Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ra'ayina ba sai yanzu da lokaci ya qure,"


"Bamu kira ka dan ka mana rashin kunya ba tijararre, tinda kai ba a fara abin arziqi da kai bai koma na tsiya ba, da kai da Aeeshaa dika mallakin mune, zamu iya zaba maku wanda muka so, ko sisin ka bamu buqata, zamu aura maka ita, za kuma akai ma ka ita gidan baban ka na kabuga, in kaga dama in an kaita kar kaje gidan, kace ba ka auren, tashi ka bar mana nan dan iskan yaro kawai,"


Hajja ke shafa hannun General a hankali, saboda yanda ta kula ranshi ya baci matuqa, cikin rashin kunya ya miqe zai fice, Aeeshaa da taji dik abinda ke faruwa ce ta shigo, idon ta na tsiyayar da hawaye, ta durqusa a gaban General da ke cikin matsanancin fushi.



"Baba General ka taimaka min kar ku auramin wannan fasiqin, kar ku hada aurena da shi yafi qarfina ba zan iya auren shi ba, dan Allah kar ku jefa rayuwata cikin halaka, na sani tin tasowa ta ba wanda ya damu dani, ba wanda yake jin me nake so, ko meye vana so, dik abinda aka so yankewa ake akaina, na tabbata in mahaifina na nan zai tsaya min, dan.....



Wani gigitaccen mari taji ya sauka a kuncin ta, tana juyawa ta ga Umman ta tsaye,


"Lallai wuyan ki yayi kaurin da har zaki sa iyayena a gaba kina aibata jikan su a gaban idon su, wato tarbiyyar da na maki kk son nuna masu ko? Sai ki bi mahaifin naki shi da ya fimu son ki ya tafi ya barki bai tafi da ke ba,mara mutunci, durqusa ki basu hakuri,har Khaleefa din,"


Khaleefa na jin haka ya sa kai ya fice, dan shi wannan drama ba da shi ba, sun dade basu aura masa itan ba, ko kuma sun dade ba su fasa bashi ita ba, dik dayane a wajen shi, bakin ta na rawa ta fara bawa kakannin nata hakurin abinda ta aikata, zuciyar ta kamar ta fito waje, ji take da ta san Yayan mahaifin ta a Katsin ina yake can zata gudu.


"Khadeeja bai kamata ki saurin dukan ta ba, ra'ayin ta take fada, amma Aeeshaa ina son ki gane, ita mace budurwa iyayen ta ke zaba mata mijin aure, bazawara ita ke da 'yancin zabar miji, dan haka ki hakuri da zabin General, inshaa Allahu ba za ki dana sani ba, maza jeki, ki yi alwala magrib tayi, Allah ya sanya maku albarka,ya kare dikkan abin qi,"


Cikin rangaji irin na mayen damuwa take takawa, zuwa dakin, Umman ta ta bita da kallon tausayawa a cikin zuciyar ta, ta sani bata kyauta ba,amma ba zata iya jayayya da mahaifan ta ba,ba su mata wannan tarbiyyar ba,dole ne diyar ta itama ta zama mai biyayya.



General ne ya tashi dan zuwa masjid, yau Khaleefa bai je ba, Sabeer kawai ya gani, ya kada kai, wato dan an masa fada shi yasa yayi fushi har da sallar ma,Allah ya shirya.



Har Umma ta tafi bata nemi ganin Aeeshaa ba, dama Aeeshan ta san za ai hakan, bata sa a ka ba, dan haka tana idar da sallah ta haye gado ta nade cikin bargo, saboda ciwon kan dake damun ta, Hajja ce ta shigo dauke da mug, ta hada mata shayi mai kauri, da kuma plate dauke da faten dankalin turawa, wanda ya sha kayan lambu, da kayan ciki.


"Tashi kici wannan ki sha magani sai ki kwanta, kin yi sallar isha'i ko?"


Daga kai tayi,sannan ta fara sauka,ta daukar wa kan ta alqawari bazata sake ma kowa musu ba har qarshen rayuwar ta,sai dai in abin da ya sabawa Allah ne, shi kadai ne ba zatai ba, ta kula rayuwar ta bata da amfani a cikin iyalin ta,abinda suke so shi suke mata, koda kuwa shine abu na qarshe da ta tsana a rayuwar ta, ba ruwan su.


Abinci ta fara ci, Hajja na kallon ta da tausayawa, bayan ta gama ta sha maganin ta koma zata kwanta, Hajja ta riqo ta, ta jingina ta da jikin ta.


"My dear, ki sanar dani me ke ranki game da Yayan ki, in baki son shi ko kina da dalilin da yasa kk kira shi fasiqi ki sanar dani, ni na fara sha'awar hada ku, saboda ke ta gari ce, shi kuma halin shi bamu da tabbas akan shi, muna saka ran, ko me yake aikatawa mara kyau, zaki zama sanadin shiryuwar shi, wannan dalilin yasa na sanar da General ra'ayina da tinani na, amma a yau in kk ce baki so,ga dalili kwakkwara, xan warware maganar nan, kin dai fi kowa sanin dik abinda nake so, shi General ke so,so tell me, i am here for u my dear,"


Hajja na magana tana tinani, tabbas tinda suka ce suna saka ran ta sauya shi, is either suna da masaniyar mugayen halayen shi,ko kuma suna zargin yana da mugayen halayen ne, dan haka is of no use ta tsaya masu bayani, dan haka kawai ta amince, Allah ya bata ikon zama da shi da amana, kar ta cutar da shi, kar ya cutar da ita, kuma zata miqawa Allah zabin rayuwar ta, dik abinda yake alkhairi Allah ya mata, ya kare ta daga sharri.



"Kinyi shiru baki ce kmai ba,"



"Na amince da zabin ku, Allah ya shige maba gaba,"

Rungume ta Hajja tayi sannan ta mata kiss a goshi,


"Allah ya miki albarka,"


Nan ta dinga vata labarin zuwan su England, da su America, da sauran qasashen waje, da irin qauyancin da tai kan ta waye, ta saba,just to cheer her up, tin Aeeshaa bata dariya har ta fara, sai da ta kula tana jin bacci ta miqe tace ta gudu wajen dan tsohon mijin ta.



Tana fita,Aeeshaa ta shiga sabon shafin tinanin yanda rayuwar aure zata kasance mata da Yah khaleefa.



*********************






Da safe Sabeer yaji labarin amincewar Aeeshaa, hankalin shi ya qara tashi, lallai yana son maso wani, tinda ta amince shi me ya rage masa ya zauna anan, da hanzari ya wuce office, yana neman transfer ko kudu ne a hankada shi, inda ba zai sake ganin ta ba sai ya so.


Aeeshaa ta so su hadu da shi, dan ta koka masa dik abinda ke zuciyar ta, ko hakuri ya bata ai ta samu sauqi, he is no were to be found.



*******************



Hajja da kan ta take saka driver ya kai su gwammaja, shagon DUBAI, inda suke saida kayan da ke maida tsohuwa yarinya, islamic chemist ne, suna saida kayayyaki na gyaran jiki,sabulai kala2, na slimming, mai na slimming, na stretch mark, kayan mata masu kyau da inganci, zuma mai kyau, turarukan wuta,hummm abun sai wanda yaje shagon kawai, ga sauqin kudi, dan suna saida kaya ne akan farashin sari.



Aeeshaa kunya ta dinga ji, amma Hajja ko a jikin ta, haka ta dinga yi ma Ibraheem da Haruna bayanin aurar da jikar ta zatai, tana son a hada mata kayan mata masu kyau, da zasu gyara ta, nan kuwa suka dinga hada mata, sai da suka tabbatar sun saka komai, suka buga lissafi, suka basu kaya suka tafi.



A zaton Aeeshaa kayan nan da ta gani za ai ta dirka mata tasha, sai taga Hajja ta adana su,ta boye.


"Kk zaro ido kamar an wurga mage sama, ba wai baki zan yanzu ba, sai an kai ki naga kamun ludayin mijin naki zan fara baki su, yanzu gyara zamu fara namu na gargajiya, natural gyara wanda ba zai lalata maki budurci ba,sai dai ya qara inganta shi, dan ba komai ake yi wa budurwa ba da sunan gyara.


Kan Aeeshaa na qasa dan kunya, ga ajiyar zuciyar kwanciyar hankalin da ya shige ta, data ji ba ita za a dirkawa wannan kayayyakin ba yanzu.



Aikin girki suka fara, hajja na son ta sake koyar da ita abincin gargajiya masu gina jiki, tinda ba laifi ta iya na zamani sosai, dan wasu ma Hajja agunta take gani.


Daga girki kuma sai Hajja ta daina barin ta cin kowanne abinci, sai mai gina jiki, da zai qara mata ni'ima,kamar ganyayyaki. Farfesun da yaji kayan qamshi,shayin da yasha kayan qamshi da minannas kadan, sannan tana mata kwadon zogale, da alayyahu, tare da tumatur mai yawa, da albasa.

Gashi kusan koda yaushe tana markade mata cucumber da carrot, tana hadawa da sugar, zuma da dan gishiri kadan ta sa ta shafe mata jikin ta da shi, bayan ta gama ta jiqa lalle ta tace ruwan ta sa ta wanke jikin ta da ruwan, tin Aeeshaa bata so, ita kan ta sai taji tana so, fatar ta ta sauya, kyaun da tai ko ba kwalliya in ka kalle ta sai ka qara.



Cikin wata daya, Aeesha ta sauya, harda girma sai da ta qara,ga shi ta cika sosai hips da da dik inda ya kamata ajikin ta sai da dik su ka ciko, saboda hadin ganyayyakin da ake bata, kunya take ji ta zauna ba Hijab, dan haka kullum cikin doguwar riga da Hijab take.


Sabeer dai har yanzu basu hadu da Aeeshaa ba, ta hango shi yana fita da mota daga gidan, ya koma aiki can Ibadan, yayi kyau, yayi qiba, ya aje saje, sai daga masa hannu take, amma bai tsaya ba, ya ganta ko bai gan ta ba, daga shi sai Allah suka san hakan.



Cikin bacin rai, da rashin jin dadi ta juya zata koma ciki, aikuwa sai a kan qafar shi, da guiwar hannun ta ta naushe shi a ciki, bata ko sani ba, 'yar qara ya saki, ya dafe wajen,da sauri ta kai hannun ta kan nashi, tana taba cikin tare da furta,


"Wayyoo Allah na, dan Allah kayi hakuri, Yah khaleefa ban sani bane, dan Allah kar ka dake ni, na tuba, ba zan sake tafiya ina waige ba,"


Sake baki yayi yana kallon cikin idon ta, wanda ya ciko da hawaye,yayi wani irin kyau, ga hannun ta mai laushi data dora akan nashi, (ba dole hannu yayi laushi ba tana shafa man kwakwa, da alayyadi, tare da man ridi, wanda hajja ta zubawa madarar turare mai dadin qamshi)


Labbam ta yabi da kallo, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tai sauri janyewa, ta dirirce, bai da niyyar motsawa ko bata amsa, da gudu ta nufi cikin gida, Hassana da komai ya faru akan idon ta kasancewar tana qasan bishiyar mangwaro dake gidan ce ta saki tsaki, ta juyar da kan ta ta sake qanqame wayar ta, a ganin ta da gayya ma sukai hakan dan ranta ya baci, Khaleefa ji yayi kamar an zare masa laka.



"Allah ka gaggauto da ranar bikin nan kusa".............




*Kuna cikin 'Yan Ameen ko kuwa? Nidai nace.........πŸ™ŠπŸ˜†*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*







Page 9:








Qarfe tara da wasu mintuna Hamdiyya ta zo da mijin ta, wanda a ranar yake son su koma, cike da murna da farin ciki suke ta gudanar d harkokin bikin, wanda su kadai suke farin cikin su, amarya da ango zuqatan su kamar ana dana masu wuta suke ji.



Can gidan Umman Aeeshaa ita da qawayen ta suna na su bikin,amma nunawa take ita kam ba wani hidimar biki da zatai, Hajja kuwa na riqe da jin takaicin ta ,ta dau alwashin itama sai ta dandana mata taji yanda Aeeshaa ke ji, Allah ya kaimu a gama bikin lfy, ai in fillanci take ji ta fita zama bafulatana tinda ita ta haife ta.


Qarfe 11 daidai aka daura auren Khaleefa da Aeeshaa akan sadaki dubu hamsin, aure ne daya halarci manyan masu hannu d shuni daga kan manyan 'yan siyasa zuwa 'yan kasuwa.


Kowa ka gani cikin farin ciki yake amm bnda Ango,shi ko dan yaqen nan ma yaqi yi,Sabeer ke ta gaisawa da mutane sai ka rantse shine angon ma, amma cikin zuciyar shi shi kadai yasan me yake ji, ba bu wanda ya kula ya zame ya bar wajen, mota ya fada ya kife kan shi ya na sauke numfashi mai nauyi da zafi, shikenan, shikenan Khaleefa ke da sa'a ba shi ba, Khaleefa ya fishi sa'a a rayuwa, ina xai saka kan shi yau, Aeeshaa ta zama mallakin wani, numfashin shi ne ya fara barazanar dauke masa, da sauri ya kunna motar ya bude window ya tada ta a guje, ya bar wajen, iska na ratsa shi amma ji yake kamar a cikin rana yake.



Bai tsaya a ko ina ba sai gidan Umma, yana zuwa ya shige dakin shi, ya kulle,kuka mai sauti ya sake, bai damu ba kowa ye xai ji shi ba zai iya riqe wannan baqin cikin ba, kuka yake kamar wani qaramin yaro yana birgima a gadon shi, hannun shi riqe da saitin zuciyar shi, ji yake kamar zata fashe dan kumburin da yaji qirjin shi ya yi, ga wani maqaqin dauri a wuyan shi ya qi shigewa yaqi ficewa.


Kwankwasa qofar akai, hakan bai sa ya daina kukan ba, da qarfi take kwankwasawa, dan taga wucewar shi, cikin kukan da yake son ya danne ya miqe yana layi ya bude qofar, juya baya yayi, xai koma, ta dora hannun ta akan kafadar shi


"Haba yaron Umma? Komai yayi zafi maganin shi addu'a ga Allah ya yaye ma bawa, ina hankalin ka ya tafi zaka manta da Allah a wannan yanayin da kk ciki, ba yanda zanyi ne da ban bari an yi wannan auren ba,"

Da sauri ya katse ta, cikin daga mata hannu, idon shi sun yi jawur saboda kuka.


"Umma baki taba min laifi ba a duniya domin ke uwata ce, amma a wannan karon bana ganin laifin kowa sai naki, ke ce silar yi ma Aeeshaa auren dole, da kin ja ta a jiki ba ki nuna mata tsana da wai itan 'yar fari bace da ta zayyana maki me take so, meye bata so, sannan da kin cire kunya sanda akai hadin nan,d kin tsaya mata kin ce bai maki ba, da kin kwatar ma diyar ki 'yancin ta da aka danne mata.....




Da qarfi ya tafi zai fadi sakamakon marin daya ziyarci fuskar shi ba tare da zato ko tsammani ba.


Cikin kokawa Umma ke magana.


"Kana da hankali kuwa? Baba General ya yanke hukunci nace baimin ba? Yau ko ni na kawo rashin kunya a duniya Ubana yayi wa diyata miji da babban jikan shi ai baxan musa ba, kenan kana nufin na yi ma mahaifana tashin kunya akan abinda suke da iko akai, dani d ita dik mallakin su ne, ba zan taba musanta masu ba, .....my boy, ka kwantar d hankalin ka, kayi hakuri, ka nemi wata, Allah ya baka wadda ta fi ta, na san kana son ta, kana qaunar ta, amma ya zama dole ka yi hakuri da son ta, ka yafeni akan abinda na aikata wanda bai maka daidai ba,"


Juyawa tai zata fita, dan zuciyar ta ta mata nauyi, bata taba zaton tana son Aeeshaa irin haka ba, ashe dik abinda take mata aikin banxa ne,son nan da take qin nuna mata yana nan danqare a ran ta,kuka take buqatar yi itama,dan sai yanzu ta ke hangowa diyar ta ta xaman quncin da zatai da Khaleefa, a halin shi d suka sani shi din ba wanda zai yi laushi bane ba tare da an ci baqar kwakwa ba.


Kamo hannun ta Sabeer yayi yana kuka, ya durqusa.


"Umma ki yafemin ba zan sake abinda na aikata maki ba yanzu, amma ina neman izini zan koma bakin aikina a yau, ba zan iya ci gaba da zama ba, zuciyata kamar zata fashe haka nake ji,"



Cikin tsananin tausayin shi ta ke shafa kan shi, tana hawaye,


"Na amince maka ka koma bakin aikin ka dana, amma ka bari sai gobe, yanxu zakai dare, Allah ya maka albarka, ya sauqaqa maka abinda ke damun ka a zuciyar ka, Allah ya sanya ka a cikin bayin shi masu hakuri,"


"Ameen Ummana,"


"Xauna na kawo maka abinci kaci,"


"Umma bana son cin komai, ki dai hadan tea ya isheni, shima magani nake son nasha ko na rage jin zogin da kaina yake min,"



Bata musanta masa ba ta fice tana gyara fuskar ta, amma qawayen ta sai da suka gane tayi kuka, nan suka hau tambayar ta me ya same shi ya shige kamar wanda aka koro? Murmushi kawai tayi tace bashi d lafiya ne, nan suka jinjina shaquwar dake tsakanin su, dan baida lfy take kuka itama.




Sai d ta dafa masa ruwan tea din da kayan qamshi ta hada masa mai kauri da maganin ciwon kai ta dora a tray, inda kayan gara yake ta nufa da plate, ta zuba masa dibilan da cincin da dai sauran abin bikin a plate ta nufi dakin nashi, shiru taji dakin gashi bata ga alamar kayan Sabeer ba, ajewa tayi ta hau duba dakin, tsaf har toilete ta duba baya nan, zama tai a bakin gadon zuciyar ta cike da baqin cikin abinda Sabeer yayi, ashe ba zai ji maganar ta ba yanzu, ya hakura zuwa gobe.


"Allah ya kiyaye hanya,Allah ya kare min yarona dik inda yake, ya Allah ka sauqaqa masa wannan qunci dayake ciki"



Dauke kayan tayi ta fita da su, haka sika yi wunin bikin da qawayen ta ba wani kwari a jikin ta, tausayin Aeeshaa da Sabeer ke dawainiya da ita, gashi ko a qawayen ta ba wadda ta sakewa sike dan maganar Aeeshaa da ita balle ta yi masu maganar ko zataji dan sanyi a ran ta (sai ko maganar ta cinye ki tinda ke kk jawo, kunya kamar a rugga)



***********************



"Dan Allah General a kai yarinya dakin mijin ya ba sai an yi wani yawace2 ba,ina ce nan yarinyar nan ta zo a yi biki gaba daya anan qi tai, abu tuwona mai na, sannan naga ba wai ta damu da yarinyar nan bane, da za a b tawa da kai ta kawai akai"


"Hajja tawa kenan, ke in banda abinki ya za a kai yarinya dakin miji ba tare da mahaifiya ta sa mata albarka ba? Tana raye ba a mace ba? Habaaa kar ki sa wannan a ranki, whatever it is mahaifiyar ta ce, and in banda abinki ai can ma mutane zasu je,ina ga shine dalilin ta na qin zuwa, ai tana da qawaye, kuma ga wasu daga 'yan uwa ma musamman dangin mahaifin yarinyar ai sun je can bayan an gama anan, dik dai ba sauqin mu bane da kuma samun wajen kwana, canfa shine asalin yarinya nan ne gidan iyayen ta, nan gidan kakannin ta ne, so ki cire komai a ran ki ku kai ta can, daga nan sai a wuce da ita gidan mijin ta, Allah ya muku albarka ya baku zaman lfy, Allah ya kare ku daga dikkan sharrin mutum da aljan,"


Aeeshaa da take riqe jikin Hamdiyya da Sai kuka take, kewar mahaifin ta ya dame ta, ga uwa tana da ita amma kamar bata da ita,jin ta take kamar marainiya, ga miji mara halin kirki, amma ba wanda ya bincika ganin shi din na gida ne, da mahaifin ta na nan ai da shi ya bincika kuma zai tsaya mata akan wannan lamarin da kowa ya rufe ido akai.


Sai lallashin ta suke, Balqis sarkin kuka da tausayi ganin kukan Aeeshaa kawai na kuka ya sa ta kuka itama.


Haka akai ta shiga motoci abokan aikin Khaleefa na tuqawa suna wucewa da wasu gidan Amaryar wasu gidan Umma, Khaleefa na tsaye jikin motar shi data sha wanki, dan ya sha alwashin ba mai daukar masa mota da sunan wani kai amare, ai akwai motoci a gidan ayi amfani fa su, yaga me daukar tashi.


Niko nace rabon ka dauka da kan ka ne,tinda in baka bada key ba wa zai ja motarπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚




"Dannema mai qaton kai, kai kullum a aske kamar bayahude, zo nan ka kaimu gidan Khadeeja, daga nan mu wuce gidan naku, tinda gaka tsaye,"


Juyawa yayi yana waige2 kamar ba da shi ake ba.


"Khaleefa ka kiyayeni, da ubanwa nake da in ba kai ba,dare nayi kowa ya wuce kazo ka kaimu kana tsaye uban wa zai kaimu in ba kai ba?"


Cike da rashin kunya da qunquni yake takawa zuwa gefen driver, da qarfi ya zauna yana masifa, ko kula shi Hajja batai ba suka shiga suka sauna su Uku, Hamdiyya da ita Hajjan sai Aeeshaa, daga can Hamdiyya zata tsaya mijin ta sai dauke ta, su kwana gidan iyayen shi washegari su wuce garin su,anan zasu dauki matar Uncle din Aeeshaan su kaita gidan ta.




Har suka isa ba mai cewa komai,sai da suka fita zasu tafi Hajja ta dawo baya,



"In ka cika kai dan iska ne ka tafi naka waje baka kai amarya va, zaka ga tijara, zan nuna maka ni kakar ka ce ni na haifi uban ka"


Banza yayi d ita, ya bude motar ya zira qafar shi ta waje, kallon bayan su yayi lokacin da zasu shiga gidan, wowww Aeeshaa ta yi kyau ba kadan ba.


Doguwar riga ce scarlet red,da wasu stones masu kyalli, ta baya tayi tsaho, ta gaba an barta daidai qafar ta, ta gaban rigar ya dago mata albarkatun qirjin ta masha'Allah, ba a cika mata fuska da kwalliya ba, an mata mai sauqi mai kyau, ga kuma wani dauri da ta sha na zamani, mayafin shara2, hips dn ta abin kallo ne, tana matuqar jin kunya, amma a dole haka a ka sa ta sanya wannan rigar.



Kauda kai yayi, ya zaro wayar shi, ya hau chatting d Rebbeca, hira kawai suke zubawa ta batsa kamar suna ganin juna ko suna taba juna haka suke jin su.


(Jarababbe kawai)



A zaune Umma take qawayen ta dik sun tafi sauran dangin mahaifin Aeeshaa, suna shiga gidan wata kwalla ta taru a idon umma, Aeeshaa da gudu ta fada jikin ta ta saki wani marayan kuka, qanqame ta tayi kamar ba zata sake ganin ta ba.



Umma shiru tayi tana jin wani qaunar diyar ta na ratsa ta, hawaye sai zuba yake ta kasa tsaida shi, a hankali ta janye jikin ta tana fada,



"Meye haka zaki wani zo ki riqe ni, sai kace wadda za a kai ma dodo ita, dan uwan ki ne ba wani bare ba, dole ki masa biyayya, Allah ya baku zaman lfy ya sanya albarka, ta shi ki daga ni ni,"


"Ai shi mai hali in bai halin shi ba sai kowa ya zaci ba shi din bane, da an bi ta tawa ko ganin ta zaki yi ma?"


"Hajja dan Allah ku bar wannan maganar, muje kunsan halin Yah Khaleefa, yanzu na san yana can ya qagu mu kai masa amaryar shi, aunties ku tashi muje, dare nayi"



Da sauri Umma ta nufi dakin ta, kuka sosai take ji, tabbas yau tasan ba zata taba iya bacci ba.



Aeeshaa bin qofar tayi da kallo tana tsananta kukan ta, dik fuskar ta tayi jawur, ka wani matsanancin ciwon kai da ke damun ta, a hankali ta miqe kamar ba zata iya tashin bama, ta fara takawa zuwa waje.

Da gudu Ameena ta fito tana kuka ta qanqame Aeeshaa, ta kasa magana sai kuka take,Abdul na tsaye yana kallon su,dik rashin kunyar shi yau sai yaji baya son Aeeshaa ta bar su, amma a fuskar shi sam ba wani emotion.



Da kyar aka raba su, Aeeshaa ta kasa cewa komai itama, sai shessheqar kuka.


Yana ganin su ya yi saurin shigewa motar dan ba zai so su ga yanayin dayake ciki ba, kashe data yayi ya zauna kamar su yake jira, ya bata rai.


Da gudu yake tafiya sakamakon titin da ya zama ba motoci sosai



"Dan uban ka ka tafi damu a hankali, kar ka je ka kashe mu, mara mutunci, ni ban san haka kk ba, ko dan da ba na shiga harkar ka ne, oho, amma iskancin ka Khaleefa yawa ne da shi"



Auntyn Aeeshaa ce tace



"Hajja kiyi hakuri, kar ki mai fada gaban amaryar shi, Allah ya kaimu lfy,"




Hajja dai bata samu tai shiru ba har suka isa zagin Khaleefa take tn kumawa, sai masifa take masa, har suka isa.



Bayan sun aje amarya suka hau masu nasiha gabaki dayan su, Hajja harda shafa kan Khaleefa ana masa nasiha cikin lallashi, da kuma dan kokawa, ita a dole ya rage baqin rai.



Ganin dare na yi ya sa Hajja miqewa, Aeeshaa ji tai kamar ta bita su koma, tsananin tsoron Khaleefa ya hana ta shan iska da kyau.


Drivern gidan Baba General ne zai maida su, dan bai wuce ba yana jiran su zo ya maida su dama.



Gida ya rage daga Khaleefa sai Aeeshaa ko mai gadi babu, saboda sabon gida ne, ba su samu mai gadi ba tukunna.


Sai da ya tabbatar kowa ya

Please Login or Register in order to submit comment