Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali2 ta fahimci cewar mijin ta fa ya rasu, ya barsu bari na har abada, dik da ta san hakan tafi son ta zauna nan, daga wannan lokacin halayen ta suka sauya, da Aeeshaa yar gata ce a wajen ta, amma yanzu kwata2 gani take in ta sa ta a rai itama wataran mutuwa zatai ta bar ta, dan haka take janye ta a ran ta da jikin ta,Sabeer shi ya ci gaba da zama da su, bayan rasuwar mijin goggon tashi, nan ya ci gaba da karatun shi kafin daga baya ya tafi qarin ilimi, sun shaqu sosai da Aeeshaa, ba kadan ba.



Suna shiga Khaleefa yana qoqarin fita,


"Lahhhh ga Yah Khaleefa Umma, Yah khaleefa !"



"Malama ki daina cika mana kunne kin san ba kula ki zai ba,"


Murguda baki Ameena tayi, dan ita mai son mutane ce.

Khaleefa ne ya leqo kan shi ta window, ya daga masu hannu, tare da motsa labban shi, babu wanda yasan me yake fada, Sabeer yaji haushin hakan sosai, dik da dama ba wani jituwa suke ba, amma a qalla yayi tafiya, domin zumuncin dake tsakanin su ma ai ya nuna kulawar shi.


Shima yaqen yayi masa ya daga hannu, ya sa kai a da mota, Khaleefa shima ficewa yayi abin shi.


"Wai fa Yah Khaleefa na nufin wannan daga hannun da yaqe haqoran harda ke a gaisuwar,"


"Na sani, muje ciki, matar shi nada aiki matuqa,"



Da murna Sabeer ya yi bangaren mahaifan shi, inda suka taru suna taya shi murnar kammala karatun shi da cikakkiyar nasara, Umman su Aeeshaa bangaren Hajja ta nufa.


Hira suke sosai, Hajja tayi gyaran murya, tare da kiran sunan Umma.


Cikin maida hankali kan mahaifiyar ta ta, ta aje cup din dake hannun ta, ta amsa,



"Khadeeja, na dade ina tattauna wannan maganar a zuciyata, amma bansan ya zaki dauke ta ba, shiyasa ban sanar da kowa ba, ina son muyi maganar dake da farko,"




"Hajja wannan wace magana ce mai mahimmanci haka?"



"Magana ce akan Aeeshaa, ina ganin tinda yanzu tana aji biyar na sakandire, ya kamata a tsayar mata da mijin aure, danni ban yarda da dogon karatun nan na boko ba aure ba, me kk gani?"


Kunya ce ta kama Umma, wai yau tayi girman da ake maganar aurar da diyar ta, ga wani kewar mijin ta daya kama zuciyar ta, kamar daga sama taji sunan da Hajja ta ambata, sannan wai fa shi take jiyo muryar Hajja tana cewa za a hada auren su da Aeeshaan ta...........





*Wadda ta canki sunan wanda za a aurama Aeeshaa zan bata biyay* πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ







*BY HAERMEEBRAERH*









Page 3:







"Me kuke tattaunawa ne haka, Tinda na shigo nake jin muryar ki?"


Zama yayi tare da kallon Khadeeja wadda ta bude baki, kamar tana cikin rudani.


"Ina fada ma Nana Khadeeja ra'ayina ne game da maganar da muka tattauna, amma naga kamar hankalin tama baya tare dani,"



Da kyar ta tattaro murmushi ta saka a fuskar ta, ko ba komai Aeeshaa diyar ta ce, kaza na taka dan ta ba dan bata so ba, sai dan ta ladabtar da shi, anya zata iya yin shiru akan wannan hadin da Hajja ke so kuwa?


"Baba barka da yamma,"

"Barka dai 'yar baba, ya abokina da matan nan nawa masu yanga?"


Sunkunyar da kan ta qasa tai sosai, saboda ita din akwai kunya matuqa, amma in ta bangaren kasuwancin tane, ko da qawayen ta ba wannan maganar wai kunya.


"Suna lfy, munzo da su Abdul, Hajja qarama tana gida, kasan ta da aiki, ga son karatu, tace zata zo amma ba yau ba"

(Sannu Umma da gilla qarya😏)


"Allah sarki, gaskiya Aeeshaa tayo halayya irin ta ki uwar gida na, komai na dabi'un ta naki ne, Allah ya qara maku kyakkyawan hali ku yi koyi da Nana Aeeshaa,"


"Ameen,"


Suka amsa, waya Baba General ya dauka, ya hau kiraye2, sai dai kawai suji yana fadin,


"Assalamu alaikum,...... kazo da iyalan ka, ina neman ka......yauwa sai kun shigo,"



Miqewa Umma tayi dan zuwa wanke hannun ta, da tai ciye2,


"Ina zaki? Ai zaman kusan naki ne, dik da naga ba kizo da Aeeshaa ba amma maganar nada mahimmanci wajen Hajjan ku, ya kamata a yi ga yau,"



Wani abu ta hadiya mai daci, dan indai bata bata ji ba, wannan hadin bai mata ba sam.


"Hannu zan wanke kafin su iso,"


"To...to... je ki, ki dan taho min da abin sha,"


Hajja ce ta miqe da sauri tana bawa mijin nata hakurin rashin kawo masa abin sha da batai ba, nuna mata yayi babu komai, tayi zaman ta, ga Khadeeja nan, ai ba sai ta tashi ba.

(Uwar gida wannan ba dalili bane da zai sa miji ya dawo taqamar kina da yara ki make a gefe, qafa daya kan daya, kina kallo kina watsa inibi, da juice, ki sa yara su kaima baban su komai, ke bazaki je ba, in mijin kine ya aminta, saboda baya son wahalar ki, baya son kin gama aiki, ki wahala, ya amince yara sukai masa, kuma kka tabbatar har ranshi ne, shikenan, amma baki da dalili in ba shi ya aminta ba)


Daya bayan daya suka dinga shigowa, Abdul da Ameena kusa da Hajja suka zauna, amma daga baya Baba General yace su shiga ciki suyi wasa, sai da suka qara minti bakwai kafin mai sarauta Khaleefa ya shigo, yana wani babbata rai, ya samu gefe ya zauna shi kadai, da kyar ya bude baki yayi sallama ya gaida su, in badan sun kalli leben shi ba, ba mai gane me yake fada.



"To da farko dai zan yiwa Allah godiya daya bani zuri'a kyakkyawa,mai riqo da addini kamar ku, kuma ina maku godiya akan hadin kan ku da zumun cin ku, musamman kai Abubakar, ka riqe zumunci guda biyu, na farko na 'yan uwantaka, sannan na abokantaka, ka tsaya tsayin daka iyalin Salihu basu koka ba, kuma qanwar ka da take bazawara bata wulaqanta ba, Allah ya saka maka da alkhairi,"


"Ameen,"

Kowa ya amsa, banda mai muqami, (Khaleefa).

"Toh saboda wannan zumunci naku ya qara qarfi, hajja da ni mukai tinani, muka ga tinda Aeeshaa ta kusan kammala Secondaryn ta, me zai hana da ta gama a aurar da ita, tinda a wannan zamanin ba kowacce yarinya bace zaya fara makarantar gaba da Secondary ba ba tare da ta lalata rayuwar ta ba,"



Khaleefa ne ya dan ja guntun tsaki, dan za ayi maganar yarinyar nan me zai sa sai an wani kira su? Kawai dan a hana shi shan iska.

Sabeer kuwa wani farin ciki ne ya lullube shi, musamman da yaji an yabi mahaifin shi, kuma anyi zancen auren Aeeshaa, tabbas addu'ar shi ta shekara da shekaru zata amsu, musamman yau dinnan haka kawai yake sake jin ta sabuwa a zuciyar shi, tin da ya dora ido akan ta yaga yanda ta koma; yaji bai ma kan shi zaben tumun dare ba.

Hassana dake zaune, tana qunquni a ran ta, na ganin ita da ta girmi Aeeshaa nesa ba kusa ba ba wanda ya yi maganar aurar da ita da abin son ta, sai qaramar yarinya kamar Aeeshaa, ita Degree gare ta bangaren Accounting, amma Baba General ya hana ta aiki tace sai sanda tai aure tayi a gidan mijin ta, a yanzu ma bata da samari, ina ga ta fara aiki? Ai gudun ta zasu nayi suce tafi qarfin su.


"Kai Khaleefa nayi2 ka samar ma kan ka macen aure, amma girman kai ya hana ka, na san komai lokaci ne, na so ace na baka dama ka zabi wadda ta yi maka, dan kai auren soyayya irin nawa da kakar ku ka more aure, amma ka tsaya ruwan ido, kamar jira kk a kawo maka mace daga gidan sarkin makka,to mun yanke shawarar aura maka Aeeshaa dik sanda ta kammala makarantar ta,"


Su ukun a tare suka miqe tare sa furta,



"Whattt!!!!"


"Yes, Khaleefa nace zai auri Aeeshaa, meye naku a ciki da kai da ke?"πŸ‘‰πŸ‘³πŸ»β™€πŸ§•πŸ»




Komawa Sabeer yayi, cikin tsananin takaici, da qunar rai, tare da karyewar zuciya mai tsanani, idon shi ya kada yayi jawur, jijiyoyin kan shi sun firfito.


Hassana kuwa kuka ta saka, amma qasa2, yanda Maman su kawai ke jin ta, sai zungurin ta take da qafa amma bata daina ba.



"Ina sauraron ku, wannan reaction din da kuka nuna min na meye? Baku goyon bayan hukuncin mune ko mi?"


Shiru wajen, Umman su Aeeshaa, ba abinda take sai ambaton Allah, wannan wanne irin hadi ne? In bata manta ba, ta san Hassana ke matsanancin son Khaleefa, kuma daga alama Sabeer na son Aeeshaa, ba dan kar a ga rashin kunyar ta ba, lallai da tai bayani, amma bari ta jira ko yayun ta zasu fahimtar da Baba General.


"Ba fa na so ina magana ana min shiru, alama ce ta hukuncina bai ba, kuma a cikin ku ba mai iya bayyana meke ran shi, in ba zaku amsa ni ba kowa ya tashi ya bar min parlour,aure ne inshaa Allah ba za a fasa ba, dan in ta wannan shashashan ne ba zai aure ba ina jin, yaro kamar wanda aljana ta aura,"


"Allah ya sanya alkhairi, ya musu albarka gaba daya, ai bamu da abin cewa Baba, sai dai mu maka godiya da fatan qarin imani da nisan kwana mai albarka,"

Cewar Baba Basheer kenan.

Baba Abubakar ma addu'a yayi da sanya albarka, daga nan Umma ta san magana ta tsaya a haka kenan, itana addu'a tai ma mahaifan ta, da godiya, nan yaran suka fice, Hassana ko gaban ta bata gani dan kuka, tayi bangaren su, Maman ta taso bin ta, dan ta lallashe ta,amma ta zauna dan su ci gaba da hirar su ta zumunci kamar yanda suka saba bayan an yi taro makamancin haka.


Maman Khaleefa ita hadin ba wai ya dame ta bane, bata da wani ra'ayi akai, amma Baba Basheer yayi murna da hakan, dan yana zargin danshi aljanu sun taba shi, bai taba zancen mace ba a rayuwar shi, kuma bama yaso a masa.


Kamar zai tashi sama, haka ya ke tafiya, dakin shi, hannun shi a kan shi, ya kai ya kawo haka yake shafa kan, kamar zai kankaro fatar kan nashi.

A kan gado ya fada, yana furzar da wata irin iska mai zafi, wannan wane irin hukunci ne haka? Shi yace yana son wannann kwailar yarinyar ne? Me zai da ita, manyan mata ma bai kalla ba balle ita, gaskiya an cuce shi, a rayuwar shi yana son ya ga ya samu mace babba, mai hankali, mai kyaun jiki,wadda ba zata na tara masa yara ba, dan kar jikin ta ya baci, wadda komai ta saka zai zauna a jikin ta yayi dass,ko Hassana abinda yasa bai son ta, tana da sakakkken jiki, ya sha ganin ta da daurin qirji, ko ya shiga kaida Bappan shi, ko kuma Baba General ya aikashi wani abun, gaba daya nonon ta sun sake, shi kuwa yanda ya saba kallon fina-finan turawa, yana ganin su kyam ba karkata, kamar zasu tsokane ma mutum ido ba abinda zai kai shi auren wadda nonon ta yake a kwance.



Su suke ganin shi shur2, amma shi ya san mugun dan duniya ne a qarqashin qasa, kallon fina2n batsa ba wanda ya fishi, a rana sai ya kalli film sama da kala biyar na batsa, ya toshe kunne dan kar a jiyo shi, dakin shi akwai bandaki, da dan qaramin parlour,lokuta da dama in ya dawo daga wajen aiki, musamman na dare, in ya fito kan ya isa gida, ta hanyar Airport yana karkatawa wani hotel, nan zai sha iska, yaci abinci, mata na gilmawa yana kallo, in yaga wadda jikin ta ya masa suyi ciniki, ya biya, ya huta da ita ya dawo gida, ba wanda ya san yana aikata hakan, daga Allah sai shi, sai kuma matan da yake hakan da su.


Halin shi mafi muni bai bawa ibada hankali ba, kwata2 shi khamsa salawat bai damu da sauke su ba, balle ya qara da nawafil, amma dan ganin ido, in yana gida,iyayen shi na gida yana riga kowa zuwa masjid.


Kowa a iyayen shi zasuce Khaleefa ba ruwan shi, sai dai hana da matsala wajen miskilanci, sannan sukan bada shaida akan shi din mai ibada ne, kuma mai riqo da addini ne.


Akan idon ta ya wuce, dan haka ta share hawayen ta,ta sake gyara jikin ta da fesa turaruka,powder ta gogawa fuskar ta mai cike da pimples, ta shafa man lebe, ta fice zuwa dakin shi, ta gaban Sabeer ta wuce bai ko san ta wuce va, tsabar damuwar da yake ciki, shawara ya yanke ba zai koma gidan nan ba, ya bar zama dasu, dan ba zai iya ganin ta ba bayan an mallakawa dan uwan shi ita, da sauri ya bat gidan, dan kar Umma tace yaje su wuce gida.


Kwance ta ganshi, yana kallon sama.


Qamshin da take ne ya sashi kallon bakin qofa, ta lankwashe hannayen ta ta turo su gaba, alamar tsoro da fargaba.

Cikin isa da ikon shi ya furta.

"Me ya kawo ki dakina?"

Bata ji me ya fada ba, dan haka gab da shi ta matsa ta ce.


"Na'am? Me kace Yah khaleefa?"


A tsawace ya amsa ta da,


"Nace me ya kawo ki dakina?"

Cikn sarqaqqiyar murya tare da durqushewa a gavan shi tana mai zubda hawaye masu zafi na tsantsar son da take masa tace,



"Yah khaleefa dan Allah ka rufan asiri ka aureni, ka fada ma Baba General ni kk so, ko baka so na na amnce zan zauna d kai a haka, zan baka kulawar da uwa ke bawa dan ta, kai fiye da haka ma, zan jiyar d kai dadin da ko a mafarki ba ka taba tsammanin samu wajen wata ba, Yah dik abinda kk so shi zanyi, ba zan aikata wanda baka so ba..""




Hannu ta sa ta shafo cinyar shi, a qoqarin ta na riqe masa riga, wata zabura yayi yai baya, tare da daga hannu ya wanke ta da wani irin marin da bai san ya mata shi ba, ko dafe wajen batai ba, ta sake jan rigar shi



"Yah khaleefa ka dake ni, indai zai sa kaji dadi, ni dai fatana dan Allah ka aureni, dan Allah kar ka gujeni,"



Fisge rigar shi yayi, ya ja hannun ta, kamar wanda zai ce mata wani abun, can kuma ya fasa, dan in ya sanar da ita dalilin dayasa bai son ta ya ci mata fuska, kuma wannan me nacin zata ce zata ci gaba da manne masa, dan hakan ba zai zama kwakkwaran dalili ba a wajen su, hanyar waje yayi da ita, still yanda ya riqe ta kamar zai mata magana, suna zuwa bakin qofa ya bude ya hankada ta ya rufe.



A parlourn gidan ta hadu da Ameena,wadda take zaune jikin Maman khaleefa suna hira, da sauri Ameena taje kusa da ita,



"Adda Hassana sannu, faduwa kikai?"


Wani kallo ta wurgawa yarinyar da sauri Ameena ta janye ta koma gefe, wani tsaki Hassana taja, ta fice a bangaren.


"Daga ina kk?"


"Daga wajen Yah Khaleefa nake,"


"Kk ce masa me? Ya aure ki? Kar yabi umarnin manyan shi? Tinda ke kin zama baki jin magana, na yi qoqari na hakurtar dake akan son da kk ma Khaleefa ba mai yuwa bane, khaleefa ba cikakkiyar lafiya ne da shi ba da dikkan alamu, ko kin aure shi wahala zaki sha, namiji mai cikar halitta haka ace mace bata gaban shi? Me kk tinani?"




"Ummee, na maki alqawari sai Yah Khaleefa ya aureni, ko zan rasa raina wajen neman soyayyar shi ba zai auri waccan banzar ba, this s my promise, ki rubuta ki aje......."






*Hummmmm,,, kuna ta abun ku ita wadda kukeyi ma domin ta bata san anayi ba baiwar Allah*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ






*BY HAERMEEBRAERH*







Page 4:






Da qarfi Ummen su Sabeer ta fizgo ta, ta fada jikin ta, tare da bige qafar ta ta dama a jikin daya daga kujerun da suke a zagaye a parlourn,



"Idan na sake jin irin wannan kalaman abakin ki, zaki ga yanda zan saba maki,namiji har ya isa ya shga tsakanin ki da 'yar uwar ki, qanwar bayan ki ma kamar Aeeshaa? Kina nan kina haukan ki yarinyar nan ko sanin me ake ciki batayi ba, na tabbata bata son Khaleefa,in ba ke ba ban ga me son shi da aure ba, muma dan yana a matsayin dan mune muke son shi, ina kk hangowa kan ki rayuwa mai dadi da wannan miskilin yaron da ko dariya ban taba ganin yayi ba da girman shi dai, kalaman ki sun tsoratar da zuciya ta,me kk shirin aikatawa? Tarbiyyar da muka baki kenan kina cin alwashi? Kin san ma'anar cin alwashi kuwa? Ki gaggauta cirs shi a ran ki ki nemo wani ki aura, wannan shine magana ta ta qarshe da ke, kin fi kowa sanin halina"



Kuka ta saki mai ban tausayi, wannan wane irin so take ma Khaleefa,bata san tana masa irin wannan son ba sai da hakan ta faru, cike da tausayawa Ummeen su ta rungume ta tana lallashin ta, tare da fada mata kalamai ma kwantar da hankali da nutsuwa.


(Lallai kunyi dacen uwa, tabbb da wata uwar ce, ba zata yarda diyar ta ta zauna ranta na quna ba akan saurayi, sai sun shiga boka sun shiga malam sun janyo hankalin shi, wanda daga qarshe abun kansu zai juye, tinda the moment da zai gano asiri aka masa kashin su ya bushe, dan tsanar da zai ma mace sai tafi ta da, ga shirka an aikata, zunubi kan zunubi, kuma a qarshe an rasa son da aka nema, ko shekara nawa zakuyi da namiji, ko kantin kwari kk haifa masa saboda yara, da asiri ya karye zai ta mamakin yaushe ya aure ki? Nan zaki fara fuskantar walaqanci kala2, mu kiyeye,, asiri da tirsasa so ga namiji baida kyau, akwai wanda suke ganin ya halatta ka ma miji a siri dan ya so ka, sai suke juya abun da neman taimako, kinemi taimako wajen Allah mana, nasara na wajen Allah, shima bokan ko malam din Allah ne ya bashi iko, yake abinda ya ga dama, dan Allah ya kama shi a lahira, dan haka in kinga zaki bi boka ko malam ku dunguma zuwa wuta bismillah, in kuma zaki tashi ki motsa jikin ki ki rage kitse ki sallah, kuma ki samu lada, dannan Allah ya biya maki buqata, marhabun dake)



Umma ce ta leqa bangaren su Khaleefa domin kiran su Ameena su wuce gida, da sallama ta shiga, da gudu Ameena ta fada jikin ta,bayan ta zauna Maman Khaleefa ta koma ta zauna itama, shir sukai, yanzu sun zama surukai, cann Maman Khaleefa ta nisa tace,


"Khadeeja in kina ganin wannan hadin bai maki ba karkiji komai ki sanar dani, zan ma Abban su magana, a yi wa Baba General bayani sai a fasa, dan na kula kamar baki son wannan hadin, kar ki damu ba zan ga laifin ki ba, Khaleefa mutum ne a baibai, ba ka gane gaban shi bare bayan shi, ni kaina hakuri nake da shi,balle qaramar yarinya kamar Aeeshaa."



"Aunty ni ba ni da wata matsala ta bangare na, matsala daya ce dama, naga kamar Hassana ke son shi, kuma an juya an bawa Aeeshaa shi, hakan anya anyi daidai kuwa?"


"Kar ki damu, Baba General na sane da hakan, ya duba yanda Khaleefa bai son Hassana ne kwata2, a haka da halin shin nan na shiru2 ma ya aka qare, balle bai son abu? Amma a qalla sukan gaisa da Aeeshaa, na kula har 'yar tambaya yana mata ya makaranta? Ki fadan a gidannan banda ina kwana ko ina wuni wa Khaleefa ke kulawa? Tin da ya shiga shekarun balaga yaron nan ya sauya halaye, ya tashi daga mai son mutane zuwa wannan mummunan hali, mun kai shi asibiti yafi a qirga dan aga ko akwai abinda ke damun shi, amma inaa,"



"Aunty babu wata matsala,Allah ya shige mana gaba,"


"Ameen"


"Ku shirya mu wuce ku kuma,"


"To Umma, amma ni fa naga Yah Sabeer ya fita kamar yana kuka,har yanzu bai dawo ba, wa zai maida mu gida?"


"Muje na gani, in ya dawo ya maida mu, in bai dawo ba sai mu tafi,"


Sallama sukai, sannan suka shiga bangaren su Sabeer, cikin fara'a Ummeen su ta masu maraba, Hassana ta hade girar sama da ta qasa, dan ummeen su ta mata fada taji ba shi zai sa ta sakar wa da goggon nata fuska ba, har yanzu haushi suke bata.


"Aunty Sabeer fa? Yana ciki ne ya zo mu wuce gida, dare nayi,"



"Sabeer kam ban shigo na isko masa ba, sai dai ki gwada wayar shi,"


"Ok to bari muje waje, na jira magariba ta gabato,"


Keys din su Hassana ta miqa mata ta dauke kai, a ran Umma tana tausaya ma diyar yayan nata, amma ba yanda zatayi, karba tayi, ta kama harda hannun ta, sannan ta daga kan ta, suka fuskanci juna,



"Hassana i knw what is going on between u and ur brother, but i can't do anything about it, i wish i can do something, u ar both my children, and i love u so much, bana son abinda zai bata ran ku, yanzu abinda nake son ki maida hankali akai shine, addu'a, in rabon ki ne Khaleefa Allah za baki shi,koda kuwa ya auri Aeeshaa ne, tinda ba haramun bane, share hawayen ki kinji?"



Kuka Hassana take sosai, sannan haushin Goggon nata ya ragu mata, ta fuskanci itama ba a son ranta akai hadin ba.



Goge hawayen ta tayi, daga nan sukai Sallama suka fita, ta kira wayar Sabeer amma taji ta kashe, tasan za ai haka.

**********************




Azkar take koda suka shiga gidan, direct Ameena ta je wajen ta tana murnar ganin ta, kamar wadda suka shekara basu tare, Abdul dakin shi ya wuce danyin alwala yayi sallah, Umma ce ta zauna a kujera tana nazarin abubuwan da suka faru, tana tinani ta sanar da diyar taga ko ta bari sai ta kammla karatun ta?


"Umma nace sannu da dawowa, ya kuka baro su?"


"Lafiya, debon ruwa kuma mara sanyi, me kk dafa?"



"Tuwon masara nayi da miyar busasshiyar kubewa da busasshen kifi, da ganda,"



"Zubomin, ki ajen a daki, bari naje nai sallah,"



Amsawa tayi sannan ta miqe dan cika umarnin mahaifiyar tata,


Lokacin da ta shiga dakin tana sallah, dan haka ta aje, nan ta ga yanda Umman nata ta wurgar da kayan ta, jaka takalmi a qasa, mayafin data yafa a gado yana reto yana taba qasa, sarqa da dan kunnen data saka a gado ta watsar, dakin da ya sha gyara mai kyau,ga qamshi mai dadi, ta mayar haka daga dawowar ta.


Cikin yar shagwaba bayan Umman ta idar Aeeshaa tace,



"Umma baki ga yanda na gyara maki daki ba ne? Diba yanda kk bata Ummaaa,"



"Na bata din,nace na bata din, dakin ki ko nawa? Gyaran ma d dik qura,"



Saida Aseeshaa tayi dana sanin wannan magana da tai, fada Umma ta fara tayi ta kuma.


Kanta a sunkuye ta fara debe kayayyakin, tana saka komai a muhallin shi, wai ace magana mao dadi ta gagara a tsakanin su, tana kammalawa ta fita, ranta na mata suya.

******************





Cikin dare Sabeer ya dawo ya kwashr kayan su daya bayan daya, ya sa mai gadin gidan ya rufe gate, shi kuma ya wuce, ba zai taba iya ci gaba da zama da Aeeshaa a gida daya ba, bayan sanin wannan mummunan labari.


Yana mota yana tafiya, cike da tinanin rayuwar da kullum yake tsara masu, ya ga motar Khaleefa, baqin glass gare ta ta kowanne gefe da gefe, amma ta gaba haske ne da shi, ta nan ya hango an kwantar da kujerun motar, tsayawa yayi da tashi motar daga neda da su, sai da aka dade, sannan yaga wata yarinya ta dago tana maida rigar ta, Khaleefa ne shima ya taso ya na gyara rigar shi, matsanancin mamaki ne a fuskar Sabeer, m hakan yake nufi? Bai gama tunani ba, yaga Khaleefa ya fito, yarinyar ta fito itama, kudi Khaleefa ya bata, ta tsaya tana kadasu, tare da yi masu kiss, tana wani karairaya a gaban shi, shi kuma ya rungume hannayen shi, daga masa hannu tayi zata tafi, ya daki ***** ta baya, ta sake kada masa su, sannan tai gaba.



Sabeer sumane kawai bai yi ba dan tsoro da mamaki tare da tashin hankali, yaushe Khaleefa ya ke harka da mata? A kusa da unguwar su, dama haka halin shi yake ko kuma dai yau ya fara saboda damuwar dayake ciki? Dan ya kula bai son hadin shima sam, anya yau ya fara, kuma khaleefa ne harda wani dariya da wani yi mata wasa, kaiii mafarki yake.



Yana nan yana tunani bai san khaleefa

Please Login or Register in order to submit comment