Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sa masa ido,"



Kashe wayar tai ta kalli Aeeshaa cikin tausayawa.



"Hajja akwai abinda nake son na nuna maki game da Yah Khaleefa,"



"Bana buqata, sai yanzu? Yanzu kk ga damar ki sanar dani ko ki nuna min wani abu game da mijin ki? Tin yaushe nake bin kan ki akan hakan? Kin nuna min? Riqe abin ki, nima na riqe abinda na sani akan shi, har a dawo daga dik gidan uwar daya tafi"



"Tafiya Hajiya?"



Banza Hajja ta mata ta shige kitchen, tar da kwalla mata kira akan taje suyi aikin abinci.........







*Team Sabeer me kuke gani game da shirun Hajja akan wannan lamari?.... Team Khaleefa me mutumin ku ke aikatawa a ABJ n a bamu mu sha...๐Ÿ˜…*
๐Ÿ’…๐Ÿผ *KUN MAKARO* ๐Ÿ’…๐Ÿผ








*BY HAERMEEBRAERH*








Page 22:







"Hadiza ni fa ban gane maki ba kwana biyu, kwata2 kin rage walwala, sannan yanayin jikin ki ma kin sauya, anya Hadiza? Kar ki sa na dinga maki zargin da ba haka bane, abinda nake zargin ki da shi bai kamata ace kina tare da shi ba duba da ke din bazawara ce"


"Goggo ki fito fili kice ciki ne da ni, yes ciki ne da ni, kuma cikin Khaleefa ne mijin Amarya,"


"Ya Allah, Ya kareem, Ya mannan, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wayyo Allah na,ya Allah ka sa mafarki nake, mummuna kar ka tabbatar da wannan lamarin,"


Kuka Hadiza ta fashe da shi, sai yanzu abun ke bata takaici, ta bata wayon ta, d tarbiyyar da Goggo ke bata a kullum, albasa batai halin ruwa ba.


Goggo ce a harzuqe ta nufe ta,

"Kukan me zaki? Ashe dik tarbiyyar danake baki a banza? Dama tin da naga fitar ki ta yi yawa addu'a ta Allah ya kiyaye mu kar ki dakkon magana, ashe ba zaki riqe maraicin ki ba da zawarcin ki har Allah ya kawo maki miji na gari, bayan kin san yanzu 'yan matan ma ba mijin suka samu ba, kowacce mace ta qanqame mijin ta bata son kishiya, koda kuwa mijin mai ra'ayin qara aure ne kin ban kunya, da ke da dikkan zawarawa masu aikata zina suna fakewa da zawarci suna aikara zina,tir da halin ki, tir da ke,"



Goggo fada kawai take ji take kamar ta rufe ta da duka, ba dan ta kai zuciya nesa ba da har ciwo sai ta jiwa Hadizan mummunam ciwo kuwa, dan a rayuwar duniya ba abinda ta tsana irin zina, ga shi Allah ya jarabci zuri'ar ta da ita, wannan mummunan labari in ya yadu a dangin su daga na uba har nata ai sun shiga uku, qara nesanta za ai da su, kuma ga mutan unguwa za su shiga bakin su, ohhh Hadiza ta dakko mata magana.



"Goggo dan Allah ki zauna kiji,ki daina daga hankalin ki, abinda ya faru ya faru,"


Dik daurewar Goggo sai da ta zabga mata magigicin mari wanda ya sa ta daina ganin haske na wasu mintina.


"Hadiza kar ki kaini maqura na maki abinda bana fata,dan uwar ki har kina da abin fada? Har ni zaki kalla cike kar na daga hankali na? Kin dagan shi tsaye ya zan ya kwanta yanzu, baki son na damu kk dau matakin wulaqanta ni, bani da buri wanda ya wuce na sama mana abinda zamu kai bakin mu, amma ke burin ki bai wice na ki watsar min da mutumci na ba ko? Allah ya shirya ki Hadiza?"



Hadiza ce ta fara magana cikin kuka sosai,

"Dan Allah Goggo ki hakuri, ki yafe min,inshaa Allahu wannan abun daya faru ba zi rusa komai ba indai kin ban hadin kai, so nake na aure shi, kinga shikenan mun samu surukin da zai dauke mana wahalhalin da muke ciki ko?"


"Ke yanzu kina ganin har kina da darajar da wani zai aura kuma? Me kk tanada da zaki ba namiji? Na farko dai na hana ki shafe2n mayukan nan na zamani kin kafe, fari banaki ba kowa ya gani ya san ba naki bane,dik yanda mai shafa mai ya so boyewa kar a gane wallahi sai an gane, kin zubda mutuncin mi a wajen mutane dan zasu gan ki baki waye ba, ke din ba ki da tarbiyya,ke mai sabon Allah ce kin sauya halittar da ya maki, kin raina Allah wa'iyazu billah, kina nuna masa bai iya halitta ba, ke ce kk iya, subhanallah,Hadiza baki iya girki ba, nayi2 ki koya kin qi, Hadiza baki da tsafta, da girman ki komai sai na maki in ban ba gidannan ya ruve dan qazanta ko?Hadiza ibada bata dame ki ba dik da damun ki da nake na saki gaba dan ki yi amma inaaa, Hadiza kwata2 ke ba yariyar kirki bace, kan wani ya fadamin na sani d kaina"



"Goggo.....kiiikiiii....yaaafeeminnn, inshaa Allahu na daina dikkan abinda kk ce, na tuba Goggo, daga yau na daina aikata dik abinda Allah yace, bana son na shiga wuta goggo, wayyooo Allah na, Allah ka yafe min, ya Allah kai me gafara ne kana son masu tuba Allah ka yafe min,"



Hadiza fa da gaske take kukan nan, kamar zata shide, gane cewa da gaske tame neman gafarar Allah da ta ta ne yasa ta rungume ta,tana lallashin ta, tar da kwantar mata da hankali.



"Goggo yanzu zubar da cikin za ai? Wata biyu ne da kwanaki, na je asibiti an tabbatar min da hakan,"



"Sam ba zamu zubar ba,yanda kk dakko sai kin haife shi,ina tausaya wa wannan mata yanda zata ji cin amanar da kk aikata mata,"


"Goggo na fiki tausaya mata yanzu, a da ina ganin itace babbar maqiyyiya ta,amma yanzu na fuskanci ni ce maqoyyiyar ta,kuma na cuci kaina,dan yanzu haka shi baya nan, ya tafi shaqatawa da wata karuwar shi,"




"Karuwar shi?"

Goggo ta fada cikin zaro ido da dafe qirji.


"Eh Goggo,kuma naji yace gidan su ma neman shi ake, Gogge ya kamata mu sanar da iyayen Shi zancen cikin, kar a zo daga baya suce basu san zancen ba,"



"Dan Allah kyale ni for now na ji da baqin cikin dake zuciya ta, na gaza a matsayina na uwa, na gaza, na gaza wajen baki tarbiyya da kula da dikkan abinda kk so, na gaza matuqa,"



Kuka Goggo take sosai, qirjin ta har dagawa yake, saboda tana ganin laifin ta ne hadiza ta lalace.



(Goggo kin iya qoqarin ki, sana'a harda saida quli kinyi a shekarun da wasu suna can suna cashewa a gidan miji, babban laifi na dangana shi ga dangin uban Hadiza da basu taimaka maku ba financially, sannan kuma sun gaza wajen tsayawa a koda yaushe suna zuwa Hadiza taji akwai namiji fa akan ta da yake kula da ita, har da matsalar dangin ki Goggo ba ke daya bace, saboda da basu dorawa kan su girman kai ba na in kana da shi muyi da kai, in baka da shi ba zamuyi d kai ba, rayuwar mace bazawara wadda mijin ta ya mutu ita daya akwai illa a barta sakaka, musamman gata da diya itama bazawara, ku dubamin Umman Aeeshaa, da dangin ta suka tsaya mata suka ja ta a jiki, aka hada su da namiji yake zaune da su, bayan ya tafi Umman Aeeshaa dik da tsananin ta yayi yawa amma ba laifi an samu Aeeshaa mai kyakkyawan hali matsala daya bata da wayewa ta zamani dan haka bata san ya zata tafi da rayuwar gidan auren ta ba, har ta samu na sarar gyara tauratauran mijin ta ba, so ni dai a ganina Goggo kar ki dorawa kan ki laifin, ko ya kuka ce fans)



Hadiza na zaune tana qulla irin rashin mutuncin da zata yiwa Khaleefa, dan haka miqewa tayi ta yi wanka, ta shirya cikin shigar ta da take yaudarar mutane ta leqa taga Goggo na kan sallaya dan yin sallar asr, fita kawai tayi dan tasan Goggo ta san ina zata hanawa za tai, bata shirya haifar dan da bai da uba sananne ba.



***********************







"Hajja dan Allah kiyi hakuri, ki saurari me zan fada maki, kar ki ga laifi na akan qin sanar dake abinda ke faruwa agidan aure na, ba wai soyayya ce tsakani na da Yah Khaleefa ba, komai zai min a cikin hakuri zai min nima haka,dan haka ban ga dalilin da zai sa na kawo qarar shi ba. Rayuwar shi dama ya saba ta tin kafin nazo, ni shaida ce, sai da nai kuka,nai roqo kar a hada auren mu, Hajja ke kk ban hakuri kuma na hakura, hakurin na ci gaba da yi dan baki nuna min yanda zan kwaci kaina ba in ana musguna min, Ummana bata koya min ba, Hajja laifi na ne?"



Hajja da sauri ta rungume Aeeshaa dake kuka, dan iyakar gaskiyar ta take fada, (ku kula da wani abu, still Aeeshaa bata fadi aibun Khaleefa ba fa har yanzu, saboda bata son aibata ma Hajja jikan ta a gaban idon ta, tana son komai Allah ya bayyana masu shi su gani, domin addu'ar ta ke nan a boye kullum, hakan ne zai bata qima a idon kowa da daraja da daukaka, da kuma soyayya da tausayawar kowa)



"Aeeshaa ki yafe mana, mune muka tura ki inda zaki wahala, da na san boyayyen halin wannan dan banzan da ba zan dage a hada ku ba, a tinanina shi din mutumin kirki ne, MUN MAKARO yanzu, cuta ya riga ya cuce ki, ki kwantar da hankalin ki, yau yau dinnan za a dakkon dan iska ko da kuwa a kan magajiyar karuwai yake kwance ba karuwa ba,"




Kunya ce ta kama Aeeshaa ta sunne kai, hira suke ta tabawa, suka ji horn din motar gidan.


"Is time, saka hijab muje,"



Saqo Hajja ta duba a wayar ta, nan da nan ta fara kiran yaran ta gaba dayan su, har Umma.


Sojoji ne majiya qarfi, wanda in aka hada mutum goma da daya sai sun ji a jikin su, dan dukan mutuwa zasu mashi, su biyu ne, sai muzurai suke, dik wata cika da bunqasa da kamalar Khaleefa ta bace, Sabeer ne da Hassana suka fito, Hassana na ganin wasannan gidiga2n ta koma baya tana karkarwa, meke faruwa? Sabeer ma dan namiji ne, ya sa ya tsaya yana matsewa tare da tambayar su su din su waye?



Banza sukai da shi, sikabi kwatancen Hajja, dayan ne ya leqa cikin mota ya damqo Khaleefa, ya wurgo shi waje, Khaleefa dai ba baki, yayi magana bai san wadannan mutane me aka umarce su smasa ba, dan haka a gaba ya wuce tin kafin su yi magana da muryar su kamar aradu.


Motar Umma da Keke napep din Hadiza a tare suka iso, bude masu akai kowa ya shigo, Umma na kallon Hadiza Hadiza na kallon Umma, kowa da abinda yake saqawa a ran shi..............................













*Ba zan iya aje ku cikin jira da jimamin me zai faru ba, thanks for the love, Uhibbukum fillah,Allah yasa nima domin shi kuke so na ba domin novel baโค*
๐Ÿ’…๐Ÿผ *KUN MAKARO* ๐Ÿ’…๐Ÿผ







*BY HAERMEEBRAERH*








Page 23:







Kowa ya taru a parlour, Hajja ta fita waje da sojojin da tai ta sawa aikin kula da shige da fice Khaleefa waje, kudi ta dakko masu yawa ta basu amma sam suka qi amsa, saboda sun sani ba zasu biya General abin da ya musu ba na kyautatawa.


Haka tai ta masu godiya, ta koma ciki, General kan shi yayi mamakin wannan abu, dan baida masaniya akan ko daya, kowa jira yake yaji me Khaleefa ya aikata da aka masa wannan kamun kazar kukun, banda Baban shi, dan Baban shi ya san tabbas Hajja na sane da iskancin da yake aikatawa, shine dalilin taron, ran shi baqiqirin saboda taron akan ahalin shi ne.



Sallama tayi a bakin parlourn ta jira akai maya izinin shiga,



"Baiwar Allah daha ina?"

Umma ta tambaye ta,


"Khadeeja bar ta ta zauna, zaman itama ya shafe ta,tin sanda na gan ki dama na san ke ba alkhairi bace a cikin iyalina, zauna kema,"



Hadiza dik jiki a sanyaye, to me aka sani game da ita kuma?

'Yau na kawo kaina makasa, dan naga wasu qattin sojoji a waje bayan dattijuwar nan ta gama.masu magana naga sun qame, Allah k kare ni kar a nadan duka,'


"Assalamu alaikum, kamar yanda kuka sani, dik wani abu mai mahimmanci muna masa zama, saboda mu samu mafita in muka hada kai wajen warware dikkan matsalar mu, dan haka wannan karon ma ni Hajja Aeeshaa na gayyato ku dan na sanar daku halayen Khaleefa wanda mu kakanni da iyayen shi bamu san yana dauke da su ba, wanda ko mai Khaleefa ya zama a yau, zan dorawa ma ku laifi iyayen shi da General kan shi, sakamakon sangarta shi da akai, wanda kullum fada na kenan da yana yaro, ba laifi bane bawa yaro gata, amma irin wanda akai ma Khaleefa yayi yawa, kasancewar shi jikan fari a gidannan, yasa aka shagwaba shi, komai extra ake masa akan sa'o'in shi,kar na cika ku da surutu, ku duba wannan hotunan, sannan ke kuma ki nuna masu abinda kk gani a wayar ki,"



Nan da nan Aeeshaa ta shiga wajen hotuna inda tai screenshot din hoton Hadiza da Khaleefa, Hajja ta rarrabawa iyalan ta hotunan da aka wanko mata,


Masu salati na yi masu hawaye ma nayi, masu kada kai da bude baki nayi,kowa da irin reaction din shi, a sannan ne Aeeshaa ma ta samu ganin hotunan, Hadiza kam ba baki, sai raba ido take,saboda in wasu suka kalli hotunan hannun su sai su kalli Hadizan,


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,yanzu Khaleefan mu shi ke aikata wannan mummnan zunibai? Camerar mutum ta dauke ka haka Khaleefa ina ga vedio da zaka gani na kan ka a lahira wanda daga ubangiji yake har na dakunan da ka shiga ka aikata laifi sai an dakko? Mun fita dikkan haqqin ka Khaleefa, gaskiyar ki ne Hajja laifi dik namu ne musamman ni, a ganina shine jikana na farko, shi yasa na shagwaba shi, na bashi dikkan gata, ashe gata na yawa? Abinda zaka saka mana da shi kenan? Zina?da auren ka? Ka ban kunya Khaleefa, ka kuma fita daga raina,"


Kuka General ya fashe dashi dik daurewar da yake ba zai jure ba, irin wannan hotuna haka.


"Ita wannan din wace ce, wannan dai gata a gaban mu,"


"Ita ce inajin wadda ka kk cewa zaku Abuja ko? A kai ku club mai tsada, tin da ka tafi ja kashe wayar ka,ko ina baka nan, ba yanda za ai a gan ka ko a ji ka,"


Tashi yayi ya hau dukan Khaleefa, ko ta ina duka yake, Maman shi kallon shi kawai take, ta kasa koda kukan ne, lallai wannan zamani na da abin tsoro, zina tayi yawan da har yaro zai na aikata ta iyayen shi na zaune baki bude basu sani ba, kuma mutane na gani, dan ga shi Khaeefa da Hadiza a bainar jama'a tana shagwaba yana lalashin ta wani ya dauke ta, wani a mota suna shan ice cream, na wayar Aeeshaa ma suna shan Ice cream ne a rana daya ne da wanda sojojin suka dakko, sannan ga in da ya aje ta, ga inda ya shiga gida itama ta shiga nasu gidan, ga inda da Aeeshaa tai ta fiya take satar jiki ta shiga da sanda take fita, har time sai da suka rubuta a jiki,



Aeeshaa ma kukan take, nan da nan Sabeer ya dinga tina ganin shi da yayi da wata, har ya tambayi mai gadi ya qaryata shi, ya rufa magana.



Hassana sai godewa Allah take da bai hada ta da shi a matsayin miji ba, da har zata cuci kan ta akan son zuciya.



"To yanzu dai kun ga ko nace mun ga waye jikan mu, kuma dan ku, in ka yi qoqarin boye mana halayen ka munana, Allah yana kallon ka, dan haka yanzu meye hukuncin daya dace da shi, dan ba zai zama an kyale shi ba,"




"Da farko da kan a yanke hukunci ya kamata aji me ya kawo wannan yarinya,"


Kallon kallo sukai da Khaleefa, ya mugun ba Hadiza tausayi, Aeeshaa ma sak da ta tausaya masa, dan da alama ya ci uban bugu wajen sojojin nan wajen masu taurin kai, bakin shi a kumbure yake kamar wani barawo, rigar shi ta yage ta gaba, da gani an jijjiga shi yafi a qirgawaya sani ma ko da rigr suke daga shi sama?


Amma da alamar har yanzu bai laushi ba, saboda yanda yake wani ciccin magani.


"Ke yarinya me ke tafe da ke?"


Ido ya ma Hadiza yawa, dik sanyin AC dake wajen bai hana ta zufa ba, musamman in ta kalli idon General da Hajja, idon Hajja yafi firgita ta, tin randa suka fara haduwa idon Hajja ke mata gizo, yau ma cikin rudani ta fara magana,


"Ddddamaama ci ci...ciiikiiii neee dddadddaaniii, shineee immm shinee immm....."


"Ya isa dalla, munji, yanzu wanne hukunci ne kuke ganin ya dace da wannan dan iskan,dan nayi alqawari sai na dandana maka azaba da wulaqancin da ka dinga yi wa wannan yarinyar, dik da taurin kan ta ya qi ya bar ta ta fada min irn zaman da kukai, amma na gano wasu abubuwa daga kalaman wannan maciyar amanar, ta saqon messages din ku, da kuma randa naje gidan naku,"


"Hajiya ke ce kikai zurfin tinanin gyara iyalin nan namu, da yin binciken da bamuyi ba da fari saboda son zuciya da kuma ganin dik gida ne ba lallai ne a yi bincike ba, dan haka mun bar maki wuqa da nama ki yi hukunci akan wannan lamarin, ni mijin mi na amince maki da ki yanke hukunci dari bisa dari,,"



"Na gode, Muhammadu kana da haqqi akan dan ka, me kk gani ya dace? Ko ke mahaifiyar shi kuyi magana,"


"Hajja ko wanne hukunci kk yanke daidai ne,"



Juyawa tayi taga yanda Khaleefa ke wan cika yana batsewa, wai shi tantiri,


"Dama na fada maka ni na haifi uban ka, dik wani tantirancin ka na dame ka na shanye, akwai ranar da asirin ka zai tonu, yau ce ranar, dan haka ni na fara qauna da sha'awar a hada auren ku ko? Yanzu na qara tinani akai nace ka sauqaqe mata auren, dan uban ka,in ka min taurin kai na ci uwar ka, kar ka ganni haka inna da ke ka sai an maka ruwan zafi a wajen, maza ga takarda da biro nan rubuta mata saki, ko kana so ko baka so,"




Da mamakin kowa a wajen budar bakin Khaleefa da ya kumbura yayi sintim shine,

"Balle ma bana so, auren da aka qaqabamin, bana so, ban taba son ta ba, kuma bana jin nan gaba zan so ta, taje na sake ta saki uku, "


Wani irin abu ne mai zafi ya soki Sabeer a zuciya, Aesshaa ake wulaqantawa haka, mace mai daraja a wajen shi, amma Khaleefa yayi asara, yayi asara mabayyaniya.



Ya ja takarda ya rubuta, ai Hajja bata san ta isa gaban Khaleefa ba, sai saukar maruka ya dinga ji, ko damar dafewa bai samu ba, sai da ya kifa,



Nishi take tana haki,tare da magana,



"Ba baki nake maka ba, amma Khaleefa zaka ga rayuwa, zaka ga rayuwa ta yanda ba ka taba tsammanin ta ba, zaka dora hannu ko a gaban mu ko a bayan idon mu ka yi kukan abinda ka aikata, Allah shine shaida mun fita haqqin ka,.....ke kuma, ki je gida, zamu kula da komai naki har ki haihu, bayan haihuwa zan sa a aura maki shi, ko kina so ko baki so, ni na yanke hukunci baki da miji sai shi, sai dai in Allah ne bai nufa ba.....tashi ki bar nan.




"Auwal, John!!! Come and lock him for me, don't set him free untill i said so,go with him,"



Tinawa da karon su ne yasa Khaleefa fashewa da kuka, ji yayi wani tsoro da kadaici ya kama shi, ai bai gama tinani ba yaji anyi sama da shi, ko qasa vaya tabawa, haka suka tasa qeyar shi a gaba, suka wuce da shi.




"Yanzu magariba ake kira, ke Khadeejaa ki je ki debo yaran nan ku rufe gidan, sabon mai gadin dana kai maku shi zai ci gaba da zama har n gama sa ke anan,.....kin rifen baki kin daina kukan nan ko sai na kokkora maki mari? Mara zuciya kawai, namamajon kikewa kuka? Dan ya rabu dake dubun shi na son ki"



Diff kk ji, dik da ba hakan ne ya sa ta kuka kadai ba, tausayin kan ta take, da qananan shekaru ta zama bazawara.


"Hajja Allah ya miki albarka, ya sanya ki a aljannatul firdausi, ba dan ke ba da ina nan ina daga kai a abokai daga 'ya'yana har jikokina ba dan banza,ba dan ke ba da rayuwar iyalina na cikin wuta ban gani ba, bayan Allah yace mu kiyaye kan mu da iyalan mu daga wuta, Hajja kin dauki role din miji yau na sama hotiho,"




Baba General ke zubda hawaye a karo na ba adadi, a yau, da kyar kowa ke bashi hakuri, sallah suka tashi suka tafi, Maman khaleefa da kyar ta tashi, sai da Ummen sabeer ta taimaka mata, a sannan ta samu kuka ya kwace mata, dan ta ne ya sama hamshaqn mazinaci haka, tana nan ba abinda ta sa a gaba sai kudi, da son gayu, bata san halin da yake ciki ba, bata damu da ina yaje, me yasa yayi dare ba, iyayen yanzu gani suke mace kawai ake ba tarbiyya, namiji daya balaga an gama da shi, bayan maza na ingiza mata yin zina, dik da matan ma ba a bar su a baya ba.



Sallah suka tafi kowa da abinda ke zuciyar shi.


Sabeer bai san a wanne hali yake ba, tsakanin baqin ciki da tausayin 'yan uwan nashi, ji yake kamar yaje ya lallashi Aeeshaa, Ameerah sai kuka take.



********************









Wani qaramin gida ne kamar ma hayar shi akai, masai na qasa, komai na qasa amma an masa plasta, da siminti, katifu uku ne a gidan daki biyu,daya na Khaleefa, daya na su, sai bandaki, daya,da kitchen, bandakin a rufe yake ruf, amma ba qofa, dakunan da gani sabbin qofofi aka sanya masu, na qarfe ne masu kwari sosai.



Ledar dakin mai kyau, amma ba zanin gado a katifar.

Wurga shi sukai, suka rufe, yana ta ihu, yana su bude shi, kar ya fusata, wanda aka kira John ne da gurbatacciyar hausar shi yace,


"Me sa ka yi in ba ah bude ka ba?"


Yana muzurai, lafewa Khaleefa yayi, ya yi shiru, idanun shi fal hawaye..............





*๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐ŸคฃAllah de ya biya Khaleefan Mero Tsokana๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ*
๐Ÿ’…๐Ÿผ *KUN MAKARO* ๐Ÿ’…๐Ÿผ







*BY HAERMEEBRAERH*






Page 24:









"Daga ina kk? Ashe dik maganar da mukai dake ba zaki dauki ko daga daga ciki ba ko? Ke rayuwar ki yanda kk so haka zaki yi ba wanda ya isa ya hana ki ko ya saka ko ko? N roqi Allah daya shiryar min dake, (kuna ganin rashin ji irin na Hadiza amma hakan bai sa mahaifiyar ta zazzage ta va, ko ta aibata ta, ko ta tsine mata, a'a sai fa mata fatan shiriya)"



"Goggo ba wani wajen naje ba, gidan su Khaleefa naje, kiyi hakuri ki zauna kiji me ya faru, da na je din,"



Zama Goggo tayi, Hadiza ta labarta mata komai,Goggo ta yabawa qoqarin iyayen Khaleefa na hadin kan gyara masa rayuwa,ba su damu da girman shi ba, da shi din magidanci ne, ba su kalli shekarun shi ba, suka hada qardi d qarfe suka hukunta shi haka, lallai da za a na samun iyaye irin na Khaleefa da wasu abubuwan sun ragu.



"To ba wannan ba kinyi salla?"



Sosa hanci ta fara, in bata manta ba ko ta la'asar batai ba ga magrib ta riske ta, ana neman yin isha'i ne ma yanzun.


"Hadiza ina maki nasiha kiji tsoron Allah, ki kiyaye dokokin Allah,Allah sai ya kiyaye ki,Allah ya baki rai, ya baki lfy, ya baki arziqi na wajen zama da ruwa kina iya diban ruwa kiyi wanka ki fice yawon tazubar amma alwala da ba zaki wahala bama tana maki wahala, kina iya kwantawa kiyi awa biyar kina chatting amma ki ware minti shabiyar kiyi sallah yana maki wahala,kina iya yin rawa wai san motsa jiki ki ta zufa,amma sallah na maki wahala, lallai Hadiza imani kk rasa, da kinyi imani da Allah kin kuma san yana kallon ki a dikkan abinda kk, numfashin ki daya bya fita face da sanin Allah, qifatawar idon ki daya baya kasantuwa face Allah ya gani, Hadiza da kina da imani da kin san hakan, da kin gyara rayuwar ki kin maida sallah abin so,kuma da kna yin ta da nishadi da shauqi, inace nan kk satar jiki ki tafi wajen dik wani qato da kk so? Ashe Allah

Please Login or Register in order to submit comment