Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

center table din wajen.


"Kar ki kuka, ban so tambaya ta ta saka ki kuka ba, bana burin aikata abinda zai saki zubar hawaye, bayan irin abubuwan da kk fuskanta a baya, dan Allah ko yafe min, inshaa Allahu zan ci gaba da adana son ki a raina, har qarshen rayuwa ta, na rayu da son ki tin kafin auren ki, yanzu ma zan iya jurewa indai hakan ba zai sake saki zubar hawaye ba,"



"Dama kana so na.... kana sona ka bari aka bayar dani inda zan azabtu? Me yasa tin tini baka furta kana so na ba sai yanzu?"


"Aeeshaa abinda magabatan mu suka yi mai kyau ne hadin zumunci, kinga da yayi dadi da tini kina cikin farin ciki, rashin yin dadin shi ne babban baqin ciki na da dana sani na,"

Aeeshaa bata san wanne irin baqon feelings bane wannan, nauyi da zafi take ji a qirjin ta, na meye to? Ko dan bai sanar da ita yana son ta bane? To in ya sanar da ita ita din sanin meye so tai da zata damu akai? Tabbas wannan ne so abinda take ji yanzu, wani irin hadi ne na farin ciki, tausayi, haushi da nishadi, infact ba zata iya expressing din me ye a ran ta ba,


Ameerah ta janye a jikin ta ta shige daki da sauri2, fadawa tayi kan gadon ta, tana tsiyayar da hawaye, daga baya kuma ta fara murmushi, tana qanqame pilo,


"Ashe da rabo na a duniya da wani zai furtan kalmar INA SON KI, ashe ban MAKARO BA, kalma mai dadi daga bakin mutum kyakkawa da kyawun halaye da dabi'u, Allah na gode maka, Allah na gode maka, ina son ka Yah Sabeer, Allah ya sa alkhairi ne hakan,"




Ameerah ce ta shigo dugui2, ta furta


"Baabaa....baabaa.."


Dariya Aeeshaa tayi ta daga ta, tana ta murna, ta fita,


"Yah Sabeer kaji me Ameerah tace yanzun nan?"


"Me ta ce?"


"Cewa tayi Baba, ina zaune na ji ta shigo ta ce baba,"



"Kaiiiii Aeeshaa,"


"Da gaske nake, na taba maka qarya?"


"Sosai ma"


"Yaushe?"


"Dazu"


"Me nace?"


"Cewa kikai baki so na na maki yaro da yawa,"


Ya turo baki irin na shagwaba tare da maqale hannayen shi a qirji, shi a dole yayi fushi,


"Yah Sabeer ni fa ban ce bana son ka ba,in ban so ka ba wa zan so? Kai ne mutum na farko dana kasa tantance wane hali nake a ciki, daga sanda ka furta min kalmar So, shiga ta daki na gano nima ina son ka Yah Sabeer, Ina son ka, Ina son ka,"



Hawaye ke zuba a idanun su sosai, musamman Sabeer, da gar wani kukan dadi ya sake, ji yake yau kamar an dauke masa wani abu mai nauyi a qirjin shi,



(Sai kace budurwa, ko meye na kukan😚)




Nan suka zauna ta debo masa abinci,itama ta zuba nata, suna ci suna hirar masoya, Sabeer sai aman soyayyar dake ran shi yake mata, ita kuwa gaba daya dadi ya sa bata jin ma dadin abin cin, ajewa tai a gefe kawai tana sauraren shi, wani irin dadi na ratsa ta, sannan son shi na qara shiga cikin kowanne saqo na gabban ta.


"Hhhhhhhhh Yah Sabeee ka cinye abincin fa, ko na qaro maka ne?"


Dubawa yayi yaga ashe abincin ya qare yake ta spoon, yana kwaso babu, dariya sukai tayi,


"Wata rana fa tare zamu ci abincin nan ko? Ina baki kina bani a baki,"


Kunya ce ta kama ta ta rufe idon ta, amma cikin ran ta fata take Allah ya nuna mata wannan lokacin.


Har Umma ta dawo, da yaran, Sabeer na nan bai tafi ba, Umma ta fahimci akwai wani abu dake faruwa, tabbas kuma koma me ne ne mai dadi ne.


Bayan magrib Sabeer ya tafi gida, ya bar Aeeshaa da kewa, dan ji tai kamar kar ya tafi.



"Umhummm a bani labarin wannan abun farin cikin,"


Umma ce ta fadi hakan, a daidai lokacin da take zaune a bakin gadon Aeeshaa, tana taya ta ninke kayan Ameerah, suna sakawa a wajen kayan ta.



"Ummaaaa....ni ba komai"



"Yanzu ba da ba ne Aeeshaa, in da dane ko kula da ke ba zan ba bare na gane halin da kk ciki,kuma har abada zan koma ga mahalicci na ina dana sanin hakan, ki sanar dani ko me ke saki farin ciki, ko Sabeer ya furta maki maganar da ke ran shi ne?"




"Kin san me ke ran shi ne?"


Cikin share hawaye Ummah tce


"Kwarai na sani, wannan dalilin ne ma yasa na so kar a hada auren ku, da Khaleefa, amma ba zan taba iya yiwa iyayena musu ba, musamman akan ki,"



Hadiye wani daci tai a ran ta, ta yafe ma Umman nata, wannan na cikin abinda ya faru a baya ne, so ba wani abun kokawa a ciki, sai su fusknaci gaba.



Dan haka hira suke tayi akan yanda abun ya faru, Ummah na ta jin dadi kamar wata qawar Aeeshaan, daga baya ta bata shawarwarin yanda zata yi ta qara samun mazauni a zuciyar shi na dindindin.




***********************








Hadiza ciki ya shiga watan haihuwa, Goggo ta maida hankali wajen kula da ita sosai, Hadiza kullum kuka da daga hankali take, what if ta mutu fa wajen haihuwar dan shege me zata ce wa Allah? dik iya qoqarin Goggo na kwantar mata da hankali abun ya gagara, ta rame tayi baqi, dan ta daina shafe2, kalar ta ta fito, amma sai quraje kamar a kankare mata su, da ka hango ta ciki kawai zaka fara gani, sai sirisirin qafafun ta.


In ba Goggo data haife ta ba wanda ya santa da girman ta ba lallai ya gane ta ba.




"Ki yi wa Hajja waya ki sanar da ita yanda ake ciki Goggo,matar nan na da kirki ki kasa sakewa da ita, da ba ta da halin dattako da ko gidannan ba zata zo ba, kina ganin cin mu, shan mu, da komai namu yanzu su suke yi, kayan jarirai da komai ta siyo ta kawo, ba abinda ya dame ta da wai mutane zasu ce dan su ne ya mn ciki, fatan ta ta rabu da duniya lfy, ta tadda Allah cikin aminci,kinga sauran kwana uku, yanda likitoci suka ne na haihu, ya kamata a sanar da su,"




"In kk fara magana ko gajiya baki yi, ba za a fada ba,sarkin wawaye, zama zatazo tayi dan zakk haihu?kin ma bari ki haihu a sanar da su ko,"



"Shi kenan Goggo yanda kk ce,dan Allah kwadanta mana zogalen nan mu ci,"



"Haka dai kuka iya ke da cikn naki ci ba,sai kun cinyen dan jarin qulin, in ya fito bai kawo kudin cefane ni da shi ne, in mace ce wanke2 na kullum sai tayi sau biyu,"


Murmushi mai hade da emotion Hadiza tayi,da ma ace cikin nan na sunnah ne da taga gata, a haka ma Goggo na nuna mata gata, lallai da cikin Sunnah ne sai ta rasa ina zata saka ta.





Kwana biyu da faruwar Hakan Hadiza da dare ta fara naquda, tin tana kuka har ta gaza kukan, fadi take tana kumawa..



"Da na san haka hauhuwa take da naji maganar ki Goggo na rufe qafafuna , da ko qofar gida ba zani ba sai sa izinin ki, wayyoooo Goggo mutuwa zan, Khaleefa Allah ya isa ban yafe maka ba, duniya da lahiraN Wayyoooo Aeeshaa ki yafe min,ban taba neman gafarar ki ba ki yafe ni mutuwa san yi, wayyyoo a taimaka min,"


Bakin ta Goggo ta make,


"Dan girman Allah ki daina mana wannan dan iskan kukan, ba zaki kira sunan Allah ba sai tonon silili da iface2, in kk mutu kina wannan hayaniyar fa?"


"Na tuba, na tuba Allah na tuba ka yafe min,ba zan qara cikin shege ba, ni ko na halal din ma ba zan ba, wayyoo Allah na, natuba,"




Hajja suka kira ta aiko da mota, sannan tace suma gasu nan zuwa, asibiti aka wuce da Hadiza mai kyau da tsada, nan midwifes suka shiga dawainiyar taimaka mata dan ta haihu lfy.




Shigar su da awa daya da mintuna Hadiza ta sauka lfy, ta samu Yaro namiji, kar ku ga kuka wajen Goggo da Hadiza, Hajja ma dik qarfin zuciyar ta da ta zo sai da ta koka, kuka tayi sosai, ganin yaro lafiyayye sun samar da shi ta gurbatacciyar hanya.



Haka akai ta zuwa asibitin har da Aeeshaa, ta zo duba Hadiza ko dan Goggo, da kma Umarnin Hajja, koma me ya faru ya faru, Hadiza dai zata shiga zuri'ar su, dan haka dole ta san ya zatai ta hada kan su, kuma ta kula da Aeeshaa bata dau abun da wani nufi ba, ko a jikin ta, har daukan yaron tayi, Hajja ce ta amsa waya.



"Ku shigo daki na biyar, nan muke, Auwal ku tsaya waje, ni dai yaron nan ya nuna ya nutsu ne amma har yanzu ina tsoron shu'umancin shi, kar ya samu hanya ya gudu,"



Khaleefa na tsaye kusa da Auwal yaji komai, kuma ran shi ya baci, ya gyarun ma amma matar nan har yanz bata yarda da shi ba, a yanda yaci azaba, kuma ya sha wa'azi kala2 da take kunna masa, da wanda take masa in yau aka bashi mace karuwa ba sai dai ido ba, na dama kullum neman gafara yake, rai a bace ya shiga dakin



"Hajja ki daina min haka bana so, ki sallami wadannan qattan banzan, ni ba zan yarda ina tafe gardawa na bina ba,"



"Gaka nan qaton banza, barka kazo an maka haihuwa amma kana zancen banza, ku bashi dan shi, ya masa addu'a, da kiran sallah, ga shi nan,"


Amsar yaron yayi, nan take soyayyar shi ta shiga ran shi, kama suke sak, amma shi baqi ne yaron, kalar maman shi ya dakko kenan, kiran sallah ya mishi dama da hagu, sannan nan take ya rada masa suna da Ahmad, hawaye yake cike da quncin samar da wannan kyakkyawar halittar ta haram, ba su yaron yayi ya fita yana kuka sosai, waje ya samu ya zauna, Auwal na kan shi, hakuri yaji Auwal na bashi, yau ce rana ta farkk kalma mai dadi da ta hada su.


Share hawayn shi yayi,ya miqa masa hannu suka gaisa John ma haka.



Aeeshaa ce ta fito tana amsa waya,



"Na'am Yah Sabeer ka iso? K gani nan zuwa, na aje masu abincin, ka dakko Ameerah? Dan na san rikicin ta yawa ne da shi, tin da akai yayen nan kamar wadda akai wa mugun abu,"


"Mugun abu akai mata mana,ke dai yi kixo mu koma gida, yau so nake mu dan je shoping, a siyo mata kayayyakin da zai debe mata kewar maman,"


Dariya Aeeshaa tayi sannan tace,


"Yah Sabeer kenan Abban Ameerah, bari na masu Hadizan Sallama kar su ga na tafi haka kawai,"



Juyawar nan da zatai ta gan shi, cikn tsananin tsoro tayi baya, tare da zaro idanu waje, fuskar shi tayi jawur kamar garwashin wuta..........






*Kai kuma fushin me ye? Ko manja ka shafa a fuskar bamu da labari?😚*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*








Page 28:







"Da uban wa kk waya har kk cewa 'yata 'yar shi?"

"Ban gane kana tambayata da wa nake waya ba, ina ruwan ka dani? Ohhhh sorry na manta ashe fa kai yayana ne, ina magana ne da Yah Sabeer, kuma uban Ameerah ne tinda ko kaqi ko kaso qanin ka ne shi,"


"Me ye a tsakanin ku da kk kashe murya kk magana kamar kina magana da mijin ki?"


"Inshaa Allahu mijina ne, Allah ya amsa maganar ka, kana da matsala akan hakan?"


"Baki da hankali ne? Da yarinyar tawa zaki wani auren? Kuma ma Sabeer a dik mutane?"


"Yarinyar ka auren ka ne akai na? Sabeer akan dik mutane ai gwanda shi akan ka ma ba mutane ba, kaga ba zan iya sa'in sa da kai ba a mutane, yanzu bakina ya bude, zan iya kwana kana fada ina fada, amma ba mutunci na bane, saboda haka in kana da magana ka zo gida bayan mun dawo daga shooopinggggg,"



Juyawa tai ta shige dakin da aka kwantar da Hadiza, zuciyar ta wasai ko haushin shi datake ji da babu, dan ta samu ta fidda abinda ke qulle a zuciyar ta ta, ya isa haka, haba, mutum kamar wani shaidan.


Sallama ta musu Hajja ta mata fatan alkhairi, ta ce ta gaida mata su Ameenaa, ita kuma ta bada saqon gaisuwa zuwa Baba General, ta wuce, Khaleefa na ganin fitar ta, yace shima gida zashi, su kai shi ha dakko diyar shi, ba zai bar ta a hannun su ba,


"Amma dai ka san ba wai umarnin ka muke bi ba ko? Kai kk bin umarnin mu, in kana so bi umarnin ka kaje ka nemi izini wajen Hajja,"


"Comw on, yarinya ta ce fa wajen wani qato, ba zan taba yarda ta zauna wajen su ba,"



"Kaiii....zo nan,"



Bammm ta maida qofar ta rufe, kallon qofar yayi ya lumshe ido cikin bacin rai, wannan tsohuwar fa tana ban matsala.



"Meye matsalar ka da Ameerah da kuma Aeeshaa da ba saka iya barin mu koma gida ba, a asibiti zaka zo kana sai da mana halin ka kowa na karba,"


"Hajja ba ki ji wai fita zasuyi da Sabeer da Ameerah ba?"


"In na ji sai na hana su? Ba diyar su bace suma, beside kace kai baka son yarinyar nan, ga wadda kk so nan kayi cikin shi ai ba aure ko? Kuma da alama ya shiga ran ka tinda yanda ma ka dauke shi daban ne, har suna ka rada masa, so kar na sake jin maganar Aeeshaa a bakin ka balle Ameerah da Sabeer,in zaka yi maganar su inji alkhairi, yarinyar nan sai in ta girma ta ga damar kula ka amatsayin uba, ba mai bata ka a idon ta amma ba wanda zai baka ita mahaukacn banza kawai,sai kayi kamar ka samu lfy, sai ka qara bazama,"


"Hajja kina nufin banda hankali kenan,"


"Kwarai d gaske, in kana da hankali wanda yake son naka kana da kamar shi ne, Sabeer dinnan da kk gani kwanan nan na san ya dade yana son Aeeshaa a sanadin a baka ita ya hakura, ba dan haka ba da Ameeran ma tashi ce, ka mata sakin hauka saboda kan ka na hayaqi ance ka sake ta, kuma naga dai ba son ta kk ba, tinda ka fada aura maka akai ba kai kace kana so ba,"



"Ni yaushe na taba cewa ban son ta, ni ba wanda ya taba jin nace bana son ta,in ma na fada nace na janye, kawai dan ba sona ake ba shi yasa komai nayi bana daidai, dik wani abu da ba ko son nayi ba na daina ba yanzu, kum nace in son mada min mata ta da 'yata yanzu, ba shikenan b a maida ta shi ya samu wata,"



Hajja ba zata iya da wannan haukan ba, yi masa bayani ma baida amfani, saki uku a gidan uban wa aka taba maida shi?



"John ! Auwal ! Ku maida min shi gida,"



"Wai ya za a dinga min abu kamar wani barawo ko wani dan kidnerping? Ni to ba gida zani ba zanje na dakko mata ta da diyata,"


Ko kula shi basuyi ba suka sashi gaba, da kallon ka taka mu fita ko kasha na jaki kuma a ka zamu fidda ka, sarai ya san kallon, tinda ba yau yake tare da su ba almost a year now.


Ranshi bace ya fita yana zuba sauri, mota ya bude ya fada ya qame qam,sai muzurai yake yana tsaki,


Bayan sun isa gida ne ya shige dakin shi, in ya rufe ido Aeeshaa yake gani, yanda take waya take nishadi da annashuwa, bai taba sanin wannan side din nata ba, ashe mace ce mai cike da so da qauna a zuciyar ta, farin ciki da nishadi na baibaye da ita, ashe shi ne fitilar daya disashe ta, bai san yana kuka ba sai da yaji sautin a kunnen shi, ya so ya riqe kukan amma inaa ba zai riqu ba, fashewa yayi d kuka sosai, yana sambatu,



"Aeeshaa ki yafe min, k yafen dikkan munanan abubuwan da na maki, ban taba zatan zaki zama mace mai mahimmanci a rayuwa ta haka ba, a zatona jikin ki kawai nake so,ashe zuciyar ki ma ta shiga tawa, a daidai lokacin da NA MAKARO, dik abinda kk min a zaman mu mai dadi ina fatan Allah ya dadada maki fiye da hakan kema, Allah ya sa ki farin ciki Aeeshaa, Allah ya raya Ameerah, Allah ya baku zaman lfy, dole na karbi qaddara ta ta auren Hadiza, ni na jawa kai na, Allah na gode maka daka nuna min gaskiya ka bani ikon bin ta, Ya Allah ka yafe min munanan aikin dana aikata a baya,Allah ka kare ni da aikata laifi a kan sani na a gaban rayuwa ta, inna aikata laifi a bisa kuskure Allah ka yafe min,"


Shessheqar kuka yaji, ya juya daga durquson da yayi a qasa, mahaifiyar shi ce riqe da abincin shi kasancewar Hajja na asibiti bata dawo ba, yau dai tayi waya tace Maman shi ta kai masa, cikin murna kuwa ta debi abincin, ta kai masa, tana shiga taji yana kuka, yana addu'a, wani irin dadi ne ya wanke zuciyar ta, da na gari abn so ne ga kowa, samun suruka kamar Hajja abin na da wahala a wannan zamani, wadda zata tsaya ta jajirce don ganin ta kare ahalin ta daga wuta, ta samu nasara sosai, ba abinda za su ce ma Hajja sai dai Allah ya mata kyakkyawan qarshe,ya qara mata shekaru masu albarka ta ci gaba da sa su a hanya.



"Son tashi ka ci abinci, inshaa Allahu Allah ya amsa dikkan abinda ka roqa, kai dai ka ci gaba da zama yaro na gari, in kayi haka ka gama komai a rayuwar ka, zo kaci abinci, kar yayi sanyi,"



"Mama kema ki yafen dik abinda na maki a rayuwa ta, inshaa Allahu na maki alqawarin zamowa yaro na gari abin alfaharin ku, na dau darasi, da girmana ana bani kulawar qananan yara, tarviyya aka koma ban daga farko saboda watsi da nai da wadda aka min ina yaro, na gode wa Allah daya yo ni a cikn ahalin nan,"


"Sauran Baban ka da Baba General, ya kamata ka nemi gafar su, sannan ka samu Hajja ka mata godiya na musaman akan kulawa da lamarin ka da tayi,"


"Inshaa Allahu, ita na san me zan mata, su Baba kuwa yau yau dinnan zan nemi gafarar su,"




Abinci yaci yayi sallar Asr, yayi wanka da kyau, yana zabga qamshi yaje masjid ya dawo, a parlourn Hajja ya tadda iyayen nashi maza ya basu hakuri, kuma sun gamsu Khaleefa ya shiryu, dan haka sun yafe masa, sun kuma sanya masa albarka, Hajja ce ta fito cikin kwalliya kamar kullum, Khaleefa ne ya kalle ta, cikin zolaya yace,


"Gaskiya uwargida kin hadu, da zaki ban dana da yau mun fita on a date just me and u, dan na nuna maki irin yanda nake son ki a raina, kuma na nuna maki godiya ta a gare ki bata da iyaka,"



Cike da jin dadi Hajja ta kada ido kamar wata budurwa tace,


"Why not?"


"Da izinin wa?"


"Ohhh dear don't be a jalouse husband,"



"K na bada izini amma a dawo da wuri,"



"Yes sir"


Mayafin ta ta dakko, ska jera, ya riqe hannun ta, Baba General yayi gyaran murya, juyawa sukai sika kalle shi,cikin daure fuska ya nuna da hannun shi alamar ya sake mata hannu, dariya aka dauka a wajen, Baban Khaleefa har yana kwallar farin ciki, suna fita su John suka taso,



"Not even today man, we ar going on a date, a date, bama buqatar kowa, na sauya ku kun sani, ba saida ta zan je nayi ba,"



"Kuje abun ku muma fita zamuyi, ina ruwan mu da kai?"



"Ba ku da ruwa tabbas amma kar ku ce zaku bi mu yau, i want to show her my appreciation thats all,"




"K man sai kun dawo, Allah ya kiyaye, u better watch it,dik inda ka shiga muna da ido a wajen,"


Hannun Auwal ya saka a gaban idanun shi, alamin muna ganin ka.



Budewa Hajja mota yayi wadda take ta dariya, wato kowa bai yarda da Khaleefa ba, ta yarda da fitar nan ne dan shima ya shaqata, ya dade a nade a gida, sannan hakan zai sake bata damar cusa mishi aqidar da take son ya kasance yana da ita.



Wanj fancy restaurant suka je, ga kudi ga kyau, zama sukai, aka kawo masu abinci da abin sha, suna ci suna hira, mutane ana ta kallon su, ga tsohuwa ta sha gayu kamar amarya, ga yaro, matashi mai jini a jiki, kowa dai ya gan ta yaga kamilar dattijuwa, kamannin da suke ne ke korewa kowa shakku da zargi, dan mu ta nan wajejen hausawa ba kowa ke fita da matar shi on a date, ko a je cin abinci ba da sauran irin dabi'un nan na turawa da larabawa.


Hajja tayi nasara wajen koyar da Khaleefa wasu abubuwan na rayuwa masu mahimmanci, yaji dadin fitar d sukai sosai, bayan sun fita ya kaita shoping, taji dadi kwarai, ashe Khaleefa is so sweet ba wanda ya san hakan, yanzu gashi yana ta nuna masu halin shi mai kyau.



Daf magrib suka isa gida, kusan sai da ya yi wa kowa siyayya, musamman Ameerah da Aeeshaa,sai Hadiza da yaron su, Hajja ta taya shi zaban kayayyakin wanda suka dace.



**********************






Yau wata hudu kenan da haihuwar Hadiza,Hadiza ta murmure, sai dai har yanzu bata dawo da hasken ta ba dan tayi alqawarin daina sabon Allah ta hanyar shafe2n mai da zasu qara mata fari, Goggo ta tsoratar da ita sosai, akan hukuncin masu sauya halittar Allah.



Parlourn Hajja a cike yake da baqi, Aeeshaa da Umman ta da su Ameena dik sun zo, Iyayen Ammar gau zasu zo, da wasu dangin Baban Hadiza dan saka ranar aure, abinci da abin sha ne cike a parlourn, sai raha ke tashi da hirarrakin iyayen nasu, Hassana kuka kawai take na farin ciki, wai yau ita za a sakawa rana, Aeeshaa na ta lallashin ta, can qasan ran ta tana tinani bata ji fa ance saka ranar harda nasu ba, ko dai ba yanzu su za a mallaka masu junan su ba ne? Gaskiya sun matsu su gan su a inuwa daya, ai ya kamata a hada dika a huta.


"Tinanin me kk?"


"Ummah ban ji ance za a saka rana har da mu ba, naji ance na Adda Hassana da Yah Ammar, Yah khaleefa da Hadiza,mu fa?"



"Aeeshaa qaniyar ki, wato kin matsu ki bar ni ko?"


Kwatawa tai a cinyar Umma nata cike da shagwaba ta dora habar ta kan kafadar ta,


"Ummaah u knw how much i love u,just curious to knw za a hada dami kk a'a,"


"To nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito muji,.....ke kuma ki daina mana kuka haka, ai murna zaki ba lokacin kuka bane wannan, ki godewa Allah, dama wani jinkirin alkhairi ne, gwanda ki aure a makare, akan ki auri wrong parson,"


"Haka ne Ummah, can't help it, kukan kawai ji nake yana zuwa,"


Ummeen ta da ta shigo dauke da abin sha ta zauna, tace,


"Yaran Ummee me ake tattaunawa ne?"


Da sauri Aeeshaa tace,


"Ba komai,"


Dariya suka sa dika, tabbas akwai wani abu kenan tinda take sauri kar a sani,


"Tambaya ta take wai da su za a saka rana ko ba su,"


"Su su wa?"


"Ita da Sabeer mana,"


"Ummaaaahhh,"


Tashi tayi ta bar wajen tana buga qafa irin na shagwaba, daidai lokacin Sabeer da Ammar suka shigo, Ammar baki har kunne, Sabeer fuskar shi a daure, kallon shi tai idon ta a waje, kar dai ba sa rana da su ba...........😨😨😨😨😨😨











*Tabdi jamm aiko da na je na sake dasa sabon zama a gidannan, wa zai raka ni😑😑*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*











Page 29:







Da hannu ya mata alamar su je waje, ta kitchen suka je suka tsaya daga waje,


"Yah Sabeer me ya faru, naga fuskar ka babu walwla?"





Dan sosa kan shi yayi ya gyara tsaiwa,


"Naji ana ta saka rana ba a kira sunan mu ba, sai daga baya wai naji Baba General na cewa mu in an tashi nasu an daura auren mu, kamar bamu da wani mahimmancin da za a mana yanda aka masu, cikin bayyana muma fa ranar mu za a sa, kamar yanda ake maganar nasu,"


Dan murmushi tayi, ta kai fuskar ta tana leqa tashi, wai d gaske fushi, qin kallon ta yayi da, sai daga baya suka hada ido, nan da nan idon shi ya kawo haske saboda nutsuwar daya samu ta hanyar kallon fuskar ta.


(Ya ke 'yar uwata, kin san kuwa tasirin kallo? Kallo ya na da mabanbantan amfani, daya daga cikin amfanin kallo shine ki kwantar ma da mijin

Please Login or Register in order to submit comment