Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan, amma ina da baqo, sabon Alhajin nan da nai ne ya zo yau ma, sai ruwan nera yake min, yaushe zaka shigo?"


Tsaki yayi ya katse wayar ya qarasa rufe gate din ya shige gida, zama yayi a kujera, qamshin Aeeshaa ne yake dukan hancin shi, ido ya lumshe yana hango surar ta mai kyau, wani irin shauqin son kasnacewa da ita ne ya kama shi, no ta ya fara dubawa a wayar shi, ko saving bata samu arziqin a mata ba, nan take yayi saving da

"Ayshaa"


Sannan ya danna dn kiran ta,har ya fara shiga ya katse me zai ce mata?


Aeeshaa na zaune da Hajja da Baba General suna hira, taga flashing, dubawa tai taga no ne kawai, ajewa tayi,


"Wa ke kiran ki?da daren nan, 11 ta kusa fa,"



"Hajja ban san no ba flashing ne ma ba kira ba,"


"K ki kira kiji ko qaye mana, baki san me kiran ba ko yana da uziri amma ba kati,"


"K Hajja, bari na kira,"



Kiran no tayi, Hajja da Baba General suka ci gaba da hirar su.

Tayi ringing na farko Khaleefa ya na tinanin dauka ko bari, har ta katse bai tantance ba, kira ne ya sake shiga, dagawa yayi tare da amsa sallamar ta,



"Wato dan kin raina ni shine zaki fita daga gidannan ba da izini na ba ko? Wake da iko da ke daya wuce ni? Umarnin wa ya kamata ki bi tsakanin ni da Hajja?"


"Naka,"


Tashi tayi idon hajja akan ta, tana nazarin ta, nan take ta gano Khaleefa ne ya kira,murmushi tayi.


"Abinda ya faru shine na yi iya qoqarina Hajja ta bari ka dawo taqi, ni kuma bani da no ka, shi yasa, Hajja kuma taqi kiran ka tace sai ka dawo da kan ka,"



"Amma ai kome za ai ya kamata a fara sanar dani, ko dan an auramin ke sai aka ce banda iko ko 'yancin sawa da hanawa?"


Aeeshaa na jin ikon Allah yau, abinda ba ita ta aikata laifi ba da izinin magabatan su ta fita amma an tsare ta da fada, shiru ta masa ya gama fadan shi da surutun shi bata ce masa komai ba,sai hakuri datake ta jera bashi, sai da ya gama fadan sannan ya fara sakkowa,


"Ya cikin? Yana dai fita a hankali ko? Kina ganin alamar zubar shi ko?"


"Eh kullum yana fita kadan2,"๐Ÿ˜œ


Cikin murmushi take amsa masa.


"Murmushin me kk?"


Kaiii gano ta yake?๐Ÿ˜จnan da nan ta kama inda2,

"Dama naji dadi da ka kira ne kawai๐Ÿ™Š๐Ÿ™‰"


Rintse idon ta tayi, daga ina wannan maganar ta fito,....dan murmushi yayi shima,


"Koh?"


"Eh"

'Wayyoo meke damuna ne?.... ba komai kare qaryar da kikai ne ta farko ba wani abu ba'


"Kin kwanta ne?"


"A'a na dai koma dakina, kai fa?"


'Wayyooo Ummana what is wrong with me?'


"Ni na kwanta ke kawai nake son kasancewa da, amma an nuna min ban isa ba da iyalina an dauke min ke,"



Wani abu taji ya ratsa ta, wanda bata san meye shi ba,qanqame wayar tayi,tana sauraran sautin nimfashin shi, gaba daya ya saukar mata da kasala,



"Hello? Kna jina kuwa?"


"Ina jin ka,"


"Bakice komai ba"


"Yah Khaleefa kayi hakuri, ba laifina bane, da da yanda zan dana zo gare ka, kasan koda bamu son juna ba zan taba hana ka abinda Allah ya yi naka bane, bana daga cikin matan da suke sanya kan su cikin fushin Allah da sanen su, sai a bida kuskure,"


'Sarkin wa'azi,oho miki yau dake nake son na kashe arna ta wayar nan,bari nai amfani da wa'azin naki nima'


"Indai kin san haka ne to ya kamata ki ban haqqi na yanzu,"


"Yah Khaleefa ta yaya?"


"Baki sani ba?


"Eh tinda baka kusa bana kusa, ya zan na baka haqqin ka?"


Idon ta ne ya kawo hawaye,' Oh mutumin nan yana buqata ta kuma an fada mana in miji ya nemi matar shi bata biya masa buqatar shi ba Allah da mala'ikun shi na fushi da ita, yanzu ya zatai?'


"Kina jina ba?"


"Eh ina jin ka,"


"Yauwa tashi ki rufe qofa sosai da key,ki dawo,ki saka rigar baccin ki mai kyau a jikin ki, ki jira ni zan sake kiran ki, amma ta whatsapp ai naga kina yi ko?"



"Eh ina yi"


Kashe wayar yayi. Ta tashi ta leqa parlour va kowa, an kashe wuta, komawa tai tana jin kunya, dan ta san Hajja ta gano dawa take waya, umarnin Khaleefa ba wanda bata aikata ba, tana tinanin to zuwa zai ko ya abun yake?



Khaleefa kuwa daki ya koma ya cire kaya, ya bar boxern shi, ya haye gado, ya kunna laptop, nan ya shiga whatsapp, ya lalubo ta, vedio call ya kira yaji shiru, daya duba dai yaga bata online,tsaki yayi ya kira ta, yace ta kunna data, kunnawa tai ta kwanta, a zaton ta chatting zasuyi, sai mamakin su take, ohhh wato dan an raba su shine yanzu yake son ya na kula ta, taushe magana mao dadi ta taba shiga tsakanin su?



Yana ganin ta online har wani lashe harshe yake, kamar tsohon maye.


"Hey"


"Assalamu alaikum"


๐Ÿ™„
"Wa'alaikumussalam"



"Bari na kira ki vedio call, "


"Ok"


Hijab din ta ta dakko d sauri ta saka, aiko yana kira ta aje wayar yanda zai dinga ganin ta.


Khaleefa kafin ta amsa har ya zare boxern shi, yana jiran ta dauka, aiko tana dauka tai arba da Khaleefa hannun ta na rawa ta kashe, qirjin ta na bugawa, ko da suna tare ai bata taba ganin shi a haka ba tin ganin da ta masa a gidan su tana aimin sabon shi.


Meye hakan yake son yi,


Message ya turo mata yana ta zabga masifa, wai ta wulaqanta shi, yau sai ta kwana cikin fushin Allah, ya kira dan ya samu su yi abun su ta waya tinda an dauke ta, amma take neman wulaqantashi, to yanda ta wulaqanta shi itana sai Allah ya wulaqanta ta.


Kuka kawai take, tana karantawa, amma ai aikata hakan zai iya jawowa su aikata haramun, tinda in suka fara hirar da zata tada masu sha'awa dole zasu biyawa kan su buqata da hannayen su,hakan kuma haramun ne sosai to ya zatai ne? Ga shi can sai fushi yake da ita harda kira mata wulaqanta a wajen Allah,


"Kije ki riqe abin ki, xan kira wasu su ban abinda kk hana min"


Dummmm gaban ta ya yi muguwar faduwa, kiran shi ta dinga yi amma yaqi dagawa, daga qarshe ya kashe wayar shi, message tai ta turawa ta whatsapp tana bashi hakuri yaqi dubawa ma kuma tana ganin shi online, ina zata saka kan ta yau tinani tai tinda yaqi saurarar uzirin ta shikenan, gwanda ta barshi ai ba yau ya saba ba dama.



"Kaji tsoron Allah a dik abinda kk aikatawa yana ganin ka,"




"Da tsoron ki zan ji, kar ki kawon raini dan kinga na nemi wani abu wajen ki, haqqina ne ba dan haka ba ke baki isa na tsaya ina maki magana ba ma,"



Kashe data tayi, ta kwanta, can ta tashi, ta kunna, still yana online, shiga contact din ta tayi, tana duba numbers da take da, tana cikin dubawa taga Hadiza ma na whatsapp ashe, murmushi tayi, tana shiga contact din hadizan sai ta ga tana online,murmushi ta sake yi,



"Ohh Hadixa ko dawa ake hira da tsohon daren nan?"


Sallama ta mata, Hadiza ta gani taqi amsawa, can ba a jima ba sai taga message daga Khaleefa, da sauri ta duba,


"Ke sauka online, in kuma da wani qaton kike hira sai naji,"


Baki bude cike da mamaki ta sauka, wai ita ke magana da wani qaton, to a ina?lallai Khaleefa ba dama, to ita da bata kula shi ba ya akai yasan tana online? Ko kuma duba wa yayi yagan ta? Oho dai yaje yaci kan shi ta sauka.


Addu'a tayi ta kwanta, bacci ne mai nauyi cike da mafarke2 kala2 na ban tsoro da kuma nishadi ya mamayi baccin ta.


Allah ya tabbatar mana d alkhairi kedai Aeeshaa.



***********************



Tinda Aeeshaa ta tafi khaleefa bai je gidan ba, yau cikin Aeesha ya shiga wata na tara kenan, iyakar shi yaje wajen Rebecca ko ya dau Hadiza su faki idon mutane su shige gidan su sheqe ayar su, ta fita,ko suje inda suka saba zuwa.


A hankali son kasancewar ta matar Khaleefa ke shigar ta, da kawai so take suna debema juna kewa, amma yanzu auren shi take son yi dan ta dandana daula itama.


Wani babban abin haushin kullum sai sunyi waya ko chatting da Aesshaa, taji lafiyar ta wai da babyn ta, tayi2 taji cikin Aeeshaa akan zaman su da mijin ta taqi sanar da ita komai, sai tayi ta tambayar ta khaleefa ya je kuwa? Aeeshaa kullum sai tace mata me yasa take tambaya, taqi dai bata takamaimai amsa.


*********************


"Kasan Allah yau in baka zo gidannan ba sai ka ci Uban ka, kar ka ga ina daga maka qafa kana kiramin aiki in ka dawo ka gaji, kuma kana waya da ita, na gaji da jin uzirirn ka,kazo yau dinnan, dan matar ka ta wuni naquda, anjima in mun daidaici abin yazo gadan2 zamu kai ta asibiti"



"Haihuwa kuma Hajja? Wace irin haihuwa? Ko dai bari?"


"A'uzubillahi min kulli sharrin dan uban ka, wanne irin bari? Ciki wata tara cif ana xancen haihuwa, dan ka ja mana mugun baki kk kiran bari; sai dai ka barar da abincin ranar ka shegen yaro mai mugun fata,ga babar ka nan tin safe take sintiri akan yarinyar nan, tinda uwar ta ta zama baqauyiya, taqi zuwa, in baka zo ba nan da minti 10 zaka isko mana a asibiti"


"Kuje na taho,'


Hajja ta kashe waya tana ta masifa,


"Dik iskancin dake kan ka ka gama, bari ta haihu lfy hankalina ya nutsu waje daya, ai na gano inda kk zuwa yanzu daga wajen aiki, ba wajen karuwa ba ko wajen magajiyar karuwai ne sai na sa an kulle ta an kulle gidan nata, 'yan iskaa marasa tsoron Allah, ba abin tausayi irin Baban ka da General, sun aminta da kai matuqa kana xan kana iskanci,ita ma sallamammiyar matar taka ba zata iya fada ba kamar wanda kaiwa asiri ka rufe mata baki, dik to zan iya daku dika, marasa mafadi kawai,"



(Dama alaqar su Hadiza aka hango tafi ba hashi ni fai๐Ÿ˜ก)



Asibitin da take zuwa aka kai ta, likitan na ganin ta yaggguta sallamar wanda yake gani, ya miqata wajen daya Dr. Dan yana matuqar son taimakawa Aeeshaa.


"Sannu Aeeshaa, abin yazo kenan, ku shiga da ita, ina mijin naki? Ko har yanzu yana kan bakan shi na zubda cikin,"


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, me nake ji haka?"


Da biyu yayi maganar, dan kamannin Aeeshaa da Khaleefa kamannin wannan dattijuwar, tabbas wata mata ce mai mahimmanci a rayuwar su, dole ya fadi hakan dan ta sa ma ma'auratan ido, Aeeshaa kuwa bata son sirrin gidan ta ya bayyana, kullum addu'a take Allah ya gyara mata lamarin ta, bata son asirin Khaleefa ya tonu, ko da ba mijin ta bane zata so ya shiryu ba tare da kowa ya san meke faruwa ba, amma likitan nan ya sa Hajja zata matsa sai ta san komai.


An shiga da Aeeshaa Hajja da Maman Khaleefa hankalin su ya kasu kashi biyu, dama baya son haihuwa? Amma Aeeshaa taqi fadawa kowa? Lallai wannan yarinya a gaishe ta, sai tinanin haihuwar ta.




Hajja ce ta dauki waya ta kira Umman su Aeeshaa,



"To bafulatanar daji, tana dakin haihuwa sai ki mata addu'a"



Kit ta kashe wayar ta, danta san indai Khadeeja ce bazata samu kyakkyawar amsa ba.


Hassana da ummeen sabeer na gida suna aikin tarbar baqo ko baquwa, farfesun naman rago Ummeen Sabeer ke dafawa, Hassana ta dora ruwan wanka a bangaren Hajja, sai addu'a take Allah ya sauki Aeeshaa lfy.



Likita ne ya fiton yana washe baki,



"Mama a bani goron albishir gaskiya,kafin na fadi kinyi Amarya,"



"Alhamdu lilLAAHi ai ka riga ka fada, ga wanda yayi amarya nan, mu kam diya ce muka sake samu,ga uban yarinya kuma anan,"



"Baba General ne ke wannan maganar daidi lokacin da yake qarasowa, bai taho ba sai da ya biya office,din Baban Khaleefa ya dakko shi sannan ya taho da khaleefan, in ka gan shi da Baban khaleefa sai ka rantse abokai ne,babu ruwan shi da daukan kai ma yaran shi, yana jan su ajiki sosai, komai tare sukeyi musaman na family.


Khaleefa ba mai gane yanayin shi, fuskar nan kamar kullum cike da munafushin murmushi.


Hajja wani kallo ta watsa masa na zamu gaura da kai ne.



Dakin da aka gyara mai jego da baby suka shiga, nan kowa ya dinga yabawa yana ganin qoqarin Aeeshaa na haifar wannan narkekiyar yarinyar.


Khaleefa na ramuve a gefe, ya rasa kallon mutuwar da Hajja take wurga masa.


Karambani ya kaishi daikar yarinya daga Hannun Baban shi bayan ya gama yi mata addu'a..............







*wayyooo cikina๐Ÿคฃ๐ŸคฃWhat do u think will happen guys?๐Ÿคฃ*















*hummmmmmm wata sabuwa*







*Khaleefa w........ka daban yacin in baka tuba ba๐Ÿ™Š๐Ÿ™Š*๐Ÿ’…๐Ÿผ *KUN MAKARO* ๐Ÿ’…๐Ÿผ









*BY HAERMEEBRAERH*






Page 19:






"In ka taba ta sai na sare hannayen ka da wannan silver din, dan uban ka ba barin ta kk son ayi ba? A zubar d cikin ko? Kar ta zo duniya, hummmm na maka murna a asibiti muke, da agida muke sai na maka dukan da zai tabbatar maka da sauran qarfina, shiyasa mutane ke cewa ni babar ka ce ba kaka ba, dan iska mara mutunci bar nan, ai ko ba kai za ta rayu, akwai uban ka akwai kakan ka, har suna dik zasu saka mata,ban taba sanin baka da mutunci har haka ba khaleef, ka fita nace ko? Ko kayi ajiya je anan din?"



Kuka Aeeshaa take yi saboda a kwace take amma jiri take gani, jinin nan fa ya qi tsaiwa, Hajja ko a zaton ta korar da akao wa Khaleefa ne ya sata kuka,


"Kema taki uwar xanci in baki rifen baki ba,bari dik mu koma gida, in baki fadan asalin zaman ku ba ni da ke ne, mun tattara mun miqa ki muna ganin shi mutumin kirki ashe dik rufemu yayi"



"Hajja bata numbashi,"

"Subhanallahi kira likita da sauri,"


Likita ne ya shigo da azamar shi, Khaleefa ba wanda ya san sanda ya bar wajen.


Ana ta qoqarin bata taimakon gaggawa, likita ya sanar da su Hajja jini e bai tsaya ba,da sauri ta fita dan koma gida, driver ne ya maida ta, sai azalzalar shi take yayi sauri, Hajja akan Aeeshaa bata da sauqi, wannan karon ba zata yi wa kowa da wasa ba, tinda aka dano ta sai tai harbi zata huce.


Tana isa gida, Hassana da Ummeen su sukai ta mata barka, hankalin ta tashe take amsawa, gyada ta debo danya, ta wanke ta jiqa sannan ta zuba gishiri kamar cokali daya da kadan, barin ta tayi kamar minti sha biyar, ta jiqu bayan ya fara kamar barewa d kan shi, ruwan yayi jawur, sai ta tsiyaye ta saka a gora, da azama ta shirya ta koma asibitin.


Taje Aeeshaa ko motsawa bata yi, tana nan kwance, an smau jinin ya rage zuba, dan haka ta bawa likita maganin da ta kawo, tace a bawa Aeeshaa zai tsaida jinin, musu ya tsaya mata akan ta hakura zuwa wani lokacin.


"Ina da 'yancin da zan bata da kaina, amma na baka, in wani abu ya samu jikata sai nai qarar ka, ni da ka ganni nan cikakkiyar 'yar boko ce ba 'yar gargajiya ba, balle kace zan mata wani abun da zai cuce ta,yanda nake son ta ko uwar ta bana so haka, maza amshi ku san ya zakuyi ku dura mata ta shanye,"



Amsa likita yayi, ya shiga ciki suka sa mata Hajja na kallo, dan bata yarda ta barshi ba yaqi bata.



Suna nan zaune kamar awa daya, ta farka, tana jin yunwa, kowa sai murna yake,jini ya tsaya, ba wata matsala yanzu, sai satar kallo yarinyar take,


"Amshe ta ki riqe abin ki, ke kinfi kowa sanin ciwon nunawa yaro qiyayya, ke zaki bawa wani labari ma, amshe ta ki mata addu'a ki sa mata albarka, sannan ki tauna dabinon nan ki bata, a bata zamzam dinnan, Allah ya muku albarka, ya qara maki lfy ya yara mana ita da imani"



"Ameen Hajja na gode sosai, Allah ya ja mana da ranki,"


"Ameen Aeeshaa ta, maza bata kema ki ci abincin, hada mata shayi kai Muhammadu,"



Mugun kunya ne ya kama Aeeshaa da taga Baba da kan shi yana hada mata shayi cikin farin ciki da kuma son yin hakan.


Mama sai qoqarin amsa tayi take ya dakatar da ita,


"Basshi kawai ke zuba mata abinci, ai ba wani abu bane, diyata ce fa, ko kin manta ne?"


Murmushi sukai, ran Hajja yayi fari, a qalla Aeeshaa bata maraicin uba sai Uwa, gata kusa amma kamar itace ta mutu.


(Hajja bata da labri fa yanzu Umma tana zuwa wajen Aeesha a sace)



Waya ta dauka ta kira Khadeejan,


"Ta sauka an samu mace, in kinga dama kizo ko ki zauna, muna nan muna dik abinda ya dace uwa tayi, "


"Hajja dan Allah kiyi hakuri ina nan tafe in kun koma gida,"


"Kar ma kizo ki zaman ki,"



Kashe wayar tai tana ta mita, Baba General ya san an tabo masa mata, ya fi kowa sanin a wannan yanayin ya yi shiru ya mata biyayya shi yafi masa alkhairi.


************************




Khaleefa daya koma gida,kwanciyar shi yayi ya na baccin rana, ko a jikin shi, dan an hana shi daukan yarinya ai dama shi bai so aka haife ta bama, suje suyi ta dawainiya su suka ga zasu iya.



Bai farka ba sai wajen magrib, qamshin abinci yaji, kawai sai Aeeshaa ta fado masa a rai,


'Amma wannan ba irin girkin ta bane, girkin ta ai tada shi zai a barci tsabar dadin qamshin shi, and ta haihu ya za ai tazo yi masa girki'



Sauka yayi a gadon yana murje idon shi, daga shi sai boxer, dan shi yana son zama haka, tafe yake kamar baccin bai ishe shi ba, ganin ta yayi a tsaye a bakin qofar shiga dakin, sanye da rigar shi, ta riqe ludayin motsa miya, ba ko dogon wando, ta daurs gashin ta data qara a bayan kan ta, tana wani rausaya.


"Hadiza? Yaushe kk zo? Me kk yi haka? In wani ya shigo ya gan ki a haka fa?"


"Sai kace masu amaryar ka ce ni?"


Dan dariya yayi ta baki da hankali ya shige toilete, ita kuwa dadi ne ya kashe ta tayi tsalle ta fada gado, tana wurwurga qafa tana murna, ita a dole Khaleefa yaji dadi tace ita amaryar shi ce.



Bayan ya fito ta kammala shirya abinci, suka zauna suka ci,shidai kwata2 ba zai ce ba dadi ba, ba kuma zai yaba ba, sai jira take taji ya yaba, taji shiru, dake 'yar variki ce sai cewa tai,


"Gaba daya yau banji dadin abincin nan ba, banga maggi ba, haka nayi shi inajin shi yasa bai dadi ba sosai,"

Khaleefa a ran shi yace

'Gaskiya mana abu ba wani dadi haka, ai na zaci iyakar kwarewar ki kenan'



"Ayyaa aiko yn nan baki kula bane, ba laifi ai za a iya ci haka,"


Kada ido tayi


"Dan ma renon Goggo ce,kasan tsoffin da suna girki ba maggi kuma yayi dadi,"


"Haka ne kam, kamar yanda kk da dadin ba,"


Anzo wajen, nan da nan ta washe baki, sauri2 suka gama ci, ko kwashe plates ba ta san tai ba, sai shi ya fara kwashewa dan vaya son datti, yana shiga yaga kitchen kaca2 a aiki daya ta maida shi kamar an dade ana aiki ba gyara, ledojin maggi ya gani, kawai ya kada kai, maggi an tafka shi an gode Allah, ko a zaton ta maggi shije girki oho?


Gyara wajen ya fara tana taya shi, ita fa bata son aiki sam, haka suka kammala, a kitchen din ta dafe shi,nan da nan suka fara aikin na su na rashin mafadi,Khaleefa Aeeshaa kawai yake hangowa, inama zata zama romantic haka, ai da ita zai wannan lamari a kitchen, haka dai sukai ta sabawa Allah hankalin su kwance.




**********************






Ranar suna, yarinya an rada mata suna Khadeeja, suna kiran ta da Ameerah, Umma kam ta aje kunya a gefe, dan ba dan Adam din da zai dora idon shi ya kalli Ameerah ba ta kwanta mashi a rai ba, ba dan wai tsananin kyau ba, kawai haka Allah ya yi ta, har wanka Umma ke yi mata, sai dai a idon mutane ba ruwan ta da Aeeshaa balle wata Ameerah, da an ragu zata dauke ta tayi wajen su Sabeer ta mata wanka, ta gyara ta, taba Hassana ta maida ta ciki.



Yau su Hamdiyya, Bilqis,da Hussaina zasu koma gidajen su, bayan sun cika qanwar tasu da abubuwan gyara dan taimaka mata ta dawo kamar sabuwar amarya, sun gama shiri tsaf sun ma kowa sallama, zasu tafi Hajja ta fito dan yu masu sallama, Aeeshaa na dauke da Ameerah, sai daga masu hannu take kamar kar su tafi.


*********************





Dare ya yi, Khaleefa ya kasa samun nutsuwar dayake nema, Hajja ta hana Aeeshaa daukan wayar shi, ko a jikin ta, da ta samu hutu itama da jarabar shi,IG ta shiga tana kallon pictures, suna ta gani farkon kamar Hadiza, kuma an qarshen kamar wani yare daban, amma ga hoton Hadiza nan a jiki.



Dannawa tayi ta shiga, sai duba picture take, hotuna ne masu mugun kyau, kamar ba Hadizan data sani ba, kayan dake jikin ta kwata2 ma ita bata taba ganin ta da su ba, kaya ne masu tsada, daga jaka har tufafin da takalmi zuwa agogo, to ko dai kama ce ba Hadizan data sani bace, gidan. Ma da akai hotunan bata gane ko daya ba, dan ba gidan su bane, wani vedio da Hadizan tayi ta qawata shi da flowers dan kar a gane inda take ne ya tabbatar wa da Aeeshaa tabbas Hadiza ce, dan a parlourn ta akai vedion, sai hotuna da ta dauka a dai2 dinning table, kuma da alama wannan rigar ta Khaleefa ce ga hular shi nan akan Hadiza,tana wani karairaya, tana fadin ta kusan yin aure masoyan ta su sanya mata albarka, nan ba da jimawa ba zata turo masu hoton mijin da zata aura.


'Ikon Allah, amma wannan parlourn kamar nawa, kuma rigar Yah Khaleefa ce na ke gani, da hular shi, sai ta dan yafa mayafi'


Dubawa tayi taga post din ya kai kusan sati daya.


Shiru dai tayi tana nazari, can zuciyar ta ta dinga saqa mata


'In ma Hadiza shi zata aura ko a jikina sun dace, suje su qarata, balle ma ta san ba shi Hadiza ke nufi va'



Dubawa tayi taga yana online, taso ta masa magana amma sai taqi, kawai sai ta saka hoton Ameerah a status, da Dp, sai ta rubuta, (Allah ya albarkaci rayuwar ki my baby Khadeeja, AKA Ameerah)




Yana hawa, Khaleefa shi ya fara gani, murmushu tayi, tace


"Kai da Hajja taurin kan ku daya, tinda ta kore ka kaqi dawowa, itama taqi neman ka,na tabbata ko sunan yarinyar baka sani ba,ta kuma hana kowa ya neme ka, ni dai ina gida ina hutawa ta abuna, ko a jikina,"



"Sunan ta kenan? Allah ya raya maki ita,gata kyakkyawa kuwa,"


"Ameen na gd,"



"Turon hoton ta,"


"No"



"Why?"

"Saboda tawa ce ni kadai,"



"Ohhhh"



"Yehhhhh"



Sauka tai online,ranta bai mata dadi ba, wai kenan yana nufin har yanzu bai amshe ta a matsayin diyar dayake so ba, ita kadai ta mallake ta, ba komai, ta ji ta yarda, muje zuwa, zako kaga rashin M, dan kuwa komai Hajja ta yanke kan ka kai ka sani.



Shi kuwa sai maimaita kallon hoton Yarinyar yake, sabods ba laifi ta masa kyau,



Sake hawa Aeeshaa tayi, tayi ta saka hotunan su na suna, wanda tayi kyau sosai, ai da wani bacin rai Khaleefa ya mata audi,



"Kina hauka kk saka hotunan ki haka? Gaba daya qirjin ki ya fito, dalla malama ki cire kafin ran ki ya baci,"



"Kar ka damu muna da Omon wanke wa koda baka siyo ka kawo mana ba,"


'Wayyooo ina yiwa mijina rashin kunya, na shiga uku'


"Baki da mutunci dama, ni kk fadawa baqar magana haka, ki jira gobe kiga abinda zan maki,"


"Allah ya kaimu, xan so ganin me zaka iya aikatawa ina gaban Hajja gatana,๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ"


Abun ma dariya ya koma bata, haka sukai ta Chatting da audio yana mata masifa tana kunna shi tana bashi haushi, daya kula bata masa rai kawai take son tayi sai ya sauka onlinem


"Xaman yarinyar nan a gidan hajja ya zo qarshe, Hajja ke koya mata dik wani walaqancin da zatamin, yarinya mai nutsuwa da kamun kai, komai na aikata sai dai ta ban hakuri, ita ce ke fadi in fada yau, inaaa koya mata akai, Allah ya kaimu gobe,"



"Ahhh Ummu ameerah baki bacci ba?"



"Auntyyy๐Ÿ™ˆ eh ban yi ba,"


"Yah diyata?"


"Tana lfy, ya nawa babyn? Hope kuna lfy?"

"Lfy qlou, bari gobe zan bada no ki wajen wata qawata Haermeebraerh ta samin ke a group din ta,

Please Login or Register in order to submit comment