Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fada masa,


"Kaga ni ba zan hana ka aure ba, wa ce ce ni? Wane matsayi na ke da shi a wajen ka? Daga biya ma kai buqata? Ni ba sai ka biyani ba,nima na gani ina so, so kawai in kaje kaga amarya bata maka ba zaka iya dawowa nan, ko da yaushe qofa bude take a wajen ka, haka zalika koda ta maka in kaji kwadayin zuwa ka sha madara zaka iya zuwa nan, baka da case,"


Bai musa mata ba, kuma bai amsa mata ba, wanka ya shiga,biyu har ta gota, alwala ya yo, ya fara sallolin da bai ba, yana idarwa tana kwance daidai tana kallon shi, ya kula in bai da gaske ba ba zata barshi zuwa ko ina ba,


"Ai ka bari kaci abinci ko?"


"No thanks zani gida,qanne na na san sun zo, nemana da zasuyi tayi ne zai tabbatar ma da mutan gidan mu ba gida na kwana. Ba, so sai wataran,"



Har bakin qofa ta raka shi, tana zuba masa salon karuwancin ta.



*******************






"Gaskiya amarya ki fito mana da angon nan naki haka, mun gaji da jira, tin dazu ko wayar shi ma ta daina shiga,"



Cikin jin kunya Aeeshaa ta sauke kai qasa,


"Adda Hussai ni ina ni ina boye babban mutum kamar Yah khakeefa, na san aiki ne dai ya boye shi,"



Hassana dake gefe tai murmushi, dan yanzu ta sauke komai a ran ta, tin bayan zuwan 'Yan uwan nata da suka bata shawarwari, da kuma nuna mata rashin dacewar su ma kwata2 da Khaleefa, suka bata shawarar ta yi hakuri, ta tsananta addu'a inshaa Allah mijin ta na nunawa sa'a na nan tafe, sun yi ta bata misalai kala2 kafin zuciyar ta ta aminga da bayann su.



Qarar motar shi ce ta sa Balqis miqewa da kyar tana tura tsohon cikn ta,


"Sai na riga ku, dan na gane qarar motar shi har na gaji,"


"Taka da sauri Iya beji, Allah ya sa kije ya gwasale ki, kin san halin shi ai, ba a iya masa ya dangin gidan maza,"



"Habaa kar ki masa mummunan zato, muna kyautata wa 'yan uwan mu zato, yanzu mu dade bamu ga juna ba haka ya gwasale ni?


Miqewa tayi da kyar da qaton cikin ta a gaba, ta nufi waje, rufe mota yayi dauke da tarkacen shi a hannu, ya nufi cikin gida, cikin zumudi ta tarbe shi,


"Yah Khaleefa barka da dawowa, mun dade muna ta jiran ka, sai yanzu ka dawo, nayi missing din ka sosai,"


"Ah Balqis ya kk? Ya mai gidan? Sannun ku da zuwa, bari na dan huta a gajiye nake,"



"Muna lfy Yah, ban so hakan ba, na so mu zauna mu yi hirar yaushe gamo,"


Murmushi ya mata sannan ya yi gaba, ba tare da yace komai ba.


Dariyar su Hussai taji a bayan ta, aiko nan da nan ta hau,su kuma cike da tsokana suka maimaita me Khaleefa ya fada,

"Ah Balqis, ya kk? Ya mai gidan, bari na dan huta a gajiye nake,"


A tare suka kwashe da dariya, banda Aeeshaa da take murmushi, da kuma Balqis da ta cika tayi famm.


Bata kula su ba ta wuce bangaren Hajja, kayan lefe ne a qasa Hajja na dagawa tana ajewa,tana ganin su kuwa ta manta da haushin su Hassana, cikin fara'a ta qarasa ta zauna daf da Hajja.



"Hajja ba ko gayya,abun 'yar haka ne ma?"


"Na so kiran ku sai na manta na bar wayata daki, shine nake ta roqon Allah ya kawon wani a cikin ku, sai a kira mutan gidan suga lefe, abinda babu sai a fada a saka,"


"Hajja hoo, wannan kaya haka meye babu, ai komai sai son barka, ni fa tinda aka fara maganar bikin nan banji kuna maganar Aunty khadeeja ba, ko ita ba ita a harkar ne?"



"Bar wannan baqauyiyar,ko wa ya fada mata ana kunyar dan fari oho, ni da nake da namiji ma, hirar mu muke sha, da auren baban ku ni na tsaya nayi komai, amma ita wai kunyar diyar fari take, diyar fari ai abokiyar hirace,abokiyar shawara; abokiyar farin ciki da koka baqin ciki,ita ta sani, ba abinda ba zan ma Aeeshaa ba tinda takwara ta ce,"


"Wannan gaskiya ne,mun shaida,dan baki hada ta da kowa ba,"



Inji cewar Hussai da ta shigo, tare da Aeeshaa da Hassana,Aeeshaa na ganin kayan tasan na lefe ne dan haka ta gudu daki, dariya sukai ta mata, dan itama akwai kunya.


"Amma Hajja banga turaren da nake matuqar so ba, wanda kk sai min zuwan ki Hajji na qarshe, har yanzu ko saudiya naji za aje sai na bada sautun shi,"

"Ohhh haka ne abun, ni ai ba turare aka ban ba, tashi ka fiya naci aka ba wa Mine, sai jallabiyya da aka ban, meye sunan turaren?"


"Ni da ke daya ne? Ni ce qarama dole aban tsaraba tafi taki, sunan shi Sirrati, Arebian ne, ya hadu matuqa, suna shigen qamshi da lailatussahrah,"


"Ai kuwa sai an nemo shi, ko sautu sai a bayar,"


"Ohh yaran zamani, wato kun yaba turaren, nima ba a barni a baya ba, sai an siyo dani,"


Dariya sukai, a haka suka ci gaba da kawo abubuwan gayu da qamshi wanda ba a saka ba, sun kira 'yab uwan su dan ganin lefe, anyi2 Umma tazo taqi, ta turo Ameena da Abdul.


Baban su sabeer har Katsina ya je ya kai masu katin daurin auren Aeeshaa da Khaleefa, sunyi kurna sosai, na nuna masu mahimmancin su, sun kuma yi alqawarin ziyartar bikin.



*********************






Sauran kwana uku biki, har yau ango da amarya basu zauna waje daya sun tattauna ba da sunan zasu zauna a inuwa daya nan da wasu kwanaki, kullum sai dai su hadu a kan hanya, General ya ma Khaleefa umarni yau ya je bangaren Ummeen su Sabeer ya gana da Amaryar shi, kar kuma yaji ance bai je ba.


A yau din ne mutan Kt suka iso, mata uku, namiji daya, wanda yake shine Yayan mahaifin Aeeshaa, ta yi kuka sosai da kuma murnar ganin shi, yana matuqar kama da mahaifin ta, matan shi masu kirki, kamar su goya ta dan murnar ganin ta,sun kawo mata tsaraba kala2, wanda yake namu na mata sai suka damqa shi hannun Umman Sabeer, yamma nayi Uncle din ta ya dau matan shi suka koma gidan su Aeeshaan, can zasu sauka, dik da cewar Hajja taso su zauna anan, a cewar ta, in Umman taga an barta ita daya ta zo harkar bikin dan dole ai.


**********************








Khaleefa ke ta tinanin ya zai yaje bangaren ummeen su Sabeer zance da wannan yarinyar da baifi ya aike ta kira masa budurwa ba, ga shi Rebecca sai waya take masa, dan yau kwata2 bai fita ba, 'yan kwanakin nan ko laptop bai cika dauka ba, dan ya samu mace ba sadakin kowa, ya more ya kama gaban shi.

Turaren shi ya qarasa fesawa, dan so yake daya gan ta ya wuce wajen beccan shi.



Hussaina ce ke tsarawa Aeeshaa kwalliya, kamar yau za a kaita dakin ta, dik dan Khaleefa ya gani ya yaba, ta tsaya sosai ba dan komai ba sai dan Balqis da ke zaune tana miqo kayayyakin, yanda ta ke zumudi kai kace wani auren soyayya ake shiryawa.



Simple make up suka mata, amma fuskar ta sai sheqi take dan kyau,hijabi ta dakko zata saka, har suna hada baki wajen fadin,


"Habaaa yarinya ai ko a riga aka haife ki ba zaki saka hijab dinnan ba,"


Dariya sukai dika, sannan Balqis ta yafa mata mayafi kalar kayan ta


"Adda a haka zanje?"


"Wataran ma ba kaya zak yawo a gaban shi,"

Duka Hassana ta kai ma Hussai.


"Babbar banza kawai,"


Cikin jin kunya ta sinqe hijabin ta a jikin ta, tana zuba gaban Parlourn ta warware ta saka, a ranta tace,


'Ina na isa yawo a gaban wannan mayunwacin matan da wannan shigar, inaaa Ya Allah ka taimakeni, ni tsoro ma yake ban'


"In bazaki shigo ba ki fadan ina da abin yi,"


Da sauri ta shiga ta samu waje ta zauna nesa da shi, a takure, cike da jin tsoron shi.


'Ji wannan ko meye haka taje yi? An fada mata kowacce mace nake bi oho?'

(Yo ba gwanda ita ba ma, kai da ke shiga ramin shaddar kasuwa dan rainin wayo kawai😏)


Shiru sukai,ba mai cewa komai, a qashin gaskiya turaren ta ya masa dadi, ba kadan ba kuwa amma dan baqin hali ya hana ya yaba ko da kwalliyar ta ta ne ma.


Karkacewa yayi ya zaro kudi masu yawa, da gani zasu kai dubu dari ko sama, wurgawa yayi a gaban ta.


"Ga shi nan na san wataqila ace na bada, dan ku mata akwai ku da bidi'a baku tinanin ya aka samo kudi amma kuna son kashe su,"


Wani kallo ta masa, sannan ta tura kudin har gaban shi da hannun ta.


"Kar ka damu Yah, ai ba kai ka nemi aure na ba dama, kar ka manta matar sadaka ce ni, baka ni akai kyauta,ba mai buqatar kudin ka,"



Cike da mamaki, ya kalle ta, itan ma shi take kallo, tana jin tsoron shi yes, amma ba ta daukan wulaqanci musamman akan abinda bata roqa ba.


Miqewa yayi, cikin fushi, ya ja hannun ta da qarfi ya matse, dole ta sa ta miqewa tsaye dan azaba, wani irin kallo yake mata na tsantsar tsana da jin zafin rashin kunyar da ta masa, lallai yarinyar nan daga ta gan shi ba kaya shiyasa take qoqarin fara kawo masa raini?



Gyaran murya suka ji daga bayan su, cikin mamakin ta kuwa Sabeer ta gani, da qarfi ta fizge hannun ta ta gudu bayan shi tana kuka, kallon kallo sukai da Khaleefa,kafin Khaleefa yayi qwafa ya fice.


Juyawa Sabeer yayi, ya na son bata hakuri, amma qamshin ta, da kyaun ta suna fizgar shi, idon ta rufe, a hankali ya taka ya bar wajen.


Bude ido tayi tare da share hawayen ta, ta bude baki zatai magana kenan taga ba kowa a wajen,

"Ina Yah sabeer? Ko dai gizo yake man? Me ye zai sa yamin gizo to? Yah Sabeerrr.............





*ku taya ta nemo Sabeer pls, tana cikamin kunne*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼










*BY HAERMEEBRAERH*








Page 8:







Duba shi ta shiga yi, idan ta hawaye, yau so take ya fada mata me ta mishi yake gudun ta, koba komai shi kadai ta sani ta saba da shi, shi take jin zata iya sharing komai da shi vataji nauyi ko kunya ba, bata sani ba wataqila laifi ta masa shiyasa yake gudun ta.


Qofar dakin shi taje, tai ta kwankwasawa, yana tsaye jikin qofar, a hankali ya saka key, shiru ta danyi, dan taji motsin saka key din, a zaton shi ta hakura ta tafi, da sauri ya murda ya bude, zai leqa ta, sukai gware, baya yayi, yana taba wajen, itan ma haka, wayancewa yayi da,


"Me qaton kai kawai, ji yanda kk sa na bige,"


"Yah ni da kai an ga mai qaton kai ai, Yah Sabeer me nama ne, in wani laifi na maka dan Allah ka yi hakuri ka yafe min na tuba ba zan sake ba, ba zan sake makamancin shi ba ma ko mene ne balle nayi irin shi, ka daina guduna, ka sauya wajen aiki, for only god knw why, amma zaka tafi ko sallama,ina ta bin ka ina kiran sunan ka haka ka fice baka tsaya ba,nice baka son gani ko?"


Tana maganar ne cike da zubar hawaye, kukan ta na qona masa zuciya, baya son ganin koda bacin ran ta ne balle kukan ta, yana son ya bata amsa amma me zai ce mata? Ina son ki? So nake ni na aure ki ba Khaleefa ba? Inaaa ba zai taba yuwa ba.


"Look dear, ni ba wai gudun ki nake ba, yanayin aiki ne haka, kuma ranar na san inna tsaya sai na makara ban tafi ba, in ban manta shagwabar ki ba kina qarama ko nan da can naje sai kinyi ta kuka, kina rikici, ko dake ban sani ba yanzu kin zama babba wataqila kin daina ko?"


Cikn wasa ya qarasa maganar tashi, itan ma murmushi tayi,


"Yah zauna na baka labarin abubuwan da suka faru da baka nan, kuma ina son ka ban shawara, akan Yah Khaleefa, akwai wani sirri nashi da ba na son fada, amma bana son abun, bana son mai yin abun, dan haka nake jin tsanar wannan auren namu, Yah dan Allah ka ban shawara ya zanyi?"


Gaba daya ya shagaltu da kallon ta, a dan watannin da yayi sai yaga ta qara kyau da girma, ga shi for the first time ya gan ta da kwalliya mai kyau haka, hannu tasa ta gaban idon shi,


"Yah magana nake fa,"


A dan firgice ya dauke kan shi, ya kalle ta again,


"Immm kin ga ko zamu bari nayi wanka na ci abinci, bana gane komai yanzu, muguwar yunwa nake ji, kin san ni da ci,"


🙄🙄"amma dai matar ka ta shiga uku, ko daga qafar girki na rana daya ba za ta samu ba,"


Tashi tayi ta na tafiya tana sanar da shi anjima zata dawo, su qarasa magana, ya amsa da to, ta koma wajen su Hajja, nan ta samu Hussai ta dakko kudin da Khaleefa ya wurga mata, suna ta mata dariya, wai amaryar qauye an mata kyauta ta ajiye, ango ya tafi tabiyo sahu ta dauka taga babu, tana son tai kuka, yaqe ta musu ta shuge daki.


Yanda auren nan ke qaratowa haka zuciyar ta ke tsananta bugawa, Sabeer ya tare a gidan Umma, dan bai ma sake komawa ba balle ta gan shi tace zasuyi magana, ba zai juri kallon ta ba, bai san me zai iya aikatawa ba da wanda ba zai iya aikatawa ba indai a gaban ta ne.



*********************





"My baby ina kk son tafiya ne wai? Gobe fa daurin auren ka, na sani in ka tafi ba zaka sake dawowa ba,ka bari na kwashi rabona mana plssssss"


Wani irin narkewa take a jikin shi, shi kuma yana lumshe ido,kamar wadda aka mintsina ta tashi, tambayar ta yayi


"Lfy?"


"Lfy qlou ina zuwa, zan dan qaro abin sha ne, naga wannan ya kusan qarewa kuma ina jin yunwa,"

Dan gidan ta madaidaici , amma fa mai shegen kyau, dan gaskiya da alama a qasar waje aka gano tsarin itama aka mata, ko kuma wasu masu basirar ne suka tsara gidan, iya haduwa da kyau ya hadu, wani Minister ya mata kyautar shi, amma yanzu basu tare.


Kukun ta ta yi ma umarnin ya hada masu abinci, ta lissafa masa abinda take son ya kawo masu, sanan ta bashi wata kwaya ya saka masu dika a abin sha, cikin murmushi da takun qasaita ta koma dakin, in da sabo kukun ya saba ba yau yake mata aiki ba.


"Hey babe, sorry na barka kai daya,"


"Ba komai, kamar wani baqo, come here,"


Takawa tai kamar mai tausayin qasa ta kwanta gefen shi, wasannin su suke, suna ta dariya, waya ta shiga masa, yana dubawa yaga Baba General ke kiran shi, dan guntun tsaki suka ja a tare, bai ji dadin yanda tai tsaki ba, dan ba hurumin ta bane, in shi yayi bai sa ta taya shi ba, wani mugun kallo ya mata for the first time.


"Meye naki na tsaki, ko zan iya sanin dalili?"

Kame2 ta fara,dan ganin wani irin kwarjini daya mata, nan take tsoron shi ya kama ta, inda inda ta fara, cikin tsawa ta fara mata magana,


"Kina jina ko, hurumin iyalina ba naki bane, ba ruwan ki da ya nake tare da su,in ina tare dake ina tare dake, in naga dama na je wajen su na tafi, kakana ne fa, kk masa tsaki, ko wayar ki ya kira?"


"Babe plsss kar ka min wannan fassarar,ni fa nayi tsaki ne kawai duba da yanda ranka ya baci, bana son abinda zai bata maka rai ne kawai,"


"Ba hurumin ki bane, ki san matsayin ki, this is my grandpa, ba abokin wasan ki bane, ki riqe wannan,"


"Yes babe, and i am so sorry, i will make it up to u, plss don't be angry, smile for me, plsss,"



Yau fa taga kalar Khaleefa da bata san yana da ita bama, ko alamar ya sakko bai nuna mata ba, kayan shi ya fara zurawa,cikin damuwa ta taso zata hana shi ya mata wani kallo ta koma ta zauna, me wannan yake nifi ne, zata sa a hada wannan uban abincin a banza ne? Kuma yau wai har ita namiji kema wannan kallon da rashin mutuncin bata ci....... tab di jam akwai aiki gaban ta kenan, Khaleefa bai jiqu da qaunar ta ba,( lallai vata san waye Khaleefa bane, tama samu yana yi da ita ne)


Akan idon ta ya gama shiri ya fice ba ko magana.


Ranta in yayi dubu ya baci kuwa, cikin bacin rai,ta yi ma wani saurayin ta waya, na ta gayyace shi su dora abinda basuyi da Khaleefa ba, sigari kuwa ta sha ya kusa biyar, daga qarshe Shisha ta dakko ta fara zuqa( mata da maza ku kiyayi shishar nan, illa take ma bayyani ba a boye ba, wanda ke son rayuwar shi da lfy a ciki; bai wahala ba bai wahalar da dangi ba ya guje ta)



A zaune suke a kan kujeru suna ta hira, suna dariya, ga 'yan uwan su harda na Yola sun zo, gobe daurin aure, sai bayan an daura ne za a yi gagarumar dinner, wadda Baba Genera y gayyaci manya2n qasar nan, za ayi dinner din ne mata da maza, kowa zai zo da iyalan shi dika, domin taya Baba General murna.


Aeeshaa na gefe in an abun dariya ta murmusa, abinda ke damun ta ba kadan bane, ga rashin Umman ta, ga miji dan iska, yanzu ace Umman ta ta jata ajiki ai da ta sanar mata, da kunya ta ce ma Hajja jikan ta babba dan iska ne, ta ina ma zata fara mara vayani?


Wuce su yazo yi Balqis ta gaida shi, yi yayi kamar bai ji ba ya shige, bushewa da dariya sukai, babbar diyar Uncle din Aeeshaa da tazo itama Fateema ce ta dakatar dasu,


"Kuka sani ko ango ance ya kawo kudin dinner ne account yayi qasa? Kun san fa maza da biki ya qarato da sun fara fada da kowa kenan 😆"


Nan da nan kowa ya sa dariya har Bilqis data bata rai, kowa ya ci gaba da fadin albarkacin bakin shi.


"Gani,"

Kallo Baba General ya bishi da shi, cikin takaici, sannan ya nisa yace,



"Anya mun yi wa Aeeshaa adalci in muka aura mata kai? Anya ba zamuyi dana sanin wanan auren ba? Daga ina kk? Jiya ina sane da baka kwana gidannan ba,na kira ka baka ga damar amsa wa ba, ba tarbiyya ka shigo min ba sallama, sannan kace min gaka, wazaka nunawa baqar zuciya? Nine fa na haifi uban ka, ka ko san ko baban ka a wajena ya gaji zuciya bare kai dorin dosano,"



"Shifa wannan fadace2n da gore2n ne baya so, ai bashi yace a haife shi a nan din ba"


Qunquni yake,amma General yaji shi tsaf, Khaleefa bai aune ba bai san daga ina hannun ya biyo ba yaji wani makakken mari a kuncin shi na hagu,gabadaya parlourn sai da ya dauka, Aeeshaa da ta shigo dan komawa daki qamewa tayi, jikar tsohon soja kenan, hannun ta a rufe da bakin ta,cikin ta ne ya bada wata irin qara mai sauti, da sauri ta bar wajen,ta shige daki.


"KAII KHALEEFA kar kaga ina daga maka qafa, ina bin ka da lalama, dik wani qunci da baqin hali da rashin kunya tare da qin 'yan uwan ka da kk akan idona yake, rashin kunyar ka har ta kai ina magana kana man qunquni, kuma kana yi wato yanda zanji sabida baka da kunya ko? To ka sani daga yau sai yau, in na sake ganin rashin da'a a tare da kai ba a gabana ba ko a gaban waye sai na mummunan saba maka, tashi ka ban waje, kuma kar ka sake ka fita ko ina, gobe auren ka, mara mutunci kawai,"



Khaleefa wanda bakin shi yake a sake, dan mamaki, da tsoron ganin yanayi Baba General wanda tinda yake bai taba ganin bacin rai irin haka a fuskar shi ba, da saurin gaske ya zuba guiwowin shi a qasa yana bama Baba General hakuri,da kyar ya hakura dai da Hajja ta fito ta sake bashi hakuri sannan ya hakura.



Abu dayane a ran Khaleefa yanzu; fansar marin nan, akan Aeeshaa zata fada, tinda ta ga sanda aka mare shi, kuma a sanadin auren aka mare shi, dan haka ya ma matsu a daura masu auren............







*Mugu ta Allah ba taka ba to*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼






*BY HAERMEEBRAERH*







Page 6:








A duqe take kan guiwowin ta, idon ta a rufe, bakin ta na rawa, hawaye face2 a fuskar ta, dik wanda ya gan ta zai zaci gamo tayi d fatalwa, ko aljanu, tsabar tsoron dake kan fuskar ta, babu wanda bai san iskanci ba, tabbas Khaleefa kura ce a cikin fatar rago, ba qaramin dan basaja bane, a zaton da take masa, tsabar nagartar shi da kirkin shine yasa baya son hayaniya, tsoron Allah ne yasa baya son kula matan da ba muharraman shi ba, sannan yana tsoron Allah ne akan kalaman shi kar ya fadi sabon Allah shi yake hana shi yawan magana, ashe yana boye mugayen halayen shi ne.


Gani tayi ya gogr hannun shi da tissue ya tako inda take, d sauri ta fara qoqarin tashi ta gudu, amma santsin qasan wajen da yanayin rigar da tasa mai santsi sai zamewa take, Allah2 take wani ya shigo saboda ihun da tai,amma shiru, matsalar irin gidajen nan masu manyan qofofi kenan,Maman su na can parlour, zai wahala taji tinda babban parlour ne, qara zata sake saki, kafin ta kwalla ya damqe mata baki.


Magana yake son yayi, amma bai ma san ta ina zai fara ba, cikin zare ido, da tsoratar da ita ya fara magana,


"Abinda kk gani ya tsaya a tsakanin mu,in kuma kina ganin ba zai tsaya a tsakanin mu ba sai kin fada ma wani,ni ba zan hana ki ba, tinda ba tare dake nake yawo ba, amma ki kuka da kan ki, dik abinda ya same ki, da mahaifiyar ki dda qannen ki, je ki zaki iya tafiya, ba zan iya dogon surutu ba,"



Tsoron shi ne mai tsanani a tare da ita, kuma shima ya fuskanci hakan, dan haka ya qara daure fuska, ya nuna mata bai damu ba, in taga zata iya risking rayuwar ahalin ta, cikin sauri ta qoqarta fita, da sauri ya bi bayan ta ya fixgo ta,


"Me ma ya kawo ki waje na, bayan kin gaishe ni ban amsa ba shine dan naci sai kin biyo ni,"

Bakin ta na rawa sosai ta furta,


"Baaabbbaa Geeegggeneral keee kiran ka,"


"Shit ! Me zan yiwa tsohon nan ne? Ya qaqaban auren da ban so, ya sani zullumi da zancen nake kwana nake tashi, kiran na meye yanzu kuma, me kk ji yana magana akai?"


"Baan san ni ba nima,"


"To goge idon ki, kuma ki nutsu, kafin ki jawon magana wajen tsohon can, dan na kula bai hada ki da kowa ba, "


Da saurin ta kuwa ta fara gyara fuskar ta, da dikkan wani abu da ke buqatar gyara a jikin ta, yaji dadin yanda take tsoron shi, hakan zai bashi damar yin abinda ya so kenan, da kyau.



Komawa ciki yayi, dan bai isa fita a haka ba, dole sai ya dan watsa ruwa, ita kuwa data fita a parlourn shi, bata ga kowa ba, ta godewa Allah, dan bata son wani ya tambaye ta me ya faru.


Tap din flowers ta nufa,ta kunna tana ta watsawa fuskar ta ruwa, tana koka me ta gani, wannan abu ba zai taba barin kan ta ya huta ba, bata san sanda zata daina hango wannan mummunan gamon ba,wataqila sai bayan ran ta, bai kula da ita ba sanda ya wuce, tana ganin shi ta manne jikin queen of the night dake shuke a kusa da wajen da take saye, har sai da ya wuce, qamshin turaren shi mai sanyi da dadi ta shaqa, dazu kafin suyi mummuna gamon nan, ta yaba da qamshin, amma yanzu qarni da wari yake mata, da sauri ta sake splashing ruwa a fuskar ta, ta shaqi iskar wajen, idon ta rufe, sai da taji hankalin ta ya kwanta sannan ta fara komawa ciki.



"Tinda gata ta zo kawai ku fara komai na shirye2n bikin, ni me zance, yarinyar da na ninka shekarun ta amma wai ita kuke son hada ni da ita, in ma nace bana so baji zakuyi ba, ko ra'yin ta na tabbata bakuji ba, shekara nawa a tsakani, tin tana aji biyar baku nemi

Please Login or Register in order to submit comment