Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufe, sai dai ba zan maki alqawari akan kowacce mace ba, yanzu lokaci ne na jin dadin mu ko ya kk ce?"



Hawayen farin ciki ne ke gangaro mata, ashe da rabon ta zata ji kalamai masu nutsar da zuciya, ashe bata MAKARO BA, juyawa tayi ta qanqame shi sosai, tana murmushi,tare da godiya.


"Yah Sabeer na gode sosai, inshaa Allah zan ci gaba da son ka, da kula da kai, da jiyar da jai dadi fiye da yanda kk tinanin ji, zan saka farin ciki, zan maye maka gurbin kadaicin da ka yi a baya na rashi na, har sai ka ji kamar mun dade muna tare, INA SON KA YA SABEER"



Wani abu ne mai sanyi da dadi, ya daki zuciyar shi, shima rungume ta yayi sosai, suka ci gaba da romancing juna su, daga baya suka yi wanka suka yi nafila sannan suka kwanta baccin gajiya.




*********************




Ammar yaso ya kwana da amaryar shi a daren su na farko da aure amma hakan bai samu ba, sai a daren washegarin ranar da su Bilqis suka koma.


Ammar yayi mamakin samun Hassana a cikakkiyar budurwa, saboda kwata2 bai sawa ran shi hakan ba, kasancewar ta mai Degree, kuma wadda ta dade va aure, a zaton shi yanda zamani ya lalace ba lallai ya samu budurci wajen yar sakandire ba, a gaskiya ya jinjina na iyayen ta ba kadan ba.


Manna ta yayi a jikin shi, yana shafa bayan ta, tare da lallashin ta, sai rada mata addu'o'in alkhairi yake da godiya, dadi tin daga fatar ta zuwa tsokar jikin ta da jijiyoyin ta zusa qashi da bargon ta take jin kalaman shi, sunsunar qirjin shi take tana jin dadin qamshin jikin shi, ashe zata ga wannan ranar? A gaskiya wani jinkirin alkhairi ne.



Amare sun sha bacci mai dadi, inda washegari suka hada kai da mazannsu dannsamar wa kan su abin karyawa, a tare suka gabatar d komai, Hassana sai shagwaba ake zubawa, Ammar kamar ya maida ta ciki.


Bangaren Hadiza da Sabeer sun tashi cikin gamsuwa da juja su da nishadi da farin cikin kasancewar su miji d mata, amma sun damu da rashin lafiyar da ta sami Khaleefa matuqa, dan Hadiza kawai ta hakura ne, amma taso a danqara da safen nan.


Da ya fita masjid dan yin sallah, bayan an idar ya dau hanyar gidan su, yana mota yana tinani, wa zai tinkara da wannan matsalar? Shi dai ba zai iya fada ma maman shi ko baban shi ba, balle Baba General, akwai kunya.



'Hajja, itace mafitar mu a wannan lamarin'


Murmushi yayi, ya qara saurin motar tare da godewa Allah da ya bar masu wannan tsohuwa da ran ta da lafiyar ta.



Akan sallaya ya isko ta,tashi yayi yace zai dawo, ya isa bangaren Maman shi dan su gaisa, nan ya tadda Bilqis Hamdiyya da Hussaina sun koma da sassafe.


Bayan sun gaisa da Maman shi, suka hau hira da Bilqis, taji dadin hakan sosai, dan ita mace ce mai son dangin ta matuqa, Ahmad na hannun ta tana bashi abincin yara,ga nata diyan a gefe, yaji dadi sosai, Ahmad sai dariya yake masa, nan ya dauke shi, yana masa wasa, da zai tafi da kyar Ahmad ya yarda ya koma wajen Maman shi.




Abinci ya tarar Hajja na ci, nan ya zauna ya sa hannu suka ci gaba da ci, bayanin komai ya mata, ta tsaya cak, tanakallon shi, maganar na shigar ya,


"Tashi muje mu dawo, yanzun nan,"



"Ina zamu? Inda zaka samu maganin matsalar ka,"


Da sauri ya kwashi keys din shi ya bita qofar dakin ta, hijab ta saka suka fita, ya dau hanya sai gwammaja, shagon DUBAI, nan suka je ta masu bayanin matsalar shi, yana ta wani babbasarwa, aka mai hadin magunguna ya aje ta gida yana ta mata godiya,




"Allah ya muku albarka dikan ku, ban da kamar ku,na godewa Allah daya sa ban zama uwar banza ba, surukar banza kuma kakar banza ba,ka kula da kan ka ka kula da iyalan ka da haqqin Allah, maza jeka gida kan tace na kwace miji ran girkin ta,"



Dariya yayi ya boye magungunan ya dau hanyar gidan shi.........





*Wassshhh na so kammalawa a wannan page din, amma aradu na gaji, yau banda appetite din rubutu🤣*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼








*BY HAERMEEBRAERH*









Page 31:







Bayn ya aje motar ya wuce masjid a qafa dan qarin samun lada.

Sai da yayi sallah ya koma motar shi, ya bude magungunan nn ya sha wanda zai iya a lokacin, ya boye sauran yakoma ciki,Hadiza an sha wankan qananan kaya, dik da bata dawani shape sosai ba lifi sin mata kyau, sai zabga qamshi ta ke, kwantawa tai a jikin shi, tana kukan shagwaba, wai ya dade, hakuri ya fra bata, sai qara wani zamewa take tana goga qirjin ta a nashi, Khaleefa fa dama abinda yake so wajen mace kenan, lalubo bakin ta yayi suka fara kissing junan su, suka dire a kujera tana saman cinyar shi,


"Baby ina kaje?"

"Daga gidan Hajja nake,naje naga Ahmad, ba zan iya kwana ban gan shi ba,"


"Humm lallai ne, ni kuma kasan me? Inna gan shi sai naji na tsani kai na kwata2, na tsani rayuwar da na aikata a baya, wannan sakamakon abinda muka shika ne,ga girbi nan munyi, ina tsoron sanda zai girma yaji wannan mummunan labarin"



Da qarfi ake buga gidan su, Khaleefa aje ta yayi a gefe cikin kulawa,yayi mata kiss a lips a hankali yace yana zuwa.



Bayan ya fita ya ga mai gadin su yana fada da wata, ta lullube kan ta ko ta ina, ba dan ya san ta ba ba zai gane wace ce ba.


Tana ganin shi ta tafi d gudu ta fada jikin shi,


"Sugar ka taimake ni, na shiga uku tinda nake ban taba shiga tashin hankali irin wannan ba, dan Allah ka taimaka min,"


"Muje ciki, amma sake ni, dan yanzu ba Khaleefan d kk sani bane a da, yanzu iya halal dina na tsaya,kuma na sake aure,ko me kk gani ciki bana son ki samin baki a lamarina, wajen zama kk nema muje zan baki,"




Ciki suka shiga,tana neman taimako ina ruwan ta da auren shi, ta rayu ma kawai shine babban burin ta,



Hadiza ce tsaye jikin window tana hango komai, kuma taji dadin yanda Khaleefa ya janye ta a jikin shi ya kora mata jawabi.



Suna isa ta sauna kamar batai ba.


"Babe ku zauna ina zuwa, bana son inna shiga naji wani damuwa,kawo mata abinci d ruwan sha,"


Dan dik wanda ya gan ta ya ga a yunwace take,



Bayan ta ci abinci ya dawo, ya zauna, cike da nutsuwa da kamala,sannan ya tambaye ta me ya faru, kuka ta sake, sai da tayi kuka mai isar ta ta fara bashi labari,



"Bayan sojojin nan sin tafi da kai, ina zaune a club ina jimami, ina ta zuqar sigari, ina korawa da wine, naga wani sanannen dan siyasa, yana ta kallo na, na dauke kai ban kula shi ba,guards din shi ya aiko su uku akan su nemi izini na naje mu kwana da shi,bayan na amince danaji maqudan kudin d ya furta zai ban nan d nan na amince, muka tafi,



Wani katafaren gidan shi dake garin na Abuja muka nufa, tin da nake ban taba ganin gida mai kyau irin shi ba dk yawo na a Nijeria, we had fun, sosai, a ranar da zan tafi yana ta min shagwabar bai so na tafi dan haka na tsaya nace in zai qara kudi me zai hana? Amma ya bari naje hotel din da nake na debo kayana, nan ya ban key din wata motar shi,naje n debo kayana na koma, nan na ci gaba da zama na watannin da ni kaina ban sani ba,muna sheqe ayar mu, kasan inyamuri d son kudi,amma banda shi,hannun shi a sake yake, dan haka mukai ta kashe kudi, ya bata ni d kudi sosai, watarana muna kwance da shi bayan kammala sex, ina ta busa sigari kamar yanda na saba after sex, ina gamawa na tashi domin watsa ruwa, sai naji jikin shi ya saki, na zaci bacci ne, nayi wanka na dawo na saka kayan bacci, kawai sai naga kamar bakin shi a sake baya numfashi, bayan na duba sosai sai naga,......😭😭😭ashe yaaaamuuutuuu😭😭😭"



"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ya mutu !!!"



Daga kai tayi cikin matsanancin kuka, Khaleefa da Hadiza sun kadu da wannan labarin,


"Shine fa na tattara, na rufe shi kamar yana bacci,na saka kayana, na dau akwati na, na kunna sigari na na fto kamar ba komai, motar da muka saba fita, na fita daga garin Abuja a daren, ashe labari ya bazu, ko da na dawo Kano qofar gidana cike yake da 'yan sanda da sojoji, kwana nayi na fita a motar na gudu, wasu ne suka kula da motar suka sanar da hukuma,tin daga nan nake gudu,bana can bana nan, dan Allah Sugar ka taimaken, in aka kamani kasheni za ai, ni garin mu ma zan koma, in komai ya lafa,"



"Kar ki damu, zaki zauna anan har na sama maki wajen da zaki koma,"


"In an isa shegiya nake, wace karuwar ce zata sauna min a gida? Tabd jam, ai ba zata sabu ba bindiga a ruwa, tashi zaki yanda kk rarrafo ki fice, yau auren mu kwana biyu ba zaki rusan jin dadina ba, rannan kin kirani qaramar karuwa, naji yanzu jice da shi na har abada mutu ka raba,ke babbar karuwa ina connections din ki, da ba zasu wanke ki ba yanzu?"mu sauna dake muma ki kashe mu?"


Sai ga Becca an kwanta a qasa ana ba Hadiza hakuri, Khaleefa ne ya daka ma Hadiza tsawa,yace kar ta sake magana,shiru tai ranta bace,aiko indai zata zauna ita gida zata shiga,in yaso sanda ta tafi ta koma.


"Gidan mu zan je sai ku qarata dama mai hali baya fasawa ai,"


Wani mari Khaleefa ya bata, d sauri ta dafe kuncin ta, hawaye na tsiyaya,


"Ni ka mara?"



Daburcewa yayi,ya bita zai kamo ta ta ruga dakin su d gudu, binta yayi a baya, suna shiga ya ja ta ya matse da qarfi,tana ta rusa kuka tana tafiya za tai,kuma sai ta fada Hajja ya aje karuwa mai kisan kai.


"🗣👂🏻 ke ki nutsu,kina ta hauka ni mahaukacin ina ne zan barta anan? Hukuma ta san na bata kariya ni kaina kama ni za ai, ki ci gaba da bori ki je gida, zan kira police a wuce da ita yanzu, ai inna nuna bana tare da ita gaba sa tai,"


Kissing din shi ta hau yi,sannan ta sake shi ta saka doguwar riga, ta sa mayafi tana ta masifa ta fice, yana bata hakuri,


"Sugar kayi hakuri na sa matar ka ta bar gida,"



"Ba komai, ina zuwa,"


Daki yaje ya samu no Sabeer yace ya tura masa kowacce no ta bokan shi masu damara, nan d nan ya tura masa, through message ya fada masu komai, sannan yace su zo ga address su wuce da ita,yana saune yana tura saqon ba tare da ta gani na.


Hira sike tayi, ta tashi ta rage kayan jikin ta, sai da Khaleefa yayi yaqi sosai d zuciyar shi wajen danne kwadayin daya taso masa, Rebecca ta hadu matuqa, ga kalar fatar ta mai kyau,magrib aka kira yace bari yaje yayi sallah, yana tashi ana buga gate,'yan sanda ne suka zagaye gidan ko ta ina,Khaleefa leqawa yayi dayaga sune ya ce mata yana zuwa.


Taso ta leqa taga waye, sai tayi tinanin ko Hadiza ce? Koma waye yau dai sai ta dan dana Khaleefa ta dade bata yi komai ba,yau ta samu abinci da wajen kwana ai ta samu dan tayin kwana ko?



Da qarfi aka bude qofar 'yan sanda suka bayyana, ihu ta saka,ta fara zagin Khaleefa yan maqale da hannayen shi, ko a gikin shi,suka fice da ita, sai fadin take


"Bani na kashe shi ba, bani bace, ya riga ya mutu kafin na bar gidan, Allah bani bace,"




Ba wanda ya kula ta haka suka tankada qeyar ta cikin motar kyauta.



Hadiza na waje,tana jiran su fice ta koma gidan ta, tana shiga ta maqalqale Khaleefa kamar za a kwace mata shi tana sauke ajiyar zuciya.



Bayan sun yi sallah suka yi karatun qur'ani da azkar, kafin su gama an kira isha'i,sallah sukai suka ci abincin da bai ci ba tinda ya dawo.


Sannan suka yi wanka sukai brush, Hadiza sarkin qalqale jiki aka sha gayu, Khaleefa tin da Becca na nan maganin nan ya fara masa aiki, kafin su gama komai suje bacci ya gama jiquwa a jikin shi, a ranar dai Hadiza ta sha mamaki matuqa,dan ko a baya bata taba jin Khaleefa haka ba.


Sai santi take zubawa, abinda khaleefa ke so kenan, mace ta yaba kwazon shi, ta nuna masa shi din ba kamar shi,ai kuwa ranar shi ya sama macen,dan kuwa washegari shi ya gyara gida, yayi girki, Hadiza na maqale dik inda yayi, tana nuna masa ita fa yayi ya gama ya sammata,sai yayi dariya yace me zai sammata? Tace abun nannnn, a haka zasuyi ta dariya suna hira cikn so da qauna.



Sai da sukai wata biyu Maman khaleefa ta bada Ahmad da akaiwa Yayen dole aka dawo da dashi, ta roqe su da su basu shi ya koma wajen ta da zama,Khaleefa yaqi, amma Hadiza ta ma Mama alqawarin zasu na kawo shi lokaci zuwa lokaci yana zama da ita.



***********************




Ameerah na gidan Ummah, ta zama 'yammatan Umma, Sabeer kam yau yace zai je ya dakko diyar su tinda Umma ta murje ido ta hana su, zai aje kunya a gefe ya amshi 'yar shi, Aeeshaa na ta masa dariya, dan in yana fada wani dadi ke kama ta.


Ameenaa da Abdul ne suka je gaida su, inda suka tafi da Ameerah, tana shiga taga Sabeer da gudu ta sauka a jikin Abdul tana kiran


"Baabaa"


Sabeer ne ya daga ta sama, yana kissing din ta suna ta dariya, abun gwanin dadi.



Sun jima suna hira,Aeeshaa na tsokanar Ameena da cewa waye saurayin ta ne itana da alama auren wuri za a mata, dan tana da girman jiki,


"Ni ban da saurayi Adda, na wa nake da za ai mganar aure na? Gaskiya ni sai na yi digiri nai digirgir,"


"Ba a gaban Umma ba yarin ya kin sani ai, ko jiya me tace maki?"



"Rabu da ita wasa take, kuma naga dai nice auta ai bazata so na bar ta ba da wuri,"


"Hummm a dai bar maganar har ki qara girma, amma aure da wuri wajib,"


Sai yamma suka tafi, bayan sun isa sukai waya da Aeeshaa,daga nan Umma ta karba,sukai ta hira, tana bata wasu daga cikin tips din da zasu qara mata zaman lfy d kuma ni'ima.


*********************



Bayan shekara biyu,Aeeshaa na dauke da ciki wata takwas, Hassana ta haifi 'yan biyu suma.mata, Hadiza har yanzu dai ba haihuwa, suna nan da Ahmad dai.


"Ni gaskiya sai naje suna,"



"Ni gaskiya ba zaki baaa,"



"Uhummmm plssss naaaa,"



"Uhummmm nooo naaaa,"



"Dan Allah Abban Ameerah ka barni naje ko a jirgi ne,"


"Ki haihu a hanya? Ni dai ki bari ki zauna ki ta aikin lada shawara ta kenan,"


Harar wasa ya jefa mata,tinawa yayi Ameerah na gidan Hajja, dan haka ya kama ta ya daga sama, a kan katafaren gadon su daua sha gyara ya aje ta,nan da nan ta gano shi, zillo ta hau yi zata sauka ya qi barin ta, salon daya fara mata ne ya sa ta manta da komai d kowa,dan walaqanci har ni danake lahe a bakin qofa, sai hakura nai d dakko maku rahoto na tafi ina kukan wulaqantani da Aeeshaa tayi, wai kan mage ya fita daga leda, yarinyar nan har ta iya sumbatar miji a gaban😭😭🤧🤧🤧Yaran zamani masu zamammiyar qeya...............





*Alhamdu lilLAAH this is the end of Aeesha's tory, Allah ya sa mun amfana da abubuwan da aka koyar a cikin wannan labarin, zan ji dadi matuqa innaji comments din ku akai, musamman akan abinda ke akan kan ki kk koya, thank u all for everything.*



*Haermeen Haermmaerg loves all her fans domin Allah* ❤






*Yahhhhhhh i am so ready for this wedding,hummmm in kuka ga yanda na ke doki kamar nice Sabeer, dan na kula yafi kowa son auren, ko akwai wanda ya fishi?*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment