiyr zuciya had'ida fad'in nagode ma Allah Prince yau sede kasha bacci kawai doctor in sha Allah muguwar allurar ka tadena shiga cikin jikin Prince fiddo da allurar tayi tana dubawa alokacin da ta amsa kasancewar hijab ne jikinta yasa tayi saurin canza allurar data baccin data amso a asibiti

Zama tayi bakin bed tashiga tunanin yadda zatayi wajan fahimtar da Maher kuka tasaki Mai tsuma zuciya se ayanzu tayi nadamar rashin sanar da Maher batun fyad'en a parlour kuwa sosai doctor hankalin shi yatashi yayi yazon Iftahal tagane komine amma dayaji abinda tace se yad'an samu natsuwa Yana amsar allurar yayi saurin yima Maher sabida Kar akuma samun wata matsalar ana gama allurar Maher yami'ke yanufi bedroom d'in Iftahal yana shiga tayi saurin mi'kewa cikin zafin rai da dakakkiyar murya yace

" Ke yazama dole kisanar dani uban wannan cikin naki idan kuma kikaqi to wallahi zanyimiki hukunci mafi muni a rayuwar ki sekinyi nadamar sanina ke bama nadamar saninaba har nadamar zuwanki duniya sekinyi " wani irin kuka Iftahal tasaki ta durqushe saman gyuwoyin ta a gabanshi

Tofa danjin mak Iftahal zatace se Allah yahad'a mu a page nagaba gobe in sha Allah kuyi ha'kuri da wannan

Comments please yawan comments yawan typing

_Marmny Zarah ce_ 🀝🏻πŸ₯°πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK


IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 25 to 26

Cikin kuka tace " Prince wallahi Babu Wanda yakeda alaqa da wannan cikin se Kai Kai ne uban shi lokacin daka samar dashi bakacikin hayyacin ka tsoran samun rashin fahimtar ka yasani yin shiru zan iya yimaka rantsuwa da rayuwata wannan cikin bashida wani uba se k...... Dakatar da ita yayi cikin tsawa dafad'in " dakata karki maidani marar hankalin babu yadda za'ayi nayarda dake balle na amshi cikin dabanawa dan haka kiyi gaggawar neman uban shi wallahi badan alqawarin dana d'aukarma zuciyata ba da ayau sekin bar gidana amma kisani daga yay bana buqatar ganinki a kusa dani idan ina parlour to yazama dole ke ki kasance cikin bedroom dan bana buqatar ganin fuskarki "

Juyawa yayi zaibar bedroom d'in cikin fusata Iftahal tayi saurin shan gabanshi kama hannun shi tayi murya asarqe tace " wallahi Prince dagaske nikeyi kayarda dani wallahi kaine " fisge hannun shi yayi cikin fushi yayi hanyar fita seda yakai bakin qofar yatsaya yace " karki sake kuskuran zuwa kusadani balle ta'ba jikina idan Kuma bakijiba zakisha mamaki "

Daga haka yafita afusace wani irin kuka Iftahal tasaki shiko Maher Yana fita yanufi saman shi Zama yayi bakin bed yanajin zuciyar shi tanayin matuqar quna sosai yakejin haushin Iftahal ayanzu jiyakeyi babu wadda yatsana duk duniya kamar Iftahal Babu jimawa yaji wani irin bacci yataso mishi dole yahaye saman bed ya kwanta miqewa Iftahal tayi cikin sanyin jiki da fad'uwar gaba tafito saman Maher tanufa

Doctor zaune cikin bedroom wata 'kwaya yaciro cikin aljihun wandanshi ya kalleta yasaki murmushi sannan yace " yau zakibar duniya senaga tayaya zakibama Prince kariya " takowa yayi ahankali yaleqo parlour ganin Iftahal yayi tanufi saman Maher hakan yabashi damar fitowa nufar bedroom d'in Iftahal yayi cikin sauri yana shiga yabud'e freezer parlour ta yad'akko robar ruwa yajefa 'kwayar ciki ya girgiza yarufe yafita cikin sauri bedroom d'in dayasauka yakoma yana shiga yakira wayar Alhaji Tukur bugu 2 yad'aga wata irin dariya doctor yasaki yace " Alhaji Tukur angama nayima Maher wannan allurar itakuma nasamata wannan qwayar daga zaran tasha shikenan babu labarinta babu kuma wanda zasan abinda tasha sede awayi gari tamutu " dariya sosai Alhaji Tukur yasaki sannan yace " yayi dede doctor aykinka yanayin kyau zakaji alert mai nauyi yanzunnan " Sosai doctor yacika da farinciki yayi godiya

Iftahal tana shiga cikin bedroom d'in Maher tahangeshi saman bed kwance ajiyar zuciya tasauke tanufi bakin bed d'in kallon shi tashigayi sosai tanajin matuqar qaunar shi nasake shigarta zama tayi bakin bed tafara karanto addu'a kamar yadda wannan tsohon yabata bayan tagama tashafi kanshi sannan tashiga Kiran sunan " Saraki Saraki kusan sau 4 sannan taga yabud'e idonshi ahankali yasaukesu kanta cikin sauri yatashi zaune wani irin murmushi yasaker mata yajawota jikin shi saurin jabaya tayi tafashe da kuka ganin yadda idanunta yake zubda hawaye yasa Saraki rud'ewa jawota yasakeyi tasake fizgewa sosai hankalin shi yatashi yamiqe cikin raunin murya yace " haba my Wife kisanar dani maiyake damunki haba dan Allah nimafa zan iya yin kuka " jawota yasakeyi tasake fashewa da kuka tace

" Saraki ciki ne dani kayi sanadin sakani cikin masifa tayaya zan sa Maher ya amince cewa wannan cikin nashine ? nashiga 3 Saraki Yaya zanyi ? ina cikin tashin hankali Saraki Zuciya ta tanayin zafi tamkar zata qone kafitar dani cikin wannan tashin hankali " sosai Saraki yarud'e cikin raunin murya yace " My Wife bangane abinda kike nufiba menene yafaru Kuma maiye ciki ? Jin hakan yasa Iftahal ciro kanta daga cikin qirjinshi tace " kana nufin bakasan abinda ake kira cikiba ? to ciki nahaihuwa Ina nufin nakusa haihuwar yaro " duk da haka amma Saraki baigane abinda Iftahal take nufiba sosai Iftahal takeyimai misali daqyar yagane wani irin murmushi yasaki yace " kenan zamu zama mu 3 cikin duniyar mu " wata irin runguma yayi mata yace " my wife nayi farinciki zamusamu yaro shikenan zan zama Dady ko kamar yadda rannan naji wani yaro cikin TV nan yanacema baban shi " jin haka yasa Iftahal sake fashewa da kuka tace " naso ace Maher shine yakeyin wannan murnar sabida shine zahiri na bakaiba Saraki Kai wani abune daban bakada wani........ "

" Amfani ko haka zakice My Wife niko nikeda amfani agareki tunda nine nazama silar samuwar wannan babyn sannan kisani inajin qunar zuciya idan kika nunamin Maher yafini mahimmanci agareni My Wife nine dadyn babyn ba Maher ba Kuma Ina tsananin sonshi dan Allah kimanta da wancan Maher d'in bashida abinda zai baki kitaho gareni zan baki duk kan alkairi dan Allah My Wife kibar wannan kukan inajin zafin hakan cikin zuciya ta Kuma kaina Yana sarawa " yaqarashe fad'ar hakan yana share qwallar data gangaro saman kyakkyawar fuskar shi sosai Iftahal tashiga kallon shi sabida matuqar mamaki cusa kanta tayi cikin qirjinshi tace " haba Saraki na banason ganin wannan qwallar asanina Saraki na zuciyar shi tsaye take abune mai wuya ganin hawaye shi dan Allah kabari nima nabari " murmushi yasake yi yace " idan Kika bari nima zan bari " sake tabbatar mishi tayi tabari janta yayi saman bed din yacusa hannunshi cikin rigar ta saurin riqe mishi hannun tayi cikin raunin murya yace " dan Allah my wife karki hanani ganin yadda ya marayrayce mata yasa tasakar mishi hannun saka hannun nashi yayi yajanye rigar tata wani irin nishi yasaki sabida yadda yayi ido 4 da breast d'in ta nan take jikin shi yad'auki rawa hannu yasa yafara shafar su cikin sauri sauri

Sosai yafara rud'ewa kafin wani lokaci yafara fita cikin hayyacin shi qoqarin cimma burinshi yashiga yi ganin haka yasa Iftahal saurin riqe hannun shi cikin raunin murya tace " kayi ha'kuri Saraki banida kafiya fa " fisge hannun ta yayi yasake maidawa saman breast d'in ta sake riqe hannun tayi cikin fushi da tsawa yace " kibarni my wife kullum haka kike fad'a to wallahi yau bazan barkiba maiyasa kika bari nasan mahimmancin abun nasan dad'in shi sekuma kihanani sanadin yin shi yasa zamu samu baby dan haka bazan iya ha'kuri ba yau daga haka yasake cigaba da sharrafara kafin wani lokaci tuni yasata duk jikinta yayi sanyi tanaji tana gani yashiga kusantar ta tayi tunanin zataji zafi kamar wancan ranar setaji akasin haka sed'an abinda ba'a rasaba tsayin lokaci Saraki yana aykin abu 1 sannan yasamu natsuwa sake jawota yayi yarungumai cikin tsananin soyayyar ta itako Iftahal baqaramin wahala tashaba cikin zuciyar ta tace

" Inama ace asalin Sarakin ne wannan danasamu farinciki marar misali Allah kasa yasamu lafiya cikin gaggawa yatuna dakomi ganin yanashirin yin bacci yasa Iftahal cemai yatashi suyi wanka babu musu yami'ke yasureta cak har cikin toilet d'in tare sukayi wanka suka fito sashi tayi yacanza kaya sannan suka koma suka kwanta babu jimawa bacci yayi gaba dashi tashi Iftahal tayi tashiga kallon shi yadda yakeyin baccin cikin natsuwa tsayin lokaci tana kallon shi sannan tafita daga bedroom jikin ta duk babu qwari

Nigeria

Shigowa cikin parlour Abba yayi hannun shi riqeda invitation card dayawa Zama yayi yakira Ummi cikin sauri tafito daga bedroom Zama tayi kusada shi miqama mata invitation d'in yayi yace " gashi nan kirabama duk wanda yadace kiramin Shukura " babu mushi tashiga kiran Shukura cikin sanyin jiki tafito daga gefe tazauna tace barka da dawowa Abba amsawa yayi cikin farinciki " yauwa Shukura ga invitation card Nan seki rabama qawayen ki da duk wanda yadace sannan kitashi kije zakuyi magana da Zayyat yana part d'in su " jin haka yasa Shukura jin wani irin 'bacin rai to amma babu yadda ta'iya dole tami'ke tafita cikin 'bacin rai tashiga cikin part d'in nashi zaune Zayyat yake hannun shi riqeda waya yanatafaman chart ko Zama batayiba tace " maiye dalilin ka nason ganina " duban ta yayi yace

" Ikon Allah to kizauna mana kiji " tsaki Shukura tasaki tace Allah yasauwa'ke nazauna nayi mai kaga idan bakashirya sanar daniba nizanyi tafiyata kasan bana ciki da Sha shanci " miqewa Zayyat yayi yace " Ok nikam Ina matu'kar son Sha shanci shinema dalilin Kiran naki dama tambayar ki zanyi size din fant da burar ki shine dalilin Kiran idan kinshirya sanar dani ina saurara idan kuma sekinyi tunani to Zaki iya tafiya " daga haka Zayyat yacigaba da latsa wayar shi Sabida matu'kar 'bacin rai Shukura kasa motsawa tayi balle tace wani abu

USA

Iftahal tana shiga cikin bedroom tatsaya a parlour bud'e freezer tayi wannan robar ruwan tad'akko tabud'e zatasha

Comments please

_Marmny Zarah ce_ 🀝🏻πŸ₯°
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸



Please Login or Register in order to submit comment