Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

imanin bazaki iya kashe baby ba muje gida " janye hannun ta gimbiya Bahijjat tayi tace " bazan koma gidan kaba Zaffar sabida abu 2 na farko nasake tabbatarwa Mahaifiyar ka bata sona sannan bazan iya cigaba dazama a cikin gidan kaba bana ganin baby hakan babban tashin hankali ne agareni " taqarashe fad'ar hakan cikin tsananin kuka

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_ πŸ‘ŒπŸ»πŸ€πŸ»πŸ₯°
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 69 to 70

Cikin tashin hankali matuqa Akeey Zaffar yace haba " my world karkimin haka kimanta dabatun Momy ay yanzu kowa yagane gaskiya Kuma kowa ya tabbatar bakida lefi idan kikamin haka toni Yaya zanyi Babu baby Kuma baki wane irin tashin hankali kikeso nashiga ? " Kafin tayi magana Barrister Maher yadafa bayanta cikin qayatatcen murmushi shi yace " haba Aunty na karkiyi haka kibi mijinki Kuma inaso daga yau kininka farincikin dakike bashi kihad'a hadda na baby kibashi duka kimanta da zancen Momy kibarta da abinda dazai dameta sabida na tabbatar ayanzu taji nauyin abundatayi miki to kibarta da wannan kuje gida muma zamutaho wajan jana'idar kuyi haquri inasakeyin gaisuwa agareku Allah yajiqan baby kuma in Sha Allah namuku alqawarin Sena gano duk Wanda yakeda saka hannu cikin wannan kisan azaman kotu nagaba Kuma in sha Allah wannan zaman shine naqarshe "

Daga haka Maher yajuya yashiga mota duban Akeey Zaffar Gimbiya Bahijjat tayi idanunta cike tab dahawaye tace " kayi haquri nakasa manta munanan maganganun Momy ne shiyasa nace haka har abada daniiiiii da kaiiiiii da'imannnnn da'imannnnn " cikin rawar murya tafad'i hakan rungumai ta yayi hawaye suna gangarowa daga cikin dananun shi dede lokacin ACP Kabir ya'iso gurinsu Sallama yayi musu Akeey Zaffar ya amsa cikin tausayawa yace

" Ina fatan babu wanda yamin muguwar fassara idan dabanyi hakaba tayaya za'agano wanda yakashe mana baby har ahukuntashi ? Bahijjat banyi hakan da niyyar cutar dakeba tabbas nima zuciya ta takasa yarda to amma a wannan lokacin dole kece abin zargi gaskiya kinyi sa'a Barrister Maher yayi tako Ina cikin lokaci kad'an zama 1 a kotu har yagano wani qulli abinda mu muka kasa gashi har anwankeki dan Allah karkibar shi yakoma USA muna buqatar irin shi cikin qasarmu Zaffar Ina fatan bakayimin muguwar fassara ba fatan abotarmu tana nan "

Dafa kafadar shi Zaffar yayi yace " maiyasa zan qullaceka bayan kaine kayi jagora wajan gano Wanda yakashe min baby na dabaka d'aka lamarin ba nikam alokacin bazan sanar makowaba zan rufe abin sabida inajin tsoran Kar narasa matata sannan Kai zargi kayi itako Momy na Kai tsaye tace itace tayi kisan kenan itama senabarta a a Kabir muna tare har abada godiyama yakama ta nayimaka " duban Gimbiya Bahijjat yayi yace " amma kamar gimbiya taka tanajin haushina karki manta nifa hukumane haqqine akaina na binciki duk wani mai lefi afuwan gimbiya Bahijjat " jinjina Kai tayi tace " haba yawuce amma daba'a gano wannan gaskiyar ba shikenan kayi jagora wajan kasheni " kafin yayi magana

A Dede lokacin akfito da Ayna za'a nufi gidan yari da'ita cikin kuka Momy tadubeta tace

" Maiye wannan kika aykata Ayna wannan wane irin baqin ciki ne ? dawane ido zan kalli gimbiya Bahijjat har ga Allah nayi zaton itace Kuma kece Kika Dasamin shakka akanta sabida akodayau she kece kike cemin tana cutar da baby a bayan idon Zaffar ashe qarya kikeyi nazata tuni kin haqura da Zaffar tunda gashi ayanzu kin kusa aure amma kafin ayi wannan zaman na kotu dan Kam yanzu banga Wanda zai yarda ki auri d'anshiba idanma Wai kinrayu kenan ba'a kashekiba "

Kuka sosai Ayna takeyi tace " wallahi Momy yaudarata sukayi gashi bansan kosuwaye suba nashiga 3 Momy dan Allah kisamu Barrister Maher yashiga cikin wannan lamarin yazana ni nala'be a bayanshi dan Allah Momy banaso namutu yanzu " cikin takaici Momy tace " dawane idon zan dubi Saraki nayi wannan maganar dashi ay nariga nayi kuskure d....... " kafin Momy taqarasa maganar ta sukaji harbin bindiga kafin a Ankara Ayna tafad'i cikin kokonto 2 mutuwa ko rayuwa cikin wani hali cikin sauri ACP Kabir yabada umarnin a kamo koma waye su Barrister Maher kuwa tuni sukam sunbar gurin kafin faruwar lamarin suna gaf dashiga cikin masarautar Kiran Iftahal yashigo cikin wayar shi murmushi yayi yad'aga jin kukanta yasashi tashi zaune dede daga kishin gid'en dayake yace

" Lafiya Sonahh yi gaggawar sanar dani abinda yake faruwa " cikin kuka tace " Shanwul yafita dasu Irfan supermarket sabida sun matsa sosai bayan sungama sun fito shine wasu sukazo aguje suka d'auke Ibban da Islam suka sasu cikin mota suka gud........."

Wata irin tsawa Maher yayi Mata wadda tasaka driver jan wani irin mugun burki " garin Yaya haba Sonahh wannan wane irin Sha Shanci ne maiyasa yafita babu security Kuma baseda nace karki bari sufitaba ? " Yanzu inashi Sha Sha Shan Shanwul d'in yake inasu Irfan ? "

Cikin kuka take " gashi nan Suma gasunan sekuka sukeyi amma Kaka yabama security umarnin nemosu duk inda suke " Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuuunn Sonahh nashiga 3 "

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 71 to 72

Kashe wayar yayi su Ammin kuwa basusan abinda yake faruwa ba sabida ba mota d'aya suke da Maher ba suna Isa Maher ko jira a gyara parking baiyiba yafito yanu part d'in nasu cikin sauri yana shiga Irfan yarugo ya riqe qafafunshi yana kuka " dad Ina Ibban da Islam dad kadawomana dasu dad idan su Islam basudawoba bazan sake cin abinci ba " cewar Iman daketa shar'bar kuka kasa Koda motsa yatsan shi Maher yayi sabida tunanin shi yatsaya cak yamarasa maizeyi miqewa tsaye Iftahal tayi tanufi gaban Maher wata paper tamiqa mishi cikin kuka tace " sun jefar da wannan paper bayan sun d'auki su Ibban amma Shanwul yace kamar basusan sun jefarba nakasa bud'e cikinta sabida bansan mai zanganiba "

Amsa Maher yayi cikin sanyin jiki yabud'e rubutu ne kamar haka

_haba kekuwa karki damu ayau zanyi wani ayki wanda zansamu wasu manyan kud'i komi zezama dede aykin wani babban mutun ne sunanshi Alhaji Tukur dawata hjy idan nagama zanzo karki nemi waccan number ga wacce zaki sameni nan ************ sannan dan Allah baby Ina buqatar kud'i koda rancene kiyi kituromin ta wannan account number ********** Ina jiranki senajiki my baby "

Murmushi Maher yayi yadubi Iftahal yace " kwantar da hankalin ki my Sonahh namiki alqawarin zandawo miki dasu Ibban nan kusa " lallashin yaran yashigayi Dede lokacin su Ammin suka shigo cikin tashin hankali kwantar musu da hankalin Maher yayi sannan yakuma fita a qofar kotu kuwa cikin gaggawa akanufi asibiti da Ayna cikin gaggawa akacire bullet d'in dayafasa kashin kafadar ta sannan aka gyara gurin duban ACP Kabir doctor yayi yace

Tabbas kasheta akasoyi amma anyi rashin sa'a tana raye Kuma zata farka zuwa yamma in Sha Allah " jinjina Kai ACP Kabir yayi sannan yasa akasa jami'an tsaro masu yawa ciki dawajan asibitin

Gidan hjy Himla su jaga suka nufa dasu Ibban kallon yaran tayi tasaki murmushi tace " gaskiya aykinku yayi kyau amma naso duka kuka kwasomin yaran amma dukda hakan yayi kuje senanemeku fita sukayi duban Alhaji Tukur tayi dake gefanta tace " Yaya batun Ayna " wata irin dariya yayi yace inada tabbacin tana kiyama ayanzu haka Kuma basusamu nasarar Kama Wanda yayi harbin ba Sha Sha shun Wai sunkaita asibiti "

Duban su Ibban Alhaji Tukur yayi yace " Kai kutashi tsaye " ko kallonshi yara basuyiba sakeyin tsawar yayi nanma shiru cikin mamaki yace " Kai waiku bakuda tsoro ne ? " duban shi Ibban yayi yace " mu dad da mom tsoran Allah sukace muji banawani ba kuma sunce idan masifa tasamemu mudinga cewa Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuuunn la'ilaha illa antassubahanaka inni kuntu minazzalumin zamuji zuciyar mu tayi sanyi Kuma Allah zai kawo mana mafita sabida babu wanda ya'isa yayima wani abinda Allah baiyimai ba "
Zaro ido Hjy Himla tayi tadubi Alhaji Tukur tace " kaji yara se shegen wayon tsiya " jinjina Kai yayi yace haka kuwa amma aymu buqatar mu musashi yajanye wannan shari'ar gara yabama wani dan wallahi idan har mukabari yasake shiga kotu tofa tabbas asirinmu yagama tonuwa gaskiya munyi kuskuran saka waccan banzar yarinyar cikin aykinmu gashi komi Yana neman lalace mana "

Murmushi Hjy Himla tayi tace " Ina babu abinda zaifaru Saraki zai iya yin komi sabida yaranshi Kuma zai iya barin komi sabida su tunda mukasamu nasanar sace yaranshi komi zaitafi dede " Kama hannun Ibban da Islam tayi tanufi cikin bedroom dasu

Babu jimawa tafito Kai tsaye tanufi Alhaji Tukur zama tayi kan cinyar shi tashiga shafashi turrr dai da irin wannan rayuwar cigaba da aykata masha arsu sukayi jan shi tayi zuwa wani bedroom d'in nadaban tsayin lokaci suna aykin abu 1 sannan suka fito kallon bedroom d'in da'akasakasu Ibban yayi yace kibasu abinci dan tafiya zanyi dasu na tabbatar jininsu zaiyimin amfani " duban shi Hjy Himla tayi tace

" A a Alhaji Tukur babu kisan wa'innan yaran cikin wannan tsarin mude wannan shari'ar mukeso yajanye idan muka kashe yarannan tofa wallahi zamujama kanmu bala'i babba "

Tsaki Alhaji Tukur yayi yace " aykin banza kin manta burina akan Maher da uwarshi nikam banason farincikin su idan nakashesu to tabbas zasuyi baqin ciki nahar abada kamar yadda Zaffar da Gimbiya Bahijjat zasu kasance cikin baqin cikin rashin baby to inaso Sarauniya Batol da Saraki sukacance cikin baqin ciki fiye danasu dan haka zantafi dasu yanzu sabida idan nayi jinkiri zanyi rashin sa'a sabida yadda suke ambaton Allah zasu iya kubuce mana "

Yana kaiwa nan yanufi cikin bedroom d'in amma abin mamaki babu kowa saurin nufar toilet yayi nanma babu su duba ko'ina nacikin bedroom d'in yayi amma Babu su Ibban fitowa yayi cikin tashin hankali yadubi Hjy Himla yace

" Ina suke ? " Cikin mamaki tace " suwa " yaran Maher Mana basa cikin bedroom d'in ko Ina har cikin toilet naduba Kuma babu wata qofa tafita aciki " aguje Hjy Himla tashiga cikin bedroom d'in tasake dubawa sannan tafito cikin harabar gidan suka nufa duba ko Ina sukayi amma babu su tambayar mai gadi sukayi yace

" Hajiya kefa kikace naje nagano miki idan ankawo kayan Nan shine natafi dawowata kenan "

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”
πŸ’”
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* πŸ’“β£πŸ’˜

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... πŸ“–πŸ–Š

πŸ—‘πŸ’” FURUCI!!!!!πŸ’”πŸ—‘


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

πŸ…Ώ 73 to 74

Cikin tashin hankali suka dubi juna ciro wayar shi Alhaji Tukur yayi yakira yaran dayaba umarnin kamo su Ibban bayan and'aga yashiga tambayar shi cikin sauri cikin mamaki yace " haba Alhaji mukuma tayaya zamusan inda yara suke bacin munriga damun danqasu a hannun ku gaskiya kude duba kumamu Kam wallahi kud'in mu mukasani dan babu abinda yashafemu " tsawa Alhaji Tukur yasakar mishi yace " sannu mararkunya to Kam yazamadole kuzo kutayamu nemansu idan aka gansu semubiyaku kud'in ku " cikin fusata barbar yace " to Alhaji Tukur idan Kuma ba'agansu bafa ? " Wannan Kuma kutashafa idan banga yaraba tofa babu yadda za'ayi nabiya kud'i " kashe wayar shi yayi murmushi barbar yayi yadubi abokan aykin nashi yace

" Lalle kam Alhaji Tukur baisanmu bane muje kuga yadda zanyi masa "

Daga haka suka fita tafiya sukayi mai nisan gaske zuwa wata unguwa wadda babu yawan mutane sosai cikinta sannan suka tsaya kiran wayar Alhaji Tukur Barbar yayi bayan yad'aga yace

" Yanee Alhaji munsamesu guduwa sukayi kazo bayan wannan katon gidan gonar muna wajan amma kataho mana da kud'adanmu idan bahakaba to bazamu baka yaranba idan Kuma kadad'e zamuyi tafiyar mu sabida munada wani aykin bayan wannan " kafin Alhaji Tukur yace wani abu barbar yakashe wayar duban Hjy Himla yayi yace angansu bari naje na amsosu " tashi Hjy Himla tayi yadakatar da ita yace " kibari naje kinsan halin yan'iskan yarannan yanzu zandawo " cikin sauri yafita komawa tayi tazauna

Yana fita yashiga mota yajata aguje Kai tsaye wajan su barbar yanufa yanazuwa yakashe mota yafito fitowa barbar yayi daga la'ban dayake yanufoshi duban shi Alhaji Tukur yayi yace " Ina yaran ? " barbar yayi dariya yace " aydama nace maka sekabamu kud'in mu " ciro wayar shi Alhaji Tukur yayi yace bani account number ka " bashi barbar yayi dandanan 500,0000 suka shiga cikin account d'in barbar jinjina Kai barbar yayi yace " sun qaraso zomuje nabaka yaran " binshi Alhaji Tukur yayi suna Shan kwana wani yajagayo tabaya yashaqama Alhaji Tukur wata powder a hanci kafin wani lokaci Alhaji Tukur yafara gani dishi dishi cikin rud'ewa yace " Kai maikuke Shirin aykatawa ne "

Wata irin muguwar dariya barbar yayi yace " Kai dalla ware kusamin shi a mota kabiyamu wasu kud'i Yan kad'an shine keke neman renamana hankali to kuwa zakasha mamaki kusashi da sauri Kai shiga motar tashi itama munyi ceqwara ta " sashi sukayi cikin bot d'in mota suka bar gurin

Anyi lallashin duniya Amma Iftahal takasa denayin kuka shiko Maher tunda yafita baidawoba a gidan Akeey Zaffar kuwa ankawo gawar baby har anyi mata sutura duk dasu Sarki Zaid akayi jana'idar hadda barrister Maher daga nanne yabar gurin cikin tashin hankali Momy tanufi room d'in da'aka kwantar da Ayna Amma Sam akahanata shiga sabida ACP Kabir yace koda babanta ne yazo Kar asake abarashi yashiga dole takoma cikin qunar zuciya Mahaifiyar Ayna da Abban ta kuwa sunshiga cikin mugun tashin hankali

Duban agogon dake banne jikin bangon parlour ta Hjy Himla taduba tsaki taja sannan tasake Kiran wayar Alhaji Tukur akaro nababu adadi miqewa tayi cikin tashin hankali afili tace

" To Ina wannan mutumin yashiga ? badai nizai renama hankali ba ? ayko dana nunamishi nafishi iya shirya tuggu " Kiran wayar barbar tayi bayan yad'aga tace " Kai Ina Alhaji Tukur ? " cikin nuna rashin fahimta yace " kamarya fa Hjy ? nagade shi Alhaji Tukur bayaro bane qarami dazaki Kama nemanshi dan karya 'bata tuni mu munbashi yaran yatafiyar shi muma munkama gabanmu dan haka karki sake kirana idan Kuma Kika sake to wallahi sena wular dake "

Daga haka yakashe wayar shi cikin razana damaganar barbar Hjy Himla tashiga jagaye parlour dede lokacin Abdul yashigo cikin tashin hankali rungumai Hjy Himla yayi yace

" Momy nashiga 3 Lubna nacuceni tasakani cikin masifa Momy dan Allah ki ceceni nasan idan inadake banida wata damuwa Kuma na tabbatar Zaki tsayamin akan komi " sosai zuciyar Hjy Himla ta tsananta bugu cikin rawar baki tace "

" Kabar kukan sanar dani meke faruwa ? Mai Lubna tayi ? " cikin kuka yace " Momy Lubna ce tacemin nasaka kaf dukiyata cikin wata kwangila zansamu makudan kud'i jin zanyi kud'i sosai yasa nayarda nasiyar dakomi nawa batare dakin saniba hadda kadarorinki Momy amma dukda haka tacemin kud'in basu kaiba tasani naciyo bashin banking har 30 million amma Momy tun jiya nanemi Lubna narasa nakira wayarta batashiga se d'azu takirani da number dabata qasar nan ba tace min " Kai Sha Sha Sha kasani babu wata kwangila nayi hakanne dan kawai nakwashe kud'in ka duka kayi tunanin dama Wai sonka nikeyi Ina dukiyar kawai nikeso Kuma nasamu dan haka ni namabar qasar Egypt kaje kaida jakar uwar taka kusan yadda zakuyi kubiya bashin banking nan idan Kuma bahakaba kaje gidan yari idan kaga dama kasakeni idan Kuma kaga dama kabar igiyar auran nawa akanka nide bazakasake ganinaba har abada Sha Sha Sha kawai " cikin tashin hankali nanufi gidan su amma abin mamaki megadi yacemin Wai dama hayace suka Kama Kuma suntashi tun kwanaki 5 dasuka wuce " nashiga 3 Momy gidan danike ciki da wannan qaramin company kawai suka ragemin Koda nasiyar bazasu Kai kud'in banking dana amsaba dan Allah Momy kitaimaka banason zuwa gidan yari kece kike cemin bazanyi kukan rashin komiba Kuma Zaki tsayamin akan komi Momy........ "

Wata irin gigitacciyar tsawa tadaka mishi wadda tasashi saurin jabaya tundayake batata'ba yimai kwatankwacin irin wannan tsawar ba zama tayi aqasa tamiqe qafafu tsayin lokaci takasa cewa komi zuwacan

Tafasa wani irin ihu wanda yasa Abdul fita aguje kuka tasaki jin irin kukan da Hjy Himla takeyi yasa Abdul dawowa duban shi tayi cikin tashin hankali dafad'a tace

" Tabbas Kai Sha Sha Sha ne Lubna gaskiya tafad'a munacikin daula Amma lokaci d'aya kamaidamu mugayen matalauta nashiga 9 Abdul idan Kai 3 kashiga ni 9 nashiga Abdul dole sekaje gidan yari nan ayanzu Kam bazan iya yimaka jagora akan komiba Abdul kasakamu cikin tashin hankali "

Kuka Abdul yasaki yace " haba Momy to wallahi sede muje tare ay kinada hanyar samun fiyeda 30 million ga mahaifin ki Nan gakuma Yayanki nan Sarki Zaid gakuma Saraki d'an yayanki kaf d'in su kowa Don ne amma kibarni naje gidan yari Ina wallahi sede mutafi tare " wani irin baqinciki Hjy Himla taji yataso yatokare zuciyar ruri wayarta tad'auka da qyar ta'iya daga wayar cikin tashin hankali akace mata

" Hjy akwai babbar matsala fa Ayna tana raye kuma gashi gobene shiga kotu fa idan bakiyi wani abuba tofa tabbas munshiga 3 Hjy na tabbatar idan har akashiga kotu da Ayna gobe Kuma shima Barrister Maher yashiga tofa tabbas mukam munshiga cikin wahala nashiga 3 hjy Himla kinjefani cikin masifa " cikin wata irin murya Hjy Himla tace " garake shiga 3 kikayi nikuwa da cikin shiga 9 nike ayanzu kuwa nashiga 1000 bama 100 tabbas yazama dole nabar qasar nan ayau basegobeba kema kiyi takanki " daga haka takashe wayar tashiga cikin bedroom aguje shima Abdul binta yayi agujan

Ahankali Alhaji Tukur yake bud'e idanunshi saukesu yayi kan Maher cikin razana yazaro ido murmushi Maher yayi yace " kayi mamaki ko ? kad'an daga cikin basirar Barrister Maher Ibban Islam kuzo yaganki " duban yaran yayi cikin matuqar mamaki yace tayaya haka tafaru ? " Murmushi Maher yayi yace

" Kafara bani wannan amsar tukun da 500,0000 da 10 millions wanne yafi ? Cikin rawar baki yace 10 millions " murmushi Maher yasakeyi sannan yace " to sune nabiya akamin ayki 2 nafarko aka dawomin dayarana na biyu aka qwamusomin Kai wa'inda kasa suka sacemin yara suka kaimaka sune nasaka suka koma sukasake d'akkomin yarana har cikin bedroom d'in dakuka kaisu sauran bayanan yadda akayi zakajisu a kotu gobe in Sha Allah yarana muje ko dama nace ma mom d'in ku in Sha Allah zandawo Mata daku nan kusa "

Dariya Ibban yayi yaje kusada Alhaji Tukur yace " kagani dama munce maka Allah zaibamu mafita tunda mundogara dashi kaima idan dashi kadogara zamu gani " Jan kunnan shi Islam tayi tace " Ina Ina Ibban wannan baiyi Kama da wanda yadogara ga Allah ba daya dogara dashi dabaze tutar dakowaba balle qananan yara kamar mu muje gida d'an uwana Ina kewar Irfan da Iman muje muji abincin mom d'in mu Mai dad'i ta sumbacemu kamar yadda tasaba kullum sau 3 yau gashi iya 1 mukasamu " riqe hannun ta Ibban yayi yace " zamusamu na 2 yanzu idan munje " murmushi Maher yayi yace " kagani Alhaji Tukur har abada cikin farinciki zamu kasance kagudu kafin zuwa gobe idan zaka iya "



Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
πŸ—‘ *!!!FURUCI!!!* πŸ—‘
πŸ’”πŸ’”πŸ’”


Please Login or Register in order to submit comment