Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi, ba mai dawowa, dan haka ya shiga ya watsa ruwa, ya sauya qananan kaya, ya feshe jikin shi da turarukan shi masu qamshin gaske, ya du key din motr shi ya nufi dakin Aeeshaa.


A zaune take bakin gado, tayi kuka har ta gaji, sai shessheqa take, idon ta na zubo da hawaye, lokaci zuwa lokaci tana sharewa.


Bataji sanda ma ya bude qofar ba, sai jin an jefo mata abu tayi a cinya.

"Tashi muje ki rufe gida, zan fita, in bani kk ji ba kar ki sake ki bude qofa, dan akwai 'yan iskan unguwa masu shiga gidan amare su masu fyade kuma suyi sata,"


Wani irin mugun tsoro ne ya kama ta, da sauri ta miqe tana waro manyan idanun ta waje, shi ko murmushin mugunta ne ya subuce masa,


'Zaki san an maren akan ki, azaba sai kin sha ta har kin gudu da qafafun ki'



Wasu sabbin hawaye ne ya sake balle mata


'Oh Allah in laifi na yi ka yafe ni, ka sassauta ma rayuwata wannan azabobi danake sha'


"Kina ma jin me nake fada kuwa?"


"Immm.....ammmm yi hakuri me kace,"



"Oh bakiji ma me nake fada ba ko? Kiyi bacci na dawo baki buden ba ki gani,"



Ficewar shi yayi, kamar ta bishi ta hana shi barin ta ita daya, a parlour ta zube tana kuka mara sauti, dan muryar ta ta dusashe sosai saboda kuka.



Bai tsaya a ko ina ba sai gidan Rebbeca, ta masa alqawarin kan ta yau, indai ya baro amaryar shi ya je gare ta, amma da alama ba zai samu ba, dan in ban bata ji ba abinda na jiyo a cikin gidannan shi khaleefa ya jiyo😨😨😨😨









*Allah sarki Aeeshaa me kuke gani game da rayuwar ta? Shin mutum mumini dama na shiga wahalar rayuwa haka? Mu tattauna dan samun ilimin junan mu*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼








*BY HAERMEEBRAERH*







Page 10:





D sauri ya kashe motar shi ya qarasa jikin qofar shiga qayataccen parlourn, yana kusantar wajen kidan da dariyar Rebecca na qara shigar masa kunne, murda knob din yayi ya tura kai ciki, mummunan gamo yayi da wani garjejen magidanci, Rebecca na kwance saman cinyar shi tana rawa a jikin shi, yana saka mata kudin qasar amurka a dan kamfan ta, ta juya baya dan haka bata ga shigar shi ba.



"Kai waye kai zaka shigo mana waje haka?"


Banza Khaleefa yayi dashi, daidai lokacin Rebecca ta waiwaya ganin wanda ake wa magana, wani abu ta hadiya sakamakon ganin wani irin kallo da Khaleefa yake mata, bata son ta rada shi, tana matuqar jin dadin shi, in ta rasa shi wadannan Alhazan sai dai suji dadi da ita, bata wani morar su sai kudin su.


"Give me a minute Alhaji na,"

Kissing din shi tayi a lips ya lumshe ido,ya gyara qaton tumbin shi ya kwanta a kujerar yana jiran ta.


Hannun Khaleefa tai niyyar kamawa ya kwace ya dau hanyar fita.

Da gudu ta bishi ta sha gaban shi, direct qasan shi ta kai hannun ta tana juya jikin ta a nashi, kundai san Khaleefa da jaraba, nan da nan ya rikice, ya manna ta da jikin motar shi,


"Me yasa zaki min haka, kin san wannan me kama da aladun zai zo zaki gayyacen?"



"Ka yi hakuri my sugar, ban san zai zo ba, na gama shirya maka kaina kawai yamin waya wai naje na dakko shi, nan zai kwana, in banda jaraba ko gidan shi bai je ba fa, ya sauka anan, daga tafiya suka dawo da His highness amma ya zo min nan, ka san ina samu a wajen shi sosai, shi ya sai min motar danake hawa yanzu, ka min hakuri zuwa jibi ko gata,"


Janye ta Khaleefa yayi dan takaici, har gata? Yaushe zai iya kaiwa gata bai jishi yana service ba, inaaa.


Komai bai ce ba y bude mota ya shige, bin shi tai tana ta kwankwasa glass din ko kula ta bai ba ya fice, yarfe hannu tai ta kama goshin ta, ta san kan ya sakko sai ta dade, damuwar ta har ya je ya kwana da amarya tafita komai ya aje ta a gefe, haske ta yayi da fitilar motar shi sanda zai fita, wani.matsanancin sha'awa ke dawainiya da Khaleefa, musamman da ya ganta daga ita sai bikini.


Da mugun gudu yake komawa gida.



Zaune take tana ta rera karatun qur'ani a hankali, kuma cikin ikon Allah a hankali ciwon kan ke sauka, amma goshin ta na zafi wannan kuma ta san harda bacci.


Horn taji ana dannawa da qarfin tsiya,aiko da gudu ta miqe ta je waje, tana son ta bude bata san waye ba, ko barayin ne suka zo, wani qara cikin ta ya bada, in sune anya zasuna horn haka?


Shahada tai ta bude, koma waye ta san ba mai cutarwa bane tinda har yayi horn.



A guje ya parker motar shi ya fita, ko bi ta kan ta bai ba ya shige,


'Ikon Allah ni zan rufe ma gidan,'


Rifewa tai tayi ayatul kursiyyu ta tofa ta koma ciki, hankalin ta ya kwanta tinda ya dawo lfy xata iya baccin ta yanzu.


Kayan ta ta cire bayan ta shiga bandakin dake dakin ta, wanka ta fara, sannan tayi alwalar bacci,ta fito, duba kayan sawa ta shiga yi, da dikkan alamu, kayan ta anyi mistake an kai mata wani wajen dan nan daga atampopi sai laces da dogayen riguna ta gani.

'Ina to suka saka min qananan kayana da n bacci ni Aeeshaa?'


Dubawa take amma iya abinda take ta karo d su kenan, hijab ta saka babba, ta nufi dayan dakin, dan dubawa ko can aka aje mata.

Daki uku ne a gidan manya, sai parlour biyu babba d qarami, da store sai babban kitchen sannan wajen dinning, gidane wanda kwararren magini ya tsara shi, Hajja da kan ta ta zabi kayayyakin dakin, kai har na kitchen ma, da su Balqis na ganin za a saka kaya marasa kyau tinda Hajja ce zata zaba, a ganin su tsohuwa me ta sani na zamani, Aeeshaa mamakin ganin kyau da tsaruwar wajen take,tama manta me ya fito da ita,ta leqa nan ta leqa can.



Qarar TV taji a daya daga cikin dakunan, gashi irin nishin da taji watannin baya da suka wuce a dakin Khaleefa a gidan su shi take sake jiyo wa, duba lokaci tayi taga qarfe 2:12am, d sauri2 ta qarasa bakin qofar, ta kasa kunnen ta dan ta tabbatar da me take jiyowa.


Khaleefa wanda ya maida hankali wajen sabon Allahn shi d ya saba ne ya ga inuwar mutum a bakin qofar dakin shi, dakatawa yayi, yana kallon wajen, murmushin mugunta yayi daya ga ba a bar wajen ba, ya tabbata ita ce, yau zai maganin ta, ta yi na biyu gobe bazata sake na uku ba.


Sauka yayi a gadon nashi, ya qarasa fidda boxern shi, ya nufi bakin qofar dakin, shiru yayi na wasu daqiqu da basu wuce biyar ba, da qarfi ya bude qofar, aiko da ka ta fada dakin, cike da tsananin tashin hankali da kidima take qoqrin yin magana,amma A ta kasa fita.


Da hanzari ta rufe idon ta, ganin Khaleefa ba komai a jikin shi, tsaya mata yayi qere2 yana kallon yanayin yanda take a tsorace, murmushi yayi sannan ya bata rai

"Ke me kk min a qofar daki? Labe ko?"



"Ahhhh.....ahhhh Yah Khaleefa, naji kamar hayaniya ne shhhhshiii neee na ce barrrii naji, dan Allah ka rufan asiri kayi hakuri ka yafemin ba zan sake ba,wannan alqawarri na dauka har abada ba zan sake zuwa inda kk ba sai ka kirawo ni, tsautsayi ne ya sa na kasa maka kunne,"



Hayaniyar ta na damun shi, cike da tsawa ya dakatar da ita,


"Keep quit stupid! In kk qara cewa tak anan sai na babballaki, ba mai taimakon ki, wuce muje,"



"Ina😨"


"Ciki"


"Ayi me?"


"Irin wancan, kar ki sake magana or else...."



Gum tai da bakin ta tana tsinewa karambanin daya sa ta kasa masa kunne,ba halin ta bane, azal ce ta janyo ta,yau ta shiga uku.



"Bude idon ki da kyau ki kalla, dik abinda kk ga anayi kema shi zaki min,in kuma kk qi, sai jikin ki ya gaya maki yau, ba dai an aura min ke ba? Ai kn talatta a garen, so kar ki damu"




"Dan Allah, dan soyayyar ka da Annabin rahama ka tausayamin, ni ban taba kallon irin wannan sabon Allahn ba, ka tausaya min ka barni na tafi, inshaa Allahu hanyar ma da kabi ba zan sake bi ba, in ba kai ja kirani ba, ka tausayamin bani da lafiya,"



Yanda take maganar ya mugum bawa Khaleefa dariya,dik iskancin shi na shiru2 yau ji yake kamar ya kwanta dan dariya.


Sai da ya yi dariya sosai, ita kuma tana tsugunne tana kuka, sannan ya bata rai, ya nufe ta gadan2, ya cire hijabin ta, mayafin da ta yafa sanda aka kawo ta shi ta daura, ba abinda yake boye a jikin ta, Khaleefa tinda yake kallon fina2n iskancin shi bai taba kallon mai dirarren jiki irin na Aeeshaa ba, wata matsananciyar sha'awar ta ce ta kama shi.



Dambe suka fara, zai cire xanin ita kuma tana qoqarin kwacewa.


Ta san ko a islamiyya an sanar dasu saduwar aure, da yanda miji ke zuwa matar shi a daren farko, bata ga daya daga cikin wannan ba, ko ba komai ba zata so Allah ya azurta su da zuri'a a wannan halin qazantar ba,yana kallon film din batsa sannan ya sadu da ita inaaa, yau sai dai ya mata duka, amma ba zata bar shi ba.


Hannun shi ta kama ta sakar mashi cizo, tin qarfin ta, da sauri ya sake ta, yana yarfe hannu, diba tai a guje zata fita, ya sa qafa ya yarfar d ita a qasa, faduwa tai tare da sake qarar azaba, ta gaji matuqa, qoqin rashi take ya bi ta ya kwanta a jikin ta, shi kan shi ya gaji, bai zaci tana da qarfi haka ba.



Mutsu2 take dan ya daga ta ta gudu, amma da ta san me xai haifar da batai ba, domin dik albarkatun qirjin ta ke taba nashi, nan da nan kuwa jarabar shi ta dawo dabuwa.....



Qarfe 4:01am, Khaleefa ne kwance a gefen Aeeshaa, wadda ajiyar zuciya kawai take,tana tsiyayar d hawaye ta gefen idon ta, sama take kallo, ido bude, bata gane komai a saman, ji take kamar ba a duniyar take ba.


Qasanta kamar an sa abu mai kaifi an yanka haka take ji, ko hannun ta bt iya dagawa,b binda ke mat yawo akai,illa yndaya dinga saduwa d ita kamar ba zai barta d rai ba, ga shi yana yi ya na sauya maimaita film din da yake kallo, ba addu'a, ba komai daya danganci sunnah, sai kace arna.



Kuka mai qarfi ta fashe da shi, mara sauti, saboda muryar ta ma bata fita, ta dade tana kuka, ko motsawa bai ba, dan tini bacci ya share shi


Yunquri ta dinga yi dan tashi amma ta kasa, ko dukan da ya mata ma da ta qi tsayawa ai ya isa sa jikin ta tsami, fuskar ta har kumbura tayi saboda marin data sha, wai ace musulmi ne ke saduwa da mace yana kallon wannan iskancin, remote ta qoqarta ta janyo daga hannun shi, kashe wa tai gaba daya, tare da sakin tsaki,



"Yan iska kawai, Allah sai ya sakamin ba zan taba yafe maku ba dikan ku,"😭😭😭😭


Juyi yayi ya ringumo ta, ya ci gaba da baccin shi, hawayen baqin ciki da tsana mai tsanani ne suke zubar mata a idon ta, ashe Yah Khaleefa tantiri ne haka?


Kiran sallah take taji a kunnen ta, ba halin tashi,har ta gaji d kukan ma, sai sake ajiyar zuciya take.


Tana ji tana gani aka gama sallah ta kasa tashi, daga baya ma bacci ne mai nauyi ya dauke ta, ga gajiyar biki, ga ta Khaleefa.


8:00am ya farka, saboda alarm da ya saka a wayar shi, kullum in 8 tayi sai ya buga saboda koda ya makara ya tada shi, a hanzarce ya tashi yayi wanka, ya shirya, zai fita ya kalle ta, yaji wani irin abu ya tsarga masa a jikin shi, na tsantsar gamsuwa da yayi d ita a daren jiyan, kada kai yayi tare da shafar cinyar ta.



"Zamu je dake, kina da zaqi sosai,"



Farkawa tai, suna ido hudu ta zabura tana kare qirjin ta, ido tsilli2 take kallon shi cike da hawaye, tana kada masa kai.


"Calm down babes, ba yanzu ba, ki jinyata min kan ki, naga waje, sai na dawo,"



Ficewa yayi ba tare dayaji me zata ce ba, kamar mutumin kirki, manyan kaya ya saka, wanda suka karbi cikakken halittar jikin shi mai kyau, ka rantse dan gidan limamin makka ne, a nutse ya durqusa gaban ta, dan bai taba zaton zata zo da sassafen nan ba.



"Hajja ke ce da asussuban nan?"


Baki ta bude daga baya ta wara hannayen ta alamar daquwa.


"Amshi naka, nace amshi naka, maras kunya, yanzu ka duba agogon hannun ka kuwa? Tara na safiya yanzu, ga abinci can na sa an dafo maku, ina Aeeshaan take?"



Cikin alamar wai yaji kunya, ya shafa kan shi, ya nuna mata hanyar dakin, murmushi Hajja tayi, da dikkan alamu, an yi nasarar gamuwa😉, kuma yanda fuskar shi take dauke da annashuwa ya samu abinda ake nema kowacca diya mace ta kai gidan auren ta.


Miqewa tai cikin kuzari irin nata,dan ita sam badan fatar ta data fara nuna alamar ta kwan biyu ba ba zata ce mata tsahuwa ba.


Har ta kusan isa dakin ya yi wani sufa sai gashi a qofar dakin, hannu ya daga mata, ya bude qofar ya shige da gudu ya tattara disc din dake qasan dakin, ya tura qasan gadon, ya daga dik wani abun iskancin shi, sannan ya fice.



Hajja dai qara murmusawa ake, jikar ta ta kai budurci gidan aure lfy, lallai Khadeeja an gaishe ta, ta yi qoqari, dik wani haushin ta da Hajja ke ji sai taji ya kau.



Aeeshaa dai na bakin gado, tana zare ido, kan ta ya daure, meye hakan ke nufi? Ko wani abun ya gani zai gudu ya barta, kuka ta fara, ta ja jiki da kyar xata tashi, da hanzari hajja ta tare ta, tana jera mata sannu.


Zubewa tai a jikin Hajja tana kuka kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, sai kuka take tana gwana numfashi.


Tsam hajja ta rungume ta tana matsar kwalla itama, tare da zagin Khaleefa a ran ta, na rashin tausayin marainiyar Allah da bai ba, da dikkan alama ta mai gardama ya hada mata da duka, bai la'akari da sabuntar ta ba.

"Sannu Aeeshaa, Allah ya shiryi Khaleefa ya yi hankali, shi ko dan lallashin nan babu, ji fuskar ki kamar an gasa biredin saba'in, ta tashi tai luhu2, wannan dan iskan yaron da bai fita ba sai na ci mai uba, Allah ya saka maki, muje na gasa maki jiki, jikina ya bani ba mutunci ne da shi ba sai kin wahala shi yasa na taho d kaina, tinda ba wanda zan aiko, Hussai ta koma ita da Hamdiyya, Balqis ba zata iya ba tayi nauyi, zata zauna har dai ta haihu, muje kar na cika ki da surutu"


"Hahhhaajjjaa kkkooo salllaaahh bann baa faa"


Sai ta fashe da kuka.


"Yi hakuri muje na tayaki ki gyara sai ki wanka kiyi sallar, Allah saka maki mugu azzalimi kawai,"



Ruwan zafi tin tana kuka in ta shiga,har sai da taji kamar kar ta fita ma, wankan tsarki tayi kamar yanda aka koyar d su a islamiyya, sannan ta fito.

(Yana da matuqar mahimmanci malaman manyan aji na islamiyya suna koyar da mata harda mazan ma yanda ake gudanar da rayuwar aure a musulunce, in ma ba a koya masu anan ba yahudawa da nasara zasu koya masu, ta haka ake samun lalatattun yara, kuma namiji dik gurman shi yayi aure bai san farillan daya kamata ya hau kan shi ba balle sunnoni, ayi aure namiji ya hau mace kamar awaki, ba nafila ba addu'a ba komai, saboda islamiyya ba a koya masa ba, iyayen shi ba su koya masa ba, wai ai mace kawai ake koyawa, to wasu matan ma ba a koya masu komai, akwai wanda wallahi iyayen su ne suke koyar da su komai na xaman aure kafin auren, har yanda zasu magana da tafiya gaban matan su, amma wasu wai kunya, gaskiya a daina kunya a inda bai kamata ba)



Kaya ta tarar Hajja ta debo mata marasa nauyi, doguwar riga ce da bra da pant sai dankwalin kayan da hijab.


"Bazan sallah anan ba Hajja muje can,"


Da kyar Hajja ta gane me ta fada, ta yi tsananin tausaya ma Aeeshaa, roqon ta Allah ya sa khaleefa ya dawo; sai ta masa dukan tsiya (kar dai ki ji ma kan ki ciwo yar tsohuwa).




Bayan tayi sallah, ta tsaya yin azkar, tana yi tana kuka, ita nata daren farkon a haka yazo mata, gaba kuma bata san wacce irin rayuwa za tai ba da Khaleefa.


Hajja ce ta leqo tagan ta, zama tayi a bakin gadon, ta yi ta mata nasiha.


"Ba a yi ma miji musu, sai dai in ya umarce ki da aikata sabon Allah, wannan kuwa ko kashe ki za ai kar ki biye masa, amma in ba sabon Allah bane ba a yiwa miji musu, yanzu dibi fuskar ki? Wannan cin zali d mi yayi kama?"



Hajja sai d ta tabbatar Aeeshaa ta ci abinci, ta qoshi, ta yi bacci ta huta sosai, sannan sukai azahar ta wuce gida.



Tana wucewa Aeeshaa taje dakin Khaleefa ta kwashe kayan baccin ta tsaf da komai nata da aka aje mata acan, ko wanne me neman maganan ne a cikin tayun nata ya aje mata kaya a dakin shi oho.


Tinani tayi, ya kamata ta sake dafa masa wani abi tinda akwai kayan abinci, wanda aka kawo ya jima aje, ga shi bata ko san lokacin da zai dawo ba.



'Ohhh ni Aeeshaa nan kuma Allah ya kawo ni, Allah ka dafa min kar ka barni d kaina😢 ba zan iya ba'



Sai fa tayi la'asar ta fara girki mai rai d lafiya ta gama, ta sake qalqale wajen, dan ba wani datti bane akwai, tana zaune taji ana buga gidan, hijab din ta babba ta zuba taje ta bude.



Wani dattijo ta gani, yaja ganin ta ya durqusa a qasa, yana kwasar gaisuwa, ai d sauri itama ta duqa, bata san ko wane ba, ba a mata tarbiyyar babba ya gaida ta ba har da durquso.


"Baba ban san kai wane ba, amma koma waye kai dan Allah ka tashi, ka daina duqa min"



Dan miqewa yayi kadan, ya tsaya a gefe, kamar akwai wanda yake jira.


Drivern gidan Hajja ne ya leqo suka gaisa da Aeeshaa sannan ya mata bayanin mai gadin su kenan,


"Ok Allah sarki, dazu munyi maganar kuwa, bismillah baba muje daga ciki, sai dai mai gidan baya nan, ka shiga ka zauna ka huta zan kawo maka abinci, kafin ya dawo, sai ku yi magana,"



"Allah ya miki albarka hajiya na gode, suna na Adamu, Allah ya bani ikon yin abinda ya kawo ni,"


"Ameen Baba dan Allah kar kana kirana hajiya, Aeeshaa sunana,"


Driver sallama ya musu, a kullum shi dai yana yaba tarbiyya irin ta Aeeshaa.



Baba Adamu dakin data nuna masa ya shige ya aje yar ledar kayan shi, yana ta kallon wajen, yana godewa Allah, an sha gwagwarmayar rayuwa, yanzu ga gida harda katifa makekiya, ga wata kujera da ledar daki, ga bandaki ai shi kam sai godiya.


Abinci ta kawo masa da ruwa, ya ci ya kwanta baccin gajiya.



Daf d magrib Khaleefa ya dawo, ya maka horn kamar shi kadai ne mai mota a unguwar.

Baba adamu ne ya fita d sauri, dan budewa, Aeeshaa kuwa hantar cikin ta ce ta kada, da sauri ta dora qaton hijabin ta akan dinkin atampar data saka, tana zaune tana zare ido tare da cin frtan hannun ta, ko dame zai dawo? Sai Allah.


"Waye kai?


"Ranka shi dade nine sabon mai gadi da Hajja Aeeshaa ta aiko na zauna anan, dan kula da gidan,"


"Dan sa ido dai, ba gadi ba, zo nan,"


Matsawa yayi da mamaki a fuskar shi, kudi Khaleefa ya zaro masu yawa, ya miqa ma Baba Adamu, ya ce yaje ya sallame shi, kar kuma ya koma gidan Hajja ya ja masa surutu, dan ko an dawo da shi ba zai zauna ba, bai son sa ido.


Cike da mamaki da jin takaici yaje ya dau kayan shi ya bar gidan.


Bude qofa yayi, ya fice yana ta tsaki, ya kwashe kayan shi ya shige ciki.

Lokacin ta tada sallah a daki, sai kwala mata kira yake, kamar a wata unguwar take ba a gidan ba.


Daidai ta yi sallama tana qoqarin fita suka hadu, ranshi bace ya ke mata wani irin mugun kallon..............
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼






*BY HAERMEEBRAERH*




*SAMEERA, Bilkisu mai gado, Ameena,Mero Tsokana😝, Muheebbah,......da dikkan masu comment akan wannan novel thank u, comments din ku na shiga ta da kyau2, yana sa ni jin baku novel din gaba daya😘 One love from Haermeen Haermmaerh❤*






Page 11:






"Me kk yi ina ta kiran ki ba zaki zo ba, ba za kima amsa ba na san kinji ni, raini ne ya shiga tsakanin mu?"




"Yah Khaleefa Allah kar ya nuna min ranar da zan raina ka, sallah nake ban ji ba, kayi hakuri,"


Tsaki ya ja sannan ya qarewa dakin nata kallo, lallai da gaske wadannan tsoffin ke son suyi zaman aure, meye babu a dakin nan? Ga wani qamshi dake tashi na musamman, kallon ta yayi yaga yanda take saka hannu a hijab tana kare qirjin ta kar su dga ya gani, cikin daure fuska ya ce,


"Meye hakan? Meye amfanin rufe qirjin ki d hannu bayan kin dora hijab? To bari kiji, daga yau sai yau, kar na sake ko da wasa na gan ki tare da hijab, in ba fita zaki ba ko sallah kk, kina jina ko,"



Tabbas ya shirya cin zalin ta ne wannan, cikin matse kwallar data taru mata ta daga masa kai alamar taji,


"Baki d baki ko?"


"Ina da shi, naji, inshaa Allahu zan kiyaye.....ga abincin ka can na a shirya maka,"



Banza yayi da ita yana kallon ta yana jiran ta fara bin umarnin shi tin yanzu, gane hakan ne yasa ta sauri cirs hijab din, tana kame2n me zatayi next dan ta bar gaban shi.



Da sauri ta sakada ta gefen shi, tayi hanyar dinning, abincin ta bude ta fara zuba masa, dambun cuscus ne data dafa fari amma ta saka masa kayan lambu da albasa mai yawa, sai tayi miyar dankalin turawa da kayan ciki, sannan ta hada masa fruit salad mai mugun dadi, yaji ayaba, da madara, ga lemon abarba da lemon zaqi da ginger data masa, Khaleefa yaso yayi miskilanci yaqi ci,amma inaaaaa wane shi, abincin kwararru bai isa kauda masa kai ba.



Zama yayi yana wani babbata rai, ya fara cin abincin, wani irin gardi ne yake ji na ratsa shi, dan masifa sai dai yayi fada, kallon ta yayi, yana muzurai,


"Ina ruwa? Ko ahaka zanci ina shaqewa?"


"Yi hakuri ga lemo dana hada maka nan,"


Tsiyaya masa ta fara ya wani daki table din,


"Ruwa na ce maki ba wannan ba, kina gani yana shaqe ni ba zaki yi sauri ba?"



A kidime ta wuce dakko masa ruwa tana hawaye, meye abun fada, ga cuscus nan na ta shigewa, amma dan zalinci sai ya zabure ta haka.


Tana dawowa da ruwa taga jug empty, sai muzurai yake,



"Dakko ruwa ne kawai zai sa ki dade har mutum ya galabaita kisa shi shan abinda bai niyya ba, ke fa kina sani hayaniya, tinda na hadu dake na zama me yawan surutu,ki kiyaye abinda zai sani magana, in ba haka ba ranki zai mummunan ba......"



Wata arniyar gyaza ya sake, alamar qoshi ya tabbatar masa, ita dai bata gama gane komai ba, abincin ba dadi ne? Bai qoshi ba haka ya tura? Kwata2 bata gane komai ba, fatan ta dai ya daina wannan daukan zafin, tinda ba abinda ta masa sai alkhairi.



Tana nan tsaye tana tinani ya wuce ta, wanka ya shiga ya fito, isha'i ake ta kira a unguwar tasu, abinci ta dauka da niyyar kai wa Baba Adamu, ta saka hijabin ta qato har qasa abinci na qasan hijabin, tana fitowa daga kitchen ta gan shi ya dora qafa daya kan daya da remote a hannu, ya sauya wannan tasha ta rawa ya kai wannan ta kida, durqusawa tai kadan tace,


"Yah zan kai ma Baba mai gadi abinci,"


"Na kore shi,"


Zabura tai baya kadan,


"Yes na kore shi, ke zakina buden gate ki rufe, ko da wasa kar naji magana a gida, in an tambaye ki kice tafiya yayi ko na aike shi,"



Hawaye ne ya

Please Login or Register in order to submit comment