Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amarya mai rowa nan ta zo gaida mu yau,"


Wata dattijuwar mata ce mai tsananin kamala, da nutsuwa,tare da annuri a tattare da ita, tana ta soya quli2.


"Ahhh lale maraba da ke amaryar me rowa,"




Dan dariya Aeeshaa tayi, tare da hadiye yawun daya yanko mata, ganin quli mai zafi, ga qamshin nan kamar ana soya kaza.


Gaisawa sukai, ta gabatar masu da kan ta a matsayin Aeeshaa, sannan ta basu hakuri akan mijin ta ne bai son kowa yana zuwa mata, kuma bata son kowa yaje, ta masu bayani yanda zasu fahimta, suka kuwa fahimta din, sannan ta musu alqawarin xata na shigowa in dai ta samu izinin shi, sannan zata roqe shi yana bari ko Hadiza ce tana shiga mata hira.


Nan da nan Goggo ta gane me ke tattare da Aeeshaa, dan haka bata bata lokaci ba wajen debo mata quli mai zafi ta aje mata a gaban ta.


Aeeshaa kamar wata mayya haka ta dinga cin qulin nan,Hadiza nata bata labarin su,inda Goggo ta koma suyar ta.


"Mahaifina ya rasu, a da mahaifina na da hali dan kasuwa ne, muna cikin rufin asiri, kinga dik girman gidannan da kyaun shi abinda zamuci ma wahala yake mana, ba mai taimaka mana daga ni sai mahaifiya ta, mahaifina ya rasu sakamakon rashin lfy da yayi na qanqanin lokaci, kafin ya rasu ya min aure da dan abokin kasuwancin shi, muna zaune lfy, lokacin da mahaifina ya rasu ya fara sauya min, yana min rashin mutunci harda duka da zagin iyaye, ni kuwa na ga ba zan dauka ba na nemi saki, da farko yaqi, amma daga baya iyayen shi suka zuga shi ya saken na dawo gida, yanzu haka ina zaune da mahaifiyata danake kira da Goggo, dangin mahaifina va mai taimaka mana, a da kuwa kan ya rasu qofar gidannan da cikin gidannan dik dangin mahaifina ne, Gaoggo tai ta dawainiya da su, dangin ta ma basu cika zuwa ba, saboda kowa ya kama qasa, zumuncin su suke yasu yasu na masu akwai, da da take da shi da ita ake yi, kasancewar ta babba, amma yanzu da ta rasa ko rashin lafiya tai ba mai zuwa duba ta.



Yau dinnan ta fara soya quli saboda tace ana samu a sana'ae ga quli ga mai da zata fidda, amma akwai wahala,"



"Wayyoo Allah ya jiqan mahaifan mu, ya qara rufa asiri, bari na koma bamu kula da lokaci ba har an kusan magrib,"




Suna can suna hira zuwan Khaleefa uku bata nan, dik inda hankalin shi yayi dubu ya tashi,ina taje to?



Hadiza ce ta rako ta dauke da ledar quli2 a hannun ta, da gyada mai gishiri, wanda sukai ta ja in ja da Goggo kan ta anso, musamman da taji halin da suke ciki, sai dai ta digawa Hadiza ayar tambaya akan wasu abubuwa data gani a tare da ita.




Bude gidan take Hadiza na riqe da ledojin a hannun ta, ya qaraso.


Hadiza na ganin shi ta kafe shi da ido kamar tsohuwar mayya, jikin Aeeshaa ne ya dauki rawa, cike da tsoro ta qarasa budewa ta bude gate ta shige, ko amsar kayan wajen Hadiza batai ba,



"Wayyooo Allah ka kawon a gaji, tabbas ban kyau ta ba na fita ba da izinin shi ba, ya Allah ka tausaya min kar ya kashe ni😭😭"


Khaleefa ne ya gama parking ya fito,


"Ke ina kk qoqarin shiga ne?"


"Amarya zan bawa ledar nan, quli taje siya gidan mu, tana son ta maka kwadon letus,"


Aeeshaa da ta dawo rufe gate, a tsorace baki sake take kallon Hadiza, irin wannan qarya haka nan take ba ko gezau a tare da ita,kamar iyakar gaskiyar ta ta fada.



Kallon Aeeshaa yayi, ya amshe ledar ya gani da gaske quli ne, ya gyada kai ya wuce tare da sake ledar a qasa.


Wata iska Aeesha ta sake, mai mugun qarfi tare da dafe cikin ta da taji yana murda mata.


"Hadiza yaushe kk qirqiri wannan maganar?"



"Shiiiiii.. maza rufe ki shiga kan kiyi laifi, in yace da magaribar nan kice nema akai tayi ba a samu ba,in kina da letus kin tsira in baki da shi ki ce kin zaci akwai ne,"



"Innalillahi, Hadiza qarya fa kenan,"


Ko kula ta batai ba ta wuce gida, Aeeshaa ta ja ta rufe gate, sai sanda take ta shiga gidan, bata gan shi ba,ta je kitchen ta ko yi sa'a tana da letus da cabbage, ba ma idean yin kwadon akan ta,nan da nan ta fara daka quli, tayi kwado, zuba nata tayi, ta zuba masa na shi, ta dakko da juice da snaks ta kai masa, (bata rabo da snaks saboda yunwa ko baqi, uwar gida in kk saba koda cincin ne ba a rasawa gidan ki wallahi kin kama matakin riqe gidan ki, coz ko miji ya dawo baki gama a binci ba zaki zuba masa, wanda ba a fata ma ki zama daga cikin matan da basu gama girki da wuri, sannan in yara gare ki, kin makara baki masu abin tafiya da shi skul ba zaki iya hada masu da juice da wani snak din su tafi, kan su dawo kinyi abinci mai nauyi,da zasu ci su qoshi, kuma baqi kin huta kame2n me zan basu?)


Kwankwasa dakin shi tayi, ta ji ya yi banza da ita, ta jima a bakin qofar bai amsa ta ba, Khaleefa ko sallar isha'i bai ba, an wuni sabawa Allah jikin shi har wanu ciwo yake masa, dan haka yayi wanka ya kwanta yake bacci.


Gajiya tayi ta maida fridge, ta dau nata ta hau ci tana lumshe ido.




Bayan tayi sallah ta kwanta bacci itama.



**********************







Aeeshaa fa yau ta burkife, Khaleefa yayi tsawar yayi ihun taqi shiru, ba dan komai ba sai dan motsin da take ji a cikin ta, ga shi ta yi qiba yanzu, dik da ba sosai bane ramar nan ta kau, hasken ta har tsoro yake bata in ta kalli madubi, shi kuma baida masaniya akan masu ciki, dan ba wani shiga shirgin mutane yake ba balle yace ya san ya ake yi.


Ga takaicin ta yayi qaryar ba su gari, sunje yankari, ga shi tana jin boobs din ta na ciwo, dan haka yau dik yanda taso ta daure kasawa tayi, so take taga Hajja ko Umman ta ko Maman shi ko Ummeen Sabeer, haka akai sunan Balqis har ta koma bata je ba, ita kuma in zata zo yace mata sunyi tafiya.


Yau ba yankari ba ko cikin garin baushi suka je sai sun dawo, Hadiza ce ta koya mata wannan dabarar, tace tai ta kuka ko ya dake ta kar tai shiru, har sai ya gaji dan kan shi ya kai ta gida.


"Enough !!!n ke jaririya ce dazakina min wannan dan iskan kukan kina wani buga qafa?"


Sake rikicewa tayi da wani kukan harda kwantawa a qasa, tana kiran sunan Hajja.



Takaicin ta ya kaima Khaleefa ko ina, dan haka ya bata rai yace,


"Dakko hijab muje,"


A duqe ta dakko ta bi shi, har ya shiga mota ya na jiran ta bude gate, tsabar rashin imani da tausayi irin na Khaleefa, mamakin shi ya daina kama ta yanzu.


Zuwa tai ta kama tana son ta ja ta kasa, ganin ta kasa ya sashi fita yana ta masifa wai bata da amfani yanzu, komai ta daina masa, sai an magana tace bata da lfy,amma ya san maganin ta bari su dawo, ita dai tayi shiru tana jiran ya bata izinin shiga, kar ta shiga tayi laifi, infact bata san ma ta ina zata zauna ba, gaba ko baya oho.



Tsayawa tai ya daka mata tsawa.


"Dallah ki shiga gaba mu je, in ba haka ba na fasa kai ki din naga abinda zai faru,"



Ai kafin ya rufe baki ta shige gaba, tsakanin murna da tsoron wanne irin ciwo ne za a ce yana damin ta, dan daga nan so take su wuce asibiti, ba dai ta son suje da shi ne kawai.


Sanda suka isa, Aeeshaa ta sha wani abu mainsuna mamaki, domin kuwa khaleefa ne ya bude mata mota, ya rungumo ta, sannan ya kai bakin shi kunnen ta, yana mata magana, tare da yashe haqora.

"In kk kuskura wnai ya gane irin zaman da muke zan shayar dake mamaki in mun koma,kuma zan iya qoqarina naga baki sake zuwa ba sai kin shekara"



Murmushin yaqe ta fara, Hajja na zaune a waje tana shan iska cikin shuke2n dake bangare guda a cikin gidan, ta daga kai ta kalle su, cike da farin ciki da tsantsanr sha'awar su ta qaraso tana fadin.


"Lale maraba da amare da angwaye, lallai ne, shiyasa ashe aka daina ganin ku, wannan dan kadafin ya bi ya maqalqale ki kamar zai shige jikin ki, bar ta ta zo nan dallah kamar wadda za a cinye,"



Yana sake ta Aeeshaa ta je da gudu ta fada jikin ta ta saka kuka, Khaleefa ya cika famm, bata ji me yace ba kenan,


"A'ah mene ne na kuka?"


"Hajja nayi missing din ki sosai,ina Baba General?"



"Ya fita, kin san shi in ana wani abun haka daya danganci sojoji yakan leqa, kar ya xauna a gida wai tsufa ya masa mummunan kamu inji shi"


Dan dariya suka yi, suna tafiya ciki Khaleefa yace,


"Ai bakiji yanda ta matsu mu zo ba, bata jin dadi kwana biyu, nayi2 na kaita asibiti taqi, wai ita na kawo ta wajen ku, shine nace bari dai na kawo ta, indai hankalin ta zai kwanta,"



"Ahhhh kayi dabara da ka kawon ita ai, Alhamdu lilLAAH ashe da rabon zan ga dan ku, Allah ya sauke ki lfy ya sa a haifi mai albarka,"



"What ar u saying? What do u mean?"


Shine tambayoyin da duka watso ma Hajja,



"Ina nifin kina dauke da ciki, sai dai ban san wata nawa bane tinda ni ba likita bace,ke in banda ke yaushe rabon ki da al'ada ? Ko kina yi?"


Sai a sannan ta yi nazari, tabbas yanzu kusan wata hudu bata gani ba, abun na damun ta kashhhh amma ita wawuya ce, ya bata taba wannan tinanin ba?

Hawaye ne ke zuba a idon ta ta rasa na me ne, farin ciki ko baqin ci.


Gaba dayan su suka kalli Khaleefa dan ganin reaction din shi akan wannan lamari................








*Me kuke tinanin khaleefa zai yi? Zai zo cikin? Xai qi cikin? Shin zai yarda ma tana dauke da ciko?*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ






*BY HAERMEEBRAERH*








Page 14:










Yanayin Khaleefa ba bu mai iya cewa ga shi, hangowa kawai yayi ta haihu, wannan kyakkyawan jikin nata ya sauya ya tattare ya tamuqe, aikuwa za a yi ta, dan kuwa sai dai su rabu, tinda ba wai son ta yake ba, yanzu ma saboda kyaun jikin ta yake daga mata qafa,


'Ai kuwa daga nan sai a asibiti a zubar da cikn nan, ba zan dauki hatsarin rasa kyakkyawan jiki irin wannan ba'




"Ya ya dai kayi shiru?"


"Wato Hajja murna ce ta min yawa, Allah ya sauke ki lfy Habibty, Allah ya kawon babyna lfy ko mace ko namiji, i will love u both with all my heart,"


Kafe shi d ido Aeeshaa tai, kalaman shi ina ma gaske ne,ko da ba son shi take ba itama is good to hear love word from ur man.


Hajja ce ta qara rungume ta, tana taya ta jin dadin kalaman Khaleefa,



"Alhamdu lilLAAHi yanzu ba ga shi har an wuce wajen ba, da kuna ta baqin rai za a hada ku aure, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala ba zai hango ba, yanzu gashi harda albarkar aure, kunga ko ai sai godiya, Allah ya kare ku daga dikkan abin qi, kuje yanzu ku gaisa da iyayen ku, in yaso muje asibiti tare kan General ya dawo,"



Wani baqin ciki Khaleefa ya hadiye tare da lumshe idon shi d suka fata sauya kala.


"Hajja ai ba sai kinje ba, kiyi zaman ki kawai, zamu je, abinda dubawa ne kawai zasuyi suga wata nawa ne, kuma daga nan zan kaita ta dan yi shopping,ko kina nufin shima da ke zamu ki takura mana?"



Cikin dariya da jin dadi Hajja ta shafa Aeeshaa ta baya, sannan tace,


"Ohhh yaran zamani, kuje, in yaso daga baya munji labari daga wajen ka, kuma ya kamata ka saima yarinyar nan waya, haba, yarinya na zaune in ka fita ai ko gida ta kira muji lfyr ta, in kuwa ba ku rage tafiye2n nan ba nan ma cikin nan na cikin hatsari, innaji ba daidai ba na zo na dauke ta, sai ta haihu na dawo ma da ita,"



"Bama zakiji komai ba, Hajja ba dan ba dan ba dana ce sa idon ki yayi yawa,"


"Kaci uwaka, ni in iya shege kk ji na fika, kaji min dannema, sa idon me na maka? Da Allah ya sa na aje duwais dina waje daya bana zuwa maku akai2, nan Mamar ka ta so taje na hana ta? Saboda banji labari Khadeeja ma taje ba, ya kamata a baku waje kar ana yawan xuwa maku, saboda gudun kar kuna daukan zugar mutane, shine zaka ce na sama ido, bari dik sati zan dinga zuwa dan uwaka kaga sa ido ai,"



Yasan zata iya da sauri ya duqa gaban ta yana dariya, inda jikin shi ke gugan na Aeeshaa,


"Yi hakuri uwar gida sarautar mata, wasa dama nake, ai in ba dan ke ba da nayi asarar samum mace kamar Aeeshaa, ke dai ba abinda zan iya ce maki sai addu'ar Allah ya qara rayuwar ki tsaho da imani,"



"Ameen,shi yasa kk burge ni, akwai tsoron Allah, da sanin ya kamata, yanzu bakin ka ya bude,wato ka samu wadda zaka na hira da ita ko? Mu ka maida mu 'yan iska ba mu isa ka mana magana ba da"


Dariya sukai banda Aeeshaa data matsu ya tashi a wajen, Khaleefa al'amarin shi yafi na tsohuwar karuwa ban mamaki. Yana namiji ya iya hada magana, da kissa da munafurci, da fuska uku.



Tausayin kan ta ne ya kamata ta lafe jikin Hajja.


"Ta shi mune wajen su Mama mu gaida su sai muje asibiti ko dear,"


'Dear my foot, mugu kawai'



Sun shiga tana cin abinci, ganin su ya sata tashi ta tari Aeeshaa, kallon kayan jikin ta kawai take, wanda gaba daya zasu kai dubu dari, in aka dauke dankunnen ta na gold, murmushi take ta zabgawa da masu lale, a babban parlourn nasu suka zauna, Khaleefa ya gaida Maman nashi. Aeeshaa ma cikin kunya sosai ta gaida ta, amsawa tai tare da debo masu abinci ta aje masu a dinning, ta masu izinin zuwa su ci.


Aeeshaa ta ci abincin sosai, sai taji dadin shi sosai, Khaleefa sai kalloj ta yake, dama haka take da ci? Lallai dole ta cika tai fam haka.



"Khaleefa in kun gama ka zo,"



"K ma na gama ma muje,"



Murmushi tai ma Aeeshaa wanda bai kai zuci ba, Khaleefa ya bi bayan ta.




Suna shiga daki ta hade fuska sosai kamar bata taba dariya ba.

"Mama lfy?"


"Ba qalao ba, yanzu d hankalin ka, ka kashewa yarinya kudi haka a jikin ta, ka duba kayan ta daga jaka har takalmi zuwa suturar dake jikin ta sun kao dubu dari zuwa sama.da hakan, bamda dankunnen zinaren dake kunnen ta,tinda akai aure baka kawo ta ba, yau da kuka zo in banda baqar rowa irin taku ko 'yar tsaraba ba zaku zo mana da ita ba, ku kuma kuna can kuna cin dadin ku, dibi yanda yarinyar nan ta yi qiba tai mui da ita, kai kan ka kalle ka, da haka kk? To bari kaji, yanda kk kula da ita nima haka zaka na kula dani, in ba haka ba zaka hadu d fushi na,"



"Dan Allah kiyi hakuri,inshaa Allahu dik abinda kk so shi za ai,"



Kudi ya sa hannu a aljihun shi ya bata,kimanin 20k, amsa tai ba dan ta yaba ba, ko ita tana da sama da su a gidan, dan haka a ciki ta masa godiya, tashi yayi zuciyar shi ba dadi,ko da ba son Aeeshaa yake ba, baya son kowa yana mata abu mara kyau, a bar masa matar shi, in yaga dama ya mata kirki, ko akasin hakan.


"Tashi muje,"



"K bari na ma mama sallama,"


"Dalla malama.nace muje ko? Ko taurin kai zaki fara min,"


"Ayya ba haka bane, kayi hakuri,ba zan sake maka.musu ba,"



Kan ta a qasa suka fice, mama na kallon su ta window tana qara lissafa kudin kayan Aeeshaa.



Bangaren su Sabeer suka nufa, a tsaye ya tsaya yana gaida Ummeen su Sabeer, Hassana na kitchen ta fito, kallo daya ta masa zuciyar ta ta hau harbawa da mugun gudu, saboda Khaleefa ya yi wani irin kyau, bata jima da dawowa daga gidan Bilqis ba data raka komawa gidan ta, hadiye wani abu tayi da ya tsaya mata a wuya, ta gaida shi, Aeeshaa ma saurin gaida ta tayi, ta amsa mata cikin sakewar fuska, dan yanzu bata jin haushin ta sam, itama ba laifin ta bane da aka aura mata shi.



"Muje,"


"To,..... Ummeen ya labarin Yayana? Shiru, kuna waya kuwa? Ko ya dawo?"



"Yana nan lfy Aeeshaa,kullum......




"Zaki wuce muje ko kuwa?"



Da qarfi ya dage labulen da bai kafu d kyau ba daya fado, itama bata sake waiwayar kowa ba ta fice, daga Ummee har Hassana sun fuskanci wani lamari a tare da hakan, lamarin tsoro da fargaba tare da tashin hankali a tsakanin ma'auratan.


"Ikon Allah, sai kace wani kububuwa,"


"Babu ruwan ki Hassana, Allah ya kyauta,kin gama ne?"



"Eh sauran kadan,"


"K wuce ki qarasa abinda kk, ba ruwan mu a lamarin su, Allah ya kare abin qi,"


"Ameen Ummee,"



A waje kuwa Khaleefa ya hade girar sama da ta qasa, akan mi Aeeshaa zata tambayi Sabeer, sai kace an fada masa wani abun ne dan ta tambaya, tinda ita bata san ma halin da Sabeer ke ciki ba game da ita har yau.




Tana shiga ya ja mtar d qarfi, Baba mai gadi ya je ya bude shima da gudu.


Basu tsaya ko ina ba sai wani asibiti, dake kan hanyar unguwar tasu, private hospital ne mai tsada da kwararrun ma'aikata, nan da nan ya bude mata file, ta bi layi, akai mata BP da gwada nauyin ta, tana zaune kamar minti goma, aka kira ta ta shiga.


Miqewa yayi ya bi bayan ta.

Gaisawa sukai da likitan, sannan ya fara bayani.


"Doc dama na kawo mata ta ne dan Allah a taimaka a cire mata cikin da take dauke da shi, yarinya ce, ba zata wuce 20 ba, bana son abinda zai taba lfyr mata ta, beside i am not ready to have a baby,"



Kan Aeeshaa na duqe tana ta share hawaye masu zafi, dan tin da taji ciki gare ta ta ji soj cikin, itama tana son ta ga dan ta a duniya,amma qarfi d yaji ana neman a raba ta da shi, kallon Doctor tayi, idon ta yana nuna a tausaya mata,ba wanda zai ga Aeeshaa a lokacin bai tausaya mata ba.


Likita ya karanci halin Khaleefa a bayanan shi, mugunta ce kawai zata sa a cire cikin ba komai ba, kuma in yaqi amsar request din shi zai iya zuwa wani wajen a cire cikin da qarfin tsiya.



"K yallabai an gama, amma zan baka shawara, yanzu wannan gwajin da akai ma matar ka ya nuna tana dauke da mummunan hawan jini, wanda cire cikin nan zai iya jawowa a rasa rayuwar ta, so zan baku magani, ta dinga sha, nan da wata biyar inshaa Allah zai fice gaba daya, yanzu da tasha zai dinga fita kadan2, har ya gama fita dika, sannan zan saka mata kwata kwayar magani yanzu a gaban ta, inshaa Allahu, za a samu na sara, shawara dai d zan baku shine ku dinga yawan zuwa ina duba ta ana saka wannan kwayar maganin"


Aeeshaa kukan ta ne ya qaru, lallai wannan likitan bai da imani, kuma bai san aikin sh ba, Allah ya saka mata ta dinga maimaitawa.


"Yanzu zamu je mu auna muga wata nawa ne cikin, in ba damuwa?"


"Nooo ba damuwa,nima zan so naji wata nawa ne ai, amma likita kana ganin wata biyar bai yawa ba?"



"Kar kaji komai, ai kamar yau ne, a hankali zai dinga fita sabida matsalar datake da ita,ba dan matsalar nan ba ni da kaina zan markade ko meye a mahaifar ta ya fice,"



"Innalillahi😨😨😒😭😭😭"


Aeeshaa ce ta furta hakan cikin zaro ido da fashewa da kuka mai tsanani,


"Shut up stupid, anan ma sai kin nuna halin naki ko, naji maganar nam wajen Hajja kiga yanda zan maida ki,"



Murmushin yaqe yayi kula da Doc. Na kallon su.

Nan take Dr. Ya qara tabbatar d zargin shi, ba yau ya saba ganin maza na son a zubar da cikin halak ba, masu shegu su zubar masu na sunna su zubar sabida dalilin son zuciya.


"K madam muje damin scanning din, ba anan ake ba,ki kwantar d hankalin ki ba wani matsala, zai fita a hankali, ba zaki san ma yana fita ba saboda maganin da zan baki zai hana maki jin zafi,"



Wani daki suka je, likita yayi yayi Aeeshaa ta fada masa meke faruwa a tsakanin ta da mijin ta,amma sam taqi, wannan abina ya shafi iyalin su ne, ya yi aikn shi kawai tinda shima ba imanin gare shi ba.


"Look baiwar Allah, Aeeshaa kk ko? (Daga masa kai tayi) k, kinga na fahimci halin mijin ki, shi yasa na ke tambayar ki taimaka maki zan, dan inna bar shi ya kai ki wajen wasu, zubarwa zasuyi a banza,na sha ganin cases haka, so ki amince min zan taimaka maki,"


"Dan Allah ka tausaya min,ina son cikin nan, kar ka zubar min, bamu sn ma cikine dani ba sai da muka je gida yau, kakar mu ke fada, yanzu tana jiran result ne, dan Allah kar a zubar min da abinda ke ciki na😭😭😭"


"Ki daina kuka, inshaa Allah sai kin haifi abinda ke cikin ki,"



"Allah ya yarda, na gode,Allah ya saka maka da alkhairi,"


"Ameen, kwanta yanzu na duba na ga ni,"



Scaning akai mata, daga qarshe likita ya gano cikin ta ya kai wata hudu, amma ya yi takardar qarya, yace wata biyu ne.


Ko da ya sanar da Aeeshaa plan din shi, tayi murna sosai, sannan wannan maganin da yace tana zuwa ana saka mata antinatal care zata na zuwa, ya rubuta har da lokacin daya kamata tana zuwa, ya bata magungunan da zasu qara mata lfy da abinda ke cikin ta.



"Yallabai u ar good to go, amma akwai shawara sai ka jure, zaka dan dakata da yawan saduwa da ita, ya zamana lokaci zuwa lokaci ne, saboda mu samu maganin mu yayi aiki da wuri,"


"Ba damuwa na gode Doc, na gode sosai,"



"Akwai bayanai dake cikin wannan takardun dana rubuta zaka samu dik abinda kk nema,"



Aeeshaa kan ta a qasa, ta qi bari su hada ido da Khaleefa kar ya fahimci kwanciyar hankalin da ta samu.


*********************







Khaleefa ya fita sha'anin Aeeshaa kullum amma yana sata gaba ta sha magani, ko neman ta ya hakura,sai dai sanda jarabar shi ta motsa akan ta zai je dakin ta yayi ta romancyn din ta har sai ya biya buqatar shi, Rebecca kuwa kamar sallah dan.murnar samun khaleefa akai akai, ba damar ta tambayi dalili.


Da lokacin Antinatal yayi Aeeshaa zata dau adaidaita sahu ya kai ta asibiti, taga gama ta koma gida.



Umma tayi murna sosai d labarin cikin da Aeeshaa ke dauke da shi, amma ko da wasa bata sa maganar a labban ta ba balle wani ya ji, kayan yara unisex take siya a boye in taje sarin kayan ta.


Lokaci zuwa lokaci takan je gidan, tai kicin2, wai ita a dole kar a gane murna take zatai jikaπŸ˜’πŸ˜‚.


**********************





Ziyara ce ta musamman yau Maman Khaleefa zata kai ma su Aeeshaa, dan ta kwana biyu bata ga dan ta ba, sannan bata ji aike ba, yau so take taje taga meke hana shi zuwa, in ma dan Aeeshaa na da ciki ne ya daina bata kulawa zatai maganin su dika.............





*Allah ya kai hankalin Hajja kan ki Maman khaleefa kici.......πŸ™Š*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*








Page 15:









Aeeshaa na ta bacci Mama na ta kwada sallama, ko da a cikin mafarki bata ji sallamar nan ba, Mama dik ran ta ya baci, daki2 ta fara bi tana leqawa, ganin irin dukiyar da aka kashe a gidan ya qara bata haushi, yaran ta da akai ma aure ba wanda aka kashewa wannan dukiyar, (kamar Khaleefan ba dan ta bane) kwafa tayi, lokacin da ta isa dakin da Aeeshaa tai daidai take baccin ta cikin kwanciyar hankali, daga ita sai 'yar qaramar riga red mai hannun vest iya cinya, dik ta tattare sama, sai pant din ta red, ganin hakan bai sa Mama komawa baya tai sallama ko kwankwasawa ba har Aeeshan ta farka.

Qarasawa tai ta tashe ta, cikin magagin

Please Login or Register in order to submit comment